Hausa Novels

YARENA ADDININA COMPLETE HAUSA NOVEL

YARENA ADDININA +++++++
FARKON LABARI

Related Articles

Garin Doko gari ne mai yalwar jama’a masu sana’u daban-daban wasu Manoma, wasu *yan kasuwa suna yawan zuwa cin kasuwanni a garuruwa daban-daban. *Yan garin yaren Hausa suke yi saboda haka Hausawa ne yawancinsu, sai wasu kadan Fulani a garin. Garin yana karkashin karamar hukumar Garki dake Jihar Jigawa.
Yau daren goma sha hudu don haka garin ya gauraye da hasken farin wata, ko kwandalarka ce ta fadi a kasa zaka iya ganinta saboda hasken farin wata. Matasan Samari da *yan mata wadanda shekarunsu basu wuce goma zuwa goma sha biyar ba sune suke shawagi suna tsalle-tsalle suna wasanni kala-kala da alama suna jin dadin yanayin garin a yau. Ga hasken wata tar ga wata iska mai sanyi na kadawa.
Suhaif saurayin da babu mai iliminsa, kyau, nutsuwa, hankali da tsantsar iya kwalliya da gayu, yana fitowa daga gidan Kakarsa sai ya tsinci kansa da samun wani dan dakali a kofar gidan ya zauna yana kallon yaran da suke wasanni kala-kala yana murmushi shi kadai. Yana tuna baya lokacin da suke kamar haka suma sunyi duk irin wannan. *Yan maza suna wasan langa, wasu na wasan *yar buya. *Yan mata kuma gada suke yi. Wata zabiyar yarinya ce mai zazzakar murya ta ware murya ta fara rero waken gada ta ce.
“Uwar miji ta zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Uban miji ya zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Da kishiya ta zagen na lillisata na kaita Ofishin *yan sanda sun lillisata sun juyata sun kaita lahira sai gata a duniya.
Iyaraye nanaye aiye raye iye nanaye *yan mata.

Dariya ta kubcewa Suhaif ya fada a bayyane ya ce “Kai mata, mace bata son kishiya. Sai ga dandazon mata *yan kai amarya sunzo wucewa za’a kai amarya gidan mijinta. Mata dauke da kwallayen alkaki da nakiya na gara. Wata guda daya daga cikinsu ta goya amarya a baya, sai rera waka kawayen amarya suke yi. Suhaif ya bisu da kallo har suka wuce. Gefensa kuma wata kanwarsa ce (cousin) dinsa mai suna *Yar Hajja tana zaune da fitila a gabanta tana sayar da kwai ana *yar fashe, duk wanda aka fasa nasa an cinye shi sai ya bawa wanda ya fasa kwan ya cinye. *Yar Hajja ta ware murya ta rada tallar gyada da karfi ta ce
“Ta soyu da manda rangadau.
Tayi arewa da filin dakata amaro,
Sai ta sake rerowa,
“Goro goriye goro daushe, goro dan Kano dan Kaduna wanda bai ci ba yaci sabo.

Cikin tsokana Suhaif ya ce da ita “Ke zabiya rufe bakin kar sauro ya fada miki. *Yar Hajja uwar son kudi bayan tallar Koko da kike da safe, kiyi ta dan wake da rana da daddare ma sai kin sayar da goro da Kwai da gyada amaro. Bari inzo inci alakoro. Ya taso ya zo gaban farantin *Yar Hajja ya tsaya. “Yar Hajja ta ce “A’a bana bayar da alakoro sai dai ka saya, wallahi Babangida ka cika son kudi duk kudin da kake jidowa idan kaje Kano kace baza ka saya ba sai dai alakoro kai ko tausayina baka ji. Suhaif ya kyalkyale da dariya ya ce “Kaji ta wai kudin da nake jidowa a Kano kamar wani barawo, kudin ma jido shi ake yi a Kano? Ai kin fini son kudi, lashe money sunanki fa. Ya kai hannu zai dauki kwai daya sai *Yar Hajja ta janye farantin ta ce “Wannan Kwan nawa ne na kashin kaina amma gyada da goro na Hajja ne kakata kuma kakarka ce babu abin da zata ce maka. Ya ce “Ni ai ba tsoho bane bana cin goro. Bana cin gyada kuma tunda ni ba mayunwaci ba ne kwai ni zanci. *Yar Hajja ta dauko kwai daya ta mika masa, ya karba ya mikawa wani yaro a kusa dashi. Sai ya fisgo kwan gaba daya farantin ya ce da yaran dake wajen “Ku shirya yanzu zan rarraba muku kwai ku ci kyauta sai kuyi mata wakar yayi kwantai. *Yar Hajja ta fashe da kuka ta tashi da gudu zata shiga gida taje ta fadawa kakarsu cewar ga Suhaif nan zai rabar mata da kwanta. Suhaif ya kwalla mata kira ya ce tazo ta karbi kudin kwanta zai siye ya bata kudinta. Ta dawo tasha kunu ta rike kugu. Ya zaro *yan dari-dari guda uku sababbi fil ya mika mata ya ce “Kudin kwan nawa ne? Nasan baifi dari biyu ba ga dari uku nan ki rike, uwar son kudi. Ta kyalkyale da dariya ta rafsa buda tana murna ya saye kwan duka harma ya kara mata kudin. Suhaif ya dinga rabawa *yan mata da yaran dake zazzaune a zagaye da fitilar *Yar Hajja kowacce ya mika mata sai farinciki ya rufeta daya bayan daya yake binsu. Daga karshe sai ya hango wata budurwar yarinya a can gefe a zaune da jakar kayanta a gabanta. Ya ce “Waccan kuma wacece ta tafi gefe ta zauna ita kadai? *Yar Hajja ta ce “Mu ma bamu santa ba, bamu taba ganinta a garin nan ba, tun dazu tazo ta sauna tana kallon mu. Munyi mata magana tayi shiru. Suhaif ya karasa gareta, ya mika mata sauran kwan dake hannunsa guda biyu. Tasa hannu ta karba. *Yar Hajja ta dauko fitila da sauri ta zo tana haska wannan baiwar Allah, sai taja mayafinta ta rufe fuskarta, Suhaif ya yiwa *Yar Hajja tsawa ya ce ta daina haskata sannan ta tafi da fitilar. Suhaif ya durkusa a gabanta ya ce “Yan mata ya sunanki ne? Ta yi shiru bata amsa ba. Ya sake cewa bamu sanki a garin nan ba, haka baki yi kama da *yan garin nan ba. Daga wanne gari kika zo? Tayi shiru bata amsa ba. Yana shirin jeho mata tambaya ta uku sai yaji ta rushe da kuka mai tsanani. Yaji hankalinsa ya tashi ya hau lallashinta yana cewa “Daina kuka Allah Ya baki hakuri na daina tambayar ki. Can da kukan ya tsagaita sai ta dago da wasu dara-daran idanuwanta farare sol ta dube shi cikin wata sanyayyiyar murya ta ce “Ina so insha ruwa ko zaka taimake ni da ruwa? Ya ce “Zan taimake ki da ruwan sha *yar uwata. Ya tsura mata ido yana kallonta yana mata murmushi, sai ta sunkuyar da kai kasa. Ya kwallawa *Yar Hajja kira ya ce taje cikin gida ta dauko kwanan shan ruwan Hajja Kakarsu sabo, ta kawo masa ruwan sha mai sanyi na tulu. *Yar Hajja ta tashi ta nufi gida don dauko ruwan sha.
Suhaif ya sake duban Yarinyar ya ce “Idan na taimake ki da ruwan sha, zaki taimakeni ki fada mun sunanki da kuma inda kika fito? Ta gyada kai kai tana jujjuya kwai biyun dake hannunta. Ya nisa ya ce “Kawo kwayayen in bare miki. Ta mika masa ba tare da ta kalleshi ba. Kafin ya gama barewa *Yar Hajja ta kawo ruwa a cikin kwanan sha, mai sanyi kuwa tamkar daga firij ya karba ya mika mata. Lallai ta kwaso kishirwa kusan kwanan shan duka ta shanye, kadan ta rage. Ya mika mata kwan sai yaga ta karba tana ci bayan kishirwar data kwaso da alama akwai jin yunwa ma a tare da ita. Suhaif ya ce “Gashi kuwa kwan ya kare dana suyo miki wani sai dai gyada da goro. Ta girgiza kai ta ce “Ya isa na gode. Har yanzu a durkushe yake a gabanta. Ya nisa ya ce “Ina jiran amsar tambayata. Tayi narai-narai da ido ta ce “Sunana Fatima ana cemin Iman. Daga tashar *Yankaba na hau motar Gumel, kudin motata bai cika ba shine masu motar suka saukeni anan garin suka ce anan kudina ya kare. Ya ce “Ke kuma Gumel kike so kije suka sauke ki anan Doko? Yanzu idan aka baki kudin motar zuwa Gumel shi kenan matsalarki? Iman ta rushe da kuka ta ce “Gumel din ma idan naje bansan inda zani ba, bansan kowa ba kuma. Suhaif ya gyara tsugunansa ya ce “Iman ban gane ba, baki san inda zaki ba kenan? Ta kara rushewa da kuka mai tsanani tana cewa “Ban san in da zani ba, ban san kowa ba a duniyar nan. Ya bude baki yana mamaki can ya ce “Iman yi shiru ki daina kuka in tambayeki. Ina Iyayenki? Cikin kuka ta ce “Ni a Makka a ka haife ni, uwata ta rasu kwanannan, ubana kuwa tun ana goyo na ya rasu. A Makka muke zaune, sune kadai suka rage min bansan danginsu ba. Shine askarawa masu kame a Makka suka kamoni. Suhaif ya girgiza kai cike da tausayi ya ce “Oh my God! Yi shiru Iman insha Allah zan taimakeki. To amma abunda ya daure mun kai shine daga jin Hausarki kun dade a Makka baku da takardar shaidar zama (igama)? Iman ta sharbe hawaye ta ce “Wahala da wulakanci nake sha tunda iyayena ba su bar min wata dukiya ba, aikin gidan larabawa suke yi kuma daman bamu da takardar zama, ina yawo askarawa suka kamani suka kawo mu kasar, bansan kowa ba a Nigeria. Kukan ya sake kece mata. Ya girgiza kai yayin da tausayinta ta sashi kwalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button