Technology

Yadda ake aiki da Rocket

A yau rocket shine abun sufuri wanda ake amfani da shi domin shiga sarari ko aika kumbo, ko kuma harba tauraron dan Adam zuwa sarari. Rocket shine abun sufuri wanda ake harbawa cikin sarari idan za a je duniyar wata idan za a yi binciken kimiyya. To a wannan rubutun za mu yi bayanin yanda ya ke aiki.

Injin rocket kala biyu akwai wanda ake cewa solid propellant engine, da kuma liquid propellant engine. Amma a darasin za mu yi bayanine akan yanda rocket mai amfani da liquid propellant engine ya ke aiki. Saboda ya na da karfi da sauri da karko da kwari fiye d solid propellant engine.

Ga bayanin yanda rocket ya ke aiki
1. Rocket ya na aiki a karkashin ka’idar motsawa wanda za a ce tureni in tureka. Ka’idar tureni in tureka ita ce ka’ida ta uku abun da wannan ka’idar ta ke nunawa shine idan kasa karfi akan wani abu ka na turashi, shima wancan din zai sakama karfi wanda zai turoka baya.

Misali, idan ka dauki balan balan (balloon) ka hura mata iska, ko ka cikata da iska, sai ka rufe bakinta ta yanda iskar cikinta ba za ta futa ba. Daga nan sai ka bude bakin nata ka na bude bakinta sai ka saketa. Ka na saketa za ka ga ta na yin sama yayin da iskar cikinta ta ke yin kasa. Abun da ya ke faruwa shine iskar da ta ke futowa daga cikin balan balan din ta na yin kasa yayin da ita kuma iskar ta ke tura balan balan din zuwa sama.

2. Shima rocket haka ya ke aiki. Daman cikinsa akwai gas masu wadanda wadanda aka tanadesu a cikin wani madauki. Shima wannan madaukin a samansa akwai wani madaukin. Wadannan madaukai guda biyun akwai wani karamin madauki a kusa da su ana kirashin combustion chamber. Madauki na saman shi ake kira fuel tank, madaukin kasan kuma shine oxidizer tank.

3. Yayin da sinadaran da su ke cikin fuel tank da oxidizer tank su ka shigo cikin combustion chamber su ka hadu a take za su fara konewa sai su yi kasa su wajen nozzle.

Rocket staging
Daman wajen nozzle an yi sa a matse wannan gas din da ya ke futowa daga combustion chamber shi ya ke danne iska ta yi kasa, ita kuma iskar ta na tura rocket din ya yi sama. Bayan rocket din ya fara tafiya idan ya yi nisa daman ya na da stage guda hudu. To stage na farko zai yanke ya fado kasa, saboda gas din da suke cikin fuel da oxidizer tank din sa sun kare.

Gimbled thrust
Bayan stage na farko ya yanke ya fado, gudun rocket din zai ragu, sai kuma stage na biyu a take zai fara aiki stage na biyu shima kaman stage na farko ya ke sai dai gas din da ya ke cikin stage na farko ya fi yawa. Bayan stage na biyu ya fara to za a bukaci rocket din ya dan kwanta ko karkace saboda bawai sama zai tafi a mike ba.

Idan rocket ya yi can sama ba a mike ake so ya tafi ba, ana bukatar ya karkace ko kwantawa ta wata kusurwa kadan. Idan zai kwanta ya na bukatar abun da ake kira torque a turance. Torque shine karfin da zai juya abu. Torque ya na samuwane ta hanyar nozzle din jikin rocket din.

Lokacin dai zai karkace nozzle dinsa ne zai karkace, sai rocket din shima ya dan kwanta. Bayan rocket din ya kwanta yanda ake bukata sai nozzle dinsa ya dawo yanda ya ke a farko. Sai ya ci gaba da tafiya. Shima stage na biyun sai ya yanke ya fado kasa.

Stage biyun ya na yankewa, ya fado stage na uku kuma na karshe zai fara aiki ya ci gaba da tafiya har sai gudunsa ya kai saurinsa saurin tafiyar kilomita dubu ashirin da takwas duk awa daya (28, 000kmph) sannan stage na uku zai fado.

Deploying payload
Stage na uku kuma na karshe ya na fadowa, zai tura satellite din daga nan sai satellite din ya bude solar panels dinsa. Sannan ya fara zagaye duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button