RUGUNTSIMI COMPLETE HAUSA NOVELS

1⃣RUGUNTSUMI!
®NAGARTA WRITER’S
ASSOCIATION
WRITTEN BY
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
STORY BY:
Hauwa M. Jabo
EDITTED BY:
Benaxir Omar
Lokaci – lokaci yakan kai kallo ga agogon sa
dake d’aure bisa tsintsiyar hannunsa, fuskar nan
tasa sam babu walwala saboda ya tsani abinda
bature ke kira da (African time).
Yanzu kam ransa ya gama baci, idan kayi
la’akari da yawan tsakin da yake Ja, yau ya
tashi da nishadi duk lokacin da ya tuna yau ne
yake cika shekara 28 da haihuwa, sai ga
abokinsa Ahmad yana nema ya bata masa
lokaci wajan zuwa partyn da budurwar sa Teena
ta hada masa.
Sunyi dashi k’arfe bakwai da rabi zai zo ya
d’aukesa amman gashi yanzu ana neman k’arfe
takwas harda rabi na dare, gashi abokansa sun
isheshi da kira bama kamar Teena ba, wacce
kusan ko wane minti daya sai ta kirasa.
Izuwa wannan lokacin ransa yakai matuka
wajan baci kiris kawai yake jira yai bindiga ya
fashe.!
Wayarsa yazaro daga cikin aljihunsa yasake
gwada lambar Ahmad sai dai har yanzu ba a
daina ce masa (is not available) ba, bacin
ransa yafi na d’azu, a fusace ya mike tsaye da
niyyar yayi tafiyar sa koda kuwa bisa mashin
ne, dama yaso ya hau machine ya wuce tun
dazu sai yayi tunanin ba ajinsa bane a gansa ya
sauko saman machine
Jin karar mota a bayansa yasa shi saurin
juyawa, kicibin idonsa cikin na Ahmad, idonsa a
hankali suka kankance ba tare da saninsa ba,
cikin tsananin bacin rai yake kallon, sam baiyi
murna da ganinsa ba, illa ma wani mugun
haushinsa daya kamasa.
Dogon tsaki yaja tare da saurin kauda kansa
tamkar ma bai sanshi ba.
Da sauri Ahmad yafito daga cikin motar yasha
gabansa tare da riko hannunsa gaba daya yana
fadin
“Dan Allah Jan kayi hakuri wallahi matsala
aka samu, tun 6:30 na shirya na fito gida
nashiga mota, sai kawai tsoho na yakira ni wai
na kaisa gidan abokinsa Alh Hamza, wallahi dan
kawai banida ikon cewa bazanje bane, shiyasa
nayi fuska nakaisa haka nan”
“Sannan nayi ta k’ok’arin naga na sameka a
waya amman inaaa sam hakan ya faskara, kayi
hakuri abokina nasan ban kyauta ba.”
ya fada yana kokarin tallabo habarsa, yana mai
murmushi.
Zuciyarsa ce ta danyi sanyi ba tare da yace
komai ba, ya lumshe idonsa a hankali ya
bud’esu, ya juya ya nufi motar Ahmad,
murmushi Ahmad yayi ya rufa masa baya,
Ahmad yaja suka fara tafiya, tare da kure karar
kid’an motar, yana girgiza kai alamar yanajin
d’ad’in yadda kid’an ke fidda sauti.
Yadan karkace kai yakai dubansa ga JAN
wanda ke kallon gefen titi da alama har yanzu
bai gama hucewa ba, ganin hakan ne yasa
yafara jansa da hira jefi jefi, amman sam JAN
yayi tamkar badashi yakeyi ba, yaki tankawa.
Ganin hakan ne yasa Ahmad rage gudun da
yakeyi ya gangara bisa gefen titi yayi parking.
A fusace JAN yace
“Wane irin rainin hankali ne haka? Ya zaka ja
ka tsaya alhalin kasan cewa jiran mu akeyi!?Kai
ni idan kana takama da wannan rubabbiyar
motar ne zaka min wulakanci bari insauka inbar
maka abinka!”
Yafara kicin – kicin bud’e Marfin motar, dariya
Ahmad ya kwashe dashi yana fad’in.
“Au! Aini da na dauka kurma na d’auko acikin
motar tawa. Ashe yana magana har ma da
fitsara, ya za ai na maka mutunci na d’aukoka a
motata kana wani daure min fuska, kana
kumburi kamar wani fulawa, shi yasa na faka
idan ka sauko daga dokin zuciyar sai mucigaba
da tafiyar! Koya ka gani?”
Ya fada yana ma JAN kallon tak’ama .
Tsaki kawai JAN yayi yakoma yazauna
yasaki kofar.
Ahaka suka k’arasa wajan taron wanda ke
shake tam da yanmata da samari….
2⃣RUGUNTSUMI!
Nan da nan kallo yadawo kan motar su JAN,
kasancewar su kadai ake jira.
Teena ce ta taho cikin wani irin salo mai
d’aukar hankali, tana tafiya gaba daya jikinta
rawa yakeyi, har ta k’araso gaf da motar kafin
ta sanya hannu ta bude murfin motar inda take
da tabbacin cewa nan JAN ke a zaune, gaba
daya ta zube a jikinsa, cikin sigar shagwaba
take fadin
“JAN meya tsaida ka harzuwa wannan
lokacin ?? Kaduba fa yanda gunnan yacika duk
kai daya ake jira har friends d’ina sun fara mita
dan gajiya, wasu har sun tafi.”
Duk wannan maganar tanayin shine da
harshan turanci kasancewar ta yare hausar bai
wani zauna a bakin taba, dago kanta yayi yana
kallon cikin idonta ahankali ya manna mata
sumba a goshinta yana fadin
“kinyi k’yau sosai sweetheart” fari tayi da
manyan idanuwanta, tace
“Harma na kaika? sweet JAN”
murmushi yayi wanda yasa kumatunsa lotsawa
alamar dimple, dan yatsanta ta tura acikin
ramin tana wasa a gurin.
“Sweet JAN ina k’aunar wannan dimple d’in
naka,” murmushin yakuma yi yace
” Yanzu dai tsaya nayi miki my sweet
Teena.?”
Gilashin motar aka kwankwasa, wanda ya sa
suka dawo hayyacinsu, Ahmad ne wanda tuni
yadade da barin cikin motar, yace
“To jarababbu kufito ku ake jira kun tara
jama’a kun wani kunshe a mota kuna……”
Dasauri JAN yatari numfashinsa da fadin
“To d’an sharri babu abinda mukeyi! Tallafota
yayi suka fito daga cikin motar nanfa DJ yasaki
kida, ihu aka soma yi anayi masu tafi saboda irin
haduwar dasukayi, nan dai aka shiga gudanar da
komi yanda yadace cikin tsari irinta yan boko,
kokuma ince irinta manyan yan bariki wayanda
suka san kan duniya,
Anci ansha an cashe son rai ansha an bugu
sam baka iya tantance dan musulmi da akasin
hakan acikin su, hidimace irin ta yayan bariki
wayanda suka san hannunsu, daga k’arshe
kowanne yaja hannun budurwar sa suka kara
gaba.
JAN ne kamar kullum yayi wanka ya dauki ado
da ganin sa kaga namijin Duniya, Sai dai ba abin
Duniyar, kwalba ce ba Mai, sabida duk layin su
bazaka sami wanda yakai JAN wanka ba,
a haka ya fito kamar bayason taka kasa.
“Mamasko ni zan fita,”
Yar dattijuwar matar ta kalleshi, cikin fara’a da
addu’a samun sa’a.
Ya fito yana murmushi kai tsaye shagon
Abokinsa ya nufa domin ya sami rancen 1k, Sai
dai anyi rashin sa’a abokin nasa baya nan sai
kanin sa, tsaki yaja hadi da cusa hannun sa
cikin sumar kansa da taji mai sai kyalli takeyi.
Jiki a mace ya fito shagon yayi tsaye yasa
hannun hagun sa ya rike kunkumi yana shafar
kansa da dayan hannun sa,
Wata mota ce Kirar mercedez Ta faka, wata
dattijuwar mata ce ta fito sanye cikin shiga ta
alfarma,
Tana tauna chingam a hankali har ta k’araso
kusa dashi, a hankali ya daga kai ya kalli
dattijuwar matar, wanda ya haifar masa da wani
mummunan faduwar gaba, ya rasa gane me
yakeji game da ita, lokaci daya itama dattijuwar
ta dago Ido suka hada Ido dashi, gaba daya
kanta ne ya kwance, hakan yasa hatta tafiya ta
kasa yi, ta dabirce har ta matso kusa dashi, a
hankali ya sako mata wani murmushin da ya
kara rudar da ita, ba ita kadai ba hatta shi a
rude yake a lokacin saboda dukkan su sun rasa
gane yanayin da suka samu Kansu a ciki.
Bata bata lokaci ba ta mai magana hadi da
tambayar sa kwatancen wani gida….
3⃣RUGUNTSUMI
Ya shagala da kallon ta har ta Kare bayanin
inda take nema, Amma kuma shi bai ma ji me
take fada ba, saida ta maimaita masa sannan ya
gane Ina ta nufa, ya gane gidan da take nema
Sai dai da Nisa daga nan zuwa can hakan ya
basu damar shiga motar ta dan ya nuna mata
gurin.
Tunani dukan su sukeyi tun bayan shiga motar
da yace mata ta mike wannan hanyar har takai
karshen hanyar yana tunani ,tana tunani,
Dukan su suna jin junan su har cikin Ransu,
wani SO ne da shakuwar junansu sukeji Wanda
ya haifar musu da matsananciyar kasala hadi da
dogon tunani,
Dattijuwar ce ta dawo cikin hayyacin ta lokacin
da ta masa wani kallo, Amma Ina shi ya fita
zurfafa.
“Bamu kawo bane har yanzu?”
Ta fada tana mai rage gudun motar kadan, a
hankali ya dawo hayyacin sa, ya juyo ya kalleta
ya maka mata wani gigitaccen murmushi,
Wanda saura kiris ta saki kan motar da take
sarrafawa cikin gwaninta,
Dauke kansa tayi daga kallon ta a hankali ya
furta,
“Mun saki hanyar tun chan baya, sorry ban
kula bane, sai mun dan koma baya kadan.”
Ba tare da damuwa ba ta juyar da kan motar
ta koma baya, har suka isa gidan da take nema,
bata bari ya tafi ba saida ta karbi number sa
hadi da masa babbar kyauta, wacce zan iya
cewa tunda yake a Duniyar nan, bai taba rika
50k a hade ba sai yau.
Murna kamar ta kashe shi, ya fito neman 1k
Allah ya bashi 50k daga kwatance.
Gaskiyar magana yafi jin dadin ganin matar akan
kudin da ta bashi, saboda wani jinta yakeyi cikin
ransa Wanda ya rasa gane dalilin hakan, gefen
gidan ya koma ta yanda zai hango ta, har ta
Kare abin da take ta wuce yana labee yana
kallon ta.
Hajiya ma ta rasa nutsuwarta tunda ta hadu
da yaron take jin ta rasa sukuni, jiki a mace ta
karasa Abuja.
Wani katafaren gida ta nufa Wanda ko a
Maitama ,Shi gida ne na alfarma, Gida ne da ya
amsa sunansa gida,tayi Horn ba bata lokaci aka
bude mata ta shiga cike da tak’ama ta
gogaggun mata wayanda suka san kan duniya,
Wayar ta ce tayi kara, ta duba hadi jan tsaki, har
wayar ta stinke batayi ko gigin daga wayar ba.
Ta fito da key ta bude kofar ta shiga a gajiye
saboda tayi doguwar tafiya, ta fada saman wata
sofa dake gefen palon, wayar ta, ta janyo ta fara
Nemo number Dan saurayin da ya tafi da duk
wata nutsuwa tata, saurayin da ko sunan sa
bata sani ba, saurayin da take jin kamar sun
shekara suna tare, ta danna number sa.
Duk da cewa ya dade yana farautar Kiran ta,
hakan Bai sanya tana Kira yayi gaggawar dauka
ba, Sai da ya dauki lokaci sannan ya daga cikin
son jin muryan wacce yake tsammanin ji.
Itace kuwa, sun gaisa cikin natsuwa da kulawa
a kowane bangare
“Sorry baka gaya min sunan ka ba,”
Murmushi yayi mai sauti, Wanda da ace gaban
hajiya yake da sai tayi suman zaune.
“Sunana JALAL AMEEN NAZEER Amma
abokai na suna kirana da JAN“
Sunan ya mata dadi, cikin natsuwa ta
maimaita JALALUDDEN
Sunyi waya sosai, har take tambayar sa aikin
da yake, ya gaya mata shi student ne, ba tayi
gigin gaya masa abinda ke ranta dangane dashi
ba haka Shima bai fada mata ba, Amma kowa
yana jin dayan sa a ransa.
A haka suka Kare waya cike da kewar junan
su, hajiya cike da shaukin Jalal, yinin ranar ta
maimaita sunan nashi yafi a kirga.
JAN kuwa bai tambayi sunan ta ba, kuma da
gangan yayi haka, saboda ya sami wata dama
da zai kara jin muryan ta, tabbas yana jinta har
cikin ransa, gaba daya ya rasa natsuwar sa
yinin ranar,
Baima gane yayi xurfi ba saida dare, lokacin da
yazo bacci anan komai ya chanza, kasa bacci
yayi, anan yayi amfani da damar sa ta dazu ya
danna Kiran wayar ta ba tare da damuwar komai
ba.
“Sorry Hajiya na manta ban tambayi sunan ki
ba, kiyi hakuri na kiraki cikin dare kila ma mai
gidan yana kusa,”
Zuciyarsa ce take harbawa lokacin da yace mai
gidan ta, saboda bayason yaji amsa wacce yake
tunanin zata iya tarwatsa masa kwakwalwarsa
cikin daren nan idan yajita.
Daurewa yayi Amma kuma zuciyar sa ta
chunkushe,
Daya bangaren kuma Hajiya dariya tayi ta
manyan mata wayanda suka san kan duniya,
kasa hakuri yayi yayi sauri ya katse wayar, cikin
mamaki Hajiya ta kara Kiran sa, amma sai ya
sami kansa da kasa daukar wayar, karshe ma
kashe wayar yayi saboda zullumin amsar da zai
samu daga bakin Hajiya……
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.blogspot.com
RUGUNTSUMI 4—-6
By Hauwa jabo 00:29 No comments
5⃣RUGUNTSUMI
NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION.
WRITTEN BY:
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
STORY BY:
Hauwa M. Jabo
EDITTED BY:
Benaxir Omar
Wayar tayi kusan 20mnt a kashe, karshe Ya
kasa hakura kawai ya kunna wayarsa, ko second
biyar ba’ayi ba sai ga sak’on Hajiya,
“Lafiya naji wayar ka a kashe? Idan ka kunna
let me know.”
Ajiyar zuciya yayi hadi da shafa fuskanshi.
Bangaren Hajiya kuwa tana ganin delivery
report alamar sakon ta ya shiga jiki na rawa ta
danna kiranshi.
Bai dau wani lokaci ba ya daga, saboda ya
kagu ya k’ara jin muryan ta
“Lafiya ka kashe wayan ka?”
“Sorry Hajiya batir din ne yake bani matsala,
Amma insha Allah gobe zan siyo wani'”
“No no noooo! Ka bari gobe zan aiko maka da
waya, dazu ban baka amsar tambayoyinka ba,
sunana Hajiya Kubra sannan mijina kuma”
Gaban shi ya fadi had’i da sarkewar yawu,
Wanda yasa yayi wani guntun tari,
“Sannu ko ba kada lafiya ne!?”
Ta fada cikin kulawa,
Saboda hankalin ta ya tashi jin yana tari,
“No I’m OK,”
“Yauwa, Nace mijina Allah ya masa rasuwa
tun shekaru 15 da suka wuce banida yara,
yarona Allah ya masa rasuwa shekara 13 da
suka wuce,”
Wata nishadantacciyar ajiyar zuciya yayi, hadi
da feso iskan bakin sa waje,
Cikin jin dadi lafazin ta yace,
“Allah yajikansu Hajiya,”
Nan dai suka yi hira sosai Wanda zai kaisu
kusan awa uku suna waya, ko wannen su baya
son rabuwa da Dan uwan sa a lokacin, da zance
daya ya Kare, sai daya ya kirkiro wani aci gaba
da hira, har Sai da dan chajin wayarsa ya Kare
Tass sannan aka daina wayar.
Cike da tunanin juna suka kwanta, sannan
aka kwana da tunanin juna, abinda yafi ba ko
wannen su mamaki yanda suke jin juna a
zukatan su.
Baza su iya fassara shi da sunan SO ba,
saboda abin da sukeji yafi gaban Soyayyah
budurwa da saurayi,
Wata shakuwa ce sukeji wacce ba Wanda yasan
asalin ta bare tushen ta kowa yana jin haka a
tare dashi.
Tun da safee ya wuce gurin Mai chajin layin
su saboda basu kwana da wuta ba kuma yana
son yaji ya kwanan Hajiya Kubra, Amma kuma
rashin sa’a mai chajin bai bude ba.
Jiki a mace ya dawo gida, dabara ta fado
masa ya dauko wayar Mamasko ya cire sim
card dinta ya chusa nasa, mssg ne suka shigo
har guda hudu, biyu tana tambayar lafiyar sa,
daya sai da safee ta masa, dayan kuma good
morning ne.
Murmushi yayi ya bata amsa cikin tsananin
kulawa.
Siyayyah ce take gudana a gurin nan Hajiya
Kubra da JAN ba kama hannun yaro kuma
soyayyah din nan duk cikin waya suke darzanta,
ba Wanda ya sake ganin wani ita tana Abuja shi
kuma yana Nasarawa state, kulawa ta ko wane
bangare, har takai hajiya tana nema masa
transcript a Abuja saboda ya dawo nan yaci
gaba da karatunsa, ya Aminta da hakan sai dai
baya jin zai iya barin Mamasko ba, saboda haka
dole yasan yanda zaiyi da abarsa.!
Kamar kullum JAN tare da abokin sa Ahmad
suna bubbudawa kamar yanda suka saba, JAN
akwai wanka har na daukar hankali, gashi da
kwarjini a idon mutane,
Bazamu tsaya siffan tashi ba kawai dai zamuce
yes JAN ya had’u iya haduwa.!!!
RUGUNTSUMI6⃣
Tafiya sukeyi ta takama, duk inda suka gifta sai
an bisu da kallo, bama kamar JAN ba, wanda
idan kaganshi sai ka rantse d’an wani
hamshakin mai arziki ne saboda tsabagen iya
daukar wankansa bayan wankan ne kawai ba
aljahu..
Tattaki sukeyi acikin unguwar bawai dan sunsan
inda zasu ba, saran su kenan dama, da zaran
yamma tayi za a dau wanka na fitar hankali,
ashiga zagaye unguwa daga k’arshe ayima
majalisa tsinke, nan za a zauna zaman kashe
wando har zuwa sanda za ai kiran magrib.
Ahmad ne yadubi JAN yana fad’in “wai kai
baba yau naga sai wani shan kamshi kakeyi hala
hajiyar taka bata taboka bane yau??”
Wani irin kallo yayi masa sannan ya dauke
kansa ahankali yayi dan tsaki,
“gabana keta faduwa yau tun safe!”
Yakarasa maganar yana sosa kansa, haka dai
gaji da zama suka mike suka ci gaba da zagaye
unguwa shiga nan fita can daga k’arshe suka
yada zango a dayar majalisar su wanda ke
shake da matasa irinsu, ana ganinsu aka fara
ihu irin ta matasa ana fadin JAN! JAN!! babban
yaro! Wani irin gaisawa suka shiga yi da hannu
irin ta matasa daga k’arshe suka zauna aka
shiga hiran, duniya,
“Wow Kaya!!!!!!!”
Gaba dayan su suka kai dubansu wajan, dan
sunsan me kalmar ta Najib take Nufi
Cikin natsuwa take takunta kanta akasa
tamkar wacce batason taka kasa, doguwa ce
sosai, saidai tanada kira mai kyau, wanda ake
kira da Coca-Cola shape, ta hadu iya haduwa
tamkar ita ta zana kanta, daganin shigar jikinta
kasancewa babbar yarinya ce! Da alama kuma
hutu yazauna ajikinta, kalar fatarta tafi kama
data y’an hutu,
Lokaci daya gaban JAN yayi mugun faduwa
jikake Ras!! Rasss!!!! Ido yakuramata saikace
tsohon makahon daya warke daga makanta,
Azuciyar sa kuwa fadi yake tsarki ya tabbata ga
ubangiji makerin wannan yarinya! Sam yakasa
samun natsuwa jikinsa har wani kyarma kyarma
yakeyi, gaba daya hankalinsa ya dauku akanta,
tuni sauran abokan nasa sundawo haiyacinsu
kallo yakoma kansa, shikuwa ko kifta ido bayayi
dahaka harta bacewa ganinsa tashige wani
lungu, Ajiyar zuciya mai k’arfi yasauke tare da
shafa sumar kansa da hannunsa na dama,
dariya suka kwashe dashi gaba d’ayansu suna
fadin “wannan kayan kalar kace JAN” saidai tuni
hajiya tayi mata fincinkau” acewar Ahmad
wanda ke leka fuskar JAN, harara yasakar
masa yana fad’in
“nace maka ina sonta ne?? Komai ka maida
ni?? Watau gani na mamajo sarkin mata ko??”
Dariya Ahmad yafashe dashi wanda yasa
JAN fusata haryakai masa duka, dariyar dai
Ahmad yacigaba dayi, wani wawan tsaki JAN
yayi ya mike a fusace zai wuce, kirara suka
shiga yi masa wanda yasashi murmusawa dole
ya koma ya zauna,” haba JAN! JAN kud’i, JAN
gida , JAN mota. Na hajiya Kubra bada kanka
asare kaje gida kace ya fad’i.”
Haka dai suka ci gaba dajansa har zuciyar Sa
tayi sanyi, dama shi saurin fushi garesa ga
zuciya naban mamaki.
Najib ne yace kut!!! Amman fa baba Aradu
yarinyar can akwai k’ugu kutumar uba Kai
wannan y’a ta hadu k’arshe…..
www.fiddausi.wordpress.com
www.jabohauwa.wordpress.com
7⃣ RUGUNTSUMI
NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION
WRITTEN BY:
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
STORY BY:
Hauwa M. Jabo
EDITED BY:
Benaxir Omar
Suna tsakiya da maganar wannan kayan da suka
gani, wayar shi tayi kuka a hankali ya fito da ita
daga aljihunsa, cikin tak’ama da isa ya fara
magana, kasancewar duk dandalin nasu ba mai
waya iPhone 6 sai shi.
Hajiya ce cikin sauti mai d’aukar hankali ya
daga wayar ya fara magana.
Munjiyo muryan Hajiya tana cewa
“Bebena Ina son ganin ka fa, sabida Ina
tsananin kewar ka.”
Wani murmushi yayi, Wanda Saida ya saka ya
rufe ido ya bude su a hankali, duk lokacin da
yake waya da hajiya yana samun kansa cikin
natsuwa da nishadi.
Soyayyar su hadi ne daga Allah bawai sune
suka hada Kansu ba., shakuwar har ta wuce
tunanin mai tunani.
Wannan ne karo na farko da hajiya ta nemi
JAN akan yazo Abuja gurin ta, bayan kokarin da
takeyi na maida shi garin gaba daya.
Baiki tayin nataba, sabida Shima yana son ya
k’ara ganinta ko zai sami peace of mind.
Sun Kare waya akan Saturday zai shigo ya
ganta.
Gaba daya wayar da yayi da hajiya ta mantar
dashi wasu kaya da jabir yake tadin an gani.
Guntun tsaki yayi
” Man ka mana shiru please, wannan fa
karamin kaya ce da zakabi ka rude a kanta”
Ahmad yace,
“Ai dole kace kananan kaya ne tunda kana
tare da manyan kaya.”
Gaba daya dariya suka saka.
Suna mai kirari da na Na hajiya Kubcy.
Shi kuwa sai wani shan kamshi yake yana daga
gira.!
Haka suka Kare sunbatun su, suka watse da
buruka kala kala.
Zaune yake yana chin tuwon da Tsohuwar sa
ta kawo masa, jefi jefi suna hira.
“Yauwa Mamasko, wallahi ina tunanin skull
zasu maidani Abuja da karatu, sabida Ina cikin
students dinda ake alfahari da su a makarantar.”
Wangale baki tayi sabida kusan duniya ba
abinda uwa takeso gaba ga samun ci gaban
yayan ta.
Babu musu ba komai ta fara masa addu’ar
samun nasara.
Tausayin ta ne ya kama shi, har yaji kamar
ma kada yayi tafiyar, Amma Ina bazai iya barin
hajiya ba, dole yaje yayi tozali da wacce take
sanya shi farin ciki.
Cikin kwarewa ta yaran da suka san kan
duniya yace
“Kinga Mamasko jibi Saturday, zanje na cika
wasu form kila zanyi sati daya a chan mi xan
kawo miki daga Abuja.”
Baki sake Mamasko tace
“Ba matsala Allah ya maka albarka ya kaimu
jibin, ni idan kaje lafiya ka dawo lafiya ya fiye
min komai.”
Nan dai sukaci gaba da hira tsakanin da da
mahaifi….
Mamasko sunan da Jalal yake Kiran ta dashi,
Amma sunan ta na asali Hajjo Sa’adatu ne.
Su biyu ne a gurin ta, shi sai yayarsa Jaleelah,
wacce tayi aure tun tuni harda yayan ta kusan
6.
Sun taso cikin rufin asirin Allah, asalinsu Yan
Kano ne, tsangawamar dangin miji yasa Hajjo
Sa’adatu ta bar Kano ta dawo Nasarawa state
da zama, inda anan tayi renon yayan ta Lokacin
Jalal yana da shekara 7 a Duniya, Jaleelah kuma
shekara 8, da gadon mijinta ta data samu ta
sayi gida a nan Nasarawa state ta zauna itada
yayan ta.
Bayan Yan shekaru anan ta sake yin Aure,
Amma mijin sai ya tsangwami yayan nata, tuni
ta kashe auren ta dawo tarbiyar yayan ta,
wanda farin cikin su ya fiye mata komai a
duniya.
A hakan tayi ta Sana’ar ta har ta samu karbuwa
a unguwar, kuma tana tafiye tafiye tana siyo
kaya tana badawa sari, akai akai takanje Kano
gun dangin iyayen ta da wannan ta shahara,
kuma duk unguwar an Santa.
8⃣
JAN ne yake hada kayan sa don zuwa gurin
hajiyar sa, wacce Saida ya zabi mafi kyan kayan
sa, wasu ma sababbine ya siya, sannan ya ma
Mamasko sallama ya kama hanya sai Abuja..
Bai Sha wahala ba sabida tun daga lokacin da
ya shiga mota suke waya da Hajiya, idan kaga
baya waya to network ne ya dauke, har ya iso
garin Abuja.
Bata bari aka k’araso tasha ba tasa aka sauke
shi ta dauki kayan ta suka wuce gaba.
Murna a gurin su ba’a magana kamar su hadiye
juna dan farin ciki.
Hajiya ta chaba ado irin na rikakkun matan da
suka san kan bariki, sai wani fari da Ido takeyi,
shi kuma sai narkar da nashi idon yakeyi, kowa
dai da kalar salon Jan hankalin da yakeyi.
A kan hanya ta tsaya ta masa siyayyah sosai
har suka isa gida, hira sukeyi suna chin abinci..
Wani bakon abu da suka fuskanta shine
kunyar junan su sukeji, sai suka ijiye akan
Soyayyah da kunya ai ita ce soyayyah.
Sun Kare cin abinci sannan suka dawo suka
zauna Palo, hajiya ta tsinci kanta da tsananin
kunyar JAN, Shima hakan kunyarta yakeji sosai
da sosai, sabida haka yau dukda tsananin jin
JAN da takeyi aranta ta kasa fuskantar shi da
zance wani abu makamancin abinda takeji a
ranta.
Haka yayi kusan sati daya amma ba abinda ya
shiga tsakanin su, illa tattalin juna hadi da
tausayin juna da sukeji,
Kusan kullum sai sun fita, duk wani guri na
shakatawa saida Hajiya takai JAN, kuma haka
zata kasa ta tsare kayan ta, duk da cewa idan
yana tare da ita baya ganin ko wace irin mace a
matsayin mace, hakan bai hanashi hango kayan
da suka fi na gaban sa ba.
Hajiya gata a matse sabida duk satin nan bata
samu fita rage zafi ba, gashi gobe zai koma
gida.
Sabida hakan ba zata iya barin sa ya koma a
hakan ba, dole sai ta biya tata bukatar.
Waya tayi da kawar ta ta gaya mata halin da
take ciki.
Kawar tata tayi mamaki, sabida tasan Hajiya
Kubra ko cikin Yan bariki ita karshe ce, sabida
idan taga namiji ranta ya biya idan shine
limamin masallacin garin to sai tasan yanda tayi
ta biya bukatanta dashi, kuma ba asiri ba komai
kawai dai makirci da kissa irin na tsohuwar yar
bariki.
“Haba Hajiya kamar ke wannan yaron…..”
Hajiya tayi sauri ta katseta
“Please! banason dogon sharhi, nasan abinda
xaki fada, nidai ki gaya min ya zanyi, yau kissa
bata aiki yaseen..”
Dariya kawar tata tayi sosai, ta tabbatar da
cewa abin ya girmama da har Hajiya ta kasa
samun kansa, sannan tace,
“To nidai idan irin haka ta faru dani nakanyi
kokari na saka musu kwaya ne su fita hayyacin
su, sai kuma na basu maganin karfi ta yanda
jikin su bazai mutu ba kinga basa cikin hankalin
su kuma ga karfi na musamman da suke samu,
to komai lafiya kenan.”
Dariya suka sheke da ita, daji kaji manyan
mata. Haka tabi shawarar kawarta.
Batayi kasa a gwuywa ba ta nemi abinda aka
umurceta ta saka masa, duka biyun kuwa ta
samu, ta saka masa a gurinda bazai gane ba,
nan danan ya fita hayyacin sa.
Saidai matsalar ita ta kasa bashi kanta, gashi
tana gani available, kuma wannan shine last
chance da take dashi, karshe itama sai ta yanke
hukuncin kawai bari dai tasha kwayar.
Tasha sosai kuma ta kara bashi yasha, dukan
su hankullan su sun fita fita jikkunan su, sannan
suka sami damar aikata abinda zukatansu suke
muradi.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.!!!
Www.hauwajabo.blogsport.com
www.jabohauwa.wordpress.com
www.fiddausi.wordpress.com
8⃣ RUGUNTSUMI
NWA
Written by
Fiddausi Sodangi
Hauwa Jabo
Shine yasoma farkawa tamkar a mafarki haka
yake ganin lamarin, zuciyar sace tayi wani
mummunar bugawa a rikice yake duban jikin sa
yana duban hajiya wacce keta sharar bacci
hankalin ta kwance.
Haka nan yatsinci gabansa na fad’uwa lokaci
zuwa lokaci. Yafi minti goma yana zaune bisa
gadon sai raba ido yake tamkar wani tsohon
munafuki, sai nazari yake a zuciyar Sa shi kam
tunda yake taraiyya da mata bai taba cin karo
da irin hakan ba,
“JAN!!! JAN!!! Hajiya ce ke kiransa cikin wani
irin rikitaccen murya mai rikita y’an maza,
lalubar gadon tashiga yi alamar tana neman sa
kuma hary yanzu bakinta bai bar kiran sunan sa
ba “JAN!!!”
Hannunta ya koma yarike da sauri ya saki
wani irin yarrr!!! Yaji ajikinsa, a hankali tashiga
bude narkakkun idanuwanta akansa, bai san
sanda murmushi ya kufce a bisa fuskar sa ba,
shikam yanajin hajiya kubra har a zuciyar sa.
Jawo sa tayi a jikinta tafara sarrafa shi cikin
k’warewa irin ta manyan y’an bariki way’anda
sukasan yau da gobe a harkar.
“Yau satin Jan d’aya a gidan Hajiya Kubra, sun
gurji juna son rai. Jan jinsa yake tamkar awata
sabuwar duniyar yake, harwani haske yakara da
kiba acikin y’an k’wanakin nan. Sam baimaso ya
tuna cewa gobe zai koma nasarawa duk kuwa
dacewar y’ar tsohowar sa nanan makale a
zuciyar sa.
Gaskiya hajiyata wallahi zanyi missing dinki
sosai idan nakoma, yafad’a yana mai dubanta,
wani irin fari tayi masa da ido tare da kid’asu ta
kara shigewa Jikinsa tace karka damu Jan
nanda sati biyu zaka dawo nan gaba daya, kaga
babu abinda zai kara mana shamaki dajuna koya
kace?” takare maganar nata tana mai shigar da
idanuwanta cikin nasa, ajiyar zuciya yasauke
yace Hajiyata wallahi banaso ina nisa dake kona
sakan daya, murmushi mai kayatarwa tayi tace
my sweet Jan! Kanada babban matsayi a cikin
zuciyata.
Murmushi yasaki Wanda harsar da wushiryar
sa ta baiyana kumatun sa ya lotsa, d’an
yatsanta ta tura cikin ramin tana wasa dashi a
hankali tayi magana acikin kunnansa tamkar mai
rad’a Jan inason wannan dimple din naka yana
kara kayatar da fuskar ka, murmushi yakuma yi
yace har kin tuna min wata budurwa ta Teena!
Tana bala’in son dimple dinnan itama. Dif hajiya
ta d’auke wuta tare dayin kicin kicin da fuska
tamkar ba ita ba, nan danan Jan yasha jinin
jikinsa, fuska a murtuke ta dubesa kanajina ko?”
ni macece mai tsananin kishi akan abinda
nakeso sam banida mutunci akan kishi, dan haka
ka kiyaye karka kuma ambatar ko wace mace
agabana kai ko a baya nama ban baka iziniba!
Ta karashe maganar cike da izza.
Jikinsa a sanyaye yake dubanta, kai Jan
kalle ni nan? Na rantse da Allah zan iya kashe
kowace yarinya akanka! Wallahi zan iya aikata
komi akanka dan haka ka kiyaye baka bakowace
irin mace a duniyar nan! Ido waje Jan ke
kallonta zuciyar sa tamkar zata fad’o kasa dan
bugawa…
9⃣ RUGUNTSUMI
NWA
WRITTEN BY:
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
STORY BY:
Hauwa M. Jabo
EDITED BY
Benaxir Omar
Tun da yaji maganar hajiya akan wata mace
yasan cewa tana da kishi, haka komai ma
zata’iya aikatawa akanshi, ganin haka yasa yayi
Alwashin bazai kara zancen wata gaban ta ba,
koda kuwa Mamasco ce.
JAN da Hajiya sun d’and’ani zumar junan su, ta
yanda ba abinda zai iya rabasu da juna sai dai
mutuwa, saboda suna baiwa junan su kuluwa ta
musamman.
Da kyar ta barshi ya dawo gida.
Bayan ya baro Abuja da sati daya.
Hajiya ta kasa hakuri da rashin sa kusa da ita,
haka tayo balaguro har Nassarawa ta biyoshi ta
kama Hotel, anan suke holewarsu son ransu.
JAN shida Mamasco suna hira kamar yanda
suka saba duk daren Allah, saboda duk dare sai
sunyi hira shi da tsohuwarsa, duk son da yake
yiwa Hajiya Kubra baya iya barin Mamasco yaje
gunta ya kwana, sai dai su yini tare, tun safee
idan yasa kafa ya fita baya dawowa sai dare,
hakan yasa Mamasco bata gane komai ba,
saboda baya kwana chan, ranar ma da taga
sammakon nashi yayi yawa take tambayarsa mi
yake fita yayi a waje tun safe har yau assabar
da ba karatu. sai yace mata kawai duk yana
k’ok’arin cika takardun komawa Abuja ne, ita
kuwa sai tayi ta zuba masa addu’a da fatan
Alkhairi.
Kamar kullum yau da dare ya dawo a gajiye,
saboda hajiya bata bari ya huta ba, saboda
tsabar jaraba irin ta
Hajiyarsa.
“Mamasco komai fa ya kankama, jibi ne zan
wuce Abuja karatu na.”
Ya fada yana kallon fuskarta.
Mamasco cikin jin dadi tace
“To Jalaluddinina, Allah ya taimakeka ya baka
sa’a a dukkan lamuran ka,”
Cikin farin ciki da murnar addu’arta ya amsa da
Amin.
Ta mishi nasihohi akan ya kula da kansa da
karatunsa kada ya biyewa mutanen Abuja
karatunsa ya lalace, batason tarbiyar da ta
masa ta gurbace.
Ranar da yamma ya fara har hada kayan sa
domin tarewa gurin muradin rayuwarsa.
Tunanin Mamasco daya ina zai rika samun kudi,
musamman rayuwa irin ta Abuja mai tsada.
Data masa maganar, cikin kulawa yace,
“Kada ki damu Mamasco, makarantar tamu, su
zasu dauki nauyin komai nawa, zasu bani duk
abinda nake bukata, sannan kinga inada
diploma, da ita zan nemi aiki, kinga ko anan zan
iya samun kudin da zan rika wasu lalurorina
dasu”
Baki washe tace
“To Allah ya shige maka gaba ya baka sa’a a
rayuwarka.”
Ya amsa da amin.
Ta tayashi sun hada kayan sa gaba daya,
bayan ya kare yaje gidan yayarsa ya mata ban
kwana kuma ya roki yayar tashi akan ta baiwa
Mamasco Zainab ta rik’a tayata zama da
taimaka mata da yan guntayen ayyuka, kada ta
zauna ita kadai kadaicin zai mata yawa.
yayar ta aminta da hakan, tace masa da mijinta
ya dawo zata gaya masa, duk da cewa tasan zai
aminta amma sai ta gaya masa sai a kawota.
Hakan yafi dacewa mata sunayi bawai dan
kinsan mijinki yana aminta da abu ba, sai kawai
ki aikata, No idan dai yana da hakki to dole ne ki
sauke hakkin nasa kamin ki zartar da hukunci,
saboda zaki iya aikata abinda bai kai ya kawo
ba amma shi kuma ganin yanada hakki ba’a
gaya masa ba sai yaji haushi har ku sami
sabani.
Mamasco ta bashi kudi masu yawa amma sam
yaki karba, har saida yaga tayi fushi sosai
sannan ya karba, a ransa ya raya cewa da yaje
bada dadewa ba zai dawo mata da kudinta akan
ya sami aiki ne.
1⃣0⃣
Ranar laraba itace ranar da JAN yayi ma Abuja
tsinke, ya rasa me yake ji, dad’i ko rashin dadi,
bangare daya yana jimamin barin Mamasco ya
tafi gun wata mace, ban gare daya kuwa zuciyar
shake take da farin ciki, da haka har suka isa
Abuja kamin su isa ta tsaya wani babban Mall
ta masa siyayyar duk abin da take ganin zai
bukata, daga nan suka wuce Gida.
Rayuwa juyi_juyi.
JAN ya sami kansa cikin rayuwar jin dadin da
bai taba tunanin samu ba, ya dauka iya mafarki
ne abin nasa zai tsaya, ashe hakan zata
kasance a rayuwa, jin dadi ko wane iri yana
samu kulawa da tarairiya a gun Hajiya ba’a
cewa komai.
Ta siya masa motar zamani, da ita yake
fasawa skull.
Yauma shine cikin shigar kananan kaya yana
taje sumar sa gaban madubi, hajiya ce ta
rungumesa daga baya, cikin wani irin salo na
daukar hankali tace dashi.
“Please babyna da kun k’are lecture ka dawo
gida, a matse nake kaima ka sani.”
Ta karashe maganar kamar za tayi kuka tana
kara shigewa jikinsa, tsohuwa sai bariki.
Murmushi yayi ya juyo shima ya kara
matseta a jikinsa, hadi da mata peck a kumatu.
“Hajiyata na fiki matsuwa, yau fa kusan
kwana bakwai kenan,”
Ya fada yana kashe kama ido.
Kasan cewar tayi period ne dukansu a matse
suke musamman ita, saboda ita ba karamar
jarababbiya bace, tun bai saba da jarabarta ba
har ya saba, saboda kwana bakwai dinnan da
yayi bai samu abinda yake bukataba ji yayi
kamar ya kurma ihu!
“Kada ka damu, kamin ka dawo nayi wanka
yau, yau komai at your service baby na.”
Ta fada tana kanne masa ido daya.
Murmushi yayi ya shafa mazaunan ta da suke
a cike, suna tsananin burgeshi a jikinta.
Da marmarin juna suka rabu.
Ya fito yaja motarsa, a hanya ya fara wasu
tunane- tunane,
Meyasa Hajiya bata bashi kudi?
Meyasa komai sai dai ta masa? Ko ta sakashi
gaba ya dauka ta biya masa?
haka rayuwarsa zata kare bashida na kansa?
Tun zuwansa sau biyu ya aikawa Mamasco kudi
suma na farkon nata ne da sauran chanjin da ya
rage masa ya hada ya tura mata.
Na biyu kuma tsintar su yayi a motar sa dala
$500 ya baiwa hajiya tace ba nata bane shi
kuwa yasan natane sune ya chanza ya aikawa
Mamasco rabi Ahmad sarkin k’orafi rabi, saboda
Ahmad gani yake yana saman kaya amma ya
manta dasu, bayan tare suke fadi tashi, kuma
duk da abin Ahmad ake burga wa yan mata.
Da wannan tunanin ya isa skull har ya dawo.
A hanyarsa ta dawowa ya gaya ma Ahmad
abinda ke faruwa saboda abin ya fara damun
sa, Ahmad ya bashi shawara akan kawai ya
mata magana tunda tana sonsa komai zata iya
masa.
Haka kuwa akayi, ya iso gida yaci ya koshi, da
ganin kwalliyar da Hajiya ta zuba yasan cewa
shi kawai take jira su fara aikata masha’a.
Kallonta yayi ya dan takure fuskarsa,
Nan da nan ta fahimci cewa akwai abinda yake
damun sa ta zagayo cikin sigar kissa, dan
murmushi yayi a zuciyarsa.
Ya kame, ita kuwa kamar zatayi kuka,
“Baby na lafiya naga ka bata fuska? Ko skull ne
wani ya taba min kai”
Banza ya mata, ta fara shafashi tana neman
biyan bukatarta,
Tsayar da ita yayi ta hanyar fadin.
“Stop it pls.”
Da sauri ta dawo gaban sa ta zauna dirshan,
idonta har sun kada sun fara zama jaaa,
“Me yake faruwa JAN?”
Ta fada tana mai kaskantar da kanta da muryan
ta a gabansa,
Kwabe fuska yayi yace.
“Ba komai”
Ya fada yana kokarin tashi tsaye.
Riko masa hannu tayi ta zaunar dashi.
Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan
lokacin da ta sake mar hannu ba.
Wucewa daki yayi yana murmushin mugunta.
1⃣1⃣
Ta sami kanta da kasa binsa daki sai kaiwa da
kawowa takeyi.
Ta sak’a ta warware karshe ta yanke
shawarar binsa kawai dakin taji me yake damun
sa.
Fitowarsa wanka kenan, suna hada ido sai
wata danyar sha’awarta ta motsa masa, shikam
yana son wannan tsohuwar kamar ya hadiyeta,
gashi tasan kan duniya, ta iya sarrafa namiji tuni
ya suku kuce, ta fahimci hakan ta idonsa,
saboda ta kula duk lokacin da sha’awar sa ta
motsa a idonsa take fara ganewa.
Matsowa tayi ta rungume kayan ta suka fara
sarrafa juna,
Saida ko wannen su ya gamsu sannan suka
hakura da juna, bacci ya bige dashi saboda ya
gaji sosai, ba kadan hajiya ke bashi wuyaba a
gurin ba.
Ya farka yayi wankan tsarki ganin ta yayi
zaune gefen sa tana mai murmushi, mumushin
ya mata shima,
Suka zauna kusa da juna, kamar bata son
magana cikin yanga da kwarkwasa tace
“Dazu saura kiris kasa zuciyana ta buga,
please wa ya taba mun kai?”
Kallon ta yayi da narkakkun idonsa, cikin tashi
kissar yace da ita
“kada ki damu Hajiya ba komai”
Murmushi tayi ta fara rarrashinsa har saida ya
fada mata abinda yake damunsa,
Bata masa gaddamaba,
Kuma ta aminta akan zata rika zuba masa kudi
yana komai nasa da kansa.
Dama bata bashi kudi ne dan kawai kada ya
baiwa wasu matan, shi yasa ta zabi ta rika
masa komai da kanta.
Ya nuna mata cewa matan yanzu ko ba ko
kwandala zasu iya bada kansu ga namiji idan
har suna sonsa, ta yarda da hakan saboda itama
abinda takeyi kenan.
Tun daga wannan lokacin ta fara zuba masa
kudi ba na wasa ba, sai dai yaji Alert abinsa…
1⃣2⃣
Watansa uku kenan gun hajiya, ta mayar dashi
kamar mijinta duk lokacinda take bukatarsa zata
nemeshi shima hakan, wani abu da suke
fuskanta kuwa shine duk lokacin da suka kare
lalatarsu sai su rik’ajin sunyi ba daidai ba,
wannan dama duk mai aikata aiki mara kyau
yanajin hakan sai dai kawai yaci gaba da
aikinsa.
Karshen wannan watan ya shirya tafiya gida,
saboda Ahmad yana matsa masa sosai, idan
yana tare da Hajiya har Mamasco mantawa
yakeyi da ita.
ta hanashi tafiya saida ta fara period da tasan
cewa ko yana nan ba abinda zai iya mata
sannan ta barshi ya tafi, akan sati daya zaiyi ya
dawo.
Ya shirya ya hada tsofaffin kayan sa akan zai
kaiwa abokansa da suke zama tare a dabar su,
da duk wani tarkace nashi ya wuce sai gida.
Da motar sa yaje saboda su sami ta fasawa, sai
dai baiyi gigin karasawa da ita gun Mamasco ba
saboda zata titsiyeshi akan ina ya sameta,
hakka kaya masu tsada bazai bari ta gansuba
kada tayi zargin wani abu. duk wajen su Ahmad
ya barsu ya isa ma Mamasco da kaya niki niki.
Murna a gurin ta ba’a ko magana.
Sunyi hira sosai na yaushe rabo, dama d’a da
mahaifi sai Allah.
Yawo sukeyi shida Ahmad da jabir a motar sa,
yanzu kam basa fita da motar Ahmad, da motar
JAN ake yawo, sun zaga gari sun ci kudi anje
gun tsofaffin yan matan sa da kawayensa.
Yau Kwanan sa uku a Nassarawa, ranar sun
fita zaga gari a hanyar sa ta zuwa gidan mai
saboda man motar tasu ya kusa karewa, Jabir
ne da karfi yace,
“Kuut yaseen itace!”
Gaba dayan su suka waigo suka kalleshi, suka
kai duba gunda suke ga yana kallo,
Gaban sane yayi mummunan faduwa lokacin
da ya hangota. Da karfi sa yace,
“Yes itace. Yeah! Yeah!! Yeah itace!!! ” abinda
ya rika fada kenan yana jinjina kai, har yasa
suka juyo suna kallonsa.
“Kai JAN kada ka kashemu mana”
A hankali ya dawo daga kallon ta, yama manta
da cewa tukin mota yakeyi, ya kalli Jabir yace
“Jabir itace fa!”
Jabir yace
“Eh ina ganin ta na tunata.”
A hankali ya fito motar suma suka fito suka
tunkareta basa shayin komai.
Tsaye take tana waya tana ta murmushi.
Da ganinta kasan tana cikin hutu, shigar jikinta
ta bayyana tarbiyanta.
Bugun zuciyar JAN take tsanan ta lokacinda
suke dada matsawa kusa da ita.
Tsayawa chak yayi lokacin da ta dago idonta
ta kalleshi hadi da wani lalataccen murmushi,
mai nuna natsuwa, wanda shi kansa yasan
wannan murmushin ba nasa bane saura kiris ya
kife a gurin lokacinda yaji tace
“Luv U 2 ma bobo”
Www.fiddausi.wordpress.com
Www.jabohauwa.wordpress.com
Www.hauwajabo.blogsport.com
RUGUNTSUMI
1⃣3⃣to2⃣0⃣
NWA
WRITTEN BY:
Hauwa M. Jabo
Fiddausi Sodangi
STORY BY:
Hauwa M. Jabo
EDITED BY:
Benaxir Omar
Numfashin sane yaji yana neman d’aukewa jin
ta kira wani da bobo, dak’yar yasamu ya daidai
ta natsuwar sa, gaba daya yarinyar ta tafi da
imaninsa, wani irin abu yake ji a zuciyar sa
game da ita.
Ita kuwa cikin natsuwa da taku na hadaddun
mata ta wuce kamar batasan Allah yayi ruwansu
a gun ba, duk da cewa bata kalli gefen su ba
kawai wucewa tayi saboda tasan zasu biyota.
Ahmad ne yarike hannunsa jin kalaman dake
fitowa a bakinta, cak suka ja suka tsaya.
JAN ya k’ara kallonta daga sama zuwa kasa
wata irin tafiya ce takeyi cikin yanga.
bazai iya tantance meye aransa ba game da ita,
ya fara taku zai nufi kanta Ahmad ya riko
hannunsa “ina zuwa JAN?” ya fizge hannun
sannan yace
“gunta mana, sai angwada ake sanin na
kwarai”
Ya fada yana ya gyara rigarsa shi dole babban
yaro sannan ya nufi inda take tafiya.??
Sallama yayi ahankali ta dago idanuwanta don
ganin mai wannan
sanyayyar muryar, da sauri ta kauda idonta ta
mayar kasa da suka hada ido, Yarrrr taji tsigan
jikinta ya tashi don shima kallonta yakeyi ko
kiftawa bayayi, aranta kuwa cewa take ‘ko don
kaga kana da ido masu kashe jijiyan mutum
yasa kake kallona haka, toh karyanka ni sai
Bobo na’ a fili kuwa amsa sallamar tayi sannan
taci gaba da tafiya, binta yaci gaba dayi yayinda
take sauri saboda kar ya tsaidata sabida batada
lokacinsa take gani, shikuwa binta yake har ta
isa wani gida ta shige, tana shiga ta rufe gate
din, shikuma ya tsaya yana jira yaga ko akwai
wanda zai fito daga gidan, yafi minti goma a
tsaye don harya juya zai tafi wani tsoho yaleko
zai dauki buta dasauri ya nufe shi “Baba ina
wuni? inada tambaya” tsohon ya kalleshi sama
da kasa sannan yace “meya faru?” JAN ya
gyara tsayuwarsa sannan yace “Baba akwai
wacce ta shiga ciki yanzunnan, nace inaso nayi
sallama da ita amma ta shige ko zan san
sunanta?” Tsohon ya kalli JAN sama da kasa
ganin yadda yake magana da karfin gwiwanshi
sannan yace
“Hannatu kake magana? fara doguwa ko?”
dasauri ya gyada kai sannan yace ” ae ita!
wallahi baba da alheri nazo Hannatu sunanta
kenan” tsohon ya kuma kallonshi ya leka
bayansa yaga ko da wani abu yazo yaga dai da
sayyadansa (kafafu) yazo babu babur balle
mota, saidai dan gayune, a ransa yace irin
gayun yarannan masu bakar karya ba ko kobo.
gashi yarinya masu nemanta babu na kafa don
haka kawai yayi murmushi sannan yariko
kafadan JAN ya janyoshi sannan yace “kaga ita
Hannatu nemanta shine zai baka wahala, yanzu
dai kayi hakuri idan ka samu wata Allah ya baka
ko?” JAN ya kalli tsohon duk da bai gama
fahimtan me yake fada ba ya ce “toh baba!
nagode” ya mayar da hannunsa cikin aljihu
sannan yaci gaba da tafiya don komawa gun
daya baro Ahmad tare da motarsa, cike da
takaicin rashin magana da Hany, duk da cewa
ya kwallafa ransa cewa tabbas yazama dole
agaresa yanemi Hannatu.
Tundaga nesa ya hango Ahmad ya tsura masa
ido yana jiran karasowar sa, d’aure fuska yayi
dan yasan tsiya zai mashi tunda ya tsura mashi
mayun idanuwansa. Aikuwa yana karasowa
Ahmad ya kwashe da dariya harda bugun motar,
dariya yaketa shak’awa tamkar wani sabon
mahaukaci, JAN ya kulu iya kuluwa sai kallonsa
yake yana sake saken abinda zai masa…..
1⃣4⃣
Cikin daure fuska yace
“Muje idan ka kare dariyar ko,”
Ahmad bai daina dariya ba yace
“Hope ka karbo numbar ta, sabida nasanka
akwai nasarar samun number mnyan kaya,”
Ya fada yana kokarin bude motar ya shiga,
banza JAN ya mishi,
Jabir ya kalleshi
“Ya kukayi da ita my Man?” ya tambaya cikin
nuna kulawa, key ya yiwa motar sannan yace,
“Wallahi bata kulani ba amma dai nan ne gidan
su gobe zamu dawo ko?”
Ya fada yana kallonsa,
Murmushi Jabir yayi
“sosai zan rakoka ko banza zansha AC “
dariya sukayi gaba dayan su, har suka isa ban
tanka Ahmad ba, shi dole fushi yakeyi dashi.
Washe gari JAN bai ma nemi Ahmad ba Jabir
kawai yama waya suka dau wanka basu tsaya
ko inaba sai gidan da ya ga Hany dinsa ta shiga.
Da motarsa ya tafi dan kada a raina masa
wayo.
Baba maigadi yama magana ganin sa da mota
ya fara washe baki yana masa kirari, bai bata
lokaci ba ya sallamesa ya kuma gaya masa
bukatarsa,
“Ai dan saurayi ita hannatu ba yar nan bace,
yar kano ce da sunyi hutu take zuwa nan, da
yake akwai yan mata a nan gidan sai suyita
yawo a gari”
Ya karasa yana washe baki,
“To baba yanzu ya zan sameta kenan?”
“Eeh to! Kasan yaran zamani amma bari na
shiga ciki na gani”
A dudduke mai gadi ya shiga gida yana sake
saken yanda zai fuskanci lamarin, dama ya
saba.
“Hannene Hanenne”
Hannatu yake kira yana washe baki,
Tana ganinsa tasan anzo wurin tane,
“Yadai baba mai gadi? Da wace kala yazo
yau?”
Yayi dariya sabida ya gane mi take nufi.
“Ai ina gaya miki irin wannan ce kunburarra,
mai kan jirgi, gaban ta da bayan sun tafi sitiree”
Ya fada yana mike hannu alamar stret.
Kwashewa sukayi da dariya gaba dayansu,
“To baba zan iya fita masa haka ko sai na
chanza kala?”
“Ai kawai ki shiga ciki ki saka yan kayan nan
masu mai dake yar charas chas.”
“Heheee baba kace babban kamu zanyi” ta
fada tana wucewa daki da gudunta.
” yauwa ki shafa wannan abin na saman ido ki
labta jan baki Hannenena”
Hajiyar gidan ce ta fito sauri yayi ya kame dan
yasan fada zata masa, sum sum ya fice.
Da yake yasan halin Hannatu yana fitowa yace
ma JAN.
” Ai yallabai ka taki sa’a yanzu koda na shiga
tana shiryawa zata unguwa kaga sai ka gyara da
ta fito sai ka tareta ku sossoye”
Dadi JAN yaji ya kara sallamar baba mai gadi,
baba ya wuce yana ta murmushi.
Ba’a kai minti hudu ba sai gata ta fito tana ta
fadace fadace ita ala dole wani take jira baizo
ba har yanzu.
JAN ne ya fito daga cikin mota yana taku irin
na mazan da suka san kan duniya.
Da murmushi ya karaso gunta, ita kuwa kamar
batasan ma da zuwan sa ba, ta ganeshi sarai
kawai basarwa tayi, kirjinta ne yake dukan uku
uku lokacin da yake kokarin karasowa gunta.
Yanda take jinsa bata taba jin wani saurayi
hakan ba, ji take kamar ta ruga sabida abinda
takeji aranta tace wannan wane irin abune farat
daya ko jiya fa haka ta rikaji, shima a nashi
bangaren abinda yakeji game da ita kenan
kamar dai yanda yake jin na Hajiyarsa.
Sallama ya mata, cikin natsuwa ta amsa dan
kada ya gane yanayin da ta shiga,
Wayarta ta dauka ta fara fake call.
“Haba Yaya tun dazu fa kai nake jira muje
Jabonation Mall, amma har yanzu baka zoba
Allah wucewa ta zanyi na gaji da jira.”
Bata jira komaiba tayi kamar ta kare waya ta
saka wayar cikin jaka.
“Kinga kuwa nima Jabonation Mall din zani, sai
muje na karasa dake ko?,”
Cikin yanga ta amsa da
“No nagode yaya zaizo ya kaini”
Haka dai JAN yayi amfani da duk wasu makamai
nashi har saida yayi nasarar daukarta zuwa
Jabonation Mall din, a hanya ne suke dan taba
hira har suka karbi number junansu.
1⃣5⃣
Dan lokacin da yayi a Nassarawa saida yayi
kokari ya saba da Hany.
Ya kamu da sonta sosai da sosai, sabida ya
kasa tantance itada hajiya wa yafi kauna?
Bangaren Hany ma haka ya tafi da dukkan
wani imani nata, tunda ta fara Soyayyah dashi
ta fara tunanin yin fatali da duk wasu samarinta
sabida JAN takeji kamar wani bangare na jikinta.
A dan kwana hudun da ya rage masa saida ya
nemi hajiya ta kara masa wani sati daya sabida
a yanda ya gaya mata kawunsa ne Allah yama
rasuwa.
Bata damu sosai ba, saboda itama tafiya ta
kamata zuwa kasar Jamus, hakan yasa sai ta
aminta akan ya zauna di mn yadai kula mata da
kansa, duk da taso ta tafi tare dashi amma
hakan bata samu ba.
Soyayyah suke da Hany kamar ba gobe, kuma
shi har ga Allah ba son da yake ma sauran yan
matansa yake mata ba, auren ta yakeson yayi,
saboda yanda yake jinta a ransa bazai iya taba
cutar da ita ba.
Ya kawo ma Mamasko ita a matsayin wacce
zai aura idan ya kare makaranta, Mamasko taji
dadin haka sosai tayi ta saka masa Albarka
dama tanason yayi aure tun tuni.
Mamasko tace Hany ta mata kama da wata
kawarta amma kuma tasan ba yarta bace.
“Yanzu gobe zaka tafi ka barni?”
Hany ce take zubawa JAN shagwaba, ji yake
kamar kada ya tafi ko kuma ya tafi da ita,
“Wallahi Hany ba da son raina zan tafi na barki
ba, ji nake kamar na wuce dake gaba daya, dole
idan na sami lokaci naje Kano na gaida su Dady
sai mu fara maganar Aure, dan gaskiya bana
son a dau lokaci, ina sonki kusa dani”
Ya fada yana lumshe ido,
Itama lumshe idon tayi,
Nan dai suka dagargaji soyayyah sukayi ban
kwana da junan su.
Ya koma Abuja cike da kewar Hajiya da Hany,
baisan son wacce yafi yawa ba, dukansu yana
sonsu kuma yana tsananin tausayinsu.
“Oh my baby! Bakasan yanda nayi missing
dinka ba, plaese kada ka kara mun nisa, idan
baka tare dani ban san yanda rayuwata zata
kasance ba.”
Janyota yayi jikinsa,
“Hajiyata bakisan irin azabar da nasha ta
rashin ki kusa dani na wannan lokacin, sati biyu
ne but jinsa nakeyi kamar shekara biyu.”
Tallabo fuskan ta yayi da hannayensa duka
biyu ya fuskanceta, idon sa cikin idonta
“I luv u Hajiyata”
“Luv u too” abinda ta fada kenan,
A ranar dai sun nuna ma juna yanda sukayi
kewar junansu, sabida ita kanta hajiya saida taji
ta gaji a ranar, duk da kasancewarta jaruma
sosai, amma ranar saida ta gaza.
Hany da JAN suna darzar soyayyarsu son ransu
ba tare da Hajiyarsa ta sani ba, har takai anje
gaisuwar iyaye.
1⃣6⃣
Tafiya tayi tafiya JAN da Hajiya an zama daya,
duk tafiye tafiyen da takeyi dashi take tafiya, shi
kuwa yana biye da ita kamar jela, gata kam yana
samunsa bako kadan ba, motsi idan yayi a
idanun hajiya yake yinsa, tabi ta kasa ta tsare
kuma har rakawa takeyi, tana biye da duk wani
moving nasa tana bincike, a skull a kwai masu
saka masa ido haka idan ya fita motsa jiki tana
sawa ana bibiyarsa, kusan wata bakwai bata
taba kamashi da wani abu da ya sabawa
tsarinta ba, wannan dalilin yasa ta daina
bibiyarsa tasa aka daina kula dashi ta aminta
dashi 100%.
uwa uba da so da kauna da yake nuna mata
hadi da kulawa, wanda yafi komai mata dadi a
rayuwarta.
Ta fara tunanin mika masa ragamar
dukiyarta, amma idan ta tuna wasu abubuwa sai
ta fasa.
JAN ne kamar yanda ya saba fita ya dau
wanka kamar yanda Hajiyarsa ke bukata, ya fito
suna tafiya tare da Hajiya suka shiga wani Mall
kowa yana gefen yana zabar abinda yakeso.
Charaf idonsa suka fada akan Hafsa, sanin
halinta yasa yayi kokarin boyewa, amma ina,
kamin ya kauce tuni ta hangoshi, iya karfinta ta
kwala masa kira “JAN.!!!” Da gudunta taje ta
rungumeshi, tsoro hadi da razani ya kamashi,
Hafsa dai tsohuwar budurwar sa ce da sukayi
Diploma tare, daga nan ta wuce Cyprus karatu,
tun daga lokacin basu kara haduwa ba sai yau,
sun gurji duniya ita dashi, Hafsa irin yan matan
nan ne da basuda kunya bare tsoron Allah, ko
gaban mahaifinta zata iya rungumar namiji,
saboda bata dauki haka a bakin komai ba illa
wayewa,
Da sauri yayi kokarin banbareta jikinsa kada
hajiya ta gani, amma ina har Hajiya ta hangosu,
bata sakeshi ba saida ta sunbaci kumatunsa,
duk a idon Hajiya,
ta sakesa ta dafa kafadarsa tana dariya,
“JAN kalli yanda ka zama babban yaro,” ta
kallesa daga sama har kasa tana murmushi,
“Hmmm naga bakayi murna da ganana ba at
all.”
Ta fada tana lumshe idonta, Hajiya ce tayo
kansu gadan gadan, da yake ya bata baya so
bazai iya hango Hajiya tana tahowa ba, Hafsa
ce kawai ta ganta, Hannun sa ta janyo
“Dallah muje waje Alkah JAN m miss u much,
what of u?”
Ta fada tana janyo hannunsa suka bar layin
kamin Hajiya ta kawo har sun bar gun, haukace
kawai hajiya batayi ba, kamar zararra haka ta
biyosu tana wani wawan sauri.
Hafsa kuwa har tana kokarin jantoshi su fita
ta sami gu suka zauna cikin fari da ido tace
“Oya kana mamakin ganina ko shiyasa ko
magana ka kasayi tin dazu”
A hankali ta tashi tsaye ta janyo kumatunsa da
hannuwanta ta turo baki alamar tana masa kiss.
Daidai lokacin Hajiya ta kawo zuciyarta tana
tafarfasa, bata tsaya bata lokaci ba
Ta wanke Hafsa da wani bahagon mari.
Hafsa dagyar ta iya bude idonta sabida saida
taga taurari da aka mareta din nan.
1⃣7⃣
A hankali idonta suka bude hajiya ta gani
gabanta tana huci tana nunata da yatsa, sam
bataji abinda Hajiya ta fadaba, amma lokacinda
ta dawo hayyacinta ta fuskanci cewa magana
takeyi, saida hafsa ta saita natsuwarta, sannan
ta daga kai ta kalli Hajiya ta kalli JAN da yayi
wata uwar zabura ganin hajiya ta mari Hafsa
“JAN wacece wannan??”
Abinda Hafsa ta iya tambaya kenan sabida taga
wani abu daya daure mata kai tare da Hajiyar.
Bai bata amsa ba sai wani turus da yayi, cikin
daga murya ta sake tambayar sa, daidai nan
hajiya tayi tsaki ta kama hannun sa zasu bar
gurin Hafsa da karfi itama ta kamo hannunsa ta
rike, Hajiya ta rike Hafsa ma ta rike, suka
sakashi a tsakiya,
Hafsa ce ta maimata tambayar ta
” JAN who is she?”
Ta tsareshi da ido, ya kasa bata amsa Hafsa
kam ko rashin kunya tasan da zaman ta, Hajiya
ita take barikin tsofaffi ita na yan zamani takeyi,
Tana rike da hannun sa ta zagayo gaban
Hajiya ta kalleta daga sama har kasa, abu daya
ne data hango a idon hajiya wato kishi karara
shi zaisa ta aikata abinda take da niyyar
aikatawa.
” bansan koke wacece ba, amma ki sani Nice
budurwar JAN da zai aura kuma ko kinki ko
kinso sai munyi aure sabida soyayyar mu hadice
daga Allah, “
Ta kamo fuskar JAN iya karfinta dan kada yayi
kokarin kwace kansa tamasa kiss sosai sannan
ta sakesa, ta waigo ta daddage iya karfinta ta
wanke hajiya da mari,
Jikin JAN ne ya fara rawa ya daga hannu iya
karfinsa zai mari Hafsa amma hajiya ta rikesa
iya karfinta
“Dont do it, budurwarka ce fa.”
Sai wani huci yakeyi har cikin zuciyarsa yakejin
marin da aka yiwa hajiya. Hafsa kam wucewarta
tayi cikin taku na isa.
A hankali Hajiya ta sake masa hannu tana
kokarin barin gurin, rike mata hannu yayi amma
ya kasa magana.
Wani kallo hajiya ta watso masa baisan
lokacinda ya sake mata hannu ba, sayayyar da
ba’ayi ba kenan.
Mota ta fada ta fara sharara gudu bata nufi
gida ba, bata ma san ina zataje ba, saida ta fara
fita cikin gari ta kama hanyar Nyayan sannan
taja gefe ta tsaya.
Abu daya ya fado mata a rai tsohon mijinta da
ya kamata turmi tabarya da wani gardi a gidan
sa kuma a gadon sa.
Da yake ko a lokacin tsohuwar yar barikice ko
motsi batayi ba, mijin nata ne yayi kakarin kashe
wanchan mutumin, dagyar wanchan ya samu ya
gudu, ita kuma anan ta zube kamar ta suma, ya
fara jibgarta amma ko motsi batayi ba, karshe
sai ya fara tunanin ko lafiya, haka ta dabir tar
dashi akan cewa abu ya fesa mata ta fita
hayyacinta sannan ya mata fyade, daga baya
mijin nata ya dawo jinyarta.
1⃣8⃣
Ta nuna masa gaba daya jikinta a mace yake
hatta hannun ta bata iya dagawa wannan dalilin
yasa ya kasa mata komai.
Kuka takeji amma ta kasa yin kukan ji take
kamar ta hadiye zuciya ta mutu, sai ganin
yarinyar takeyi a idonta tana kissing din Mafi
soyuwar halitta a gurin ta.
Wani sanyi ya taso mata, wanda yake hade da
tashin zuciya da sauri ta bude murfin mota
kawai ta fara kwarara amai, kamar hanjin cikinta
zasu fito waje, har saida ta galabaita ya zama
bata iya komai anan gurin, takai minti goma a
gurin dagyar ta samu ta daddafa ta shiga mota
sai dai ta kasa tuka motar, tayi kokari ta kashe
AC ko ta sami sassauci, tayi baya ta ijiye kanta
wani dogon ajiyar zuciya tayi wanda ke nuna
tsananin damuwa da bakin ciki tattare da it.!
JAN kuwa daga gurin kasa motsi yayi, sai
tunani yakeyi wace kaddara ce ta hadashi da
Hafsa a wannan lokacin?
Yarinyar rabonsa da ita anfi shekara 4 amma
yanzu lokaci daya tazo zata bata masa duk wani
plan nasa,
Har ga Allah baya son bacin ran Hajiya, sannan
bayason abinda zai taba masa ita ko kadan.
Jiki a mace ya sami taxi ta saukeshi gida, abin
mamaki koda yaje bata nan, yayi kusan awa
daya yana leke leke ko zata shigo shiru bata
dawo ba har kusan awa biyu bata ba labarin ta,
Ya gama rudewa, ina ta tafi?
Abinda yake tunani kenan, wayoyinta suna sam
bata dagawa har ya gaji ya daina kira, ya kasa
ci, ya kasa sha, sai safa da marwa yakeyi a
palon, karshe sai yadan kishingida da yake ya
gaji sannan ga damuwa ta mishi yawa, nan
danan bacci yayi awon gaba dashi.
Hajiya ta kare amaye amayen ta, ta sami dan
sassaucin abinda takeji ta tuk’o mota tayo gida,
ganin kofa a bude ta tabbatar da ya dawo gida,
wani kololon bakin ciki ne ya turnuketa da ta
tuna yanda Hafsa ta rika tsutsar bakinsa, rufe
ido tayi amma ina! Saida ta sake wani amai nan
gefen flowers kamin ta shiga palon a daddafe ta
shigo palon, kina ganin ta zaki tabbatar da tasha
wuya sabida gaba daya ta fita hayyacinta, hatta
tsufan da take boyewa da shafe shafe yau ta
taji wuya ya bayyana a fili.
Kwance ta ganshi yana sharar bacci abinsa,
bata iya karanto damuwa a cikin fuskarsa ba ji
tayi kamar ta rufeshi da duka, cikin sassarfa ta
wuceshi dakinta ta nufa, kamar an tsikareshi ya
tashi daga baccin da yakeyi.
“Hajiya kin dawo”
Kamar an mata Allura ta tsaya chak, ta kasa
waiwayowa kuma ta kasa tafiya,
Tafiyanshi taji bayan ta wanda ya tabbatar
mata da cewa yana son karasowa gurin tane,
wani haushinsa taji wanda ya saka mata energy
tuni ta wuce daki cikin kuzari kamar ba itace ta
sharari amai dazuba.
Baiyi kasa a guiwa ba ya biyo bayanta saidai
kamin ya kawo ta datse kofar da key ta shige
dakin.
Samun kanta tayi da rusa wani matsananchin
kuka.
Ita kuwa ya akayi ta bari son wannan karamin
yaro har ya mata wannan mummunam kamu
haka ?? tabbas idan tayi wasa zai illata
rayuwarta sabida ya riga ya chafko zuciyarta.
Kuka take kamar ranta ya fita.
Yana tsaye bakin kofar yana jiyo sautin kukan
ta, amma kofa a kulle, zagayawa yayi ta dayan
kofar dakinsa wacce take shigowa dakin nasa,
yayi sa’a a bude take tanan ya shigo.
Halin da ya ganta a ciki bama gaskiya bane,
sabida bai taba tunanin haka ta hargitseba.
Yazo kusa da ita zai zauna cikin tsananin kuka
harda majina tace dashi
“Get out JAN! I said get out i dont wana see u
again”
Bai tsaya sauraren ta ba ya nufota ya kamata.
1⃣9⃣
Yana kokarin rungumeta tana dukan sa a kirji,
tana kuka tana fadin ya fitar mata a daki.
Wani Kukan ne mai tafasa zuciya ta fashe dashi
“Na tsaneka JAN banason ganinka! na tsaneka
banason ganinka!! Na tsaneka bana son
ganinka!!!” Abinda take maimatawa kenan tana
wani irin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya JAN
ya rude, ba abinda ke masa dadi musamman
ganin Hajiya tana masa wannan kukan, tabbas a
haihuwar wuri ta haifeshi, ga kudi Allah ya bata,
amma itace take masa wannan kukan kamar
ranta zai fita,
Sam batajin rarrashin da yakeyi, sai fadar take
ta tsaneshi, wannan kalmar ba karamin wargaza
masa tunani takeyiba,
” ka sakeni Jalal bana son ganin ka”
Wata irin tsawa ya daka mata wacce ta aiko
mata da mala’ikar natsuwa, tuni ta natsu tayi
shiru, ta lafee a kirjinsa, a hankali ya fara
bubbuga bayan ta kamar ana rarrashin yaro
karami.
A hankali taji natsuwa tana sauko mata, yaci
gaba da mata waiwayi, ko minti uku ba’ayiba sai
bacci ya d’auketa ba karamin wuya tasha ba,
tsayawa yayi ya kare mata kallo, tabbbas
wannan matar akwai kishin bala’ee, sai kace ta
gansu turmi tabarya, yanzu ta masa haka inaga
ta sami labarin Hany, guntun tsaki yaja, a
hankali ya zame jikinsa ya janyo pillow ya daura
mata ya fito dakin, ko minti biyar ba’ayi ba sai
gata ta tashi kamar an tsikareta,
Sai kace wacce tayi wani mafarki, ko ina ta
zagaye bata ganshi ba, chan ta hangoshi hanyar
kitchen yana waya, kuma ga dukkan Alamu
wayar ta munafunci yakeyi, zuciyarta take cewa
taje gurinsa wata zuciyar na ce mata kada kije
ki jiyo bakin ciki, a hakan ta tsaya amma wayar
taki karewa, bugun zuciyarta yake daduwa duk
lokacinda ta waigoshi, sai taga kamar ma yana
dariya, a hankali ta tashi ta shigo kitchen din
kalmar da ta fado kunnen tace ta nemi ta
wargaza mata kwakwalwa.
“Wallahi Zan iya rabuwa da ita koda zan
dawwama cikin bakin cikine..!!!
Www.hauwajabo.blogsport.com
Www.jabohauwa.wordpress.com
By Hauwa jabo 11:31 No comments
2⃣0⃣ RUGUNTSUMI!!!
NWA
Written by
Hauwa M. Jabo
Fiddausi Sodangi
Story by
Hauwa M. Jabo
Editted by
Benaxir Omar
Wani bakin ciki ne ya tokareta, bata san
lokacin da ta fizge wayan ba da karfi ta wurgar
akasa, wanda tuni ya fashe a gurin, tana hushi
kaman mayunwacin zaki, domin ji take kaman ta
rufe shi da duka , shi kanshi ya tsorata domin
bacin ran da yagani a fuskanta dazu bai kai na
yanzu ba, jikinshi ya fara rawa kaman wanda
aka kama yana sata.
“Jalal ni kake cewa zaka barni koda zaka mutu?”
Ta fada da wata irin raunatacciyar murya mai
ban tausayi, ta dago kai ta kalleshi,
“Maimaita abunda kace” ya kalleta idonshi
arazane ya sunkuyar da kai tare da cewa
“fada kawai nake yi, wata ce da naje Nasarawa
taji labarinki take tsorata ni akan zata fadawa
Mamasko abunda ke faruwa”
Duk da yasan maganan shi tayi kama da na
rainin hankali amma danne zuciyarsa yayi
kaman dagaske yake nufi sannan cikin wayo
irinta mayaudaran maza yace “taji labarinki da
kuma irin zaman da mukeyi, budurwa ta ce ada
amma mun rabu wallahi, shine fa take cewa na
rabu dake ko ta fadawa Mamasko, kinga kuma
Mamasko bata da ishashen lafiya kar ta tayar
mata da hankali tazo ta hanani tahowa nan
dinma, shine yanzu nake lallabinta inaso nasa
acikin abokai na ko kudi sukai mata domin su
toshe bakinta” duk da radadin da take ji da
haushinshi da takeji ta tsinci kanta da
amincewa da maganarsa, ta gamsu sosai anan
taja wani numfashi wanda shi kanshi sai da yayi
mamaki sannan tace
“Jalal miye gaskiyar zancen da wannan
yarinyar ta fada dazu? Pls kada ka boyemin
komai dan Allah”
Ya gyara tsayuwarsa sannan yace,
“Hafsa tsohuwar budurwatace shekara kusan
shida da suka wuce,”
Nandai ya bata labarin Hafsaa daga farko har
karshe, Hajiya ta gamsu da bayanin sa,
“kayi hakuri don Allah, amma ka daina yimin
haka, wata ran zan iya hadiyan rai na mutu, ina
tsananin sonka fiye da duk wani abu dana
mallaka ,ka rufa mini asiri don girman Allah ka
taimakeni JAN”
Yadda take riko hannunshi take rokonshi yayi
bala’in tsoratashi har ta janyoshi suka shiga
daki aka fara aikin masha’a waiyazzubillah muna
neman tsari.
Duk da cewa rabin hankalinshi yana kan Wayan
da ta fasa, yana tunanin Hany dinsa, domin
kuwa yasan zata yita nemanshi, sannan zata iya
shiga tashin hankali tayi tunanin ko wani abu ya
sameshi, don haka rabin tunaninsa yana kan fita
siyan sabon waya, amma Hajiya kam taki
barinsa sai karfe goma na dare tabarshi ya fita,
aikuwa yana wanka yace mata zaije dominos ne
yasiyo pizza anan wuse2, bata yi musu ba ganin
babu wani nisa sosai, yana fita bai tsaya bata
lokaci ba yaje neman waya, duk da bai gama
sanin kan gari ba shine gam village, shine
bannex bai samu wayan ba, don haka kawai
yafara bin titi ko zai ga shagon waya, ahaka
yasamo wani ba tare da duba sunan shagon ba,
yashige yasiyo sabuwar waya da sabuwar sim
sai dai babu masu register, nan dai ya tuna
akwai wata tsohuwar sim da yakeda, donhaka
dasauri ya binciko motan ya dauko ya jonata
acaji ya sayi kati sannan ya kunna dama ya rike
numban Hany da sauri yakira, muryanta a dishe
ta dauki wayan, alamun taci kuka.
“Babyna me ya sameki?” jin muryarsa yasa
takara fashewa da kukan, tuni ya kara rudewa
yafara bata hakuri, duk da bai san dalilin kukan
ba, amma yasan bai wuce shagwabar da ta
sabayi masa bane, saboda kusan kullum Hany
sai ta masa kuka wai ita ta matsu yazo suyi
aure.
Ya isa gida Hajiya bata gane komai ba, saboda
haka kai tsaye daki ya shiga, ya boye wayar sa,
Hajiyace ta shigo dakin kamar an korota, shi
kansa Jan saida ya firgita,
Cikin tsananin kulawa da natsuwa tace.
“Jalal”
Sai kuma tayi shiru, dago ido yayi ya kalleta,
matsowa tayi kusa dashi ta kama hannayensa
duka biyu ta rike,
“Jalal so nake muyi Aure.”
Www.hauwajabo.blogsport.com
Www.jabohauwa.wordpress.com
Www.fiddausi.wordpress.com
2⃣1⃣RUGUNTSUMI!!
NWA
Written by
Hauwa Jabo
Fiddausi Sodangi
Editted by
Benaxir Omar
Zuciyarsa ce tayi wani irin bugawa a rikice ya
nanata kalmar ta takarshe “Aure!!? Kara damke
hannuwansa tayi cikin nata tace “eh! Jalal aure
nakeso muyi, ina ganin wannan hanyar ce kawai
zaisa in mallake ka yanda nakeso hankalina zaifi
kwanciya zanfi samun natsuwa! “wani irin kallo
yakeyi mata ido cikin ido, kai tsaye yashiga
girgiza kansa alamar zancan ta bai shige shiba,
ido ta tsare shi dashi tana fadin “JAN! Kalli cikin
ido na kace baka sona bazaka iya auran
tsohuwa ba sai intabbatar dacewa lallai kai……
” Katseta yayi dasauri ta hanyar saka bakin sa
cikin nata yana mai girgiza mata kai, hawaye ne
yafara gudu bisa fuskar ta dasauri ta ture sa
daga jikinta cikin rawar murya tace “Jan bazaka
iya aure na ba ko?” cikin wani irin salo irin ta
mazan bariki yashiga yi mata dadin baki hade
da kalamai masu dadi wayanda zasusa hankalin
ta ya kwanta, daga k’arshe ya amince akan
cewa zai aure ta,
Shagalin bikin JAN akeyi babu kama hannun
yaro, biki ne na karya da kece raini naira tayi
kuka sosai awannan shagalin biki Ango yadaukar
ma kansa k’arya inda ita ma amarya ta nuna
masa tafisa iyawa, Amarya Hannatu tayi kyau
har ta gaji iya haduwa ta hadu ba karya, Ango
Jan sai shiga kala kala akeyi ana sakewa sai
kace wani ma’aikacin gwamnati, kowani mai
arziki, party har kala biyar akayi yabarwa
samari yan kwalisa abin fadi cikin unguwa, an
daura auran da misalin k’arfe biyu da rabi ranar
juma’a bayan an sakko sallar juma’a, daurin
auran yasamu halartar dubbannin Jama’a, bakin
ango sam yakasa rufuwa sai kace gonar
auduga.
Amarya ta shige gidan ta wanda musamman
Jan yakashe makudan kudade wajan gina shi
( kudin hajiya da ta bashi daman amfani
dashi) ,gida ne madaidaici nagani na fadi, ya
hadu yakuma tsaru iya tsaruwa sai dau muce
Allah yabada zaman Lafiya!
Sati biyu Jan yayi a suna gurzar amarci shida
amaryar sa, ji yake tamkar karya koma abuja
amma idan yatuna hajiyar sa a bangare daya
gabansa har faduwa yakeyi yana tsananin
tsoron hajiya tasan abinda ya aikata domin
Kuwa yana ganin yaci amanar hajiya ya
munafurce ta, har a zuciyar sa yanajin babu
dadi abinda yai mata saidai babu yanda zaiyi ne
kaddara tariga fata! Acewar sa haduwar sa da
Hannatu hadi ne daga indallahi! yasan ko a
mafarki auren hajiya ba nashi bane, zai ci
kudinta dai sannan ya biya bukatunsa.
www.hauwajabo.blogsport.com
www.jabohauwa.wordpress.com
www.fiddausi.wordpress.com
[28/10, 10:46 p.m.] Antinsu: 2⃣2⃣ RUGUNTSUMI!!!
NWA
Written by
Hauwa M. Jabo
Fiddausi Sodangi
Story by
Hauwa M. Jabo
Editted by
Benaxir Omar
Shiryawa yayi tsaf, yayinda Hany take langwabe
kanta idonta ya ciko da hawaye alamun kuka
take son yi, ya kalleta tare da cewa
“zan dawo dai, ki kwantar da hankalinki”
aikuwa kaman jira takeyi ya tanka tuni idonta
ya fito da sauran hawayen fuskarta, ta fara
kuka, ya janyota jikinsa yana lallabata, har
yasamu tayi shiru sannan yace
“duk abunda kike so akwai a gida sati biyu
kawai zanyi na dawo kinji?”
ta gyada kanta sannan sukayi sallama ta masa
addu’o’i sosai wanda tuni yaji sanyin jiki da ya
tuna abunda zaije ya tarar a abuja, yaci
amanarta kenan fa, amma wani zuciyan yace
‘hanyan samun abuncinku kenan, gwara ka je
dai’ haka kuwa yafice ya nufi abuja cike da
fargaba wanda shi kanshi bai san dalili ba.
A haka ya koma Abuja da tunani kala-kala, yana
isa wani kallo da Hajiya ta masa ya tabbatar da
cewa ta gane komai,
Shiganshi gidan ya sameta a falo tana waya duk
da kananun kaya ne ajikinta sai yaji bai ji komi
ba aransa ba kamar da idan ya hada ido da ita ji
yakeyi ta tafi da imaninsa, haka kawai yaji baya
sha’awanta, saidai yana jinta aransa kamar
yanda yake jinta ada, haka ta mike ta
rungumoshi cike da farin ciki mai hade da
zullumi, Ganin kallon da take masa, Sai ya dan
rude, idonsa suka firfito waje sukayi kwala-
kwala, nan take itama Hajiya ta kara sauyawa
ganin chanji tare dashi, Sai take ganin kamar ya
gane abinda ke faru wa da ita.
Dabara ce ta fado masa nan danan ya kame,
Murmushi ya Sako mata Wanda ya haifar
mata da kasala.
“Kamar bakiyi missing dina ba, come on
mana!”
Ya ware hannuwansa, cikin sassarfa ta taso ta
fada girjinsa cike da mutuwar jiki, shi Kuma ya
maida hannuwansa ya rufe.
Tana jin bugawar zuciyar sa sosai Shima haka,
nan dai ya fara sarrafata ba tare da ya tsaya ya
huta daga doguwar tafiyar da yayi ba,
Bayan sun kammala ne ma a lokacin yaji aransa
ashe baisan dadin kwanciya da mace ba, nan
yagane asalin banbanci tsakanin hajiya da
hannensa dama ina za’a hada? Tsohuwa da
yarinya, Hannensa ta mallaki komi yayinda
hajiya kissa kawai zata nuna wa hanne, anan
take cewa
“baka da lafiya ne?”
“a’a mekika gani? Kece ma kika min Kama da
mara lafiya”
ya fada alokacin da yake janyo towel zai shiga
bandaki.
“Na ganka ba kaman daba, kaman baka yi
kewata ba, kwata-kwata bangane maka ba”
gabansa ne ya fadi ya kirkiro murmushin dole
sannan yace
“habawa! meyasa kike fadan haka? kawai dai ina
tunani ne?” . Da sauri ta tashi tare da cewa “
tunanin me?”
“Kin ganki, Kema Sai kin gaya min abinda yasa
naga chanji tare dake,”
“Yes zan fada but kai ka fada”
“Okay, dama kanwar Mamasko bata da lafiya
za’a yi mata aiki inaso inbiya mata kudin amma
bandashi” wani tsaki taja tare da cewa
” haba meyasa kake haka?!! shine ba zaka fada
min ba? ba nason haka! komi kake so kana
fadamun zan biya maka bukatunka indai zaka
sani farin ciki nima”
dama abunda yake son ji kenan domin tunaninsa
Hany yadda yabarta agid a duk ya karar da kudin
da yake dashi a biki, kuma yakamata yatura
mata kudi shima kuma ya tara saboda idan rana
ta baci musu, domin yana ji ajikinsa kaman za’a
sami matsala nan gaba musamman idan hajiya
ta gane yayi aure.
2⃣3⃣
“ATM card ta miko masa ya saka aljihu,
“Okay Na fadi nawa saura naki”
tashi tayi ta fuskanceshi.
Sai Kuma ta kasa magana, ya dawo ya tallabo
fuskanta, sabida ya gane cewa ba abinda yake
tunani bane, wani abin ne daban take son fada
mishi, Amma Kuma ta kasa,
“Tell me mana! Nasan akwai zance cikin
bakinki,”
Kallon sa tayi jiki a mace,
“Jalal dama…”
Sai Kuma ta sakeyi tayi shiru,
“Dama me? Dama akwai abinda ba zaki iya
fada min ba?”
Kara matsowa da ita yayi jikinsa,
“Dama Jalal I’m pregnant”
Ta fada hadi da runtse Ido tana jiran amsarsa.
Numfashinsa ne kawai bai dauke ba, komai
nasa tsaya wa yayi Chak.!
Cikin rashin kuzari ya dago ido ya kafa mata,
dugar da kanta tayi kasa,
“How? Ya Hakan ta faru Hajiya? Ya zaki bari ki
dauki ciki?”
Dago Kai tayi cikin salon kissa, duk da cewa
cike take da fargabar mi zai faru amma kuma
sai ta dake sosai,
“Wallahi ban san yanda hakan ta faru ba,
saboda ina shan magani duk wata, bayan allurar
da nayi ta shekara biyar.”
Girgiza kansa yayi,
“No Hajiya, No…. Da kina shan maganin da
bazai shigaba, wallahi ki sani bazan taba
haihuwa ba Aure ba, No” .
Abinda ya rika nanatawa kenan,
“Jalal naso muyi Aure tun hakan bata faru ba,
amma Kuma Sai Allah yayi nashi ikon”
“Allah yayi nashi ikon ko ke kikayi naki ikon?
Hajiya da gangan kika dauki wannan cikin sabida
kina son Na Aure ki, sannan idan har kina ganin
sabida wannan cikin zaisa na aureki kinyi
kuskure,”
Ya fada yana nunata da yatsa, duk da yanajin
radadin yin hakan,
Mike wa yayi tsaye ya bata baya,
“Idan har kika ga na Aure ki, to ki tabbatar da
sai an zubar da wannan cikin.”
Bai tsaya komai ba ya wuce dakinsa, ya barta
nan zaune,
Zuciyar ta ce take bugawa.
Ta tuna abinda likitanta ya gaya mata sgekaru
uku da suka wuce.
“Hajiya idan har kika bari ciki ya shigeki to
lallai Sai kin haifeshi, saboda mahaifarki tayi
yaushi sosai, idan har akayi kokarin zubar da
cikin zaki iya rasa rayuwarki gaba daya, kinga
dai yanda kika sha wannan karon, kiris ya rage
ki harba kiyama, saboda haka Ina dada
shawartar ki kada ki kuskura kiyi kuskuren
daukar ciki, idan kinyi Kuma to ki shirya
haihuwarsa saboda bazai ciruba”
Numfashi ta sauke, a hankali ta fada tare da
shafa cikin,
“Jalal bazan zubar da rayuwa ta ba,”
Ta kara shafar cikin,
Wannan shine ciki Na farko da taji tana so Kuma
tana kauna a rayuwarta,
Hajiya tayi ciki kala kala, tana zubarwa, hatta
haifaffen ciki ta taba yarwa saboda tsabar
ta’addancinta.
Wasu hawaye ne suka gangaro mata lokacin da
ta tuna margayin mijin ta.
“Maman Ummi dan darajar Allah kada ki sake
zubar min da ciki, zanyi farin ciki idan har kikayi
allura ta hana daukar ciki bawai ki rika zubar
min da yayaba, inason kayana.”
Hararan sa tayi, hadi da masa tsaki,
“Wallahi bazanyi allurar komai ba Kuma duk
ciki ya shiga idan har banso shigar sa ba, to
kuwa zan zubar da banza, saboda ba dan
haihuwa nake zaune gidan nan ba, bazan zauna
yara su mayar dani tsohuwar karfi da yajiba.”
“Maman Ummi ki….”
Tsawa ta daka masa, tuni ya nemi hanyar barin
dakin, bakin kofa ya tsaya,
“Idan har kika kara zubar min da ciki Allah ya
saka min duniya da lakhira, sannan Allah ya
hanaki ciki lokacin da kike neman sa, ko ya baki
cikin lokacin da maishi baya bukatar sa,”
Ya sa kai ya fita wannan tafiyar ita tayi
sanadiyar mutuwar mijinta, Kuma ita sanadin
arzikinta, saboda kudin diyyar da aka bata nashi
sunada yawa tunda jirgine ya kife dashi.
Taci gaba da kukan ta,
Yau gata da mafi soyuwar ciki Amma maishi
baya so, lallai addu’ar tsohon mijinta ta karbu,
Haka dai taci kukanta har ta gode Allah, nan
barci yayi awon gaba da ita…
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.blogsport.com
www.Benaxiromar.com
By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
07039625239
Ruguntsumi 24-28
By Hauwa jabo 00:54 No comments
2⃣4⃣ RUGUNTSUMI!!!
NWA
written by
Hauwa M. Jabo
Fiddausi Sodangi
Story by
Hauwa M. Jabo
Editted by
Benaxir Omar
A firgice Hajiya ta farka a sakamakon
mummunan mafarkin datayi, gaba daya jikinta
ya jike sharkaf da gumi duk kuwa da sanyin AC
daya gauraye d’akin, ido taketa rabawa saikace
an tsare mage a kotu, gaba daya jikinta rawa
yakeyi tamkar mazari
A rikice takai dubanta ga kofa j!in anturo da
karfi, Jan ne yashigo cikin shigar manyan kaya
sai walkiya yakeyi tamkar wani sabon ango, ya
dawo daga turama Hany dinsa kudine ko kallon
ta baiyi ba ya raba gefe ya wuce.
Ita Kam da tunanin ya zatayi da wannan cikin
ta farka bacci, jiki a mace ta tashi ta leka
dakinsa, har ya tube kayan jikinsa, waya yakeyi
Kuma ba alamar damuwa tare dashi, batajin ko
kalma daya da yake fada, ta gaji da tsayuwar ta
ta jiyo jiki a mace ta koma dakinta,
Cikin ta shafa a hankali, tana tunanin ya dace
taje asibiti a duba mata cikin wata nawa ne,
saboda ba wasu alama da takeji na ciki illa
kasala sai tsallaken wata da tayi, shiryawa tayi,
ta fito karo tayi dashi a Palo ya hada tea zai
shiga daki kallon ta kawai yayi ya kauce kansa,
Ya rasa gane mi yasa bai daina son ta duk
abinda ta masa.
Mi yasa yake tsananin tausayin ta.??
Bata damu dashi ba wannan karon saboda tafi
bukatar farin cikin sa akan komai, asibiti ta nufa
ta yiwa Dr. Bayani.
An mata test da duk abinda ya dace, aka
tabbatar mata da cewa ba tada ciki ba alamar
ciki, tayi bakin ciki wani gefe Kuma farin ciki,
Farin cikin ta shine zasuyi aure tunda ba cikin,
bakin cikin ta tana tsananin son cikin.
Ta koma gida ta kai masa result din ta ba yabo
ba fallasa yaji dadi a yanda ya nuna mata.
A daddafe yayi sati daya saboda ya matsu ya
koma gun Hany dinsa,
“Hajiya Ina son naje Nassarawa Na gaida
gida”
Ware ido tayi hadi da kwantowa jikinsa,
“Haba Jalal duk yaushe ka dawo da zaka
matsu ka koma, kodai ka fara gajiya danine”
Ta fada cikin shagwaba,
“No No, Hajiya, Mamasko ce take damuwa
akan nazo kadaici ya mata yawa.”
Haka dai ya cita da dadin baki ya samu ya ya
lallaba ya tafi.
Zaune take saman kujera tana karanta hausa
novel, ta jiyo karar mota amma sanin cewa bai
gaya mata zai zo ba yasa taci gaba da aikin
karatunta, har ya shigo bata ma san ya shigo ba,
tsaye yayi yana kallon ta yana murmushi.
A rayuwarsa ba abinda ke sanya shi farin ciki
duk ya gansa sama da Hajiya Sai Hany dinsa,
Kuma har yau ya kasa tantance son waye yafi
yawa, zai iya cewa Hajiya So ne mai hade da
tsantsar tausayi, ita Kuma Hany So ne da wata
irin shakuwa.
Kamar ance daga kanki kawai taga mutum
tsaye yana kallon ta, wani ihu ta saka tayi tsalle
taje ta rungume sa, cikin shagwaba
“Shine zakazo baka gaya min ba”
Tallabo fuskarta yayi ya tsura mata ido, ya kasa
cewa komai, ya shafa fuskarta ya mata
murmushi,
“I luv u Hany”
Abinda ya iya furtawa kenan, a hankali ta kara
shiga jikinsa
“Luv u too”
Matseta yayi gam jikinsa a hankali yake rada
mata a kunne…
“Ur love is all I crave 4, my heart want more
and more.”
Lumshe ido tayi ta rasa abinda zata fada masa,
bugun zuciyar sa ne ya karu lokacin ta fara
kokarin nuna masa nata salon.
Sun faranta ran juna tsaye a gurin, ya kasa
sakinta Sai kace za’a masa kwacenta, kokarin
kwace kanta tayi, ta nema masa koda ruwan
sanyi ne, kara matseta yayi sosai
“This is ur permanent resident, so stay here till
people take me in their shoulder.”
Toshe bakinsa tayi ta dan daki girjinsa,
“God forbid, kada ka kara fadan haka please.”
Haka dai ya rika sarrafata har Saida ya biya
bukatar sa….
Yana son Hany komai nata burgeshi yakeyi,
Zaune yake ita Kuma ta Dora kanta saman
chinyarsa suna hira, wayarsa ce tayi kara, lokaci
daya suka kalli wayar dake gefe, Hajiya ce ta
Kira, ya kasa dagawa har ta tsinke karo Na biyu
ta sake ringing nan ma bai daga ba,
“Bakaji ana waya bane?”
“Sheeeeeee!!” Ya Dora hannun sa a kan labban
sa, murmushi kawai ta masa taci gaba da
abinda takeyi, karshe silent ya saka wayar.
Saida ya share kwana biyar sannan ya koma
Abuja, ya tafi da shirin neman gidan da zai saka
Hany, saboda ta masa nisa sosai, gashi kullum
yana son ganin ta kusa dashi.
Ya isa gida koda yaje Hajiya tana nan ciki, tun
bakin gate ya fara mamaki ganin bakuwar mota
a gidan abinda bai taba gani ba, ya isa yaji kofa
a kulle gashi baida keys saboda haka sai ya
zaga don yasan ta baya kullum a bude kofar
take, ya shiga ba tare da shayin komai ba, kai
tsaye dakinsa ya nufa ya ijiye kayan sa yayi
wanka, bai tsaya neman taba saboda yasan bata
gidan, fridge ya nufa ya dauko drink mai sanyi
ya kora, dariya ya jiyo tana tashi a dakin Hajiya,
Kuma dariyar mutum biyu ne, mikewa yayi ya
leka,
Hajiya ce zaune itada wani Alhaji da gani
dukiya ta zauna masa,
Zuciyar sa ce ta shiga harbawa wani kishi ya
taso masa, wanda yasa ya manta cewa ya taba
shiga farin ciki a rayuwarsa.! Kai tsaye dakin ya
shiga, Hajiya ce ta mike da sauri,
“Jalal! Yaushe kazo?”
Idonsa na kan wanchan dattijon, gadan gadan
yayo kansu,
Kamin ya kara so tayi sauri tace
“Wannan shine Alhaji Bello yayana ne,” burki
yaja jin tace yayanta ne, saidai bai yarda ba,
dago ido yayi ya kalleshi ya dawo da dunan sa
kan Hajiya.
Mutumin hannu ya mikawa Jan, cikin mutuwar
jiki shima ya mika masa hannu, sun gaisa sama
sama ya fice dakin da sauri, a gurguje ta
sallami Alhajin, ta nufi gun Jan.
Tana shiga ya juyo ya kalleta, idonsa sun kada
sunyi jajir.
“Hajiya muje masallaci a daura mana Aure”
Shi kansa baisan lokacin da ya fadi hakan ba.
Dago ido tayi ta kalleshi cike da mamakin
abinda ya fada,
Ta tabbata mayen kishi ne ya dibeshi yake
wannan surutun,
Janyo shi tayi jikinta, nan danan ya sami
natsuwa, baisan mi yakeji akan wannan
tsohuwar ba, wani guntun tsaki yaja.
Bata dai tambayeshi komai ba, haka ta saka
mar ido har ya sauko dan kansa.
2⃣5⃣
Yau lahadi yaune aka daura auren jalal da Hajiya
Kubra akan sadaki dubu hamsin.
An daura auren a masallacin nan unguwar,
Hajiya kam duk ta gaya ma danginta tayi Aure
Amma ba Wanda ta nunawa mijin kawai tace ta
sami wani Alhaji ne zasuyi aure, dama zaman
kanta takeyi.
Batayi wani biki ba illa kara shiri da tayi akan
nada, dama a shirye take to saida ta kara wani,
Sun darji amarci duk da ba sabon Abu bane a
gurin su Amma yanzu sunfi da zakewa.
Tafiya takai tafiya, yau Auren Hajiya da Jalal
wata goma kenan inda Hany shekara daya,
dukan su ciki suke dashi, Jan ya samu kansa
yana son duka cikkunan kamar ransa Amma
yana tsoron yanda zai fada ma Mamasko yana
da wata mata har da ciki bayan Hany, wannan
abin duk ya tunashi dai yaji bakin ciki, Sai yaji
rashin kyautawarsa ga mahaifiyarsa, ga wani
tashin hankali da yakeji a cikin kansa haka
kawai, yafi kyautata zaton ko asiri aka masa
saboda da yawa suna son Hajiya Amma ta kisu
ta Aure shi, Kuma sun gaya mishi sai sunga
bayan sa.
Uwa uba gashi yanason ya dawo da Hany
Abuja saboda ta masa Nisa sosai, Hajiya tun
tana complain akan yawan zuwansa gida har ta
daina yanzu ta saba, duk weekend yana hanyar
garin su.
Ya dukufa neman gida har Allah yasa ya samu,
Yanzu ya Sami gida madaidaici a zone 4, anan
zai tare shida madam dinsa Hany. Tunda ya
gayama Hany zasu koma Abuja murna kamar ta
kasheta, saboda dama ta tsani yawon hanyar da
yakeyi duk sati, nan ta fara shirye shiryen
komawa Abuja, ga cikin ta da ya dan turo zai
Kai wata shida zuwa bakwai, baisan ita da
Hajiya wa zai fara haihuwaba.
sun dawo Abuja cikin nasara, saboda duk abinda
yake tsoro ko daya bai faruba, Hajiya bata gane
komai ba, dan yanzu gaba daya dukiyarta tana
hannun sa, shi yake tafiyar da komai. Sai dai
matsala daya ya zai raba musu kwana ba tare
da wanin su yayi zargin wani Abu ba,
Hany bata ganin sa da dare Sam, saidai da rana
yazo yayi abinda zaiyi ya koma gun Hajiya, Sai
assabar da lahadi yake kwana gida, shi Kuma
Sai yace ma Hajiya ai yana tafiya gun Mamasko
ne. Jan kenan mai Hajiya da Hany.
2⃣6⃣
Hajiya ce kwance saman sofa tana lallatsa
wayarta mantuwa tayi da wasu kayan ta da tayi
order kusan shekara daya aka tsaresu a border
dazu an gaya mata an sakesu, jiki na rawa ta
tashi ta tura cikin ta tayo cikin dakin sa, abinda
ya fado kunnen tane yasa ta manta mi tazoyi
dakinsa.
“Ooh my Hany I will send U”
“My Hany”
Maimaitawa tayi cikin hade girar sama data
kasa,
Murmushi ya sake mata, ya ware hannuwansa,
ta kasa masa musu ta fada jikinsa ya
rungumeta, ya shafa cikin nata yayi kasa da
kansa ya dora a cikin,
“Yaron Dady yaushe zakazo? Kaga Dady?”
Cikin sa’a kuwa cikin ya motsa,
“Laaaa kaga yana motsi, yaji abinda kake fada”
Dariya ya Sako, Wanda ya kara fitar da kyansa,
“Yaron Dady yasan Dady nasa, kayi sauri ka
fito inason ganinka,”
Cikin motsi ya karayi, batasan lokacin da ta
wangale da dariya ba, gaba daya ta manta da
zancen wata Hany da taji ya fada.
Haka ya mantar da ita zancen Hany gaba daya,
har ta gaya masa abinda tazo fada masa, sunyi
akan zai tura yaransu suje su dauko kayan.
Bayan sati uku.
Shigowar Jan kenan daga gidan Hany wacce ciki
ke bata wuya yanzu, sam batayi laulayiba sai
yanzu take yinsa, tare yake shida abokinsa
Ahmad wanda yakawo masa ziyara daga
Nassarawa, da yake Ahmad yasan komai shi
kadai yasan Jan ya Auri Hajiya,
sauri yakeyi yashige dakinsa tunkafin Hajiya
ta fito ta iskoshi, dan kuwa jikinsa inbanda
kamshin turaran Hany babu abinda yakeyi,
zaune yabar Ahmad a falo yana duban TV. Tun
kafin yakarasa dakin yaji muryar Hajiya na fadin
“oyoyo sweet Jan sai yanzu kashigo nagaya
maka bana son wannan sabon halin daka dauko
nayin dare awaje!”
Rungumosa tayi ta baya tana shakar
kamshinsa,
Dasauri tasake shi tare dayin baya tana zazzare
ido, gaban sane yayi mummunar faduwa, cikin
garaje take magana
“Jalal daga ina kake? daga ina kake nace ka
gaya min daga wajan wata yar iskar kake?”
magana take tana haki tamkar wacce taci
uban gudu,
Na dade Ina Kula da chanjinka idan nazo
tambaya Sai ka dauko min wani zance daban.
Duk kwana kinnan haka take tirtse shi da
tambaya wata ran idan tasoma fada zaku zaci
hauka tasoma yi,
Yau Kam ba sauki saboda ta hau sosai, kwalar
sa taci hade da makure sa cikin hargagi take
fadin “Jalal baza ka gaya min ina kake zuwa ba
kowani dare?”
wannan shine karo na farko dayaji tsanar ta ta
darsu a zuciyar sa, amma Kuma still akwai
tausayin ta kwance a cikin zuciyarsa, da idan
tanayi yana zaton tsabagen son datake masa
ne, ayanzu kuwa dauka yake tsabagen hauka ne
dason zuciya irin nata, wani munafukin
murmushi yasaki irin na mayaudaran maza, cikin
murya kasa kasa nawanda yasha shaka yashiga
fadin
“haba Hajiyata tayaya ki ke tunanin zan iya
kula wata mace aduniya bayan ke? Mai kamar
ki mezaiyi dawata Mace aduniya? Aini wallahi
kin isheni rayuwar duniya, banga macan dazan
duba inmata duban mace ba! Inaso ki kwantar
da hankalin ki kidaina damun kanki dani danni
banida matsala kodaya!”
Harara ta sake masa
“Jalal a haife Na haifeka wallahi, saboda haka
kada ka nemi ka raina min wayo”
Kashe mata ido daya yayi ya daga gira,
“But yanzu dai ni Mijin kine uban yayan ki,”
Sasautowa yayi kasa ya shafi cikin
“Yaron Dady kaga Mum dinka tana nema ta
kashe maka Dady ko,”
A hankali cikin nata ya shiga motsawa, Baki
Hajiya ta washe tareda sakinsa tana fadin
“Wannan yaron da kishin Dadyn sa yake, da ka
kawo karata Sai ya shiga nusata,”
“yauwa dan halas, shiyasa kake burgeni nake
alfahari dasamun ka a matsayin abokina Kuma
dana, Kaci gaba da mata wrestling a ciki” dariya
suka saka gaba daya,
Juyowa tayi ta fuskanceshi,
“,My Jan! Ni macece mai tsananin kishi
yakamata kadinga kiyayewa dan Allah,”
rungumota yayi a jikinsa yana fadin,
” bakida matsala dani Hajiyata ki kwantar da
hankalin ki wani sabon shop muka shiga nida
Ahmad shine na dau turaran nadan fesa inji
inyanada dadin kamshi sau daya ma na fesa
Ahmad yace min ai wannan turaran na mata ne
shine namaida na ajiye bama musaya ba muka
fito,”
nan danan Hajiya tasamu natsuwa a zuciyar ta
tayarda da abinda Jan yagaya mata, zuciyar ta
fes! Duk da cewa ta dade tanajin yana wannan
kamshin, Murmushi Jan yayi Yana mata wani
irin duba mai wuyar fassarawa!
Ahmad dake zauna yana duban su yana Kuma
sauraran abinda ke faruwa yayi gyaran murya
wanda yasa Hajiya saurin juyowa dan sam ta
manta da wani a palon, gaban Jan yai mugun
faduwa dan yafi kowa sanin halin Ahmad da iya
gulma tamkar mace, dan haka yayi saurin tsare
shi da shanyanyun idanuwansa masu kama da
kalar bacci, dole Ahmad ya hadiye abinda
keson fitowa daga bakinsa badan yasoba,
yashiga gaida hajiya cikin fara ‘a ta amsa tana
wage baki……….
2⃣7⃣
Hany zaune tana hada wasu kaya da suka
siyowa baby jiya, wayar Jan ce tayi kara, bata
kulaba dan ya mata kashedi akan kada ta
kuskura ta taba masa waya, mamaki ma take ya
akayi Jan ya bar wayarsa ya shiga wanka,
Bata kula ba haka har akayi Kira Na biyar, ta
tashi ta dauki wayar ta nufi hanyar bayi ganin
an sake Kira Kuma an rubuta Hajiyata yasa ta
daga wayar, saboda tayi tunanin Mamasko ce,
“Hello Hajiya Ina wuni”
Gaban Hajiya ne ya fadi jin mace ta daga
saidai jin tace Hajiya yasa bata kawo wani
dogon Abu a ranta ba,
“Lafiya yau, Ina Jalal yake ne”
“Eh yadan fita ne yanzu zai dawo Amma”
“Ok” sai ta kashe wayar.
Bata natsu ba sam ta kara Kira,
Hany cikin ladabi ta kara daga wayar,
“Yarinya wacece ke?”
Hany Murmushi tayi wato dai Mamasko naji da
Jan, Sai taji ko wacece,
“Hajiya nice fa.”
“Nice Hannah,”
“Ke wace hannatu Kuma, “
” Hajiya nice fa Matarsa”
Gaban Hajiya ne ya fadi tuni idonta suka
chanza,
Jan ne ya fito ya kalleta mika masa wayar tayi
tana kokarin goge masa ruwan jikinsa da towel.
Dakatar da ita yayi hadi da daka mata wata irin
tsawa,
“Uban wa ya Baki damar daukar min waya
harda fadin ke mata tace?”
Wannan tsawar tayi sanadiyar murdewar cikin
ta,
Bai kashe wayar ba Kuma Hajiya ta jiyo abinda
yafada.
Wurgi yayi da wayar ya fara safa da marwa a
dakin, idonsa sun kankance lokaci daya, hannu
yasa ya dafe kansa, bai tsaya kula Hany ba data
durkushe a gurin, da sauri ya saka kayan sa Sai
gida.
Hajiya ya gani tsaye kamar an mata mutuwa,
jikinsa ne yayi sanyi, dafe kansa yayi ya juya zai
fita saboda yasan mai faru wa ta Riga ta faru,
Daga baya Hajiya ta riko rigarsa,
“Wacece Hannatu Jalal”
Dago Kai yayi Yana kallon ta, idonsa sun chanza
gaba daya, baice da ita komai ba, gurgiza kai
yayi,
Ya bukaci ta sakesa, Amma ya kasa, janyota
yayi jikinsa,
Nan ta shiga rera masa kuka mai tsuma zuciya,
yayi rarrashi har ya gaji, batayi shiru ba,
Daga karshe kwantar da ita yayi ya zauna bakin
gado, ya dade dafe da kansa, daga karshe ya
bar gidan gaba daya, yana fita ta janyo wayarta.
“Hello kabeer, don Allah jalal nake son ka kula
mun da shige da ficen sa duk inda zashi a rika
binsa har a tabbatar min da abinda yakeyi Ina
yake zuwa.”
“An gama ranki ya dade”
Bata jira komai ba ta kashe, Saboda tsab zai
cika ta da surutai.
Ya koma gida Hany ya gani takure gurin da ya
barta, bata dago kai ta kallesa ba, tausayin ta
ya Kama shi, yazo ya fara rarrashinta itama,
“Miyasa zakaji haushi dan Na daga wayar
Mahaifiyarka”
Taci gaba.
“Da ace banga an rubuta Hajiyata ba wallahi
bazan taba daga wayar kaba, but kayi hakuri
kaji”
“Ya wuce ki daina damuwa”
“Amma naji muryan Mamasko ta chanza, bata
ma fa ganeniba Saida nace nice matarka.”
Numfashin sane ya tsaya Chak.
A hankali ya runtse idon sa, baice mata komai
ba, baya yayi da kansa ya kwanta ya fada tekun
tunani.
2⃣8⃣
“Hajiya mun gano yana zuwa wani gida a
wuse, kullum idan ya fita gidan ki chan yake
wucewa
Yakan dauki awa biyar achan sannan ya wuce
gun aiki, haka kamin yaje gidan ki Sai yaje chan
yayi kamar awa biyu sannan ya fito, assabar da
lahadi ma chan yake tarewa gaba daya, baya
fitowa gida sai Monday da azzahar Sai yazo
gurin ki,
Yana shiga da kayayyaki a gidan dukkan alamu
macece a gidan Amma bamu tabbatar ba, mun
karbo number gidan zan miki SMS dinta, haka
Kuma yana…”
” Enough!!!”
Ta dakatar dashi da karfi, bata tsaya jiran komai
ba ta fito gidan kamar mahaukaciya,saidai bata
san Ina zata nufa ba, wuse ta wuce ta fara raba
ido, Kabeer ta kira saidai wayarsa a kashe take,
zuciyar ta kamar ta fashe saboda tsananin ta
tashin hankali,
“Maman Ummi kece a duniyar nan.”
Idonta ta dago dasu, mutumin da suka rabu ba
girma ba arziki ne gabanta, kamar ta sauke
akansa, saidai Kuma batason ya gane halinda
take ciki, saboda gani take batada makiya a
duniyar nan kamar su.
Murmushi ta kirkiro,
“Haji Sani ya bayan rabo,?”
“Sai khairan Maman Ummi, kin gujemu iya
gaskiyanki, ai Sai ki waiwayomu koda sau daya
ne,”
A ranta tsaki taja,
“Hmmm abubuwa sun min yawa,”
Ta fada a takaice, idonsa yakai gun tulun cikin
ta, murmushi yayi,
“Gashi Ummi Zata sami kanwa Kema Kuma
zaki sami jika ko.”
Kinsan Ummi tayi Aure tun last year,
“Uhum.”
Bata ce masa komai ba bayan haka,
Zagayowa yayi ya shiga motar,
“nidai sauke ni gidan yata,” bai jira mi zatace
ba, ya zauna ta tada motar saboda ta matsu ta
sallamesa ta tafi aikin gaban ta, ya shiga mata
kwatance har suka isa gidan da zashi,
“Don darajar iyayen ki ki shigo ciki,”
“Malam Sani please bana son shishigi in my
life,
Ka fita Sai an jima.”
Bai koyi motsi ba haka ya shiga rarrashinta har
ta aminta ta shigo ciki. Tana shiga ta daga kai
ta kalli number gidan No 75Q
Suna shiga ta daga kai ta kalleta tsab ta
ganeta yarta ce Ummi.
“Ummi.!”
Wacce aka kira da Ummi ta kalleta ba zata iya
tuna ta ba Amma dai suna tsananin Kama da
ita, duk bacin ran da Hajiya take ciki bai hanata
farin cikin ganin yarta ba, wacce ta yafe
shekaru masu yawa sa suka wuce, saboda son
rai irin nata, nan dai Alhaji Sani ya gaya yarinyar
cewa Maman tace, Hajiya tafi kowa farin ciki da
wannan, taji dadin fitowar ta yau.
Mama bari Na kira muku shi yana ciki kuwa, da
sauri Ummi ta nufi daki don tado da mijin ta,
daidai lokacin sakon Kabeer ya shigo wayar ta,
Kamar ba zata bude ba Sai Kuma ta bude,
House No 75Q
Migewa tsaye tayi kamar an mata allurar
mutuwa, yayi daidai da fitowar surukinta,
A hankali ta bude ido ta kallesa,
Suna hada ido ya kasa gane mi yake ciki tsaya
wa yayi komai nashi ya daina motsi.
” Jalal kaine mijin yata Hannatuannatu “…..
Ruguntsumi mijinta mijin yarta………
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.blogsport.com
www.Benaxiromar.com
2⃣9⃣RUGUNTSUMI!!!
Written by
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
Story by
Hauwa M. Jabo
A rikice Hajiya Kubra ke nuna sa da yatsa
tana fadin,
” Jalal kaine mijin yata Hannatu?
Innalillahi………”
bata karasa ba tayi k’asa rike da kugunta tana
fadin “
“Washh! Wash!!” Da gudu Jan yayo kanta yana
fadin “subuhanalillahi Hajiya! Hajiya!!” Tuni tafita
haiyacinta sai wani irin nishi takeyi tana cije
baki, gaba daya Jan ya rude ya rikice sai faman
tambayar ta yakeyi “Hajiya Meye ke miki
ciwo,baya ne?” Saboda lokacin da Hany ta kirasa
bata gaya masa cewa mahaifiyarta bace, shi ya
dauka tsabar kishinta ne yasa ta wannan
binciken.
“Ko cikin ne?”
duk a gigice yake jero mata wayan nan
tambayoyin,
“Hany wacce tayi mutuwar tsaye saboda
tsabagen Al’ajabi da mamakin ganin halin da
wacce aka kira da mahaifiyar ta tayi a
sakamakon ganin mijin ta da tayi, sai a wannan
lokacin ta sami karfin halin fadin
“Jan inajin fa haihuwace za tayi asibiti ya
kamata mukai ta”maganar da Hannatu tayi ne
yazame masu tuni akan abinda yakamata suyi,
nan da nan kuwa suka kinkimeta zuwa waje a
motar ta suka sakata hannatu ta zauna da ita a
baya yayinda Jan ke tukin motar bakon su
Kuma a gaban motar,
Gudu Jan keyi na fitar hankali tamkar zai tashi
sama burinsa bai wuce ya gansu a asibiti ba a
duba masa Hajiyarsa ba Fadi yake a zuciyar sa
‘shikenan ya banu ya lalace asirin sa yagama
tonuwa asirin boye yafito fili’.
Daya zuciyar sa ke raya masa me zai hana
kawai ya wawashe dukiyar Hajiya ya kara gaba
abinsa, yaje ya dauki yar tsohuwar sa da Hany
dinsa su canza gari, kai suma bar kasar gaba
daya ta yanda babu yanda za ayi a ganinsa.
A hankali yasauke ajiyar zuciya yayin da dayar
zuciyar ta sa ke fadin ‘kai Jan ka kwantar da
hankalin ka kawai tunda ga halin da Hajiyar take
aciki, ba Sai ka gudu ba dafa ta mutu yanzu
dukkan dukiyar ta yazama naka tunda bata alaka
da kowa bare asan tama mutu.
Dan guntun tsaki yaja a hankali yake furta
idan Hajiyata ta mutu ai nima na mutu dan bana
jin zan iya rayuwa ba tare da wannan yar
tsohuwa ba! Gabansa ne yayi mummunar
faduwa daya tuna kalmar ta takarshe, “Jalal
kaine mijin yata Hannatu!!!?”
Ya tabbata baiji da kyau bane saboda ta gaya
masa yaro daya ta haifa kuma ya mutu, sauri
yayi ya kawar da wannan tunanin mara dadi.
A jiyar zuciya mai karfi yasauke har sai da
bakon nan yayi saurin duban sa.
“Hannatu kuwa ta kasa gane a wani yanayi
take ciki, murna takeyi daganin wacce aka ce
itace mahaifiyar ta wacce sam bata amsa
matsayin ta na uwa a gurin taba, domin kuwa a
ganinta sam ba tayi mata adalci ba da yafe ta,
ta sallamata a lokacin da take tsananin bukatar
ta bata taba waiwayar taba koda sau daya ne
tsawon shekarun nan sai yau da Allah yasa suka
hadu a dalilin da ita kanta bata sani ba, wannan
wace irin uwa ce da bata son yar ta data haifa
da cikin ta?” a daya bangaran na zuciyar ta
kuwa tana mamakin abinda yasaka ta shiga
wannan halin dan kawai sunyi ido hudu da mijin
auran ta! Shi dama Sun san juna ne? Kokuwa
akwai wani abu a tsakanin sune? “Hmm Gaskiya
tana tsananin bukatar amso shinta! Shin wa zai
amsa mata ne Jan kokuwa Hajiya wacce ke
kwance bisa cinyar ta. Gabanta ne ya yanke
yafadi rass!!! Ganin jikin Hajiyar ya saki bata
motsi, a gigice tace
“kawu!Tafa daina motsi kalla ka gani!! “
Dasauri yajuyo yana duban fuskar ta, yana fadin
“Innalillahi…….” Wani mahaukacin burki Jan
yaja motar tashiga tangal tangal Allah dai ya
tsare ta tsaya cak, cikin wani irin sauri tamkar
ya kifa yazagayo ta dayan kofar, jijjiga ta
yafarayi yana fadin
“Hajiya! Hajiya!! Dan Allah karki tafi kitashi
Hajiya!” Dakyar bakon da aka kira da kawu ya
lallashi Jan kafin ya natsu Amman sam yaki
yarda yayi tukin saidai shi kawun yaci gaba da
tukin yayin da Hannatu ta koma gaba shikuma
Jan ya kankame Hajiya a bayan motar.
Sosai kawu yayi gudu da motar har Allah
yakai su asibitin lafiya Jan sai sambatu yake
tayi, nan danan aka gungura Hajiya bisa gadon
daukar marasa lafiya, dakin haihuwa aka nufa da
ita kai tsaye, likitoci biyu mata ne suka rufu
akanta cikin kwarewa da aikin su tsawon wani
lokaci anata abu daya amman har yanzu
haihuwa shuru, Jan kuwa tamkar ya tura kai
cikin dakin haka yake ji, sai faman safa da
marwa yake tayi a tsakanin dakin haihuwar da
reception din, tuni yafice a hayyacinsa harma
bai san me yake fadi ba,
Likitar ce tafito fuskar ta a daure tace masu
tana son ganin su a office dinta, wani irin
harara Jan yasakar mata cikin hargagi yake
fadin “dallah malama ki fadi duk wani abinda
zaki fadi basai daya daga cikin mu yabiki ko ina
ba Amman ki tabbatar bace min zakiyi matata
ta mutu ba!!”A gigice Hannatu tayo kansa, taba
fadin “JAN hauka kakeyi ne? kwakwalwar ka ta
tabune dakake kiran mahaifiya ta da matar ka?
Gani nan fa tsaye gaban ka kake kiran wata da
matarka” cikin rashin damuwa da hayaniyar da
sukeyi a tsakaninsu likitar ta fara magana domin
kuwa ta kule da maganar da Jan yagaya mata.
“dama so nake ingaya maku bazata iya
haihuwa da kanta ba sai anyi mata aiki dan
kuwa mahaifar ta tayi laushi dayawa ta sha
haihuwa fiye da kima wanda hakan yasa bazata
iya haihuwa da kanta ba dan haka kai da kake
ikirarin mijinta ne kazo kasa Hannu.”
ta wuce abinta tabar su nan sake da baki kuka
Hannatu ta fashe dashi da karfi tare da sakin
Jan wanda yarasa awani duniyar yake ciki
shima,
Shin abinda ya jiyo ma kunnen sa gaskiya ne?
Da gaske Hajiya mahaifiyar matarsa ce,
Ko Kuma rudun da ya shiga ne yasa kunnuwan
sa sake jin hakan.?
“Da karfi ya juyo yayi gun Hany da ta durkushe
tana wani matsanan chin kuka”
Kukanta ya bayyana masa abinda yaje tunani,
tabbas Mamanta ce,
Tsaya wa yayi kamar an dasashi a gun, komai
nasa baya aiki,
Likita ce ta kara fitowa tana maseefa.
Ganin yanayin da suke ciki yasa tadan
sassauta, komawa tayi tazo da wata takarda
Amma ba Wanda ya iya karba cikinsu,
“Idan fa Baku saka hannu ba zata mutu”
Gaba dayan suka zabura suka yo kan Dr. Da
nufin karbar takardar Jan aka baiwa ya saka
hannu.
Hany ta shiga yanayin da bata San kalarsa ba,
numfashinta ne ya fara chijewa yana yin sama-
sama zuciyar ta tamkar ta fito waje ta rasa
gane me takeji.
Kuka yakeyi tamkar jiniya irin yanda yara
kanana suke yi idan sun kare kuka, sautin
wannan kukan yafi dafa zuciyar mai sauraren sa
fiye da kuka.
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.tk
www.Benaxiromar.com
3⃣0⃣RUGUNTSUMI!!!
Written by
Fiddausi Sodangi
Hauwa M.Jabo
Story by
Hauwa M. Jabo
Kuka mai sauti,Shin da wanne zaiji, da
surukarsa matarsa ko kuma Yar matarsa Kuma
matarsa.
Karo Na farko da ya fara dana sanin abinda
ya aikata,
Haka suka kasance a gurin, Hany ta dawo abin
tausayi lokaci daya har ta chanza kamanni, Jan
da baya ma son ya dago kai ya kalli Hany, ya
kwana da uwarta ya kwana da ita, sannan duk
suna dauke da cikin sa, dafe kai yayi iya
karfinsa ya cije lebensa, wasu konannun hawaye
ne suka fito masa, hadi da wata kara kamar
mahaukaci sabon kamu……
TUNA BAYA….
“Baffa ni Kurba zan Aura”
Alhaji shafi’u ne yake fada ma mahaifinsa cewa
Kubra yakeson ya aura, Amma mahaifinsa yaki
aminta da hakan sabod rashin kamun kan Kubra,
“Shafi’u bawai bana son farin cikinka bane,
nima zan so ka auri duk wacce kake so,Amma
yana da kyau ka gane mace ta gari tafi komai
dadi a duniyar nan, sannan zaka sami yaya Na
gari ta hanyar ta, yarinyar nan kowa yasan
gantalalliya ce ga uban kwadayi da yake
damunta haka zaka….”
Katse mahaifinsa yayi ta hanyar dakatar dashi
da hannu.
“Baffa ko wace iri ce ni Ina sonta Kuma zan
Aure ta.”
Yana fadar haka ya mike ya wuce yabar iyayen
sa zaune,
“Kin dai ji yanda mukayi dasu”
“To kenan ba zaka Aure ni ba?”
Ta fada cikin muryar yaudara,
“Zan aureki mana, ai tunda iyayen ki sun
amince shikenan banida burin da ta wuce Kasan
cewa tare dake”
Haka sai Kubra da shafi’u suka nace akan Sai
sun auri juna iyayen shafi’u basason auren sam
haka dai aka lallaba aka kai amarya dakinta,
Zaman su suke cikin kaunar juna da baiwa
juna kulawa har Na tsawon wata daya,
Mafarin rigimarsu shine cikinta Na farko, ita
batason ciki shi Kuma yana son ciki haka ta
sakashi gaba da cin mutunci, karshe tayi yan
jike jikenta na gargajiya ta zubar da cikin ta na
farko.
Sunyi rigima sosai daga baya ya hakura,
Ya maidata gun su baffa lokacin da tafiya ta
Kama shi kasar tura domin gudanar da ayyukan
sa Na yau da kullum.
Kubra ba tada jinkirin rashin namiji kusa da
ita, hakan yasa ta fara tunanin yanda zata rika
fita waje dan kawar da sha’awarta, ta kuwa
samu, dan tana zillewa taje waje tayo yawon ta
zubar dinta ta dawo, har takai tana lalatarta da
kanin mahaifin mijin ta, har takai ta samu ciki
dashi kamin mijinta ya dawo, nan dai tayi yanda
tayi ta zubar da cikin nan.
Kubra bata zamo suruka ta gari gun surukanta
ba, kullum cikin ci musu mutum ci take, masifar
safe daban ta yamma daban.
Haka har mijinta ya dawo daga tafiyar da yayi,
cikin nasara saboda ya samo alkhairi mai tarin
yawa, haka ta shiga ta fita ta hana iyayen
mijinta komai.
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.tk
www.Benaxiromar.com
Ruguntsumi end
By Hauwa jabo 12:32 No comments
⃣1⃣RUGUNTSUMI!!!
Written by
Fiddausi Sodangi
Hauwa M. Jabo
Story by
Hauwa M. Jabo
Ta mallake mijin da duk wani abu da ya mallaka,
Kuma ita ba boka ba malami da tsabgegen
makirci take tafiyar da komai nata.
haka taci gaba da gudanar da gurbatacciyar
rayuwar ta, tana juya mijin da danginsa son
santa, gefe guda Kuma tana tare da wasu
mazan, saboda ita bata taba yarda da cewa
namiji daya zai iya biya mata bukatar ta ba.
Duk lokacin da mijin ta yayi tafiya lokacin zata
saka kafa tabar gidan har Sai ana gobe zai
dawo take dawo wa, hakan yasa duk cikin da
tayi Sai ta zubar saboda ita kanta ba zata gane
cikin na waye ba, cikin farko da ta tabbatar
cewa Na mijinta ne bayan Wanda ta zubar shine
wata tafiya da tayi da mijin nata sukayi wata
hudu, to tunda taje bata sami kowa ba da zasuyi
lalatar su, hakan yasa ta bar cikin.
Alhaji shafi’u yaji dadin cikin sosai, hakan
yasa ya dauki son duniya ya daurawa cikin, har
Allah yasa ta haifi cikin, aka saka ma yarinya
sunan maman shi wato Hannatu.
Hannatu ta sami gata a gun mahaifinta fiye da
yanda ake tunani,
Duk da cewa Hajiya Kubra ta haihu bai hanata
bin mazan taba,
Ga igiyar Aure akanta, ga Kuma shegen bin
maza, tun mijin bai sani ba har ya fara zagin ta,
har zargin sa ya tabbata,
Lokacin da ya gane abinda takeyi ba karamin
case sukayi ba saboda yana sonta Kuma yana
kishinta,
Amma ita ko a jikinta,
Kuka ma ta saka masa wai yana tuhumarta da
bin maza, haka dai aka mamushe case din har
Allah ya kara bata wani cikin, shima cikin bata
zubar dashi ba saboda ta san mijinta ne mai
cikin, saboda a lokacin tadan sassauta bin maza
saboda wannan rigimar da sukayi da mijinta.
ta haifeshi ta sami namiji.
Rayuwar Hajiya Kubra ba abar kirki bace,
saboda tun tana yan mata take bin maza har
tayi Aure bata daina ba,
Taci gaba da tafiyar da rayuwar ta cike da
kazanta ta kwamacala, ana ahaka takuma yin
wani cikin wanda suka sha rigima ita da
maigidan nata akan cewa saita zubda shi, rufe
ido yayi yai mata kaca- kaca amman hakan bai
sa tafasa abinda tayi niyya ba.
Suna acikin wannan hali ne tafiya takama sa
zuwa indiya cike da fargabar tafiyar gudun kada
ya tafi ta zubda mai ciki ya dube ta asafiyar
dazai bar kasar yace “Maman Ummi ina hadaki
da girman Allah kada ki zubda min cikin nan
wallahi Maman Ummi Allah ya aza min kaunar
wannan ciki naki”.
Tun kafin ya kare maganar sa ta katse shi
tahanyar daka mai tsawa
“dallah Mallan rufe min baki! Wallahi wannan
cikin tamkar nacire shi nagama ne! Angaya
maka ni akuya ce ni dazan zauna inta tara maka
y’aya kamar sakara! Salon wahalar su ya tsofar
dani inzama tsohuwar karfi da yaji ko?” to
badani za ai wannan iskancin ba.”
Zaiyi magana takuma daka masa tsawa wanda
yasa shi nufar kofar fita dasauri, har yasaka
kafa awaje yajuyo yace,
“Maman Ummi, idan har kika zubda wannan
cikin Allah ya saka mani duniya da lahira!
ubangiji Allah ya hanaki haihuwa a lokacin da
kike tsananin bukatar shi ko kuma ya baki shi
yakasan ce uban dan ko yar bayada bukatar
shi.”
Mikewa tsaye tayi ta nufosa dasauri ya fice ya
bar mata gidan, wannan tafitar dayayi ne
yazamo ajalinsa sunsamu hatsarin jirgi a hanyar
su tazuwa inda babu ko mutum daya daya tsira
acikin su.
Anyi rabon gado kamar yanda addini ya tanada
kubra taci gaba dazama da yaranta acikin gidan
ta, mutuwar mijin ta ya daketa sosai sai dai
bayan wani dan lokaci da tafita takabanta taci
gaba da sharholiyar ta, sam yaran basa samun
kulawa a gun mahaifiyarsu, ana haka yaron
namijin yakamu da ciwo wanda bai kwana ko
daya ba Allah ya amshi kayan sa, sam kubra
bata damuba tacigaba da harkar gaban ta,
arzikinta sai dada karuwa yakeyi domin kuwa
kasuwanci sosai takeyi abinta, ga ta da sa’a duk
wani kasuwanci ta sa saka gaba,
Gefe guda masu kudi suna sonta da aure Amma
sam bata aminta saboda tana kallon Aure a
matsayin abinda yake takura rayuwarta da
kwana da namijin da take bukata, hakan yasa
ko sun nemeta da Aure take mai dashi abin
shiririta da holewa, tayi suna a bariki, dalilin da
yasa dangin mijin sukaga Hannatu bazata samu
tarbiyar kirki ba yasa yan uwan mijin karbar ta,
wanda ba karamin rigima akayi ba, Ganin batada
lokacin tsaya wa rigimar ya yasa ta sallama
musu ita, akan cewa ya murjeshi musu ita har a
bada, ba zata nemeta ba suma kada su nemeta
da yar,
Iyayen ta ma sunyi sunyi Amma Ina ko a jikinta,
mahaifinta da bakin cikin ta ya bar duniya,
mahaifiyarta kuwa tayi-tayi, Amma Ina, addu’a
take Amma ba abinda ke chanzawa, har ta
hakura ta bar ma duniya ita, har Allah ya karbi
ranta.
Bata kula da dangin ta sam, gasu cikin
matsanancin talauci ita kadai ke harkanta.
Hajita Kam Arzikin bana yaci uban nada, saboda
babu kasar da bata zagawa, daga karshe ta
tattara tabar kasar gaba daya, tafi shekara
goma a ingila daga karshe ta tattaro ta dawo
Abuja dazama tacigaba da gudanar da rayuwar
ta mai cike da kazanta wanda ko kare baici,
ahaka ne kuma ta hadu da Jan gundarin
rayuwar ta. To kunji tarihin wannan baiwar
Allah.
3⃣2⃣
Anyiwa Hajiya aiki cikin nasara an fiddo mata
kyakkyawar diyar ta Mace mai cike da koshin
lafiya, ankai ta wani daki inda aka sanar dasu
Jan cewa zasu iya shiga suga Yar da aka haifa,
sai dai abin mamaki babu wanda yayi yinkurin
zuwa ganinta daga mijin har y’ar,
Hany jikinta ke rawa tana wani numfashi sama-
sama kai da gani Kasan bata cikin hayyacinta,
ko motsi batayi ba illa wata ziza da take mai
Kama da kukan yara.
kawun ne yayi karfin halin shiga dakin dan yaga
halin da take ciki, yasame ta tanata sharar
baccin ta fuskar nan tata tayi fayau, jikinsa a
sanyaye ya dauki diyar ya tsura mata ido,
tsawon lokaci yana rike da y’ar yana sake sake
a zuciyar sa jiki ba laka ya ajeta tare da zaro
wayar sa ya kira can garin dumin yasanar dasu
halin da ake ciki, waje yakoma yasami su Jan
har yanzu acikin hali na kidima, nasiha yashiga
yimasu mai ratsa jiki, daga karshe yasanar dasu
gobe insha Allahu sau ran dangi zasu iso dan
asan yaza ayi a warware wannan babban
matsala, cikin kuka Jan yace dan Allah kawu a
biya a dauko min mahaifiyata domin in roketa
gafara nasani hakkin ta bazai barni inzauna
lafiya ba yakare maganar cikin matsanancin
kuka abin gwanin ban tausayi.
Haka wayan nan bayin Allah sukai kwanan bakin
ciki babu wanda ya runtsa acikin su, musamman
Hany da tafi Kama da zararriya, da ka ganta
zaka fahimci hakan.
Washe gari misalin karfe hudu na maraice
dangin hannatu suka iso tare da mamasco
wacce duk ta rikice dajin wannan mummunar
labarin,
Tundaga harabar asibitin gaban Mamasko ke
faduwa tamkar zai fado kasa Jan na ganinsu
hankalin sa yakara tashi bama kamar daya hada
ido da Mamasko ba, tuni yanemi natsuwarsa ya
rasa ji yake tamkar ya sheka da gudun tsiya,
Hany ta mike a guje ta fada kan kakarta tana
kuka mai tsuma zuciyar mai saurare,
A haka suka dunguma zuwa cikin daki inda uwar
gaiyyar ke a ciki a kwance tuni ta dade da
farkawa sai kuka takeyi tamkar ranta zai bar
jikinta.
Ahaka suka shigo dakin gaba dayan su bakin
su dauke da sallama, Mamasko itace tazama
kar shan shigowa, ido hudu Mamasko tayi da
Hajiya Kubra, wani irin salati Mamasko tasaki
ta nuna ta da yatsa hade da yanke jiki tafadi
Hajiya Kubra wacce tayi mutuwar zaune tuni ta
rikice jikinta yahau kyarma bakinta na rawa
tashiga fadin wacece wannan!?” babu wanda
yabi ta kanta tuni Sun rufa akan Mamasko
wacce tayi dugowar suma, Hany ce tabawa
uwar ta amsa jin bakinta yakasa daina furta
wacece wannan datake ta fadi, kuma da alamun
ta kagu taji amsar tambayar tata, “Mahaifiyar
JALAL ce” ihu Hajiya Kubra tasaki tana fadin
“Kada dai kuce min JALAL DAN WANNAN
MATAR NE……..”
www.fiddausi.wordpress.com
www.hauwajabo.tk
[24/11, 9:20 p.m.] Hajiya: RUGUNTSUMI
End
Ba Wanda yayi ta kan Hajiya, illa gun Mamasko
da aka nufa ana son ta far fado, Hany kuwa
gaba daya bata iya ko daga kafa, ga cikin nan
da ya mata mahaukacin nauyi, duba ta kai gun
mahaifiyarta da taga gaba daya ta kara fita
hayyacinta, Sai wani surutai takeyi Wanda ba ta
gane mi take fada, takai duba da jinjirar da ke
kwance tana sharar bacci, kaninta Kuma dan
mijinta, zuciyar tane ta rufe ta daina gani gaba
daya. ta rasa mi takeji, bakin ciki ko nadama,
tabbas rayuwarta cike take da bakin ciki, ta
rasa gatan uwa, ta tashi gun dangin uba dan
gudun gurbacewar tarbiya, Amma Kuma Sai ya
zama bata sami kulawa ta musamman a gun
wayanda suke takama da sune iyayen taba, har
takai ta auri mijin mahaifiyarta.
Ta tuna lokacin da Jan yazo da zancen
aurenta, k’anin baban su bai tsaya binciken
komai akai ba, kawai yace ya turo
magabantansa tamkar sun gaji da ita aka aurar
da ita ba bincike ba komai, wannan yasa auren
su bai dau lokaci ba.
Hayaniyar ce ta karu a gun, wanda yasa
hankali ta ya dawo jikinta, ta dawo dogon
tunanin da takeyi.
Mahaifiyarta ce take wasu surutai.
Tamkar wata zararra haka Hajiya ta dinga
fadin
“Mekuke nufi?”
kada dai kuna nufin Jan d’an wannan matar ne?”
wayyo nashiga uku na lalace ni Kubra ?” wani
irin ihu tasaki tamkar ba itace akaima aiki ba, da
sauri Hannatu ta riketa duk kuwa da tsananin
haushinta da takeji, ganin zata fado daga gadon
tana sambatu.
Ruwa Jan ya shafa ma Mamasko a fuska, tasaki
wani irin ajiyar zuciya a hankali idanuwanta suka
shiga budewa, kuka tafashe dashi tana kokarin
tashi tsaye, Jan ne ya kamata ta mike tana
nuna Hajiya Kubra wacce ke kuka tamkar ranta
zai fita.
Wani irin mugun kallo mai wuyar fassarawa
Mamasko tashiga aikawa Hajiya Kubra dashi
tana nunata da dan yatsa, murmushin takaici
Mamasko tayi tashiga fadin
“Malamar islamiya kenan! Ai shi Allah ba
azzalumin bawan sa bane sai wanda ya zalunci
kansa! Da dukkan alamu kinyi amanki ne kika
lashe! Dan abinda idanuwana suka gane min,
kunnuwana suka jiye min gangar jikina ya bani
hankalina da tunanina suka raya min shine Jalal
kika Aura! Bayan kingama watsewa dashi, lallai
wannan ishara ce Allah ya fara nuna maki tun
anan duniya! Lallai ko baccin mutuwa nayi na
farka bazan mance wannan mummunar fuska
taki ba.”
Ta gyara tsayuwarta ta koma fuskantar
Hajiya Kubra wacce ke ta raba ido tana kuka,
rike da zuciyar ta wanda kemata barazanar
tarwatsewa, ta nuna Jan da dan yatsanta,
“kinga wannan dan dake tsaye? shine wannan
tatsitsin jaririn wanda ki ka haifesa daga karshe
kika dire min shi kika gudu kika barni dashi cikin
qishirwa mai tsanani.! Wanda tun daga ranar
ban kara sakaki a cikin idanuwana ba sai yau da
Allah yatoni asirinki, kikai Amanki kika lashe
dakanki saboda tsabagen son zuciya irin naki!”
“Zaki iya tuna ranar Assabar da muka hadu
dake a kasuwa??
Kina sanye da babban Hijabi?, Kika ce mun ke
malamar islamiya ce, kina bani rikon jinjirin nan”
ta nuna Jan da yatsa, “Wanda Na tambayeki
sunan sa, kikace mun Muhammad? Nace
bashida lakabi kikace mun kina zuwa?
Sabida tsakanin kukan da yakeyi, dan kishin
da yakeji, kikace bari ki karbo masa ruwa?
Tin daga ranar ban kara ganin ki ba, kin tuna
ranar?”
Murmushin takaici Mamasko ta kara Saki, akaro
na karshe tace to malamar islamiya, wannan yar
dakika haifa da danki na cikin ki ” Y’A CE KO JIKA?“
takuma juyawa ta nuna cikin dake jikin
Hannatu tace shi kuma wannan na ciki dabai zo
duniya ba ” D’AN KISHIYA NE KO JIKA?“
Gaba daya dakin yayi tsit bakajin komi sai sautin
kukan Hajiya dake tashi,
Tabbas ta tuna lokacin da ta gudu daga sayen
ruwa ta baiwa Mamasko rikon jinjirinta ta gudu
ta barshi yana tsalla ihu.
Jinjirin da shine cikin shegen ta na farko tun
kamin tayi Aure,
Lokacin da tayi cikin duk wani abin zubar da ciki
tasha amma cikin yaki zubewa, iyayen ta sun
ringumi kaddara har ta haifi cikin amma ita ta
kasa rungumar kaddara inda tayi alwashin sai ta
salwantar da da jinjirin ta ko wace irin hanya,
sabida ba zata bari mijin da zata Aura ya gane
cewa ita ba budurwa bace.
Wannan dalilin yasa ta barwa Mamasko rikonsa
tayi amfani da damar siyo ruwa ta gudu ta bar
mata shi.
Wata gumza ta saki, mai kama da kakarin
mutuwa.
A gurin kowannan su na cike da tsananin
mamaki da Al’ajabi na wannan lamari dake
faruwa, Jan wanda ke tsaye tamkar an dasa
shi, kwakwalwarsa nata hautsinawa, yama rasa
awace duniyar yake ciki Jikinsa sai rawa yakeyi
zuciyar sa na zaiyano masa kalaman Mamasko.
“wai me wannan yar tsohuwar take nufi ne?
Tana nufin shi Jalal ya auri uwarsa data
haifeshi da cikinta bayan ya gama lalata da ita
daga karshe yai mata ciki harta haifa masa
y’a?” Ya kuma auri kanwar sa wacce suke uwa
daya har yayi mata ciki haihuwa yau ko gobe?”
” No!!!!!!!!!!!!”
Yafada dawani irin karfi ya dunkule hannuwa
tamkar mai shirin danbe, wanda ya jawo
hankalin likitoci zuwa dakin, lokaci daya yafara
wata irin dariya yana zubar da hawaye, yana
fadin “No! No!! No!!! Ba ita bace!!!” Sai Kuma
yasaki wata dariyar mai karfi yana fadin
“yes! Yes!!”
Sai yau ya gane son da yake ma Hajiya son d’a
da mahaifine.!! Ya gane tausayin ta da yakeji
tausayin da gun uwarsa ne, tabbas son uwa gun
danta daban yake, sau da dama ya kan rasa
wane irin
yakeji game da Hajiya, Hannah ma haka yakeji
game da ita, itama Hajiya tana jin hakan , Hany
ma takan ji haka, Sai suka tafi akan cewa
soyayya ce daga Allah.
Gadan-gadan yayi kan Hajiya ya shaketa yana
dariya, hawaye na sauka a saman kumatunsa,
yana fadin
“No! No! Ba ita ce Mamata ba Yes! Yes!
Mamasko tace kece Mamata” Yana jijjigata iya
karfinsa yana wannan sunbatun,
Duk Wanda ya kallesa yasan ya sami tabuwar
hankali, Da kyar likitocin da kawu sukai nasarar
banbaresa ajikin uwar sa Hajiya Kubra.
Wani irin ihu yayi hade da zabura ya watsar
dasu ya fice da gudu.
Da gudu daya daga cikin likitocin ya rufa
masa baya tare da yi ma masu gadi izinin rufe
Gate din asibitin Amman ina tuni Jan ya arce a
dari, da kyar suka kamo shi suka masa allurar
bacci sannan ya yiyi bacci.
Hannatu kuwa lokacin da ta fahimci mijinta
yayan tane, bayan sunun mijinta ya auri uwarta,
Ashe shima uwarsa ce, cikin ta ya fara
murdawa, ta durkushe tana murkususu da
alamar nakuda ne yakama ta babu wanda ya
lura da ita sai dawowar dayan likitan cikin dakin
shine ya kula da halin datake ciki, nan danan
aka nufi dakin haihuwa da ita abin gwanin ban
tausayi.
Da sauri likitan da yayi saura a cikin dakin ya
karasa gun Hajiya wacce ke wani irin kakari rike
da zuciyar ta, gaba daya kuka mutanan cikin
dakin keyi babu mai lallashin wani kawu ne
kawai mai karfin halin dayake ta tausar zuciyar
sa, batare da zuciyar sa tayi rauni ba.
Likitan ne ya umurcesu da su basu waje zai
duba Hajiya wacce tuni tafice a hayyacin ta.
BAYAN AWA UKU
Likitan dake kula da Hajiya ya fito fuskar sa cike
da gumi, da sauri suka nufosa da kyar ya iya
bude bakinsa yace kuyi hakuri tashiga COMA
Amman in sha Allahu nan da kwana bakwai zata
farfado, daga haka bai kara cewa komi ba yayi
gaba abinsa.
Likitan dake kula da Hannah shima yafito ya
sanar dasu Allah ya sauke ta lafiya ta sami da
namiji, itama mai jegon tana lafiya lau.
Ajiyar zuciya suka saki gaba dayan su zuciyar
kowanne na raya masa wani abu daban.
Jaririyar da Hajiya ta haifa aka miko masu,
Mamasko tasaka hannu biyu da karbeta zuciyar
ta na harbawa, ta tsurawa diyar ido tana kallon
ikon Allah gaba daya diyar kama take da Jan
tamkar kwabo da kwabo. Likita ne ya fito da
jinjirin da Hany ta haifa, Mamasko cikin kuka
tasa hannu ta karbesa, Shima kamar su daya da
Jan, Kuka take kamar ranta zai fita, tayi burin
Jalal ya hadu da mahaifiyarsa Amma ba ta
wannan mummunar hanya ba.
Kallon yaran take tana hawaye su Kuma Sai
bacci suke abinsu, su Kam an cutar dasu basu
san hawa ba basu san sauka ba.!!!
BAYAN KWANA HUDU.
Tuni an sallami Hannatu, kakarta ta matsa
lallai sai dai su koma dan ta kula da jikarta, dan
gaba daya bata cikin haiyyacinta tayi wani
zurum, Kuma taki baiwa jinjirin Nono ko
karbansa ta kasa yi, idan ta tuna cewa ta kwana
da yayanta Sai taji tamkar Allah dauki ranta dai-
dai wannan lokacin, wace irin jarabawa ce Allah
ya mata? Ko wane lokaci tunanin da take yi Sai
ta fashe da kuka, bayan Wannan ba abinda
take yi, duk ta lalace ta koma tamkar gawa,
haka suka wuce kowanne ransa babu dadi.
Mamasko ce ta tsaya da Hajiya saboda tausayin
jaririyar da Allah ya aza mata, wacece take kallo
a matsayin yar jikanta, ga uba chan har yanzu
bai dawo hayyacinsaba.
BAYAN KWANA TARA.
A yaune Hajiya Kubra ta farka, sai dai batayi ko
minti goma ba Allah yayi mata rasuwa
kasancewar zuciyar ta tariga ta buga.
Allahu Akbar.!!
Likitoci sunyi kokarin daidaita hankalin Jan Sai
dai abin yaci tura, ya riga ya rasa hankalinsa
gaba daya, zuciyar sa ta kasa tariyo masa
yanda ya kwanta da mahaifiyarsa da Kuma
kanwars har dukan su suka haihu, ya kasa iya
wannan tunanin, daya fara Sai kawai komai ya
tsaya masa, Sai ya fara dariya, yana zubar da
hawaye, yana jin ya za’a yi ma hakan ta
kasance, sai yana kallon abin a matsayin abin
da bazai taba yiwuba ba, wannan dalilin yasa ya
kasa samun hankalin sa.!
Hannatu ce ta karbi diyar Hajiya Kubra bayan
komi ya lafa tacigaba da rikon ta, tayi bakin
cikin mutuwar mahaifiyarta, dukda cewa ta tsani
halayyar ta Amma tana kaunar uwarta, duk
lokacin da ta kalli Jinjirar wacece aka saka ma
suna Zainab Sai taji tausayin ta, idan ta girma
ya zata rayu? Ya zataji idan taji cewa dan
uwanta shine ubanta, kakarta itace uwarta.?
Ta kalli yaron ta, shi kuma yayan uwarsa shine
mahaifinsa.
Tun da ta dawo bata kara son komawa asibiti
ganin yayan ta mijinta ba.
Bayan shekara 6
Jan ne ya warke sumul kamar bashine yayi
hauka ba, sai dai ba gayu ko kalilan tattare
dashi, kana ganin sa kaga ustazu,
Gida ya nufa gun Mamasko ya ci abinci, wani
dan yaro ne da yarinya suka shigo, sun dawo
daga makaranta, suna ta hayaniya,
“Baba kace jainab ta bani book ena”
Janyo hannun su yayi gaba daya ya
rungumesu ya fashe da kuka.
Yau ya zama uban kanwarsa.
Mamasko ce mai bashi hakuri da wa’azi duk
lokacin da abin ya motsa masa, Sabida har yau
idan yace dai tuna abinda ya wuce to Sai yayi
haukar nan tashi, saboda kwakwalwarsa bata
daukar wannan tunanin.
Haka rayuwa ta kasance ma wayannan bayin
Allah, cikin bacin rai da nadama,
Sau dubu Jan ya kalli yaran sai ya tuno abinda
ya faru.
Amma ya rungumi kaddara kada ya aikata
abinda mahaifiyarsa ta aikata Allah ya masa
jarabawar da tafi ta farko.
Hannatu ma ta hakura har ta sake aure chan
kano, sai dai har gobe ta rasa walwarta gabaki
daya.
*ALHAMDULILLAH WANNAN SHINE KARSHAN
WANNAN GAJEREN LITTAFI NA RUGUNTSUMI!!
*
A madadin Fiddausi Sodangi dani Hauwa M.
Jabo muke muku fatan alkhairi.
All yasa mu amfana da darussan dake ciki, nasu
hali irin Na Hajiya Kubra Allah yasa su gyara.
Muna godiya da masoyan wannan littafin Allah
ya saka da alkhairi ya bar zumunci sai mun
hadu wani karon.
Gaisuwa ga member NAGARTA WRITER’S
ASSOCIATIONS.
M. Jabo
& Fido sodangi
www.hauwajabo.tk
www.fiddausisodangi.wordpress.com
By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
07039625239