Technology

Yadda zaka tura katin waya daga layin MTN zuwa Airtel

 Kamfanin MTN da Airtel sune manyan kamfanonin sadarwa a Nigeria, sune kuma suke da hannun jari mafi girma a nahiyar kasashen Africa kamar Nigeria da Africa ta kudu. Yana da kyau ka koyi yanda zaka iya tura katin waya wato transfer daga layin MTN zuwa Airtel saboda kana da bukatar hakan musamman idan kai dan kasuwa ne.

Tura katin waya daga layin MTN zuwa Airtel yana da sauki kuma yana da amfani sosai. Hakan kuma zai taimaka musamman idan kana amfani da layin na MTN da Airtel din.

Yawancin mutane sukan yi transfar airtime daga layin MTN zuwa Airtel domin samun sauki saboda Airtel sunfi saukin data da cin kudin kira akan MTN.

Yadda zakayi transfar airtime daga layin MTN zuwa Airtel

Wannan tsarin zai taimaka maka idan ka koyi yadda zakayi share din airtime daga MTN zuwa Airtel saboda dalili na ujila kona kasuwanci. Misali, wani mai layin Airtel zai bukaci ka tura masa kati daga wurinka domin yin kiran gaggawa. Sannan service din zai baka damar samun wata rara yayin dogon kira na kasuwanci kona gaggawa. A maimakon kira ta layin MTN, saika tura katin zuwa layinka na Airtel domin yin magana da yawa tare da kudi kadan.

1. Yadda zaka tura kati ta layin MTN ta hanyar sako

Da farko ka canza network din wayarka zuwa kan MTN.

Saika bude app din rubuta sako.

Saika rubuta Transfer [fili] lambar wanda kake son turawa [fili] Adadin yawan katin [fili] sai kuma Transfer PIN (misali.  Transfer 08038637119 150 6459).

Saika tura sakon zuwa 777.

Zasu turo maka da request cewa ka zabi tsakanin YES ko CANCEL.

Saika tura YES ko CANCEL zuwa 777 domin tabbatarwa ko sokewa transfar.

2. Yadda zaka tura kati daga layin MTN zuwa Airtel ta hanyar amfani da USSD code

Wannan tsarin shine alternative na wancan, amma dukansu zaka iya aiki dasu insha Allah. Kuma maganar gaskiya wannan tsarin is available ga duk wani mai amfani da layin MTN 24/7.

Da farko ka canza network operator din wayarka zuwa layin MTN.

Ka danna *600*lambar Airtel na wanda kake son turawa*adadin yawan katin*sai pin dinka na transfer(misali. *600*08038637119*100*0000#).

Zasu tura maka sakon verification domin tabbatar da transaction din.

Yadda zaka tura data daga layin MTN zuwa Airtel

Ka danna code din transfer na MTN wato *131*2*3# idan kanason tura data daga layinka na MTN zuwa Airtel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button