Technology

Yadda zaka fassara sautin muryarka zuwa yaren da kake so

Assalamu Alaikum, en uwa barkanmu da wannan lokaci ya kuke ya hakurin kasancewa tareda mu, acikin darasin namu nayau zamuyi bayani ne akan wani application wanda yake sananne ne ga galibin masu amfani da Android.

Wannan application sunansa Google Translate wanda kamfanin na Google suka samar dashi. Aikin wannan application bai takaitu akan fassara rubutun text ba akan yanar gizo dana takardu. Zaka iya amfani da wannan service din wajen fassara maka sautin muryarka har wayau.

Zamu sanar daku yadda zakuyi hakan akan wayoyin ku na Android.

Saidai yana da kyau kasan cewa baza ka iya fassara sautin muryarka daka dauka kai-tsaye tareda wannan service ba. Sai dai kayi playing files dinka yayin da shi Google Translate yana sauraron yanda zai fassara maka content dinka zuwa yaren da kake so.

Yanda zaka fassara muryarka a Google Translate a waya

Da farko, ka dauko application wanda yake free ne akan Google Play saika bude shi.

A cikin application din a kasa kwanar hagu, ka bude displayed language.

Daga wurin “Translate From” menu, saika zabi yaren da asalin sautin muryarka yake.

Saika taba language a dama sannan ka zabi yaren da kake son fassarawa zuwa gareshi.

Bayan ka zabi dukkan yarukan, a kasan application din, saika taba microphone iconIdan application din ya tambayi izinin shiga mic din wayarka, ka bashi dama.

Yanzu sai kayi magana da mic din wayarka, misali kayi magana da yaren hausa shi kuma Google Translator zai ke fassara maka maganarka zuwa yaren larabci a misalance kenan.

Zaka iya sauraron fassarar idan ka taba sound icon.

Idan kuma kana son fassara sautin muryar dakayi saving dinsa, kayi transfar su zuwa ga wata wayar sannan ka kunna ta yayinda shi Google Translate yake saurara.

Bugu da kari, idan kana hira da wani wanda bakajin yarensa shima baijin naka, a kasan application din, ka taba “Conversation” option. A shafin dazai bude maka a gaba, dakai da wanda kake hirar za kuke gane yaren juna ta hanyar fassara kowane yare.

A shirin mu na gaba insha Allah zamu kawo muku yanda zaku fassara hoto da  Google Translate app.

Zaku iya sauke wannan application din a kasa

                           Danna anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button