Technology

Minene 5G network?

Duba da yawan bunkasar masu amfani da wayoyi tare da computer a yanzu ana bukatar hanyar sadarwa mai karfi kuma mai sauri. A kullum masu amfani da na’urorin zamani su na kara habaka. Habakarsu kuma za ta sa aikace aikace su yi wa network yawa. Domin haka habakar masu amfani da na’urorin zamani ya na nufin network din mu da kansa ya na bukatar habaka.

A shekarun baya a lokacin farko farkon shigowar wayar salula, wayoyi su na amfani da network wanda su ke iya kira tare da aika sakon SMS da shi. Wadannan wayoyin a na iya cewa su na amfani da network din da za iya kira 1G. Daga baya kuma sai aka fadada wayar ta yanda za a iya aika sakon hoto mara nauyi, da kuma sautin murya mara tsawo wato sakon MMS. A wancan lokacin wayoyi su na amfani da network din 2G.

Amma a farko farkon karni na ashirin da daya (21th century) futowar wayoyin da ake iya shiga internet da su musamman Motorola, da Sagem, da Symbian da sauran wayoyi masu masu Java ya sa bukatar network mai karfi ta karu. Haka kuma shi kanshi network din idan aka fadada shi zai yi aiki da sauri, domin aiyuka sun yi masa yawa. Wannan bukatar ta network mai karfi ita ce za a iya cewa ta kawo hanyar samo network din 3G mai saurin aiki fiye da network din da su ka gabaceshi.

Sannan bayan shigowar wayoyin Symbian da Java, shigowar wayoyin iPhone da iPad da Android ya tilasta aka bullo da network mai matukar sauri da karfi domin shiga internet da samun damar kira ba tare da wata matsala ba.

Menene 5G?
5G ya na nufin 5th Generation, wato zurriya ta biyar a tsarin network. 5 ya na nufi biyar, generation kuma ya na nufi zurriya, amma bawai zurriyar mutane ba, ana nufin su wayoyin an tsarasu zurriya zurriya. Saboda haka zurriya ta farko 1G, network din su bai kai na zurriyar da su ka zo bayansa ba.

Abun da wannan zurriyar ta ke nufi shine fadada hanyoyin sadarwa. Idan mu ka duba a shekarun baya a na amfani da turken sadarwa wajen samar da sadarwar internet da sadarwar kira da tura sako a wayoyin salula. Daga baya kuma a ka fara amfani da tauraron dan Adam, wanda ya kawo sadarwa mai karfi da kuma matukar sauri.

To duba da yawan masu amfani da internet ya karu ya sa aka bullo da optical fiber cable wadanda aka shimfidasu a karkashin kasa da karkashi teku. Bullo da fiber cable ya kawo sauki tare da magance matsalar rashin saurin da network ya ke yi a wasu bangarorin duniya.

Domin ci gaba da samun cikakkun bayanai, tare da karin haske game da fasahar zamani, a ci gaba da kasance da shafin nan. Za mu dakata a nan da fatan ana amfanuwa da darusan kimiyya da fasaha wadanda mu ke rubutawa a shafin nan.

Sannan duk mai tambaya, sai ya yi kasa wajen comment ya rubuta mana. Mu kuma za mu amsa masa idan Allah ya sa mun sani. Daga karshe kuma mu na fatan sake ganinku tare da abokanku a shafin nan. Mun gode, a huta lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button