Technology

Yadda zaka kare gmail dinka daga hackers

Assalamu Alaikum

A koda yaushe ana samun masu kutse da yawa da suke harin asusun Gmail, amma munzo muku da wasu saukakan matakai daza kubi ku kare kanku daga masu kutsen.

Akwai abu guda daya kamata ka sani, na farko asusun email dinka na kasuwanci yafi tsaro sama dana asusun Gmail na personal — matakin tsaron su ma ba iri daya bane. Wannan dalilin yasa service din Google gmail ke fuskantar harin masu kutse saboda tarin bayanan da suke akai.

Yana da kyau ka dauki matakin gyara da hannunka ta hanyar kunna wadannan matakan tsaron da Google ya samar.

Password & two-step verification

Yawanci da yawan mutane suna saka ranar haihuwa ko sunan wani masoyi ko masoyiya ko komai ma a matsayin password. Amma yanzu wasu services din basa karbar irin wadannan ko kadan; yayin da saka saka password ana bukatar ka hada lambobi da bakake domin saita ko wane account.

Zaka kuma ka iya amfani da password manager ka kirkiri password kuma kayi saving dinta ta yadda da zarar ka bukata kawai zakayi amfani da ita kai-tsaye.

Bayan ka saka password, saika kunna matakin tsaro na gaba wato secondry verification system.

Shi wannan matakin zai kara maka tsaro ga asusunka na gmail.

• Amma kana bukatar wayar Android idan kana son yin wannan aikin

Da farko ka danna Sign-in & security>2-step Verification idan kaga alamar “On” to a bude yake, amma idan yana off ga yadda zaka kunna shi

Kawai ka shiga wurin da aka rubuta 2-step Verification saika danna Set Up>Get Started saika saka password dinka

Daga nan ka danna Sign-in da zarar ya bude maka saika kunna 2-step Verification. Yanzu duk lokacin da kai (ko wani daban) yayi kokarin shiga account dinka saiya samu yarda daga wayarka wato login request code.

Mun gode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button