Yadda zaka gane wadda yake binka akan Twitter

Manhajar Twitter babban wurin hada mutane ne daban-daban da bayyana ra’ayoyi da samun labarai da dumi duminsu. Twitter zai sanar da kai a kowane lokaci ka samu sabon mabiyi kuma ya nuna maka adadin mabiyan da kake dasu. Bugu da kari, Twitter baya nuna wadda yayi unfollows wato wadda ya dakata da bibiyarka duk da cewar akwai matakin sirri na privacy settings. Alhalin hakan ma dalilin matakin daukar kariya ne, amma wani lokacin kana son kasan waye wannan kuwa wadda yayi unfollows naka. Munyi sa’a akwai wani application da zai iya wannan aikin. Baza kasan hakikanin wadda yayi unfollows naka ba kafin kayi installing app din, amma shi app din zai baka bayanan sa kan cewar idan yana hade da asusunka na Twitter.
Amsa daya a takaice:
Domin ganin ko sanin wadda yaki binka akan Twitter, ka hada asusunka da daya daga cikin wadannan amintattun apps din da zaka dauko ko shafin yanar gizo.
Ta yaya zan gano wadda yaki bina akan Twitter?
> Akan kwamfuta (Windows)
> Akan Android
> Akan iPhone ko iPad
Yanda zaka gane wadda yaki binka akan na’urar kwamfuta
Hanya mafi saurin gano wadda yayi unfollow dinka akan Twitter ta hanyar amfani da kwamfuta itace yin amfani da shafin yanar gizo na daban l. Akwai shafukan yanar gizo da yawa acan, amma ka nutsu wasu daga cikin shafukan suna da hatsari wajen tsaro tunda dole saika sahale musu shiga asusunka na Twitter. Amma mun baka zabin shafin Unfollowerstats, shafi mafi fadin amfani tare da matsayin da yake babba.
Shafin na bada shiri kyauta ga asusun Twitter tare da sama da mabiya dubu talatin 30,000 amma suna bada tallace tallace. Zaka kuma iya yin tracking na follow back domin ganin asusun da kafi jan hankalin mutane akai. Sannan idan ka biya hakan zai kawar maka da ads kuma su baka jadawalin girman asusunka.
Yanda zan gane wadda yaki bina l akan Android
Saboda Twitter baya nuna wadda yaki binka, akwai app daza kayi amfani dashi amma akwai dan kudi da zaka biya akan wani aiki na musamman. Amma kada ka zarge su madamar kana son gamsuwa da hakan, to kayi amfani da aflikeshon na Nomesigue.
Aikinsa bawai kawai ya nuna maka wadda yayi unfollow naka ba, amma zaka iya sanin wadda ma baiyi following naka back ba, shakikan abokai, sannan zaka iya ganin wasu daga cikin mabiyanka wadda basa hawa. Kari akan haka, zaka iya raba asusu tare da sama da Twitter furofayil ashirin.
Yanda zan gane wadda yaki binka akan iPhone ko iPad
Idan kana amfani da iOS, wasu manyan application suna amfani da Who Unfollowed Me on Twitter. Sabis din yadan jima kusan shekaru takwas kuma yana karbar updates akai-akai a rayuwarsa. Yana da salo mai sauki da zaka shiga analytics ka duba filters domin samun sabbin mabiya. Akwai bonus ma na dark mode.
Tsarin da suke bayarwa kyauta dinma ya isheka ka samu dukkan bayanan da kake bukata.