Yadda zaka hana ayi adding dinka a group na WhatsApp

Hanyar da zaka hana ayi adding dinka a group na WhatsApp dole saida izininka.
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna godiya kuma muna jin dadi kwarai da gaske Allah ya bar kauna da kuma soyayya.
A yau cikin shirin namu munzo da hanyar da zaku hana ayi adding dinku a group na WhatsApp dole saida izinin ku ko kuma yaddar ku.
Kamar yadda muka sani mutane suna damuwa sosai duk lokacinda sukaga an sanya su a wani group na WhatsApp ba tare da saninsu ba wani abin takaicin ma sai kaga kwata kwata mutum baima san mai number da ya sanya shi a group din ba kawai sai tsintar kansa yayi a cikin group din.
Wani group dinma sai kaga bai dace ace an sanya ka a ciki ba saboda abubuwan da akeyi na shirme da shiririta…
Haka idan mutum babba ne ko kuma sunansa ya yadu idan wani ya samu number sa shikenan sai ya sanyashi a wancan group din ko kuma ayi ta sanyashi a group group.
To yau dai wannan abin yazo karshe domin babu wanda ya isa ya sake sanyaku a wani group na WhatsApp dole sai kunga dama kuma kun amince..
Idan baku aminta ba dole saidai su hakura domin babu yadda za suyi daku..
Da farko kai tsaye kuje gurin wasu madanne guda uku da suke sama bayan kun shiga cikin WhatsApp dinku sannan kai tsaye saiku tafi gurin da aka rubuta setting.
Bayan kun shiga gurin da aka rubuta setting saiku tafi wani guri a kasa da aka rubuta “account” saiku zabi gurin da aka rubuta privacy bayan ka shiga a kasa za kaga inda aka rubuta group kai tsaye saika shiga.
Zakaga gurare guda uku bayan ka shiga zaka ga gurin da zaka iya barin kowa yayi adding dinka a group ko baka sanshi ba wato gurinda za kaga ansa ALL, sai kuma daya gurin wanda zaka iya barin sai wanda suke da number ka ne ko kuma kake da number su ne kawai zasu iya sanyaka a group bayan ka amince.
Sai daya gurin kuma inda kaine zaka zabi wanda zai iya yin adding dinka a group din
Daga nan saika zaba shikenan an wuce gurin.