Yadda zaka ka karawa wayarka sauri

Assalamu Alaikum Warahmatullah, ‘yan uwa barkan mu da wannan lokaci, da sake kasancewa daku a wani sabon darasin. A yau zamu sanar daku wasu hanyoyi daza kubi ku karawa wayoyinku gudu da rashin jinkiri wajen aiki.
Watakila kana da bukatar sake sayan sabuwar waya saboda wayar da kake amfani da ita ta tsufa ko rashin samun upgrade akai-akai, to ga wadansu sirrika daza kuyi amfani dasu wajen kara gudun wayoyinku. Bari mu shiga zuwa darasin ba tare da bata lokaci ba.
Kamar dai kowace irin na’ura, koda manyan wayoyin Android da tablets suna nuna halayyar jinkiri ko gajiyawa gwargwadon yawan amfani dasu da kuma shekarunsu. Wannan yafi zama gaskiya akan kananan wayoyin Android wadanda su ba ko yaushe suke da tsari da kuma fasahar daukar application na zamani ba. Amma karka ji komai — anan akwai abubuwa 15 daza ka iya yi ka karawa wayarka ta Android sauri kuma ka debe shekaru kana amfani da ita ba wata matsala.
Kula da update
Da yake ba duka sabon sofwaya updates ne ke karawa wayar Android sauri ba, masu kera wayoyin yawanci suna sake canza wasu abubuwa da gyara softwaya lokaci zuwa lokaci. Kadan ne daga cikin tsaron facis da kuma magance wasu matsaloli na bug sune suke karawa waya samun fikira ta gaba daya.
Wasu daga cikin wayoyin Android ana duba updates dinsu ne lokaci bayan lokaci, amma kadai a karkashin wasu sharadai. A irin wannan halin, yafi dacewa daka rinka duba updates da kanka idan ka rasa kowane updates. Cikin sauki ka tafi zuwa cikin Settings > About Device > Software Update saika taba Check for updates.
Dakatar da apps din da suke kan waya na tun asali.
Da yawa daga cikin mizanin wayoyin Android, ya nuna cewar mafiya yawan kamfanonin kera wayoyin Android suna dora musu wasu apps da wani lokacin ma bama a amfani dasu. Wannan musamman ga wayoyin Android na kasa kasa, da masu karbar tallace tallace da zaka ga suna pushing services akan wadda kake amfani da shi sosai. Misalan irin wadannan sun hadar da theme, kida/bidiyo fileya da kuma dibayis sikana apps.
Kuma sau da dama saika ga kamafanin wayarka sun kare ka daga kawar da ire-iren wadannan apps din, har yanzu zasu iya kuma baka damar dakatar dasu. A wani bangaren kuma, alhalin baza ka iya goge su ba, zaka iya batar dasu a wata nahiyar inda baza su taba budewa ba — manually ko automatically. Zaka iya dakatar da apps daga Settings > Apps > Installed apps menu. Zaka kuma iya kunna mazabin nuna apps na kan wayarka.
Sokewa izinin apps marasa amfani
Idan baka son dakatarwa ko kawar da wani application, amma kana sonsa da cin ganima ko yaya ne ma, to ka janye masa lasisin izini. Saboda aikin da yake yi wadda ake ganinsa ido da ido a wani bangaren yana da kyakykyawar illa ga kuzarin wayarka. Kashewa wasu izinonin kamar location access da autositat zai rage yadda application din zai cigaba da aiki a bayan kasa.
Cikin sauki ka nemj zuwa Settings > Privacy > Permission manager domin samun bayani cikin sauri na app permissions.
Wata hanyar kuma, ka danne kan application din akan screen din wayarka, saika taba App Info, sai Permissions.
Yin rebooting akai akai
Wasu lokutan, jinkirin na’ura ana magance shi ne ta mafi saukin hanyar kunnawa da kashewa. Ba abune mai wahala ba — kashewa da kunna wayarka wato kunnawa da kashewa yana goge apps da akayi amfani dasu a baya, da tsarin bakgirawun app da sauran abubuwan da aka kara a wancan lokacin. Cikin sauki ka danne makunnar wayarka saika taba Restart.
Daga nan wayarka zata zama cikin yanayi mai kyau a cikin kwanaki kalilan. Anyi sa’a ma wasu daga cikin manufakcara sikin kamar Samsung One UI zai baka damar shirya lokacin da wayarka zata ke restart da kanta a lokacin daka saita. Zaka iya saita shi yanayi akan wasu kwanakin mako. Sauran manufakcarori na Android da suke da irin wannan fasahar sun hada da Oppo, Xiaomi, da OnePlus.
Gogewa tarkacen cache na kowane app
Wannan dabarar zata iya taimakawa idan ya kasance ka farga da wasu apps akan wayarka da suke shirme sama da kowanne. Web browsers da sauran apps gaba-daya masu amfani suna tara tarkacen bayanai ko wane lokaci ka nemi bude wani sabon shafi ko shafin yanar gizo. Wannan kuma yana rage kuzarin application zuwa kasa.
Zaka iya maganin haka kodai ta hanyar goge app’s cache ko kuma ka sauke shi gaba-daya. Amma mun fi bada shawara akan na dazu, danshi baya goge sauran bayanai kamar logins, histori, da firiferanses. Daga screen din wayarka, ka taba da kuma danne kan application din har sai menu ya fito. Sannan, ka nemi zuwa App Info > Storage > Clear cache.
Gogewa tsoffin hirarraki (chats) da abubuwan daka dauko a internet na daga wakoki da bidiyoyi
Kamar yadda bayani ya gabata a baya, app akan wayarka zai iya samu lodi da yawa tare da isasshen lokaci da kuma amfani. Hakan yana faruwa ga apps na hira suma. Misali WhatsApp,ba iya ajiye bayanai daka dauko yake yi ba akan ma’ajiyarka, amma ajiyewa duka chat din akan ma‘ajiyar bayanai. Wannan yakan zama babbar matsala akan na‘urori marasa sauri, musamman idan ya kasance ka dade baka hau WhatsApp ba zaka karbi dubunnan sakonni marasa adadi.
Magance wannan matsalar mai sauki ce amma tana da dan matsi. Zaka rinka goge duk wata hira maras amfani kowane sati. Kar kuma ka manta da goge fayil na wakoki da bidiyoyi suma. Wannan zai taimaka wajen karawa wayarka sauri wurin galeri app da image picker.
Musanya manyan applications da kanana wato lite apps
Applications marasa nauyi suna bada saukakkiyar hanyar samun tagomashi akan wayarka daga manyan applications masu yunwar zukar caji. Misalin app din Facebook na Android yana da mas’aloli na dorawa waya kaya da yawa. Sauran kamar Instagram da Twitter wani lokacin suna da matsala suma kamar budewa na bidiyos wadda wayarka itace keda alhakin rikewa.
Apps marasa nauyi suna da saukin sha’ani wajen saurin lodin da kara saurin amsawa wato da zarar ka shiga zasu bude. Idan kana son wannan to ka rinka amfani da apps kamar Facebook Lite da Messenger Lite domin karawa wayarka sauri.
Yin amfani da apps na yanar gizo
Su kuma apps na yanar gizo sutura ne ga website hade da karin wasu fasahohi, zaka iya daya daga cikin web browsers kamar Google Chrome. Yayin daka shiga birauzarka ta yanar gizo a karon farko, za’a sanar dakai cewa ka kara ta akan screen dinka. Idan kana son wasu zabin, ka duba wadda Starbucks, Twitter da Uber suka bayar.
Barin home screen ba tare da abubuwa da yawa akan saba
Widgets, walfefa masu motsi da sauran abubuwan motsi akan screen din wayarka suna da illa bawai kadai ga fafomans na wayarka ba har ga lafiyar batir. Zaka iya kashewa hakan akan saitin lanca na wayarka zaka kuma iya shiga ta hanyar Google app a maimakon haka. Wata hanyar kuma bayan wannan, kana amfani da launcher mabanbanta ta haka ne zaka samu zabuka da suke marasa nauyi koma bayan wadda suke na asali ne.
Dakatar da apps daga auto-update
Wannan ya hada da apps dake Play Store da ofdet din apps na wasanni da suke faruwa su da kansu, irin wadannan suna barin user intafase ya zamto mai rauni.
Domin dakatar da irin wadannan apps din daga automatik ofdet, cikin sauki ka bude Play Store, saika taba kan hotonka na furofayil naka a sama saika zabi Network firiferansis. Daga karshe, cikin sauki saika canza saitin Auto-update zuwa “Don’t Auto-update apps.
Kanayin factory reset
Idan wasu daga cikin wadannan hanyoyin basu baka wani kyakykyawan sakamako ba, to faktori riset zai iya taimakawa wayarka da dawowa da martabarta na da. Kamar yadda sunan ya nuna shi faktori riset yana samarwa da softwaya na wayarka dawowa zuwa yadda take a farko.
Idan kana son yin factory reset na Android dinka ka tafi zuwa Settings > System > Reset options > Erase all data/factory reset saika bi dukkan sharudan da zasu biyo baya.
Dakatar da hands-free Google Assistant
Shi Google Assistant yana taimakawa idan kana bukatar yin wani abu cikin gaggawa. Bugu da kari kuma yawan running sabis na bukatar cinye babban wuri akan wayarka da kuma illata kuzarin waya. A irin wannan halin zaka iya dakatar da bakgirawund functionality idan kana son wayarka taci gaba da sauri.
Domin kashewa hands-free Assistant, ka tafi cikin Google app saika taba hoton profile dinka (wadda yake zaune a sama-dama da screen). Daga nan, saika nemi zuwa Settings > Google Assistant > Hey Google & Voice Match saika kashe fasahar din. Karka kuma damu — zaka iya ci gaba da amfani dashi Assistant din kodai ta hanyar dannewa home button ko kayi kawar daga kodai kwanar kasa Idan kana amfani da Android gesca. Idan kuma kana amfani da wayar Samsung, ka rinka la’akari da dakatar da Bixby Voice shima.
‘Yan uwa wadannan sune a takaice hanyoyin daza kubi ku karawa wayoyinku sauri ba tare da suna yin jinkiri ba.