Minene operating system (OS)

Operating system shine bangare mafi amfani, kuma mafi mahimmaci ga kowace waya ko na’ura. Domin shike dauke da kowane bangare na na’ura – shike umartar kowane bangaren ya yi aikin da aka umarcesa. Operating system ya kunshi gaba daya application na cikin na’ura, sannan kuma shine masarrafarsu a cikin na’urar. Idan babu operating system duk wata na’ura ta zama banza, wato ba ta da wani amfani, ko muce ba ta iya amfanin komai.
Operating system shike baka dama ka yi magana da na’urarka alhalin kai baka iya fahimtar yarenta, itama bata iya fahimtar naka yaren. Operating system shike tafiyar da waya ko na’ura – domin babu wani aiki da waya ko computer za ta yi wanda operating system bai sani ba. Operating system shike kunshe da ma’ajin bayanai, da bangarorin aiki daban-daban. Application masu yawa suke tafiya a lokaci daya a kansa.
Operating system shike tafiyar da software da hardware ta na’ura domin aiwatar da wani aiki da aka umarci na’urar ta yi. A yau akwai operating system iri daban-daban, kaman:
1. Windows OS
2. iOS na iPhone da iPad
3. OS na Android
4. KaiOS
5. macOS
1. Windows OS
Kamfanin Microsoft ya kirkiro Windows a tsakiyan karni na ashirin (mid 1980s). Bayan nan kuma ya cigaba da kirkiro Windows, amma dai shahararru wadanda aka fi aiki da su sune Windows 10 wanda su ka futar a cikin shekarar 2015, da Windows 7 a shekarar 2009, da kuma Windows Vista a shekarar 2007. Windows shine operating system din dake aiki cikin na’ura mai kwakwalwa (computer) ta saman tebur (desktop) ko ta saman cinya (laptop) – da kuma wayar Lumia.
2. iOS ta iPhone da iPad
Kamfanin Apple ne ya kirkiro operating system din wayar iPhone da na’urar iPad. Wayar iPhone dai ta fara shigowa kasuwa kusan tare da wayar Android a 2007 – amma har yanzu ba mu da cikakkun bayanai game da tarihin iPhone, saboda haka sai a yi mana uzuri.
3. OS ta Android
Kamfanin Google ne suke samar da operating system din wayar Android. Tun bayan da ragamar kirkiro operating system din Android ta dawo hannunsu, Google sun kirkiro version dayawa – mafi shahara sune Marshmallow wato version 6, da Nought wato version 7, da Oreo wato version 8, sai Pie ko Android Q wato version 9, wanda aka fadada shi ya zamo version 10 da aka fara aiki da shi daga karshen 2019 zuwa yanzu.
4. KaiOS
KaiOS wani operating system ne karami mai yanayi kaman na Android, sai dai shi karami ne idan aka kwatantashi da Android – kuma wayoyin dake zuwa da shi kananane masu keyboard. Operating system din KaiOS har yanzu bai yi yawa a yankunan Africa ba. Ya fi yawa a gabashin duniya – sannan shi din ma ba mu da bayanai sosai game da shi.
5. macOS
Kamfanin Apple ne ya kirkiro operating system din macOS, wanda da farko ake kira OS X. Operating system din macOS ya kan zo a na’urorin Apple kamansu na’urar Macintosh, da na’urar Mac. Wasu daga cikin version dinsa sun hada da Mojave wanda su ka futar a shekarar 2018, da High Sierra wanda suka futar a shekarar 2017, da kuma Sierra wanda ya futo a shekarar 2016.
Linux
Linux dayane daga cikin dangogin operating system wanda ke bude – wato kowa zai iya juyashi yanda yake so. Ba kaman Windows ba wanda kamfanin dake kerashi ne kadai ke iya juyashi yanda yake so. Linux dai da shi ake tafiyar wayar Android.
Zamu dakata anan amfanuwa da darusan da muke wallafawa a shafin nan. Muna godiya bisa ziyartar shafin nan da kukeyi – kuma mu na fatan sake ganinku. A huta lafiya. Arewastar