Technology

Yadda zaka boye asusunka na Twitter

Manhajar Twitter wuri ne da mutane ke musanyan ra’ayi da bayyana maganganu na muhawara. Wadda ire-iren wadannan hirarrakin ana yinsu ne da nufin kowa ya gani kuma ya karanta — bayan haka, wannan ke sanya irin wadannan maganganu a fagen farko. Amma tare da kowane irin dalili, wasu mutanen sun zabi su sirranta asusunsu na Twitter kuma da ka’idar shiga, kawai sai dai ya zama dan gayyatar baki. Idan kaima irin wannan dabarar taja ra’ayin ka, to ga mafitar  yadda za’a bullowa lamarin.

Amsa daya a takaice:

Domin mayar da asusunka na Twitter zuwa private akan na’urar desktop da kuma na wayar hannu wato Android, to ka tafi zuwa Settings and Privacy–>Privacy and safety–>Audience and taggingSaika zabi akwatin dake cewa Protect your Tweets.

Yadda zaka sirranta asusunka na Twitter 

Akan desktop bashon na Twitter, zaka tafi ne zuwa Settings and Privacy–>Privacy and safety–>Audience and tagging. Idan ya kaika shafin saika danna akwatin dake cewaProtect your Tweets. Za’a iya tambayarka ka tabbatar da lambobinka na sirri wato faswod domin yarda da abin da kake so. Bayan kayi haka, idan ka kalli duk rubuce rubucenka na Twitter wato tweets daka yi zaka gansu a boye. Sannan mabiyanka suma haka zasu gani, sannan duk wani wadda ke son bibiyarka nan gaba dole zai nemi izinin shiga asusunka domin ganin bayanan ka. Wannan neman izinin kuma za’a sanar da kai ta Twitter notification.

Yadda kuma zaka sirranta asusunka na Twitter a cikin waya (Android ko iOS)

Akan wayar Android ko iOS kuwa, shima tsarin iri daya ne da wancan. Ka taba hotonka na profile a sama kwanar dama.

Saika taba hanyar daza ta kaika zuwa Settings and Privacy—>Privacy and safety—>Audience and tagging. Saika zabi akwatin dake cewa Protect your Tweets.

Me yasa wasu mutanen ke mayar da asusunsu na Twitter firabet?

Akwai yanayin dake nuna sha’awar sirranta asusu na Twitter. Idan misali kana neman aiki, kana son kare dukkan wasu bayananka daga shigar mutane, musamman idan bayanan sun banbanta da sauran bayanai na yanayin yau da kullum. Za kuma ka iya samun kanka a cikin yanayin aiki amma kuma baka son abokan aikin ka ko clients dinka su san ra’ayin ka ko samun wani abu a gareka da zasuna kallonka dashi.

Wani yanayin daban kuma shine, zaka iya tsintar kanka a wata kasar da basa lamuntar abin da kake fada ba, wadda wasu lokutan ma akan dakatar da ita kanta manhajar Twitter din a irin wannan kasashen.

A karshe dai, zaka iya zama mutum kamar kowa dake son cikakken sirri. A irin wannan halin zaka iya kula da wadda zai shigo maka cikin furofayil dinka.

Shin zaka iya neman asusun da aka sirranta na Twitter?

Amsa itace eh, asusun da aka sirranta na Twitter zaka iya sacin dinsa. Amma baza ka iya ganin kowane tweets na wannan asusun ba har sai mai shi ya yarde maka da shiga.

Shin idan kayi likes alhalin asusunka yana firabet shima zai zama firabet kenan?

Idan kayi liking tweets na wani daban karkashin asusunka na sirri, zai nuna akan tweet din dakayi, amma username dinka bazai bayyana ba tare da hotonka na profile da sauran bayananka na zahiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button