yadda ake hana waya shan data

Assalamu Alaikum,
Amfani da data a wayar Android ayau yana da matukar muhimmanci. Saboda da ita ne zaka samu damar kasancewa akan layin sadarwar zamani na intanet domin haduwa da ‘yan uwa da abokan arziki dama duniya baki daya.
To amma hakan yana nufin sai kana da datar da zaka cigaba da kasancewa akan layin intanet.
Yanayin farashin data yanzu ya zama abin daya zama, saboda datar tayi tsada kuma ga saurin karewa nan da nan. Wasu sukan kashe datar wayarsu domin samun saukin rage cin datar amma hakan ba shine mafita ba, saboda yayin da kashe datar wayarka kuma babu damar kasancewa online kenan.
Har wayau, akwai wasu dabaru da zaku gwada domin rage yawan karewar data da wuri.
1. Turn On Data Saver Mode
Kowace wayar Android tana da wannan fasahar. Abinda kawai zakayi shine ka shiga ‘Settings’ saika danna mobile data, saika kunna data saver. Wannan zai taimaka maka wajen dakatar da talluka marasa kan-gado da suke bayyana akan wayarka lokacin da kake amfani da ita.
2. Restrict Background Data Use
Background data itace — wasu applications ne da suke aiki a sirrance ba tare da sanin kaba. Wannan yakan sanya zukar data sosai. Applications kanyi amfani data domin gano sakonni, talluka, sanarwa da sauransu.
Ka danna “Connections” ko “Mobile networks”
Saika danna “data usage”
Ka danna kan “mobile data usage”
Daga nan saika cigaba da dakatar da background apps to restrict “background data usage”
3. Set Data Limit
Kayyadewa amfani da datar ka zai kare wayarka daga cin data mai yawa. Hakan zai dakatar dakai daga wuce iyaka. Ga yadda zaka saita data limit:
Ka shiga “Settings”
Saika danna kan “data connection” ko “mobile network”
Saika danna kan “Data usage”
Daga nan saika seta tsarin bill na wata-wata daya dace dakai
Sannan saika kunna shi, zama ka iya kunna data saving lokacin daka fuskanci cewa ka fara riskar data limit dinka
4. Reduce Your Use Of Social Media
Yawan kasancewa akan layin sadarwar zamani/media yana daya daga cikin kyawawan hanyoyin da suke cinye data da wuri. Ka kayyadewa kanka amfani da social media, musamman yadda ka dade akan apps masu cinye data sosai.
5. Use A Data Saver For Your Browsers
Browser apps dinka suma suna cinye data da wuri. Dalili kuwa shine browsers suna samar da hotuna masu quality sosai kuma suna bada dama ga tallukan intanet su hadiye maka data cikin kankanin lokaci. Domin gujewa hakan, ka kunna “data saving mode” akan browser apps din.
6. Reduce Your Data Usage On WhatsApp
Automatic media download a WhatsApp shima yana cinye data da wuri. Domin ceton datar ka, zaka iya dakatar da downloads marasa amfani daga WhatsApp groups ko kuma na sakon personal. Zaka iya downloading nasu idan ka so a lokacin daka bukata. Ga yadda zakayi:
Ka shiga “WhatsApp”
Saika danna “Settings”
Saika danna “Storage and Data”
Saika danna kan “media auto-download” domin dakatar da media auto download
Wannan zai taimaka insha Allah wajen rage karewar data da wuri. Fatan zakuji dadin hakan.
Mun gode.