Technology

Yadda zaka kashe comment akan posting na Facebook

‘Yan uwa barkanmu da wannan lokaci tare da sake kasancewa daku a wani sabon darasin, ayau munzo muku da guzurin yanda zaka kashe comment naka ko na wani a Facebook.

Ba kowane fostin yake da amfani ba akan manhajar Facebook, saboda akwai fostin da yake public wato kowa zai iya gani. Idan dubban mutane masu maban-banta ra’ayoyi zasu iya ganin abin daka rubuta ka dora a matsayin fostin, a wannan halin ka tabbatar zaka samu wasu dubban ra’ayoyin mutane suna musu da nuna rashin jin dadinsu kodai wani abu a bangaren comments dinka. Amma idan shafi ne da kai wato, wannan kuma dokar kace zatayi aiki. Zaka iya tirsasa wasu dokoki ta hanyar kashewa bangaren kwament daya shafi fostin na gaba daya ko kuma wani fostin guda daya na musamman.

Amsa daya a takaice:

Domin kashe comments na public post, ka tafi zuwa Settings–>Privacy–> Public post saika taho kasa zuwa Public post comments–>Who can comment on your public posts?

Sai kayi kasa ka zabi Friends. Idan kuma kana son kashe comments na mutum daya akan wani post da yayi, saika tafi zuwa post in question, saika taho kasa, ka danna Who can comment on your post? Saika zabi wani abu koma bayan Public.

Yanda zaka kashe comment na duk public post a Facebook

Idan fostin ya kasance na gaba daya wato fablik akan furofayil dinka, to anan baza ka iya kashewa comments ba gaba daya ba. A maimakon haka, abinda zaka yi shine canzawa zuwa kwament na firibilej ga abokai kadai. Wannan zai dakatar da wasu na waje daba a san suba daga shiga zantukanka na Facebook, idan kuma daya daga cikin abokanka na Facebook shi yake janyo rikici, abinda kawai kake bukata shine ka yanke abota dashi.

Yanda zaka kashe kwament akan kowane fostin, ka tafi zuwa Account settings—>Privacy—>Public postSaika taho kasa har saika ga Public post comments—>Who can comment on your public post?

Saika taho kasa akan menu box din ka zabi Friends.

Akan wannan gabar, kadai abokanka ne zasu iya comment akan fostin na gaba daya.

Yanda zaka kashe comment na mutum daya akan Facebook

Idan kana fuskantar rashin jin dadi akan wani fost guda daya, zaka iya kashewa fublik kwament na iya shi kadai.

Acan sama a hannun dama da fostin din, ka danna wasu digo guda uku. A cikin menu, ka danna Who can comment on your post?

A cikin akwatin daya bayyana a gaba, kana da zabi guda biyu domin dakatar da kwament na fublik akan fostin dinka. Zaka iya saita shi kodai zuwa Friends, ko Profiles and Pages you mention (a cikin fostin din). Saika zabi abinda kake so ka danna Done.

Yanda zaka kashe comment na group post a Facebook

Facebook group yakan iya zama babban wurin gina al’umma amma kula da kwament shine babban aiki ga manyan guruf. Watakila wannan shine dalilin daya sa kake da wurin gyara da kula da comment. A cikin Facebook groups, zaka iya dakatar da hira gaba dayanta a cikin tracks ta hanyar canzawa zuwa kwamentin fonkshin na gaba daya post din.

Domin yin hakan, ka danna wannan digo guda uku na kwance a can sama a hannun dama na akwatin posting din. A cikin menu, ka zabi Turn off commenting.

Yanzu kwament  sekshin din zai bace. Daga nan babu wadda zai iya comment. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button