Technology

Yadda zaka sakawa duk photon da zaka tura password babu mai iya budewa sai wanda ka fadawa password din

Wannan App din zai baka damar sawa photon da zaka tura password kuma mutum bai isa budewa ba har sai ka fada masa password din..

Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke?

A yau cikin shirin namu munzo muku da wani sabon application ne da zai baku damar sawa photon ku password lokacinda zaku tura shi sannan ku mayar dashi zuwa PDF ta yadda mutum bai isa budewa ba har sai kun fada masa wannan password din..

Dalilin mu na kawo wannan application din kuwa shine sauda yawa wani yakan so ya turawa wani photo ko kuma ya turawa wata to amma bata da waya wannan yasa saidai ya tura a wayar wani ko wata su kuma su nuna wa waccan din, wasu kuma kafin su nunawa wanda ake so su nunawan ma sai kaga sun bude sun gani har ma wasu sun sake gani kafin akai ga wanda ake so su gani din.

Wanda hakan yana kawo damuwa sosai tsakanin mutane, dan haka muka kawo wannan application din wanda zai baku damar saka password a photon da zaku tura kuma babu wanda ya isa budewa sai wanda kuka fadawa password din.

Bayan haka wannan App din zai baku damar gyara photonku yayi kyau..

Zaku iya yin scanning na takardun ku da wannan application din.

Sannan akwai abubuwa da yawa da yake da nasan zasu dauki hankalin ku.

Ga duk masu bukatar saukar da apps din su duba kasa gurinda muka rubuta danna nan saisu danna zasu sauke application din 

                          Danna nan 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button