Yadda zaka yi screenshot akan kowace irin kwamfuta

‘Yan uwa barkanmu da wannan lokaci, tare da sake kasancewa daku a wani sabon darasin. A yau da ikon Allah zamu sanar daku yadda zakuyi screenshots akan kowace irin na’urar kwamfuta.
Daukar screenshots yakan zama dole akan na’urar kwamfuta a lokuta da dama, musamman idan bukatar hakan ta taso da kuma wayoyin hannu a yau. Bugu da kari, yanayin daukar screenshots akan na’urar kwamfuta kuma yakan yi wahalar aikatuwa fiye da daukarsa a waya. Dan haka yasa muka shirya muku wannan darasin domin daukar screenshots akan Windows, Linux, Chrome OS da kuma na’urar kwamfuta ta Mac.
A takaice
> Yanda zaka dauki screenshots akan Windows PC
> Daukar screenshots akan Linux PC
> Yanda zaka dauki screenshots akan Chromebook
> Daukar screenshots akan Mac
Yanda zaka dauki screenshots akan Windows PC
Anan ga manyan hanyoyin daukar screenshots akan Windows PC.
> Ta hanyar amfani da PrtSc wato (print screen) key — sai kayi hit PrtSc key akan kibod, ka bude Microsoft paint, sannan ka danna Ctrl + V wato fest kenan. Sai kayi save fayil. Zaka iya taba key na Windows + PrtSc domin saving dinsa kai-tsaye zuwa fikca -> Screenshots folda.
> Na biyu kuma ta hanyar amfani da snipping tool — ka danna Windows key + Shift + S ko kuma snipping tool key idan ya kasance akwai shi akan kibod din kwamfutarka. Zaka zabi irin snip din da kake so, sannan kayi kilikin na image din acikin notification kayi edit sai kayi sebin nashi.
> Ka danna Windows key + G domin gayyato Xbox game bar. Ka danna kan kyamara aikon a cikin kafca window domin daukar screenshot.