
Yanda zaka nayin chatting ba tare da Internet ba
A wannan darasin zamuyi bayani ne akan yadda zakanayin chatting da bluetooth ba tare da ka bude data ba.
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.
Karamin bayani akan wannan
Sunan wannan Application din (Briar), zaka same shi a play store kuma sama da mutum dubu dari ne suke amfani dashi, dan haka kaima zaka iya jin dadin amfani dashi
Amfaninsa
Wannan wani Application ne wanda zai baka damar zabar mutanen da kake so kuna yin chatting a sirrance, kuma zaku iya yi ba tare da network ba. Misali idan kana so kana yin chqtting da budurwar ka a sirrance ko matar ka ko a bokinka zaka iya amfani da wannan application din a saukake.
Kuma bashi da wahala kwata-kwata
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma’ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Leave a Reply