Z E E Y A D – Page 51

[The Abandoned Prince]
*NA*
JIDDAH BINT MUHAMMAD
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
051…
_________Buɗe idanun ta da sukayi mata nauyi sosai ta fara, koh ina na jikin ta ciwo yakeyi mata, abubuwan da ya aikata mata cikin dare ne suka shiga yi mata playing a kwakwalwa,lumshe idanu tayi wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo mata.
Da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe zaune tanajin yadda ƙasan ta keyi mata zugi sosai duk da kuwa irin ruwan zafin da ya taimaka ta shiga a jiyan cikin dare.
Yaye bargon dake rufe da ita tayi tana sauƙo da ƙafafun ta ƙasa, da kyar ta iya yunƙurawa ta miƙe ta nufi bathroom.
Wanka tayi sosai ta sake gasa jikin ta, sai a sannan ta ɗan ji dama-dama sakamakon ruwan zafin da ta sake shiga.
Fitowa tayi ɗaure da wata ƴar guntun towel tare da zuwa ta zauna bakin mirror.
Hand-dryer ta ɗauka ta shiga busar da jiƙaƙƙen gashin kanta da ta wanko, sai da ta tabbata ya bushe tass kafin ta gyara shi tana parking ɗinsa a baya sai sheƙi da ƙamshi na musamman yake tayarwa.
Lotions masu kyau da ƙamshi ta shiga mulke jikin ta dashi, tana cikin hakanne ZEEYAD ya buɗo ƙofar ɗakin ya shigo bakin sa ɗauke da sallamar wanda iya le6en bakin sa ne kawai sukayi motsi.
Sadda kai ƙasa DEENAH tayi cike da jin kunƴa har ya ƙaraso yana dafa kujerar da take kai.
Ba tare da ta ɗago ɗin ba ta kai hannu ta ɗau deodorant ta shiga shafawa a jikin ta.
Ganin yayi shiru har wannan lokacin ne ya sanƴa ta ɗan ɗago da kanta tana kallon cikin mirror ɗin nan suka haɗa ido kafin kuma ta sake saurin maida kanta tana ɗan turo baki.
Hanci ya kai yana shinshinar daddaɗar ƙamshin gashin kanta, kafin kuma ya sumbace ta a wuya tare da yi mata raɗa a kunne yace “Good Morning Baby.”
Cikin rawar murya take faɗin “Please ɗan miƙa min Hijabin chan.”
Kallon ta yayi ta cikin mirror ɗin kafin yace “What Hijab?.”
“Gashi chan.”
“Ni ban gani ba” ya bata amsa.
Ɗan ɗagowa tayi ta kallesa kafin tace “Baka fah duba ba, idan ka juya bayan ka zaka ganshi.”
Cikin kallon ta yake faɗin “Maybe sai dai idan zaki tashi ki nuna min inda yake sai na ɗauko.”
Ɗan turo baki tayi cikin shagwa6e fuska tace “Please Abyaaad.”
Yadda tayi maganar cikin langwa6ar da kai ne yayi bala’in tafiya da imanin sa, hakan ya sanƴa shi sakin baki yana kallon ta.
Sadda kanta tayi tana wasa da ƴan yatsun hannayen ta.
Murmushi ZEEYAD yayi kafin ya bar wurin zuwa closet room ɗinsu, ganin ya tafi ne ya sanƴa ta saurin miƙewa tana zuwa inda Hijab ɗinta yake ta sanƴa shi kafin ta sake dawowa gaban mirror ɗin ta cigaba da kwalliyar ta.
Shi kuwa fito mata yayi da kayan da zata sanƴa a hannun sa, murmushi kawai yayi ganin sai wani 6o66oye jikin ta take, shi kuwa babu abinda bai ƙarewa kallo ba a daren jiya.
Ajiye mata kayan yayi kan bed kafin yace “Idan kin shirya YAZEED is waiting for you downstairs kizo a canza miki sabon bandage.”
Kai ta jinjina masa kawai, tana ganin ya fita ta miƙe tsaye ta taka zuwa bakin bed ta ɗau kayan da ya fito mata dashi ɗin.
Ba tare da ta cire Hijabin ba ta shiga shiryawa dan kuwa bata yarda koh yana la6e yana leƙen ta ba.
Cire Hijabin tayi tana nannaɗe shi, nan kuwa ta jiyo muryar shi a bayan ta yana faɗin “Seriously?.”
Juyowa tayi nan ta ganshi ya haɗe girar sama da ta ƙasa yayi folding hannaye a ƙirji yana kallon ta.
Dama ta sani yana nan la6e yana leƙen ta, murmushi tayi kawai tana zuwa ta rataye Hijabin inda shi kuma ya ƙaraso cikin ɗakin yana riƙo waist ɗinta ta baya tare da saƙala kansa ta wuyan ta, cikin cool voice ɗinsa yace “Are you sure ban ji miki ciwo ba?.”
Shiru DEENAH tayi tana rarraba idanu nan tace “What?.”
Sake holding ɗinta yayi tightly bakin sa saitin kunnen ta yace “Well last night was full of…, i really don’t know how to describe it, but you are so very very special babe.”
Kunƴa ne ya kama DEENAH idanu ta runtse tana jin yadda palms ɗinsa ke yawo a cikin ta, hannun ta ta kai kan nasa tana riƙewa kafin ta shiga zame jikin ta.
Sake riƙo ta yayi yace “Am sorry i made you cry yesterday, i mean na ƙara miki ciwo akan wanda kikeji…”
Katse shi tayi da faɗin “It’s alright, am fine” dan kuwa ta lura ma kamar bayida isasshiyar kunƴa kwata-kwata.
Murmushi ZEEYAD yayi yana juyo da ita tana fuskantar sa, kallon cikin idanun ta yayi kafin ya saki murmushi yace “Idan kin warke gabaɗaya, we’re going on a honeymoon daga nan kuma zamu wuce Nigeria ki gaida ƴan gida” ya ƙarashe cikin ɗan jan ha6ar ta.
DEENAH bata san sadda ta saki wani irin murmushin farin ciki ba, nan tace “Really?” cike da farin ciki da zumuɗin da ya darsar mata lokaci guda.
Kai ya jinjina mata cikin murmushi, rungume shi tayi ƙam cike da farin ciki tace “Wow am so happy” kafin kuma ta ɗago tana duban sa tace “Yaushe zamuje.”
“Idan kin warke gabaɗaya” ya faɗa.
“Nidai gaskiya na warke yanzu” ta faɗa cikin muryar shagwa6a.
Ɗan waro idanu yayi kafin yayi murmushi yace “Sabida kinji nace zan kai ki kiga ƴan gida, i can’t take you there like this coz babu tantama idan na kai ki a haka then ba zasu bar ki ki dawo ba” ya faɗa cikin rashin jindaɗin abubuwan da ya faru da ita ɗin kafin ya ɗaura da faɗin “And it’s all my fault, the blame is all on me, tun ba’a je koh ina ba na kasa baki kyakkyawar kulawa and i hate myself for that.”
Saurin cupping fuskar sa tayi tana kallon sa tace “What are you saying Abyad, ka bar faɗin haka komai da kaga ya faru damu then a rubuce yake haka Allah ya ƙaddara rayuwar auren mu zata kasance, ba laifin kowa bane but jarabawar mu ce haka, i know we’ve gone through alot in life but that doesn’t mean zamu baiwa kanmu koh wasu laifi akan dukkanin abinda suka faru, those that did wrong to us Allah ne ya ƙaddara hakan a garesu but sun kasa controlling ƙiyayyar su a garemu tare da rungumar yadda Allah ya ƙaddara musu rayuwar su shiyasa ƙarshen su batayi kyau ba, i know you and i know how much you love me koh da da wasa ne ba zaka ta6a attempting yin wasa da rayuwa ta ba, na shaidi hakan tun ba yau ba, i just can’t imagine what my life will turn without you Abyad, so stop blaming yourself i know kana dukkanin ƙoƙarin ka na ganin ka kula dani but 6ata garin dake biye da rayuwar ka suna neman hana yiwuwar hakan, ba kai kaɗai ne yakamata ace ka kula dani ba, nima lokaci yayi da zan kula da kaina dama kai kanka, we will now both look after each other and make sure that no harm ever visit our ways again, just promise me that you will always be there for me though nasan kullum you always stood for me a duk lokacin da wani yaso cin zarafi na, nima i guess lokaci yayi da yakamata na kula da kaina and make sure ban kar6i duk wani cin mutunci koh zarafi daga wurin wani koh wata ba, na daina nuna tsoron su a fili, domin kuwa maƙiyi na samun hanƴar cutar da kai ne a duk lokacin da yaga wani gazawa tattare da kai musamman idan ya hango tsoron sa a cikin idanun ka then ya dinga farautar ka kenan har sai ya cimma burin sa, banason ka sake baiwa kanka laifi akan dukkanin wani abu da maƙiya zasu yi mana nan gaba ba fatan hakan nake ba, and i know insha Allah ba zasu sake samun damar ƙuntata mana koh cin galaba akanmu ba” ta ƙarashe tana shafa gefen fuskar sa.
Kallon ta kawai yake har ta kai aya a zancen nata, murmusawa yana rungume ta tsam a jikin shi yace “Insha Allah, we’re ready to fight our enemies, and ke kanki yanzu kin ƙarfafa min guiwa fiye da tsanmanin ki, i love you so much DEENAH, you really mean the world to me” ya ƙarashe cikin raunanniyar murya yana rubbing bayan ta.
Murmushi DEENAH tayi, ji take wani irin farin ciki na fizgar ta, though ta san bai wuci alƙawarin zuwa Naija da yayi mata ba.
Ɗagowa yayi yana cupping fuskarta, murmushi tayi ganin yadda yake kallon ta, kissing lips nata ya shiga yi har sai da yayi mai isar sa kafin ya ɗago yana sake bata peck a goshi.
Gyalen kayan jikin ta ya ɗauko daga kan bed ɗin yana yafa mata a kafaɗu kafin ya riƙo hannun ta su fito.
Tun daga kan stairs ɗin take hango JALILAH da YAZEED dake zaune babu mai yiwa juna magana a cikin su, duk sai taji babu daɗin hakan sam baikamata ba atleast JALILAH ta cancanci kulawa daga gun YAZEED koh dan kyawawan halayen ta ma.
Taimaka mata yayi ta sauƙo daga stairs ɗin kafin ya zaunar da ita daga cikin couchs ɗin dake zube a kyakkyawan falon.
Murmushi JALILAH tayi mata tana tasowa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗun ta tace “How are you doing DEENAH, ya lafiyar jikin ki?.”
Maida mata martanin murmushin DEENAH tayi tace “Alhamdulillah.”
“Good Morning DEENAH, how is your health?” cewar YAZEED dake facing ɗinta.
Amsa masa tayi da da sauƙi kafin kuma ya ɗau first aid box ɗin gaban sa yana ƙarasowa inda take zaune.
Bandage ɗin ƙafar ta ya shiga warware mata kafin ya sake yi mata dressing wurin yana ɗaura mata sabo, inda haka yayi wa hannun ma.
Kallon ZEEYAD dake tsaye akansu yayi kafin yace “Ka 6ata min lokaci bayan you know Hospital zani.”
Idanu ZEEYAD ya ɗan waro yace “Actually ba nine na 6ata maka lokaci ba, it was DEENAH” ya faɗa yana nuna DEENAH dake zaune.
Waro idanu itama tayi tace “No it wasn’t me” ta faɗa tana hararar ZEEYAD ɗin.
“Ofcourse i know it wasn’t you, coz nasan ba zaki 6atamin lokaci ba.”
Murmushi tayi tana ɗan yiwa ZEEYAD dake tsaye gwalo.
YAZEED ne yace “Alright, i will take my leave, see you later.”
Rakiya ZEEYAD yayi masa kafin su fice DEENAH tayi saurin faɗin “Baka yiwa matar ka sallama ba.”
Duk juyowa sukayi inda Jalilah kuma ta sadda kanta ƙasa, ɗan murmusawa YAZEED yayi yana kallon ZEEYAD da ya zuba masa ido shima yana jiran abinda zai ce.
Hararar ZEEYAD yayi in a whisper yace “How do i said it?.”
Murmushi ZEEYAD yayi shima cikin raɗa ya shiga faɗin “You walk gently to her, bind your kneels down, lean her hands gently and look straight into her eyes then you say Bye Wifey am gonna miss you so badly.”
Kunkumi kawai ya riƙe yana kallon ZEEYAD ɗin, kallon sa ZEEYAD yayi nan yace “Come on do it.”
“You think this is a joke, i just want to do it yadda ba zataji wani iri ba.”
“Then you must do as i told you, it’s the only way da ba zataji wani iri ba.”
“Are you guys planning something?” ya faɗa yana kallon DEENAH da ta tsare su da ido tana kallo.
Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi yace “Go on with it bro” ya faɗa yana nuna masa hanƴa.
Kai kawai YAZEED yayi nodding yana takawa zuwa inda JALILAH ke zaune, ɗan duƙawa yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ɗanyi gyaran murya yace “Am leaving for work, da akwai abinda kike buƙata na taho miki dashi?.”
Kai kawai ta girgiza masa alamun a’a tace “No nothing.”
“Are you sure?” ya sake faɗa yana kallon ta.
Kai ta jinjina masa nan yace “Alright, bye then.”
Ɗan murmusawa tayi kawai tana jinjina kai, kallon DEENAH dake kallon su yayi kafin ya ɗan saki murmushi yana sauƙe 6oyayyiyar ajiyar zuciya, juyawa yayi yana takawa zuwa wurin da ZEEYAD ke tsaye yana ɗan 6oye dariyar dake son zuwa masa.
“Best friends never make fun of each other talkless of best brothers” cewar YAZEED yana ficewa daga falon nan ZEEYAD ma yayi saurin mara masa baya.
Kallon DEENAH JALILAH tayi kafin tayi murmushi tace “Zan iya taya ki zama?.”
Kai DEENAH ta jinjina mata tace “Sure.”
Murmushi JALILAH tayi dan kuwa koh ta koma part ɗin YAZEED ba daɗin zama takeji ba koh dan rigima da tsokanar da Sairah ke damun ta dashi ma.
Ba’a jima ba ZEEYAD ya dawo, kallo ɗaya yayi musu yana haurawa sama coz atleast yakamata ya ɗan basu space koh sa samu suyi hira sosai koh dan su saba da juna ma sannan DEENAH ma ta rage wasu daga cikin damuwar ta.
THREE WEEKS LATER
_______Sosai DEENAH ta warke taji sauƙin jikin ta, a yanzu har ta saba da zaman part ɗin nasu ita kaɗai, kasancewar ZEEYAD ya saya mata waya kullum tana cikin waya da ƴan gida hakan na rage maka kusan kaso 70 cikin damuwar da take ciki, ga kuma wata iriyar kulawa ta musamman da take samu daga 6angaren ZEEYAD da Grandma ɗinsa hatta mai Martaba ɗin ba’a barsa a baya ba wurin nuna mata ƙauna da kulawa.
Hakan ba ƙaramin baƙanta ran Sairah yake ba, ganin duk cikin surukan sa yafi ɗaukin DEENAH haka ma sauran mutane kowa ji da ita yake ita ɗin da ba komai ba.
Tsaye take gaban mirror tana rolling gyalen peach abayar dake jikin ta, dan kuwa so take ta kaiwa JALILAH da bata gajiya da zuwa duba ta ziyara ita ma yau.
Sosai tayi kyau cikin shigar tata, wayar ta kawai ta ɗauka tare da fitowa tana sanƴawa ɗakin nasu key kafin ta shiga sauƙowa ƙasa.
Bayin dake ta aikace-aikace ne tace dasu “Ku bar aikin haka nan, zan fita idan na dawo zan ƙarasar da kaina.”
Cike da girmamawa suka tattari kayan aikin nasu suka fice.
Bin bayan su tayi tana rufo ƙofar falon, wasu bayi mata ne da aƙalla zasu kai biyar suka doso ta dawuri ganin kamar fita takeson yi.
Saurin ce musu tayi “Kuje ku huta bana buƙatar rakiya ba nisa zanyi ba.”
Kasancewar part ɗinsu na kallon juna ya sanƴa kawai kwalta ta tsallaka tana shigewa ciki babu wanda yayi yunƙurin tsaida ta saima gaisuwa da tayi ta kwasa har ta isa ga falon ƙasa wanda yadda komai na part ɗinsu haka ma wannan ɗin yake.
Zama tayi cikin ɗaya daga couchs ɗin falon, wata kuyanga ce ta ƙaraso inda take tare da faɗin “Sannu da zuwa ranki ya daɗe gimbiya, da wa kikeson ayi miki sallama?.”
“Da uwargidan” ta bata amsa a takaice.
Duƙar da kai tayi cikin girmamawa kafin ta shige wani lungu cikin falon.
Ba’a wani jima ba sai gata baiwar ta dawo tace “Tace na iyo miki iso zuwa ciki.”
Miƙewa DEENAH tayi tana mara mata baya, JALILAH ta gani a kitchen da alama dai abincin rana take ƙoƙarin haɗawa.
Murmushi ta sakarwa DEENAH dake shigowa inda ta maida mata martani.
Kujera DEENAH taja daga cikin kujerun dining ɗin kitchen ɗin tana zama, kafin kuma wasu bayin su shiga serving ɗinta.
Wanko hannu JALILAH tayi kafin tazo taja kujera kusa da DEENAH tana zama tare da faɗin “Kece yau a gidan mu?.”
Murmushi DEENAH tayi kafin tace “I thought yakamata nima yau na shigo, koh bakomai zan huta da gori.”
“Gaskiya kam kin wanke kanki” ta faɗa cikin ɗan dariya kafin ta ɗaura da faɗin “Kin zo a daidai, favorite ɗin mijin ki nake ƙoƙarin haɗawa, mai zai hana ki koya ki dinga yi masa?.”
Murmushi DEENAH tayi kafin tace “I will love to.”
Miƙewa tsaye JALILAH tayi tace “Come and have a look then.”
Miƙewa ita ma DEENAH tayi tana mara mata baya zuwa inda tukunƴar girkin take, sosai ta maida hankali gun abinda JALILAH ke koya mata ɗin har suka kammala.
Serving musu tayi bayan sun kammala girkin, suna cikin ci Sairah ta faɗo kitchen ɗin.
Tsaye tayi tare da riƙe kunkumi tana aika musu da wani irin mugun kallo.
Murmushi JALILAH tayi tace “Sairah?, ki ƙaraso mana ki zauna.”
Kallo ta ƙare mata sama da ƙasa kafin ta buɗi baki tace “Mai kike taƙama dashi ne?, i was waiting for my lunch tunɗazu only to find out kin ajiye wannan abar kuna cin abinci tare, ina nawa kason toh, kema dai kinsan ba girki na iya ba bale kice zan girka da kaina naci, idan ma kina tunanin akwai bayin da zasu girka su bani naci ne then miye amfanin ki, you know how to cook well that means kece zaki dinga yi mana girki muna ci baki ɗayan mu, wane irin salon rainin wayo kuma kika 6ullo dashi na hana ni abincin rana, a gidan miji na, i can’t believe you JALILAH.”
Shiru JALILAH tayi mata kamar wata mai tsoron ta, kallon ta DEENAH take ganin koh zata tanka mata amma batayi hakan ba, kenan ya tabbata tsoron ta takeji dagasken.
“You know what, dole ne Ummie taji wannan maganar.”
“No please” cewar JALILAH ɗin tana miƙewa tsaye ta ƙaraso wurin ta tare da dafa kafaɗun ta tace “Ba sai maganar yaje gun Ummie ba, am sorry i thought we’re sisters and…”
Yarfar da hannun JALILAH tayi tace “Sisters with who?, listen JALILAH ni fah kawai ina zama dake kuma ina ɗan kula ki coz i have no other choice, but that doesn’t mean zaki dinga yimin dukkanin abinda ranki keso dan kawai an baki matsayin uwar gida ba shi ke nufin zaki yimin abinda ranki yaso bane…”
“But ban hana ki abinci ba, abincin ki a ajiye yake, why don’t you try to make some peace koh da na kwana ɗaya ne a tsakanin mu, you always have a way of insulting me koh da abu bai kai ya kawo ba, sannan bakida aiki a kullum sai ɗaura min sharri a gun Ummie, babu abin dake a raina wanda ya wuce muyi zaman lafiya tsakani na dake but you always have a way of mocking and criticizing me a duk abinda nayi, and yarda da Ummie keyi dake a kullum shi ke ƙarfafa miki guiwar cigaba da halayen ki, why don’t you understand cewa ni banason rigima atleast you should try to make some peace with me tunda har kika gane ni rigima ba abinda na kware a kai bane.”
“Hmm, Peace?” ta faɗa tana kallon ta kafin ta ɗaura da faɗin “I never learnt what that was, bansan shi ba bale nayi zaman shi dake, ke kishiya ta ce which means am sharing a Husband with you, how do you expect me to make Peace with you then?, ban ɗau kishiya a matsayin abokiyar zaman lafiya ba, sai dai kuma kash you’re so fucking calm sam banso halayen ki a haka ba…”
“Ba zan ta6a yin rigima dake ba, ina faɗamiki ne sabida kin fara kai ni bango, kiyi ƙoƙarin gyara halayyar ki towards me please.”
Murmushin gefen baki ta saki kafin tace “Ai baki ma fara ganin komai ba tunda har dani kike kishi kaɗan kenan kika gani daga cikin abubuwan da zan iya aikatawa, sannan zan so ace na tunzura ki na kai ki bango ɗin sabida rigima cikin jinin jiki na take, bansan wani abu wai shi lumana koh makamancin sa ba, maganar da kikayi min yanzu ki tabbatar shine sanadiyyar buɗewar ƙofar duk wasu fitintinun da zasu cigaba da wakana tsakanin mu nan gaba, you just wait and see muddin ina cikin gidan nan then keda farin ciki kunyi hannun riga kenan, this is my promise to you” tana faɗin haka ta fice a fusace daga kitchen.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka sauƙowa JALILAH a ƙunci tana bin inda Sairah tabi da kallo.
Juyowa tayi ga DEENAH da ta zuba musu ido tunɗazu tana kallo, murmushi ta ɗan saki kafin tazo taja kujera ta zauna.
Koh kaɗan DEENAH batayi mata magana akan rigimar tasu ba, sai ma wani shafin hirar ta daban da ta buɗe har sai da taga Jalilah ɗin ta saki jikin ta sosai kafin ta tashi ta tafi.
_________Zaune yake gaban sa ɗauke da system ɗinsa yana dannawa, DEENAH dake kwance tayi matashi da laps ɗinsa ne ta kira sunan sa a hankali “Abyad?.”
Rufe Laptop ɗin yayi kafin ta tashi zaune tana kallon sa, cikin kulawa yake kallon ta kafin yace “Seems like akwai magana a bakin ki, tell me.”
“Abyad it’s about JALILAH.”
“What about her?” ya faɗa yana kallon ta.
Shiru tayi kafin tace “Baka fahimci tana cikin damuwa ba?.”
Ɗan murmusawa yayi kafin yace “Well ni kullum ke nake gani ba wata ba, how then zan san irin halin da take ciki.”
Abinda ya faru tsakanin JALILAH da Sairah ta kwashe ta faɗa masa kafin ta ɗaura da faɗin “You should talk to you YAZEED he is their Husband and i know ba zai rasa hanƴar tackling ɗin issue ɗin ba, atleast JALILAH deserves to be loved, cemin fah tayi mahaifin ta da yayan ta koh taje gidan su sunyi ta ya6a mata baƙar magana suna sanƴa ta baƙin ciki in the other hand kuma YAZEED’S Mom tana yarda da dukkanin abinda Sairah ta faɗa mata akan JALILAH ita kuma ba zata so ji daga bakin ta ba sai ta hau ta da faɗa tana gaya mata baƙi, and YAZEED in the other hand sam shima baya nuna mata wani damuwa iyaka cin su gaisuwa ne kawai tsakanin su, talk to him please i know yana jin maganar ka sannan zai ɗau shawarar ka, kaji.”
Huci ya fesar kan ya numfasa yace “Alright, i will talk to him tunda hakan kikeso, you happy?.”
Kai ta jinjina masa nan ya rungumo ta jikin sa yana patting bayan ta a hankali yace “Your wish is always my command Queen.”
Murmushi DEENAH tayi kafin kuma yace “Jibi zamu tafi Honeymoon ɗinmu, i know zaki so yin nesa da nan for sometime.”
Cike da farin ciki ta rungume shi tightly tana murmushi tace “Allah ya kaimu.”
Agogon dake manne jikin wall ɗin falon ya duba kafin kuma yace “It’s getting late, mu kwanta haka nan.”
Ɗagowa tayi tana tashi tsaye, shima ɗaukar system ɗinsa yayi tayi gaba yana biye da ita.
Canza kayan ta tayi izuwa silky doguwar rigar bacci, kafin ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito tare da nufar Bed ta kwanta bayan ta tofe jikin ta da addu’a.
Shima ZEEYAD canza kayan sa yayi izuwa brown Jallabiya ya ɗauro alwala kafin ya kashe musu hasken ɗakin, ƙarasowa yayi ya rage musu hasken side lamps ɗin kafin ya haye kan bed ɗin yana janƴo ta jikin sa.
Hannun ta ɗaura kan nasa dake manne a cikin ta a haka har bacci ya ɗauke ta.
Cikin bacci yaji kamar ana hura masa iska mai tsananin zafi koh wanda ake kwarawa dukkanin jikin sa ruwan zafi.
Tun yana iya daurewa har ya kasa ya shiga buɗe idanun sa da sukayi tsananin kaɗawa yayin da zuciyar sa keyi masa zafi da wani irin raɗaɗi haɗi da bugu tamkar zai faso ƙirjin sa ya fito.
Buɗe idanun sa ke da wuya yaga shigewar wani irin baƙin hayaƙi cikin jikin sa.
Runtse idanu yayi sakamakon wani irin zafi da zugi dake ta ƙara sukar zuciyar sa haɗi da fatar jikin sa.
Ƙame jikin sa da ya fara rawar sanƴi yayi yana jin kamar wanda ake yayyanka tsokokin jikin sa a haka har ya faɗi ƙasa dafe da saitin zuciyar sa, daga nan kuma duhu mai tsananin gaske ya mamaye masa idanu.
Alarm ɗin ƙarfe ukun da ta saita a wayar ta ne ya shiga ringing, idanu ta buɗe tana janƴo wayar daga kan bedside drawer tare da kashe alarm ɗin, zaune ta miƙe ta shiga karanto addu’ar tashi daga bacci kafin ta kunna bedside lamp tana maida duban ta gefen da yake kwanciya, wayam ta gani dan haka maida duban ta tayi ga inda suke sallah nan ma dai bata gansa zaune ba.
Miƙewa tayi ta sauƙo daga kan bed ɗin ta shiga takawa zuwa bakin ƙofa, jin ƙofar tayi a rufe alamun dai ba’a fita daga ɗakin ba.
Wutar ɗakin ta kunna take ɗakin ya gaurayu da haske, bathroom da nufa tare da buɗewa ta shige sai dai tayi dube-duben ta bata ga kowa a ciki ba, tsoro ne ya fara kama ta, toh ina yayi?, shine tambayar da ta yiwa kanta.
Takowa tayi da niyyar zuwa ta duba closet room taji tayi tuntu6e da abu take ta faɗi ƙasa dan sam bata lura dashi ba, ƙara ta ɗan saki sakamakon goshin ta da ya ɗan bugu kafin tayi saurin maida duban ta kan abinda tayi tuntu6e dashi ɗin.
ZEEYAD ta gani kwance, ba tare da ta kawo komai ranta ba ta rarrafa zuwa inda yake hannayen ta ta ɗaura kan ƙirjin sa ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa akan ya tashi suyi sallar Nafila.
Gani tayi koh motsawa baiyi ba “Abyad?” ta sake kira a hankali.
“Abyad ka tashi mana” ta faɗa tana sake jijjiga shi.
Ji tayi kodai wasa yakeyi mata ne tashi tayi ta ɗauko ruwan gora kafin ta shiga yayyafa masa, nanma gani tayi koh gezau baiyi ba.
Dropping ruwar gorar tayi yana faɗi ƙasa kafin ta durƙusa da sauri tana manna kanta da ƙirjin sa tare da saurarar bugun zuciyar sa.
A razane ta ɗago zuciyar ta na dukan tara-tara, sake maida kanta tayi dan koh tana tunanin bataji bane mai kyau, nan ɗinma dai thesame thing ta sake ji.
Ɗagowa tayi da sauri idanun ta na tara hawaye ta shiga lalumar jikin sa, hannun sa ta ɗaga tana saurarar pulse ɗinsa, sakin hannun tayi da sauri tana ja da baya kafin kuma ta shiga girgiza kanta cikin kukan dake zuwan mata ta shiga faɗin “No… no… this… this can’t be… you can’t be dea..” bata ƙarasar ba ta sake rarrafawa da sauri tana komawa wurin nasa tare da ɗago da kansa tana rungume shi a ƙirjin ta, fuskar sa ta shiga kallo kafin tace “I know you’re kidding me, i know you’re not dead, maybe… maybe you’re sick… yes i know you must be sick that is why you’re unconcious” ta faɗa cikin tatta6a fuskar sa zuwa wuyar sa da yake sanƴi babu alamun zazza6i.
Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri tana zuwa ta lalumo wayar sa kafin kuma cikin rawar hannu ta shiga neman numbern Grandma.
Kafa wayar tayi a kunnen ta lokacin da ya shiga ringing, har ya katse bata ɗaga ba, dan haka ta sake dialing sai a karo na uku kafin ta ɗaga kiran, ba tare da DEENAH ta jira cewar ta ba ta shiga faɗin “Grandma… Grandma kizo dan Allah Abyad ba shida lafiya… dan Allah kizo da wuri” tana faɗin haka ta katse wayar da sauri tana komawa wurin sa tare da tallafo kansa tana sake kiran sunan sa “Abyad dan Allah ka tashi, kada kayimin haka you can’t be dead now, baikamata ka tafi ka bar ni ba i will be doomed without you Abyad dan Allah ka buɗe idanun ka and talk to me i beg you Abyad please” ta ƙarashe cikin kuka sosai tana shafa fuskar sa.
Bai fi da 5mins ba Grandma ta ƙaraso kafin ta shiga kwankwasa ƙofar tana kiran sunan “DEENAH.”
Da sauri DEENAH dake rungume da ZEEYAD ta tashi tana ƙarasawa bakin ƙofar ta buɗe, tare da riƙo Grandma cikin kuka take faɗin “Thank GOD you’re here, ina ta tashin shi tunɗazu baya motsi bansan mai ya faru dashi ba.”
Hankali tashe Grandma ta ƙarasa inda yake kwance da sauri tana kallon sa a hankali kuma ta shiga kiran sunan sa “Boy” tana shafo fuskar sa.
Cikin kuka DEENAH tace “He isn’t waking up tunɗazu nake tashin sa amma baya motsi, am scared kada wani abin ne ya same shi.”
“He will be fine insha Allah, i know he will be fine, ɗaukomin waya na kira YAZEED.”
Da sauri ta miƙe tana zuwa ta ɗau wayar sa tare da miƙawa Grandma, amsa tayi kafin ta lalumo wayar YAZEED ta shiga buga masa.
Firgigit Sairah da wayar ke riƙe a hannun ta tayi lokacin da ya ɗau vibration, ganin mai kiran ne ya tabbatar mata da cewa aikin su ya tafi according to plan, ta san DEENAH ce mai kiran, murmushin gefen baki ta saki har kiran ya katse bata ɗaga ba.
Wani kiran taga ya sake shigowa shima har ya tsinke bata ɗaga ba, kira na uku taga ya sake shigowa dan haka tayi rejecting call ɗin, har sau uku ana sake kira tana rejecting kafin ta rubuta text message da faɗin “Stop disturbing Bro” murmushi tayi kafin kuma ta danna send button take text ɗin ya tafi.
Goge duk wani call log da text ɗin tayi yadda dai ba za’a gane ta ɗau wayar ba, kafin kuma ta shiga settings tayi disabling ɗin fingerprint ɗinta da ta sanƴa, wayar ta ta ɗauko kafin ta yiwa Sarauniya Hafeezah text da We did it, everything went according to planned” tare da danna send button ya tafi.
Lalla6awa tayi izuwa ɗakin YAZEED dake bacci kamar ma wanda baisan inda kansa yake ba, ta ajiye masa wayar sa tare da ficewa cikin sauri.
Wurin Hafeezah kuwa murmushi ta saki bayan tayi receiving text ɗin Sairah “So now let’s see how you become the king, muddin ina raye only YAZEED can be the King no one else, you were my biggest problem but now that i have get ridden of you i feel like the world is my hands” ta ƙarashe cikin dariya ranta fari sol sabida ta gama da ZEEYAD sai dai wanin sa kuma ba shi ba, tunda taji nan da jibi za’a naɗa shi Sarki kamar yadda Abdulhakeem ya sanar da ita hakan ya sanƴa batayi ƙasa a guiwa ba ta aiwatar da shirin ta bayan ta sami wani babban boka da ya kware wurin aikin sa.
Dariya tayi kafin tace “Let’s see who you Surprised then your Highness, idan bakayi surprising ɗinsa wurin naɗa sa sarki ba, ni nan nayi surprising ɗinka da gawan ɗanka gobe da safe, so prepared to cry the tears of true remorse your Highness, your dearest son is no more, let’s see who you give your throne to then” ta faɗa cikin gimtsewar fuska.
6angaren Grandma kuwa mamaki ne ya cika su ganin abinda YAZEED yayi musu.
DEENAH ce tace “Grandma, ki kira Sadeeq i know he will be here soon.”
Kallon ta Grandma tayi kafin tace “Kafin Sadeeq ya iso nan yanzu gari zai iya wayewa, sabida tsakanin gidan su da nan akwai nisa sosai.”
“But what do we do Grandma, we’ve to save him kafin wani abin ya same shi” ta faɗa cikin kuka.
Kallon ZEEYAD da baya motsi Grandma tayi, sosai jikin ta yayi bala’in sanƴi dan kuwa bata tunanin inda akwai rai tattare dashi, ta san maƙiya sunyi nasara akan shi.
Sunkuyar da kai tayi wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo mata, a hankali itama ta fara sakin shessheƙar kuka ganin angama mata da ɗan jikan nata wanda shi kaɗai ne yanzu gatan ta a duniya.
Cikin rawar murya DEENAH dake kallon ta tace “Grandma, maiyasa kike Kuka, bai fah mutu ba, bashida lafiya ne kawai.”
Shiru Grandma tayi mata tana cigaba da kukan ta.
“Grandma?” ta sake faɗa wasu hawayen na sake biyo ƙuncin ta.
Kallon ZEEYAD ɗin take, tayaya ma za’a ce ya mutu, yes ta san Allah ne mai rayawa da kashewa a duk sadda yaso but tayaya za’ayi ace Abyad ɗinta ya mutu?, ta san bai mutu ba wani abin kawai maƙiyan sa sukayi masa.
“Grandma, dan Allah mu kai shi asibiti a duba shi koh wani abin ne ya same shi da baya motsi” ta faɗa cikin kuka tana kallon Grandma.
Goge hawaye Grandma tayi kafin kuma tace “Bari naje waje na kira wadannan masu gadin suzo mu kaisa asibiti” ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin.
Kallon ZEEYAD tayi tace “Insha Allah you will be fine, no harm can come to you.”
________Sosai DEENAH ke kuka a gaban gawan ZEEYAD da akayi masa shiru makwancin sa ne kaɗai ya rage a kaisa.
Sosai fadar da ɗau shiru kukan ta kaɗai akeji, YAZEED ne ya faɗo cikin fadar tamkar wanda ake korar sa, turus yaja ya tsaya yana kallon ɗan uwansa dake sanƴe cikin sutura irin ta matattu.
Idon kowa a wannan wurin yayi jaa sosai alamun dai sun sha kuka Except Hafeezah da Sairah da nasu kukan ya kasance na munafurci ne, Grandma kuwa sobbing kawai takeyi yayin da mai Martaba shima ya kasa barin kan gawar ɗan nasa, da ka gansa kasan yana cikin shock da ɗimuwa koh kukan ma ya kasa yi.
Ɗaya daga cikin ministocin ne ya ƙaraso wurin a hankali yace “Yakamata a kai Yarima ZEEYAD makwancin sa haka nan, tunda har anyi sallahr azahar ɗin.”
A tsawace DEENAH tace “No… babu wanda zai ta6a shi i know bai mutu ba, ku ɗan dakata zuwa anjima kaɗan ni nasan zai farka amma yanzu kam bai mutu ba” ta faɗa cikin rungume shi.
Shiru kawai mutumin yayi yana ɗan ja da baya cikin sanƴin jiki.
Cire audugar dake hancin sa DEENAH tayi tana jefarwa tare da faɗin “Idan ma yana raye tayaya zamu sani da wannan abin a hancin sa, i know he isn’t dead doguwar suma kawai yayi…”
Grandma ce ta katse ta da faɗin “What are you doing DEENAH?, likitoci sun tabbatar mana da cewa Boy baya…”
“They are liars, babu abinda suka iya, ni mijina bai mutu ba, mu ɗan jira zuwa anjima kaɗan zakuga ya tashi.”
Shiru Grandma tayi mata tausayin ta na kama ta, ita kanta jurewa kawai takeyi, amma dai abin da duba.
Cikin dashewar murya sarki yace “Azo a kaishi.”
Ɗagowa DEENAH tayi tana kallon sa kafin ta shiga nodding kanta tana kare shi daga mutanen dake zuwa da niyyar su ɗauke shi ɗin.
“No… no… no please, kada ku tafi dashi bai mutu ba, dan Allah ku kyale ni wallahi bai mutu ba, babu ta yadda za’ayi ace ya mutu, let go of me” ta faɗa tana kwacewa daga hannun wadanda suka riƙe ta ɗin tabi bayan su da gudu.
Da sauri YAZEED ya taro ta, fuzge hannun ta tayi daga riƙon da yayi mata cikin 6acin rai kuma take faɗin “Let go of my hand, you’re happy now aren’t you?, i know kafi kowa murna da mutuwar sa though nasan bai mutu ɗin ba, duk soyayyar nan da kake nuna masa ba na tsakani da Allah bane, ashe kana ɗaya daga cikin maƙiyan sa masu son ganin bayan sa…”
“DEENAH…” Grandma ta katse ta.
Ba tare da DEENAH tayi shiru ba ta cigaba da faɗin “Don’t stop me Grandma, you saw it ai, kema kinsan abinda ya aikata, dah ace yayi responding a wannan lokacin then maybe Allah ya taimake mu mu iya ceto rayuwar sa, but what did he do, ya nuna cewa bai damu da ɗan uwansa ba, sannan dukkanin wata soyayya da yaye yi masa was all fake.”
“Stop it now” cewar Hafeezah cikin tsawa tana ƙarasowa inda suke kafin ta ɗaura da faɗin “How dare you accused YAZEED of your husband’s death, wa ya baki gut ɗin yi masa magana in such a manner?, ki kiyaye harshen ki or else…”
Ba tare da tsoron komai ba tace “Or else what, what will you do, nima kashe ni zakuyi, well then why don’t your just go ahead sabida na tabbata nice next target ɗinku, but i will make sure that kun girbi dukkanin wani abinda kuka shuka, ran Abyad ɗina ba zai ta6a tafiya a banza ba, you must all paid a heavy price for his death this is my promise to you, i will make sure you all regret it.”
A tsawace Hafeezah tace “Take this mad girl out of my sight, akan mijin ki aka fara mutuwa ne kokuwa?, mijin ki ya mutu ne ba tare da an gano abinda yayi silar mutuwar sa ba, hakan na nufin lokacin sa ne yayi, no one is to be blamed for his death.”
“You’re all to be blamed, you monsters, you will all regret this i promise.”
“Watch your tongue DEENAH, ashe haka kike bakida tarbiyya, Ummie need to be respected…”
Katse Sairah tayi da faɗin “This woman here means nothing to me da har zanyi respecting ɗinta, she is nothing but a devil…”
“DEENAH” Grandma ta kira ta tana zuwa taja hannun ta su fara tafiya.
Dukda haka bakin DEENAH bai rufu ba take faɗin “I know you’re all behind this, and i will make sure you all regret it.”
“She is totally out of her mind, how dare her” cewar Hafeezah.
YAZEED da jikin sa yayi matuƙar sanƴi kallon tuhuma yayi wa mahaifiyar tasa, bai ce dasu komai ba yaja ƙafar sa ya fice daga fadar, zuciyar sa na matuƙar zafi sosai koh kaɗan maganganun DEENAH basuyi masa zafi ba dukda baisan akan mai take basa laifin mutuwar ZEEYAD ba.
Yana fita yaji an fizgo shi zuwa wani lungu.
Kallon Hafeezah Nazeerah tayi tace “How cruel Hafeezah” tana faɗin haka itama ta bar cikin fadar ƴaƴan ta suka mara mata baya ya saura Hafeezah, JALILAH, Sairah da kuma Rahinah.
Mugun kallo Hafeezah ta watsawa JALILAH da fuskar ta yake sha6e-sha6e da hawaye kafin ta daka mata tsawa da faɗin “Ke kuma mai kikeyi tsaye anan, zaki iya ficewa ki bisu banason shashancin banza.”
Da sauri tayi hanƴar ficewa daga fadar.
Ajiyar zuciya Sairah ta sauƙe kafin tace “Wow so finally, nice nan zan zamto matar sarki, i can’t wait to see that day.”
Murmushi Hafeezah tayi kafin tace “Hakane, but first we will have to get rid of this so called JALILAH sabida ke kaɗai nake buƙata ki kasance mata ga YAZEED.”
Murmushi tayi kawai tana ta saƙe-saƙen abinda zatayi cikin ranta.
________DEENAH ce rungume da Grandma, a yanzu kam kukan zuci kawai take, sosai yanayin ta ya canza, bata iya koh da kwakkwarar motsi ne daga inda take zaune, sosai takejin ta so empty, she can’t believe wai ZEEYAD ɗinta ya mutu, sai dai kuma dama Ubangiji maɗaukakin Sarki da kansa yace dukkanin mai rai mamaci ne, zai ɗauki ran wanda yaso a lokacin da babu wanda yayi tsanmani haka kuma ya raya wanda yaso a lokacin da kowa ya cire rai da samun lafiyar sa, ya kan ɗauki ran bawa ba tare da yayi koh da ciwon kai bane, wannan shi ake kira kana naka Allah na nashi, sai dai ita har yanzu tanaji a jikin ta ZEEYAD bai mutu ba, sai dai kuma dole ne tayi haƙuri tunda har zuwa wannan lokacin ba’a zo mata da labarin bai mutu ba, hakan na nufin dagaske ya mutu ɗin kenan, ba zata kuma sake ganin sa ba har duniya ta naɗe, runtse idanu tayi sakamakon wani kukan da yazo mata, gimtsewa tayi kasancewar Grandma ta hana ta yin kukan.
Sosai takejin zazza6i da wani irin hajijiya dukda a zaunen take, ji tayi zuciyar ta na tashi tanajin amai na zuwa mata.
Miƙewa tayi da sauri tana faɗawa toilet ɗin ɗakin Grandma ɗin ta shiga kwaro aman wanda duk ruwa ne ma kasancewar babu abinda ta sanƴa a cikin ta tun safe.
Riƙo ta Grandma da ta biyo ta cikin tashin hankali tayi ta shiga jero mata sannu.
Wanke bakin ta tayi kafin ta riƙo ta su dawo cikin ɗakin.
Ji tayi ba zata iya zama ba dan haka kwanciya tayi tanajin yadda jikin ta ke rufuwa da zafin zazza6i.
Sosai Grand ɗin ta sake shiga wani tashin hankalin kuma, babu abinda take jerowa DEENAH sai sannu cike da damuwa.
_“What are you saying?.”
“I mean he isn’t dead, i saw him moving his eyes at the hospital, it was indeed a miracle coz gwaji na farko da nayi masa ya tabbatar min da cewa ya mutu, but by the time da na lura da cewa ya motsa idanun sa na sake running wani test ɗin only to find out that he is still alive.”
“You know this kuma ka bari aka kaisa makwancin sa?.”
“Yes i know it, but i decided to keep it a secret hakan ya sanƴa ni yi masa allurar da zai sanƴa shi unconcious for 8hrs, so ba zama zamuyi yanzu ba we’ve to find a way na ganin mun tono sa before he gets suffocated, i thought that yaga wani abu before incident ɗinnan hakan ya sanƴa ni keeping this as a secret har sai munji daga garesa.”
“Then what ate we waiting for?, we should get him back now.”
“The problem is that masu gadin maƙabartar,ya zamuyi dasu?.”
“Leave that to me, kai kuma kaje ka fara shirye-shiryen komai tukun.”
“Yes” ya faɗa kafin duk su fice.
TWO DAYS LATER
________Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubowa Grandma a ƙunci sakamakon result ɗin DEENAH da ya fito.
Kallon DEENAH dake kwance kan bed hannun ta ɗaure da drip tayi tana sake maida duban ta cikin papern hannun ta.
Kallon ta Umma dake zaune gefen ta tayi tace “Lafiya dai koh, meke damun DEENAH?.”
Miƙa mata result ɗin tayi nan ta amsa itama ta shiga karantawa.
Jikin ta ne yayi sanƴi sosai itama tana tausayin DEENAH ɗin dama kuma tausayin yadda rayuwar ɗan dake cikin ta zai kasance babu mahaifi.
“DEENAH nada juna biyu na tsawon sati biyu” cewar Grandma cikin muryar kuka.
YAWAN COMMENT, YAWAN TYPING
Ku duba 52 yana a qasa.
*MHIZZ JIDDHERR……………..✍🏽