Technology

Yadda zaka kira mutumin daya yayi bulokin din lambar ka

Yadda zaka kira mutumin daya yayi blocking din lambar ka 

Hanya mafi sauki wajen kiran mutumin daya rufe/dakatar da lambarka daga shiga ko kuma kiran lambar da akayi bulokin za’a iya hakan ta wadannan hanyoyi da zamu zayyano a kasa.

Shin kasan yadda zaka kira mutumin da yayi bulokin lambarka ko kiran lambar da aka rufe?

Idan har mutumin da zaka kira ya dakatar da lambarka daga shiga wurinsa, kuma kanason kiransa! Kayi tunanin meyasa yayi bulokin lambarka kafin kaci gaba tukuna. Ka tabbata baka da matsala da kowa, idan kiran da kake wa mutum kirane mai muhimmanci kuma mai ma’ana, to ka karanta wadannan dabarun domin kayi unblock lambarka.

Anan zaka san yadda akayi bulokin lambarka yayin kiran wani

Wadannan sune hanyoyi mafi sauki wajen karya kiran block number ko restriction.

1. A maimakon kayi ta kiran mutum da lambobi daban-daban domin samun mutum, amma kuma duk da haka baka same shi ba zaka iya abin da ake kira da “ encrypt” wato bude bayanan mutum ta hanyar ilimin na’ura ta yadda zakayi unblock sannan ka kira shi ko ka kirata

Kana bukatar gyara lambar kafin kira saika saka#31# kafin saka lambar.

Misalin yadda zakuyi shine:

#31#07086798565.

Da zarar ka danna wannan lambobin, zata bayyana da private number akan wayar wadda ka kira.

Kada kuma ka damu cewar ana blocking naka idan kayi amfani da lambobin#31#, dalilin haka kuwa shine yayin daka kira mutum da haka bazai san komai game da kai ba.

Abin lura

Amfani da wannan dabarar bazai boye lambarka a dukkan kiraye kiraye dakake yi ba, wannan ya takaitune kawai ga lambar daka kara da #31#

Ko

Kayi amfani da lambar *67 shikuma wannan zai bayyanar da lambarka a matsayin  “Unknown” ko “Private” number. Saika danna lambobin kafin lambar wayar dazaka kira, misali:

*67-406-821-XXXX. Wannan dabarar tana aiki ne akan wayar hannu da kuma wayar gida wato Landline amma bata aiki bangaren abin daya shafi cinikayya na kasuwanci.

2. Yin amfani da application wadda zai baka lambobi barkatai

Idan kana amfani da wayar android kai-tsaye ka tafi zuwa Google play store ko App store ga masu amfani da iPhone ka dauko daya daga cikin application wadanda suke kyauta ne wadda zasu hado maka tarin lambobi barkatai. 

Zaka iya amfani da lambobin da suka baka domin aika sako da kiran wadda baya amfani da wannan app din, za kuma ka iya kiran mutumin da baya da wannan app din. Wannan kuma itace hanya ma mafi saukin kiran mutumin da yayi bulokin naka.

Ga daya daga cikin application mafi sauki me suna “Phoner app”, shi phoner app zai kirkirar maka da lambobi na musamman saika zabi lambar da kake so kayi kira ko tura gajeran sakon sms harma da MMS. Wannan app din zai baka random lambobin daza kayi amfani dasu na wani lokaci.

Zaka iya duba wasu apps din irin wannan akan yanar gizo domin bada lambobi irin wadannan.

Babban amfanin wannan app din shine baya nuna hakikanin eriya  code, itama eriya code din random yake nunawa ta yadda wadda ka kira bazai yi zargin cewa ga ta idda kiran yazo ba.

3. Boyewa aidantiti naka

Wannan tsarin shikuma zai cigaba da baka damar amsa kira daga mutanen daka sani, amma idan ka kira lambarka bazata bayyana ba sai dai ta bayyana a matsayin “Hidden”.

Domin boye lambarka ga masu amfani da iOS (iPhone), saika tafi zuwa Settings. Saika tafi zuwa “Phone” section na cikin settings, saika zabi “Show My Caller ID”. Saika tura shi zuwa matakin “Off”.

Ga masu amfani da Android kuwa saiku tafi, Settings > Call Settings > Additional Settings > Caller ID saika zabi Hide Number. Dukkan kiran daza kayi zai zama unknown za kuma ka iya tsallakewa jerin bulok.

Domun ganin saran bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button