Hausa Novels

MU GANI A ƘASa Hot Love Page 1-6

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

Related Articles

©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

Page 1-2

Godiya ga Allah (S A T) da ya sake bani dama da iko da sake zaman rubuta muku wannan labarin, dubun tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzonmu Annabi Muhammad (S A W). Da fatan zaku bini sannu a hankali domin jin inda wannan karon labarina ya nufa.

Haƙƙin mallaka na Ummu Affan ne, ban yadda a juya mini labari ta ko wacce siga ba, ko ɗaurawa a wata kafa ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne. Sannan ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi domin kowa ba idan yazo daidai da rayuwarki/ka a rashi ne.

Ɗungurungun littafin nan sadaukarwa ne ga Auntyna Ƴar’uwata Ta gaban goshina ta ƙasan zuciyata MARYAM MODIBBO wato ADDA Maman Hamdana da Hamd. Ke ɗin ta daban ce Zinariya kike a zuciyar Abbansu Humaid.🙈💃😍

Masu san na musu talla a pages na littafina zasu iya magana cikin farashi me sauƙi mai tallah shi ke da riba.

Bismillahir rahmanir rahim.

ABUJA NIGERIA

Sanyayyiyar iskar damina ce ke kaɗawa a daidai lokacin, gari ya yi luf da ni’ima ya yin da sararin samaniya ya yi fayau dashi gwanin burgewa da ban sha’awa. Tuƙi yake cike da ƙwarewa yana sharara gudu saman lafiyayyar kwaltar da ke birnin tarayya Abuja. Yayi tafiya me nisa kafin ya iso babbar unguwar tasu ta Asokoro. Wani katafaren gate ya dosa inda ya buga hurn, da sauri Maigadi yazo tare da wangale mishi ƙaton gate ɗin ya kutsa hancin motar shi ciki. Sannu da zuwa Officer ke masa hannun shi kawai ya iya ɗaga mishi. A cikin babban harabar gidan ne ya samu guri ya yi parking, kusan minti biyu kafin ya iya zuro ƙafarshi daga motar, ƙafar tashi mai sanye da ƙayatattun baƙaƙen takalmi sau ciki ce ya zuro a hankali kamar mai tsoran fitowa. A hankali kuma sassan jikin ya fito da shi, “Ma sha Allah” Ƙyaƙƙyawa ne ajin farko. A hankali yake tafiya kamar mai tsoran takawa hannun shi ɗauke da ƙatuwar wayar shi yana duba saƙon da yaji shugowar sa tun yana tuƙi. Dan tsaki yaja ganin mai saƙon kafin ya zura wayar cikin aljihu ya doshi hanyar da zata sada shi da parlourn gidan. Da gudu ta taso tare da nufarshi da niyyar faɗawa jikin shi “Oyoyo Yaya Aliyu!” Ta furta da tsantsar farin ciki. Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, chak ta tsaya jiki a matuƙar sanyaye. Ƙarasawa Yayi gaban Amminsa dake tsaye tana kallon abin da ke faruwa. Zaunawa yayi saman Cushin yana me duban Ammin tashi. “Barka da hutawa Ammi!” Ya furta cikin sanyi bazaka taɓa cewa shine yayi maganar ba, sakamakon laɓɓansa ne kawai suka motsa idan ma ba kusa dashi kake ba, ba lallai ne kaji me ya furta ba. Wani kallo ta ma shi ba tare da ta amsa ba, ta mayar da kallonta ga yarinyar da ya nunawa ko in kula wacce ke tsaye kamar gunki har zuwa lokacin. “Sareenah tsayuwar ta isa haka, ko baki gaji da kallon nashi ba ne?” Cike da kunya tayi wani far! Sai ta juyo a sanyaye tare da zama gefen shi. “Abuturrab har yanzu halinka na nan ko? Ko ka mance wacece Sareenah a gareka ne?” Wuci ya fesar me zafi kafin ya ce”Ammi yunwa nake ji” Ya faɗa da nufin ɓangarar da wancen zan cen. Kallonsa take ko ƙittawa babu, wani murmushi ta saki wanda ita ce kawai tasan ma anarsa kafin ta kalli Sareenah “Ki kai mishi abinci part ɗin shi” “No Ammi!” Ya furta kamar zai yi kuka. “Ki kawo mishi anan” Girgiza kai yake amma ya kasa cewa komi sakamakon kallon da Ammi tayi mishi. Tashi tayi a gurin yabi bayanta da kallo har ta ƙarashe hawa saman benen, sanyayyar ajiyar zuciya ya saki ƙirjin shi na wani irin bugu. Bai san time ya ɗan ja yana gurin zaune ba sai da Sareenah ta ƙara so tare da ajiye tray ɗin dake hannunta. “Yaya Aliyu ga abincin!” Ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefensa. Da sauri ya miƙe yana jifanta da wani mugun kallo, ƙala bai iya ce mata ba ya miƙe tare da nufar ƙofar parlour. “Abincin fa? Ko na biyoka da shi part ɗinka?” Ta jero mishi tambayoyin a lokaci guda, juyowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata. Yana fita kai tsaye part ɗin sa ya dosa, komi fes-fes kamar yadda ya zata. Kai tsaye bedroom ya wuce yana zuwa komi na jikinsa ya cire tare da faɗawa toilet, wanka ya yi ya ɗauro alwala sannan ya fito ɗaure da towul ɗaya a hannunsa yana goge sumar kan shi. Mirror ya nufa inda ya shafa maya-mayansa tare da feshe jikinsa da turaren sa mai daɗin ƙamshi, Ƙananun kaya ya saka dogon wando tare da riga t-shirt sai ya ɗora wata me kauri ta sanyi me haɗe da hula, sakamakon yanayin garin na sanyi. Ya so ya huta amma kiran sallar ta Azahar da ake ƙwala kira a masallacin ƙofar gidansu ne ya sashi nufar hanyar fita daga badroom ɗin. Yana fita kai tsaye masallaci ya nufa.
Sareenah bayan fitarsa da gudu ta hau sama bedroom ɗin Ammi, tana shiga ta sami Ammin na waya da gudu ta ƙarasa tare da faɗawa jikinta ta saki wani kuka. Ba shiri Ammi tayi sallama da wacce suke wayar tare da sanar da ita anjima zata kirata. “Sareenah lafiya kuwa?” Ammi ta tambayeta bayan ta ajiye wayarta saman ƙaramar durowar dake kusa da ita. Cikin kuka wanda zallarsa shagwaɓa ne da sangarta ta ce “Ammi Yaya Aliyu ne! Mene ne na masa ya tsane ni haka?” Da sauri Ammi ta katseta ta hanyar ɗaura ɗanuatsanta saman laɓɓan Sareenah “Kar in kuma ji” Ammi ta faɗa tare da kawar da ɗan yatsanta kafin tacigaba da cewa”Shi har ya isa? Bai kai matsayin tsanarki ba Sareenah kicigaba da shige masa kamar yadda na nuna miki a juri zuwa rafi dai, nasan dole wata rana tulu zai fashe.”
“Har zuwa yaushe ne tulun zai fashe Ammi? Kin san dai yarda Yaya Aliyu ke zuciyata!” “Ke dai Sareenah albasa ba ta yi halin ruwa ba, da tayi tabbas ba za ta yi yaji ba tun da har na ce miki haka to ki ɗauka mana, kin san bana san ɓacin ranki” Ammi ta faɗa tana sharewa Sareenah hawayen dake zuba a fuskarta. Numfashi ta sauke tare da lafewa jikin Ammin tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, sannan tasan wacece Ammi bata faɗin ƙarya sai abin da ke ƙasan zuciyarta.
Fitowarsa daga masallaci ba ɓata lokaci ya ɗauke key ɗin motarsa, cikin tafiyarsa ta alfarma ya doshi harabar gidan, tun daga nesa ya dannawa motar key ta buɗe yana zuwa ya faɗa ciki tare da kunnawa. A ɗari ya fita gate ɗin gidan daman tuni Maigadi ya buɗe masa tun lokacin da yaga ya doshi motar. Wani gidan abinci ya nufa na manya sai wanda ya amsa sunansa ke cin abinci a gurin. “Barka da zuwa ƴallaɓai” Wata murya siririya ce tayi maganar. Bai ɗago kan shi ba, tun bayan zamansa saman kujerar haka jin maganarta bai sa shi jin zai ɗago ba, duk kuwa da jin bugun zuciyarsa da ya tsananta. “Me kake buƙata?” Maganar ɗazu ta ƙara ratsa masarrafar sautin sa, bai ce ko ci kanki ba wata farar talarda ya ga an ajiye mishi, sai lokacin ya kai idanuwansa kan takardar, abinci ne da nasha da dangin na ƙwalama kala-kala rubuce a jikin takardar. Pen ya ciro gaban rigar shi tare da making abin da ke buƙata tare da ture takardar da baya jin zai iya magana miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi. Ta ɓangarenta kuwa tun bayan parking ɗinsa Madam (Shugabar gurin abincin) Ta ce”Ke Tataah ga kostoma nan jeki gurinsa” Cikin sanyinta ta miƙe tana ta fiya sulow kamar yarda take, daidai zamansa ta ƙarasa tare da tambayarsa abin da yake buƙata. Jin shuru ta ɗago idanuwanta ta dubesa, gabanta taji ya bada dammm! Haka ta daure ta kuma tambayarsa cikin sanyi amma bai bata amsa ba sai ta saka mishi takardar tana mai jin haushi a zuciyarta sakamakon ko in kula da ya nuna mata. Ganin abin da yayi a ranta ta ce”Uhmm! Masu abu da abin su, tabbas a rashin kira karen bebe ya ɓata” Tana duba irin wannan izza da girman kai na wannan mutumin. Lokacin da Madam ta ce taje tsoro ne ya fara ɗarsar mata sakamakon yadda ƙadangarun bariki ke kai mata haushi a gurin, tana tsananin tsoron zuwa tambayar abin da masu sayen abinki ke buƙata saboda wasunsu maganar banza suke mata, a kallon farko ta ɗauka shima hakanne musamman da ta ganshi matashi sai ta fuskanci maganar nan ta kowa da halinsa amma wannan kuma girman kai ke damunsa, da wannan tunanin ta ɗauki takardar tare da nufar gurin Madam ta miƙa mata. Komi da ya buƙata aka haɗa masa tare da ba Tataah ta kai mishi, tsaye tayi a gurin tana kallon yarda yake danna wayarsa bai damu da kallon kowa dake gurin ba. Jin tsayuwar mutum kuma ba a ce komi ba ya sashi ɗagowa a hankali, idanuwansu ne suka gauraya da na juna, sauran kaɗan tiren hannun Tataah ya sun ɓule saboda tsorata da tayi da yarda da tsinci gabanta na dukan tara-tara. Da sauri ya saka hannun ya amshi Tray yana jan dogon tsaki duk da shima yaji shock a haɗa idanuwansu amma ba zaka taɓa gane hakan ba. Wani banzan kallo ya aika mata da faɗin “Noneses baki da hankali ne zaki ɓata ni?” Da sauri ta juya tare da barin gurin. Duk bayan saƙon ɗaya sai yaja tsaki jin zuciyarsa ya yi sam babu daɗi, yunwar da yake ji ne yasa shi buɗe abincin ya fara ci, amma da ya tuno fuskarta sai yaja tsaki da haka ya cika cikinsa, Drink ya ɗauka yana sha a hankali yana amsa wayar da ake ta kiransa tun ɗazu. “Aliyu ka shugo ne?” Abin da aka faɗa daga can ɓangaren kenan, sai da ya kurɓi lemunsa ya haɗiye sannan ya furta “I akwai wani abu ne?” “Ɗan renin wayau, mu muna nan muna jiranka kana shanya mu!” Robar lemun ya ajiye tare da cewa “Faruuk bacci zanyi” Ƙit! Ya katse kiran daidai miƙewarsa. Gurin biyan kuɗi ya dosa tare da barin gurin cikin sauri.
Tataah dake leƙensa ganin yarda motarsa ta fita harabar gurin a sittin ta sauke numfashi nan take kuma idanuwanta suka kawo ruwa, kawar da abin da yazo mata tayi tare da dosar gurin zamanta. Ba ita ta bar gurin ba sai gabda magrib lokacin da ma’aikatan dare suka iso, gurin Madam taje inda ta bata sallamarta na ranar. Ƙarasawa tayi gurin kayanta tare da ɗaukar babban hijabinta da ke gurin wanda ya tsufa sosai, sakawa tayi ta ɗauki ƙaramar jakarta tare da kularta. Madam ta kai mawa ta zuba mata abincinta na rana da na dare wanda take basu, to ita bataci sai zata tafi take amsa. Kai tsaye bakin babban titin ta nufa domin samun Kekenapep da zai mayar da ita gida, ta tare kusan napep uku amma rashin daidaitawa yasa suke wucewa domin a kullum nera ɗari biyu ta ware domin zuwanta gurin a ɗari ta koma ɗari, idan bata samu wanda zai kaita a hakan ba to tana haƙura har ta samu. Tana tsaye gurin rungume da kularta da jakarta, yadda garin ya kaɗa hadari ne ya bata tsoro duk ta cure guri guda, tsoranta ɗaya karta ƙara hamsim ya zama ɗari da hamsim taci bugu gurin Gwoggonta domin duk wanda ta tsayar haka yake ce mata. Shada tayi akan ta sayar ta hau tasan dai bugu kam sai ta shashi haka ta fara ƙoƙarin tsayarwa amma duk wanda ta tsayar basu tsayawa sakamakon hadarin da ya ƙara turniƙe garin na Abuja har yayyafi aka fara, duk ta tsure sai kama hijabinta take daidai tsayuwar wata ƙatuwar mota. “Yan mata ina zaki?” Mai motar ya tambaya bayan yayi parking ya buɗe gilas ɗin gaban motar. Gabanta ne ya buga amma bata da zaɓi dole a wannan lokacin tana amsa mishi saboda tana buƙatar temakon nasa tabbas. Cikin rawar murya da sanyi ta ce”Maitama zani” “Hanyar za mubi zo mu rage miki hanya” Ma tuƙin motar ya faɗa domin sai yanzu na lura ashe su biyu ne cikin motar, matasa ne da baza su wuce 32 ba, ba yadda ta iya dan har ruwa ya fara sakkowa, ganin ya buɗe mata back sit da sauri ta shiga tare da furta “Na gode” Tun da suka hau titi ba wanda yayi magana har suka isa Maitama sai lokacin Matuƙin motar ya tambayeta inda zai ajiyeta domin an tsuge da ruwa sosai. Da sauri ta ta ɗago fuskarta domin ta cure guri guda sanyin gari da na Ac dake kunne a motar ya ƙara mata jin sanyi gashi daman basu shiri da sanyi har wata ƴar kyarma take. Kwatanta masa tayi har ƙofar gidan da suke zaune ya kaita. Tana niyyar fita ya ce”Sunana Faruuk ke baki faɗa mini naki sunan ba” Gabanta ya buga sosai “Faruuk!” Ta nanata cikin sanyi ta ce”Na gode sunana Tataah!” Daga haka ta fita da sauri, da gudu ta shiga cikin madaidaicin gidan. Tana motar Faruuk yayi abokinsa dake gefe mai suna Ma’aruf ya ce”Faruuk ka cika kwashe-kwashe daga temako mene ne kuma na faɗa mata sunanka da tambayar nata, bakaji rainin wayaun da ta maka ba wai Tataah wannan suna ne?” Murmushi ne ɗauke fuskar Faruuk ya ce”Tun da kaji ta ce haka to sunan nata kenan, ni fa ban faɗa mata sunana da wata manufa ba, kamar yarda ban tambayi nata da niyyar komi ba” Taɓe baki Ma’aruf yayi tare da lumshe idanuwanshi da haka suka ƙarasa gida.
Tataah tana shiga kai tsaye ɗakin Ummanta ta nufa.
Da sauri ta ƙarasa gabanta ganinta kwance kamar yarda ta barta tun safe, daman tasan hakan zata kasance, kular hannunta ta ajiye tare da cire hijabin dake jikinta, kama mahaifiyar tata tayi tare da saka fillow ta jinginar da ita jikin bango. “Sannu Umma!” Ta furta cikin tsananin jin tausayin mahaifiyar tata, kallonta kawai Ummar ke yi ko ƙittawa babu, tsumma ta ɗauko tare da share mata miyun dake zuba a gefen bakinta sannan ta ɗebo ruwa ta kafa mata kai, sosai Ummar tasha ruwan da alamar ba ƙaramin ƙishi take ji ba ‘Dole taji ƙishi Tataah tun safe fa’ Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita. Bata cika mata ciki da ruwa ba da sauri ta ɗauko abincin da tazo dashi tare da cokali ta fara ba Umman, ta ɗan ci ba laifi sannan ta ƙara mata ruwa tasha, duk bayan minti ɗaya tana jerowa Ummar sannu. Ganin Ummar ta ƙoshi sai lokacin hankalinta ya kwanta ta ci ragowar itan ma tun safe sai yanzu take ci, bayan ta gama sake tattare ƙaramin ɗakin nasu tayi tare da ɗaurawa Umma alwala jin ana kiran sallar Magriba ita ma fita tayi ta ɗauro. Salla ta gabatar ita ma Umma a yadda take zaune take tata a haka. “Tataah! Tataah!! Tataah!!!” Yarda taji muryar mahaifinta na ƙwala mata kira yasa ƴan hancin cikinta murɗawa. Tana ƙoƙarin miƙewa sai gasu sun shugo ɗakin shi da Gwoggonta, jiki na rawa ta duƙa ƙasa “Gwoggo sannu da gida…” Tsawa ta daka mata “Baƙar munafuka algumguma me baƙin hali baƙar fuska! Ashe kin dawo hakima mandiya shine kika barni ina ta jiranki” A sanyaye ta ce”Kiyi Haƙuri lokacin da na shugo ana ruwa ne shiya…” “Dakata mini haka!!” Ta katseta ta hanyar daka mata tsawa. Baba ya ce”Amma me na ce miki akan idan kin dawo gidan nan?” Tuni idanuwanta suka cika da hawaye “Kace na fara zuwa na gaisheta tare da bata duka kuɗin aikin” “To uwar waye ya ce yau ki karya dokar” “Kuyi haƙuri wallahi ruwa akeyi lokacin” “Karya ne ai kafin magariba kike dawowa kuma sai da aka kira sallah aka fara ruwa” Da sauri Baban ya kalli Gwoggo da ba hakan bane amma kallon da ta wurga mishi ne yasa yayi saurin cewa”Haka ne” Jawota Gwoggo tayi tare da fara kilarta tana cewa”Saboda kin raina maganar ubanki danni nafi ƙarfin ki rainani, kin zo gurin nakasasshiyar uwarki da bata da mamora to bani kuɗin da uwarki gantalalliya kawai, a haka zaki ƙare a gantale ke da uwarki!” Jiki na rawa tana kuka ta ta miƙa mata kuɗin duka, Allah yaso ta cire ɗari biyun motar gobe da kuma ɗarin ta ta yau da Allah yasota aka rage mata hanya, dan da tasan tana cirewa bazata bari ba.. Tana amsa ta turata ta faɗi tare da tasa Baba gaba suka bar ɗakin. Tataah ɗagowa tayi tare da sakin ƙara ganin hannunta da ta ɗora a goshi da jini, sake kama goshinta tayi tare da sakin kuka…..

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

©FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

Page 3-4

Motsin da taji Ummanta nayi ne yasa ta saurin juyowa, da sauri ta ƙarasa kusa da ita. Hawayen da taga Umman nayi yasa ta mance da ciwon da ke goshinta, “Umma kuka? Mene ne ya faru? Dan Allah ki dena kuka Ummata!” Ta ƙarashe maganar ita ma tana hawayen tare da sharewa Umman nata hawayen. ‘Ina ma ina iya magana, ina ma komi nawa yana motsi, ina ma ina da lafiyar da zan iya tsayar da zubar hawayenki, Tataah da bakiyi kuka ba har ƙarshen rayuwarki’ Abin da Umma ke faɗa a zuciyarta kenan sai dai kamar yarda ta faɗa tabbas bata da damar hakan a yanzu. Tataah kuwa ganin tana goge mata hawayen amma wasu na zuba sai ita ta dena kukan nata cikin karyewar murya take faɗin “Umma na bari kema ki dena, zubar hawayenki tamkar ana ɗiga mini dalma ne a cikin jikina na bari” Ta faɗa da sakin dariya-dariya wacce take ta zallar yaƙe tana dariya amma hawaye na zuba. Jin ana kiran isha’i gabatarwa sukayi sannan Tataah ta jawo wani yaƙunannan zani ta shimfiɗa a inda zata kwanta ta gyarawa Umma kwanciyarta a saman tabarmar da ta gama fita hayyacinta sai zanin da ta shimfiɗa mata, wani tsohon bargo ta ɗauko ta lilliɓe Umman sakamakon ruwan saman da akayi ya sakar da sanyi me shiga jiki ita kuma ta rufe da hijabinta, haka bacci ya kwashe su daman suna sallahr isha’i take bacci saboda asubar fari take tashi. Ilai kuwa tun huɗu na asuba ta tashi alwala ta farayi tazo ta gabatar da nafila da yiwa Ummanta addu’ar samun lafiya kullum sai tayi wannan sallah dan roƙawa Ummanta samun sauƙi gurin sarki Allah. Bayan idarwarta fita tayi ta fara share tsakar gidan wanda hasken sola ya mamaye ta ɗayan gidan dake jikin nasu ne, mai gidan ya basu wannan ƙaramin suke zaune to har solar dake gidansa ya jona musu. Bayan kammalawarta ne ta shiga kitchen wanke-wanke tayi tare da gyara kitchen ɗin dake kaca-kaca kuma kullum sai ta gyara amma haka zata dawo ta iske shi kamar anyi yaƙi da kaya a cikin shi, fitowa tayi daidai kiran sallar asubahi wanka tayi da ruwan sanyi sai kyarma take saboda sanyin da ake sannan ta ɗaura alwala ta shiga da ruwa tayiwa Umma wacce ta iske ta tashi alamar gaisheta tayi sannan ta jinginar da ita domin tayi sallah. Ita ma ta gabatar da tata, ko man shafawa bata da zarrar shafa shi domin basu dashi, ta daɗe zaune tana lazumi ƙarfe shidda nayi ta miƙe ruwa ta bawa Umma tasha sannan ta gyara mata kwanciya tare da tofa mata addu’o’i cikin sanyinta ta ce”Kiyi haƙuri Umma yau ma haka zan fita ba tare da kinci komi ba, anan babu shago balle na sayo miki ko wani abu ne da nera ɗarin jiya, amma kiyi haƙuri har na dawo” Ɗan lumshe idanuwanta tayi wanda shine kawai ke aiki a jikinta alama ce ta mata da ba komi, jiki a matukar sanyaye ta fita tare da ja mata ƙofa. Kamar yadda Babanta ya sanar da ita ƙa’ida ne taje gaida Gwoggo kafin ta wuce haka ta shiga amma sai ta iske tana barci kamar kullum Baba ne zaune bakin ƙofa yana wankin Gwoggo da yaranta biyu mace da namiji ƙanne a gurin Tataah. Sudees da Tataah ta girma da shekaru biyu sai Ruhaima wacce ta girmi Tataah da shekara ɗaya amma sune BAba ke yiwa wanki, har ƙasa ta duƙa. “Baba ina kwana” Da sauri ya ɗago dan sam bai lura da zuwanta ba sai maganarta yaji, duba gefe da gefensa yayi dan ko gaisuwarta Gwoggo ta hana ya amsa a hankali ya ce”Lafiya ƙalau Tataah zaki wuce gurin aikin ne?” Gyaɗa kai tayi alamar “I” Ba tare da ta ce komi ba, shuru ya biyo baya na ɗan wani lokaci a hankali ya ce”Ki tashi kije kawai basu tashi bacci ba” Miƙewa tayi tana tafiya a hankali ba tare da ta ce ƙala ba, yabi bayanta da kallo yana girgiza kansa. Tayi tafiya mai nisa kafin ta iso bakin titi sannan ta daɗe tsaye kafin ta samu abin hawa, lokacin da ta isa gidan abincin bakwai saura minti goma, hamdala tayi domin ƙa’idar shiga gurin bakwai ne bata san latti kamar yadda aka gargaɗe su da hakan shiyasa take fitowa da wuri. “Baki latti har kin iso?” Ɗan murmushi tayi bata ce mishi komi ba, ciwon da ya gani a goshinta ne yasa shi salati tare da faɗin “Ciwo kikaji?” Sai lokacin ta tuna da ciwon ta ce”Faɗuwa nayi!’ Tare da wucewa dan bata san wata magana kuma akan ciwon. Lawan abokin aikinta ne a gurin suna ɗan gaisawa da shi amma ita ba da kowa take magana ba saboda kamun kai da gudun shiga abin da bai dameta ba. Gurin masu girki ta ƙarasa tana temaka musu duk da ba aikinta bane amma tana sa hannu don sam bata da ƙiwwar aiki, suma duk suka tambayeta ciwon abin da ta cewa Lawan shi ta maimaita musu, wajen takwas duk an gama wasu yayin da kuma wasu aka barsu a wuta saboda karsu huce. Mutane ma banbanta ne ke ta shugowa gurin abincin saboda sunan da gurin ya yi ana son abincin gurin sosai ko ba komi akwai tsafta ga daɗin abinci.
Tun bayan barin shi gurin abincin yake yawan tuno fuskar yarinyar, yaja tsaki yafi cikon masaki, kai tsaye gida ya wuce daret part ɗinsa ya shiga saman bed ya faɗa nan take kuwa barci me nauyi ya ɗauke shi. Ya daɗe yana barcin har zuwa lokacin da aka fara ruwan sama, sanyayyen sanyin da ake ne ya ƙarawa barcin nashi armashi ya shige cikin bargo ya naɗe yana kwasar baccinsa. Yaye bargon da akayi ne yasa shi buɗe idanuwa a hankali, idanuwansa suka sauka akan Faruuk dake riƙe da bargon, guntun tsaki yaja tare da gyara kwanciyarsa ba tare da yayi magana ba. “Aliyu magana fa nake” Ma’aruf da ya ƙarasa shugowa ne ya ce”Kai sai kace baka san wane ne Aliyu ba, ka barshi fa idan ba haushi ne kake so ya kar ka ba” Zaunawa Faruuk ya yi bakin bed ɗin yana faɗin “Tun jiya da yake ƙasar jajayen can nake kiransa yana wulakantani amma ba komi na shi auren zai zo ne?” Jin abin da Faruuk ya faɗa ne yasa shi tashi yana ɓata fuska “Auren wa?” Ya tambaya so silent, Ma’aruf ya ce “Aurenka! Ko bazakayi ba ne?” Ɗan smile ya saki na gefen baki kafin ya ce”Ku dai fitinannu Allah ya baku sa’a, ku dena lissafi da ni” Dariya suka saka su biyun har da tafawa “Ana maganar fitina har kai kayi magana Aliyu, wannan baccin ma da kake daga gani na wahala ne” Cewar Faruuk. Tsaki Abuturrab yaja tare da miƙewa ya nufi bathroom ba tare da ya ce musu komi ba, su kuwa dariyar shaƙiyanci sukaci gaba da yi mishi. Bayan ya fito dukansu sukayi alwala sannan suka wuce masallaci jin ana tada salla. Ko da suka dawo cikin gidan suka nufa Ammi tasa house girl ɗinta ta shirya musu komi. Aliyu ko kallon abincin bai yi ba, Faruuk daman yasan baci zai yi ba hakan yasa duka suka tashi kai tsaye motar Faruuk suka hau duka suka nufi Husse two gidansu Faruuk. Ammi da ta fito bin gurin tayi da kallo sosai ranta ya ɓaci da ganin abin da sukayi “Abuturrab!” Ta furta da huci kafin ta tuno Faruuk “Shege yaro da maƙar fuskarsa irin ta uwarsa wallahi duka sai nayi maganinku mtsuuuw!” Ta ƙarashe maganarta da jan tsaki. Sareenah wacce ta fito yanzu ita ma bin gurin tayi da kallo kafin ta ce”Ammi ina su Yaya Aliyun?” “Yadda kika ga gurin wayam haka nima na fito na gani, ai kin san wannan Faruuk ɗin idan har suna tare komi yayi shi Abuturrab ke yi” Sareenah da idanuwanta yayi ja saboda ɓacin rai ta ce”Wallahi ba tun yau ba na tsani Faruuk kina ganin ko gani na yayi sai ya dinga mini wani kallo a raine” “Barni da shi daga shi har uwarsa na tsane su kuma nice maganinsu, kwanaki akan uwar Faruuk sai da mukayi faɗa da Alhaji kin san ƙanwarsa ce kuma su biyu uwarsu ta haifa sonta yake kamar me, ni kuma bazan iya jura ba” Sareenah kasa cewa komi tayi sai numfashi da take saki cike da jin tsanar Faruuk a ranta.
Sosai Mami ta cikawa su Abuturrab gaba da abinci, cikin farin ciki suka fara cin daddaɗan abinci Mami da ta kasance gwana gurin iya tsara girki. Faruuk ya kai lomar jellop rice bakin shi da taji haɗi na musamman ya ce”Mami gaskiya ko dai anan gidan zamu zauba da Rahina domin ta iya girki kamar naki?” Abuturrab ya ɓata rai kafin ya ce”Sai ana maganar mutane kana sako wannan ƙwailar yarinyar dan Allah ka din ga magana irin ta mutane” A yadda yayi maganar sai ka rantse da Allah ba shine ya yi ta ba domin laɓɓan sa ne kawai ke motsawa Faruuk ne kawai yaji mai ya ce yadda kuma ya mayar da hankalinsa wajen cin abincinsa sai ka rantse da Allah ba shine yayi maganar ba. Mami kam murmushi take ta ce”Wallahi ba dani ba wai gaɗa a hurumi, me zai jani zama da ku a gidan nan? To sai dai idan wata laluurar amma kaje da matarka can da rawar kanka” Tana faɗa ta miƙe ta basu guri, dan tasan halin Faruuk da shegen rawar kai yanzu sai ya ce zaiyi wata maganar. Faruuk ya mai da hankalinsa gurin Abuturrab bayan wucewar Mami “Limamin bayan fage me kake cewa ɗazun?” Banza Aliyu yayi masa yana ci gaba da cin abincin. “Da a maimaita mana da anji zazzafar amsa” “Mtsuw!” Abuturrab yaja tsaki ba tare da ya kuma cewa komi ba har suka ida. Ganin lokaci yaja ya ce”Malam zo ka mayar dani gida dare nayi” “Gida kuma? Wallahi baka isa ba zance zaku raka ni gurin Rahina” Ɗan zaro ido Abuturrab yayi alamar tsoro kafin ya ce”Zance? Mene ne hakan!” “Oho dai idan mun je ka san ko mene ne” Taɓe baki yayi tare da ɗaga kafaɗa cikin cool voice ɗin sa ya ce”Allah ya raka taki gona ba da Aliyu za a ganin shirme ba” Wata muguwar dariya Faruuk ya saki Ma’aruf ya ce”Ina rabaka da kiwo kana ƙyalla ta mutu Aliyu, kar nan gaba kaɗan ka afka ƙaton tafkin so kafi mu zaƙewa” “Allah sitiri buƙwi ba da ni ba” “Wai nikam ina kaji hausa ne?” Ɗan murmushi ya yi tunowa da wani abu kafin ya basar bai ce komi ba. Faruuk shi ya maida Aliyu gida kafin ya sauke Ma’aruf a nasu gidan sannan ya wuce gida dan sanyin da ruwan saman da akayi ya sakar yasa shi jin bazai iya zuwa gurin Rahina a yau ba.
Ammi da ta kasa ta tsare tana jiran dawowar Abuturrab anan bacci ya yi gaba da ita, duk a tunaninta da mota ya fita idan ya dawo dole zataji ƙarar motarsa, shi kuwa a bakin gate yasa Faruuk ya ajiye shi sannan ya shugo ta ƙaramar ƙofa, daret part ɗin sa ya nufa bai ma yi tunanin shiga part ɗin Ammin ba. Coppe ya haɗa yana sha a hankali daidai ringing ɗin wayarsa, jawo wayar yayi ganin mai kiran yaja tsaki kafin ya ɗauka. “Lafiya cikin tsohon daren nan?” Sanyayyar ajiyar zuciya ta saki wanda shi kansa da yaji ta, cikin kwantar da murya ta ce”Tun ɗazu nake turo maka saƙo ba amsa, daman so nake naji ko ka sauka lafiya?” Huci ya fesar me zafi kafin ya ce”Baheerah please ki bar ni, wai ana so dole ne?” Tun kan ya sauke numfashi ya fara jin ƙarar kukanta Ƙit! ya yanke kiran cike da fusatuwa ji yayi coppe ɗin ma ya fita ranshi kitchen ya mayar tare da shigewa bedroom sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kunna na’ura me ɗumama ɗaki. Sareenah ce ta fito cikin sanɗa ta niyyarta na barin gidan domin saurayinta ya kirata yana wuce zasu wuce club, ganin Ammi a parlour taji ranta ya ɓaci, gurinta ta ƙarasa sai ta tarad da bacci take mai nauyi ajiyar zuciya ta saki tare da ficewa daga parlourn cikin sauri. Officer na ganinta ya sara mata “Ranki ya daɗe barka da fitowa” Murmushi ta saki tare da zage zagarta ta ciro dubu biyar ta bashi. Godiya ya fara mata da wasata ta ce”Kamar kullum kar wanda yasan da fitar nan, har Ammi” “An gama ranki ya daɗe” Har takai gate kuma ta juyo “Officer Yaya Aliyu ya dawo kuwa?” “I Ya shugo tun ɗazu kuwa” Gyaɗa kai tayi tare da fita daga gidan, nesa kaɗan da gidan ta hango shi cikin baƙar motarsa da sauri ta ƙarasa, tun kafin ta iso ya buɗe mata gaban motar, murmushi suka sakarwa juna “Ma’aruf!!!” Ta ambaci sunansa cike da ƙwarewa. Tada motar yayi sai da ya hau titi ya ce”Sareenah ta Aliyu” Gabaɗaya suka saka dariya ta ce”Har kasa naji wani sanyi, amma nazu raina ya ɓaci da Faruuk ya jaku wallahi ban taɓa tsanar wani irin Faruuk ba” Numfashi ya fesar da cewa”Faruuk bai da matsala jininku ne kawai bai zo daidai ba, shi ya mayar dani gida yana wucewa kuma na samɓo nan” Dariya tayi ta ce”Shi ya sa fa nake ƙaunarka kai ma kasan kan bariki” Ya ce”Hahahaha Sareenah kenan” Da wannan hirar suka ƙarasa shahararren gidan rawar dake garin na Abuja. Guri suka samu sukayi ciye-ciyensu da shaye-shayensu abin da Aliyu ko Faruuk basu san Ma’aruf nayi ba kenan. Daga ƙarshe ma ɗaki suka kama suka gama sheɗancinsu. Sareenah bata dawo gidan ba sai wajen biyar na asubahi, har lokacin Ammi na gurin tana sharara bacci, kasancewar Sareenah ba cikin hayyacinta ta ke ba yasa bata lura da ita ba bedroom ɗinta ta wuce tana zuwa ta faɗa saman bed wani fitinannan bacci ya yi awon gaba da ita….

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

MU GANI A ƘASA…
Hot Love

© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN

GAWURTATTU BIYAR.🔥

https://hausaarewa.com/u/ummuaffan Kubi link ɗin nan domin yin following ɗina arewabooks please. Sannan acan nake fara posting kafin nan.👎

Page 5-6

Tataah Pov.
“Tataah lafiyarki kuwa?” Da sauri ta juyo don har yaso ya tsorata ta. Numfashi ta sauke tare da sakin murmushin yaƙe. Farhan ne ɗa a gurin Madam ɗin su saurayi ne sosai bai daɗe da dawowa karatunsa ba a ƙasar waje. “Babu komi Yaya Farhan!” Girgiza kai yayi tare da zama gefenta “Ban yadda ba, ko dai kina jin yunwa ne?” Tayi mamakin tambayar da ya mata, tabbas yunwa take ji amma bazata iya cin komi ba saboda tunanin halin da ta baro Ummanta, ganin tayi ƙasa da kai tashi ya yi sai gashi da abinci ya miƙa mata, da sauri ta girgiza kai alamar a’a. Zaunawa yayi yana dubanta sosai “Tataah baki yadda da ni bane” Sadda kai ƙasa tayi cikin sanyinta ta ce”Ba haka bane” “To mene ne?” Kasa cewa komi tayi ta amshi abincin dan bata san tana cika gaddama da mutum, cokali ɗaya taci ta tino da Umma ‘Yanzu a wanne hali take? Ita taci abincin ma kuwa? A’a ita ce amsar dan tasan idan suman mutuwa take Gwoggonta ba zata bata abinci ba. Hawaye ne suka gangaro idanuwanta da sauri ta goge dan bata san Farhan ya gane amma ta makaro “Tataah zan so naji tarihinki, ina jin tausayinki sosai a zuciyata” Kauda kai tayi ba tare da ta ce komi ba. “Dan Allah ki sanar da ni” “Jin sa bashi da wani amfani a tare da kai balle ni da na bayar” Zaiyi magana yaji Madam na kiransa. Ganin ya tashi da sauri ta sami leda ta juyo abincin taje cikin jakarta ta tura domin bata san ci ba tare da Ummanta ba balle har da nama yanka biyu ina zata iya ci ta bar Umma. Farhan ta hanga yana ɗaga mata hannu da alama tafiya zaiyi, gurin wanke-wanke ta ƙarasa ta wanke plate ɗin taje ta ajiye, wasu suka zo sayen abinci taje tambayarsu abin da za a kawo musu, ɗaya cikinsu ya dinga kallonta yana lasar baki, sam bata lura dashi ba sai da ta kai abincin sai ji tayi mutum ya riƙe mata hannu, da sauri ta fincike jikinta na rawa sosai. Ya ce”Dalla can na gani na yaba da yarintarki dare ɗaya zaki bani biya na musamman” Zaro ido tayi tsoro mai tsanani ya shigeta baya ta fara tana girgiza kanta ganin haka ya taso tare da riƙeta, nan fa suka fara kokawa ga mutane a gurin amma kowa harkar gabansa yake ba wanda ya damu dasu (Matsalar bariki kenan) girgiza kai take hawaye masu zafi suna zuba a idanuwanta gashi ta kasa magana, janta yake tare da nufar gurin motarshi da ita “Madamm!!!” Ta kira sunan da karfi, da sauri ta fito jin muryar Tataah. Ƙarasawa tayi gurin da sauri tana cewa”Alhaji dan Allah kayi haƙuri wannan ba irin waɗanda kake tunani ba ce, dan Allah ka rabu da ita!” Wani banzan kallo ya mata ya ce”Bana haƙuri da duk abin da naji ya mini” Girgiza kai Madam keyi cike da jin tausayin Tataah dan har cikin zuciyarta yarinyar ke bata tausayi. Tataah ganin ba wanda zai ceceta kuma wannan mugun da yayi jika da ita ba imani a kamanninsa yasa ta saka haƙoranta tare da gantsara mashi wani mugun cizo. Ai kuwa ba shiri ya saki hannun tare da riƙe hannun nasa, ita kuwa tuni ta arta a saba’in tana ihuw da kuka. Gudu take saman babban titin sam ta fita a hayyacinta, gani take kamar yana bin ta saboda tsoratar da tayi, ƙarar motar da taji bai sata tsayawa ba ta ci gaba da gudu. Ai batayi aune ba taga mota a gabanta ƙara ta saki tare da ɗaura hannu aka ta zube a gurin… Aliyu pov.
Asubar fari ya tashi tare da shiga bathroom ya ɗauro alwala ya nufi masallaci, ko da aka idar da sallah bai shugo gida ba sai wajen shidda na safe, yasan Ammi bata tashi ba dan idan tayi salah tana komawa baccin safe hakanne yasa ya koma part ɗinsa, niyyar kwanciya yake yaji ƙarar wayarsa, ɗan tsaki yaja tare da kai idanuwansa saman wayar. ‘My Dad’ abin da ya gani saman screen ɗin wayar da sauri ya ɗauka dan yayi tunanin Baheerah ce. “Assalamu alaikum” Yayi masa sallama, amsawa yayi Aliyu ya gaishesa ya ce”Daddy da safe haka, Allah yasa lafiya?” Murmushi Daddy ya yi mai sauti har Aliyu yana ji kafin ya ce”Abuturrab ya ka dawo gida?” “AlhamduLillah Daddy!” “Ka koma aikin ne” Tura baki ya yi kamar Daddyn na gabansa ya ce”No Dad ai na ɗauki hutu, sai nan da sati ɗaya” “Ok yayi Alhaji Tasiu ke sanar da ni an kwantar da Baheerah asibiti kaji kuwa” Dam gabansa ya buga amma ba yadda za ayi ka fahimci hakan ya ce”Ban ji ba zan kirata in sha Allahu” “Ya kamata kam, nima cikin satin nan zan dawo” “Tom Dad Allah ya dawo da kai lafiya” Da “Amin” Ya amsa tare da katse kiran. Bin wayar yayi da kallo yana tunanin me zai sa Daddy sanar da shi ciwon Baheerah? Tabbas ɗiyar amininsa ce amma bai taɓa kawo hakan a zuciyarsa ba ‘Allah yasa ba sanar da su tayi abin da ta sanar masa ba” Mtsuww! Yaja tsaki idan ma sanar dasu tayi can dasu gada shi ba ruwan shi. Gado ya faɗa domin yana san ya more hutunsa na satin da ya ɗauka kafin a koma fagen daga, kusan sha ɗaya ya farko wanka yayi tare da brush ya nufi part ɗin Ammi dan ya gaisheta. Ba kowa parlour yasan da wuya ma idan ta tashi fita yayi tare da wucewa gidansu Faruuk can ya karya Mami ta ce”Wallahi gara kuyi-kuyi aure ko ma huta da ciyar daku” Ƙasa yayi da kai bai ce komi ba daman tasan da wuya ta tanka miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi, bayan ya gama office ɗin Faruuk ya wuce can ya kusan awa uku sallar Azhar ta fito dasu bayan su idar yayi mishi sallama ya nufi hanyar gidan saboda miscalls ɗin Ammi da ya gani kusan biyar lokacin suna sallah ta kira shi. Yana hanya tun daga nesa ya hango kamar mutum na gudu a titi haka dai yaci gaba da rahowa hr zuwa lokacin da ya ƙaraso gab da ita a tunaninsa mahaukaciyace saboda yadda take gudu tana waugen bayanta, duk ƙoƙarin kauce mata da yake amma haka ta tunkarosa wani wawan burgi yaja daidai ƙafafuwanta ganin yadda ta zube masa a gaban mota ne yasa shi fitowa da sauri.
Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komi ba kusan na minti biyu, kafin ya koma motarsa baya yaja ya kauce mata tare da fusgar motar a sittin. Nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da bin bayan motar shi da kallo, ta daɗe a gurin kafin ta tashi jiki a sanyaye ta fara tafiya a hankali domin ƙafafuwanta ba kaɗan suke mata zafi ba, tunani ta fara ta nufi guda ko ta koma gurin Madam? Tasan muddin ta koma gida Gwoggo sai ta kusan kasheta da bugu, gurin Madam kuma tana tsoro karta koma Alhajin nan ya kuma kamata, wannan shi ake kira da gaba giwa baya siyaki, haka tana sharar ƙwalla ta nufi hanyar da zata sadata da gurin Madam domin ba wai gudun Gwoggo kawai take tsoro ba har da irin hukuncin da zata ɗauka akan Ummanta a yadda take ji da ka taɓa Ummanta gara ita ka mata ko mene ne. Taci sa’a baya gurin cike da ƙwarin guiwa ta ƙarasa. Madam na ganinta ta kamota da sauri tare da turata wani ƙaramin ɗaki. “Tataah kin san abin da kika yi, kin san wane ne wannan mutumin a ƙasar nan?” Tuni hawaye ya fara ambaliya a fuskar Tataah. Madam ta dubeta cike da tausayawa ta ce”Ya tafi amma ya ce ba zai barki ba sai ya hukuntaki, wallahi Tataah ina jin tausayinki a zuciyata a shawarce ki ajiye aikin nan” A hankali ta ɗago “Allah yasa haka shine mafi alkhairi, da mutumcina ya zube gara na bar aikin” Kularta ta ɗauko Madam ta zuba mata abinci kamar na kullum sannan ta biyata kuɗinta har da ƙari tare da mata fatan alkhairi, jakarta da babban hijabinta ta ɗauko sukayi sallama, tana tafe tana hawaye da tunanin makomar rayuwarta a gaba, shin ya gobenta zai kasance? Ta bar aikin da take samu suke ɗancin abinci a wani sau ɗaya ita da Ummanta yanzu ta bar aikin ya zasu kasance? Ga babban tashin hankalinta Gwoggo wanne irin mataki zata ɗauka idan taji ta bar aikin? Da wannan tunanin ta tare ɗan napep yau ko tayin bata da zarrar yi saboda hankalinta ba a kwance yake ba.
Ko da ta sauka ta biyashi tafi minti biyar tsaye ƙofar gidan kafin ta shiga jiki sanyaye. Ba kowa tsakar gidan hakanne yasa cikin sauri ta shiga ɗakin Ummanta, tana nan kwance kamar yadda ta barta da sauri ta ƙarasa tare da jinginar da ita jikin bango dan tasan ta gaji da kwancin “Sannu Umma!” Ta furta hawaye na zubo mata, ƙura mata idon da tayi ne ta gane tambayarta take yi me ya faru? Kukan da take dannewa ne yaƙi dannuwa ta fashe da shi amma a hankali domin bata san Gwoggo ta gane ta dawo gidan. Nan take ta fara ba Umma labarin abin da yw faru domin Ummar na jin komi amsawa ne kawai bata iyawa, sai gani tayi Umman na hawaye da sauri ta fara share mata “Umma bana so kina kuka, wannan yana ɗaya daga cikin tarin jarabawata kar ki damu” Sai ita ta dena hawayen domin Umma ma ta bari, hakan yasa ta jawo kular tare da buɗe abincin tasa cokali tare da kaiwa bakin Umma amma sai taƙi buɗe bakin daman daƙar take buɗesa kaɗan-kaɗan take ci, ganin hakan yasa Tataah cewa”Dan Allah karki sa wannan damuwar a ranki komi zai zo cikin sauƙi” Da ƙyar ta samu Umman taci sai ta rufe musu sauran da dare ta ɗauko na ledar da ta zuba da Farhan ya bata taci. A ɗaki tayi akwalar sallar azahar tayiwa Umma sukayi tare basu daɗe da idarwa ba aka kira la”asar duk suka gabatar.
Kwanciya tayi domin wani zazzafi ne ke damunta duk da yamma ce kasa ƙin kwanciyar tayi, baccin wahala yayi gaba da ita Umma nata kallonta har ta farka wajen shidda na yamma. Miƙa tayi tare da hamma fitsari take ji sosai hakan yasa ta ciro kuɗin da Madam ta bata ta ciro ta irga daidai wanda take bata kullum sauran ta ɓoye domin kuɗi sosai ta bata. Fita tayi ba kowa kamar ɗazun daman Gwoggo ko yaranta basu fiya zaman tsakar gidan ba, sun fi son rayuwar jin daɗi a rayuwarsu. Hakan yasa buta ta ɗauka tare da shiga banɗaki ta rage mararta, tana fitowa Ruhaima na shugowa cikin wata banzar shiga da bata dace da ita ba a matsayinta na musulma tana wani taunar cingam ji kake “Ƙas! Ƙass!! Ƙasss!!!” Tana gaba Tataah na bin ta a baya har suka shiga madaidaicin parlourn na Gwoggo. Ruhaima ta saki ɗan mayafinta wanda dashi gara babu a saman matsagaitan kujerun parlourn tana furta “Wash! Yau na gaji” “Sannu Ruhaima bari in kawo miki ruwa da abinci kici ki kwanta ki huta” Shugowar Tataah ne yasa Gwoggo ɗaure fuska tana bin ta da wani mugun kallo, da sauri ta zube “Sannu da gida Gwoggo!” Hannu ta miƙa mata “Ba sannu na tambayeki ba danƙa min” A sanyaye ta miƙa mata kuɗin, irgawa tayi daidai na kullum tare da cewa “Tashi ki fitar mini a parlour” Ruhaima ta ce”Gwaggo ki basu abinci na yau dan Allah” Da sauri ta juyo da cewa “Karki haɗani da Allah Baby bazan iya basu ba” “Tashi ki fita!” Ta daka mata tsawa, da sauri ta miƙe ta fita. Jiri take gani sosai tasan ciwon goshinta ne ya sakar mata da zazzaɓi ga gudun da tasha ɗazu, tana shiga ɗaki kuɗi ta cira tare da fita, tana tafe tana layi, gashi duk inda ta duba bata sami chemis ba, hankalinta ya tashi sosai ta nufo hanyar gida. Titi ta hau ba tare da ta sani ba, tun daga nesa yake danna mata hurn amma bata sani ba saboda yadda taji zazzaɓin ya fara hawar mata kai tafiyar kawai take ba tare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta ba. Daidai ƙarasowar motar daidai zubewarta a gurin a sume, a furgice ya fito daga motar duk da yaga ba wai bugeta yayi ba amma yanayin da ya ganta da alamar tana neman temako shi kuwa Faruuk Allah yasa masa zuciyar tausayi ga fara’a dawowarsa daga wajen aiki kenan yau yayi yamma sakamakon wani aiki da yayi.
Birkito da ita yayi nan take idanuwansa ya sauka akan fuskarta ‘Tataah!’ Ya ambaci sunan da ta faɗa musu ranar shi da Ma’aruf. Da sauri ya kinkimeta sai cikin mota inda ya tada ya nufi wani private hospital dake kusa da gurin, yana zuwa ƙara surarta yayi cikin asibitin nan take aka fara bata temakon gaggawa. Faruuk sai safa da marwa yake a harabar gurin ya kasa zama ji yake tamkar ƙanwarsa Nanaah da suke ciki ɗaya ce babu lafiya, kusan awa guda kafin Likitan ya fito da sauri ya nufe shi, tun kafin yayi magana Doctor ya ce”Kwantar da hankalinka ta farfaɗo, zazzaɓi ne me zafi na maleria sannan ciwon goshinta ma ya ƙara assasa mata zazzaɓin sannan tana da ulcer” Numfashi ya sauke a hankali tare da furta “Na gode Doctor zan iya ganinta?” “I Zaka iya amma ta samu bacci saboda mun mata allurar bacci tana buƙatar hutu sosai” Gyaɗa kai yayi tare da nufar ɗakin da aka kwantar da ita, tun da ya shugo idanuwansa ke kan fuskarta da tayi fayau sai ciwon goshinta da aka wanke mata shi ga allurar ƙarin ruwa liƙe a hannunta. Kujera ya jawo ta zaman masu jinya ya zauna har lokacin idanuwansa na kanta, kusan minti ashirin yana zaune gurin kafin ya miƙe da sauri jin wayarsa na ringing Mami ce ya ɗauka da sauri “Faruuk lafiya har yanzu baka shugo gida ba?” Yana ɗauka yaji muryar Mami na tambayarsa. Numfashi ya fesar ya kalli gadon da Tataah ke kwance “Lafiya ƙalau Mami wata yarinya na kaɗe da mota shine na kawota asibiti yanzu haka ina can” Kawai ya tsinci bakinsa da furta wannan kalmar. “Asibiti ya jikin yarinyar?” Mami ta tambaya a kiɗime “Ki kwantar da hankalinki ba wani ciwo taji me yawa ba yanzu haka an sa mata ƙarin ruwa ta samu bacci” “To Allah ya ƙyauta gaba, wanne asibiti ne?” Sunan asibitin ya faɗa mata tare da yanke kiran. Kusan minti talatin sai ga Mami tare da Nanaah sunzo hannunta riƙe da kwando da kulolin abinci. Kasancewar asibitin bai da wani girma sosai yasa tana shugowa basu sha wahalar gane ɗakin da suke ba. Bakin gadon ta ƙarasa bayan Faruuk ya amshi kwandon hannunta yana mata sannu, gabanta ya buga da ƙarfi ta ƙure Tataah da kallo kafin taja numfashi “Allah ya bata lafiya” Suka amsa da amin ya ce”Mami bare naje nayi sallah banyi magrib ba” Ta ce”Sai ka dawo” Fita yayi ya bar Mami da Nanaah ya nufi masallacin dake asibitin…

GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE

1, MU GANI A ƘASA..🔥
Ummu Affan

2, ABIN CIKIN ƘWAI..🥚
Ummu Maher

3, GUNTUN GORO..💥
Mom Islam

4, GISHIRIN ZAMAN DUNIYA🌎
Mrs Bukhari

5_ AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨
Miss Hajo

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

………..🥚👩‍❤️‍👨💥🌎….

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
+227 84 50 64 76

MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO

Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number….a.. 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻

infection
Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button