Hausa Novels

SO RIGAR WAHALA

 {=SO RIGAR WAHALA=} =kashi na biyar 5

Related Articles

Tunani gamida rudewa tareda jimamin irin mantuwar da na tafka su suka ramar dani a lokaci guda. Nadan motsa kadan gaba a hankali kamar mai tafiya akan kwai ba tare da ni kaina nasan inda na dosa ba, dan kuwa bansan kowa ba a garin haka kuma bansan ko ina ba ballantana na tafi izuwa wurin. Mantuwar da na tafka ita ta jefani cikin halin da na tsinci kaina a halin yanzu, domin na manta ban karbi adreshin ta ba ga kuma banida waya a hannuna a halin yanzu, sakamakon siyar da wayar da nayi, inda illahirin yan kudaden suka salwanta ta hanyar biyan kudin acaba da nasha yi dan zuwa wurinta hira. Na tsaya nai shiru a wuri guda inda kayana suka fara jikewa da gumi tsabar tunanin da nake tayi. Sa,oi kimanin uku masu kama da kiftawar ido suka shude ina tsaye a bakin kasuwar kamar mai shirin sata tun lokacin da aka saukar dani a mota, karfe tara naga kowa ya fara tattara kayansa dan shirin tafiya gida domin bisa ga dukkan alamu lokacin da suke tashi ya fara karatowa. Na duba motar da ta kawo mu naganta tsaye tun lokacin da ta saukemu, inda lokaci guda na fara hange~hange ko zanga direban domin. Tsawon lokaci can sai na hangi direban tafe ya nufo wurin motar inda lokaci guda na tareshi gamida yimar bayanin duk abinda yake faruwa dani. Ya dan yi shiru kadan na wani dan lokaci inda daga bisani yace dani: malam wlh nima ba dan garin nan bane sai dai in zaka iya kwana a cikin wannan motar to ! Ba damuwa nace dashi inda lokaci muka karasa izuwa wurin da motar take tsaye gamida bude mana ita muka shiga dagani har shi. Muna shiga ya ce dani ka ci abinci kuwa? nace dashi Eh, duk kuwa da cewa banci abincin ba dan kuwa halin da nake ciki a yanzun ba wani abinci da zan iya ci. Na mika hannu na na dauko wani ruwa na dan sha inda lokaci guda mukaci gaba da hira dashi. Tambayata ya fara yi da cewa: yanzu ya zakai kenan? Inda lokaci guda nace dashi a xahirin gaskiya yanzu na yanke shawarar komawa gida da safe dan kuwa banga wata mafita ba in ba hakan ba. Ya danyi shiru wadda bisa ga dukkan alamu yana cike da tausaya min. Muna cikin wannan hirar ne barci ya samu damar daukemu alokaci guda. Sksksksksksksksksksk ke muku patan alkhairi masoyana. Ku kasance dani dan jin cigaban wannan lbrin. NAKU=>HARUNA S~K @Haruna2671 ma 2go user.. 08160821950

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button