Technology

Mi ce ce Wallet

Wallet tana nufin lalitar da ake amfani da ita wajen ajiye kudaden Crypto, idan ka bude ta zasu baka wadansu kalmmomi kimanin 12 da za kayi amfani da su wato “private key” wadannan kalmmomi naka ne kai kaɗai babu wani wanda yake da irin naka. Mi ce ce Wallet

Wadannan Wallet din sun kasu kashi biyu akwai wanda basu a internet Wadanda ba a sauke su a waya, Sannan akwai kuma wadanda sauke aiki da fasahar Internet. 

Menene Private keys: PK Wadansu kalmmomi ne da suke a matsayin asusun lalitar ka gaba daya, domin da sune ake iya samun damar shiga cikin asusu/lalitar Wallet dinka.

Menene Public Keys: Wasu hargitsatstsun Harufa da lambobi ne da zaka iya amfani dasu wajen karbar Coin daga lalitar wasu, Misalin su kamar Account Number ne na banki.

1. Hardware wallet: Wallet ce da ake kirkira akan wani device da za’a, rika jonawa computer ko kuma Na’urar da za’a yi amfani da ita domin ajiyar Coins din Dake cikin ta, mafi akasari tana zuwa ne a irin kirar USB Flash drive, Kuma galibi masu amfani da ita sune wadanda suke doguwar ajiyar Cryptocurrency aciki.

2. Software Wallet: Wallet ce wadda kusan tafi Zama Comparabile domin itace muke aiki da ita a wayoyin mu da kuma na’urori kwamfuta din mu, suna zuwa ne Nau’in Desktop Application Wanda ake sakawa akan computer da kuma Mobile Application Wanda muke saukewa a wayoyin mu.

3. Paper Wallet: Shi wannan nau’in Wallet ne da kwata-kwata babu ruwansu da wani network ko kuma wani device, ana Printing dinsa ne a nau’in Jakar adana bayanai na QR code. 

Za’a Yi maka Printing na Private keys Dinka a Takarda daya sannan Public Keys dinka suma a takarda daban, idan zaka saka kudi ko za’a tura maka sai kawai ka bada takardar ayi scanning na code Shikenan Dama an Saita abinda za’a tura maka sai su shiga. 

Haka kuma idan zaka Duba adadin abinda ke ciki kawai za’ayi scan din takardar dake dauke da Private keys Dinka.Mi ce ce Wallet

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button