Technology

Yadda ake setin satellite

Tauraron dan Adam abu ne mai matukar amfani wajen bunkasar da ilimin kimiyya da fasahar dan Adam a yau.

Satellite shine ido da kunne ga masana masu binciken kimiyya a duniya. Yanzu haka akwai satellite sama da dubu daya su na can cikin sararin samaniya su na aikinsu, wasu su na samar da sadarwa, wasu kuma su na kawo bayanan yanayin duniya da sauran aiyuka.

https://youtube.com/watch?v=ror4P1UAv_g%3Ffeature%3Dplayer_embedded

Ga bayanin yanda satellite ya ke aiki
1. Kafin satellite ya shiga cikin sarari ya yi aikinsa, ya na bukatar isashshen karfi ko sauri wanda zai ba shi daman yin tafiya a cikin sararin sama. Idan satellite ya na waje mai nisa sosai tsakaninsa da doron kasa zai kasance ya na tafiya a hankali wato saurinsa zai ragu. Amma yayin da ya ke kusa da doron kasa kuma zai kasance ya na gudu sosai. Kenan satellite din da ya ke low earth orbit ya na zagaye duniya a cikin lokaci kadan idan aka kwatanta shi da wanda ya ke medium earth orbit ko geosynchronous orbit.

Misali, International space station (ISS), wato tashar sarari ta kasa da kasa ta na sama a nisan kilomita dari hudu (400km), kuma ta na zagaye duniya gaba daya a cikin minti casa’in da uku (93minutes) a takaice. Sannan ta na gudun kilomita dubu ashirin da bakwai da dari shida duk sa’a daya (27,600kmph). Geosynchronous satellite, wanda aka fi saninsa da Geostationary satellite ya na can sama a nisan kilomita dubu talatin da shida (36, 000km), kuma ya na gama orbit din sa a cikin sa’o’i ashirin da hudu (24hrs). Wato ya na tafiya daidai da saurin da duniya take juyawa akan tubalin tsintsiyarta (axis).

Sai kuma GPS Satellite, su kuma wadannan satellite din su na can sama a nisan kilomita dubu ashirin (20, 000km). Sannan su na gudun kilomita dubu sha daya da dari biyu da sittin da biyar duk sa’a daya (11265kmph) a takaice. Da wannan gudun a kullum su na zagaye duniya sau biyu. Wato dai su na zagaye duniya a cikin sa’o’i sha biyu (12hrs). Idan mu ka duba wadannan misalan guda za mu ga International space station ya na zagaye duniya a cikin minti casa’in da uku, GPS satellite su na zagaye duniya a cikin sa’o’i sha biyu, yayin da Geostationary satellite kuma akwana daya. Kena International space station ya fi su sauri, bayansa sai GPS satellite, sanna Geostationary satellite.

2. A yayin da satellite ya ke zagaye duniya akwai lokacin da ya ke barin asalin orbit din sa (hanyar da ya ke bi), misali, kaman International space station ya na sama a nisa kilomita dari hudu idan ya yi nesa da duniya gudunsa zai rage, sai ya yi kasa da nisan kilomita hamsin. Wato ya na tafiya a nisan kilomita dari hudu, idan ya yi nesa da duniya zai dawo kasa daidai nisan kilomita dari uku da hamsin (350km). Wannan canzawar da ya ke daga wajensa na asali ana kiransa elliptical orbit a turance.

Lokacin da satellite ya yi nesa da duniya idan gudunsa ya ragu, ya dawo kasa zai kawo tsaiko na lokaci kadan. To domin magance wannan matsalar akwai wani abu kaman bututu wanda ya ke jikin satellite ta baya. Wannan wajen ana kiransa thruster, kuma ya na futar da gas kaman yanda rocket ya ke yi. A lokacin da satellite ya yi nesa da duniya thruster zai fara futar da gas a jikinsa wanda hakan shi zai dawo da satellite din wajen da ya ke tafiya tun farko.

3. Kafin satellite ya fara zagaye duniya ya na bukatar karfi ko saurin wanda zai sai karfin saurinsa ya yi daidai da karfin gravity. Shi gravity karfine wanda ya ke jawo satellite din zuwa kasa. Satellite ya na samun wannan saurin ta hanyar karfin da rocket din da ya dakkosa. Lokacin da rocket ya dakko satellite akwai nisan da zai kai sai ya dawo kasa a daidai wannan lokacin rocket zai tura satellite ya tafi cikin sarari har sai karfinsa ya zo daidai da karfin gravity – sannan sai ya fara zagaye duniya.

4. Samun daidaito tsakanin karfin gravity da saurin satellite shi zai sa karfi biyun daya ya kasa rinjayar dayan (balanced). Satellite ya na aiki da karfin da ake kira centrifetal force wanda shine ya sa shi ya ke tafiya ya na kewaye duniya. Sannan ita kuma duniya karfin gravity dinta shi ya ke jawo satellite zuwa kasa. Daga nan sai satellite din ya fara aikinsa, idan ya na can nesa sosai sai ya tafi a hankali, idan kuma a kusa ya ke sai ya yi tafi da sauri ko da ya ke bayanin haka ya gabata a sama.

5. Bayan satellite ya samu, ya fara aiki wato ya na tafiya, ya na kewaye duniya zai fara aikin karban sakonni ya na juyosu zuwa cikin duniya. Satellite wadanda su ke a matakin LEO wato wadanda su ke daga nisan kilomita dari da hamsin (150km) zuwa kilomita dubu biyu (2000km) ana amfani da su musamman wajen samar da sadarwa internet da kuma duba yanayi. Sai kuma wadanda su ke matakin MEO wato wadanda su ke daga nisan kilomita dubu biyu (2000km) zuwa kilomita dubu talatin da biyar (35, 000km) su kuma satellite din da su ke wannan matakin ana amfani da su wajen gano inda wani ko wani abu ya ke a doron kasa.

Bayan wadannan biyun kuma sai wadanda su ke GEO, wato wadanda su ke a nisan kilomita dubu talatin da shida (36, 000km). Su kuma satellite din da su ke matakin nan ana amfani da su wajen samar da sadarwar satellite. Akwai satellite masu yawa a matakin GEO orbit, amma guda ukune kadai su ke samar da sadarwar satellite a duniya gaba daya.

Satellite ya na amfani da radio frequency ne wajen kawo sadarwar internet da sadarwar satellite wanda ake kallon shirye shiyen talabijin da sauraron rediyo musamman na kasashen duniya daban daban.

Da fatan ana amfanuwa da abubuwan da ake karantawa a shafin nan. Domin ci gaba da samun darusan kimiyya da fasaha sai a kasance da shafin nan. Duk mai tambaya ya na rubutawa a wajen comment, zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.

Mu na godiya akan ziyarar da ku ke kawowa shafin nan, mu na fatan sake ganinku, a huta lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button