Technology

Yadda ake yin restore din China phone ko da an manta password ɗinta

Watakila ka taɓa siyan wayar China da wani ya yi amfani da ita, kuma ka bukaci yi mata restore, amma abun ya ci tura, saboda ba ka san password din da wancan mutumin ya sawa wayar ba – ko kuma wayarka ta na bukatar restore, amma ba ka san password ɗin wayar ba.

Idan ka ci karo da wannan matsalar akwai wata hanya da za ka bi domin yin restore, ko kuma goge komai da ke cikin wayar. Wannan hanyar wasu code ne za ka yi aiki da su da za su ba ka daman yi wa wayarka restore.

https://youtube.com/watch?v=uQ-MxFtiaec%3Ffeature%3Dplayer_embedded

Amma kafin ka yi mata restore ko clear ɗin data ya-na-da-kyau duk wasu bayanai ma su mahimmaci na kan wayar kaman lambobin waya da sakonni ka mai da su kan layi, sannan sai ka cire layin. Bayan ka cire mahimman bayanan da ke cikin wayar sai ka danna *#12345#.

Ka na danna wadannan lambobin za ka ga wayar ta tambayeka kaman haka Do you want to clean all test data?, sai ka danna yes ko OK.

Ka na danna yes ɗin za ka ga wayar ta kashe kanta, kaman ta na yin restore. Amma kafin ka yi haka ya-na-da-kyau ka ɗauke duk wani abu mai mahimmanci kaman sakonni da lambobin waya, da kuma abubuwa kan waya.

Yin clear data zai sa duk wani abu na kan wayar ya goge – kenan duk wani abu mai mahimmaci wanda ba ka so ka rasa shi sai ka cireshi a wayar ka boyeshi.

Za mu dakata a nan da fatan a na amfanuwa da tutorial din da mu ke rubutawa a shafin nan. Sannan mu na fatan sake ganinku a shafin, mu na godiya bisa ziyartar shafin nan da ku ke yi. A huta lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button