Yadda zaka dawo da asusunka na whatsapp idan an kwace maka shi!

Kamar dai yadda muka sani,manhajar whatsapp na daya daga cikin manyan manhajojin isar da sako cikin gaggawa a wannan zamanin da muke ciki, wadda a yanzu haka a kalla mutane sama da biliyan biyu ne suke amfani dashi daga sassa daban daban a fadin duniya wadda kamfanin facebook ya mallakeshi. Bugu da kari,
kamfanin na whatsapp sun samar da wata fasahar ajiye bayanai saboda gudun masu harkar kutse, wannan dalilin ne ma yasa suka samar da end-to-end encrypted chatting experience. Kuma wannan fasahar tana taimakawa kwarai wajen kare bayanan mutane daga masu kutsen.
Su wadannan masu harkar kutsen zasu iya amfani da duk wata hanyar siddabarun karbo bayanai daga na’ura mai kwakwalwa domin samun lambobin sirri wato OTP domin shiga asusunka na whatsapp a duk lokacin da suke so, ta wannan hanyar kadai idan har suka ketare matakin tantancewa ma’ana barifikeshon kod zuwa asusun din koma wurin su cikin sauki.
Kafin mu shiga zuwa hanyar da za’a bi a dawo da asusun whatsapp idan an kwace, ya kamata mu lura da wasu irin mutane guda biyu wadda lamarin yafi shafarsu sune kamar haka:
1. Mutane na farko sune wadanda suke amfani da whatsapp amma basu taba saita lambobin tsaro ba wato “two-factor authentication” saboda haka basu da lambobin activation.
Wannan yana nuna cewar idan mutum yana da whatsapp kuma bai saita lambobin karin tsaro na ausentikeshon ba toh asusun nasa na whatsapp yana fuskantar barazana. Amma idan mutum ya saka wanna karin lambobin na tsaro to da wahala a karbe masa asusun.
Ga yadda ake saka lambobin
• Da farko idan ka bude whatsapp application dinka saika shiga; setting>account>two-step verification saika zabi lambobi guda shida wadda bazaka mantaba saika saka su bayan ka saka saika danna Done ma’ana kayi activating nashi kenan, saboda haka koda wataran ka rasa wayarka ko ka sayar da ita idan kazo shiga whatsapp dinka wannan lambobin guda shida zasu fara tambayarka daka saka su,
idan ka saka shine zai bude idan kuma ka saka ba dai dai ba toh bazai bude ba sai anbi wata hanyar daban. Idan kasaka wannan lambobin a asusun dinka na whatsapp to ko masu kutse idan sunzo wannan lambobin dai suma za’a tambayesu wadda kuma kai kadai ka santa, daga nan shikenan baka da matsala.
2. Nau’in mutane na biyu kuma sune,sun saita lambobin karin tsaron amma kuma rashin sani yasa sun sanar da masu kutsen kodai ta hanyar hira dasu cewa ka fada musu lambobin sirrinka domin dawo maka da asusun dinka wai an kwace maka shi ko wani abu makamancin haka.
Har wayau dai, akwai hanyoyi da dama da za’a iya dawo da asusun WhatsApp amma sai an kula sosai. Kamar yadda kake kokarin kare asusun dinka daga masu kutse haka suma suke bin duk wata hanya daza subi suga sun samu koda mafi kankantar bayaninka kamar irin lambobi shida na aktibeshon kwad ko OTP da za’a tura maka ta layin wayarka.
Babu wani dalilin da zaisa kaga OTP code ta layinka wadda baka san dashi ba ko kuma bakai ne kayi rigwes nashi ba, to kayi sauri ka goge shi tun kafin wani ma ya sani.
A duk lokacin da mai kutse ya kwace maka account dinka na whatsapp to zai iya karanta duk wani sako daya shigo maka sai dai bazai iya ganin sakon daya gabata ba saboda end-to-end encryption bayan wannan zai iya magana da abokanka ya kuma yi amfani da sunanka ya bata maka shi.
Ga matakan da zaka bi ka dawo da asusunka na WhatsApp:
1. Ficewa daga asusun naka na WhatsApp
Idan whatsapp application dinka yana kan waya to ka sauke shi ma’ana uninstall bayan kayi haka, saika sake dora shi ma’ana install saika shiga ka saka lambar wayarka
2. Zasu turo maka Code guda shida ta layin wayarka ta hanyar sako. Saika saka lambobin.
3. Wannan zai kaika zuwa ainihin asusunka nan take shi kuma wadda yayi maka kutsen zai bar maka asusun naka
4. Daga nan za’a dawo maka da asusun dinka, da zarar komai ya kammala ka tabbatar daka saita lambobin karin tsaro wato tu sitef barifikeshon akan asusun WhatsApp dinka, idan ma kana da adireshin email ka saka shi saboda halin manta pin naka na barifikeshon.
Watakila ka manta PIN dinka na tu sitef barifikeshon zasu tura maka backup ta email dinka, idan aka ce maka ka danna link to karka danna saboda wani zai iya amfani dashi ya sake maka kutse sai a kula.
Ya za’ayi na kare asusuna daga masu kutse?
Kamar yadda bayani ya gabata,karka kuskura ka fadawa wani lambobin six-digit number dinka, kuma saka karin lambobin tsaro na two-factor authentication yana da matukar muhimmanci kwarai da gaske.