Yadda Zaku Gane Idan Wayarku Tana da 5G Network

Yn uwa barkanmu da sake kasancewa daku a wani sabon shirin, da fatan kuna lafiya.
Yau shirin namu yazo muku ne da bayanin yadda zaku gane cewa idan wayarku tana da 5G Network.
Kamar yadda muka sani 5G Network yana aiki a kasashe da dama, wanda yanzu haka a wasu sassan kasarnan sun fara amfani dashi.
Kamfanin sadarwa na Airtel tuni sun fara aiki da 5G a wasu nahiyoyi. Amma idan kuna son sanin wayarku tanada 5G Network, ga yadda zaku duba.
Yadda Zaka Gane Idan Wayarka Tana Da 5G Network
Kai-tsaye ka bude Settings a wayarka
Saika tafi zuwa Connections
Saika taba Mobile Network
Anan saika taba Network mode
Idan ya nuna maka — 2G/3G/4G/5G (auto connect) — to wayarka tana da 5G Network.
Idan kuma wayarka tana dauke da 2G/3G 4G/ kawai, to bata da 5G Network.
Idan kana son dora 5G services akan wayarka, kawai ka zabi 2G/3G/4G/5G (auto connect) shikenan.
Abubuwan Da Zaka Lura Dasu Game Da 5G Akan Wayarka
Abu na farko daya kamata ka sani shine ka tabbata akwai 5G service a yankinku. Na biyu, ka duba idan wayarka da SIM card dinka suna supporting din 5G. Sannan ka tabbata network din wayarka ka saita shi zuwa 5G.
Wayoyin Da Suke Daukar 5G Services
Ire-iren wayoyin da suke daukar 5G services sun hada manyan wayoyin da aka saki shekaru biyu baya. Misali, Galaxy S21 series, Apple iPhone A13 series, Realme GT Edition, OnePlus 9 ko 10, ROG phone 5 ko 6 da sauransu.