Technology

Yadda zaka gane idan wani yayi bulokin dinka a Instagram

Rufewa mutum akan Instagram bashi da dadi sam ga mutumin da aka rufe. Hakan yana nufin wadda yayi bulokin dinka baya son ka da kallon abubuwan sa daya ke dorawa, ko baya son mu’amala da kai. Akwai wasu ’yan alamomi daza ka iya fahimtar anyi blocking dinka. Idan mai amfani da Instagram ya dakatar/koya goge asusunsa, dukkan bayanansa zasu bace tareda su wanda ya hadar da tarihin hirarrakinsaSo, ta yaya zaka gane wadda yayi bulokin dinka a Instagram?

Amsa daya a takaice:

Domin sanin anyi bulokin dinka akan Instagram, kana da bukatar dauko app wadda zai taimaka maka wajen gudanar da wannan aikin wadda zaka dauko a google play store (Android) ko app store (iOS) kamar irin su Followmeter. Idan kuma ba haka ba ka gwada neman profile dinsu akan browser naka ko wani account din daban domin ganin shin ka sakamakon nemansu akan search bar.

Me zai faru yayin da kayi bulokin wani akan Instagram?

Lokacin da kayi bulokin wani akan Instagram, asusunka na Instagram zai bace ne daga feed nasu. Baza su kara iya liking ko comment akan bidiyo ko hoton daka dora, kuma baza su iya shiga cikin wadanda za’a lissafa, tag, ko tura maka sako ba. Baza su iya ziyartar asusunka na Instagram ba, kuma baza su samu sakamakon ka ba yayin da sukayi searching sunanka ba.

Kari akan haka, dukkan wasu likes da comments na baya da suka yi zai bace daga kan kwantent da kake amfani dashi yanzu. Idan kuma ka yanke shawarar dawo dasu daga baya, comments da likes dinsu da suka maka baza su taba dawowa ba.

A bangaren sakonni kuwa, duk wadda kayi blocking nashi hakan bazai kawar da duk sakonnin daka tura ko karba daga garesu ba. Haka zalika shima wadda kayi bulokin dinsa sakonnin ko hirar da kuka yi zai ganshi a jerin hirarrakin da kuka yi. Bugu da kari, babu wani daga cikinku dazai sake ganin sabon sako acikin chat bayan wani yayi bulokin wani.

Yadda zaka gane idan wani yayi bulokin dinka a Instagram

Akwai maganganu kadan akan matsalar bulokin na Instagram. Bari mu tafi zuwa kadan daga cikin saukakan.

Idan anyi bulokin dinka, baza ka iya samun wadda yayi blocking dinka ba koda ta search fonkshon akan Instagram, amma ka jarraba wannan da farko tukuna.

Ka taba/ madannar alamar madubin duba rudu a kasa saika rubuta sunan wadda kake nema wato username; idan bai nuna maka sunansa ba to watakila yayi block naka. Amma akwai dalilai akan rashin nuna maka sunan wadda kake nema ta hanyar amfani da wannan tsarin din. Idan wadda kake nema ya dakatar ko goge asusunsa na Instagram, to zai bace akan platform din tareda dukkan bayanansa, ta yadda baza su nunawa duk wadda yayi searching nashi ba.

Neman su ta wata hanyar daban (ta wani asusun na daban)

Idan anyi bulokin dinka, wannan na nufin kai kadai ne user din baya son mu’amala dakai. Bugu da kari, idan kana son kara tabbatar da wani yayi bulokin dinka to ka bude wani asusun daban — ko bude asusu mabanbanta daga naka na asali — saika yi searching nashi.

Idan har user din ya bayyana lokacin dakayi searching dinsa akan daya daga cikin sabon asusun daka bude, na farko ya nuna bai dakatar da asusunsa ba bai kuma goge shi ba. Idan wannan itace matsalar, to akwai yiwuwar yayi blocking din asalin asusunkanaka.

Ta hanyar duba su akan birawza

Kayi log out na asusunka na Instagram akan browser, saika yi kokarin riskar shafin mutumin da kake tunanin yayi bulokin dinka. Zaka iya haka idan ka tafi zuwa www.instagram.com/[saika saka sunansa nan (username)].

Idan shafin asusun nasa ya bayyana, to bai dakatar dashi ba ba kuma gogeshj yayi ba na asusunsa kawai yayi bulokin naka ne.

Ta hanyar Sakonni 

Ka tafi zuwa Instagram messages dinka. Koda anyi block naka, zaka iya ganin tarihin hirarku dashi

Daga cikin chat, kayi kokarin zuwa profile dinsa. Idan babu wani abu daya bayyana, to akwai kyakykyawan zaton yayi bulokin naka.

Followmeter

Akwai application da muka samo shi abaya mai suna Followmeter. Wannan application ya kasance kyauta wajen amfani dashi; bugu da kari idan kuma kana son sayan sobsikirifshon zai baiwa app din damar shiga asusunka na Instagram, zai fada maka lokacin da akayi bulokin naka — kuma ya fada maka wadda yayi bulokin din naka.

Yadda zaka gane idan wani yayi muting  dinka a Instagram

Abin haushin anan shine babu wasu hanyoyin da zasu sanar dakai idan wani yayi muting naka akan Instagram. A gwajin da mukayi, bawai kai da akayi wa ba hatta shima wadda yayi muting naka ba’a notifying nashi idan yayi unmute naka.

A wannan wurin, ya zama wasan canki-canki. Shin baya son ka da liking post dinsa ko kallon stories nashi? Idan ka duba jerin mabiyanka kaga suna nan, so yayi muting naka. Amma watakila baya mu’amala ne da Instagram din sosai ko kuma yadau lokaci bai hau online ba.

Followmeter

Kamar yadda muka ambata a baya, Followmeter babban app ne da zaka iya amfani dashi kyauta. Ta bangaren sanin wadda yayi blocking dinka haka zalika wannan application zai fada maka idan wani anyi muting naka idan ka sayi premium subscription nasu. Zai bayyana a tab na kasa da alamar Ghost Followers.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button