Yadda zaka maida hotonka kamar na zane

A sau dayawa mukan yar da wayarmu kaga a cikinta babu sim card wanda za’a iya nemanmu ko kuma kaga wataran munasan haddace wani abu wanda ya shafi wayarmu, kamar irinsu number waya da sauransu.A don haka wannan abun ze taimaka maka sosai wajan ka rubuta number wayarka a screen na wayarka,bama iya number waya ba,duk wani abu da kake da buƙata ka saka a jikin wayarka zaka iya rubutawa a wajan batare da ka sauke wani Application ba, ta yanda ana samun matsala za’a nemeka cikin sauƙi koda ka rasa wayarka ko wani abun.
YAYA AKE WANNAN ABUN?
Kawai zakaje Setting na wayarka sekai ƙasa daga nan seka zaɓi Contact info, to anan ne zaka rubuta dukkan abunda kake so, bayan ka gama rubutawa,sekai gefe ka danna Done kai tsaye zakaga komai ya saitu insha Allah.
(Application NA FARKO)
Profile pic
Wannan manhaja me suna a sama tanada matuƙar sauƙin koyo,sannan kuma ze maida maka hotonka yanda baka tinani a cikin mintina kaɗan,ta yanda ze maida maka shi ya matuƙar burgeka sannan kuma ya baka damar ka saka shi a profile na kon ina batare da ka rage ko ka ƙara ba.
Hanyar amfani da wannan App ɗin a taƙaice
Hanya ce mafi sauƙi,kawai da zaran ka buɗe App ɗinka ze nuna maka fuska da zaɓi guda biyu, bayan ka ga wannan zaɓin daga gefen hannunka na dama a ƙasa zakaga wani waje da aka rubuta Skip, seka danna, kana dannawa ze baka fuska wanda aka rubuta Choose photo, to anan ne zaka zaɓi hotunan da kake so ka saka masa ya gyara maka shi kana zaɓa zakaga ya fara searching yana ƙirge daga 1 har zuwa 5, daga nan zakaga ya canza maka hotonka sannan kuma ya baka zaɓuka da yawa ta yanda zaka dinga canzawa saga wannan kalar izuwa wannan kalar, bayan ka zaɓa zakaga wajan save ko donload image daga nan kawai seka sauke shi a wayarka kai tsaye zaka iya saka shi a kowani profile naka.
Idan kanasan downloading wannan App ɗin
(Bayanin App na Biyu)
Goodev
Wannan App ɗin mu taɓa kawo me kama dashi a baya amma, wanan yafi sauƙi kuma yafi rashin nauyi sannan yafi wancan. Wannan manhaja ce da zai taimaka maka yayin ƙara sautin wayarka daga 100 har izuwa 200. A wasu lokutan na shagulgula zakaga munasan Raha da jin waƙe waƙe ko kuma wasu lokutan munasan karatun Alqur’ani mai girma a wani waje wanda mukesan kunna sauti me ƙarfin gaske a don haka zaka iya amfani da wannan App ɗi ko kuma ka aje shi domin gudun ko ta kwana, ta yanda bakasan lokacin da zaka buƙace shi ba.
YANDA AKE AMFANI DASHI CIKIN SAUƘI
kawai kana buɗe shi ze nuna maka zaɓi guda biyu seka danna Ok daga nan ze baka wani zaɓi me layi guda biyu anan ne zak dinga jansa sekaga Numbobin suna ƙaruwa zaɓi ƙasa kuma ze ce maka boost shima zakaga yana ƙaruwa ya danganta da inda kakeson ka kaishi, idon kanasan yaje har 200 to zaka iya kaishi, ta hanyar shiga Setting a cikin Application ɗin sannan a zaɓin ƙarshe zaka inda aka rubuta Maximum volume seka shiga nan ka ƙaro shi. daga nan sekai futa, kana jan screen na wayarka zakaganshi a ON to fa duk abunda ka kunna ƙarar daze seya kusa fasa maka kunne.
Idan kanasan Downloading wannan App ɗin …
Yanda zakai install, bayan ka danna inda mukace Danna Nan kai tsaye ze kaika Playstor daga nan zakaga ansaka Install seka danna kai tsaye ze sauka a kan wayarka.
Duka dai anan darasin namu ze dasa aya dafatan wannan bayanin ya gamsar daku yan uwa.
Wasalam mun gode.