Health

Minene ZOGALE

A YITA TA ƘARE, SHIN ZOGALE KO KAZA
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Naman kaji yana da mahimmanci ajika musamman duba da yadda ya ƙunshi sinadaran proteins dake taimakawa wajen gina jiki, saisaita nauyi, bada kariya daga cuttukan zuciya da kuma uwa uba sinadarin triftofan dake sanyawa ƙwaƙwalwa farin ciki da annashuwa.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Yayin da; ZOGALE kuma akan masa laƙabi da itaciya me abin al’ajabi (miracle tree)

Bisa nazari a kimiyyance an fitar da wasu tarin abubuwa mahimmai game da zogale da bakowane zai taɓa kawo hakan ba.

Shiyasa a inda aka cigaba har sarrafasa ake zuwa capsules supplement Ai masa samfuri irin na magungunan asibiti kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa, wanda shiyasa nasha faɗawa mutane cewa supplements ba magungunan asibiti bane domin kowa na iya yi don neman kudi, ya rage naka kasan me ka kwaso kafin ka zubawa cikin ka.

Shiyasa wani supplements din da kuke hura hancin daga ƙasar waje yake ta yiwu cikin gidanki ma kina da abinda akai amfani dashi wanda naki yafi quality ma ƙila, kurum sani ne baki ba. Amma da ankawo abu ance yana qara kaza da kaza sai kaga kamar cin yunwa🙄kuita banka amma shiru

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

◾Zogale da kuke ji da gani duk mahimmanci irin na vitamin C dake cikin lemon ɓawo 🍊 wajen gyara ciki, jini, fata, da sauransu zogale ya ninkasa vitamin sau ninki bakwai da rabi (7.5×)

◾Ayaba 🍌 nada sinadarin potassium dake taimakawa zuciya wajen bugawa da karin lafiya gami da saita karfin tafiyar jini… Amma sinadaran potassium din dake cikin zogale tak sun ninka n Ayaba sau Goma sha biyar (15x) yawa.

◾Calcium sinadari ne da akan samu cikin Madara🥛 wanda ke taimakawa lafiya ƙashi tare da ƙwarinsa da hana zagwanyewarsa wacce ka iya sa saurin karaya! Gami da taimakawa wajen samar da kwayoyin jini… Amma Calcium din dake cikin ZOGALE ta ninka wacce ke cikin Madara sau goma sha bakwai (17×)

◾Karas🥕 fruits ne me ƙunshe da sinadarin vitamin A dake taimakawa wajen kaifin gani da lafiyar idanu… Amma zogale kacal yana da Vitamin A ninkin Goman (10x) wanda ke cikin Karas.

◾Kwai 🥚 yana da sinadaran proteins dake gina jiki, amma proteins din dake cikin Zogale ya ninka na cikin ƙwai sau huɗu (4x)

◾Spinach ganye ne mai kunshe da Iron sinadarin dake qarin jini, tare da zeaxanthin dake bada kariya daga cancer…. Amma zogale tak ya ninkasa sau Ashirin da biyar (25x)

◾Almond nada sinadarin Vitamin E dake tace datti ajika, amma zogale ya ninkasa sau uku (3x)

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

A DUNKULE AMFANIN ZOGALE SUNE:

 1. Bada kariya daga matsalar ƙarancin jini (anemia)
 2. Rage raɗaɗi da tsananin ciwon sanyin ƙashi (rheumatism)
 3. Hana yawan tashin cutar kafofin numfashi ta asthma
 4. Rage tsananin cutar tari da ciwon ƙirji wanda ya shafi huhu
 5. Bada kariya daga cutukan sankara wato cancer
 6. Yana hana cushewar ciki dake haddasa taurin bahaya wato constipation mutum na kashi yana hawaye ko nishi.
 7. Yana taimakawa wajen maganin ciwon ciki, cuttukan mayanin ciki da hanji rukunin su ulcer.
 8. Yana bada kariya daga ƙullewa tare da murɗawar ciki
 9. Yana Maganin ciwon kai
 10. Yana taimakawa wajen saisaita larurar hawan jini tare da hana sa yawan hauhawa, amma ba magance ciwon ba.
 11. Yana taimakawa wajen saisaita sugar ajika ga masu fama da ciwon diabetes. Amma ba magance ciwon kwatakwata ba, saide zai taimaka ta tsaya normal level
 12. Yana maganin tsakuwoyin cikin ƙoda wato kidney stones, ko hana tsakuwoyin cikin matsalmama taruwa wato gallstones a mutane masu teɓa.
 13. Yana taimakawa wajen magance hot flashes jin zafin kafafu, jiki, nonuwa ga matan da suka shiga shekarun dena Haila (menopause)
 14. Yana taimakawa Matan dake fuskantar ciwon mara, nonuwa, kai, kafafu da sauransu idan haila ta zo musu.
 15. Yana taimakawa masu matsalar thyroid wato Hyper da hypothyroidism.
 16. Yana hana yawan tashin cutar farfadiya wato seizure ko epilepsy.
 17. Yana maganin kumburin jiki.
 18. Yana taimakawa wajen haɓɓaka lafiyar jima’i da ƙarin shauƙi
 19. Yana taimakawa wajen haɓɓaka ruwan nono ga masu shayarwa.
 20. Yana taimakawa wajen maganin kananun cuttuka da larurorin fata irinsu cin ruwa, ciwon dasashi dake jini, da raunuka ko gyambo.
 21. Ana amfani dashi wajen tace ruwa me gishiri irin na teku domin samun nasha.
 22. Yana taimakawa wajen haɓɓaka lafiyar idanu da karfin gani.
 23. Wajen qarawa zuciya lafiya.
 24. Yana taimakawa wajen magance matsalolin damuwa, ƙunci, fargaba da halin matsi
 25. Yana taimakawa masu sickler wajen rage yawan crisis ɗinsu in ana ci ko shan powder din
 26. Tohowa gashi da qara yawa da tsayin sa.
 27. Washewa da qarawa hanta lafiya musamman ga masu larurarta

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

KAƊAN DAGA YADDA AKE AMFANI DASHI WAJEN MAGANI

 1. Game da cutar ASTHMA ɗibar Garin zogale adadin Gram uku (3gram) wato kamar girgijin cokalin Madara akaɗa aruwa asha ko tafasa ganyensa adadin wanda inya bushe ansan yana iya kaiwa girgijin cokalin shan shayi kona madara SAU BIYU a rana na tsawon sati uku, yana rage tsananin cutar, yana qara kuzarin huhu ga wanda suke da asthma me matsakaicin tsani wacce kan tashi akalla sau 5 ko fi a sati.
 2. Game da ruwan nono musamman a binkicen da akai na baiwa Mata sinadarin bayan kwana 3 da haihuwa zuwa kwana 10 da haihuwa wato sati 1 anga alamun qaruwar tsatstsafowar nono daidai gwargwado.
 3. Ga masu fama da cutar yunwa ko tamowa wato Malnutrition rika basu garin zogalen suna sha ko ci na tsawon wata biyu na taimakawa wajen samun kuzari da cikowar jiki.
 4. Kamar yadda akai bayani ga masu asthma haka idan masu ciwon suga sukai amfani da wancan adadin shima yana taimakawa wajen saisaita suga ajika ko kuma cin Kwaɗonsa.
 5. Kwaɗonsa arika ci tsawon wata uku na taimakawa wajen magance matsalolin zafin jiki da kafafu ga macen da ta shiga shekarun dena haila.
 6. Ga masu matsalolin cin ruwa, raunin cizon maciji, Dandruff, kurajen jiki… Su kwaɓa garin zasui su rika shafawa agun.

MATAKAN KIYAYEWA

Musamman Mata masu ciki ganyen kurum sukan iya cin kwaɗon sa ko powder din, amma a kiyayi shan ruwan saiwarsa, ƴaƴansa ko tsintsiyar zogalen saboda suna da sinadarin daka iya sa mahaifa soma murdawa wato naquda kafin lokaci da ciki ka iya fita musamman watanni ukun karshe na ciki.

Ga masu matsalar thyroid, sugar ko hawan jini suma su kiyaye ko su tuntuɓi likitan su domin magungunan da kuke sha kusan na sauko da sinadaran dake hauhawa muku ne idan ya zamto kun haɗa da shan zogale kunga zai mugun sauka da hakan ka iya ba mutum matsala kuma….

-Thyroid hormones ka iya yo kasa da yawa…

-Sugar na iya yin low da yawa..

-Blood pressure na iya yin low,

Wanda duk hatsarin yafi na high ɗinsu, don haka mutum ya auna kaɗan tukun yagani daidai yadda jikinsa zai adapting.

Haka ma masu shan magungunan rage kitse, ko magungunan kaikayin jiki, ko kyasfi wato de (anti diabetic, antifungals, antihistamines, statins, beta blockers) da sauransu.
┈┉━┅━💕🌷💕━┅━┉┈

Yanzu sai kui alƙalanci a ilmance shin zogale da kaza wanne yafi?

A baki tabbas kaza tafi zogale daɗi…. Amma a jika kuma a lafiya ce bama kaza ba zogale yafi kwai, nama, madara, ayaba, lemo.

Fatan zakui juma’a lafiya.

✍🏻
Dr-Nuraddeen katsina
08068962793

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button