Yadda Ake Bude Folder A Cikin Computer

Barkan mu da wannan lokaci a cikin wannan shirin namu na mu koyi computer, insha Allah a wannan lokacin zamu koyi yadda ake bude folder a cikin computer bayan mun kunnata, kamar yadda nayi bayani a baya mun ga mecece ita kanta computer din sannan mun ga yadda ake kunna ta, insha Allah yau kuma zamu fara shiga cikin ta domin fara amfani da ita.
Yadda ake bude folder a computer kusan daya ne da yadda ake budewa a cikin waya sai dai ita ana amfani da mouse ko kuma shortcut key domin bude folder din, idan ka tashi zaka bude folder a ciki computer dinka abinda zakayi shine a matakin farko ka duba a jikin mouse dinka sai kayi right click ka danna zaka ga option ya fito dauke da bayanai sai ka zabi New daga nan sai ka zabi New folder kamar yadda zaku gani a hoton kasa
Idan Kun dannan gun new folder abu na gaba shine zaku iya sakawa folder din duka sunan da kuke so domin yin haka sai kuje kan folder din shima kuyi right click daga nan zaku ga gun da aka saka rename sai ku danna ku rubuta irin sunan da kukeso folder dinku kamar yadda zaku gani a hoton kasa

Don ganin video din yadda ake bude folder din zaku iya kallon videon dake kasa, nagode sai mun hadu a darasin gaba