Yadda Ake Downloading Video Daga YouTube Zuwa Cikin Wayarku Ko Computer

YouTube na daya cikin social media platforms wanda dubban mabiya shafin ke amfani dashi domin saka video a ciki da kuma masu zuwa su kalli videos din, sannan YouTube na bayar da damar masu saka videos samun kudade daga videos din da suke sakawa ta hanyar saka talla a ciki.
Kamar yadda nayi bayani mutane na zuwa YouTube kalli video a cikin manhajjar sai dai akwai wasu video din da zamu gansu a cikin Youtube kuma sun burgemu muna son muyi downloading dinsu daga cikin youtube din zuwa cikin wayoyin mu, amma kuma yawanci ba a samun wannan damar sai dai kawai mutum yayi downloading din video din a cikin Youtube din domin kalla offline.
A yau insha Allah zamuga yadda zamuyi downloading kowanne video zuwa cikin wayarmu ko computer ta hanyar amfani da wani website wanda zai bamu damar downloading tare da zabar irin quality din videon da mukeso. Zaku iya kallon video din dake kasa domin ganin hanyar da ake bi don downloading kowanne video. Nagode