Technology

Yadda zaka gane idan kayi kira ana recording dinka

Yadda zaka gane idan kayi kira ana maka recording 

Assalamu Alaikum

En uwa barkanmu da wannan lokaci, ayau munzo muku da bayanin yadda zaka gane ana recording din muryarka yayin dakayi kira

Kira a waya haryanzu yana daga cikin manyan dalilan dayasa mutane kan sayi waya da kuma amfani dasu, duk da cewar akwai applications na zamani da suke tura sakon gaggawa akan tsarin gudanarwar wayoyin Android ayau, amma haryanzu kiran mutum a waya shine tsari mafi dacewa musamman ga masu amfani da wayar hannu

Kiran waya na murya yafi saukin sha’ani da saukin samun wadda ake nema a yayinda hirar chat anayin tane da wanda yake da ra’ayi ko sha’awar hakan

Wannan dalilin yasa mafi yawancin mutane suka fi ganewa dasuyi kiran waya na murya musamman lokacin da ake bukatar abu na ujila — amma idan a irin wannan yanayin na bukatar abu cikin gaggawa ka kira mutum, wadda shi kuma daga karshe yake recording dinka ba tare da izininka ba, tayaya zaka gane hakan?

Wasu suna yin haka ne domin bada shaida akan mutum ko kuma wata kafa ta batanci ko aikata munanan laifuka

Wani abun mamakin shine, da yawa daga cikin mutane basa sanin anyi recording din muryarsu sai randa suka jita a kafafen labarai tana yawo sannan suna mamakin ya akayi haka ta faru

Babbar tambayar anan itace: Ta yaya zaka gano ana recording dinka yayin kira?

Na farko:

Beeping Tone During The Call Frequently

A kasashe da dama an haramta wani yayi recording wani mutum lokacin kiran waya ko tracking na sakon rubutu ba tare da izinin mutum ba, saboda haka wasu wayoyin sukan zo da fasahar beeping tone. Irin wadannan wayoyin mai amfani dasu zai danna record buttom, shi kuma dayan yana jin wani dan sauti kadan-kadan kusan a kowane dakika

Wannan irin sauti alama ce dake nuna ana recording din muryarka, amma wanna ba itace damuwar ba a kowane lokaci musamman idan shi wadda yake recording naka yana wurin hayaniya to baza kaji sautin alamar sosai ba, dole kana bukatar nutsuwa sosai saboda sautin ba sosai yake fita ba

Daga karshe, wannan fasahar ba akan kowace waya take aiki ba musamman wayoyin da suke dauke da applications din recording na third-party

A Loud Single Beep At The Beginning Of The Call

Yayin da wanda ka kira yake recording dinka a bangaren kiran akwai wani dan kara (beep) mai karfi da zakaji a farkon kiran, wannan yana aiki akan da yawa daga cikin manyan wayoyin Android na yanzu wadda ake kiran su da ‘Yam’ phones musamman idan an kunna recording feature akan waccan wayar

Amma wani lokacin wanda ka kira zai iya danna wata alamar daza kaji ya bada sauti iri daya da wannan amma a bisa kuskure wadda shima baisan ya danna ba

Hanya ta karshe bayan wadannan, itace kawai ka tambayi wanda kake kira idan yana recording din muryarka ko bayayi.

Mun gode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button