Technology

Yadda zaka dawo da asusunka na facebook idan an kwace maka shi.

Assalamu Alaikum, A yau wannan shafin zai kawo muku wasu hanyoyi daza kubi domin dawo da account dinku na facebook idan masu kutse sun sace  shi zaku iya wannan ta hanyar canza lambobin sirri ma’ana “faswod” ko kuma ta hanyar tura sakon neman agaji wa kamfanin na facebook a matsayin bada izininka aka shiga maka asusun dinka ba.

Ga wasu daga cikin matakan da zaku bi domin magance wannan matsalar da ikon Allah.

1. Mataki na farko shine “Resetting your password on mobile”

Da farko zaka bude facebook app dinka,shine wani me kalar shudin duhu da farar alamar fa “f” a kansa wannan zai kaika zuwa wurin saka bayanan ka idan an kwace maka asusun din kenan.

2. Na biyu zaka zaka danna “Need help”.Shi wannan link din yana kasa da wurin saka adireshin email da wurin saka faswod,wani rubutu zai bayyana inda aka rubuta;

• Forgot Password?

3. Saika danna “Forgot Password” da zarar ka danna zai kaika zuwa shafin da zaka canja lambobin sirrinka na faswod dinka.

4. Zaka saka adireshinka na email dinka ko lambar waya,saika danna wurin rubutu a saman shafin da kake, saika rubuta adireshinka na email ko kuma lambar wayar da kake amfani da ita wajen bude asusunka na Facebook.

• Idan kuma baka taba saka/ko kara lambar waya a facebook dinka ba, to sai kayi amfani da adireshinka na email.

5. Sai ka danna “Search” wani shudin rubutu a kasan wurin da kayi  rubutun wannan zai kawo maka asusun naka na facebook.

6. Sai ka danna “account recovery method” ,wannan zai baka zabi guda biyu,ma’ana tayaya kake son sakon yazo maka shin;

• ta hanyar email kake so – facebook zai turo maka wasu lambobi ta email din daka bude asusun Facebook dinka, ko kuma;

• ta hanyar sakon waya ma’ana tes- facebook zai tura maka da sakon tes na wasu lambobi ta layin dakayi rigistar asusun Facebook dinka.

7. Saika danna “Continue” shima wata alama ce me kalar dark-blue a kasa da akawun rikwabari ofshon yin haka zaisa facebook su turo maka lambobin ta email ko tes.

8. Sake neman lambobin kod.

Bayan facebook sun turo maka da lambobin (kod), amma ya danganta da wace hanya ka karbi sakon, idan ta email ne saika shiga akwatin email dinka domin daukar lambobin ko kuma ta hanyar sakon waya(tes) shima saika shiga message domin daukar Lambobin dai guda shida ne facebook yake turawa, kuma sunan sakon ma na facebook din ne.

9. “Enter the code”. Saika danna wurin da zaka saka lambobin kamar haka “Enter your six-digit code” a wurin da zaka rubuta, saika rubuta wannan lambobin guda shida da facebook suka turo maka ta hanyar email ko tes.

• Ka tabbatar baka yi jinkirin saka lambobin ba saboda zasu lalace idan suka kai adadin wasu dakiku baka sanya suba.

• Amma zaka iya danna alamar “Resend Code Option” domin sake turo maka wani sabon kod din.

10. Saika danna alamar “Continue” yin hakan zai kaika zuwaga shafi na gaba.

11. Saika duba akwatin da aka rubuta “Log me out of other devices” saika danna alamar “Continue” da zarar kayi haka duk inda aka saka account dinka na facebook kodai akan kwamfuta (computer), tablet ko kuma wayar hannu (android phone) da aka dora asusun dinka to zaiyi logging out da kansa koda kuwa shi hacker din bai isa ya dakatar da hakan ba.

12. Bayan haka saika saka sabbin lambobin sirri na faswod (ba irin waccan ta farko da akayi maka kutse da ita ba) saika danna “Enter a new password” zaka saka sabuwar faswod a cikin akwatin rubutu yananan akusa da saman shafin.

13. Saika danna “Continue” wannan na nufin ka musanya tsohuwar password dinka da sabuwa. A yanzu kuma zaka iya shiga asusunka na facebook da sabuwar faswod dinka, sannan shi wadda ya kwace maka asusunka din bashi da damar sake shiga ciki, kayi maganinsa ensha Allah.

☆ Mataki na biyu shine zaka turawa kamfanin facebook sakon neman agaji shine dakatar da asusun naka daga aiki

1. Zaka bude shafin da aka kwace maka account  din saika tafi zuwa

https://www.facebook.com/hacked/ akan browser na kwamfutar ka.

2. Saika danna wurin da aka rubuta “My Account is Compromised”. Shima wani shudin guri ne a tsakiyar shafin,yin hakan zai bude maka shafin searching.

3. Saika shiga adireshinka na email ko lambar waya. Zaka danna wurin rubutu ne shima a tsakiyar shafin, saika saka adireshin email dinka ko lambar wayar dakayi rigista da ita wadda kake sakawa yayin shiga facebook dinka.

• Idan baka taba kara lambar waya a facebook account dinka ba,to sai dai kayi amfani da email address dinka.

4. Saika danna alamar “Search” wadda ke dama da wurin rubutu ma’ana text field, wannan zaisa facebook su shiga neman asusun naka.

5. Saika danna “Enter a password” zaka saka lambobin sirri wato faswod din da zaka iya tunawa na account dinka, zakayi haka ne a wurin “Current or Old Password” tes fild.

6. Ka danna “Continue” shima wani shudin alamane a kusa da karshen shafin.

7. Da zarar ya bude maka shafin zasu tambayeka ka zabi dalilin dayasa aka kwace maka asusu kamar haka;

• Naga anyi fostin, an tura sako akan asusu na Facebook wadda bani da masaniya akai

• Wani daban ya shiga asusuna na Facebook ba tare da izini na ba

• Ni banga wani zabi na dai dai ba acikin wadannan jerangiyar zabukan

Zaka zabi daya daga cikin wadannan dalilan, ya danganta da yadda ake maka fostin a asusun din naka.

8. Saika danna “kontiniyu” wannan zai kaika zuwa farkon shafin da aka kwace maka asusun din.

• Idan ka duba daya daga cikin zabukan ba’a lissafo dashi a cikin dalili mai karfiba a baya to zaka kare ne a shafin kulawa na facebook ma’ana shafin bada taimako na Facebook.

9. Saika danna “Get started” wadda ke kasa dama da gefen shafin.Yin hakan zai baiwa facebook damar canza ayyukan da kayi.

10. Saika danna alamar Continue wadda ke kasa dama da gefen shafin.

11. Saika saka sabuwar faswod duka a wuraren da suka rubuta “New text field”da kuma wurin “Re- type New” tes fild.

12. Saika danna “Next” shima shudin rubutu ne a kasa da shafin.

13. Saika duba akwatin dayake kusa da sunan ka,saika danna “Next” yin hakan zaisa a dauki sunan ka a matsayin sunan asusun naka.

• Amma idan baka san wanna zabin zaka iya tsallakeshi zuwa mataki na gaba.

14. Saika shiga wurin da aka rubuta “Edit my information that you did’nt change’ facebook zasu bayyana maka fostin mabanbanta masu yawa da saiti da sauran canje canje aka gudanar, zaka iya amsar wadannan saituna idan har kaine kayi su, koka ki amsarsu koma ka goge su idan wani ne daban yayi maka su batare da saninka ba.

• Idan kuma sun kaika zuwa wurin gyara posting din da kayi zaka iya tsallakeshi ka tafi zuwa wani shafin.

15. Saika danna “Go to News Feed” wannan zai kaika zuwa wurin labaranka na facebook. Yanzu kana da cikakkiyar damar amfani da facebook dinka ensha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button