Yadda Zaku Ajiye Files A Cikin Wayarku Google Drive

A lokutan baya mutane da yawa suna rasa files dinsu a cikin wayarsu misali idan wayar ta fadi ko ta bata ko kuma idan an sace musu, za kuga mutum yana cewa duk hotunansa ko videos dinsa suna cikin wayarsa kuma ya rasa.
A yanzu wanncan lokacin ya wuce domin kuwa a yanzu google sun samar da software ko manhajja da ake amfani da ita wato google drive, ta wannan software din zaka iya ajiye duk wasu files dinka na waya a ciki ba tare da fargaba ba, abinda kake buqata shine email kawai indai kana da email ta shikenan.
Zakaje playstore ko app store kayi downloading google drive application sai ka saka email dinka. Daga nan zasu baka storage har 15GB kyauta ta yadda zaka dora duk wasu files dinka a ciki idan kuma files dinka sun wuce 15GB zaku iya siyan wani space din.
Domin ganin yadda ake amfani da google drive zaku iya kallon video din da yake kasa nayi bayani sosai tare da nuna yadda ake amfani da google drive din nagode.