Soyayyar Yusuf Da Fadeelah Complete

Soyayyar Yusuf Da Fadeelah
(Short Story)

COMPLETE HAUSA NOVEL DOCUMENT

Nasara Writers Association

Written By
Mummy Ayshatu

This Book Was Downloaded From Hausa Cinema, If You Want To Get More Hausa Novels
Audio Hausa Novels, Document Hausa Novels, Go To Google And Search For ‘Hausa Cinema Novels’ You Will Get And Download Free Hausa Novels In PDF Format, For Free!

Are You A Writer?
You Can Now Upload Your Novels For Free On Our Website And Get Paid; Just Contact Us
With Your Book Details. And Also, For A Copyright Claim, You Can Request To Take It Down Urgently, But Before, Ensure That You’re The Real Owner (Writer).

SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA

Rubutawa: Mummy Ayshatu

Based On Love And True Life Story

Labarin Bai Da Yawa, Idan Ya Yi Tsawo To Ya Kai 10 Page, Da Fatan Zaku Bani Haɗin Kai.

Nasara Writers Association

{{N W A}}

Nasara Abin So Ga Kowa, Domin Marubuta Da Cigaban Rubutu, Alƙalaminmu Ƴancinmu.

Page 1-2

Mafarin Labarin.
Sanyayyer Iskar damina ake kaɗawa me ciki da lullumi da ban sha’awa, misalin ƙarfe biyu na yamma ne, amma sai ka ɗauka irin huɗowar asubahin nan ne, ko kuma gab da magrib, saboda yadda garin ya yi sanyi da duhu ga iska me shiga jiki, sakamakon hadarin da aka haɗa ruwa zai iya sauka a ko wanne irin lokaci.

Tuƙi ya ke cikin kwanciyar hankali da nishaɗi, domin daga Katsina ya dawo cikin garin Kaduna. Duk da tafiyar da ya sha, amma fuskarsa na cike da annuri, wataƙil ko dan an dawo gida ne, dangi masu daɗi musamman idan kana da uwa a raye.

Har ya doshi hanyar komawa gida, sai kuma ya fasa ya nufi gidan abokinsa, daman sun daɗe basu haɗu ba sai ta waya saboda tafiyar nan da ya yi zuwa Katsina.

A ƙofar gidan ya kira wayarsa, fitowa ya yi cikin kwalliya kamar me shirin fita.

“Abokina halan fita zaka yi?” Yusuf ya tambayi abokin nasa me suna Ƙasim bayan shugowarsa motar. “Eh zani Dinner ne, sai Allah ya kawowa bikin wata ƴar uwata ake”

Yusuf ya ce”Cikin hadari irin wannan zaka dinner?”

“Dinner ce ta gida, dole ne shiyasa zani” cewar Ƙasim.

“Ayya to badamuwa bari na saukeka a hanya sai na wuce” Yusuf ya faɗa yana ƙoƙarin tada motar, sai da suka hau titi Ƙasim ya ce”Yusuf amma wasa ka ke? Ai dole ma mu shiga wajen Dinnern nan da kai”

Yusuf bai ce komi ba, kai tsaye ya shiga gidan wani mai da ke hanya ya cika tankin motarsa da mai sannan suka doshi wajen Dinner da ke kusa da Masallaci Al-mannar da ke Kaduna.

Masha Allah amarya Sa’adatu Aliyu Yola tayi ƙyau domin ƙanwa ta ke a gurin Ƙasim abokin Yusuf.

Suna zaune akan tebura suna shan coca-cola idanuwan Yusuf suka sauka a kan wata baiwar Allah ƙyaƙƙyawa son kowa, tuni yaji zuciyarsa ta bugu, zuba mata idanuwa ya yi dan da alama tana cikin dangin amaryar ne.

Kasa jurewa Yusuf ya yi domin sosai yarinyar ta tafi da imaninsa, a natse ya tashi ya fara tafiya cikin natsuwa da kamala, dan Yusuf ba dai ƙwarjini ba. sallama ya fara mata.

A hankali ta dago idanuwanta, sai da Yusuf yaji wani shock, da sauri ya daidaita natsuwarsa,

“Ƴan mata barka da yamma” ya faɗa cikin sanyin murna.

“Barka” ta faɗa cike da natsuwa da jan aji.

“Da farko da sunana Yusuf, maganar gaskiya kin mini, kallo ɗaya naji kin shiga zuciyata ina ƙaunarki, fatana ki zamo uwar ƴaƴana.”

Yusuf baƙi ne amma ba sosai ba, yana da ɗan tsayi amma ba can ba, a kwai idanuwa ga hanci bakinsa madaidaici me jerin zubin haƙora ƙyawawa, ba laifi Yusuf kyakkyawa ne kuma kallo ɗaya zaka masa kasan yana da ƙyirki da iya mu’amula da mutane.
A minti biyar ta ƙare masa kallo ya yin ta furta “Ni kuma sunana Fadeela”

“Ma sha Allah, suna me daɗi” Yusuf ya furta yana sake kallon Fadeelar wacce sai dai muce masha Allah dan tana da ƙyau ba laifi, fara ce siriri amma ba can ba, tana da idanuwa ga hanci tubalkalla laɓɓanta ƙyawawa da madaidaicin bakinta, gaskiya Fadeela ta tara duk kan wani abu da Yusuf ke so a jikin ƴa mace. lokaci ƙanƙani har mun ɗan saba a lokacin na tambayi lambar wayarta ta ba ni.

Bayan an tashi daga Dinner, hadari ya ƙara haɗuwa har an fara yayyafi, hakan yasa Yusuf kiranta a waya “Fadeela idan bazaki damu ba, kizo na rage muku hanya”

Cikin muryarta me sanyi ta ce”A’a kayi haƙuri kar na takura maka”

“Kar ki damu Fadeela babu takura anan, kice ku fito ana kamar harda su Aunty sai na kai ku gida”

“To mun gode” ta faɗa sannan suka fito na kai su gida, Aunty sai godiya ta ke masa domin zuwa lokacin tuni aka tsugage da ruwa…..

Mu haɗe a page na gaba.

SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA

Rubutawa: Mummy Ayshatu

Based On Love And True Life Story

Nasara Writers Association

{{N W A}}

Nasara Abin So Ga Kowa, Domin Marubuta Da Cigaban Rubutu, Alƙalaminmu Ƴancinmu.

Page 3-4

Cikin ƙanƙanin lokaci, soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin Yusuf da Fadeela. Hakan ne ma yasa kai tsaye Yusuf yaje Malumfashi da ke jahar Katsina ya nemi izini a gurin magabatanta kuma suka yadda suka amince da soyayyarsu.
Nan fa sukaci gaba da soyayya ba kama hannun yaro, sosai Yusuf ya yi farin jini a cikin dangin Fadeela ƙannanta maza da mata kowa Yaya Yusuf.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya sosai shaƙuwarsu ke ƙara wanzuwa har ta kai lokacin da akace Yusuf ya turo magabatanshi, ba musu ya doshi hanyar Katsina domin da gaske ya ke auren Fadeela ya ke so yayi daman shi a Kaduna karatu ya ke a salinsa ɗan jahar Katsina ne kamar yadda ita ma Fadeela a Malumfashi aka haifeta tana zaune ne a gaban Auntynta. Ya faɗawa iyayensa kuma sukayi na’am da batun aka sa wa abin albarka, sannan kai tsaye akaje neman auren Fadeela daga gidansu Yusuf, Sun amshesu cikin karamci inda aka bashi kuma aka saka aure wata goma masu zuwa.
Gaskiya ƴan uwanta da ƙannanta suna son Yusuf sosai, saboda hannunsa a buɗe ya ke, mutum ne shi mai yawan ƙyauta.
Duk ranar da basu ganshi ba kuwa sun dingi tambaya kenan, “Yaushe Uncle Yusuf zai zo?” ɓangaren Yusuf ma sosai ya ke ƙaunar Fadeela ko ɓacin ranta baya so, haka mahaifiyar Yusuf tana ƙaunar Fadeela sosai. Fadeela na son Yusuf ita ma kuma tana tsananin kishinsa har ba taso ta ga wata me suna mace kusa da shi, soboda tsantsar ƙaunarsa da kishinsa da ta ke, a kwana a tashi babu wuya a gurin Allah haka lokacin bikinsu ya yi ta ƙaratowa duk da a lokacin Fadeela tana karatu ne a School of health tech makarfi, shi kuwa Yusuf tuni ya kammala karatunsa a KASU yanzu kasuwanci ya ke kuma ba laifi yana samu, yana da rufin asiri daidai gwargwado, haka lokacin biki ya zo ranar wata asabar aka ɗaura auren YUSUF NUHU da amarya FADEELA AHMAD…..

Domin jin yadda za’a gudanar da shagalin bikin mu kasance a page na gaba.

SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA

Rubutawa: Mummy Ayshatu

Based On Love And True Life Story

Nasara Writers Association

{{N W A}}

Nasara Abin So Ga Kowa, Domin Marubuta Da Cigaban Rubutu, Alƙalaminmu Ƴancinmu.

PAGE 5-6

Biki wan shagali, Biki ne na Ƴaƴan gata. An ɗaura auren Yusuf da Fadeela sannan anata gudanar da hidimomin biki.

Anan Kaduna duk akayi wasu shagulgula, in da amarya da ango sukaci ado kamar a sacesu a gudu, da ka gansu zaka hango tsantsar dacewarsu da juna, a ranar bikin aka gudanar da ƙayatacciyar dinner wacce ƴan uwa da abokanan arziƙi suka halatta, komi tsaf amarya taci adonta cikin wani material Ash colour da akawa ɗinkin riga da siket, taci make up, ƙyawun da tayi ma faɗa ɓata baki, ango kuwa cikin ɗanyar gezna shadda riga da wando harda malinmalin, shima Ash wacce ta zauna cif a jikinsa.

Maganar gaskiya amarya da ango sun sha kyau, in da aka gudanar da fatyn cikin kwanciyar hankali, anci kuma an sha sosai, har taro ya tashi lafiya cikin jin daɗi da farinciki.

Da dare aka kai amarya ɗakinta, in da ƴan uwanta suka mata rakiya bayan nasihohin da iyaye suka mata, a Kawo aka ajiye amarya.

Ma sha Allah komi ya yi, dan ɗakin amarya kam Alhamdulillah ya yi ƙyau, two bedrooms da toilet sai kitchen, sai ƙaton parlournta da yaji kujeru na alfarma, komi cif-cif gwanin ban sha’awa. Da dare abokai suka rako ango Yusuf, in da aka haɗu da ƙawayen amarya akayi ta barkwanci daga bisani kuma akayi addu’a tare da yiwa ango da amarya nasiha, in da suka tafi suka bar ango da amarya cikin shauƙi da mararin wannan rana me tarihi a gare su.

Ma sha Allah Yusuf ya ke furtawa domin jin daɗinsa da wannan rana da Allah ya nuna musu, sunyi sallah raka’a biyu tare da addu’o’i domin nuna godiyarsu ga Allah da addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya, tun a lokacin Fadeela ta ce”My love, ɗana na fari in har namiji ne to ina so mu saka masa suna YUSUF” cike da jin daɗi Yusuf ya amsa “To in sha Allahu Allah ya bamu masu albarka” ta amsa da amin. A wannan dare Yusuf da Fadeela sun kasance cikin farinciki da farantawa juna rai sosai.

Washe gari da safe, sai shi ya temaka mata tayi wanka tare da sallah, bayan shima ya dawo masallaci da kansa ya shiga kitchin ya temaka mata sanna bayan kammala komi ya koma ɗakin, kwanciya ya yi sai wajen goma na safe suka farka, tare suka yi wanka sannan ya jata suka karya tana ta mamakin ashe ya iya girki (Ummu Affan ta ce Fadeela ruwan shayin ne girki? Dan shi kaɗai ya dafa, sauran duk a sarrafe suke, sai ƙwai da ya soya. )
Sosai Yusuf ya ke nunawa Fadeela kulawa da tattali watansu guda da aure Fadeela tacigaba da karatunta.

Ku biyoni a shafi na gaba in sha Allahu….

SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA

Rubutawa: Mummy Ayshatu

Based On Love And True Life Story

Nasara Writers Association

{{N W A}}

Nasara Abin So Ga Kowa, Domin Marubuta Da Cigaban Rubutu, Alƙalaminmu Ƴancinmu.

Page 7-8

Fadeelah tana karatunta cikin aminci, Kuma tana kula da mijinta kamar yadda shima dukan tattalinsa da kulawarsa ya miƙa mata.

Sosai suke son junansu da bawa juna kulawa, Yusuf yacigaba da kula da mahaifiyarsa da ke zaune a can Katsina yana bata dukkan kulawar da ta dace haka danginsa bakin ƙoƙari yana kula da su, dangin Fadeelah ma daidai gwargwado yana musu, shiyasa a kullum komi na sa ke ƙara gaba saboda albarka da ya ke samu daga bakin mahaifiyarsa da sauran ƴan uwa.

Yau sun tashi jikin Fadeelah bata jin daɗi hakan yasa a ruɗe Yusuf ya tayata shiryawa suka nufi asibiti. Gwajin farko likita ya tabbatar musu da Fadeelah na da juna biyu, sosai sukayi murna da farinciki da samuwar cikin hakan yasa Yusuf ƙara tattali ga matarsa, komi ta ke so cikin gaggawa ya ke mata.

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah, haka sukayi ta renen cikinsu da bashi kula, cikin na wata huɗu Fadeelah ta fara awo sannan tana ƙoƙarin kare duk wani abu da likita ta ce tayi, shima Yusuf komi yana saya mata domin lafiyarta da ta baby har zuwa lokacin da ciki ya kai wata tara.

Fadeelah ta fara naƙuda amma haihuwa shuru, Auntynta tazo suka runtuma zuwa asibiti amma babu sauƙi, a can ma haka tayi ta fama, duk Yusuf ya ruɗe ya fita hayyacinsa Addu’a ya ke Allah ya sa Fadeelahrsa ta haihu lafiya domin ya tsorata sam bai ɗauka haka haihuwar ta ke ba, kwana biyu ana abu guda likita ya ce sai dai ayi mata aiki domin kar azo a rasata, babu musu Yusuf yasa hannu aka shiga da Fadeelah ɗakin tiyata bayan ya biya komi.

Addu’a ya dungayi Allah ya sauketa lafiya domin tana jin jiki sosai, Alhamdulillah an ciro ƙyaƙƙyawan yaro namiji anyi aikin cikin nasara inda aka gunguro da ita zuwa ɗakin hutu sai hamdala suke.

Yusuf ya rungume yaron ma sha Allah ya furta cike da jin daɗi da ƙaunar yaron yau shima ya yi ɗa.

Fadeelah ta sami barci, haka ƴan uwa da abokanan arziƙi sukayi ta zuwa barka da fatan Allah ya bawa uwar yaron lafiya…..

Mu haɗe a page da ƙarshe in sha Allahu, Daman na ce muku lbrn ba zai wuce pages 10 ba.

SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA

Page 9-10

Kimanin kwanaki biyar Suka Yi a asibitin Barau Dikko aka sallamesu. Alhamdulillah jikinta ya yi k’yau sosai, haka babynta gwanin ban sha’awa.

Sosai Yusuf yaci gaba da hidima da kula da Fadeelah da babynta, Wanda Suka so sakawa suna Yusuf wato sunan mahaifinsa kamar yadda Suka tsara tuni, Amma Sai Inna ta ce ba haka ba (mahaifiyar Yusuf) yaso shawo kanta Allah bai yi ba, abinku ga manya kuma mahaifiya hakan yasa Yusuf ya canzawa yaro suna ya dawo Muhammad.

Bayan sati biyu da haihuwar akasha suna, an d’aga sunan ne saboda aikin da akayiwa Fadeelah, ranar suna Yusuf yayi bajinta k’warai da gaske, komi a wadace inda dangin da abokanan arziki ta ko Ina, gaskiyq abin ya yi k’yau kuma ya k’ayatar da kowa, in da da yamma aka rankashe da kid’a mata Sai rawa suke suna juyi, Alhamdulillah sunan
Muhammad Yusuf Nuhu ya k’ayatar, yaro kam ya yi goshi wato yazo da abin arziki sosai Sai godiya gurin Allah.

Haka Yusuf da Fadeelah sukaci gaba da tattali da kula da yaronsu Muhammad.

Gefe guda ga zazzafar soyayya da sukewa junansu kullum tamkar sabbin aure haka suke.

Sosai Yusuf ke tattalin Fadeelarsa kamar yadda ita ma ke tattala Yusuf d’inta…

Alhamdulillah Sai dai inyi addu’ar Allah ya k’ara soyayya da k’aunar juna yasa haka zaku kasance har a Aljannah.

Anan na kawo karshen wannan d’an takaitaccen labarin me suna Soyayyar Yusuf da Fadeelah Wanda labari ne da ya faru da gaske.

Wanda ya bada labarin shine Yusuf Nuhu wacce ta rubuta Fatima Sunusi Rabiu da fatan d’an labarin ya k’ayatar da ku.

Mu kasance lafiya Allah yasa da mu da duk kan alkhairansa Amin.

Ths Novel Was Downloaded From HausaCinema.Com. For Latest Hausa Novels, Please Don’t Hestiate To Search Our Website On Google, Hausa Cinema Novels. We Provide Pure, Free, Interesting And Educational Hausa Novels For Free.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*