Yadda zakayi share din data ta MTN, Glo, Airtel da kuma 9Mobile cikin sauki zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki

Yadda zakayi share din data ta MTN, Glo, Airtel da kuma 9Mobile cikin sauki zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki
Assalamu Alaikum,
En uwa barkanmu da sake kasancewa daku a wannan lokacin, ayau cikin shirin namu munzo muku ne da yadda zaku tura data/share wa abokai da ‘yan uwa.
Data sharing na daya daga cikin kyawawan fasahohin zamanin da kamfanonin sadarwar Nigeria suka saki.
Ba sai lallai mutum daya ne zaka iya samun transfar data daga gareshi ba. Zaka iya samun transfar data daga wurin mutane da yawa a lokaci guda ta yadda zaka samu isasshiyar datar da zakayi duk abinda da kake so.
Zamu fara da yadda zakuyi sharing data akan MTN, sannan mu duba yadda zakuyi akan sauran networks din.
Yadda zakayi share din data ta MTN ta hanyar USSD
Yin amfani da lambobin code wajen transfar data/sharing ta MTN itace hanya mafi saukin tura data wa wani mai amfani da layin na MTN.
Ga yadda abin yake:
Ka bude dialer ta wayarka sannan ka danna *131#
Saika danna zabin “Gift Data”
Yanzu anan zaka iya tura data wa abokinka daga balance din datar ka ko kuma ka saya masa.
Saika danna kan “Transfer from data balance”
Saika taba kan akwatin daya bayyana maka sannan ka saka lambar wadda kake son turawa datar.
Yanzu, saika zabi adadin datar da kake son turawa. Zasu baka zabi 4 — 50MB, 100MB, 200MB da kuma 500MB.
Daga nan, zakayi confirming transfar ka, datar zata tafi kai-tsaye zuwa wurin wadda kayi nufin turawa.
Wata hanyar tura/share din datar MTN zuwa wata lambar ta MTN, ka bude dialer din wayarka ka danna *131*lambar wayar wadda kake son turawa*adadin datar da kake son turawa#.
Yadda zaka tura data akan MTN ta hanyar sako
Domin tura/share data akan layin MTN ta hanyar sako, kabi wadannan matakan dake kasa:
Ka bude akwatin sakonka “Messages” akan wayarka
Saika rubuta “Transfer < Lambar wadda zaka turawa> <Adadin datar da kake son turawa> ”
Bayan ka kammala rubuta su duka, saika tura sakon zuwa 131
Bayan ka tura sakon, wadda ka turawa zai karbi sakon nan take.
Yadda zaka tura datar MTN ta hanyar MTN app
Tura datar MTN ta hanyar application din MTN tana da sauki a matsayinka na mtn user. Ga yadda zakayi:
Kayi downloading MTN App a Google Play
Sai kayi register da login acikin application din ta hanyar amfani da lambar wayarka.
Akan dashboard dinka, ka danna “Share”
Saika danna “Data”
Yanzu saika danna “New Number” ka saka lambar wayar wadda kake son turawa.
Akasa kuma zakaga inda zaka saka adadin datar da kake son turawa kuma kayi confirming transfar taka.
Yadda zaka tura data akan layin Glo ta hanyar USSD
A matsayinka na mai amfani da layin Glo a Nigeria zaka iya tura data cikin sauki zuwa wani ta hanyar USSD.
Ka bude dialer ka danna *777#
Ka danna “Data”
Saika zabi “Sahre data plan”
Saika danna na farko – “Share”
Saika saka lambar wadda kake son turawa
Sai kayi confirming ka danna “Send” daga nan zaka karbi sakon cewa ka tura data zuwa ga wani.
Wata hanyar bayan wannan itace, ka bude dialer ka danna *127*01*Lambar wadda kake son turawa*Adadin datar da kake son turawa#.
Yadda zaka tura data akan Glo ta hanyar sako
Ka bude “Messages” application akan wayarka
Saika rubuta “Share” tare da lambar wadda kake son turawa
Bayan ka hada rubutawa duka, saika tura zuwa 127
Da zarar ka tura, wanda ka turawa zai karbi sakon datar a layinsa na Glo dake wayarsa.
Yadda zaka tura data akan layin Airtel ta hanyar USSD
Ka bude dialer sannan ka danna *141#
Ka danna kan “Share data”
Saika zabi “Me2U”
Saika danna “Enter from existing balance”
Saika saka lambar wayar wadda kake son turawa
Saika danna “Send” bayan kayi confirming
Yadda zaka tura data akan layin 9Mobile ta hanyar USSD
Da farko zaka saita pin code na transfers. Gakai zaka kirkiri transfer pin, ka danna *247*default PIN*new PIN#. Lambobin default din sune “0000”.
Bayan ka kirkiri transfer pin, ka tafi zuwa dialer ka danna *229*Sabon pin*Adadin datar da kake son turawa*Lambar wayar wadda kake son turawa#
Wadannan sune matakan da ake bi wajen sharing din data akan layukan MTN, Airtel, Glo da kuma 9Mobile a Nigeria.