Yanda zaka goge whatsapp dinka daga wayar da aka sace

YANDA ZAKA GOGE WHATSAPP DAGA WAYARKA DA AKA SACE CIKIN SAUKI 

Kamar yanda kowa ya sani yanzu haka whatsapp yana daya cikin abubuwa da kowa yakeyi a rayuwarsa tayau da kullum ,amma babban abin da yake damun mutane sosai game da irin wadannan abubuwa na yau da kullum shine abin daya shafi sata , whatsapp dinmu cike yake da sirrikanmu donhaka za kaga idan an saci wayoyin mu munfi damuwa da kayan da yake ciki sama da ita kanta wayar shi yasa yau insah Allah zamu kawomuku cikakkiyar hanyar da mutum ze iya kulle whatsapp dinsa Ba tare da yasha wahala ba.

Yanda zaka goge account dinka a whatsapp

da yawa daga cikinmu wani sain sukanyi kuskure idan Allah yasa suna so su rufe whatsapp dinsu da suka bude da wata lambar saboda wani uzuri ko kuma suka kammala amfani suna so su bude wani kawai se suje suyi delete din whatsapp din wannan kuskurene yanda ake delete na whasapp account shine kamar haka

Da fari zaka shiga whatsapp dinka

Seka danna madanne 3 na sama a dama

se ka shiga settings

se ka shiga account 

seka shiga delete my acoount

ga misali nan a hoto 

Yanda zaka goge whatsapp dinka daga wayar da aka sacemaka

hanyar da ake bi a goge whatsapp ta wayar da aka sace ko ta bata hanya ce me matukar sauki ana yinta ne ta hanyar turawa company sakon Email a tsare sannan zaka iya turamusu sakon da turanci ko faransanci, sannan sakon ya kasu kaso biyu akwai na batan waya akwai na sace waya bari na nuna muku kowanne 

Da fari zaka shiga gun email dinka seka tura sako a wannan email : support@whatsapp.com

Bangaren turanci sace waya

 “Stolen: Please deactivate my account”

+234 80 xxxx xxxx

“Lost: Please deactivate my account”

+234 80 xxxx xxxx

Bangaren france sace waya

” Volé: Veuillez désactiver mon compte”

+227 xxxxxxxxx

Batan waya

“Perdu : Veuillez désactiver mon compte”

+227 xxxxxxxx

Ga misali nan a hoto yanda sakon ze kasance

wannan shine wassalamu Alaikum 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*