Yadda zaka yi scanning na takardunka akan wayar Android

‘Yan uwa barkanmu da wannan lokaci, ayau munzo muku da sabon darasin yanda zaka yi scanning din takardunka akan wayarka ta Android. 

Kayi scanning din takardun ka ka tura su daga wayarka acikin dauka daya. 

Idan kana da wayar Samsung Galaxy wadda ke tare da one UI 2 ko sama da haka, zaka iya scanning na kowane irin takarda kai-tsaye daga kyamarar wayar taka. 

Idan kuma kana amfani da mabanbantan Android skin, karka damu; Google Drive yana da sauri kuma da saukin matakan yin scanning. Anan ga yanda zaka yi scanning na takardunka akan wayar Android.

Domin yin scanning akan wayar Android, ka bude Google Drive a cikin wayarka saika danna wurin Create New–> Scan. 

Yanda zakayi scanning na takardu akan wayar Android

Idan ya kasance kana da wayar Samsung Galaxy zaka iya scanning din takardun ka kai-tsaye daga kyamarar wayar taka ba tare da dauko wani application dazai taimaka maka wajen yin hakan ba, matukar dai wayar tana dauke da One UI 2 ko sama da haka. Saboda wasu daga cikin wayoyin Samsung galaxy na shekarun baya da suka wuce suna da irin wannan fasahar, kamar yanda yanzu tuni kamfanin Samsung sun saki fasahar One UI 4 akan manyan wayoyinsu wadda suke makura wajen fasahohin zamani irin su Galaxy S20 da S21 siris. 

Cikin sauki ka cikin kyamara app daga wayarka ta Samsung galaxy saika jera takardun domin fara scanning din. Yayin daka ga wani layi mai launin dorawa wato yellow a gefen takardun, saika zabi Tap to scan. 

Za kuma ka iya matsar da kwanar takardun naka domin karawa ko kawarwa da wasu abubuwan da baka so. Idan ya kasance kana farin ciki da ita wato tayi maka yadda kake so saika taba Save. 

A lokacin da kayi sebin dinsa, zaka iya ganinsa a cikin matattarar hotunan ka wato Gallery app. 

Idan kuma kana amfani da wata wayar wadda ba Samsung galaxy ba, to anan Google Drive shine zabinka wajen scanning na takardunka. Kai shine ma zabi mafi kyau idan kana bukatar juya/mayarda scanning din naka zuwa PDF.  

Da farko dai, ka bude application din Google Drive saika taba alamar + a kasa dama. A karkashin Create new menu, saika taba Scan. 

Saika daidaita tsayuwar kyamarar wayar taka domin fuskantar takardun sannan ka taba madannin dake tsakiya lokacin daka shirya scanning din hoton. 

Daga karshe, saika taba Sebin ta yanda zai kaika zuwa dora takardun naka zuwa kan Google Drive. Zaka kuma iya juya hoton ko matsar da shi da gyara kalar hoton dai dai da yanda kake bukata. Idan kuma kana son dora scanning da yawa a lokaci guda, ka taba alamar + a cikin madannin dake hannun hagu. 

Shin zan iya scanning din takarduna tare da wayata ta Android?

Eh, tabbas zaka iya scanning na takardunka tare da Android dinka ta hanyar amfani da Google Drive. 

Ta yaya zanyi scanning na takarduna kuma in dora su akan kwamfuta na?

Kabi dukkan wadancan matakan kayi scanning takardun naka tare da Google Drive. Zaka kuma iya shiga cikin documents din naka daga Google Drive akan kowace waya. 

Ta yaya zanyi scanning na takarduna akan wayar iPhone?

Idan kana da wayar iPhone wadda take version 11 ko sama da haka, ka bude Notes app, saika taba wurin kyamara icon sannan ka zabi Scan Documents.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*