Technology

minene 5G network wace waya ke amfani da 5g network

Assalamu Alaikum, Barkanmu da wannan lokaci,barkanmu da sake kasancewa daku a wannan lokacin. Ayau munzo muku da bayanan wayar  Infinix Zero 5G daga babban kamfanin wayoyin hannu na Android wato Infinix. 

Kamfanin wayar android na infinix ya kasance babban kamfani a duniyar yau wajen kera wayoyin android wadanda suke cike da fasahar zamani,kuma kamfani mafi karbuwa a kasashen afirka karbuwar tasu ta samo asali ne daga yadda suke gina wayoyin android masu nagarta, 

juriya da kuma batiri me lasting,wadda kuma a duniyar android ayau darajar waya yana tareda yadda karfin batir dinta yake.

Kamfanin na infinix ya kasance yana samun karbuwa cikin gaggawa a wurin mutane saboda kera wayoyi masu inganci kuma a farashi me sauki kamar irin su Infinix Note 11 Pro da Zero X Pro.A bangare guda kuma kamfanonin da suke kan-kan-kan da kamfanin na infinix sune kamfanin Tecno da Itel wadanda dukansu kamfanonin china ne, 

Amma kamfanin na infinix sun kwace kaso me tsoka na kasuwancin wayoyin a kasahen afirka da yammacin Asia,wadda kuma yanzu suke shirin fadada kasuwancinsu a duniya baki daya.

Infinix Zero 5G itace waya ta farko a kamfanin na infinix me dauke da 5G network. Bayan NR support Infinix Zero 5G tanada 120Hz na refresh rate, sannan tanada inci shida da dugo saba’in da takwas (6.78 inch) na tsayinta kenan, tana da LCD screen da batir me girman mili amph dubu biyar 5,000 mAh, sannan tanada diri abin birgewa na “uni-curve”.

Infinix Zero a takaice:

Jiki (Body): 168.7×76.5×8.8mm,200g; Glass front,plastic frame,plastic back.

Display: 6.78” IPS LCD, 120Hz, 500 nits (peak), 1080x2460px resolution, 20.5:9 aspect ratio, 388ppi.

Chipset: MediaTek MT6877 Dimensity 900 5G (6nm): Octa- core.

Memory: ROM 128GB,RAM 4GB tanada wurin saka external memory (dedicated slot).

Operating system/Software: Android 11,XOS 10

Kamera ta baya (rear): 48 MP (main camera),PDAF; Telephoto 13 MP sai kuma 2x optical zoom; Depth: 2 MP. Duka dai tanada kyamara uku ne baki daya masu kyau.

> Kamera ta gaba (front 📷): tanada kyamara guda daya me dauke da; 16 MP ( wide angle).

Daukar bidiyo: Ta baya: [email protected],[email protected]/60fps; Ta gaba: [email protected].

Batir( Battery🔋): 5000mAh; fast charging 33W.

> Tanada fingerprint a gefenta da FM rediyo da kuma 3.5mm jak.

A bangaren aikin gudanarwa kuwa da karfin network infinix Zero 5G ta cika kusan duk matakan da ake bukata,domin kuwa tanada matukar gudu kuma bata jinkiri wajen aiki kasantuwar tanada wadataccen RAM saboda haka take da sauri a bangaren intanet da kuma sauran abubuwa kamar wasanni da sauransu.

Bugu da kari,a bangaren kamera kuwa Infinix Zero 5G tanada kamerori guda uku a baya, asalin kyamarar wato tanada megapixel 48 sai kuma telephoto lens da depth sensor. Tana daukar photo me kyau ga fotret sannan zaka iya yin abubuwa da dama da kamerar wannan wayar akwai options da yawa dazaka iya gyara hoto da sauran su. 

Kamera ta gaba kuma guda daya ce me dauke da megapixels 16 kuma tanada wayid angil ma’ana zaka iya buda ta idan zaku dauki hoto a cikin rukuni.

A bangaren batiri kuwa Infinix Zero 5G tanada batiri me girman mili amph dubu biyar 5,000mAh wadda idan ka cazata daga safe zai kaika harzuwa wasu awanni masu yawa kafin cajin ya kare.

Yadda take zuwa a sabuwa

Kamfanin Infinix sunyi fice bangaren kayan asessori, idan ka sayi waya kamfanin Infinix to zaka same su komai nasu neat ba wata matsala.

Infinix Zero 5G tazo ne a cikin kwali wadda yake me kauri akwai leaflet a ciki ma’ana bayanan yadda zakayi amfani da ita,bayan haka kuma akwai charger 33W da kyabil kirar type-A da type-C aciki,sannan zaka iya  musanya cajar da wani kyabil din me suna 5A domin saurin cika wayar.

Sannan akwai case wadda yake tiransifarent ne me suna TPU me karko wadda zai iya kare kamerar daga fashewa, sannan akwai masakin kunne me dauke da makiro fon a hade duk a cikin kwalin.

Infinix Zero 5G

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button