Technology

Yadda zaka sawa numbers din wayarka password koda an kira ba wanda ya isa ya dauka sai yasan pin din

Yadda zaka sawa wasu mahimman numbobin wayarka password wanda ko an kira babu wanda ya isa ya dauka sai yasan pin din…

Abubuwa suna ta faruwa wajen daukar kiran waya, wasu numbobin mutum baya so koda wasa wasu su dauka idan an kirashi saboda mahimmancin da suke a gunsa.

Wasu kuma na sirri ne dan haka baya so idan an kira koda baya nan wasu su dauka..

Haka kuma koda a gida ne miji yakan ajiye wayarsa ya shiga wanka ko kuma wani abu wanda kafin ya dawo sai kuga an kira wanda wasu matan kuma basa iya hakuri sai sun dauki wannan kiran kawai domin suji waye ya kira wanda kuma hakan ana yawan samun matsala musamman idan matar ta gane wata ce ta kira mijin nata.

To yau mun kawo muku wani application wanda zaku zabi duk wasu numbobinku na sirri ku sanya musu password yadda babu wanda zai iya daukar kiransu koda wayar tana hannun wani dole sai sun sanya password…

Da farko ku duba kasa za kuga mun ajiye muku Link din wannan application din wajen da muka rubuta danna nan, daga zarar kun dauko shi sai ku bude shi zai nuna muku wasu zabuka guda biyu saiku danna allow, daga nan zai baku damar kusa pattern ko pin sai kusa shikenan.

Idan kunsa zai nuna muku gurin da zaku zabi numbers din da kuke so ku sawa security din cewar koda sun kira sai mutum yasa password shikenan.

                        Danna nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button