Entertainment

Sabbin Dokokin Da Ake Zargin Gomnatin Bola Tinubu Zata Kafa Ga Masu Yin Wa’azi A Nigeria

Anba da shawarar kafa dokoki da sharuɗɗa kafin malami ya fara wa’azi a Nigeria kamar haka.

1- A tabbatar da dokar lasisin wa’azi

2- A tilastawa dukkan kungiyoyin addini dasu sake sabon register akan sabbin dokokin
kasa

3- A lura da asusun dukkanin wata kungiya da kuma yadda take sarrafa dukiyar yan kasa da ke
aljihun ta da sunan sadaka

4- Sannan a nemi takardun nan da ake
karantarwa, ayi syllabus na wa’azi na bai daya, Kamar yadda akeyi a Saudiyya, Egypt Dubai Qatar Morocco da sauran qasashe.

5- Duk Malamin da yaki tsayawa akan syllabus za’a iya kwace license din shi sannan a hukuntashi.

6- Sannan duk wanda aka samu ya hawa mimbari ko darasi yana zagin dan’uwan shi musulmi ko kiranshi da wani suna da bai yarda dashi ba
a kama shi a ɗaure.

7- Duk wani mutum ko kungiya daya kibin dokoki za’a daure shi shekaru masu tarin yawa, Wannan shine babban jihadi da za’a iya yi
domin ceto al-ummar Musulmi da samar da zaman lafiya tsakanin su.

Kuma wannan shi zai kare samar da irin su Maitatsine da Su Shekau masu Bok0 Haram nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button