SANADIN HIJIRA HAUSA NOVELS

🐫SANADIN HIJIRA🐫
By
💞UMMU FADEELA💞
TYPING📲
CHAPTER 01.
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
(ABUJA NIGERIA)
………..A gaggauce ta ke tura abincin bakinta tamkar zai gudu ya barta,duk ta ‘bata tsakar kitchen din da rice kai kace kaji ne suke dambe a wajen.Tsaye ta ke gaban tukunyar da bai juma ba aka sauke duba da yadda hadadden jollof d’in ke tururi, amma haka take jefa hannu ciki tana dumbusan abincin gami da cusawa a bakinta yayin da rabi ke shiga bakin saura ku ma yake bin jikinta kana ya gangara kasa ya watse.Duk yawan abincin haka ta caccakala shi ta watsar gami da ture tukunyar gefe,ledan biredi dake gefe ta janyo ta yageshi da karfin tsiya ta yanko wanda yafi karfin bakinta har ta nufi bakin dashi sai kuma ta tsaya tana kare mishi kallo kamar mai son karantar yadda aka sarrafa shi,goga shi ta farayi saman kanta da babu dankwali tana bubbugawa da karfi karfi sannan ta cire ta yayyanka shi into pieces da hannunta ta watsar a tsakar kitchen din.Da hanzari ta koma bakin sink ta kunna ruwa ta kafa kanta akai ta fara daddaka like her life depend on it,ruwa tasha fiye da kima sannan ta nufi hanyar fita kamar ba ita ta yi barnar ba.
Kofar kitchen din ta bude a hankali,kanta da babu dankwali ta leka ta tsakanin kofa da jikin ginin,kamar wacce take fahimtar abun da ke faruwa take kare musu kallo.
Hamshakiyar macece wacce ta amsa sunan hajiya ta ko wanne bangare baƙace amma jikinta yana sheki da walwali irin na hutu da jin dadi da suka samu matsugunni a gareta,shigar jikinta ta alfarmace kai kace first lady ce a wajen taron mata HAJIYA FANTA,gefen hagunta wata matar ce itama da za’a kirata da hadaddiyar mace HAJIYA TITI, suna zaune bisa kujera mai zaman mutum uku suna tattaunawa kasa kasa….
Wulkita idanunta ta yi zuwa daya gefen na cikin kasaitaccen palon da ya amsa sunan palo,still akan kujera mai zaman mutum uku wata matashiya ce da akalla zata kai shekaru talatin a duniya,jibgegiya ce sosai irin masu jiki mai gaɓa gaɓa dinnan,tana sanye da vest wadda ya bayyana damatsenta tamkar yar wrestling kanta dauke da hula sai single zani da ta daura hannunta rike da waya tana aikin daddanawa,SAUDAT,kusa da ita wata ce da zata iya kaiwa sa’anta itama katuwa ce sosai kana bata cika tsawo ba,fuskarta farine sol amma pimples yayiwa hasken tarnaki dan ya cika fuskar taf babu masaka tsinke,wanda hakan ke tabbatar da hasken ba nata bane janyoshi ta yi ta hanyar dole duba da hannunta da kafafunta da suka kasance baƙaƙe,sanye take da doguwar riga mai yankakken hannu na shan iska kwance bisa kujerar tayi filo da cinyar Saudat itama tana ta faman danna waya kamar rayuwarsu ya dogara a kaine kacokam.BADARIYYA.
Takawa ta farayi zuwa cikin palon,bata da wani jiki salau salau take kamar ka hureta ta fadi,farace tas dan zaka fi dangantata da larabawa gashin kanta da babu dankwali ya sauko har kan gadon bayanta shi ba fari ba kuma ba baki ba,kacau kacau kacau haka sound na tafiyarta din ke fita wadda ya janyo hankalin mata hudu dake palon gaba daya suka dago suna binta da kallo.Chains ne daure a kafafunta irin wadda ake daure mahaukata dashi hakan yasa duk takun da tayi yake bada kara kacau kacau,duk ido suka zuba mata suna kallonta cike da mamaki dan babu wadda yayi zaton tana cikin madafar.A zabure Saudat dake zaune kan kujerar ta tashi tana zaro idanu kamar zata fire sama ta nufi matar da bata kara kallon gefen da suke ba, “Kan babban*can,ke mahaukaciya yar macukule barnar me kika mana a kitchen?wa ya wuce dake ta nan duk bamu gani ba?me kika aikata mana na ce,”ta kuma fada a harzuke.
“Saudatu!!kul bana son abun da kike yi dinnan,ita sa’ar kice?ko bata haifeki ba ta haifi wanda ya fiki so ki kama kanki bana son ganganci” cewar Hajiya Fanta tana daga zaune a inda take.”Ammafa Ummah kina gani barna ta mana,i believe yanzu kitchen dinnan bazai shigu ba,ga hannunta da jikinta duk ya baci da abincin da masu aikin nan suka sha wuyar dafawa tsabar rainin hankali,da kinga abun da take kinsan sarai da hankalinta,”Saudat ta fada gami da daga hannun matar sama ta sake da karfin gaske.Rufe ido tayi da karfi ta bude tsabar wani irin radadin da taji kamar hannun ya rabu da gangar jikinta..Muskutawa hajiya Titi ta yi tana kallon na kusa da ita cikin kasa da murya ta ce,
“Hajiya Fanta dama har yanzu wannan bakar jarabar tana nan a gidan nan bata bi bola ba?”.Hmmmm Hajiya Titi kenan,idan kuna irin wadannan maganganun mamaki kuke bani,taya zamu barta tabi bola alhali tana damu a raye,wannan lalurace ubangiji ya daura mata kuma a kowanne lokaci zai iya yaye mata,and muma bamufi karfin Allah ya jarabcemu da irin hakan ba” cewar Hajja Fanta cike da imani.”To ai shikenan Fanta tunda ana nuna maki Annabi amma kina rumtse idanu….”Kafun Hajja Fanta ta ce wani abu suka mike gaba dayansu a firgice hadda Badariyya da dama ke kwance a kafar Saudat dazun sakamakon ihun Saudat din da suka jiyo da masifar karfi kamar zai ɓalla palon.Wani irin shaka mahaukaciyar nan ta kai mata bana wasa ba,duk iya kokarinta na son kwace kanta da take yi hakan ya gagara kai kace hannun kattin majiya karfi goma ne aka hada wajen shakarta.
Gabadayansu suka nufosu a sukwane ganin numfashin Saudat na kokarin bankwana da gangar jikinta ga idanunta da suka kwalalo waje,duk su ukun suka hadu da nufin kwatar Saudat amma juyi daya mahaukaciyar nan ta yi sai gasu dukkansu a kasa sun zube wanwar,da hannu daya ta rike Saudat daya hannun kuma ta dinga jibgansu dashi kamar wacce aka aikota yayinda a nasu bangaren suke jin dukan tamkar saukar rodi a jikinsu gashi kuma sun kasa tashi dan ba karamar buguwa sukayi da tiles dake shimfide a wajen ba.
Da kyar Hajja Titi ta iya mikewa kasancewarta mai rangwamen girman jiki,tana gama mikewa ta ranta a na kare ko gyale bata yafa ba bare aje ga batun daukar jakarta dake saman kujera da wani irin gudu ta fice a palon bayan ta sanya takalmi wari daya ta rarumi daya kuma a hannunta motar ta ta fada mai gadi ya wangale mata jibgegen kofar ta bar gidan tana ta sauke numfashi.
,,,,,,,,__
A can ciki kuwa,ta maza Badariyya ta yi ta kwaci kanta,da taimakonta Hajja Fanta itama ta mike suka yi ta kansu,gaba daya sai mahaukaciyar ta koma kan Saudat sai bugunta take kamar ta samu buhun dawa,yayinda Saudat ke ta kururuwa tana kiran “Ummah come help me”….Fanta da ta samu ta tsere bayan curtains ta shige ta buya sai zaro ido take tana hada zufa kamar wacce ta hadiye kunama,tunda uwarta ta haifeta jikinta bai taba shan bugu ba irin wannan.Badariyya kuwa kitchen ta nufa a sukwane….
Tun tana wanka a dakinta dake upstair take jiyo hayaniya da ihu a downstairs kamar da muryar Mommynta dan haka tana fitowa ko ta kan kayanta bata bi ba ta sauko da gudu daga ita sai towel yarinya ce da bazata fi shekaru goma sha biyar ba,kana ganinta kaga Saudat dan yadda suke kama…”Subhanallahi Mommmyyyy!”ta fada da karfi sai kuma ta juya a guje har jikinta na rawa ta koma dakinta,hakan kuwa ya yi dai dai da fitowar Badariyya daga kitchen rike da wani murdedden tabarya,bata yi wata wata ba ta mukawa mahaukaciyar tabarya a kafa,aiko a take ta saki Saudat ta durkushe a wajen tana sakin wani irin azababben ihu,kama Saudat dake kokarin kaiwa kasa tana ta shafa wuyarta Badariyya ta yi ganin haka Hajja Fanta ta fito itama.
Tana shiga dakin ta rarumo wayarta hadi da daddanawa ta kara a kunnenta kirjinta sai hawa da sauka yake,ji take kamar bazata samu wadda take nema ba dan shi kadai ne zai iya dakatar da abun da zai faru a gidan nan yau……
Driving yake a kan babban titin Murtala Muhammad Way dake a unguwar MAITAMA a babban birnin Abuja,wakar Justine Bieber na (Love me,love me)ne ke tashi cikin motar.Wayarshi ce ta fara tsuwwa kamar bazai dauka ba har saida ta kusa katsewa ya kama yana karawa a kunnenshi sai dai bai ce komai ba.Daga daya bangaren ta fara magana da dan sauri sauri,”Unclee where are you?idan kana gari kazo gida babu lafiya…..Bayani ta fara mishi sai dai bai jira ta gama ba ya yanke wayar kittt gami da karawa motar tashi speed kamar zai tashi sama,kasancewar ya kusa dama minti goma ya shigar dashi street nasu da ke hadadden anguwar nan MAITAMA dake cikin kwaryar abuja,shine unguwa na biyu mafi tsaruwa da tsadan gidaje bayan ASOKORO,mazauna unguwar rikakkun yan siyasa ne masu rike da manyan mukamai a gwamnati, da kuma masu harkokin diplomasiyya,sai few manya manyan yan kasuwar kasarnan….
Horn ya danna a bakin wani babban get da ya kasance baki mai yarfin golden a jiki,danna hancin motar ya yi zuwa ciki bayan mai gadi ya wangale mishi kofar,daga inda yake yana iya hango dandazon ma’aikatan gidan da suka taru waje guda dukkansu,kusan mutum goma sha biyar.ko parking mai kyau bai yi ba ya balle marfin motar cikin zafin nama ya fito,suna hango fitowarshi gaba daya suka watse a wajen kafun ya riskesu.ba tare da ya bi ta kansu ba cike da karfi da izza yake takowa har cikin wani varender mai dan fadi ya shiga sannan ya bude main door corridor ne dogon gaske a wajen,yayi tafiya mai dan tsayi kafun ya zuge wani faffadan door glass ya jefa kafarshi cikin tsararren palon da ya yi nasarar lakume setin kujeru guda biyu amma kamar babu komai cikinsa tsabar girma.
“Ya Salam!” ya furta yana dafe goshinsa gami da lumshe matsakaitan idanunsa ganin yadda palon ya yi kaca kaca,gaba daya kujerun dake palon sun kwanta upsidedown,glass center table ya tarwatse a wajen showglass manya guda biyu duk sun zama tarihi,wasu manyan madubi da aka kawata jikin ginin palon dasu suma sun farfashe,rike take da tabaryar sai rotsawa wawakeken television dake wajen tamkar Allah ne ya aikota ta ke,duk farin fatarta ya baci da jinin da glasses suka yayyankata.
“Ammi!!”ya fada cikin sanyin murya mai cike da tausayawa halin da ta ke ciki.Cak ta tsaya da abun da take yi,duk da cewa murya kasa kasa ya ambaci sunanta,hakan bai hanata jin kiran ba,juyowa ta yi ta sauke idanunta a kan takalminshi na sojoji dake sanye a kafarshi har zuwa kan wandonshi da ya kasance na sojoji shima,cigaba da daga kai ta yi har zuwa sama.yana tsaye harde da hannuwanshi saman faffadan kirjinshi ya tsura mata idanunshi da suka yi jawur kamar garwashin wuta.Fari ne sol kamar ka taba shi jini ya fito haka kuma dogone na gaske yana da zagayayyen fuska mai dauke da idanu matsakaita masu lumshewa,sai dogon hancinshi da ya sauka har kan kyakkyawan bakinshi mai dauke da redlips,babu gashi ko kadan a fuskarshi hakama kanshi babu wadataccen gashi alamar yana yawan yin aski hakan na nuna alamar shi din cikakken Soldier ne,tsaye yake kyam a kan kafafunshi sanye cikin kakin sojoji wanda ya yi masifar amsarshi tamkar dan shi aka kirkiri aikin soja.Wani irin dariya ta fashe da shi har idanunta na zubar da hawaye bayan ta gama kallonshi sai kuma ta juya ta cigaba da bugun tvn still bata daina dariya ba.
“Ammi!!plsss stop it”. ya kuma fada with low voice,kamar wanda yace ta kara ta cigaba da bugu iya karfinta,zuwa lokacin temper na shi ya fara hawa,sosai yake kokarin ganin ya yi calming kanshi down dan ganin bai shouting at her ba,idanunshi sun kada sosai jijiyar wuyanshi sun mimmike.ya kuma fadin “Plsss Ammi ki dainaaa”.amma kamar yana kara mata kaimi ne.
“I said stop it!!!!!!!”.
Ya fada da wani irin sound da ya karade illahirin gidan duk girmanshi kuwa,a ta ke ta sake tabaryar ya zame kasa jikinta ya dauki rawa kamar ana buga mata ganga,su Hajja Fanta da Saudat da Badariyya da suka makale a daki suma duk sai da suka firgita amma sun ji dadin mai takaita musu wahalan yana gari ashe,da sauri Humaira dake sama ta sauko itama jin unclee ya iso.Sosai jikin mahaukaciyar ke rawa,babu abun da ta tsana a duniya irin shouting yanzu ne zata rikice gabadayanta,takowa ya fara yi zuwa inda take ganin yadda jikinta ke cigaba da mazari har tana kokarin kaiwa kasa ga hawaye dake ambaliya saman fuskarta…Ganin yana tunkarota ta yi azamar durkusawa ta damko tabaryar da ta saki tana nunashi dashi kamar dai mai yi mashi gargadin kar ya iso gareta,bai fasa matsowa ba hakan yasa ta daga tabaryar sama da iya karfinta ta kai masa bugu lokacin da ya iso gareta…Cikin zafin nama ya rike tabaryar ba tare da ya sameshi ba,kokarin dambe ta farayi dashi hakan yasa shi kuma katsamata wani tsawa da ya fi na dazu,wani irin kara ta saki tana toshe kunnuwanta da cigaba da kururuwa kamar wuta ne ya kama a jikinta hannayenta duka biyu ya kama ya rike da karfi ya dauketa har zuwa dakinta dake nan downstairs.
Tana turje turje da ihu mai cike da kururuwa amma bai direta ba sai akan kyakkyawan gadonta dake cikin hadadden dakin da bazaka taba zaton mahaukaciya ce ke rayuwa a ciki ba.Saman gadon ya kwantar da ita cike da taka tsantsan ya zaro wani injection a aljihun bayan wandonshi,yasan idan har ta gani ba karamar dambe zasu kwasa ba anan kafun ya samu nasarar yi mata.Bata ankare ba sai saukar allura taji a jikinta,sai dai bisa mamakinsa bata kara wani yunkuri ba sai ma kafeshi da tayi da idanunta masu tsananin kama da nashi,wasu irin hawaye masu turereniya da juna suna bin kuncinta da wani irin gudu.kasa ya yi da kansa dan sometimes tana yi masa irin wannan kallon dake rudar dashi dan haka baya daurewa kallonta a irin lokacin.Kamar daga sama kamar a mafarki,kamar kuma a zahiri yaji bakinta yana motsi ta ce.
"AMEENULLAHI!!!!"
A dan firgice ya dago kanshi ya daurasu a kanta,wani irin murmushi ne ya subuce mishi wanda ya kara kawata kyakyawar fuskarshi,shekaru goma sha biyu ba wasa ba,shekaru goma sha biyu ta kwashe ba tare da ta furta sunanshi ba sai yau,shi kam wani irin godiya zai yiwa ubangiji,tun yana saurayi dan shekara ashirin take cikin wannan hali gashi yau ya zama matashi mai 32yrs.
“Ya Allah” ya furta yana tattare fatan goshinsa waje daya kafun ya dan rankwafo yana leka fuskarta ganin allurar baccin da ya mata ya fara aiki,inda yake adana first aid box a dakin nata can saman wardrobe ya janyo,ciwukan da taji ya goggoge mata ya shafa mata aidine addu’a ya tofe ta dashi sannan ya ja mata duvet ya juya ya bar dakin fuskar shi dauke da matsananciyar farin ciki da duk wanda ya sanshi zai sha mamaki ganinshi a hakan.
*_
A palo ya samu Hajja Fanta da ma’aikatan gidan suna ta aikin fitarda kayan da suka farfashe,almost an fitar da komai na palon dan ya tashi aiki except kujeru,da dan sauri ta nufoshi,.”Dan Albarka ka dawo ashe?kaga yau kuma da abun da muka tashi ko?wannan lamari dai Allah ya kawo mana karshensa ya bata lafiya”Cewar Fanta tana matsar kwallah.Fuska ya daure tamau kamar bai taba sanin wani abu dariya ba ciki ciki ya ce,”You don’t worry Ummah”daga haka baice komai ba ya kama kafar bene ya fara haurawa,kai ta dago ta bishi da idanunta dake cike da tausayawa rayuwar dan nata.Cije yatsa Saudat ta yi da karfin gaske tana ji kamar taje ta shake shi ko zata huta da takaicin duniya,Badariyya kuwa jiki na rawa ta bi bayanshi Saudat na rakata da harara,gefen Ummah ta raba zata wuce ta yi saurin cafko hannunta, “To sarkin rawan jiki ina zaki je,ke kullum sai kin nuna kanki a gaban Son?waya fada miki ana nunawa namiji rawar kai haka?”.
Fisge hannunta ta yi da karfi tana yamutsa fuska ta ce, “Ni dai kawai Anty ki barni babu ruwanki gaskiya” daga haka ta nufi saman,sake baki kawai H.Fanta ta yi tana binta da kallo.
Yana isowa bakin palonshi dake sama tana isowa cike da kwarkwasa tana makale murya ta ce, “Sojana zuwa haka kwatsam babu labar….” kafun ta kai karshe ya watsa mata birkitattu kuma lumsassun idanunshi,murya chunkushe fuska a miskile ya ce yana daga hannu, “Look Badar, i need rest plsss”.Bai kara bata daman cewa komai ba ya banko kofar hadi da murza makulli…..
*BORNO STATE*
*4:30pm BAMA LGA*
Karfe 4:30 na maraice a garin Bama dake jihar Borno.Sassanyan yanmacine mai cike da ni’ima dake kadawa ta ko ina,kowa ka gani cike yake da farin ciki.
(NUJUMUL HUDA TAHFIZUL QUR’AN)
Babbar makaranta ce ta islamiyya wadda farfajiyarta ke cike makil da al’umma zazzaune bisa kujeru na roba dake jere a cikin rumfuna da aka kawata wajen dasu,gefen dalibai daban,gefen sauran jama’a daban kana daga can tsakiya akwai wata rumfar da manyan malamai ke zaune da kuma manyan baki na mussaman.Sautin karatun qur’ani ke tashi cikin daddadan murya wanda ke alamta taron yaye dalibai da suka haddace qur’ani mai girma ake a wajen.
“ALLAHU AKHBAR”gaba daya jama’ar dake wajen suka furta bayan yarinyar dake saman stage ta kai karshe a karatun da take yi,mai gabatar da jawabi ya yaba mata sosai lokacin da ya karbi abun magana sannan aka bukaci daliba ta gaba,muryarshi dake fita ta cikin mic ne ya karade wajen “Daliba ta gaba ita ce, (FANNAH MODU BULAMA)”.
Cikin jerin daliban dake wajen ta mike cike da nutsuwa mai bayyana kamala,baƙa ce sosai babu abun da ke da haske a fuskarta sai idanunta da fararen ciki suka kasance fari sol baƙaƙen kuwa baƙiƙƙirin,sai kuma jerin hakwaranta da idan ta yi magana ko tayi murmushi suke bayyana haske,amma sabanin wannan baƙace irin sosai mai walkiya ɗinnan.Doguwace fiye da shekarunta duk da kankantarta tana da cikar halitta mai daukar hankalin mai kallonta,kirjinta a cike yake dam dam kana tana da hips mai fadin gaske wanda ya taimaka wajen shafewar cikinta tamkar babu hanji a cikinsu,tana da manyan mazaunai da idan tana tafiya suke juyawa su kadai kamar da gangan take yi sai dai hallita ce kawai ta ubangiji,bakar fuskarta dogone irin oval shape dinnan mai dauke da dara daran idanu masu yalwar lashes gazar gazar da bakinta mai dan fadi kadan da cikakkun lips irin masu tsoka da tsaga tsaga a kansu tana da dogon hanci da wani tsago da ya taso daga saman goshinta passsss har zuwa karshen hancinta,gashin girarta kuwa tamkar da pensir aka zana mata shi sun kwanta mai kyau da cikar gashi tamkar zasu hade da juna,da ka ganta kaga typical KANURI, a misalce bazata fi shekaru goma sha biyar zuwa sha shida ba FANNE Kenan ko muce FANNAH MODU BULAMA.yarinya mai kirar manya.
Mubi alkalamin Ummu Fadeela da kyau dan ganin ina ta nufa da mu ne wannan karon kuma?Da alama zamusha yawo a tsakanin ABUJA DA BORNO.
Ya Allah kasa Annabi MUHAMMAD S A W ya cecemu🙏.