Technology

Yadda zaka hana a ganka online akan Facebook

Facebook yana baiwa abokanka damar ganin kana online akan shafin ko yin amfani da application na tura sakon gaggawa na Facebook wato Facebook Messenger appIdan baka son wani yasan kana online ko wani abu, to kashe alamar kana online shine abin daya fi dacewa daka yi. Ga yadda zaka kashe alamar kana online akan Facebook dinka.

Amsa daya a takaice:

Idan kana son kashewa alamar nuna active status akan Facebook, da farko ka bude application dinka na Facebook saika tabawasu ’yan digo guda uku a kwance. Saika tafi Settings and Privacy–>Settings–>Audience and Visibility–>Active Status saika tura shi zuwa off.

Zaka kuma iya dakatar da saitin akan shafin Facebook ko Messenger app.

Kashewa alamar kana online akan Facebook app

Ka bude application din Facebook na wayarka saika taba wasu digo guda uku a kwance a sama kwanar dama domin budewa options menu. Saika taho zuwa kasa ka taba Settings and Privacy.

Saika taba Settings—>Audience and Visibility—>Active Status saika tura shi zuwa off.

Yadda kuma zaka kashe alamar kana online akan yanar gizo ta Facebook 

Shaidar nuna kana online akan yanar gizo ta Facebook yana hade ne da Messenger section. Ka danna kan messenger aikon acan sama a kwanar dama sannan ka danna zabin menu.

A cikin wannan saitin chat din saika, danna Active status.

Saika matsar da alamar ma’ana togulzuwa off acikin zabin daya bayyana. Zaka kuma iya zabar wasu daza ka saita wadda zasu iya ganin ka lokacin da kake online.

Yadda zaka kashe alamar kana online akan Messenger app

Ka bude Messenger app saika taba kan hotonka na profile acan sama a kwanar dama. A cikin options menu, saika taba kan Active status saika dakatar dashi acikin saitin.

Shin zaka iya boyewa alamar kana online daga mutum daya?

Kabi duk wadancan matakan domin canza active status akan shafin Facebook na sama. A cikin bangaren Active status, zaka samu option inda zaka zabi mutane akan jerin abokanka da zaka iya kuma bazasu iya ganinka a online ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button