Technology

Yadda zaka cire duk wani virus akan computer

ssalamu Alaikum

Barkanmu da wannan lokaci, ayau munzo muku da yadda zaku goge duk wata virus data ke cikin na’urar ku ta computer

Kamar yadda wayoyin Android suke dauke da nasu nau’ukan virus din haka suma na’urorin computer suke da irin nasu virus din, wadda sukan shafi lafiyar computer kama daga kan rashin sauri, maƙalewa da sauran illoli.

Kawar da virus a computer yana da sauki idan kabi matakan daya dace. Misali, Windows Defender tana kawar da duk wani gurbataccen files da viruses akan na’urar ka ta computer.

Har wayau, ita Windows Defender tana yin searching da kanta ta kuma kawar da duk wani abu maras amfani data samu. Kai-tsaye ka bude app din security a karkashin taskbar notification area, saika danna alamar kibiya wato Show hidden icons.

Saika danna Virus & threat protection

Daga nan saika danna scan options, amma ka zabi Full scan

Bayan haka, saika danna Scan now a kasa kenan.

Daga nan zatayi scanning na dan wani lokaci, daga karshe zata fito maka da sakamakon virus din data gano. Idan ya kasance babu virus shikenan zata fada maka cewar No threats found

Amma idan akwai virus zata fada maka ka dauki matakin gaggawa akai, shine saika danna Start actions

Daga nan zata kawar da duk wata virus da sauran lalatattun files.

Akwai kuma wasu apps masu kyau da zaka iya amfani dasu wajen kawar virus, da zarar kayi installing dinsu zasu fara maka aikin kawar da duk wata virus automatically.

Ga wadansu daga cikin wadannan apps din na Windows

Avast One Essential

AVG AntiVirus Free

Bitdefender Antivirus Plus

Wadannan apps suna da kyau sosai wajen kawar da duk wata virus da take hana sukuni wa computer.

Mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button