Technology

Yadda Zaka Gane Fake Alert

 En uwa barkanmu da wannan lokacin, barkanmu da sake kasancewa daku a wani sabon darasin.

Cikin shirin mu nayau zamu sanar daku yadda zaku gane alert na bogi wato fake alert.

Muna cikin wani zamani wanda fasahohin cutar mutane sukayi yawa, ta inda wani zaiyi amfani da basirar sa ta hanyar na’ura ya damfari mutane.

A kasa irin Nigeria wannan yana daga cikin abubuwan da yake damun mutane matuka akan komai domin kuwa hakan yana da ciwo sosai. Amma anan ga wasu abubuwa daza kasa a ranka wajen kare kanka daga fadawa cikin irin wannan halin.

Sanannen abu ne cewa ‘yan damfara suna amfani da alert din bogi na banki wajen aikata laifuka. Domin karesu daga cin kudin dabai kamata su mallaka ba yana da kyau kasan wannan.

Wane irin bayanai masu damfara suke bukata wajen tura fake alert?

Suna bukatar abubuwa kamar haka:

Na farko

Lambar wayarka da kuma,

Lambar account dinka

Ba tare da wadannan ba, yana da wahala a garesu su tura maka sakon karya, yana kuma da wahala a gareka ka samesu da zarar ka gane abinda sukayi.

Suna amfani da SIM card na musamman wajen gudanar da wannan aikin wanda shine dalilin. Domin tura maka credit ko debit alert, suna amfani ne da yadda bankinka suke tura maka sai suyi irin nasu su yaudareka.

Yadda zaka san cewa wannan sakon na bogi ne

Kowa zai iya afkawa cikin wannan matsalar, amma akwai alamomi na gargadi da duk wani wanda ya fada irin wannan halin daya sani.

Look for spelling errors

Zasu bukaci ka basu lambar account dinka, haka zalika da lambar wayarka wanda babu bukatar hakan. Wannan zai bude maka kofar cewa ba’a bukatar lambar waya lokacin money transfers.

A lokacin baza kaga wani credit a account balance dinka ba. Amma bank alert na gaskiya zai nuna maka balance dinka duka kafin da bayan sunyi maka gargadi.

Kasan adadin kudinka da yake cikin account kafin nan; idan adadin kudinka da kake dashi na yau yayi daidai da wancan amount din, to lissafinka kalau yake, amma indai ba haka ba akwai matsala kenan.

Examine your email

Kayi checking email dinka wanda yake a hade da bankinka idan ma baka dashi zaka iya kirkirar wani kayi linking dinsa da bankin naka hakan zai taimaka maka wajen sanin dukkan transactions din daka gabatar a lokacin. Kari akan haka, zaka iya ganin account balance da bank statement dinka ta hanyar sakon email.

Kayi checking tushen sakon email din da zarar ka karbi bakon sako daga banki.

The balance won’t be credited

Zaka iya duba account balance dinka ta hanyar amfani da code na bankinka wato USSD ko amfani da mobile banking app, haka zalika ko amfani da online banking ko ATM. Account balance dinka ko bayanin statement zai bayyana idan ba haka ba toh akwai matsala.

Examine the credit alert you receive to see if your available bank is listed

Idan ya kasance account balance dinka bai bude maka tare da transfer payment wanda kwastomanka yayi ba, anan zaka iya ganewa lallai wannan alert din boge ne saboda sakon da bankin masu damfara yake turowa baya nuna amount dinka daya rage a account dinka.

Ka guji danna duk wani link daza a tambayeka bayar da bayanan account dinka, ko ace maka ka bada bayanan account dinka ta hanyar kiran waya, email ko wani application. Ka kula sosai. Allah ya kiyaye.

Wasu ire-iren alert masu muhimmanci daya kamata ka sani

Wadannan wasu daga cikin alert na banki ne wanda suke da muhimmanci sosai, kuma zasu taimaka maka wajen bunkasa harkar bankinka.

Alert for debit card.

Beware of large purchase.

Big ATM withdrawal warning.

Alert for unusual account activity.

Alert for direct deposit.

Low-balance warning.

Notice about profile modification.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button