Yadda Ake Kunna Computer

Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokaci, kamar yadda a baya a cikin wannan shirin namu na mu koyi computer, munyi bayanin mecece ita kanta computer da kuma irin ayyukan da dakeyi tare da kuma abubuwan da suka hada computer din. Insha Allah a yau kuma a cikin part 2 na shirin namu za muga yadda ake kunna ita kanta computer din tare da kuma duba cikinta.
Da farko idan kana da computer laptop ko kuma desktop duk sanda zaka kunna ta, ka fara tabbatar da cewa idan laptop ce tana da chaji ko kuma ka jona ta chaji, idan kuma desktop ce ka tabbata ka saka ta a jikin socket idan laptop ce zaka duba wajen keyboard dinka wato inda ake rubutu zaka ga wata alama mai kamar zero and one wato alamar binary number wato yaren da computer take ganewa kamar yadda zaku ga hoton a kasa

Duk inda kaga wannan alamar a jikin computer dinka to itace alamar da zaka dannan domin kunna computer dinka. Haka zalika masu amfani da desktop kuma zaku duba jikin CPU dinku ko system unit dinku zaku ga alamar kunnawa sai ku dannan domin kunna computer dinku

Sannan akula duk sanda zaku kashe computer dinku bayan kun kunna, to ba dannan gurin zaku kara yi ba, akwai hanyar da ake bi a kashe computer a ilimance domin gudun samun matsala. Kar ku kashe computer dinku kamar yadda ku ka kunna ta, idan zaku kashe computer dinku zaku je taskbar a cikin computer dinku zaku ga wajen window button sai ku dannan akwai gurin da zaku ga power button sai ku dannan don kashe computer dinku., Domin ganin cikakken hanyar da ake bi wajen kashe computer dinku zaku iya kallon video din dake kasa da nayi. Nagode sai mun hadu a darasi na gaba.