Hausa Novels

MEZAN YI DA ITA HAUSA NOVEL

Da sanyin safiya ta fito daga rugar fulanin cikin wata bukka dake daga gefen rugar sanye take da kayan fulani irin usul din fulanin nan fuskarta a cunkushe da mabayyanin ‘bacin rai. Tana tafe tana kunkuni alamar ba dan son ranta ya fito ba.

Related Articles

Kwarya ce a kanta da nono a ciki a tsakar gidan ta tarar da mahaifiyarta zaune da turtsesten ciki a gabanta ta had’a kai da gwiwa . Har zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya mata’kerere a ka, bakinta a zun’bure tace “innaji zan tafi” innaji ta saki ajiyar zuciya kafin ta furta “idan kinje ki gaida modibbon saura kuma idan kin fita ki tsaya dukan d’iyoyin jama’a ko tumakinsu “ “ aradu duk yaran da ya higa gonata nima sai na higa ta uwarshi “ cikin takaici innaji ya watsa mata harara “ ina magana shatu kina cewa aradu sai kinyi to ai shikkenan kije kiyi Allah ya shiryeki ni dai ina gaya miki ki kula da kanki kina sani ba kowa ne damu a garinnan ba idan mune yau fa anjima gawa muke bana son ace har yanzu kina wannan halinnaki kowa unguwar nan yasan halinki ba mai fad’ar alherinki sai aibunki shatu don Allah ki shiryu kada kizo nan gaba kina wahala a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido “ . Duk da jikinta yayi sanyi bata fasa cewa “yo innaji sai na bari yara suna tsokanata suna ce min mai idon mujiya kamar ubansu ya rad’a min “ innaji ta mi’ke da kyar da alama cikin yayi mata nauyi murya can ‘kasa ya kama hannunta “ suyi ta fad’a miki mana kyau idanun suke musu masha Allah zaki dinga cewa idan suka fad’a miki yi sauri ki tafi kinga hadari na hadowa ki gaidar min da modibbo ki kar’bo min rubutun idan ya rubuta “. Da sauri ta fice kamar zata tashi sama tana ayyana “ wallahi innaji ba zan kyalesu ba jibgar d’iya ni kayi idan ya shiga gonata’yan kwal uba masu kan faranti “.
Da tsallanta take tafe da wa’karta duk da ‘kwaryar nonon da take kanta har da cilla sanda duk yaran da ta wuce’kus suke da bakinsu kada suyi magana suci Na jaki sai dai tana wucewa suke tuntsira dariya murya ‘kasa’kasa suke cewa “mujiya idonki a loko “ sai su taka da gudu. Shatu ‘kwafa take tana haddacesu d’aya bayan d’aya ta kuma tabbatar wallahi sai sunyi bayani.

A saman buzu ta tarar da kakanta Na gurin uba moddibo wanda ya kasance gawurtaccen malami a garin nutsuwa tayi sosai don shi kad’ai take tsoro a garin , ta ra’be gefensa ta tsuguna sai da ya kai aya sannan ya d’ago ya kalleta fuskarsa ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar da take masa “ Gashi inji innaji tace tana gaidaka “ moddibo ya girgiza kai had’e da jan’kwaryar yana girgiza kai “ ‘yar nema ai Na zata yau ma kinyi halinnaki kin zubar dashi wallahi da yau ma sai na zaneki dan na lura sam ke baki tausayin innarki idonki a tsakar ka yake d’auki ki kaiwa salame Ta adana shi a ciki” mi’kewa tayi zuciyarta a tunzire kamar ta kai masa mari ita fa ta tsaneshi bata ‘ki ya she’ka barzahu ba don ya takura mata baki kamar shantu ta fad’a a zuciyarta zanyi maganinka aradu gobe. A tsakar turken tumaki ta tarar da ita salame ta amsa gaisuwarta tana kar’bar’kwaryar nonon fuska a sake tace “ya jikin innar taki?” “ ba sauki sai na Allah yo wannan uban ciki yayi mata turtsitsi ta ina zata samu sau’ki Idan ba haifeshi tayi ba aradu duk ranar da Ta haife abin da yake cikinta sai na jibgeshi “ salame ta zaro ido tana kallon shatu da take zaro zance “ashe kuwa dai shatu da ake cewa baki da kai zancen ya kusa tabbata jaririn zaki jibga?” Ta ta’be baki “ yo idan ban jibgehi ba ai aradu ban haifu ba a cikin innaji ko sallah fa a zaune take yi gashi tun a ciki shegen karanbani garai yayi ta kwarafniya jiya fa ina kallon cikin yana wutsilniya wallahi tana cin abinci kika ji d’if tun kan yazo duniya ma ya nuna halinsa” salame ta girgiza kai tana katse’kwaryar ta mi’ka mata daidai lokacin da modibbo ya shigo yana dogara sanda “ to uwar shashashanci kina nan kina zuba kamar ‘ya’yan kanya zo ki wuce ki kai mata rubutun Allah ya raba lafiya” “ ameen “ ta furta murya can ‘kasa “ ai kai na gado a kwakwazo duk gari an sani” mai kika ce “? A guje ta arce tana fad’in cewa nayi Allah ya tashe mu lafiya salame kuwa girgiza kai tayi don ita taji abinda tace sarai don dai shi ma kunnensa yana da matsala ne.

Tun a hanya take Allah-Allah taga d’aya daga cikin yarannan sai dai bata gansu ba haka ta koma gida ranta a ‘bace da rashin cikar burinta.

Tana shiga innaji ta kar’bi rubutun had’e da nuna mata buta ta san nufin innaji tunda lazimi take ta sunkuci butar ta fara alwalar. A nutse ta tada sallah duk da rashin jinta innaji Ta tsaya sosai wajen bata ilimin addini don masaniyace sosai Na boko ne dai sai taga dama take zuwa ko idan an tura ta ta shige gonakin jama’a tayi’barna.

Suna idar da sallah innaji ta ri’ke hannunta murya a raunane tace “ shatu jikina yana bani kamar rayuwata tazo gangara don haka ya zama dole yanzu Na sanar dake labarina ko da nan gaba zaki bu’kaci haka a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido ga mahaifinki tsawon wata biyar da tafiyarsa har yau ba amo ba labari daga tafiya fatauci ina son ganinsa ban san ina ya tafi ba.” Hawayene ya ciko a idanun shatu sam bata son taji innaji tayi mata zancen mutuwa ta lura kuma kwana biyu kullum zancenta kenan. “ innaji don Allah ki daina min zancen mutuwa idan kika mutu an higa uku “ baki shiga uku ba shatu Allah yana tare dake kuma kina da gata tunda moddibo yana raye balle nasan mahaifinki komai dad’ewa Zai dawo ki share hawayenki burina kawai ki nutsu “ fad’awa jikinta tayi “don Allah ki daina cewa zaki mutu ni kece gatana “ innaji murmushi tayi tana kallon zallar yarinta a idon shatu da Ba zata gaza shekara sha daya ba. “ To ki dinga addu’a Allah ya rabamu da cikinnan lafiya naga aurenki shatu “. Da sauri ta furta ameen “

Har dare tana son jin labarin da innaji zata bata amma kuma tana tsoron zancen mutuwa don haka tayi mu’kus.

Cikin dare ta kasa ha’kuri ta mi’ke zaune “Innaji baki bani labarin ba “ murmushi innaji tayi don tasan shatu da son jin zance ta mi’ke zaune da ‘kyar ta jingina da bango.

. *
Asalina haifaffiyar garin liman katagum agarin bauchin yakubu sai dai mahaifiyata yar asalin mambilace a jihar yola acan mahaifina ya ganota ya aura shi yasa zaki ganmu da asalin kyau na fulanin usuli.

Mahaifina d’an bokone mu biyu iyayena suka haifa daga ni sai yaya ta dijama. Kasancewar mahaifina lecturer hakan yasa ya dage akan harkar iliminmu. Muka taso cikin tarbiyya da ‘kaunar juna ni da yayata mai tsananin kama dani ta girme ni da shekara hud’u. Yayata tana gama secondary samari su kayi mata ca hakan yasa babanmu yace dole ta fitar da miji duk da kasancewarsa d’an boko baya take ilimin addini yana bashi ha’kkinsa sosai. A lokacin ina ss 1 yayata ta fitar da miji a kayi mata aure da wani matashin mai kud’i ahmad manga inda suka tare cikin garin bauchi a unguwar gwallaga.

Lokacin da na shiga ss2 a lokacin muka fara soyayya da wani ma aikacin makarantar atbu inda gidanmu yake kasancwar a staff houses muke shara yake da gyaran compound d’in gidanmu soyayyarsa ta d’ibeni don kyakykyawa ne sosai . Ba wanda ya sani a gidanmu a ‘boye muke komai duk da bama keta iyakar ubangiji amma fa soyayya tayi zurfi a tsakaninmu ta yarda tabbas a lokacin idan aka hanamu aure zamu iya rasa rayuwarmu. Duk da bashi da ilimi haka nake son shi tunda yana da ilimin addini bokon ma a hankali nake koya masa a ba ca da. Ina ss 3 tashin hankalin ya fara zuwa don kuwa wani d’an abokin babanmu yace yana so na babanmu kuma yace ya bashi gashi bababnmu irin masu kafiyar nan ne sam baya juyuwa mai juyashi dama babansa ne kuma ya rasu. Hankalina ya tashi sosai nayi kuka kamar raina zai fita na gaya wa mamanmu bana sonsa ta fad’awa baba yace ban isa ba bai haifi dan da zai ce yes yace no ba. Haka mamanmu tayi ta rarrashina ita da yayata amma zuciyata Ta kasa ha’kura.
Hakan ya tunzira zuciyar Baba yace ya fasa barin sai na gama jarrabawar na ‘karasa a gidan mijina aure zai yi min.

Aka fara shirin biki hankalinmu a tashe ni da miji wannan yasa ana gobe d’aurin auren muka gudu ni da miji. Da sassafe muka wayi gari a wata ruga ya bani kayan fulani na saka sai da muka zo gidan ya sanar dani gidansu ne nan ya shiryawa mahaifinsa ‘karya akan cewa iyayena sun rasu a hanya kuma fulanin tashi ne hakan yasa suka rungumeni a gidan bayan wata biyu aka d’aura mana aure da miji duk da kullum zuciyata na bani shawarar na koma gida amma ina tsoron mahaifina. Shakararmu goma da aure kafin Allah ya kawo cikinki. Har yau a garin nnan ba wanda yasan ina da ‘yan uwa sai yanzu da nake gaya miki kina zuwa liman katagum kika tambayi gidan sarkin fulani nan ne main house na familyn babanmu koda ta Allah zata kasance. Ya fad’a hawaye na ziraro mata na tuno iyayenta.

Shatu ma hawayen take “yanzu innaji da gatanki muke ta yawo bama nan garin bama can mune har nan niger 🇳🇪 ashe asalinmu yan nigeria 🇳🇬 ne “. Innaji ta dafa kanta tace “kaddarar haihuwarki ne shatu da ta wannan cikin fatana idan kin sadu da dangina kice su yafe min na mutu ina tsananin kewarsu “. Share hawayenta tayi tace “insha Allah innaji ba zaki mutu ba da ‘kafarki zaki ga danginki “.
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚

08033748387

2

Sumul suka farka innaji ranar ta d’an ji sau’ki, har yamma shatu na tare da ita Ta kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai ‘kyalli gashin yake yasha man kwakwa kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen ‘kasar hindu don ma bata son gyarashi da ‘kyar take barin innajin ta ta’ba mata kai shima sai tayi mata jan ido.
Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba d’aya ta rasa sukuni.har la’asar tayi kafin ta mi’ke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji ta kar’ba tana murmushi “ Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da nake miki fata a rayuwarki “. “Ameen “ shatu ta fad’a murya a sha’ke. Suna idarwa innajin ta aiketa gidan modibbo kar’bo rubutu.

Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.

Ko mintuna biyu bata yi ba a gidan moddibon ta juyo a sukwane ko saurarar gwaggoji ( salame) da take ‘kwala mata kira ba tayi ba.

Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya had’e da cewa Alhamdulillah Allah innaji na d’auka kafin na dawo kin mutu” murmushi innaji tayi kafin ta furta “mutuwa ai sai lokaci yayi ayshatu” da sauri ta dubeta jin sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace “lafiya “ ta hau girgiza kai “ ji nayi kin kira ni da sunan da baki Ta’ba kira na ba “ dariya kawai tayi tana shan rubutun ta had’e da kallon shatu kallo mai nuna tsananin ‘kaunar da take mata.

Cikin dare innaji ta fara jin ciwon na’kuda tun tana daurewa har abin yaci ‘karfinta ta mi’ke da ‘kyar ta bud’e wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta rubuta address din family house d’insu ta nad’e a takarda ko bakomai bata san ya ta Allah zata kasance ba.

Da ‘karfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ru’kun’kumeta “ bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata “. Da kyar innaji ta’ka’kalo wani murmushi tana mi’ka mata takarda “ ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu “. Hawaye take yi sosai na tsananin azabar na’kuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai zatayi abinka da’kan’kantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba d’aya ya saki ji kake d’if lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fad’a musu zafin fitar rai a yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya kwasheta barcin da shine ya kaita har’karfe goma na safe.

Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken d’akin tare da tunanin me yasa innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jama’a “kuzo ku duba min innata tayi barcin zomo na tasheta ta’ki tashi “ ma’kota suka shiga gidan sai gani tayi suna fitowa jiki a salu’be ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata ta fad’a ne Allah yaji’kanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta ‘kwalla’kara sai ganinta a kayi a zube ba numfashi.
Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama Allah yaji’kan iyayenmu.

A safiyar juma’ar misalin ‘karfe sha d’aya na safe aka sada innaji zuwa gidanta na gaskiya hawaye sai zarya yake a fuskar abokan arziki kowa ya shaida innaji bata da abokin rigima to ita maganar ma bata dameta ba balle har ta samu abokin rigima. Shatu zube a cinyar gwaggoji sai mayar da ajiyar zuciya take da razana har sai da moddibo ya sake mata rubutu aka bata. To haka dama rayuwa take.

A hankali shatu ta fara sabawa da rashin innaji kullum kuwa ma’kale da takarda da hotunannan take kwana tayi al’kawarin sai ta sadu da dangin mahaifinta. Gidansu gwaggoji ta koma ta daina wanka ta daina komai wai ita ta gama jin dad’in duniya tunda innaji ta tafi ta barta. Yaran mutane kuwa a lokacin ta ‘kara takura musu musammam masu uwa raye shatu bata da ‘kiba sam amma sai ‘karfi ta gallabi mutanen garin tun ana d’aga mata’kafa saboda rashin uwa har tausayin ya kau aka fara kawo ‘kararta wajen gwaggoji. Gwaggoji bata da fad’a sam don haka shatu take’kara sangarcewa kullum da rashin jin da zata rakito ta kai yanzu har manya shiga shirginsu take musamman masu gonaki da suke kuka da ita.

Makaranta kuwa tuni tayi sallama da ita ta allo kawai take yi itama don moddibo yana cin gidansu ne da batayi ba. Gashi yanzu shi bashi da cikakkiyar lafiya yau fari gobe tsumma.

BAYAN WATA SHIDDA

Da rasuwar innaji jikin moddibo ya ‘kara tsananta, hakan yasa shi fara had’a komatsansa baya so ya mutu anan ya fito ya mutu cikin ahalinsa da suke garin yola. Itama gwaggoji hankalinta yafi kwanciya su tafi musamman saboda shatu ko bakomai a can dangi da yawa za’a samu mai tayasu kula da ita.

Safiyar wata asabar suka fito da ‘yan ‘kullin kayansu suka fara sallama da mutanen garin da suka yi dandazo a ‘kofar gida, duk jikinsu yayi sanyi musamman yara da suke kallon shatu Idanunsu fal ‘kwalla. Shatun ma kuka take ta kalli yaran tana murmushi “kuyi min tsokanar’karshe don Allah ko bakomai zan dinga tuna ku.” Shiru su kayi mata, murya na rawa ta fara binsu d’aya bayan d’aya tana cewa “ku fad’a mujiya mai idonta a loko….” Ai kuwa yara suka fara har ita suna kuka kuka, dariya- dariya a haka suka rakasu har inda mai amalanke yazo ya d’ebesu tana d’aga musu hannu suna bin amalanke , rayuwa kenan ba mamaki shikkenan tayi sallama da garin nijar. Amma ta’kudirce insha Allah zata dawo.

Kwanansu kusan biyu suna tafiya, kafin Allah ya kawo su garin yola nan suka hau motar garinsu demsa, daga demsa suka shiga wata’kur’kura ta isar dasu cikin ‘kauyensu gwamba. Ai kuwa mutanen garin suna ganinsu suka shiga fitowa ana murnar ganinsu.
Bayan sun shiga cikin gidan mai girman gaske ginin’kasa suka fara yiwa juna gaisuwa anan suke jin labarin mutuwar muji mahaifin shatu. Ashe da ya taho hatsari yayi a garin yola hakan yasa ya bada address din family house d’insu na nan kafin a kawo shi kuma rai yayi halinsa. Su kuma basu san inda zasu samesu ba. hankalin shatu ya tashi ta zube wajen har iskokanta suka ziyarceta, kowa a wajen ya tausaya mata musamman da suka ji labarin rasuwar maryamu ma. Moddibo kuwa innalillahi wa inna ilaihir raji’una yake ja kansa yana juyawa sai gani a kayi shima luuuuu ya kifa. Ai ko ana d’ago shi aka ga rai yayi halinsa. Nan kuwa koke- koke ya ‘karu shatu kuwa kuka take aljannun Na sake bugeta. Gwaggoji kuwa kasa magana tayi tana taajjabin lamarin Ubangiji ashe haka mutuwa take lokaci d’aya taji mutuwar d’anta ‘kwaya guda da rage bata dawo daga razanin ba shima mijin ya mutu, ai ji tayi ina ma ita ma ubangiji ya d’au ranta.

Moddibo kam ya dace ya mutu ranar juma’a aka sadashi da gidansa Na gaskiya. Haka rayuwa take Allah yasa mu cika da imani .

Gwaggoji daga ranar bata sake samun lafiya ba. sai dai a kwantar a tayar, hankalin shatu ya matu’kar tashi duk ta sake firgai firgai ko wanka batayi, bata so ta rasa gwaggoji a karo na hud’u Ta san idan ta rasa gwaggoji gatanta ya gama zubewa warwas. Mutanen nan taga basu da zumunci ko a yanzu haka ita take yiwa gwaggojin komai hatta da gyara jiki idan ta’bata. Iyakacinsu da su abinci shima ko yaro’karami zai iya cinyeshi.

Ranar wata juma’a da yayi dai-dai da rasuwar malam sati takwas, suna kwance gwaggoji na nishi sans-sama tace “ shatu ko bayan raina kada ki zauna ana tunda kince maryamu ta gaya miki inda magaifiyarki take kiyi tafiyarki can, wadannan mutanen kowa kansa ya sani, ga ‘yan ubanci da suka a kansu ba zasu ri’ke ki da gaskiya ba , ina jin tsoron in mutu in barki anan don haka na dad’e da tanada miki kud’in mota.” Ta fad’a tana lalube a cikin bujenta dubu goma cif ta ciro ta mi’ka mata. “Ki’boye shatu ki adana su Allah yayiwa rayuwarki albarka ya kareki daga sharrin dukkan abin ‘ki, baki da wani gata sai dangin mahaifiyarki saboda haka ki tafi can ni na san lokaci na yayi, mutanennan mugaye ne duk ‘yan uba suke da malam dalilin gallazawar da suke mana da saran ‘boye yasa muka gudu muka barsu yaranmu ta dalilin azabarsu su uku muka rasa don haka kema ba zasu barki ba….” tari ne ya fara sar’keta tuni ta fara aman jini, zuciyar shatu ta bushe Ta riga ta saba da mutuwa ta san ita d’inma mutuwar zata yi.

A Jikinta kuwa gwaggoji ta saki kalmat shahada ta mutu, ko alamar hawaye babu a idon shatu sai zuciyarta data ke wani tu’ku’kin ba’kin ciki. Ta ja mayafi ta rufe mata fuska taja gefe tana jan wani numfashi mai huci ta tabbata yanzu bata da wani gata……..

Sai asuba ta sanar da mutanen gidan mutuwar gwaggoji. Ba tare da wani nuna jimami ba su kayi jana’izarta aka kaita gidanta na gaskiya.

Bayan kwana bakwai rayuwa ta canjawa shatu zancen gwaggoji ya fara tabbata, ko abinci basa bata sai tayi musu aikatau. Karshe suka ce zata fara fita tallan nono bayan ga ‘ya’yansu mata basu d’ora musu ba.

Cikin dare taji jatau suna shawara da d’an uwansa wai su had’a ta aure da liti yaron da kowa ya shaida d’an Ta’addane, ai kuwa shatu a daren ta mi’ke Ta hau shiri tabbas lokacin barinta garin yayi a yau zata tafi dangin uwarta.

Cikin duhun daren ta fito sai dai kafin ta kai ga d’arewa’karamar katangar jatau ya hasketa. Waye nan…….
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚

08033748387

3

“Waye nan” jatau ya sake fad’a da sauri shatu ta juya tayi kamar zata shiga bayan gida, murya can ‘kasa tace “nice zan zaga ne “ tsaki yayi ya shige yana bambamin fad’an “iskancin banza da wofi kawai ki nemi frigita ni cikin tsohon dare zan yi maganinki mai kama da ifritan aljannu” shatu dai bata ce komai ba tabi bayansa da harara tana sakin ‘kananan tsaki “ aradu Allah zai kaimu lokacin da zanyi maganinku “ yana shigewa sad’af- sad’af Ta shige bayan gidan ta kuma haure’karamar katangar ta bar gidan a guje.

Shatu duk da kasancewarta yarinya da ba zata gaza shekara sha biyu tana da wayo da kaifin basira, hakan yasa bata sha wuyar kai kanta tasha ba, ta hau motar da zata kaita har cikin gari sannan aka saka ta a motar garin bauchi.


Tafiyar awowi ce ta kaisu bauchi ko daga nan ta tambayi motar katagum, yaran tasha yasa ta a motar da zata kaita tafawa balewa daga can ne zata samu motar katagum.

Suna isa kuwa kasancewar gidan babban gidane bata sha wuyar nemansa ba a kasadata da family house din nasu. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo kasancewar tayi kama da mutanennan da ake kira bararoji, jikinta dukun-dukun hakanan kanta she looks very dirty.
Sam bata damu da rufe gashin kanta ba haka take tafe wurjanjan da silifas wari da wari a ‘kafarta.

Gidane babba irin ginin mutanen da , mai dauke da d’akuna birjik a kowacce shiyya, kasancewar nan ne ainahin gidan sarauta na garin, yasha gyara sosai da paint kana gani dai kasan ba wahala a tattare da ahalin gidan. Fili ne fetal ga manyan bishiyu ko ta ina. Rashin sanin inda zata yasa ta nufar wasu yara da taga suna wasan’kwallo a harabar gidan, ganinta a gurin yasa suka arce da gudu don su tabbas zatonsu aljannahce. Tsaki shatu taja had’e da komawa can gefe da ‘kullin kayanta ta zauna.

Iface-Ifacen yaranne ya fito da ahalin gidan a rud’e suna duban yaran da suke fad’in “Aljannah Aljannah “ shatu ta girgiza kai tana juyosu daga waje a zuciyarta tace “ai kuwa sai kunci ‘kwal uwarku akan iyayenku zan huce a aljannar zan zo musu kafin na bayyana kaina “ da sauri ta hargitse sumar kanta tsaf ta mi’ke ta hau zare ido ta shagid’e hannu d’aya, Ta dumfari babbar shiyyar da taga yaran sun nufa.

Ba zato ba tsammani suka ganta a tsakiyar filin kan kace meye iyayen yara sunyi hanyar neman tsira sai tsohuwa dada da aka bari jikinta yana’bari tana fad’in innahu min sulaimanu kuyi min aikin gafara wallahi ba laifina “ shatu ta cusgune fuska ta dumfari dada ai kafin kace mai dada ta saki gudawa da fitsari a wando ganin tana shirin fad’uwa shatu ta tintsire da dariya “ ke tsohuwa dakata kada ki sume min ni ba aljannah bace kamar yarda kuka d’auka mutum ce ni d’iyar maryama ‘ya wajen d’anki Lamid’o “. Dada ta zaro ido tana kallonta kafin tace “ki rantse da Allah “ shatu taja tsaki “ kwarankwatsa ni ba aljannah bace ko kinga kofato a ‘kafata “ sai sannan dada taja dogon numfashi tana zamewa a jikin bango zata zauna. Shatu ta kalli gudawar tace tana toshe hanci. Sai sannan dada ta lura ta saka salati da sauri ta rarrafa tashiga bayan gida shatu kuwa sai tuntsira dariya take.

Sai dada ta kimtsa ta dubeta bayan ta kaita rumfarta taje ta kira matan gidan “ to duk ku fito ku ji min bayani wai wannan d’iyar maryama ce maryaman da tuni lamid’o ya sallamata ga d’iyarta mai kama da jinnu ta bayyana “ shatu ta girgiza kai a hankali ta furta “zaki bayanin wannan ma “.

Sai sannan kowa ya fito cikin tsananin ta’ajjibi ana kallon shatu wai wannan jinin lamid’o ce yarinya kamar fulanin daji ita kuwa maryama mai yayi mata zafi ta za’bi rayuwar daji akan rayuwarta cikin gata da mutuncinta “. ‘Daya daga cikin matan ta fad’a shatu ta watsa mata wani kallo had’e da cewa “ yo haka ‘kaddarar Allah ta za’ba mata kuma kada a sake a zagi uwata don kuwa bata raye aradu raine zai ‘baci “ Ta fad’a cikin karyayyiyar hausarta ta fulanin usli. Gaba d’aya suka zaro ido dada ta saka kuka “yanzu’yar nan kika ce maryama ta mutu? Innalillahi yau ya lamid’o da liman zasuji da wannan ba’kin labarin kullum zancen su na maryama ne “
Ta fad’a tana jan majina hawaye sha’be-sha’be, kafin ta share hawayenta tsaf ta mayar da kallonta kan shatu tana mata kallon ‘kurilla “ wace shaida zaki bamu mu yarda ke d’in jininmu ce d’iyar maryama daso?” Shatu ta mata wani kallon she’ke’ke aradun Allah babu shaidar da zan baku sai na cika cikina tunda ku kam baku san zuru ba kun san wahalar da na hya kafin nazo nan amma ba wanda yace min ga ko ruwa Na hya “ dada tace “kwarai da gaskiyarki ke harira kawo mata abinci ke kuma furera ki kira matar lamid’o kice ko mai suke su biyo jirgi daga habuja suzo hukuncin ubangiji ya tabbata.”

Ana kawo mata abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya dad’in abincin har tsakar kanta ga nama zu’ku-zuku wanda rabonta da cin nama tun sallahr layya ta bara idan har bata manta ba. Taci tayi nak ta sha zo’bo sai sannan ta fara washe baki tana dariya ta kalli dada “to ko ki yarda ko kada ki yarda ni d’in diyar maryama ce ga hotunan da ta bani kafin rai yayi halinsa” ta fad’a tana zaro hotunan daga bujen da yake jikinta. Wanda suka san maryama da wanda sai a hoto suka santa duk suka zaro ido dada girgiza kai “ ba shakka hukumullahi la ajabun innalillahi wa inna ilaihirrajiuna wato maryama daso sallama tayi damu “ hawaye shabe shabe dada ta saki tana sake rushewa da kuka , sai kuma ta dubi shatu tana fyace majina “ ikon Allah wato shi ubannaki bararo ne?” Shatu ta zaro ido “ kan bala’i inji uban wa?” Ta fad’a tana cizon yatsa
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-4
ELEGANT ONLINE WRITERS****

Dada ta zuba mata idanun tsofaffinta , cikin gatse tace “inji ubanki muji da ya sace mana’ya ya gudu da ita” shatu ta girgiza kai had’e da mi’kewa a katifa tayi kwanciyarta. Ba a d’au dogon lokaci ba barci yayi awon gaba da ita. Dada ta bita da harara “ wannan yarinyar daga gani ‘yar daru ce bari kakannin naki suzo ni za’a barwa ke sai na koya miki hankali tukun, ke fure kira min su lamid’on kiji sun taho “ furere ta amsa daya bayan d’aya suna ficewa daga d’akin. Koda furere ta kira wayar taji shiru ta tabbatar sun taho kenan tunda ta san ba sajin kud’in jirgi kullum a tafe suke.

Dada tana zaune tana lazimi ita kuwa shatu barci takeyi sosai abinta cikin kwanciyar hankali.

Liman na dawowa dada ta sake bashi labari, cikin farin ciki yake kallon shatu da ba abinda ta d’auko na uwarta da alama can dangin ubanta ta d’auko don ban ga kamanni ba “ ya fada yana kallon dada, dada ta ta’be baki “ yo kaima dai ka fad’a yarinya kamar bararo ko fulanin daji anyi magana tace inji ubanwa? Bari su su lamid’on suzo sa tantance idan jininsu ce ko Ba tasu ba sa san yarda zasuyi da ita, ni wallahi tulin sumar kanta ne ma da idanunta suke ban tsoro yarinya kamar d’iyar jinnu don kyau “. Malami dariyar su ta manya kawai yayi gani n shatu ta mi’ke ba tare da sanin dadar ba tana ta harararta “ yo ki fito kice min kawai baki yarda dani ba mana Allah na tuba na me zan zauna ina muku’karya “

Sallamar su lamid’o ce yasa dada yin shiru bata tanka ta bata Allah ya sani tsoro yarinyar ke bata “ maraba lale da iyayen maryama kuzo yau dai kuga jikarku d’iyar maryama “ da sauri suka ‘karasa d’akin suna watsa idonsa akanta ta kuwa ‘kuri tana kallonsu.maman maryama tace “dada kada kice min wannan jinin maryama ce?” Dada ta ta’be baki “babu wai itace maryama ta haifo muku bararoji mai kama da ubanta. Ai mama bata’karasa jin abinda zata ceba ta ‘karasa da sauri ta kamata ta rungume “ Alhamdulillah ashe zan sake ganin maryama?” Shatu ta zame jikinta “ ai kuwa ba zaki sake ganin maryama idan dai ba yau kema zaki bita yarda ta tafi ba ashe kuna sonta ku ka kasa bata burin ranta akan haka ta gudu ta bar gida ta bar gatanta ta gwammace rayuwa cikin daji “. Lamid’o zama yayi yana kallon yarinyar mai cike da tsiwa da surutu mama kuwa sake janta jikinta tayi “ mun dade muna neman inda zamu ga maryama sai yau Allah ya nufa “ cewar lamido dada ta girgiza kai “ yau ai kaga dalilin da yasa ba zaku ga maryama ba tana can ‘kungurmin dajin da ba wuta balle a samu tv ta ina zata ji cigiyarta da ake ba’kin cikina d’aya ne Allah ya dauke maryama ba tare da mun sake ganawa ba sai bararon ‘yarta da ta bar mana” dada ta fad’a tana fashewa da kuka, mama ma zama tayi da’bas a kujera tana juya maganar dada lamid’on kuwa salati kawai yake ja , yanzu maryama ta mutu maryaman da ya dad’e yana nema ya nuna mata gata dama tuni ya yafe mata , mama kuka ta saka sosai tana rungume shatu a cinyarta cikin tsananin’kaunarta sam bata damu da daud’ar da take jikinta ba. Shatu taji zuciyarta ta karye da tausayin kakanninta mutuwar innaji ta dawo mata sabuwa kar itama ta rungume mama tana sake sakin kuka mai ratsa zuciya mama ta sake rungumeta tana shafa himilin gashinta.

Tsawon lokaci suna cikin jimami kafin lamid’o ya kalli shatu yace ya sunanki?” Murya a dashe tace “ shatu “ lamid’o ya jinjina kai “ to ya akayi kika gane nan kika zo ina so naji labarinki da garin da kuka zauna da labarin rayuwar maryama a garin……. shatu ta gyara zama daidai lokacin da wani daddad’an’kamshi ya ziryaci hancinta tana d’aga ido ta hango mai sallamar da sauri ta mi’ke tana wara ido tana fad’in “innaji “ mama ta kama hannunta “ zauna aysha ba mamanki bace yayarta ce da take bi ana ce mata mammah “ mammah da take tsaye ta waro ido tace “ mama kada kice min y’ar maryama ce ina maryaman ina ‘yar uwata alhamdulillah yau burina ya cika “. Mama hawaye ya ziraro mata don Ta san za’ayi haka Ta sani sarai deejah bata da buri irin taga maryama kullum zancenta kenan. Shigowar samarin yaran deejan yayi daidai da lokacin da mama tace “ Addu’a ‘yar uwarki take bu’kata yanzu Allah yayi mata rasuwa wannan y’arta ce Aysha da ta bari “. Gani su kayi mammah kawai ta zube numfashinta na ‘kokarin d’aukewa da sauri y’ay’anta su kayi kanta suna jijjigata had’e da kiran sunanta amma shiru. Dada ce ta d’ebo ruwa ta watsa mata sai kuwa ta kawo ajiyar zuciya “mama don Allah kice min wasa kike ko mafarki nake ba maryama ta bace ta mutu “ Lamid’o ya mi’kar da ita zaune Kafin yace “ Allahn da ya fi mu son maryama ya amsheta addua tafi bu’kata yanzu sai kuma d’iyarta da ya bar mana mu dinga kallo muna jin dad’i Alhamdulillah da wannan hikima ta ubangjji “. Da sauri mammah taja shatu jikinta ba tare da ‘kyankyaminta ta rungumta tana bata sumba a gefen kumatu cikin nuna mata tsananin ‘kauna take share mata hawaye tana kallonta with so much caring , saurayin d’anta da yake gefe imran ya hau ‘bata fuska cikin tsananin mamakin mammahn da bata’kyankyamin wannan yarinyar da Daud’a ta samu wajen zama a jikinta. Zuciyarsa har tashi ta fara yi saboda mutum ne shi mai tsananin’kyankyami da tsafta har da ta siyarwa. Runtse idonsa yayi kawai ba ya ma son sake kallon wannan kwamacalar. Ya bud’e kujerarsa wata karama da ya shigo da ita daga motarsa ya zauna. Sai a lokacin dada ta kula dashi duk da’kamshinsa ya sanar da duk ahalin gidan zuwansa’kamshin turarensa na amouage interlude 53 ya karad’e gidan sanye yake cikin black jeans da white long sleeve shirt ta Ralph lauren polo ya gyara glass dinsa da yayiwa idonsa kyau ba’a ganin ‘kwayar idonsa gashin kansa a kwance luf, murya a dashe yake gaida lamid’o da dada. Dada cikin mamakin halinsa na ko da yaushe tace” jakadan turawa yaushe ka bayyana a ‘kasar.” Cije lips dinsa yayi bai bata amsa ba sai ammar kaninsa ne yace “ yau kwanansa biyu “ dada ta kyabe fuska “ ai dama shi ba zaka ganshi ba Sai a dangin uwarsa saboda sun fimu farcen susa ammar kaine namu Allah yayi maka albarka yo wannan dama fuska kamar hadarin kaji wake maraba dashi ga shegen tsurfar tsaftar tsiya da ‘kakale aikin banza ko mu har a gaya mana tsafta “ . Ammar dariya kawai yake shi kuwa imran ya’kare tsuke fuska shi yasa sam baya son zuwa gurin tsohuwar nan mai shegiyar maganar tsiya. Lamid’o ya gyara murya kafin ya dubi Aysha “ ina jinki ayshatu bamu labarin “ ai kuwa ta sake gyara zama ta jingina kanta a jikin mommah ganinta take kamar innaji wallahi. Mommahn ta kara janta jikinta duk da warin da bakinta da jikinta yake bata’kayamaceta ba tana sauraran yarda take basu labari tiryan-tiryan.

Kafin ta gama bada labarin gaba d’aya gurin kowa kuka yake har ammar banda imran da ya d’auke kai gaba d’aya haushin yarinyar yake ji ga shegen surutu kamar kanya ba mamaki ma ‘karya take ba jininsu bace idan banda haka mai ya had’a su da bararoji. Yanzu haka had’a baki a kayi da ita tazo ta cucesu mutanen duniya da basu da gaskiya musamman su d’in da an sansu a gari . “ ya kamata ku bincika kafin ku tabbatar da gaskiyarta “ hakan kawai yace yaja baki yayi shiru kamar bashi yayi magana. Momma ta d’ago a fusace zata yi magana lamid’o ya d’aga mata hannu ita kuwa shatu wata harara ta zuba masa da ya sashi ware ido yana kallonta cikin mamakin rainin da ta nuna masa sai kuma yayi Kwafa. Dada ta gyara zama “ yo saboda Allah ai gaskiya bature ya fad’a nima fa mamaki nakeyi ace wannan bararojin jininmu ce to ka fad’a ace ina ka fito don dai mune masu kalan dangi sai kuma mu had’a jini da bararo “ mommah idan ranta yayi dubu ya ‘baci ta kalli dadan kafin taja’kafar shatu ta nunawa dadar “ duk wanda ya san yar uwata maryama ya san wannan copyn kafarta ne da hannunta dada ki daina daka ta imran da shegen halinsa dinnan na bin kwakwkwafi a ina yasan maryama balle ya tantance jininta maryama da ta bar gida yana shekara guda duk’kaunar da maryama ta nuna maka ban mance da ita ba.” Imran ya ta’be baki kawai ita kuwa shatu zaro hotuna tayi ta mikawa mommah da takardar da innaji ta bata tace ta basu. Mommah na gani ta mikawa lamid’o “ Baba kalla kaga wallahi rubutun maryama ne wannan tabbas “ lamid’o ya kar’ba ya kuma shaida tabbas rubutun d’iyarsa ne.

Sun ci sun sha akayiwa maryama addua sannan su lamid’o mazauna abuja suka fara haramar tafiya. Mama tace shatu tayi wanka ta canja kaya kafin su wuce shatu ta had’e rai sam bata san zancen wanka. Mommah ce tace” haba mama na zata zaki bar min ita mu koma kano tare musamman ganin bani da y’a mace ashe maryama ce zata haifa min” mama ta girgiza kai imran yana zaune a gefe yana adduar kada Allah yasa mama ta amine banda rigimar mommah ya zata kai musu bararo gida……😂😂😂😂 To fa!
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387

ELEGANT ONLINE WRITERS……

-5….

Momma ta sake gyara murya cikin kwantar da kai ta furta “ Don Allah mama ki bar min ita kinga ke kina da wasu y’an matan ga hafsa ga nahnah ni kuwa Allah bai bani haihuwar d’iya mace haihuwar ma daga ‘ya’ya biyun ba saketa nayi ba.” Mama ta girgiza kai “ Gaskiyar magana addarsu ba zan iya ba su wadancan da kike magana ina na gansu kun kwashe kun kai can uwa duniyar turkey karatu, yanzu kuwa ita zan dinga gani kamar maryama da na rasa “. Dada taja tsaki “ kaji min wani zancen shirme Idan da wanda ya dace ya ri’ke wannan ‘ya ai dijama ce yo fisabilillahi tana da wata uwar ne bayan ita a duniya ai itace take da iko da yarinyar nan ba ke ba daga kawai kin haifi uwarta, don haka na zartar da hukunci dijama ki tafi da ita ke kad’ai zaki iya da wannan bararojin mai ido a tsakar ka ko samarinki sa ladabtar da ita musamman wancan miskilin kafi mahaukaci ban haushi da idanunsa kad’ai sun isa hukunta ‘yar banza idan ta’kamarta ido ai gidan ta tarar.” Wani kallo shatu ta watsa mata a zuciyarta tace “ sai nayi maganin wannan tsohuwar kafin ta sheka barzahu “. Liman da lamid’o murmushi kawai suke ganin yarda mama ta had’a rai alamar sam hukuncin dada baiyi mata ba sai dai ba yarda za tayi da ita. Momma kuwa sai murmushi take tana sake jan shatu a jikinta. Daga gefe kuwa imran ne yake ta watso mata harara kamar ya sha’keta ta mutu tabbas banda an kusa bikinsa zai bar ‘kasar da amaryarsa ‘yar abuja zubin london inji dada da barin’kasar zaiyi kafin a sake ganinsa kuwa sai an yara. Ya kalli agogo yana mi’kewa “Momma ya kamata muyi haramar komawa saboda akwai abinda dada ya sani a company ban kai ga hattamawa ba kuma kinga mota muka biyo “ Duk wannan dogon zancen yayi shine saboda baya so dada tace kwana za suyi yamma tayi. Dada ta zabga masa harara da ficificin idonta na tsoffi “ Ma’karyacin banza Ka dai ce ba zaka iya kwana anan ba saboda shegen gwalangwasonka kada kayi ubanka’karya salihin bawa dashi ko da yake shima ya zama d’an banza watansa nawa bai zo ya dubani ba ko don bani na haifo wanda ya haifi ubansa ba amma ko bakomai ai ubannasa aminin lamid’o ne, shikkenan dai Allah raka taki gona ban kuma ce Ka gaya masa ba bare kasa ya daina min aiken wata da ya saba ko bakomai ai d’an albarka ne tsiyarsa ta rashin zuriya ta bishi sahura dai taga takaici da jikanta baya son ziyara”. Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba har shatu idan Ka d’auke imran da ya sake kicin-kicin da fuska ya d’aureta tamau ya mayar da kud’in da yayi niyyar bawa mutanenta da ita kanta aljihu, yasa kai ya fice bayan yayiwa liman da lamid’o sallama. Dadah ta gyad’a kai “jarababbe umma ta gaida aisa gayyar na ayya ke dai dijama kin haifi ala’ka’kai.” Murmushi kawai tayi ta mi’ke tana ri’ke da hannun shatu ta furta “Allah dai ya shirya mana zuri’a bari mu wuce kada dare yayi don ma mugun gudu yake a motar “. “ wani irin gudu ki gaya masa ya tafi a hankali bana son shashanci “ lamid’o ya fada yana kallon babbar d’iyar tasa cike da kulawa ya san sosai take jin zafin rad’ad’in mutuwar nan “ kuma ki cire damuwa a ranki kada kije kiyi tunani har ciwonki ya tashi maryama addua take bu’kata yanzu, ita ta dace ko bakomai tayi mutuwar shahada tsakaninmu da ita addu’a dafatan muma mu cika da imani “ lamid’o ya sake fad’a yana kallon’yar tasa ba tare da dubi da hararar da dada take watsa masa ba “ Ba shakka zamani wato lamid’o a gabana kake lallashin ‘yarka ta fari kai Allah da ya tsinewa nasara da ya kawo boka har tayi sanadin rusa al’adarmu da dane ko inuwa d’aya ba zaka had’a da dan fari ba balle har zance ya shiga tsakaninku tur da wannan wayewa, ko da yake har gwara kai ba gani ba na tsaya ina magana da kai da iyayenan zasu dawo da sunyi tur da haihuwata kai ku tashi ku tafi kada wanda ya sake dawo min nan balle ku sake sakani rashin kunya wai da bakina nake kiran sunan lamid’o waliyazubillah duk da dai na uku ne kai amma wa ya san na farko da na biyun Allah na tuba tun kan ayi suna suka mutu ai dai kai ne dai na farkon….” gaba d’aya gurin dariya ake suka fice suna mata sallama Momma tace “ Danger number one “

Ta mudubin motar ya hango fitowarsu da sauri ya waro sexy eyes ganin da yarinyar aka fito mai hakan yake nufi wai wannan’yar dajin motarsa zata shiga kai ina impossible ai da sake.
Ya fito daga motar daidai lokacin’karasowarsu mommah tace “bud’e motar mana imran, yamma fa tayi “ ya ‘bata fuska sosai “ Momma yamma fa tayi kuma gaskiya gudu zanyi sosai why not ku kwana anan idan yaso gobe nayi muku booking flight ku taho.” Momma ta watsa masa wani kallo ta san sarai nufinsa Aysha ce baya son ta shiga motar bai kuwa isa ba zata nuna masa ita ta haifeshi “ sannu ubana to yau d’in za mu tafi idan yaso’karewar gudu ka mayar da motar taka jirgi bud’e mana malam “ fuska a d’aure tamau tayi maganar tana mamakin halayen imran da sam bata san inda ya kwaso su ba. Jiki a salu’be ya bud’e motar had’e da mi’kawa Ammar key d’in “ kuje I will manage ko a hotel ne by morning insha Allah zan bi flight na taho and make sure kuna zuwa ka kira car wash su d’au motar nan every thing na cikinta ya zama clean.” Ammar ya kar’bi key had’e da bud’e driver seat momma ta waro ido tace “ yana ina shi “ Ammar yaja numfashi don yasan fad’an momma shi kuma yana son d’an uwansa baya son’bacin ransa “ Momma zai zo ya tuna akwai yana da abinda zaiyi a bauchi “. Gani yayi kawai momman ta fita ware ido tayi tana kallon imran jingine jikin bishiyar’kofar gidan kallo da take masa ne yasa shi rusinar da idanunsa baya jurewa sun saba tun suna yara da idon take hukunta su, hanya kawai ta
nuna masa ta shige. Ransa a ‘bace ya bita tabbas ya san dai kafin ya isa gida wani ciwon sai ya kamashi.

Shima Ammar d’in kallo d’aya tayi masa ya fito ya koma d’aya seat d’in zuciyarsa fal da tausayin d’an uwansa don ya san kam yau sai ta Allah.

A salu’be ya tada motar bayan yayi adduar tafiya الحمدلله الذي سخر لنا… zuwa Karshe ya kuma ware a .c don ya kore masa warin jikinta da dum da motar tayi har da su fess turaruka. Momma tana kallonsa tana’bata rai cikin’kyamar banzar d’abi’arsa. Shatu kuwa kwafa tayi don sarai ta san ma’anarsa ta hakan wato kyamarta ma yake yi ai kuwa za tayi maganinsa kafin ta bar motar, ba mamaki ma bayan fitsari har kashi sai tayi a motar….😂😂.

Wani irin gudu yake shararawa duk a tsorace suke a motar ganin yarda yake mommah kuwa ta’ki magana sai addu’a da take a zuciyarta. Shatu kwance take luf a cinyar mommah wani barci ne yake fusgarta, cikin hukuncin ubangiji kuwa cikinta ya fara murd’awa ta daddage ta saki wata tusa da ta d’umame motar gaba d’aya Allah ne ya kiyaye saura’kiris ya saki sitiyarin motar yaja wani wawan burki, ammar ya dinga’kok’arin’kinshe dariyar da ke cikinsa amma ina sai da ta bayyana a guje ya fice tuni ya fara kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana aikin jera masa sannu. Momma kuwa duk da tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu sai dariya take yi tana’karawa momma tace “ wallahi shatu idan ya kamaki ba ruwana “ “ yo mommah ba k’yamata yake ba saura gudawa ma “ Mommah ta waro ido “ kada ki fara shatu idan ba so kike ya kashemu a titi ba kina ganin wawan burkin da ya sha Ba don Allah ya kiyaye Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu.” Shatu ta zaro ido “ momma mutuwa kuma a yanzun da zan fara jin dad’in rayuwa aradu ma ki daina wagga zance yo tunda nake ban ta’ba tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta’ ba ganinsa ba sai yau amalanke muke shiga garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya Na shigo aradu dana shiga nan na zata aljannah nake “ mommah ta girgiza kai “To kada ki sake abinda zai zubar damu a titi motoci su take mu mutu.” Ta d’aga kai. Ya huta sosai kafin yace “ Ammar jeka Kai bud’e glasses d’in motar ventilation ya shiga ka fesa air freshners tabbas Ba mamaki mommah ta d’auko ajalina “ Ammar ya d’an shafa bayansa “ bros ba zaka mutu ba just because of her sai kwananka ya ‘kare Ka dinga daurewa pls mommah bata jin dad’i the way she looked at you ka dinga controlling temper Dinka” hannu ya d’aga masa “ jeka kayi abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi muna zuwa gida I will pack everything nawa na tare “ Ammar ya zaro ido “ saura fa 4 months bikin ya zaka tare yanzu “ Imran tsaki yayi idan ban tare ba so kake na mutu ko?” Ammar ya juya yana’kunshe dariyarsa ya gama duk abinda ya sashi sannan ya dawo yana kallon yarda yake mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman “ Bros mu tafi kada dare yayi “ mikewa kawai yayi ya mi’ka masa key d’in “ muje kayi driving I can’t do it “

Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta saki baki sai barci take har da munshari ya sauke duk glasses d’in iska Na shiga motar a zuciyarsa yace “ Gwara a tafi haka “ momma dake kallonsa ta ta’be baki “ zan baka mamaki imran kada Ka shiga hankalinka “.

Idan ba’a commnts zan dakatar da book d’innan…..
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387

-6

ELEGANT ONLINE WRITERS

Ammar cikin nutsuwa yake driving har suka isa cikin garin kano’karfe 8:00 dai-dai, shatu lokacin har fitsari ta janga’ba a kujerar ba tare da sanin mommah ba.

A unguwar railway su kayi parking bakin wani tangamemen gida gari guda, da tafkeken gate, gani tayi kawai gate din ya zuge ba tare da tasan wanda ya zugeshi ba.Automatic gate ne. Ammar yayi packing a packing space. Momma ta bud’e ‘kofar had’e da jan hannun shatu a hankali ta waro ido ganin gurin da lema murya ‘kasa-k’asa tace “ shatu fitsari kika yi?” Shatu ta d’an ta’be baki “ To mommah fitsarin ne ai ya matseni kuma ina cewa zanyi zai fara masifa “. Momma tayi saurin rufe mata baki don kada imran da ya fice da sauri yaji “Muje kafin ya ankare “ da sauri shatu ta fita daga motar ammar yayi dariya yana tunanin yarda za’ayi da cakwakiyar’yar mommah da yayansa, yasan dai kwarai za’a buga show.

Suna shiga tangamemen falon kamshi ya doki hancin shatu ga sanyin A.c ta lumshe ido had’e da runtse ido tana bud’ewa tabbas dai da a mafarki taga wannan gidan to tabbas zata ce aljanna tayi mafarki da ita. Momma ta ri’ke mata hannunta ta kaita’kofar wani sashe suna shiga ta kaita wani d’aki kusa da nata “ daga yau ga d’akin Ayshata muje in nuna miki komai a toilet kiyi wanka ko da yake wannan wankan na yau yafi ‘karfinki da kaina zan miki da nace ma in kaiki saloon to bana so su fara ganin wannan daud’ar kannaki jira ni anan am coming.” Da sauri ta fita daga d’akin shatu ta sake ware ido tana kallon gadon yanzu wannan d’akina ne gado na da sauri tayi tsalle a gadon tana tintsira dariya “ ahe dai ina da gata muke zaune can a dajin Allah aradu innaji ta kwari kanta cabd’i”

Shigowar mommah yasa tayi shiru momma ta shige toilet ta zube kayan da yake hannunta duk mayukan wanke kaine da combs dama toilet din akwai dryer. Shatu ta fara’bata rai sam bata son a ta’ba mata kai da dai mommah zata gane da ta kyaleta. Momma ta zare du’kun’kunennan mayafin nata ta zaunar da ita bakin jaucuzi ta fara kunce tufkekken gashin kanta mommah tayi mamakin ganin tumulin gashin ta ji’kashi ta saka shampoo ta barshi for a minutes sannan ta fara had’a ruwan da zata dirje daud’ar Jikinta.
Sosai ta wanke kan sai sheki yake wajen wanka ne shatu Ta fara’boye-‘boyen jiki mommah Ta harareta “ zaki tsaya ko sai na ‘bata miki rai ke da ko irgar dangi baki fara ba to koma kin fara ni ba uwarki bace “. Shatu Ta d’an sunkiyar da kai mommah Ta saki murmushi “ Ashe kina da kunya.” Tas shatu Ta fito duk da dai sai a hankali zata baje amma ko bakomai anfi baya.

Fitowarta ne yasa momma ta tsaya domin ba kayan da zata bata tasa tsaki tayi tace “zauna nan ina zuwa bari na aika ammar ya siyo miki ready made kafin da safe mu shiga kasuwa “.

Tana fitowa babban falo ba taga ammar ba sai imran da yake zaune yayi wanka da fara jallabiya tas a jikinta mai gajeran hannu a jikinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga mutum mai mutu’kar tsafta. Sai baza’kamshin turare yake yunwa ce take cinsa ya aika ammar yayi musu take away don baiga alamar masu aikin sunyi girki ba, may be basu zata zasu dawo ba.” ina Ammar?” Momma Ta fad’a tana tsatstsare sa da ido , Imran murya can’kasa yace “ Na aike shi eatery samo abinci.” “ sai ka tashi kai na aikeka samowa Aysha kayan sawa ba tazo da kaya ba “ ta fad’a tana juyawa ba tare da Ta lura da waro idon da yayi ba yana ji kamar ya rusa ihu ganin zata shige yace “ kud’in fa?” Ba tare da Ta juyo ba tace “ ka siya da naka “ dunkule hannu yayi ya daki d’aya cikin d’aya kamar ya tashi sama kuma ya juya da sauri ya fice daga cikin gida.

Da yaje ma rasa mai zai d’auka yayi ya d’auko mata riga da wando Na maza kawai bayan ya kintata tsahonta yaga ba zata zarta hakan ba. yunwa yake ji sosai amma mommah Ta sashi zuwa siyawa wannan bararojin kaya.

A falo ya ajiye kayan ya nunawa Ammar “ mikawa mommah “ ya zauna a dinning ya fara cin abincin” mintuna kad’an mommah da ‘yarta suka fito Ta saka riga da wando duk da Na maza ne sai sukayi mata kyau, mommah Ta gyara mata kai an tsaga an raba biyu, jelar gashin Ta sauka har dantsen hannunta gashi mai yawa masha Allah sai ‘kamshi take kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai ya cigaba da cin abincinsa momma taja kujera tace “zauna “ Ta zauna tana hararar naman da yake ci tsoronta Allah kada ya cinye naman hakan yasa ta shiga tunanin yarda zata koreshi daga wajen ta kuwa daddage ta saki attishawa sai kuwa ga majina ta biyo hancinta da sauri ya furzo abincin dake bakinsa ya mi’ke da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa na tunzirashi yayi mata dan banzan duka kawai. Ita kuwa dariya Ta fara babbakawa “ Nagode Allah yo mommah da fa cinye naman zaiyi kaf da banyi haka ba “ mommah duk da dariyar da take cinta ta gintse tace “ baki kyauta ba kings yanzu kin hanashi cin abincin Ba kyau kada ki sake Ammar bishi da abincin d’aki”. Ammar ya mi’ke yana murmushi sosai yarinyar take burgeshi shi kam sam bata damuwa sha’aninta take zubawa.

A parlornsu ya ganshi a zaune ya dafe kansa sosai tausayinsa ya kamashi ya ‘karasa da abincin yana dafa bayansa Bros sorry don Allah ga abincin momma tace a kawo maka “ zubawa plate din ido yayi yana saurin ja baya gani yake zai hango majinar a cikin abincin murya can ‘kasa yace “ ‘dauki Ka tafi dashi ba zan ci ba ta had’a Ta cinye kana tunanin yau zan iya cin wani abin ko mai na kai bakina sai na tuna ‘kazamar yarinyar nan bitch “ ya mi’ke ya shige bed room direct toilet ya shige ya sakarwa kansa shower.so yake yaji zuciyarsa Ta daina’kuna.

Yana dawo da abincin mommah Ta kalleshi “ baya ci ne?” Ammar a sanyaye ya d’aga kai yaja kunnen shatu dake zaune “ if you try it again Allah sai Na zaneki mommah kija mata kunne “. Narai narai tayi da idonta “ To ni ina ruwa na kawai atishawace fa tazo ya zanyi da ita to “ “ Excusing kanki za kiyi ki fita kiyi haka ake yi wai ke baki da manner ne?” Kuka Ta saka “ Ni ka daina min wannan maganar ban iyata ba idan bakwa san zama na kuma kawai kuce na tafi. Ya bud’e baki zai yi magana mommah tace “ Ammar ya isa ai da gaskiyarta to ya zatayi da atishawa fisabilillahi ni fa kada wanda ya ‘kara takura mata duk wanda Ba zai iya zama ba shi ya bar gidan. Ammar ya bud’e ido “Mommah……” “kada kace komai “ ita kuwa shatu plates d’in imran taja ta fara cin naman cewa takeyi “ Yo ai yayiwa kansa ni kuwa gaba Ta kaini……” Ammar murmushi yayi ya wuce yana furta “ Allah ya shirya “.
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-7

ELEGANT ONLINE WRITERS……….

Momma murmushi Ta sake saki ganin yarda shatu take cin abincin hannu baka hannu kwarya “ ci a hankali Aysha ba inda abincin nan zaije gashi nan ma idan baki ‘koshi ba ki ‘kara saki jikinki nan d’in gidanku ne kamar yarda kowa yake ji gidan ubansa ne.” Ammar’kunshe dariyarsa yayi ganin yarda momma ta hau da yawa yasa ya koma falon ya kunna t.v . Ai kuwa shatu a zabure ta mi’ke ta isa wajen tana sid’e hannunta “ Ikon Allah yau gani ga irin akwatin kallon d’an gidan mai gari da aka kaiwa amaryrsa da ya auro a niamey, aradu wannan tayi gomanta.” Sai kuma ta fara zabura tana tsalle ganin yarda mutane ke rawa a cikin t.v d’in ta ‘karasa tana shafawa Ammar mai zaiyi idan ba dariya ba. Momma da take gefe ta dafe kai anya shatu zata gyaru ta dawo kan saiti kamar yarda take son ta ta lura’kauyancine kawai a kanta zuciyar momma ta shiga tunani. Sai kuma ta mi’ke ganin yarda ammar yake tuntsira dariya tana zuwa ta figi hannunta “ wuce muje shashasha kina zaune yana ta tuntsira miki dariya ga sabon kamu ya samu wallahi Ammar ka kiyayeni ina lura da take-takenka ta wancan ce ta fito fili shi kyamarta take kai kuwa mahaukaciya ka d’auketa to ahir ka kiyayeni “Ammar ya guntse bakinsa “ Allah ya baki ha’kuri momma amma fa wallahi dole Na samu comedy a gidan ji fa yarda take acting wallahi illiteracy d’inta yayi yawa za’a sha fama “ “ ubanka ne zai sha famar ko ni? Ina ruwanku da ita to duk zaku ci ubanku da ni kuke zancen ashe ta imran ce ta fito fili “ Ta sake kwafa suka shige part d’inta hannunta ri’ke dana shatu.

Suna shiga d’aki shatu ciki ya kad’a to an ci abinda ciki bai saba ci ba da sauri Ta kalli mommah tana yamutsa fuska. Momma Ta dubeta had’e da dafa kanta “ Me ya faru ki daina fushi ki rabu da su zan yi maganinsu ai da ni suke zancen” Shatu Ta fara matse-matse “ Ni fa mommah ba zancensu ya dameni ba yo ni ina ruwa na ai gaskiya Ammar ya fad’a. “ “ Au ni na damu kenan to meye ya dameki kike had’e-had’en fuska” “ Kahi nake ji “ Momma Ta zaro ido to “ kashin kike ji kike tsaye anan, anan zakiyi min kashin?” Da sauri taja hannunta wuce muje na nuna miki inda zakiyi don ba mamaki ma baki san toilet sit d’in birni ba” da sauri shatu ta bita ji take kamar Ta saki kashin suna shiga ta hau duba inda momma ta nuna mata shatu ta waro ido “ A wannan abin fari ‘kal dahi zanyi kahin “. Momma tsaki tayi kafin ta furta “ idan ba kiyi anan ba a bakina zaki yi ?“. Ta sake le’kawa “ Ruwa ne fa a ciki aradu ba zan zauna ba inje ruwa ya zu’keni ya tafi dani “ Momma Ta dafe kai tana kallon shatun cikin takaici “ kada fa ki sake kiyi min kashi a wando ki hau ba wani ruwa da zai tafi dake duk gidan da zaki a garinnan yawancin irin wannan d’inne sai dai idan kin daina kashin” “ To zan hau amma ki tsaya ni” “ In tsaya ki ki cika min ciki da warin kashi to ba dani ba ki hau in kin gama wannan zaki ciro kina danna nan ruwa zai zo kiyi tsarki shi kuma kashin ba barinsa zakiyi ba ki danna nan ruwa zai tafi dashi kin jini ai da kyau?” Shatu Ta d’aga tana d’ofana akan seat toilet din ta zauna. Momma ta saki ajiyar zuciya Ta ja mata ‘kofa ta fita zuwa nata d’akin a gaijye take tubus banda soyayyarta da maryama ba abinda zai kaita d’aukar shatu musamman ita da mijinta da suka tsarawa kansu rayuwar turai basa son hayaniya sam shi yasa sam basu damu da haihuwa ba sai gashi ta d’auko shatu wanda Ta san sai tayi bore kafin mijinta ya amince da zaman shatu a gidan. D’akinta ta shiga wanka kawai take bu’kata da nutsuwa.

Shatu anyi abin kai bayan ta gama tayi tsarkin ta mi’ke sannan ta danna inda akace zata kore kashin idan ta gama ai ko sai tayi tsalle ta koma can gefe tana kallon ruwan abin kuma sai ya bata dariya ta sake dannawa haka tayi- tayi kafin ta gaji ta fito a zuciyarta take fad’in “ wato hi kahin ma wani matsayi ne dashi na musamman a Gidannan cabd’i Allah ya kyauta “. Ganin momma bata d’akin Yasa ta fita tana bilayin nemanta . Ganin bata ganta ba a d’imauce Ta fara’kwala mata kira duk gidan yana amsa kuwwar muryarta.

Da sauri d’aukacin mutanen gidan har su Imran suka fito tunanin ko ba lafiya ba, abinka da ba’a saba hayaniya a gidan ba, dai- dai lokacin mai gidan shima ya bud’e ‘kofar part d’insa ya fito don bai dad’e da dawowa ba yaji tashin muryarta. Da kallo ya bisu ganin sunyi cirko-cirko suna kallonta. Had’e fuska tayi tana binsu Da kallo “ To wai lafiya naga kun saka ni tsakiya sai wani kallo na kuke.” Imran tsaki yayi ya juya ya shige part d’insu da ya san ma itace ba zai fito ba to barcin gajiya ya fara fisgarsa ya jiyo hayaniyarta kai mommah ta d’ebo musu damuwa.Ammar da ya lura da Dahdansu yayi saurin cewa “ welcome dahdah “ girgiza masa kai yayi fuska a had’e yace “ who is she?” Ammar ya mayar da kallonsa kan shatu da take fad’in “ Wannan sa ido da yawa yake uwa ta fa na kira baku ba” Ammar yayi saurin katseta “ ke are you mad kin san da wa kike magana “ “ kai ka san mai kace inace mad d’in d’an garinku sai kayi tayi min yaren birni so nawa zance maka bana so “ Ta fad’a tana ta’be baki . Cikin tsawa Babannasa yace “Ammar am asking you who is she I said?” Mommah ce Ta fito daga’bangarenta turus tayi ganin taron jama’ar gidan Ta mayar da idonta kan dahda “ Ai ban san ka shigo ba ina wanka.” Fuska a had’e yace “ Yayi kyau kai kuma amsa min tambayata wace shashashace wannan?” Mommah ta had’e fuska “ diyar tawa ce shashasha to ko baka santa ba ai bai kamata daga ganin ba’ko ka kira shi da shashasha ba er maryam ce sister ta wani abu ne?” Wani kallo ya bita dashi sai kuma ya hau step d’in da zai kaishi ‘bangarensa.” Almasifatu shi kuma wannan d’in waye da naga duk kun firgita da ganinsa “. Momma ta waro ido Allah ya taimaka ya shige bai ji ta ba Ammar ya watsa mata wani kallo “ ke ubannamu kike kira Almasifatu?” Cikin ‘ki’k’kifta ido tace “ Aradu ban san ubanka bane yo ai da ba zan kira shi da haka ba.” “ zagi na kika yi kenan ?” Cikin kufula Ammar ya fad’a. Momma Ta dafe kanta had’e da jan hannunsa “ Bafa zagin ka tayi ba Ammar sai kunyi ha’kuri da ita kafin ta goge” Ammar ya kad’a kai “ki daina bin bayanta fa mommah cewa fa tayi ubannaka?” “ To kayi hakuri mana haba su a garinsu ai ba zagi bane hakan “. Shigewa part d’insu kawai yayi yana nanata kalmar AlMASIFATU. Momma ranta had’e tace “ Maza wuce d’akinki kada Na sake ganin’kafarki a waje sai da safe nan gidan bama hayaniya mai gidan duka yake “ sum sum ta wuce . Momma Ta dubi masu aikinta biyu da suke kwana su kansu a ‘boye suke saboda mai gidan ya sha fad’a mata baya san shirgi, ‘ya’yansa kad’ai sun isheshi “ ku kuma mai kuke yi anan? Yawon d’aukar news ko?” Da sauri suka fice ita kuma Ta shige ciki sam bata san yau zai dawo ba ba abinda Ta tanadar masa. Kitchen d’in da yake part d’insa Ta shiga saboda tsantsaninsa komansa anan yake ita take masa komai bai yarda kowa yayi masa ba. don haka ma yayi kitchen a part d’insa saboda kar ma wata rana tayi gigin saka masu aiki yi masa wani abin. To ashe dai imran a can ya gado tsafta.

Sai da ta d’ora abincin sannan ta’karasa bed room d’insa . A zaune ta ganshi da news paper a hannunsa sallamar ma ciki-ciki ya amsa ba tare da ya d’ago ba “ Yalla’bai barka da dawowa ina ta magana kayi shiru wai me ya faru ne?” Ya d’ago fuska a cusgune “ Da izinin wa kika d’auko bagidajiyat yarinyar can to bari kiji in gaya miki I can’t tolerate this nonsense maza-maza gobe ki mayar da ita inda kika d’aukota ai kin san sarai bana son hayaniya yaran ‘yan uwana ma ban yarda na ri’ke ba balle wannan yaran da bata da respect don haka ki mayar da ita, saboda bana son haihuwa da yawa Na ‘ki ‘kara aure so ba wani abu da zai sani ri’keta………..”
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-8

ELEGANT ONLINE WRITERS………

Momma tagumi ta zuba tana kallon dahda “ Amma ka bari kaji er waye kafin ka fara fad’ar ba zaka ri’keta ba, er fa maryama ce maryama jinina da muka taso tare maryaman da na sha mama na bar mata, duk ba ma wannan ba bata raye wa kake so ya rike mata er ta wa take dashi idan bani ba.” Jikin dahda ne yayi sanyi “ maryama ta mutu?” Ya fad’a cikin taushin murya ba kamar yarda ya d’au zafi ba, innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, momma ta ja ajiyar zuciya kafin tace “ maryama ta mutu nima d’azu kira ya ruskeni daga katagum muka tafi a can muka samu ita wannan er tazo ita kuma take sanar damu mahaifiyrta ta mutu.” Allah ya gafarta mata Allah yasa ta huta amma ina mahaifinta?” Momma gyara zama cikin kasa da murya tace” shima Allah yayi masa rasuwa “ Tausayin shatu sosai ya kama Alhaji, ya
Hau girgiza kai yana jaddada lamarin girman ubangiji “ Allah ya gafarta musu Allah kuma ya bamu ikon sauke nauyin ri’kon maraya “. Farin ciki ya ratsa zuciyar mommah sai sannan hankalinta ya kwanta da har ya amsa zai ri’keta “ Nagode dear bari na kawo maka abincin” .

Ta fara zuba masa abincin ya dubeta “ kiyi ‘ko’kari sosai akan yarinyar nan ki koya mata tsafta uwa uba tarbiyya don sosai na lura bata da manner, insha Allah nima I will try my best naga na kula da lamarinta don kamar nauyinta ne Allah ya d’ora mana.” Insha Allah mommah kawai take fad’a zuciyarta cike da farin ciki a take a wajen ya tura mata kud’i a account ya umarceta da kashegari aje ayiwa shatu siyayya. Godiya ta sake masa ta mi’ke don fita shirin barci.

kwananta biyar da zuwa gidan amma har ta fara murjewa, jikinta yayi kyau masha Allah duk da haskenta bai fito gaba d’aya ba . Duk wani abin da bata sani ba mommah ta koyar da ita yarda za tayi amfani dashi a gidan.Ta fara kuma ‘ko’karin ganin ta daina rashin kunya duk da har zuwa lokacin da yarinta a tattare da ita.

Abubuwa da dama bata iya cinsu har a lokacin da zarar taci sai tayi aman su saboda rashin sabo sai dai son cin nama shan madara da milo kuwa har dana maza da kauri sosai take damawa ta shanye.Ammar tuni ya fara sakin jikinsa da ita kasancewar yanzu duk ta d’an zubar da rashin kunyar an samo mata malami da zai dinga koyar da ita.Imran ne baya shiga shirginta .

Yauma da wuri ta tashi, tayi saurin yin wanka da brush don kar mommah tayi mata fad’a gashi ne dai bata taje shi ba bata son gyaransa sam bata’ki kuma mommahn Ta aske shi ba kamar yarda tace.

Ganin su mommah tayi suna ta aiki a gidan ta fara tunanin ko mai zai faru ake ta wannan aikin Ta kuma lura zuciyar momma sam ba dad’i don komai a sanyaye take yinsa. Momma ta dubeta tana amsa gaisuwar da take mata cikin nutsuwa” yauwa my baby kin yi wanka maza kije kiyi break fast kizo d’aki ina son ganinki “. Amsawa tayi da sauri tana isa kan dinning , Tayi turus ganin imran a dinning d’in yana break idanunsa ya zuba mata, da sauri ta dur’kusa tana gaisheshi imran ya had’e fuska. “ ke bar nan wajen before I slap you “ kallon ‘kasa-‘kasa tayi masa “ To ba yunwa nake ji ba zaka ce na bar nan.” Harara ya watsa mata sai kuma ya cigaba da abinda yake kafin bakinsa ya furta “ Dirty Girl “ zama tayi ba tare da san abinda yace “ kin san mai nace miki?”kamar doluwa ta hau girgiza kai “ ‘kazama nace miki Alhamdulillah na kusa barin gidan sai kuci’kazantarku ku kad’ai “. Ba tayi masa magana illa kallon plate d’insa da tayi yana shirin kai tsokar nama ta miyar turmeric baki ta saki murmushi kafin tace “ Ga kanan’kazami kana cin miya kamar gudawa…..” Ai da sauri ya furzar da naman bakinsa yayi wajen sink shatu ta tuntsire da dariya a hankali ta furta “ ba’kin mugu in dai ina gidannan ka daina ci ka ‘koshi “ sosai ya kuskure bakinsa ya bita da wani kallo kafin ya wuce shatu ta ja plate taci abinci tayi nak “ Allah gaba ta kaini ba gashima har nayi’kiba ba gobe ma ka sake ce min’kazama Allah mhmmn sai kuma ta girgiza kai.”

Da kyar take nishi sai kuma ta tuna kiran da momma take mata da sauri ta shige sashen mommah a zaune ta ganta ta rakfa tagumi idonta har ja yayi. Jikinta a sanyaye ta ‘karasa ta zauna daf da ita “ Momma mai ya sameki?” Momma ta shafa kanta “ bakomai shatu anjima za’ayi ba’ki babar mai gidan nan zata zo don Allah don’t make any thing da za’a tafi dake a baki bana son kiyi rashin kunya ko wani abu kinji ki daina yawan fitowa kiyi tasa catoon a d’akin ki.” Shatu ta d’aga kai “ Tana da fad’a ne Mommah?” Shatu tace tana kallon ta , mommah ta girgiza kai “ Ba fad’a kad’ai ba zata iya sa daga ni har ke mai gidan nan ya koremu “ “ cabd’i muje ina duk wannan naman mu barhi “ Momma tayi tsaki “ ke kike ta nama Aysha Idan nama ne duk mai sau’ki ne gidanmu ma akwai ina son mijina bana son ta raba ni dashi “
“ Au to hi dahdan sai ya rabu dake “ momma ta d’aka mata duka “ sau nawa na hanaki cewa hi da he a maganarki ? Ba abinda zaki fahimta yanzu sai nan gaba zaki san and wacece hajja tashi kije Na gaya miki ba ruwanki da kowa, kuma ki dinga dur’kusawa har ‘kasa kina gaisuwa kin ji?” Shatu ta girgiza kai kawai daidai lokacin da suka ji dirin motoci a harabar gidan.

Da sauri mommah ta mi’ke cikin rawar jiki ta fice, shatu ta bita da kallo kafin ta fita taga wacece wannan da mommah bata son’bacin ranta. Babban falon ta fita duk mutanen gidan suna zaune gefe d’aya mommah ce dur’kushe tana gaida hajja murya a cunkushe hajjan take amsawa tana yatsine fuska. Ganin yarda su imran suka gurfana suna gaisheta yasa ita ma shatu ta’karasa ta dur’kusa tana gaishe su. Hajja ta zuba mata manyan idonta “ ita kuma wannan daga ina? Sabuwar mai aiki kuka yi da har kuma ta sake ta za’ke take shiga cikin ahalin gida, Ba shakka to mi’ke daga nan kafin Na kai miki mangari.” Shatu ta d’ago ido zata aikata halinnata sai kuma suka had’a ido da mommah sum sum ta mi’ke ta shige “ ina magana an min banza ga a tsohuwar banza ko nace wacece wannan deejah?” Murya can ‘kasa mommah tace “ d’iyar maryama ce’kanwata to ta rasu shine na d’aukota “. “ shine aka ajiyeta ba tare da izini na ba ko? Ni da gidan d’ana ga a baitil mali an samu wacece ma maryama a zuri’arku?” Momma ta sake sunkuyar da kai “ ‘kanwata data bar gida da dadewa “. Hajja salati tasa “ kice min’kanwarki da ta tafi karuwanci shine kika d’auko shegiyar’yarta kika cud’anya cikin tsaftatacciyar zuri’ata, zuriar da aka Haifa ta sunnar manzon Allah to kuwa ba zai yiwu ba kai imran kira min ubanka a waya.” Gaba d’aya suja juya jin takun tafiyar dahda murya a cunkushe ya shigo, shatu da take ra’be a ‘kofa ta shige d’aki wai yau ita ake kira da shegiya ai kuwa tayi al’kawarin sai ta sa matar nan kuka.

Dahda ya dur’kusa a gefenta. Fuskarsa yana d’an sakin murmushi yace “ Hajja ashe kin shigo ? Barka da zuwa ta amsa tana girgiza’kafa “ kai ka bawa shegiya lasisin zama a gidanka ?” Cikin rashin fahimtar zancennata yace “ wacece shegiya?” Kwafa tayi “ baka santa ba kenan d’iyar gantalalliyar’kanwarta maryam da ta bar gida saboda ubanta ya za’ba mata miji ta gwammace ta tafi yawan dadiro.” “ Hajja wanda ya mutu fa ya mutu mai yasa zaki dinga’bata mata gawa ba kuma yawon dadiro ta tafi aure tayi ta haifi er ta don haka wannan zancen don Allah ki daina fad’arsa “. Dada ya fad’a fuskarsa a had’e. Hajja ta sake tsuke fuska “ Ba shakka ubana to ai sai ka bari sai na zama sokuwar uwa sannan in dinga bari kana fad’a ina fad’a shashasha kawai wanda mace ta riga ta gama dashi shi yasa wannan karan da shiri na nazo kaga can to matarka ce ni na bada sadaki aka auro maka ita tunda na bika na bika ka’ki amincewa da auren shi yasa ni na auro maka ita kuma wallahi kace baka amince ba sai dai ka sake wata uwar.” Mommah wani fad’uwar gaba ne ya sameta ganin wacce aka nuna aka ce kishiyarta ce y’ar’kanwar hajjance uwa d’aya uba d’aya da ta dad’e tana zawarci kuma y’arta imran zai aura sannan ace itace kishiyarta tabbas akwai ‘kura. Dahda cikin ‘bacin rai yake kallon ta tana zaune fuskarta sai murumushi take tana rausayar da kai.

Dahda mi’kewa yayi kawai yayi hanyar fita. Hajja ta sake tunzira “ Ba shakka sallamamme ai ban gama magana ba kake shirin fita wannan yarinyar na bada awa ashirin da hud’u t bar gidannan ‘bangaren da nake sauka anan amarya zata tare yanzu ne na san kayi aure da ka auri’yar dangi, Auren imran kuma na saka rana na da wata biyu, ba’kin ciki ya kasheki dijah dama ai na gaya miki ina tafe ga dai abin takaici kishiyarki kuma surukar d’anki sai ki had’iyi zuciya ki mutu, ku matan yanzu baku da buri irin ku mallakewa mutum d’a . Momma mi’kewa kawai tayi
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-9

ELEGANT ONLINE WRITERS……..

Tana shiga d’akinta hawaye ya fara zubo mata, Tunani take sosai a zuciyarta so take ta hango laifin da takewa dangin mijinta suka tsaneta har haka, mai tayi musu? Shine abinda take tunani a zuciyarta, har ga Allah bata nufin kowa da sharri rayuwarta take free ba tare da kowa a ranta ba amma sun bi sun tsaneta.

A gefen gadon ta zauna, shatu data gefe jikinta yayi sanyi ganin mommah na hawaye, taji duk duniya ta tsani waccan Almasifatun tsohuwar a hankali ta zauna jikin mommah itama ta saki nata kukayi. Momma dafa kanta kawai tayi alamar rarrashi. Daidai lokacin Ammar da Imran suka shigo d’akin jikinsu a sanyaye suka zauna kan cushion chair d’in da take gefe fuskarsu sam ba walwala musamman ammar, sam baya son abinda zai saka mahaifiyarsa a ‘bacin rai. Ammar yayi’kasa da muryarsa “ Momma kiyi hakuri komai lokacine, kuma wata rana sai labari.” Girgiza kai tayi “ Na kai ma’kura Ammar iya ha’kurin da zan iya kenan kun san iya lokacin da nake’kunsar ba’kin cikin hajja tun ranar da na kwana d’aya a gidannan duk a dalilin mahaifinku bai auri za’binta ba, kuma ba kowa bace za’bin nata sai wannan matar da sai da ta san yarda tayi yanzu ta auro masa ita, to lamarin ya isa zan tattara in tafi amma ba zan zauna ba’kin ciki ya kashe ni ba just like bani da iyaye, gidan ubanku ne ku zauna, bare shi gashi nan zasu aura masa wacce suke so, tun yaushe nake jan kunmensa ya rabu da yarinyarnan ya’ki, saboda kawai kyanta da kwalliyarsa yana rud’arta to yaje ya aureta amma ka san Allah ba hannuna a cikin lamarin aurenka, wanda dama don a gasa min ba’kin ciki aka’kir’kiresa.”
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta mi’ke ta shiga had’a kayanta, Ammar ya ri’ke akwatin “ please mommah kada kiyi abinda baki ta’ba yi ba da yarintarki balle da girmanki please ki rabu dasu,ko mu kad’ai zamu iya share miki hawaye, kuma wallahi at this point sunyi na’karshe, kaima yaya Imran don Allah kayi hakuri ka kyale musu’yarsu ko don kwanciyar hankalin Mommah “ wani kallo Imran ya zuba masa “ meye laifin shaheeda da zan rabu da ita, ko kana tunanin a bayansu take? To kullum maganar ta tana jin haushin abinda suke wa mommah.” Wani kallo momma ta wurga masa sai kuma tayi kwafa “ mhmn ba dai shaheeda bace Imran ka aureta ban hanaka ba, tunda lokacin da na hanakan ai baka ji ba, sai dai bahaushe yace wanda bai ji bari ba…. kai kuma Ammar kada ka sake masa magana idan ta nice ma barin gidan zanyi ba sai na zauna zanga kayan takaici ba .” Imran shiru yayi yana sake zabgawa Ammar harara sai kuma yayi kwafa ya fice. Mommah tabi bayansa da kallo tana masa addu’ar shiriya a zuciyarta ji take kamar ta rusa kuka gaba d’aya sun cusawa Imran soyayyar shaheeda ta ‘karfi da yaji da yaudara da komai. “ ka rabu dashi Ammar tsakaninka dashi Addu’a ya riga yayi nisa a soyayyar shaheeda ba zai ta’ba ganin aibunta ba.” Ammar ji yayi ransa ya sake’baci idan dai da shine ko da gold aka’kera shahida sai ya ha’kura aurenta balle shi dai ban da kyan fuska bai ga mai ya gani tare da shahidan ba tana tafiya kamar sillan kara,sai iyayi da kwainane. Shatu dai tana gefe tana kallon ikon Allah, takaicin Imran kuwa ya gama cikata. Har so take taga wacece wannan da ya fi sonta akan’bacin ran mahaifiyarsa. Ammar ya cigaba da bawa mommah ha’kuri ganin ta’ki ha’kura yasa ya fita wajen bayan ya danna kiran hajiya mama mahaifiyar mommah a cikin wayarsa. Basu san me yace ba sun ga dai ya dawo da sauri ya mi’kawa mommahn wayar, ya wurga masa harara don ta san’kara ya kai ta wajen hajiya maman. Tana sallama hajiya mama ta shiga fad’a tuni mommah ta sa kuka ta fara bata labari. Hajiya mama cikin zafi ta katseta “ kishiya saboda kishiya zaki bar gidanki akan ki aka fara kishiya?da girman ki da komai kike neman zubar da mutuncin ki to ahir ki kiyayeni kina shirin auren da’kanne da ‘ya’ya, nan gaba su kuma idan sunyi wa zai musu fad’a? To ki saurareni da kyau ki mayar da akwatinnan kafin ma su gani su ji dad’i gobe insha Allah’kannenki sun zo hutu daga turkey zasu zo kanon suyi miki hutu hisham ma dama yana ta son zuwa wajen mutuminsa Ammar. Ina shatu?” Momma ta mi’kawa shatu wayar “ maza ki masa hajia mama ce “. Shatu ta kar’bi wayar cikin rashin sabo ta fara gaisheta “ lafiya lau shatu ya ba’kunta? Gobe zaki ga aunties d’inki suna ta son ganinki.” Murmushi shatu kawai tayi saboda ba ‘yan hayaniyar a kanta. Hajiya mama ta sake cewa “ Ba dai matsala dai ko?” Shatu ta girgiza kai “ Bakomai mama” To masha Allah sai kin ga sa’ko “ hajiya mama ta fad’a tana kshe wayar. A hankali shatu ta mi’ka wa Ammar waya, ganin yarda jikinta yayi sanyi yasa Ammar ya shiga janta da wasa” shatun mommah’kalau kuwa yau na ganki jiki ya mutu? Ko don ki had’u da Babarki a masifa “ harararsa shatu tayi “ Ai wallahi ba tsoronta naji ba, don dai kawai mommah ta hana ne amma wallahi da tuni ta d’ebi kashinta a hannu yo Allah na tuba wannan ‘karamar alhakin, ka san Allah da ‘kauyenmu ne yau sai na saka yara sun mata kid’an Atire.” Ammar mai zaiyi banda dariya mommah kuwa bud’e ido tayi tana kallon shatu yarda take yi da baki “ To shatu ba ‘kauyenku bane kuma anan idan kayi wa wanda ya girme ka rashin kunya kulleka ake a gidan yara don haka be careful.” Ammar ya fad’a fuskarsa d’auke da alamar tsoratarwa. Shatu ta kya’be baki “ Ai in dai ba kayi a fili ba sai mutum yayi ta bayan fage yarda za ‘a gane ba.” Ammar girgiza kai kawai yayi yace “Allah ya shiryeki shatu.” “ Tashi maza kije kiyi sallah Ayshata ai Na san kina jin maganata ba zaki jawo min abin fad’a ba “.murmushi tayi tana mi’kewa dad’in yabon da momma tayi mata da sauri ta shige toilet ta bar momma da ta zuba tagumi tunani yyi mata katutu.

Dahda da daddare da kansa ya shigo d’akin mommah ganin ko nemansa ba tayi ba. A zaune ya sameta kan sallaya da alama lazimi takeyi, jikinsa a sanyaye yake dubanta yana son matarsa shi kad’ai kuma ya san irin son da yake mata, ba don komai ba sai don yarda bata tsallake umarninsa kuma iya iyawarta take kyautata masa ba ta son ‘bacin ransa sam.
Tana ganinsa ta d’an d’auke kai idanunta yana kawo hawaye. A gefenta ya zauna had’e da ri’ko hannunta tayi’ko’karin zamewa ya matse hannun murya a ‘kasa yace”Deejah yau mantawa aka yi da abincinka?” Wani kallo tayi masa kafin hawayen idonta su zubo. Hawayen ya dinga bi da ido “ kukan na menene?” Murya can’kasa tace “ abincinka yana wajen amaryarka” fuska ya sake tamkewa kafin yace “ wace irin magana ce wannan? Kema kin san sarai ba da amincewata aka yi aurennan ba, to me yasa zaki damu kanki yarda ta shigo haka zata koma, bani da tsarin ajiye mata biyu a gidana, ba ra’ayina bane tashi muje ki bani abinci kada ki sake’bata min rai” Ya jata ya mi’kar tsaye suka fita. Hanyar part d’insa direct suka nufa. Dai-Dai lokacin hafsa’yar hajjan ta ganosu itace auta a d’akinsu da sauri taje ta sanar da hajjan. Hajja kuwa tayi saurin fitowa fad’i take muje ba dani za’a yi wannan iskancin ba muje da kaina in kai masa amaryar in kuma nuna masa ni Na haifeshi ba shi ya haifeni ba…

A bakin ‘kofar part d’in nasa ta tsaya tana buga ‘kofar da ‘karfi kamar zata ‘balle ‘kofar. Dahda ransa a ‘bace ya bud’e ‘kofar, murya a sar’ke yace “Hajja lafiya?” Kallon sama da ‘kasa ta jefa masa “ sannu isashshe har kana da bakin tambayata lafiya to ita lafiyar tana gidan ubanka wuce muje ka taho da amaryarka ita ta cancanta ta kwana a d’akinnan sai an mata kwananta uku rus da bazawara ta bata, kuma ban amince da ko bakin’kofar nan naga sillan’kafafunta ba wuce muje ka taho da matarka.” Mommah da take cikin parlourn tana jiyo duk abinda yake wakana ta mi’ke zaune zauciyrta na tafarfasa ta fice daga palrlourn.

Shatu dake zaune a main parlour tana jiyo duk abinda yake wakana tayi al’kawarin yau tsohuwar nan ba zata kwana da lafiya ba. Ta shige d’akinta tana’kissama irin abinda za tayi mata. Da sauri ta shiga tanadin kayan duk da zata yi amfani dasu. Cikin dare ta nufi d’akin da aka sauke hajja, a hankali ta murd’a’kofar Ta shiga, Hajja ta tarar ta saki baki tana barci taci sa’a kuwa hajjan ita kad’aice a d’akin tabbas shirinta zai tafi yarda take so, Ta sake kallon shigar da tayi a mudubi’kusumbi tayi sosai a bayanta ga gashinta da ta saka ya rufe mata fuska gaba d’aya sai wani farin hjibin momma da ta sin’kife jikinta dashi, ba’a ganin fuskrta Sam, Ta dur’kushe sosai kamar wada tana lan’kwashe ‘kafarta kamar a shanye take. Tsaye tayi gefen gadon hajjan kafin tasa sandar hannunta ta zunguri ‘kafar Hajjan “ Ke tashi ajalinki yau yazo tsohuwar banza mai takurawa jama’a……. A razane Hajja ta rusa wani ihu fad’i take “ ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba innahu ala raja’ihi la’kadir……
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: 🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-10

Sosai Hajja ta sake razana ganin shatu tana nufota, fad’i take “ Don Allah kada ku cutar dani ku fad’i mai kuke so nayi? Ni baiwar Allah ce ba ruwa na da kowa a duniya.” Shatu ta ‘kya’kyata wata mahaukaciyar dariya “ so muke kada ki sake cutar da hadizatu idan kuma kin’ki zaki ga sakamakon taurin kai kina ji?.” Da sauri hajja ta d’aga kai “ Na bi Allah na biku insha Allah ba zan sake komai ba” shatu ta sake kecewa da dariya bayan jin abinda tace cikin daka tsawa tace “ To rufe idonki kuma kada ki sake ki bud’e sai nayi nisa da tashi sama.” Da sauri hajja ta rintse idonta gam, shatu da sauri ta fice daga d’akin ta shige d’akinta. Ai cikin azama hajja tana bud’e idonta tayi saurin mi’kewa ta fice daga d’akin jikinta har makyarkyata yake, A tsakiyar falon ta tsaya ta dinga kwalawa mutanen gidan kira. Yarda muryar tata ta karad’e gidanne yasa d’aukacin mutanen gidan fitowa, suka tarar da ita a dur’kushe hankali tashe suke dubanta. Dahda ne yayi’karfin halin cewa “lafiya hajja?” Hajja ta zuba masa wani irin kallo “ ina kuwa lafiya ko da yake yanzu ba zan yi magana ba sai da safe kai ni falonka a can zan kwana kuma kana zaune daga gefe na Yau gamo nayi da aljannu a gidannan.” Dariya ce taso kama Ammar ganin yarda ta ha’ki’kiance take’buya a bayan dahda. Momma kuwa baki ta ta’be ta juya ta koma ciki bayan tayi wa amaryar mijinta kallo d’aya. Ita kuwa amaryar bin bayan mijinta tayi tana tsinewa hajja a zuciyrta yarda zata’bata mata daren amarci duk da tanadin da ta shirya masa ga turarukan tsubbace tsubbace da ta ambula a jikinta banda wanda ta turara sai da ta kusa samo kan mai gidan sannan wannan tsohuwar zata rusa mata shirinta.

‘Karfe bakwai nayi Hajja ta fito babban falon gidan bayan ta tasa ‘keyar dahda a gaba “ Muje ka had’o min kaf kan ahalin gidannan ina da magana dasu “ cikin tausasa murya yace” Hajja da kin bari gari ya ‘kara wayewa ….” “ Na’ki Na bari garin ya waye ahmadu nace na’ki Na bari manga uba na, saboda ba kai kayi gamo da abinda Na gani ba ko.” Tayi saurin tare shi da sababin fad’a. Shiru kawai yayi yabi bayanta zuciyarsa fal ‘bacin rai don dai uwa uwa ce da ba wanda ya isa yazo gidansa ya aikata masa haka.

A tsaye suka tarar da momma tana sake gyara cushions d’in main parlour d’in tas ta gyara gidan sai’kamshin turaren wuta gidan yake. Dahda ya bita da kallo ganin yarda tayi kyau sosai cikin wani pink lace duk da fuskarta ba fara’a amma dai bata fasa gaisheshi ba, sannan ta’karasa gefen hajja da take zaune saman kujera ‘kafa d’aya kan d’aya tana girgiza jiki fuska cike da masifa, muryar mommah a cunkushe itama tace “ Hajja barka da safiya an tashi lafiya?” Sai da Ta ‘kare mata kallo sama da ‘kasa cikin masifa tace “ ‘kalau sumul na tashi duk da ba haka kika so ba, cikin kiyayewar ubangiji na tashi lafiya, saboda kin san tsaye nake akan ‘kafafuna wajen ibada, wai ke deejah har tsubbun taki ta kai ki fara turawa mutum aljannu ? Saboda Na saka d’ana yayi aure, to albishirinki wannan auren mutu ka raba kuma idan kin tashi yau da daddare ki turo min sarkin rauhanai ma ba aljannu ba , Aljannun naki mai suka isa suyi min sunzo sun baki labarin yarda Na fatattakesu da ayar Allah.” Shatu da sauri ta juya Ta shige kitchen saboda dariyar da Ta ciyota. Hajja Ta cigaba “ kuma ni da gidan d’ana ba inda zani zama daram.” Mommah shiru tayi tana al’ajabin hajja yau kuma gingimemen sharrin da za tayi mata kenan lallai tsanarta da hajja ta girmama. Hajja ta juya gun Dahda “ kai kuma manga kana tsaye baka tambayeni ba’asi ba, yo ai dai kace hajja mai ya faru kike wannan fad’a da safiya haka tunda kai haka Allah yayi ka kamar d’an fari, to ko Mahmud da yake d’an farin baya abin da kake. Wato kana ji cikin dare matarka tayi min turen jinnu wai suna gargad’i na na rabu da hadizatu kaji fa wai dijah yanzu har tayi shaharar turo min Jinny?” Dahda ya girgiza kai saboda ‘bacin rai ma kasa magana yayi ya zuba mata ido kawai. Ammar ne cikin d’aure fuska yace “ ko dai mafarki kika yi hajja ina mommah taga aljannun da zata turo miki? Mu tunda muke gidannan ba wasu aljannu.” Girgiza kai hajja tayi sai kuma tace “ Ba shakka, ‘karya nayi maka kenan? To manga ubanka da yake zaune shine ma’karyaci ba ni ba. Ra’ayal aini yarda nake ganinka haka naga aljannu ina tofa musu addu’a suna ihu da tumami suna fad’in deejah ce ta aiko su, haka Na ‘konesu ‘kurmus ba mamaki idan kuka je d’akin ma kuka ga haya’kin da tokarsu, yo ni za’a kawowa zancen banza aljannun me Allah na tuba”. Ba wanda ya sake mata magana haka ta mi’ke ta koma d’akinta tana sake bambamin tijara. Shatu da take la’be a bayan ‘kofar kitchen ta girgiza kai had’e da yin ‘kwafa ta juya ta shige d’akinta .

‘Karfe biyu daidai ba’kin Abuja suka sauka. ‘Kannen mommah ne hisham da hafsa sai nahnah. Kyawawa dasu farare tas kamar su innaji da mommah. Shatu tana zaune tana lesson driver ya dawo daga’daukosu d’aya bayan d’aya suke bin ta da kallo ita ma tana kallonsu, Hisham ne ya bud’e mata alamar ta taho ya dube ta kafin yace If I guessed It right you’re shatu ?na canka shatu ce ko?” Da sauri ta d’aga kai hisham da su nahna suka rungumeta da ihu cikin tsananin farin ciki suna murnar ganinta hakanne Yasa Ammar da mommah da imran saurin fitowa suna murnar ganinsu , kasancewar sun dad’e basu zo hutu ba nahna da hafsa suna turkey, shi kuwa hisham mate d’in Ammar ne tare suka gama makaranta a egypt, Imran ne yayi oxford university england. Murna da hayaniyar da suke ce a main parlour ta fito da mutanen gidan har Hajja da ta fito tana dogara sandarta da yake tana da ‘kiba ciwon’kafa ya sata a gaba.

‘Daya bayan’daya take hurga musu kallo tana amsa gaisuwarsu a gatsine “ Ba shakka dijah kin ci gida kin mallake manga kin mallake dukiyarsa ga ‘yan uwanki ma sun zo sun taru a gida, kai Allah wadaran naka ya lalace su kuma wad’annan gand’an-gand’an ‘yan matan daga ina?” Nahna fuska a d’aure za tayi magana mommah ta girgiza mata kai “ Don’t say any word here ku shiga part d’ina am coming.” Kasancewar akwai tarbiyya hakan yasa basu shiga ba suka ja hannun shatu su kayi gaba su imran ma suka bi bayansu. Mommah ba tace da hajja komai ba ta mi’ke zata wuce. Cikin masifa Hajja tace “ la shakka ga ‘yar iska wato kin bawa banza ajiyata nayi tayi ko? To kinyi da gyatumarki mai kama da sadakar yallar nan kuma da ni kike zancen yau yau zasu juya su koma, kuma kaf jakunkunansu sai nazo Na caje don yanzu haka wani tsubbun suka kawo miki an ji anyi miki kishiya azo a koreta ko? Kuma idan zasu tafi ki tattara har bararojinnan su tafi da ita shaid’anun banza kawai.” Momma wani abu Ta had’iya kawai ta juya ta shige part d’inta zuciyarta na tafarfasa, itama fa mutum ce ba dutse ba dole zuciyarta zata dinga zafi da irin cin kashin da hajja take mata amma ya zata yi dole ta girmamata tunda d’anta take aure. Sai da Ta share hawayen fuskarta sannan ta’ka’kalo fara’ar dole ta bud’e’kofar falonta.

A zazzaune ta samesu tuni sun watsar da lamarin hajja sun saka shatu a tsakiya, sai fito mata da tsarabar kayayyaki suke wanda suka siyo mata a turkey da wanda kakanninta suka bata, sai nuna mata tsananin soyayya suke, hakan yasa fara’ar fuskar shatu ta kasa ‘boyuwa kowa nuna mata ‘kauna yake ashe ba zata yi maraiciba bayan mutuwar innaji, ashe yanzu ne zata fara fuskantar farin ciki a rayuwa. Ta lura kowa sonta yake idan ka d’auke Imran da yake gefe yana harararta ‘kasa-‘kasa. Hisham ya dubi Mommah kafin yace “ Hope dai by now an yi mata register a school ?“ Momma ta girgiza kai “ so muke brain d’inta ya da’n bud’e before taking her to school insha Allah” Imran ya ta’be baki cikin takaici yace “ Allah wahala kawai kuke wannan yarinyar she will never be socialized kamar yarda kuke so , rayuwar daji fa tayi ai sai a slow kawai dama kun daina wahalar da kud’inku kawai don wasting time dinku zaku yi ji fa wasu tarkace a hannunta “ ya fad’a yana nuna hannunnata, gaba d’aya gurin shiru kawai su kayi zuciyarsu kowa da mamakin imran. Hisham ne ya katse shirun yana dafa Imran yace “ Amma son banyi expecting hakan daga wajenka ko bakomai she is your bloody sister da nake fatan mu nuna mata soyayya mu kuma bata jin dad’in da ta rasa.” Tsaki yayi Hasfa ganin yarda mommah ta damu sai ta sako wasa cikin zancen “ Rabu dashi Yaya hisham bayan ma bai san yarda rana zata fad’i ba “ da sauri ya zaro ido “ wa? God forbid wallahi insha Allah rana a gabas zata fad’i ko don ba kiga babban kamun da nayi ba classy baby ga good hygiene ga kyau ga ladabi.” Tsakin da mommah ta zabga ne yasa yin shiru duk gurin kuma aka saka dariya ban da shatu da imran ya riga ya ‘bata mata rai. Mi’kewa tayi zata shige ciki taji Nahna tana cewa “ Mhmn Allah ya kaimu lokacin da zaka zo kana’yar murya “ ya mi’ke yana fad’in “ ai ko a ‘kafa aka d’aura min wallahi sai na cire na yar “ Mommah kwafa tayi tana nuna musu dinning “ Hisham close the chapter kuyi taking shower ku ci abinci duk da dai tafiyar dad’i kuka yi tafiya a jirgi” Nahna tace “ Yo wa zai zo kano from Abuja a mota.”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-11

ELEGANT ONLINE WRITERS…..

Da yammacin ranar kuwa ‘yan matan mommahn gaba d’aya suke a kitchen suna tayata d’ora sanwar dare, shatu na gefen Nahna tana tayata had’a salad. Ta dubi antynnata kafin tace “ Anty Nahna ku nawa ne’yan uwan innaji?” Nahna murmushi tayi tana dafa gashin kan shatu data gyara mata shi ya sauka har tsakiyar gadon bayanta. “ Mu biyar ne Mommah ce babba sai adda maryamu sai hamma hisham sai ni sai kuma hafsa shekara d’aya ne tsakaninmu da hafsa. Mu kad’ai ne a gidanmu babanmu bai kara aure ba shi yasa sam ba abinda yake d’aga mana hankali bamu da yawan da za’a samu sa’bani a cikinmu muna son junanmu kamar mu had’iye kanmu, shi yasa sam ba muyi Farin ciki da auren da ammar zaiyi ba, mun so ya auri jininmu ta yarda zamu sake tashi tsintsiya mad’aurinki d’aya, amma hakan bai yiwuba kana tasa Allah na tasa amma Allah’s plan is better than ours right?”murmushi shatu tayi ‘kaunar dangin innajinta yana sake ratsa ta musamman ganin yarda suke nan nan da ita. Sai kuma ta kama hannun nahna race “me kika fad’a daga ‘Karshennan ina so in iya irin maganar nan” Nahna ta sake sakin murmushi kasancewarta ma’abociyar murmushi, tana jan hancin shatu tace “ kin san turanci?” Shatu Ta d’aga kai “ Na sani innarmu idan tana koya min karatu tana yawan ce min sai na iya abcd sannan zan iya turanci “ Nahna tace “ To wannan maganar da nayi shine turanci kice kin iya abcd?” Shatu cikin dariya tace “ kai na iya fa har’karshe kuma har rubutu na iya da karatun hausa Na abcd kuma na iya su boy girl, man da woman kai har su cup fa na iya.” Da sauri hafsa da mommah suka juyo nahna kuwa murmushi tayi kice “ yarinyar tawa kanta na ja ba zama kiyi wuyar shiga school ba.” Momma farin ciki ya cikata “ai kuwa gobe za’a miki register a school ko primary 4 su kaiki shekara nawa kika ji innajinki na fad’ar shekarunki?” Shiru tayi tana lissafi sai tace “ haka dai da zata mutu ina shekara sha uku “. Hafsa tace nawa kenan a karatun book?” Wani kallo tayi mata tace “ kai mhmn thirteen d’inne ban sani ba aradu har dubu munje da innaji tace min thousand sunansa “ gaba d’aya suka hau tafa mata. Momma cikin farin ciki ta jata ta rungumeta tace “lalle maryama tayi ‘ko’kari am so proud of her .”

Shigowar amaryar dahda ce ya dakatar dasu daga hirar da suke, ko magana bata yi musu ba ta bud’e fridge tana wani gatsine sai kuma Ta d’aga waya murya cikin kissa take fad’in “ Am coming dear naje samo maka drink d’in da kace ne.” Tana fad’a tana kallon mommah da take murmushi ‘kasa-‘kasa, “0key dear yanzu zan dawo kada ka damu zan maka abinda yafi kis…….” wani kallo mommah tayi mata da yasa ta gintse abinda tayi niyyar fad’a ta juya har ta kai ‘kofa momma tace “ kice masa har ya dawo daga kadunan da ya tafine? Kuma yaushe ya fara shan drinks na general kitchen..” wata kunya ce ta kama amarya ta juya da sauri ta fice, gaba d’aya suka saka dariya a kitchen d’in mommah tace “ kaji min shashasha right now fa na gama receiving call d’in and he told me yana kaduna amma kaji makira “. Suka sake she’kewa da dariya. Nahnah tayi tsaki “ Ni ba’kin cikina d’aya mommah da kuka amincewa imran ya auri ‘yarta ba kiyi masa jan ido ba, don sun ga d’anki ya taso da nasibi ga arziki ta ko ina ‘karuwar masa yake, kuma sun lura da matsanancin son da yake miki shi yasa fa suka shiga jikinsa idan ban da haka ina imran ina wannan yarinyar tana tafiya kamar bulala, ji fa ranar da muka had’u da ita a mall wallahi nunawa tayi bata son mu ba.” cikin takaici momma ta girgiza kai “ ki rabu da imran taurin kai gareshi kamar mutanen farko sau nawa na nuna masa bana so sau nawa na hanashi, amma ya’ki jin zancena amma lokacine zan nuna masa bashi da wayo daga shi har dangin ubannasa, muje dai zuwa a kuma juri zuwa rafi….”

Ita kuwa amarya tana fita d’akin hajja ta shiga ta zauna ta gaya mata’karya da gaskiya hajja ta hau kai ta zauna. “ kika ce sun zageki zainabu?” Amarya Ta d’aga kai hajja ta kuwa mi’ke zaune “ Ai kuwa tunda suka zageki ba ke suka zaga ba ni suka so zaga aka fake dake, to kuwa ba zai yiwu ba uwarki ni na sha mama na bar mata ban ga d’an abu ta kazar uban da zai zagar mana mahaifiya na ‘kyaleshi ba ke ko da kuwa sadakar yallar uwarsu ce muje madafar “ Amarya farin ciki fal ranta ta mi’ke ta bi hajja kitchen.

Tsaye hajja tayi ri’ke da ‘kugu tana musu kallon sama da ‘kasa “ Eeh lallai kuwa ba shakka na ta’kar’kare na d’au cikin manga, Na sha ba’kar wuya a haihuwarsa ashe dai ku na haifawa, an shigo cikin daula a dafa wannan a sauke wannan,A samu na banza aci ai nak, bama wannan ba uban me zainabu tayi muku kuka zageta? Ko kuwa sa’kon zagin kuka bata taje ta isar min hamsha’kai ?” Shatu ta zaro ido tana kallon amarya murya ‘kasa-‘kasa tace “ Allah ya shirya babba da ‘karya cab” gaba d’aya kitchen d’in ba wanda bai ji maganarta ba har hajja. Amarya ta zaro ido “ ke don ubanki ni nake miki ‘karya ko hajja?” Shatu Ta sake gyara zama tace “ duk wanda yayi ‘karyar ai addu’a nayi “ a sukwane ba suyi auneba suka ga ta zuba wa shatu mari hannu bibbiyu a zafafe hafsa ta janye ta tana mata wani banzan kallo “ kada ki sake ki sake dukanta me tayi miki? “ momma ta nuna musu hanyar ‘kofa “ ku fita “ ta’kofar baya suka fice sannan ta kalli hajja “ kiyi ha’kuri ba wanda ya zageta amma tunda ta fad’a miki kin yarda Allah ya baki ha’kuri” daga haka Ta fice bayan ta watsa wa amarya kallon banza.

Hajja bata shiga d’aki ba anan main parlour ta dinga zazzaga tijara zagi ta uwa ta uba ta dinga aikawa su mommah bayan amarya ta zauna ta sake fonfata wai har taji sanda suke cewa so suke ta mutu su sake mallake manga gaba d’aya har dukiyrsa hakan yasa ta sake sauke kwandon tijara zagi ta uwa ta uba. Ran shatu ya’baci musamman ganin yarda su nahna suka fara had’a kaya wai tafiya zasuyi da sassafe zasu bi flight d’in safe su tafi, haka ma hajiya mama tace bata son tashin hankali su taho kawai. Shatu kuwa ta’kudirce a ranta tsohuwa hajja ba zata kwana lafiya ba sai Ta gwammace kid’a da karatu.

Cikin dare shatu ta mi’ke daga gefen nahna da suka kwana tare a d’akinta, sad’af-sad’af ta fice. Murd’a ‘kofar hajja tayi a hankali ta shige ta mayar da ‘kofar ta rufe, dubanta ta kai kan hajja da ta saki baki tana barci tayi, har da yawun barci ta saki dariyar mugunta bayan ta kashe fitilar d’akin da fanka har da a.c . ‘Dif d’akin ya ba’kunci duhu ga windows dama duk a rufe, shatu ta shige ‘kar’kashin gadon hajja a hankali, kasancewar ba auki ne da ita ba zuruf ta shige . Muryarta ta kumbura ta fara fad’in “ke tsohuwa ke tsohuwar banza tashi maza ajalinki yazo….” Hajja da taji maganar daga sama a razane ta farka taji d’akin d’uf misalin dai duhun kabari da ake fad’a . “Kada ki sake kiyi mana ihu ba dai kince kin ‘konamu ba zuwa mu kayi ki ‘kara ‘konamu mun ja kunnenki ba kiji ba to yau a tsakiyar dajin aljannu zaki kwana kafin gari ya waye mu zu’ke jininki…….” Hajja jikinta ‘bari kawai yake murya a razane take fad’in “ Hajja kwananki ya’kare idan ban da shegiyar ‘karyata dama mai ya kaini cewa nayi fad’a da aljannu……😂😂🤣🤣🤣

Kai yau nayi typing da yawa so that ina jiran in ga ruwan comments.

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-12

ELEGANT ONLINE WRITERS……….

Shatu tayi saurin matse dariyar da take son kamata, ta sake jijjiga ‘kasan gadon , cikin murya mai amo sosai tace “ Baki ga komai ba tsohuwa sai kin bud’e ido kin ganki a gaban sarkin aljannu yana bada umarnin a shanye jininki a yar da gawarki a daji namun daji su cinye ba dai ba kya jin magana ba mun ce ki fita daga harkar hadizatu kin ‘ki hahhhhhahhhha yau zamu sha jini ku ‘karaso maza ku d’auketa kada ku sauketa sai a dajin sarki ‘kuraizu hahhhhhahhha.” Ta sake tuntsirewa da shegiyar dariya hajja kuwa tuni ta sume tun bayan da Ta ‘kwallara wata ‘kara da duk gidan ya amsa bayan taji an jijjiga gadon da ‘karfi. Imran ne ya fara fitowa kafin su mommah suma su fito kowa yana Duban d’akin hajja inda ‘karar take fitowa. Imran baiyi wata wata ba ya bud’e d’akin da sauri ya ‘karasa gun hajja da ya gani a san’kame akan gado, ya fara jijjigata sai dai ba alamar numfashi a tare da ita, idanunsa ne ya sauka akan tsinkakken abin hannun shatu da sauri ya zaro ido bayan ya d’au abin hannun yana dudduba inda zai ganota, bai ga alama ba ya zira abin hannun a aljihunsa. Momma kuwa da sauri ta ‘karaso tana dubata a gigice take sosai hakan yasa murya na rawa take cewa “ Imran kira doctor she is unconscious “ Imran ya mi’ke yayi saurin shiga toilet nan ma bai ga shatu ba, ruwa ya d’ebo ya zubawa hajja a jikinta ,da sauri ta kawo ajiyar zuciya ihu take tana fad’in kada ku tafi dani bijahil kudrati na daina shiga sabgar dijama innalillahi.” Kowa d’akin tsit yayi yana kallonta, Imran ya kamata “ Tashi Hajja ba wani aljannu da izinin ubangiji koma akwai zan binciko su” Hajja ta mi’ke jikinta sai ‘bari yake fad’i take “muje d’akinka imran tunda manga baya nan a can zan kwana ni da d’akinnan har abada anan matattarar aljannun gidannan suke.” Ammar da yake gefe ya tuntsire da dariya sannan yace “ Hajja rannan fa cewa kika yi kunyi fad’a dasu har kin ‘konasu to yau me yasa kika kasa.” Shiru tayi tana dube-dube “ kai Ammar ka iya bakinka yanzu d’akin nan taf yake da jinnu kafin kaima su dawo kanka muje lmrana” jikinta rawa yake sosai Imran ya fita da ita daga d’akin.
‘Dakin mommah ya nufa da ita da sauri taja tunga ta tsaya “ ina zaka kaini Imran?” Fuska a had’e yace d’akin mommah mana wani abu ne?” Hajja taja baya kafin tace “ma’ana so kake naje d’akin su samu nayi su dagargazani d’akinka zaka kaini dama manga na nan ne sai ba kwana a d’akinsa gobe kuwa jirgin asuba zan bi zuwa garinmu ba zan sake kwana a gidan manga baseries kuyi min bukin na tikitin jirgi.” Ammar yace “kice ba zaki zo bikin bros ba?” Kallonsa tayi sai kuma tayi ‘kwafa ta dam’ki hannun Imran “muje d’akinnaka” Imran ya’bata fuska Kafin yace “ Ni fa hajja ba’a shigar min d’aki ni kad’ai nake amfani dashi for goodness sake ya zanyi dake idan kin so shiga toilet ki dai canja shawara idan ba zaki shiga d’akin mommah ba sai dai a kaiki d’akin amarya” “To kaini can d’in ita ‘yar banza ma ko fitowa ba tayi ba duk wannan budirin da ake.” Shi dai baiyi magana ba ya jata ya kaita part d’in amarya . Yace “sai ki buga mata ni zan tafi na kwanta” ya juya da sauri ta cakumoshi ganin labulai na motsi, tsaki yayi sai kuma ya hau dukan’kofar amarya tana fitowa ya bar hajja yayi saurin fita so yake yaje ya rutsa yarinyar can.

Ko da ya shiga d’akin ganinta yayi kwance akan gadon hajja tana ta tuntsira dariya, ko kad’an bata damu ba da taga ‘kofar d’akin a rufe da key bata da hanyar fita ta san kuma dole goben asirinta zai tonu. Tsit tayi bayan ganinsa a tsaye kamar wanda aka turo fuskarsa a had’e kamar hadarin kaji. Gadon ya’karasa ya janyo jelar gashinta sai gashi ta mi’ke tsaye tsam, fuskarta babu alamar tsoro ko kad’an. Ji yayi kamar ya mammaketa ya ja bakinta ya murd’e duk da taji zafi bata nuna masa ba sai ma ‘bata fuska da tayi “kece aljannar da ke tsorata Hajja kenan to yau asirinki ya tonu kuma sai na gayawa kowa abinda kika aikata har dahda so kike ki kashe masa uwa kenan?” Turo baki tayi tana masa kallon ‘kasa-‘kasa, ba tare da tayi magana ba, ya sake janta ta durgo daga kan gadon sai gata a gabansa, kallon mamaki yake mata ganin yarda sam ba tsoro ko kad’an a tare da ita ya rasa irin yarinyar nan ko dai da gaske tana da ala’ka da jinnu tunda ance rayuwar daji tayi. “Wato ke baki tsorata ma da laifin da kikayi ba, ji yarda kike kallona da idanu kamar na mayu d’auke idonki a kaina before i nock your head, yau a toilet za kiyi spending darenki wuce Muje.” Ta’be baki tayi an gaya masa tana tsoron kwana a toilet ne balle wannan toilet d’in nasu na ‘yan gayu ita tsoronta d’aya kada ya gayawa wannan Almasifatun Babannasu da ko idonsa bata son gani razana ta suke. Ya turata toilet d’in har zai kashe fitila da yake switch d’in a waje yake sai ya fasa ya rufe toilet d’in da key ya fice daga bed room yana mamakin taurin zuciyar shatu.

Da asubar fari yazo ya bud’eta ba don komaiba sai don baya son ya shafawa mommah black paint dole zai bar hajjan a zuwan jinnun gaske ne. Tana barci a kwamin wanka ya sameta hankalinta kwance. Tsayawa yayi yana kallon al’ajabi yarda take barci peacefully a cikin toilet idan shine ai an kasheshi baya jin zai kwana da lafiya. Ya daddage ya d’aka mata duka, ta d’anyi saurin bud’e idonta tana ganin shine ta saki murmushin mugunta don tayi targeting sai ta rama wallahi nan kwana kusa kuwa. Ta zuro’kafafunta ta fita. Shi kuma yabi bayanta. Sai da yaga ta shiga d’akinsu sannan yaja ‘kofar part d’in hajja ya fice masallachi.

Ana idar da sallahr asuba Hajja ta fito main parlour ta zauna, ko tunanin d’aukan kayan ta bata yi ba. Imran yana shigowa daga masallachi yayi arba da ita dariya taso ‘kwace masa sai dai da yake ba ma’abocin dariyar bane sai ya gimtse “ wai meye haka hajja tafiya ba shiri” ya fad’a yana jingina da bango. “ mi’kewa hajja tayi tana gyara sandarta kafin ta sake gyara glass d’in idonta ta kafeshi da ido kafin tace “ko ubanka manga bai isa yace sai na sake kwana a gidannanba aljannu na neman kassarani maza-maza muje ka kaini tashar jirgi.”Ransa a ‘bace ya juya sai kuma yace”ai dai kya yi sallama da mutanen gidan.” Ya shige sashen mommah Hajja tayi saurin bin bayansa “muje ka wani bar ni anan nifa tsoron gidannan nake ji” shatu da take la’be a window ta tuntsire da dariya da sauri hajja ta dam’ki hannun sa “kaji ko wallahi har yau suna gidannan ko baka ji abinda naji ba” hararar shatu yayi tayi saurin sakin labilan. Nahna da take zaune tana azkar ta kalli shatu “ ke lafiyarki kuwa?” Shatu taso bata da labari sai kuma ta gintse tace “zo kiga tsohuwar nan anty nahna zo kiga yarda take rawar d’ari duk tabi ta ma’kal’kale yah Imran” Nanah tace “Allah ya shiryeki shatu ko dai ke kike tsorata ta?” Da sauri shatu ta girgiza kai. Suna kallo su mommah suka rakata su kayi mata sallama.

Kashegari kuwa budurwar Imran ce ta bayyana a gidan tazo hutu a cewarsu wajen uwarta daga abuja fara ‘kal da ita har yellow take sai dai a tsaye take tsam kamar sanda shatu da take jikin window inda ta saba la’be, tana ta kallon yarda Imran yake rawar ‘kafa da budurwarsa ta kuwa ta’kar’kare tace “Muciya da zani” kasancewar parlourn ba hayaniya ba wanda bai ji furucinta ba sai da maganar ta fito tayi saurin toshe bakinta tana kallon Imran da suka yi four eyes da ita ransa a matu’kar ‘bace…..”

To fah! Shatu danger

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-13

Da sauri shatu ta ruga part d’in mommah, shima Imran yayi saurin mara mata baya, yau kam ba mai hanashi cin kwal uban shatu, a bayan mommah ya ganta tana ta dariya ‘kasa-Kasa, kamar mayunwacin zaki haka ya bita zai cafkota, mommah tayi saurin ri’keta tana furta “kai lafiya uban mai tayi maka?” Cikin ‘bacin rai yace mommah please ki rabu dani in jibgi yarinyar nan, habibteey fa take tsokana wai muciya da zani” dariya ce taso kufcewa mommah tayi saurin rufe baki wanda hakan ya sake ‘kular da Imran yayi kukan kura ya kamota mari lafiyayye ya sauke mata. Da sauri mommah ta janye ta ranta a matu’kar ‘bace “ wai meye haka ne Imran kasheta zaka yi akan wata habibty to wai ma da tace mata muciya da zani sunanta ne? Ko kuwa an canja mata suna ne ta koma muciya ina ce dai ba sunan mutum bane muciya?” Ransa a ‘bace yake sake kallon mommah kafin yayi ‘kwafa wallahi da ita take kuma zaki gane baki da wayo” Mommah ta’kunshe dariyarta ita da nahna da shigowarta kenan tace “a’a Imran kaso kanka sai dai kuma idan tsarguwa kayi ni ban ga abin damuwa ba indai ba habibteeyn taka tayi kama da muciyar da zani bace” Hafsa da Nahna suka tuntsire da dariya. Tsaki Imran yayi ya juya ya fice zuciyarsa cike da sake tsanar shatu.

Bai ganta ba a parlourn hakan ya nuna masa ta shiga sashen mahaifiyarta don haka direct d’akinsa ya nufa yana danna waya nemanta yake, sai dai sai rejecting calls dinsa take.

Ita kuwa tana can zaune fuska a tur’bune tana kallon mahaifiyarta “amma anty wannan yarinyar wacece? A gaban mutane fa ta disgani wai muciya da zani yanzu idan tasa Imran ya ankare da halittata fa ya fasa aurena” zainabu ta girgiza kai “bai isa ba bashi da wannan right d’in baby don na riga Na d’inke zuciyarsa a jikin taki tsaf ba zai ta’ba kallon wata mace bayan ke ba da sunan so” murmushi ta saki “wallahi na yarda da lamarinki anty gashi nan ma yanzu sai kirana yake tun d’azun na tabbata ya kasa sukuni ne”zainabu ta girgiza kai “ba zaki gane irin yarda na tsani Dijah bane saboda ita fa manga ya’ki aurena har an saka rana ta da yana had’uwa da ita yace ya fasa aurena bayan na tabbata ba yin kansa bane tsubbun su na fulani ne ya kamashi” Shaheeda ta girgiza kai “kullum fa anty sai kin bani labarinnan ko hadda ne yaci ace by now nayi haddarsa ni yanzu damuwata ayi a saka ranar nan na kama shi a hannuna ina son Imran to the extent.” Zainab ta dafa ta “shaheedah na sani na san kina son Imran amma fa bana so ki sashi sosai a zuciyarki don bana son lokacin da aikina zai kammala ki kawo min cikas bance kada ki so shiba a’a nafi so ma ki so shi sosai ko bakomai ba ko don dukiyarsa yaci a soshi, duk da kema na san don hakan kike sonsa da bashi da ko sisi ko shine aljannu don kyau ba zaki aureshi ba,aurenki da Imran ba fashi don nima shine burina, sai dai ina da wata manufa mai ‘karfi akan haka kuma kada ki sake ki bijire min a lokacin da bu’kata ta tazo” shaheeda murmushi tayi kafin ta janye jikinta ta mi’ke tsaye ta furta “Allah ya nuna mana lokacin bari inje in gaishe da inlaw ta kada tace bani da kunya.” Zainabu ta had’e a rai a zuciyarta tana tunanin lokacin da zata cimma burinta da ya jima a zuciyarta.

Murya can ‘kasa tayi sallama a ‘kofar parlourn idanunta akan shatu tana jin tsanarta a ranta. Momma ta amsa mata sallamar fuskarta ba yabo ba fallasa su kuwa su nahna ba wanda ma ya kalleta. Sum-sun har ‘kasa ta dur’kusa ta gaida mommah. Amsa mata mommah tayi fuskarta fal fara’a tace “Ya gida ya mutanene gidannaku?” Kanta a ‘kasa tace “lafiya lau” hafsa ta bita da wani kallo a zuciyarta tace munafuka. Shatu kuwa ‘kara ‘kare mata kallo take tana son ganin wani aibu a fuskarta sai dai bata gani d’in ba fuskarta ba yabo ba fallasa tana da kyau dai-dai nata sai dai daga ganin goshinta kasan bata da gashi tsam ta mi’ke “mommah bari na kawo mata ruwa” momma ta gyad’a kai “kin kyauta kuwa mah girl hakan yayi”

Shigowar Imran yayi daidai da kawo mata ruwan da tayi. Yana ganinta yayi saurin had’e rai. Ita kuwa shatu bata ma san yana yi ba ta isa gabanta ta ajiye mata ruwan ta kuma ‘ki yarda ta kalleta ta hau zuba ruwan, da azama Imran ya ri’ke hannunta. “Kwashe ruwan nan ki tashi daga nan kafin nayi ball dake wa yace miki ita ‘kazamace da zata sha ruwanki.” Kallonsa shatu tayi kallon da bata ta’ba yi masa sai taji zuciyarta ta buga bata ta’ba ganin zahirin kyansa ba sai yau da suka yi so close dashi, taushin hannunsa a cikin nata yasa ta zubawa hannayensu ido. Kamar a mintsineshi da sauri ya janye hannunsa, itama shatu hakan ya fargar da ita ta janye idonta da sauri ta mi’ke jikinta a sanyaye tayi hanyar d’akinta. Mommah kuwa ranta ne ya’baci tunaninta haushi shatu taji daji saboda furucin da Imran yayi a Kanta.mi’kewa tayi ita ma ta bi bayan shatunta. A kwance ta ganta akan gadon. Ta zauna a bakin gadon taja ‘kafarta “ Tashi shatun mommah tashi maza kije ku tafi da nahna za tayi miki shopping d’in school.” Da sauri ta mi’ke tana murmushi “mommah yaushe zan fara zuwa?” Mommah tana murmushi tana duban shatu ta lura shatu sam bata da ri’ko shi yasa kullum take cikin walwala ko tunani da wuya ka kama ta tanayi always zuciyarta fresh take as babies hearts. Tana kallonta ta fice da d’an saurinta. Ko da suka fita parlourn tuni suka tarar Imran ya fice da gimbiyar tasa.

Da sassafe shatu tayi shirin school ta fito kenan ta tarar da masu aiki a kitchen hannunsu duk hand gloves da alama uban ‘kyankyamin su ke yiwa girki. Da fara’a ta shiga tana kallon Daniel tace “ shugaban yan girki abincin waye wannan?”cikin gwarancin hausarsa yace “Babyn mommah kayi kyau wow!” Harara ta zuba masa “tambayar da nayi maka kenan?” Daniel yana dariya ta shagala da kallonta yace abincin oga Imran ne” murmushi ta saki tana dubansa ta juya ta shiga store cikin abinda bai fi second biyar ta fito a guje “daniel zo ka fita da ‘bera” daniel ya zaro ido “‘bera kace mai kyau you mean rat?” Tsaki taja “kayi sauri ka tsaya kana surutu sai ya shige wani wajen” yana shiga ta rufo ‘kofar da key “idan ka cireshi ka gaya min sai na bud’e.” Ta bud’e peppe soup ta tara yawu a bakinta ta tottofa ta mayar ta rufe tana dariya, sannan ta ciro wata leda a jakarta ta tsiyaya ruwan cikin shayin dariya take sosai “yau zamu ga ‘karsheb tsafta zaka sha yawuna ka sha kuma ruwan hammata ta.” Da sauri ta bud’e daniel jin Imran na’kwala masa kira.” Kaga ‘Beran?” Ta wurga masa tambayar bayan ta lura yana kallonta “ban ganta ba” ficewa tayi tana cewa “ta gudu kenan bagware wai ban gan taba sai kace ‘beran macece?”

Not edited…..

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-14

Tun da ta ganshi a parlourn hakan yasa ta zama don taga ko zaici abincin,shi kuwa yana dinning a zaune ya had’a tea ba tare da ya dubeta ba da alama sauri yake don haka da azama ya d’aga cup d’in tea d’in ya kur’ba ya kuma bud’e bowl d’in peppe soup d’in ta zuba a plate ya kai baki yana kur’ba dad’in peppe soup d’in ya ratsa har kwanyarsa ya lumshe ido yana sake zu’ka. Dariyar da shatu ta saka ce yasa shi saurin bud’e idonsa sai kuma ya had’e ransa yana dubanta tana ta she’ka dariya har da tuntsirawa,jikinsa ne ya bashi tabbas akwai dalilin dariyar tata don haka da sauri ya ture plate yace”ke zo nan” tana ‘kunshe baki ta fara shirin guduwa “wallahi kika d’aga ‘kafa daga wajennan ko da one step ne zaki ga abinda zan miki zo nan nace.” Hantar cikinta ne ya d’uri ruwa har ta juya zata wuce ba tare da taje d’in ba taji ya dam’keta ta baya gashinta yaja taji zafi sosai don haka ta runtse ido.”Don Allah ka sakar min gashi akwai zafi fa to wai mai ma nayi maka?” Tayi maganar cikin muryar shagwaba bai mata magana ba ya jata zuwa part d’insu a parlour ya wurgata saman kujera”gaya min uban me kike wa dariya ko na baki wahala nan dai ba mai cetonki balle kice wallahi idan baki gaya min ba ko school d’in da kike zumud’in zuwa ba inda zaki”Jin yace ba zata school ba ne hankalinta ya tashi duk d’okinta da takeyi zai ruguza mata shiri ta fara rawar baki”kada ki sake kiyi min ‘karya ina da abinda zan saka a jikinki in gano gaskiya don fad’a min gaskiya kafin na gano da gaskiya.” Ya fad’a cikin’kara tsare gira. Hakan ne ya sake razana ta tayi saurin cewa “idan na gaya maka gaskiyar zaka barni in wuce school?” “Fad’i ina jinki” ya fad’a yana tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Don Allah kayi ha’kuri a cikin peppe soup ne na zuba yawu na a tea kuma na zuba maka ruwan hamma…..” da sauri taga yayi toilet yana kakarin amai hakan yasa ta suri school bag d’inta tayi waje a guje. Ya dad’e yana amai kamar ya amayar da kayan cikinsa ‘karshe ya fito har wani jiri yake ji kamar ya kifa haka ya kwanta akan gado yana maida numfashi har ga Allah yarinyar nan ta cuceshi cuta bata wasa ji yake kamar ya fito da kayan cikinsa ya sauyasu ha’koransa kuwa da harshensa ya dirje su yafi sau nawa har rad’ad’i suke masa zazzafi mai zafi ya kamashi haka ya ‘kudunduna a gado duk da yana da important issue haka ya ha’kura da fitar.

A school an kar’beta ko da suka gwadata suka ga gwara kawai su kaita primary five tunda tana da sharp brain idan yaso a gida a samar mata lesson teacher.

Da ta dawo kuwa samu tayi duk gidan suna part d’insu Imran wai bashi da lafiya ta’be baki tayi ta samu abinci kawai ta fara ci ita ina ruwanta da ciwonsa mutum sai shegiyar tsaftar tsiya har da wani amai da ciwo. Taci ta ‘koshi sannan tayi wanka ta zira da wando tana fitowa ta tarar da mommah ta shigo. Mommah ta bud’e mata hannu tana welcoming d’inta tare da furta”oyoyo autar mommah ya school d’in” ta d’aga kai “
Ba laifi mommah amma fa sai an jawa ‘yan class d’in kunne bana son rashin kunya don naji suna ce min wai ra’kumi a cikin ‘yan tsaki to yau dai nayi musu na ba’kunta gobe kuwa wallahi na jaki zasu ci” Mommah murmushi tayi ta dafa ta “ba’a fad’a a makaranta baby na kada ki kula kowa kin ji’yar albarka kiyi karatunki kawai ki koma gida shine abinda ya kaiki kinji?” Murmushi tayi ta d’aga kai shigowar nahna ce yasa mommah ta tuna ruwan tea zata dafawa Imran kuma ya ro’keta don Allah da kansa zata kawo masa don yanzu tsoron ta’ba komai na gidan yake da zai iya ma da kansa zai shiga kitchen d’in ya dafa to jiri yake ji saboda tun safe ba abinda ya shiga cikinsa.Momma ta girgiza kai “kinga kuwa nahna shaf na manta abinda nazo yi bari in tashi” Nahna tana dariya tace “ya kuwa ce da kanki yakeso ki dafa masa kuma kina juyewa in kawo masa ni ban san me ya sameshi ba” mommah tace “mhmn rabu da Imran haka yake idan yana cuta sangarta ce dashi zan ga yarda matarsa zata yi da ‘kyan’kyaminsa wallahi abin yana damuna sai kace wani mai cutar tsafta.” Da kanta ta dafa tea d’in ta bawa Nahna ta kai masa.

Yana ganinta ya mi’ke zaune da kyar yana ri’ke kansa ya jingina da bangon gadon a hankali ya motsa bakinsa muryarsa ta fito “please mommah ce ta dafa kuma kina tsaye a wajen? Ibilishiyar yarinyar nan kuma bata wajen ko?” Nahna ta girgiza kai tana dariya ta tabbatar masa mommah ce ta dafa da kanta. Ta zuba ta mi’ka masa yana sipping a hankali. Lokacin shaheeda ta murd’a ‘kofa ta shigo kallo d’aya tayiwa nahna ta d’auke kai hannunta d’auke da cooler ta nufi gefen gadon ta zauna cike da kwainane sai zabga ‘kamshi take ta zauna a gefensa tana jan yatsun ‘kafarsa “am sorry Habibi ya jikin?” Nahna ta kai idonta kan hannun sai kuma ta ta’be bakinta da sauri ta fice tana mamakin rashin kunya irinta ‘yan matan yanzu sam basa iya tsare mutuncin kansu shi yasa ko auren aka yi mazan basa ganin mutunci su.shaheeda ta sake kallonsa tana murmushi “ Habibi in zuba maka abincin?” Da sauri ya girgiza kai, ta kuwa had’e rai a hankali tace “kai habibi I cooked it with my own hand fa please kaci kaji?” Cikin muryar shagwa’ba take gaya masa hakan ya sake narkar da zuciyarsa yana jifanta da wani kallo ya matsu ya matsu sosai ya auri shaheeda shi kad’ai irin son ta da yake dan’kare a zuciyarsa yana jiran lokacin da Zai amayar dashi.ta zuba a plate ta zauna tana bashi a hankali cikin sigar jan hankali.

Mommah ce ta tilasta shatu sai taje dubashi, ta mi’ke tana zun’bura baki a zuciyarta take tunanin ita mommah bata san itace silar ciwon bane ta tabbata yanzu idan taje sai ya huce haushin abinda tayi masa. Hafsa ce cikin fad’a tace “Ba zaki tashi kije ba sai na ‘bata miki rai baki san d’an uwanki bane shi duk duniya baki da kamarsa fa shi da Ammar.” Mi’kewa tayi ta fita niyyarta idan ta fita ta la’be ta dawo tace taje, sai dai a rashin sa’arta Nahna ta mi’ke tace “Bari muje na san halinta yanzu ta ‘buya tace taje.” Ta tura ‘kofar bed room d’in a hankali bayan ta shiga parlourn hakan yasa Nahna saurin juyawa ta koma. Ita kuwa shatu mummunan gamo tayi shaheeda ce a gefen Imran tana ta shafa masa fuska wai tausa take masa ta shige jikinsa sosai kamar me. Da sauri shatu ta runtse ido tayi saurin juyawa shi kuwa Imran motsin da yaji ne yasa shi saurin mi’kewa sai yaga fitar shatu da sauri ya janye jikinsa yana wa shaheeda wani irin kallo “sau nawa zan gaya miki bana son irin wad’annan abubuwan bafa wayewa bace yanzu kinsa yarinya ‘karama ta gammu a haku me kikeso tace mai kike so tayi zargi a zuciyarta?” Shaheeda marairaice masa fuska tayi “Haba habibi meye a cikin hakan kawai fa tausa ne amma tunda baka so insha Allah na daina Allah ya kaimu lokacin da zaka zama halal d’ina in nuna maka pure love da ba surki amma waccen yarinyar mai take zuwa yi har bed room d’inka?” Runtse ido yayi yana tunanin lamarin yarinyar baya ko son ganin fuskarta tsoronta lamarinsa yake bashi don haka dole ya samarwa kansa lafiya ya fita sabgarta kafin tayi abinda zai kaishi lahira burinsa ma lokacin bikinsa yayi ya tattara ya bar gidan ba sai ta ganshi bama balle ta hukunta shi da ‘kazantarta.

A ranar Dahda ya dawo amarya aka shiga giringid’ishin kama miji mommah dai ko gurinsa bata jeba balle taga abinda zai ‘bata mata rai, sai da ya gaji da kansa ya shiga part d’inta tana zaune da kwalliyarta ta tsadaddiyar atamfa ta kashe d’auri parlorn nan sai ‘kamshin turaren wuta yake yi. Murmushi ya sakar mata “uwargida ran gida barka da hutawa ni nazo gaisheki tunda ba’a nemansa” murmushin ta saki itama bayan ta gama saurararsa tace “hakan da kayi shine abinda ya kamata ka bi cikakkiyar sunnar manzon Allah ya hanya?” “Alhamdulillah” ya furta yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tabbata da itace da girki da tuni ta kai masa ruwan wanka ta kuma taimaka masa da tausa da lafiyayyen girkinta tana zuba masa tana murmushi ba dole dijah ta sace zuciyarsa shi kad’ai ya san wacece dijah ya kuma tabbatar ba zai samu kofa kwafinta bane balle wacce ta kaita. “Na biya wajen hajja wai me ya faru ne ta tabbatar min da aljannu a cikin gidannan wai ba zata sake zuwa ba” yana murmushi ya fad’a mommah ma dariyar tayi tace”Ba mamaki da aljannun a d’akin da take sauka amma mu dai bamu ta’ba gani ba” “Ni na sani na san rigimar hajja ce yanzu ba ma wannanba ta rigime min sai anyi bikin Imran nan da wata d’aya da Rabi” mommah ta saki murmushi kafin tace “Masha Allah Allah ya nuna mana me yayi saura ai ya gama gininsa Allah yasa albarka yasa abokiyar arzikinsa ce yana d’akima ba lafiya” Dahda ya mi’ke “ai naje na duba shi ina shigowa zainabu ta fad’a min Allah ya bashi lafiya yace min stress ne yayi masa yawa Imran ne akwai son kud’i baya son hutawa” mommah tana dariya tace “kyan d’a ya gaji ubansa”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-15


Tun daga lokacin Imran ya tattara shatu ya watsar a gefe baya shiga shirginta sam ko a waje ya ganta baya zama idan kuwa yana waje tazo da sauri yake barin wajen. Hakan da yake yi kuma sosai ya fara damun zuciyar shatu bata so ba sam bata so ya daina shiga lamarinta ba haka kawai take son ta dinga ganinsa tana jin muryarsa da kuma kyakykyawan murmushinsa, hakan yasa ko da yaushe take zama a main parlour kawai don yas shigo ta ganshi taji’kamshinsa ta kuma ga kyakykyawan takunsa da yake yi tamkar a cikin izza bata san daliliba haka kawai IMRAN AHMAD MANGA yake burgeta. Ba wai soyayya take nufi ba tunda har a lokacin bata san so ba kawai dai burgeta yake tsaftarsa kallonsa tafiyarsa maganarsa komai Imran manga yayi burge shatu yake sosai har cikin zuciyarta ba mamaki hakan yana da ala’ka da zamowarsa d’an uwanta kuma jininta wanda duk duniya bata da na biyunsu. Ganin ya daina shiga shirginta itama ta tattarshi ta watsar ta kama Ammar abinta da uncle d’inta Hisham da kullum suke tare indai suna gidan.

Tuni ta mayar da hankalinta akan karatunta both islamic da boko bata wasa burinta ta zama mai ilimi ta kuma iya english kamar yarda taga su Anty hafsa suna yarawa abin yana burgeta yana sata nishad’i, hakan yasa take damun mommah da zancen ita kuma mommah ta dafa kanta tace “sha kuruminki shatun mommah zaki iya turanci da ko bature england sai ya sara miki” hakan da mommah take fad’a shi yake ‘kara mata ho’b’basa taji tana so tana kuma zakwad’i da karsashin son zamowa baturiya mai yara english ba gargada ko tuntu’ben harshe. Sosai take dagewa lamarin har tsoro yake bawa mommah ganin yarda ta mayar da karatu abokinta ko da yaushe zaka sameta da littafi na islamiyya da na boko. Tsoron mommah d’aya kada karatu ya sa ‘kwalwarta ta’buwa don haka sau tari take ‘kwace littafin ta saka mata kallo ko tace tayi barci ko na rabin sa’a ne kwanyarta ta samu hutu.

Tuni su hafsa suka tattara suka koma Abuja saboda yawan damunsu da hajiya mama take da yawa akan hutun ya isa, kullum fad’a take tana ‘karawa “ Ba hauka bane abin ku tattaro komatsanku ku dawo nima ina bu’katarku idan bikin yazo kwa koma tunda dai bata da wasu sha’ki’kan da suka wuce ku” hakan yasa dole suka tafi zuciyarsu cike da tausayin mommah ganin yarda kishiya da dangin miji suka sakata gaba. Koda suka gayawa hajiya maa murmushi kawai tayi kafin tace “haka rayuwar ta gada ba yarda bawa zai zauna ‘kalau bai jarrabeka ba idan kaga Allah baya jarrabarka ma ka binciki kanka balle d’iya mace a gidan miji taya kuke zaton zata samu aljanna a ‘bagas ai dole ne a jarrabeta ko ta’bangaren kishiya uwar miji ko dangin miji, ‘ya’yansa ko d’ungurungum mijin ma gaba d’aya babu wata mace da zata ce salin Alin tana rayuwarta ‘kalau tsakanin bawa da ubangiji godiya kawai a duk yanayin da ya tsinci kansa don haka ta godewa Allah tunda mijinta na sonta saura kuma ta barwa Allah ta sha mamakin hukuncinsa ai hukumullahi la ajabun.”


Wata d’aya ya rage biki a kuma lokacin ne ‘kannen Ahmad manga mata masu ji da kansu suka iso gidan d’an uwansu da set d’in akwatinan lefe za’a wuce dasu dangin uban shaheeda da suke Abuja.

Mamaki ne ya hana momma magana da suka samu a sashenta suka ce taje taga lefen da Imran ya had’a. Baki sake take kallonsu kafin ta furta “shi Imran d’inne ya had’a lefe ba tare da sanina ba saboda bai mayar dani uwa ba ko mai?” Tsaki hameedah tayi tana tauna chewingum sai kuma ta tintsiro d’ankwalinta gaban goshi tana watsawa momman kallon raini tace “yo da ke har wata tsiya kike d’aukan kanki d’a dai kin haifa amma baki isa kice zaki juya shi ba wannan kam sai yarda muka ga dama kin dai juya ubansa mun’kyale ki yanzu kam the table

Don haka muka saka dole ya auri shaheeda mu juya shi son ranmu kema ki d’and’ani rad’ad’in da mu kaji da kike juya yaya manga ki taso kiga lefe idan kinga zaki iya idan kuma ba haka ba kya gani a jikin surikarki kuma ‘yar kishiyarki shaheedah.” Ran mommah ne ya ‘baci har ta gagara ‘ko’karta furta ko kalma d’aya ce ga hameedah yarinya ‘yar cikinta da take tsaye take mata fitsara. Suma duka sauran ba wanda bai furta albarkacin bakinsa ba sannan suka juya suka tafi suna dariya da shewa burinsu ya cika sun ‘batawa mommah baiwar Allah zuciya. Tsahon lokaci tana zaune a wajen ta kasa mi’kewa tufka take a ranta kawai da warwara tabbas idan ba’a yi wasa ta bari a kayi aurennan zasu ci galaba a kanta za kuma suyi duk abinda suka ga dama hawan jini suke neman cusa mata da ciwon zuciya,ita bata ga abinda tayi musu a zahirance da bad’inance kawai dai ‘kiyayya ce suke mata su kansu da basu san asalinta ba balle tushenta. Ya zama dole tayiwa tufkar hanci lefe dai ba zata je ta gani ba kuma Imran zai zo ya sameta zata nuna masa ita d’in nan dai itace wacce ta haifeshi ta d’au cikinsa wata tara ta kuma shayar dashi nononta na tsawon watanni sha takwas.

Tsawon lokaci mommah na zaune a parlournta ranta a matu’kar ‘bace ta gaji ta gaji da tozartawa da wulakancin dangin miji, mafita kawai take nema tun daga parlournnata tana jiyo su tana jiyo ba’ka’ken maganganu da suke jefo mata masu kama da gugar zana hakan ya ‘kara hassala zuciyarta taji kuma zata iya komai don ‘kwatowa kanta ‘yancinta ciki kuwa har da samowa Imran aure ko da a cikin d’iyoyin friends d’inta zata nuna musu tana da iko da d’anta kuma ba wata shegiya da zata yi mata tin’kaho da d’anta alhali sanda tayi na’kudarsa ko wacce cikinsu tana can shanye da baki tana barci.lokaci yayi da zata farka daga barcin da take ta amshe matsayinta na uwar d’a mai cikakken iko akansa fiye da kowa a duniya.

Shigowar shatu ne ya farkar da ita dogon tunanin da ta tafi, shatu da hanzari ta ‘karasa wajenta ta dafa takanta ganinta cikin damuwa, tana son mommah jinta take tamkar innaji don haka sam bata son ‘bacin ranta kuma zata iya gogawa da kowa idan har yace zai shiga gonar mommah.murya can ‘kasa tace “Mommah menene meye ya sameki? Wad’ancan mutanen ne ko?” Momma ta girgiza kai tana janyo shatu jikinta “Bakomai shatu yau naji ina burin dama ke budurwa ce da ma ke kin kai muzalin aure da ba abinda zai hanani aurawa Imran ke da nayi alfahari da haka”shatu ta zaro ido “aure mommah ai nayi ‘karama” Murmushi mommah tayi kafin ta furta “shi yasa a zancena kika ji nace dama, duk da haka ba matsala insha Allah ba zan rasa wacce zan ‘karawa Imran a matsayin mata ta biyu ko da hakan yana nufin za’a yi tashin hankalin da ba’a ta’ba yi ba da wad’ancan mutanen” shatu ta ja ajiyar zuciya tana kallon mommah da hawaye yaso zubo mata ta kuma tabbatar na zallar’bacin raine. A zuciyarta ta ‘kudurce tabbas sai tayi maganin mutanennan a yau kuwa ba sai gobe ba taji itama a zuciyarta dama ita d’in budurwace a aura mata Imran da kuwa tayi sa’a kuma sai taci uban shegiyar shaheedan mai goshi kamar fitilar jirgi dama ta tsaneta tunda sanda ta ganta a kanainaye a jikin Imran. Shigowar Imran ne da ‘kamshin turarensa ya sata kai idonta kansa yayi kyau sosai cikin wani black yard african attire d’inkin zamani bai kai gwiwaba haka nan hannunsa gajerene kuma rigar tad’an kama shi kad’an an yi masa ratsin light brown daga gefen aljihun da kuma rigar ta lura yana son irin kayan yawanci shigarsa kenan yayi kyau sosai duk da kansa ba hula. Bai ko kalli sashen da take ba ya ‘karasa inda mommah take fuskarta a had’e sosai. Zama yayi sosai kusa da ita yana dafa kafad’arta had’e da zubawa shatu harara, kafin ma yayi magana ta mi’ke don ta san ma’anar hararar tasa ta shige bedroom d’inta murya can ‘kasa tace kyau kamar aljanni sai zallar ba’kin hali”.

“Please mommah na mai ya faru ne naga fuskarki ba walwala? Kuma su anty fannah sunce kije kiga lefe kin ‘ki why mommah?” Kallonsa tayi kallon cikin ido kallone da tun suna yara suka san tana yi musu idan sunyi mata babban laifi. Da sauri ya rusinar da idonsa baya jurewa wannan kallon baya son sa yana razana shi ya kuma san duk sa’in da mommah tayi shi ranta ya kai ‘kololuwa a ‘baci “ please mommah am sorry duk da ban san laifina ba” “ sorry for what Imran? You are sorry because ka wula’kanta ni ka nunawa duniya bani da amfani a wajenka ka nunawa duniya dani da babu ni you can make decisions about anything aurenka Imran ace sai dai ace nazo naga lefe? Ana yar min da magana baka neman albarkata baka damu da farincikina ba ko da yaushe sai ‘bacin raina nagode kaje ka yi aurenka kaje mutanen da kake tunanin zasu baka farin ciki su baka fiye da wanda ni zan baka Allah ya sanya albarka a aurennaka but put this in your mind bani ba ‘yan uwana a bikinka ba zamu zauna muga ‘baci rai ba.” Daga haka ta mi’ke ta shige d’aki jikin Imran ne yayi sanyi ji yake kamar yace ya fasa baya son ‘bacin ran mahifiyarsa bai san me yasa zuciyarsa ta kasa ha’kura da shaheedah ba, tsawon lokaci yana zaune kafin shatu ta fito tana ‘yar wa’karta ta “uwa tana da girma mahaifiya tai mini komai” da sauri ya kalleta gani yake kamar da shi take da shi d’in kuwa shatu take amma ya kasa ta’buka komai yana juya kalaman wa’kar shatu a zuciyarsa.

Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai wajen mai gadi, da murmushi y tareta don yana son shatu musamman yarda take girmamashi ga kyauta akai akai “uwata ta kaina ya aka yi?” Ya fad’a yana mata murumushi shatu tayi ‘kasa da muryarta “Baba taimako zaka yi mi please amma bana son kowa ya sani” ya girgiza kai “ shatu danger yau kuma wa ya takaloki?” Dariya tayi kafin murya can ‘kasa tace “wasu ‘kadangarun bariki zanyi magani ga dubu biyu ‘kai’kayi zaka siyo min don Allah” Baba ya ware ido “Aa fa shatu’kai’kayi kuma mai zaki yi dashi?” Ta had’e rai idan ba zaka taimakeni ba shikkenan bara na tafi” ganin tayi fushi yasa yace “zo uwata zan taimakeki ai ba zan’ki mai taimakona ba” ta mi’ka masa kud’in tana dariya.

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-16

ELEGANT ONLINE WRITERS…..

Baba murmushi ya saki “ko waye ya shiga gonar uwata? Ko ma dai waye ya jawowa kansa yau” Baba mai gadi ya furta a hankali yana jinjina girman al’amarin shatun.

Tun yamma ta dinga zagaye gidan har ta tabbatar da windown ko wane d’aki sannan hankalinta ya kwanta taje ta ‘boye ‘kai’kayinta a ma’ajiyar da ta tabbatar babu mai ganinsa,sannan ta cigaba da harkokinta tamkar babu komai a zuciyarta.

Tana general kitchen ita da masu aikin gidan amaryar Imran ta shigo sai wani iyayi take da rawar ‘kafa.shatu ta zabgawa harara kafin ta bud’e fridge tana duban masu aiki “Imran yace kuyi masa abinci ne?” Ta tambayesu cikin kallon raini. Saratu ta girgiza kai “ai dama bamu muke masa abinci ba daniel ne kuma tun wancan satin ma ya dakatar da daniel ko ruwan tea zai sha naga a kitchen d’in mommah yake dafawa da kansa.” Kallon one by one tayi musu tana yatsine fuska “Ba dole ba,ba dole ya daina cin abincin gidannan ba gida duk an tara gayyar ‘kazamai dama zuwa nayi inyi warning d’inku kada wacce ta sake yi masa abinci ni da kaina zan dinga yiwa mijina abinci bana son ya dinga cin na kowani ‘kazami.” Shatu tsayawa tayi tana kallonta sai kuma ta tuntsire da dariya ta kalli saratu tace “saratu bani aron muciyarku akwai abinda zan gwada da ita” ta fad’a tana yiwa shaheedah kallon sama da ‘kasa ita bata ga abinda Imran ya gani a jikin wannan ba ‘kafafu kamar sillan kara. Shaheedah ranta yayi ‘kololuwar ‘baci da sauri ta cafko shatu ta fara wanketa da mari shatu ta daka tsalle ta rama sannan ta shiga ‘kar’kashinta ta tad’eta ta fad’i hakan yasa shaheedah ‘kwalla ‘kara ina shatu bata saurara mata ba ta hau kanta ta shiga lugude a ruwan cikinta. Masu aiki suna gefe sai dariya suke sun ‘ki rabawa saratu a zuciyarta fad’i take dai-dai kenan shegiya mai girman kan tsiya. Ihun shaheedah ne ya karad’e gidan hakan yasa duk mutanen gidan suka yiyo general kitchen d’in ban da mommah da take wanka. Da sauri su kayi kan shatu suka fara jibgarta tun tana ihu har muryarta ta dashe gefen bakinta da goshinta ya kumbura suntum. Ihun shatu ne ya fito da momma daga toilet riga kawai ta zira ta fito a guje dai-dai lokacin Imran ya dawo kenan shima ya juyo ihun yayi yo cikin gidan da sauri yabi bayan mommah. Momma ta tarar dasu har a lokacin dukanta suke sun mata jina-jina su saratu sai ihu suke suna fad’in zasu kasheta. Da sauri momma tayi kukan kura ta ‘kwaceta bayan ta dubesu ranta a ‘bace tace “mai tayi muku? Mai tayi muku zaku yi mata wannan hukuncin?””an daketa d’in ko zaki rama mata ne ita har ta isa ta doki shaheedah ta kwana lafiya wacece ita a gidan?”muryar tsagera hameedah ce mai wannan tsaurin idon tana fad’a tana yiwa mommahn wani banzan kallo. Imran kansa sai da yayi mamaki Ammar kuwa da ya shigo yanzu yaji furucin hameedah akan mahaifiyarsa bai san sanda ya waska mata mari ba. baki bud’e kowa yake kallonsa babbarsu falmata tace “kana hauka ne Ammar ‘kanwar ubanka ka Mara?” Ita dinma wani kallon banza yayi mata yace “‘kanwar ubana tafi uwata ne?nawa hameedan take ina ce shakara biyu ta bani shekara nawa tawa uwar ta bata da zata gaya mata magana?” Yana fad’in haka yaja hannun shatu da mommah suka fice daga kitchen d’in bayan yayiwa Imran kallon banza,yana tsaye ana zagin mahaifiyarsa ya kasa d’aukan mataki.

A bakin gado ya zaunar da mommah idanunta kawai yana zubar da hawaye, hakan ya ‘kara tunzira zuciyarsa ya mi’ke a zuciye zai fita mommah tayi saurin ri’ke hannunsa tana girgiza kai tace “kada kaje Ammar hakan ma da kayi nagode maka ko bakomai yau na san na haihu ka ‘kwatar min ‘yancina Allah yayi maka albarka d’auki shatu ka kaita clinic ayi mata dressing ciwukannan.” Kallonsa ya mayar kan shatun dai-dai lokacin da Imran ya turo ‘kofar ya shigo, murya can ‘kasa yayi sallama, Ammar jan hannun shatu kawai yayi suka fita sam baya son ma ganin d’an uwannasa gani yake kamar an canja musu shi Imran mai zuciya Imran mai tsananin son mommah mai gudun ‘bacin ranta, yau shine ya zama haka a gabansa ake cin mutuncin uwarsa ya kasa magana ya kasa kata’bus.Yana kallo suka fice ya bisu da kallo da ajiyar zuciya, sannan ya samu gefen mommah ya zauna, kansa ya d’ora a kafad’arsa wasu ‘kwalla da bai san na menene ba suna ‘ko’karin zubo masa, ya kama hannun mommah murya can ‘kasa furucin “Am sorry mommah” ya fito daga bakinsa, bata kalleshi ba illa d’auke kai da tayi “kiyi ha’kuri ita ma yarinyar bata kyauta ba na tambayi masu aiki sun gaya min duk yarda aka yi ita ta kwatantata da muciya saboda raini ita kuma tayi saurin hannu ta mareta bata san wannan yarinyar ba ‘kyaleta za tayi ba, ko ta’kyaleta a lokacin sai ta nemo abinda zata rama gaba kad’an please momma kiyi ha’kuri amma kiyi mata fad’a” wani kallo mommah tayi masa sannan ta zare hannunta “wacece yarinyar sunanta ne baka sani ba ko kuwa canja mata suna kayi Imran anya kuwa jininka ce fa ita,duk duniya ku ya kamata ku nuna mata gata tunda bata da wasu sha’ki’kan y’an uwa kazo kana ce min wani bata kyauta ba, rashin kyautawar mai tayi? ‘Dirka-d’irkan mata su zauna suyi mata jina-jina sannan ace wani bata kyauta ba to ba ha’kura nayi ba wallahi wannan karan sunyi da y’ar halak ni kad’ai kuma Na san abinda zan musu tashi ka bani wuri mai kayan haushi kawai ka zo ka cika ni da wani zancen banza da wofi zanyi maganinku ne gaba d’aya daga kai har dangin ubannaka sai na shayar daku mamaki.” Imran zuba mata ido kawai yayi ya ma kasa magana sam ba ya son hayaniya d’abi’ar dahda tsaf ya d’auko shi yasa yaji har kansa ya fara ciwo. Jan pillow yayi kawai ya kwanta a gadon mommahn ya ri’ke kansa da yake d’an sara masa.
Mommah ta dubeshi kawai tayi tsaki ta mi’ke ta bar masa bedroom d’in tana cigaba da ‘kananan maganganunta.

Koda dahda ya dawo duk da girkinta ne ranar ko ‘keyarta bai gani ba, tana part d’inta ta tasa shatu a gaba tana lalla’bata ta sha peppe soup ko kad’an ne kafin tayi barci. Amma shatu fir ta’ki yau zuciyarta a hassale take da ‘bacin rai sun riga sun kai zuciyarta ‘kololuwa a ‘bacin rai duk ‘ko’karin mommah da Ammar haka suka gaji suka ‘kyaleta suka zuba mata ido sai ajiyar zuciya take saukewa tana hura hanci.

Gefe d’aya kuwa amaryar dahda zainab ta saka shi a gaba tana gaya masa ‘karya da gaskiya a gaban y’an uwansa ta tattara lefin gaba d’aya ta d’orashi kan baiwar Allah mommah, Dahda kawai jinsu yake yana girgiza kai ya san abinda matarsa zata yi ya san wanda kuma ko da kuskure ba zata aikata ba.Da ya gaji da ji mi’kewa yayi ya shige part d’insa ransa a ‘bace shi yasa ko da wasa baya son danginsa su ziyarceshi. Sai da yayi wanka sannan ya fara jera kiran mommah a waya amma ta’ki picking,gaba d’aya jinsa yake kamar maraya ta riga ta’bata shi ta sangarta shi baya iya ta’buka komai ba tare da taimakonta shi wannan auren matsala babba Hajja ta gangamo masa sam a tsarinsa bashi da niyyar ‘kara aure. Ganin ta’ki picking calls d’insa hakan ya sashi mi’kewa ya dangana ga part d’inta.

A zaune ya sameta kan sallaya ta d’ora kanta a saman gado tana jan carbi fuskarta da alamar ‘bacin rai sosai. A hankali ya taka wajenta ya zauna a gefen gadon, motsinsa ne ya sata saurin d’ago da kai su kayi four eyes lallausan murmushi ya sakar mata yana dafa kanta yace “Haba Dija na me ya faru? Yau ko ‘yar sannu da zuwan ma babu.” Still fuskarta a d’aure ta mi’ke ta fara nad’e sallay sai kuma hawaye sharr ya biyo fuskarta ta dur’kushe a gabansa ta kife fuskarta a cinyarsa ta saki kuka, kuka mai cin rai da tunda yake bai ta’ba ganin dijansa nayi ba. hankalinsa ne ya tashi da sauri ya dafa kanta sannan ya mi’ke tsaye ya d’agata rungume ta yayi sosai yana fad’in “yi shiru ki gaya min menene me suka yi miki?” A hankali yake fad’a mata cikin cool voice. Dijah kukan take sosai kafin ya fara wiping tears d’inta a cikin wani salo na matu’kar soyayya da son cooling zuciyarta. Shi kad’ai yasan yarda kukan dijan yake d’aga masa hankali “Don Allah Dija kiyi shiru ki fad’a min wai menene? Bana son kanki yayi ciwo please.” Ganin damuwa ‘karara a fuskarsa ya sa ta tsagaita kukan nata ta fara bashi labari, tana gamawa ta d’ora da fad’in “don haka dahda na gaji a wannan karan dole ne a san abin yi ko Imran ya fasa auren can da aka ‘kir’kireshi don a wula’kanta ni ko kuma ya had’a da za’bina ko kuma wallahi na bar gidannan don ba zan zauna ba’kin ciki ya kamani ba zuciya ta ta buga Allah ne kad’ai yarda nake jin ciwo a zuciyata kullum matsalata dangin miji sun saka kayi aure ka auri ‘yar uwarsu ban ce komai ba ko bakomai hajja tana da iko da kai to nima a barni nayi iko da nawa d’an idan kuma ba haka ba na bar maka gidan ka zauna da duk wacce suke so ka aura,amma dole wannan karan nima Imran yabi umarnina a matsayina na uwarsa da ta kawosho duniya.” ‘Kuri manga yayi mata da ido ganin yarda take masifa wai dijan sa ce haka dijan sa mai ha’kuri mai sanyin hali ita masifar danginsa yasa ta juye ta koma masa mai fad’a, sam bai ga lefinta ba ya tabbata an kaita ma’kura dama ance shi mai ha’kuri bai iya fushi ba a duk sanda aka ‘kureshi dole yayi mata abinda take so ko don ya faranta mata zuciyarta ta sauka daga fushin da take idan ba haka ba yana tsoron yana tsoron ranar da zata fara mayar da martani ga hajja, ya san tabbas abin ba zai yi kyau ba.Hannunta ya kama yana matsawa a hankali,murya ‘kasa-‘kasa yace “It’s enough ‘yan mata na dijan manga gaya min mai kike so ayi?” Murmushi ta saki zuciyarta na rage zafin da take mata, ta haka manga yake samo lagonta a duk sanda tayi fushi shi yasa basa dogon fad’a suke shiryawa. Ta gyara zamanta a jikinsa tana masa kallon cikin ido “in dai manga na yana son ganin farin cikina to ya amince da ‘kudirina ta haka zaka’kwato min ‘yancina a wajen ‘yan uwanka so nake ka aurawa Imran shatu ya had’asu su biyu ta haka kawai zan nuna musu power ta nima na dasa musu ba’kin cikin da suka dasa min ba dai shatu bace ba sa so to ita zata zama kishiyar d’iyar tasu ‘yar so.” Kallonta yake cikin nazarin anya tana cikin sense d’inta idan ban da haka wacce shatun? Wannan ‘yar ‘kwailar bayan haka ta san ko sama da ‘kasa zata had’e Imran ba zai kar’bi shatu matsayin mata ba amma bari ya tambayeta wacce shatun take nufi? “Wai wacce shatun kike nufi dijah?” Ya fad’a yana sake ‘kure ta da kallo, dariya ta saki tace”au muna da wata shatun ne bayan ta gidan nan shatu na nake nufi shatu da suka yiwa duka saboda ta ta’ba d’iyar gold to ita nake nufi” girgiza kai manga yayi shima yana murmushin yace “amma dai wasa kike ko? Idan ban da haka wannan yarinyar da bata wuce 14 ba za’a yiwa aure banda haka ma kin san halin d’anki ba yarda za’ayi ya amince da wannan batun.” Momma ta marairaice fuska tana kwanciya a kafad’arsa tace “please dahda don’t say No kai kad’ai ne last hope d’ina kaga dai da kayi aure ban ce maka komai nayi ha’kuri duk da zuciyata na hurting sosai kullum a haka nake kwana amma na san dole ne kabi umarnin hajja indai kana son ganin daidai please ka cika min burina don Allah ka amince.” Tausayinta ne ya kamashi ya fara shafa bayanta amma shifa yana tsoron lamarinnan ya san halin Imran da ba’kar zuciya ban da haka ma yarinyar is too young “
Dijah ba fa wai na’ki bane ‘kan’kantar shatu nake dubawa bana son ayi abin da za’a tauye mata ha’k’ki matsayinta na marainiya kada mu cuceta ta yama zata iya kishi da shaheedah apart from that ma ta ya kike zaton Imran zai amince da auran shatu?” Murya can ‘kasa tace “shi yasa bana so ka fad’a masa ya zama sirri tsakanina da kai so nake sai dai suji an d’aura da shatu kawai ko bakomai nima power ta ta uwa ta fito Ba kuma tarewa za tayi ba har sai ta gama school, shi kuma Imran ka barni dashi na san ta yarda zan ‘bullo masa shekaru kuwa ba abin ji bane duk da ba tarewa za tayi ba mutanen da ma a shekarunta tuni sun jima a d’aki. Ni dai abinda nake so da kai kawai ya sirri tsakanina da kai nima anan ko ‘yan uwana ba zan gayawa ba insha Allah sai dai suji” d’aga mata kai yayi “zan cika miki burinki dija na ko don ki cigaba da kasance min sanyin idaniya ta yanzu tashi muje ki bani abinci I have gists for you” ya fad’a yana kashe mata ido d’aya. Shi yasa kullum manga yake narka mata da zuciyarta take kuma kishinsa don ya san salo salo na kama zuciyar mace.

To fa masu karatu ya zata kaya ne kun amince ayi auren ko a barshi tabbas dai akwai rigima kwantacciya.😂Imran mijin shatu ko ya zata kasance? Ku biyo ni next month insha Allah na tafi hutu typing wahala

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-17

ELEGANT ONLINE WRITERS…..

Cikin daren kamar an mintsineta ta mi’ke duk da jikinta da yake ciwo hakan ba zai hanata aiwatar da ‘kudirinta ba a karo na barkatai ta sake kaiwa dogon mudubinnata ziyara,shatu ta sake ‘karewa ciwuwwukan da suka ji mata kallo cikin matsanancin ‘bacin rai ta girgiza kai muryarta a dashe tace wallahi ba zaku kwana lafiya ba ayau yarda kuka saka ni ‘bacin rai sai na hanawa idanunku barci. Ta isa inda ta ajiye ‘kullin ‘kai’kayinta tana murmushi “yau akwai rawar asosa casss a gidannan” sai kuma ta tuntsire da dariya murya a ciki tace “mu zuba ni daku shege ka fasa” ko takalmi bata saka ba don kada mommah taji takunta ta fice daga part d’in mommahn cikin sand’a.

Duk windows d’in bedrooms d’insu ta dinga zugewa a hankali tana hura musu sai kuma aka ci sa’a duka gadajennasu a jikin windows suke sai da ta taka abu sannan tsawonta ya kai.tana gama hura musu tayi saurin juyawa ta shige general parlour karaf suka ci karo da Imran zai shiga sashensa bayan ya gama aiyukan da zaiyi a system d’insa a parlourn,da sauri ya kai dubansa kanta har zaiyi magana sai kuma ya ta’be baki ya shige part d’insu, shi yanzu tsoronta yake ji sosai ba ya son ya fad’a tarkonta. Shatu tayi murmushi kawai ta shige part d’in mommah tana jira a fara rawar asosa.
Tana zaune kuwa a gefen gadonta ta fara jiyo iface-iface a general parlour ihu sosai Ta jiyo hakan ya sata fitowa daga d’akinta sai taga mommah ma da dahda sun fito daga d’akin mommah. Momma da sauri tace “koma ciki shatu ke da baki da lafiya bari muje muga menene” bata so hakan ba amma hakan ta zauna kan kujera.bayan dahda ya kalleta yayi mata alamar t zauna.
A parlour suka samesu gaba d’aya sai ihu suke har da masu ludaya da
Cokula suna sosawa. Shaheeda kuwa daga ita sai guntuwar vest sai ihu take tana kiran Imran ya taimaka mata shi kuwa yana tsaye yana mamakin mai ya samesu tabbas ya tabbata shatu ce tayi musu ramuwar gayya saura ‘kiris ya saki dariya a karo na farko da lamarin yarinyar ya daina bashi haushi sai dariya, yarinya sai shed’ananci kamar zuriar shaid’anu.Dahda da mommah fad’i suke “subhanallahi mai ya faru?” ‘Kannen dahda sai cewa suke ya taimaka musu jikinsu kuwa yayi rud’u-rud’u salati dahda yasa yace suje su suturce jikinsu su tafi asibiti.amma ina lamarin ya girmama har da masu birgima a ‘kasa. Ammar ne yace “Dahda anya ba aljannnun gidan nan bane suma suka shafesu kmar yarda suka yiwa hajja” dahda ya girgiza kai ba mamaki ammar yanzu dai kira doctornmu ya dubasu” shi dai Imran yana daga gefe sai murmushi yake yana hango kuma shatu data la’be bayan ‘kofa tana zabga dariya kamar yace ga babbar aljannahr can sai dai yaja bakinsa yayi shiru kada ya jawowa kansa daga ruwan hammata ta bashi ruwan tsarki.

Kafin doctor yazo haukane kawai ba suyi ba sai da Ammar ya shigo ya sanar dasu shigowar doctor sannan Imran ya kalli shaheeda ransa a ‘bace yace “Go and cover your body ko kunya baki ji” wani kallo ta watsa masa kafin tayi magana doctor ya shigo da sauri Imran ya dafa kansa ya jata ya turata d’aki yana tsaki. Ko da ta shiga d’aki hijab kawai ta zira ta sake fitowa a guje. Doctor ya gama dubasu sannan ya fito da allura ya fara yi musu don dama dahda yayi masa bayanin ciwon. Sai kusan ‘karfe 4:00 na dare sannan abin ya lafa musu amma fa sunji jiki duk jiknnan yayi luhu-luhu balle idonsu.basu koma d’akunansu ba don suna tunanin tabbas aljannun ne tun da a d’akin da hajja take sauka suka sauka yau kam sun gasgata zancen hajja. Jin shigowar su mommah yasa shatu shiga d’aki da sauri tana tuntsira dariya. Amma mamakinta d’aya me yasa Imran bai tona mata asiri ba karo na biyu kenan yana kamata da irin wannan.shi kansa Imran tunda ya shiga d’aki yake smilling shi kad’ai ya lura yarinyar nan comedian ce ta bugawa a news.

Da safe ma basu koma d’akin ba a sashen amarya suka koma zama suna sake la’antar mommah don a cewarsu aljannu take turo musu ai kuwa indai sune su zuba su da ita gida dai baza su barshi ba sai sun kai kwanakin da suka ‘kayyadewa kansu tunda a goben zasu tafi abuja kai lefe. Hameedah tana sake girgiza ‘kafa ranta a matu’kar ‘bace tace “wallahi wannan matar muka ‘kyaleta nan gaba raba mu za tayi da yaya manga gaba d’aya dole mu tashi tsaye a kanta mu har a gaya mana malamai mu da
Muku jinin barebari.” Falmata ma cewa tayi”wallahi kuwa naga alama kuma lefe tayiwa kanta tunda hajja tace mu kai kada ma mu nemi danginta wallahi kaiwa zamuyi ke kuma shaheedah sai kin dage sosai duk abinda muka kawo miki kada kiyi wasa dashi munyi al’kawarin sai mun dasa mata ninkin ‘bacin ran da ta sakawa manga sai mu zuba mu gani tana ji tana gani Imran sai dai ta hange shi daga ness” gaba d’aya suka saka shewa har da amarya zainab. Fanna na gyara zama tace mai yafi wannan takaici ace d’anka yana auren ‘yar kishiyarka kuma zainab ke kin samu d’a daga sama kamar yarda uwarta ta samu manga daga sama suke juya mana shi son ransu.” Dariya suka ‘kara yi.

Ko da ta gama shirin school tana fitowa general parlour ta gansu murmushi ta saki ta fara wa’kar ado gwanja ta casss. A harzu’ke suke kallonta,Hameedah ta mi’ke da sauri tana jifanta da wani irin kallo “ke don uwraki da wa kike?” Shatu rausayar da kai tayi gefe kafin tace “kawai don ina wa’kata sai ki zageni” fitowar Imran da Ammar kenan sunyi shirin fita su ka ji hameedah tana wallahi sai na sake jibgarki kamar yarda nayi miki jiya shegiya mai idon aljannu.” Imran waro ido yayi yana kallon hameedah mamaki fal ransa lalle bata san sharrin yarinyar nan ba bata san itace gayyar aljannun da suke wajigasu ba, har shatu ta karkace zata yi rashin kunya Ammar ransa a ‘bace ya jata “wuce ki tafi school tun d’azu driver na jiranki kin tsaya jan magana.” Baki ta zun’buro irin na shagwa’ba “Yaya Ammar uwata fa ta zaga.” Harara ya zuba mata “kin wuce ko sai na mangareki tayi ta zaginki ma yana tsiro ne? Oya maza-maza wuce school kafin na sameki a wajen” sum sum ta wuce har taje ‘kofa ta juyo da ‘karfi tace “an fad’a d’in a sosa cass a sosa iya da razor.” Imran bai san sanda murmushi ya ku’buce masa Ammar kuwa darawa yayi sosai yace “kai shatu danger” hameedah kuwa ‘kwafa tayi tana zabgawa Ammar harara.

Kashegari kuwa suka isa abuja dangin baban shaheeda suka kai lefe ba tare da dangin mommah ko d’aya ba duk da kuwa suna cikin abujar. Haka suka dawo da sha tara ta arziki duk da suma ba lefen wasa suka kai ba lefene na gaske na gani a fad’a na kuma d’orawa a instagram,a yayata a duniya. Biki kuwa aka saka shi sati uku cif don suma dangin uban shaheedahn a shirye suke tsaf kuma masu farcen susa ne tabbas kuwa za’ayi biki na kece raini. Bayan sun dawo kano da kwana d’aya suka wuce maiduguri hannayensa dam’ke da sha tara ta arziki. Mommah ba tace musu Komai ba duk da ta tambayi Hajiya mama kuma ta tabbatar mata ba a gaya musu kai lefen ta basu ha’kuri. Hajiya mama ta girgiza kai a cikin wayar tace”Lala lala dijah ke zan bawa ha’kuri kiyi ha’kuri da jarrabawar da Allah yayi miki ta fitinannun dangi miji kina zaune ubangiji zaiyi miki sakayya suma fa mata ne kuma sun haifi mata ki zuba musu ido yanzu ubangiji ai tun a duniya yake sakayya ba kayi ba ma anyi maka ina ga kayi kiyi ha’kuri kullum shine abinda zan iya ce miki.” Hawaye ya zubowa mommah sai dai ba ta nunawa hajiya mama kuka take ba tayi godiya ta kashe wayar a zuciyarta tace “akwai ranar ‘kin dillaci ranar da zata cusa musu nasu ‘bacin ran dole ne su girbi abinda suka shuka d’a dai nata ne kuma ba zata bari su juya shi kamar yarda suke muradi ba.


A hankali awanni suka yi ta shigewa suna zama kwanaki daga kwanaki kuwa,har satittikan biki suka zo gidan a hargitse yake kowa sai shiri yake ana ji da lamarin bikin to ba dole ba ta kowane side jikan farko kuma d’an gaban goshi ake yiwa Aure,tun ana saura sati biki dahda yasa shaheedah dole ta koma gidan babanta duk da ba haka suka so ba uwarta taso ta tsaya ta cigaba da banka mata mallakin mallaka sai dai dole ta tafi. Hajja ma ana saura satin tazo ta tare a part d’in dahda daga gefe a babban parlournsa akwai wani bedroom and toilet anan ta baje danginta kuma suna d’aki mai Aljannu.

Mutanen katagum ma sun hallara ciki kuwa har da Dada tsohuwa mai ran ‘karfe. Tuni mommah ta fara gyara d’iyarta tsaf fatarta ta goge a spa haka nan an yi mata saloon gashin nnan an jawo shi tsahonsa har da na Mamaki.

Suna dawowa daga spa a gajiye suka tarar Hajiya mama tazo ita ma da ‘yan uwanta na yola ga Hafsa da Nahna da sauri shatu ta rungume uncle Hisham shi kuwa duk da nauyin da tayi masa haka ya shiga wulwulata yana fad’in a cafe a cafe ‘yar gidan mommah mai mommah ke baki ne kika yi wani fresh har glowing kike?” Kayan dad’i” ta furta tana murmushi har hushiryarta ta fito. Still Ammar yayi yana kallonta har bakinsa ya gaza shiru yace “mommah ‘karin gashi kika kaita aka yi mata da wankin fata?” Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba Hafsa tace “Ammar ko dai kana ciki ne a d’aura gobe da kai kawai.” Girgiza kai yayi “Ina ni ina rigimar shatu ni ‘kabilar ibira ma zan aura sun fi iya kula da miji” shatu ma harara ta zabga masa Allah ya kiyaye ma in aureka kayi fari da yawa ni nafi son irin Yaya Imran wanda baya magana sosai kai kuwa surutu kamar parrot.” Dariya sosai parlorn duka suka ganin Imran yana tahowa yana ware ido alamar yaji zancenta sarai. Tamke fuskarsa yayi ya zuba kallonsa akan shatu da tayi saurin jan gyale ta rufe fuskarta alamar kunya tsaki “kada ma ki saka rai da samun irina ke ai irinki Ammar d’in ne ya dace dake sai kuje ku haifi parrots d’in”Dada tsohuwa ta ta’be baki “Yo Allah na tuba kada dai inga mutum yazo yana ‘yar murya kana ganin yarinya zankad’aziyya wanke hannu ka ta’ba da mai matarka ta ka tafi ta to ku ku zama shaida ko nan gaba kada Imran yazo yace a bashi balarabiyar nan.” Tsaki yaja yana mi’kewa “MAI ZAN YI DA ITA? Ni kuwa God forbid gayyar ‘kazanta da surutun tsiya Ina da mata ta ‘yar gayu ta bugawa a jarida.” Ran shatu ne ya ‘baci tun da take bata ta’ba jin haushin kalamansa ba sai yau hawaye ya fara bin fuskarta.

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-18

ELEGANT ONLINE WRITERS

Sosai take hawayen saboda kalaman Imran sun ‘bata mata rai. Momma ta jata jikinta da sauri tana jifan Imran d’in da harara “fice min daga nan tunda burinka ya cika ka saka shatu kuka yo itama su’butar baki Tayi idan banda haka mai za tayi da kai a haife ka haifeta tunda ka ninka shekarunta.” Ficewa yayi ba tare da yace komai ba Allah ya tsari gatari da saran shuka” ya raya a zuciyarsa.

Ana gobe kamu masu tafiya abuja suka dinga dandazon tafiya dangin mommah dai ba suje ba a cewarsu bikin namiji suke zo ba ruwansu da dangin mace sun san ma kun sunje wula’kanci zasu sha,gida ya d’ad’e ba kowa daga mommah sai danginta suke Ta tsara yarda bikinsu zai kasance.Juma’a ne d’aurin aure don haka ranar asabar za suyi dinner lahadi suyi bud’ar kai ango ma alhamis d’in zasu wuce da abokansa da suka zo daga wurare da dama wasu ma ba ‘yan ‘kasar nan bane.

Don haka yau part d’insu na samarin gidan a cike yake sosai don ma babban parlour ne sai bedrooms guda hud’u a ciki don gidan dahda ba dai girma ba gari guda ne. Tana zaune a gefen dada tsohuwa tana shan dariyar labarin da dadan take bata na Imran da yake yaro yana tsoron saniya ita kuwa sai dariya take su antynta nahna suna zaune suna cire mata jan lallen da akayi mata na salatip ba ‘karamin kyau yayi ba ya haskaka kyakykyawar ‘kafarta ta.tana mi’kewa mommah Ta shigo parlourn tana dubanta daga ita sai wata riga da tsayinta yaje mata gwiwa sai skinny black pant ajikinta gashinta kuwa an tufke mata shi guda biyu ya sauka har fin gefen Kafad’unta duk da ba kwalliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu”maza jeki ki kira wo min yayanku Imran” mommah tace tana zama a kujera had’e da ri’ke kai alamar a gajiye take sosai. Ba tare da jin komai ba shatu ta fice tana jin dada na ‘kwala mata kira amma tayi shiru dada tayi tsaki “kaji y’ar banzan yarinya a haka zata fita kai ba kallabi ke kuma dijah kina kallonta ta fara fa ‘kirgar dangi ita ko ta ido bata dashi ne? ‘yar nan” mommah murmushi kawai tayi “To dada nawa shatun take?” Dada ta girgiza kai “nawa take? Wannan d’irkekiyar budurwar ake kira nawa take yarinya ta fara ‘kirgamu yanzu haka ma ta fara al’ada” mommah ta girgiza kai “Bata fara ba wallahi dada ai da ta fara nima ba zan bari ta dinga zama haka ba na san shari’a ta hau kanta” “zancen banza shari’a kuma ta yaushe tunda ga abubuwa nan sun fara bayyana” ita dai mommah shiru tayi tana jin dada na ta masifa.

Ta dad’e tsaye tana knocking a ‘kofar ba a bud’e ba
ga hayaniya ta cika gurin,ba tare da tunanin komai ba ta tura ‘kofar ta shiga. Sai kuma sannan tayi turus ganin maza duk kunya ta lullu’beta gashi duk sun zuba mata ido gaba d’aya ta diririce,idonta akan Imran da yake zabga mata harara cikin ‘bacin rai yace “fice daga nan kafin inzo nan shashasha kawai ko kunya ba kya ji wai ma mai kika zo yi?” Idonta ya kawo raurau za tayi kuka haka kawai taji tana son yin kuka ganin kallon da suke binta dashi tana ji masu fad’ar masha Allah na fad’a masu cewa wow na fad’a. Da sauri ta fara wasa da hannunta kafin tace”mommah ce ke kiranka” tana fad’a ta fita a guje ashe shatu an fara girma ana tsoron maza tana ji suka tuntsire da dariya d’aya daga abokansa yace “Imran manga wannan wacece?” Kallo d’aya yayi masa yace “Sister”duk ido suka zuba masa abdul yace “Na zata baku da sister mace koma dai menene gaskiya babyn ta had’u ina ciki.” Sai aka d’au hayaniya guri kowa yana fadin bai isaba suma suna so Aliyu da yafi kowa serious ya dafa shi “Don Allah Imran ya kuke da yarinyar nan ni dai na san ku biyu ne kacal a gidannan” mi’kewa yayi yana gyara wristwatch d’insa fuska a d’aure yace”cousin” daga haka ya fice amsa kiran mommah a zuciyarsa ya furta “mayun mata abin nasu kuma har da ‘kwailaye”yana jin su suna sake yaba surarta Ali yana cewa yarinyarnan idan ta girma wallahi za’a ja kaya musamman idan ta samu kula ni wallahi ya dawo ko yanzu ya raka ni wajen mommah na nemi aurenta. Imran murmushi kawai yake yana tafiya don ya san basu san wacece shatu ba.
Tana jikin mommah a kanainaye kamar ta shige ciki ya lura tana da son jiki kamr mage.mommah na ganinsa tace “Yauwa Imran abincinku nace ya za’a yi dashi?” “Momma wannan yarinyar me yasa take fita haka kai ba tie” mommah harara ta watsa masa “Ga maganar da nake maka kana min wata banzar magana” dada Ta gyara zama “a to kai ma dai ka fad’a kai da yake kafi uwar taka hankali nayi magana ance yarinya ce wai wannan baligar ce yarinya?shiga sai kace a garin ‘kedarai to ni da ban isa ba ance yarinyace ai ‘kafata ‘kafar yarinyar nan don na lura uwarka lalata ta za tayi ta sangarta ‘ya kullum tana cinya kamar mai shan mama to ba dani ba.” Hajiya mama dai sai murmushi take.Imran ya shige kitchen yana cewa “ki rabu dasu dada gashi nan ai samari sun fara kawo mata farmaki ba sun ganta da shigar banza ba.”Dada ta zabga salati “kai Imrana ka rantse da Allah mhmnn to dai wallahi Allah ya kyauta lamarin uwarka ni kuwa ‘kafata ‘kafar bararo wallahi”dariya yayi yana shigewa kitchen a zuciyarsa yace Ai gwara ki d’auketa wallahi dada.

Ko da ya koma zancen dai Ali ya ya tayar masa tsaki yayi “ku dai Allah ya shiryeku duk ‘yan matan garinnan ku rasa ta kulawa sai wannan ‘kwailar” Abdul tsaki yayi “Ai wallahi Imran kayi ba’kar dabara ya za’a yi da wannan a gidanmu inje neman auran wata ba zaka zauna ka jira wannan d’in ka kiwatata kaje kana auren wata ‘kemasashshiya zubin turawa ga zubin larabawa haba Alhaji wallahi ka cuci kanka.” Imran ya masa wani duban banza”God forbid Allah ya kiyaye kai ka sanni ka san waye ni kuma ka san burina na auren matured wacce ta san ciwon kanta kuma mace mai tsafta ba kuma na san mace mai tsananin kyau saboda bana son ko wani rubbish ya dinga kai idonsa kan matata so wannan bata cikin layin matan da nake so mace mai kyau ai hatsarice.” Gaba d’aya ta’be baki suka yi suna kallonsa su basu ta’ba jin mutum ma mai irin ra’ayinsa ba.Ali yace “Allah ya raba mu da auren mummuna mun fi son kyakykyawa ta shiga taro.”Imran tsaki yayi “Allah ya kyauta sai ku shirya kar’bar ciwon hawan jini don ba abinda ‘kananan yara zasu saka muku idan ba su saka muku hawan jini ba.”

Ranar Alhamis da daddare su hajja suka dawo saboda ranar juma’a ne d’aurin aure kuma sun fi son su kar’bi amarya da kansu. Ko kallon arziki ba wanda yayiwa su mommah da suke zaune a general parlour suna tayi musu sannu da zuwa, a ciki suke amsawa Hajja zube a parlour ana Ta d’aga kai ‘kafa d’aya kan d’aya tana ‘karewa Hajiya mama kallon banza ita dole sai dai Ta nuna gidan d’anta ne. Hajiya mama da yake bata iya fad’a ba ta mi’ke tana kallon mommah da dada tace “Dada muje daga ciki ku barsu su huta.”Dada ta girgiza kai “oh oh babu inda zani anan zan zauna ina kallon mai shige da fice to ina dalili zaki turani can ciki ban san mai duniya take ciki ba wanda yaga ba zai iya zama ba shi dai ya tafi amma dada kam zama daram”Hajiya mama ba tayi magana ba tayi shigewarta d’aki.dama su nahna basa nan sun tafi kar’bar d’inki tana ji hameedah na shewa tana cewa “Oh Hajja aure dai ya d’auru Allah yaso ba’a ruguza shi da surkullen fulani ba” Hajja ta masa “Da wallahi kuwa” Mommah tana jinsu ta shige kitchen ranta a ‘bace tasa masu aiki suka kai musu abinci daga haka Ta shige part d’inta wajen Hajiya mama tana dialling call d’in dahda.

Da daddare kuwa ta sake jaddadawa dahda burinta Na son d’aura auren gaba d’aya a gobe “ka d’aura a can abujan kawai dangin Ubanta ba matsala bane daga baya ta kaini har garin nayi musu bayani duk da dai basu damu da ita ba da sun damu da ita ai da sun biyo sahu.”Dahda yayi murmushi yana jan hannunta “Your wish is my command Dija na I do as you said.” Murmushi tayi tana had’a goshinsu waje d’aya.

RANA BATA ‘KARYA

Dandazon mutanene suka halarci d’aurin auren a babban masallacin Na garin Abuja, duk inda ka juya jama’a ce Imran fuskarsa d’auke da fara’a at last dai zai mallaki burin ransa shaheedah da ya dad’e yana mafarki a matsayin matarsa matured mai tsafta kuma ‘yar gayu kuma ‘yar ‘kwalisa kamar yarda yake son matarsa ta kasance. Suna zaune shida abokansa suka ji an fara shelar za’a d’aura auren ayi shiri jama’a. Ai kuwa cikin yardar Allah aka samu ba’kuncin shiru mai shela bayan mintuna kad’an ya shela cewar an d’aura auren Imran da Haleemah shaheeda akan kud’in miliyan d’aya lakadan ba ajalan ba Alhamdulillah Imran ya fad’a a zuciyarsa Finally angon shaheedah inji abokansa sai kuma suka ji an sake d’aura auren Imran da Aysha mujittafa……. gaba d’aya abokansa suka waro ido suna kallonsa shi d’in ma kallonsu yake….

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-19

ELEGANT ONLINE WRITERS….

Ina mi’ka d’umbin godiyata ga masu karatun littafinnan nagode ‘kwarai da gaske da soyayyar da kuka nuna min da littafin me zan yi da ita?burina dama saka nishad’i a zuciyarku. Ina alfahari daku I Really appreciated wallahi, da zan iya da na mayar dashi 2pages kamar yarda kuka bu’kata, to hakan ba zai yiwuba ina da scheduled da yawa so am sorry kuyi ha’kuri dani a hakan har muje inda zamu. Nagode sosai.


Aliyu ne ya dafa Imran yana dariya “Amma lallai guy d’in nan ka raina mana hankali yanzu dama mutum biyu zaka aura baka gaya mana ba” Abdul ya girgiza kai yana murmushi yace “wonderful ni bama wannan ba how comes kai da baka son hayaniya ka auri mata biyu ina cika bakin da kake mana na cewa mace d’aya ta isheka?” Yana jinsu duk suna surutunsu ya kasa furta komai zallar tunani da zuciyarsa ta tafi,sai zufa yake tunani yake wacece ita wacece ma wata Aysha da aka d’aura masa aure bai sani ba, tabbas ashe kuwa tayi shirin zama bazawara don sam bai ga dalilin da zai sa ya amince da mace har biyu ba. Koma waye ya bawa dahda wannan gurguwar shawarar. Tsawon lokaci zuciyarsa ta kasa hasasho masa shatu ce yarinyar gaba d’aya zuciyarsa ma bata hasasho masa shatu ba tunani yake a cikin ‘ya’yan abokan dahda da suka mayance masa cewa suna sonsa aka d’auki d’aya aka bashi. Bai cewa abokansa komai ba duk da surutan da suke masa, burinsa yaga dahda ko Ammar amma ba d’aya da ya gani,hakan yasa dole suka shiga motocinsu suka tafi masauki.Imran dai ya zama tamkar mutum mutumi.

Amarya shaheedah kuwa a bakin yayyenta maza da suka dawo dga d’aurin aure ta samu labari.shaheed da ya shigo a rud’e ne ya dafa ta murya can ‘kasa yace “How comes shaheedah duk cika bakin da kike yi ba zaki zauna da kishiya ba sai gashi ko tarewa ba kiyi ba angonki ya auri wata zai had’a ta dake.” Shaheedah da bata d’au zancen serious ba ta zabga masa harara “God forbid don Allah shaheed ka daina wannan wasan bana son sa as per as am alive ko kallon ‘yan mata ba zan bar habibi yayi ba balle kishiya over my death body” shaheed murmushi yayi kafin khalil ‘kaninta yace “ai kuwa kin makaro don kuwa mata biyu aka d’aurawa aure da habibinnaki ke da wata Aysha.” Da sauri shaheedah ta mi’ke tana kallonsu “please don Allah kuce min wasa kuke?what a nonsense?” Khalil da shaheed suka sake tabbatar mata haka nan sauran mutane da suka je d’aurin aurenma suka tabbatar mata,dalilin da yasa ta yanke jiki ta fad’i, tuni nmufashinta ya d’auke,hakan yasa da sauri aka rufu akanta ana ‘ko’karin ceto ranta.

‘Yan kano kuwa tuni labari ya riski zainab ta hanyar mutane masu sanar da ita fad’uwar shaheedan da dalilin fad’uwarta ta.cikin tsananin mamaki take cewa “mata biyu a haba dai ba kuji da kyau ba idan kuwa hakan ya tabbata tabbas duk wacce tayi ‘ko’karin zama kishiyar shaheedah tayi shirin riskar ba’kin cikin da zai zama ajalinta wallahi.” Da sauri ta mi’ke ta nufi General parlour inda Hajja take.tun kafin ta furta komai hajja ta tabbatar da ba lafiya ba don yanayinta ya nuna ‘karara. Da sauri Hajja ta mi’ke da niyyar ta jata su samu sirri don ganin dada a zaune da itama ta kasa ta tsare, amma ina zainab tuni ta furta abin da ya ri’ke mata ma’kogaro “Hajja da gaske ne? Da gaske ne Imran mata biyu aka aura masa da wata wai Aysha wacece ita?” Gaba d’aya gurin zaro ido su kayi, musamman Hajja da maganar tayi mata dirar mikiya, da sauri ta girgiza kai “wannan ba gaskiya bane ba yarda za’ayi manga ya zartar da wannan hukuncin bai gaya min ba sharri ne da surutu irin na d’an Adam” zainab ta girgiza kai “Hajja babu fa batun sharri a wannan zancen it’s true naji a bakunan da ba zasu min ‘karya ba kuma sun halarci d’aurin auren ga shaheedah canma ance ta sume daga kin zancen.” Hajja ta ja ta zauna ja’bar a kujera “To wacece yarinyar aka ce miki idan kuwa zancennan ya tabbata tabbas manga zai ga ‘bacin raina kuma Imran dole ya saketa koma wacece zancen banza zancen wofi kenan, ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa.” Mommah dake zaune murmushi kawai take zubawa ta tabbata yau gidannan akwai show idan har suka san wacece amaryar.tana kallonsu suka shige d’aki bayan hameedah ta tunatar dasu zancen a sirri ya kamata ayi shi.Mommah ta ta’be baki a zuciyarta tace “oho dai burina ya gama cika.”

Kowa burinsa Dahda ya dawo yaji ya gaskiyar lamarin yake.ko su Hajiya Mama mommah bata gayawaba ta ja bakinta tayi shiru tana jiran kowa yaji labarin kamar dirar mikiya tunda ta lura har yanzu basu san da shatunta aka d’aura aure ba.

Shi kuwa Imran yana can asibiti ya tasa shaheedah gaba da kallo da take ta kuka bayan farkowarta,ta kuma tabbatar da lamarin gaskiya ne.sai ga Imran ya ‘bige da jinya madadin hotunan d’aurin aure da suka ci burin aiwatarwa,irin dai wanda ake yayi a social media d’innan.
Kukan take sosai da har ya ‘karawa Imran zazzafan ciwon kai,ya kama kannasa ya ri’ke tun yana rarrashin ta da yi mata rantsuwar ta kwantar da hankalinta koma wacece idan ya tabbatar da auren sakinta zai yi kuma da gaske yake.amma ina shaheeda bata ji shi ba,hakan yasa kawai ya kama hannunta yana murzawa alamar rarrashi idanunsa a lumshe. Haushi ma lamarin ya bawa abokansa yanda take kuka kamar a kanta aka fara kishiya.Tsawon lokaci sannan aka sallamesu bayan ta gama shan drip.ana komawa gida Abbanta yace ta bari ta warware a kaita. Suna ke’bewa da Imran tace yace kawai a kaita please Imran anty na nake son gani kawai ko zuciyata tayi sanyi.” Tausayinta yasa Imran gayawa wata ‘kanwar babanta cewar a kaita kawai ta ‘karasa warwarewa a gidanta.
Haka kuwa aka yi babu ‘bata lokaci aka tafi airport dama sun yi booking jirgi.amarya dai ta tafi fuska ‘kozai-‘kozai fuska ko kwalliya babu duk da burin da aka ci na budiri a wannan ranar.

Ana kaita ko ta kan mommah da danginta ba abi ba duk da tunasarwar da dangin ubanta suke musu amma Hajja ‘kememe ta’ki yarda tace “ku shige da ita d’akinta mai aka yi aka yi wata dijah balle danginta wa ya san surkullen da suka yiwa manga ya d’aura masa aure da wata yarinyar.ku kaita gurin uwarta ni ina nan ina jiran shigowar manga tunda ya’ki d’aga waya ta.”hakan yasa ba wanda ya sake bi ta kan uwar miji duk da al’ada ta shar’anta a bata damarta a kai mata matar d’anta. Hakan sam bai damu mommah ba tunda burinta ya cika.

Shi kuwa ango Imran yana cikin d’akinsa zuciyarsa sai suya ta keyi shi mamakinsa d’aya dama ana yiwa namiji auren dole? Yana jiyo abokansa suna ta dariyar shegantkarsu.

SHIGOWAR DAHDA

Yana dawowa ya tarar Hajja da jama’arta baje a parlourn,gefe d’aya ga Dada da tata jama’ar,zancen dai ya san ake hakan yasa bai san lokacin da murmushi ya ku’buce masa ba ya san sarai za’a rina,Dijah ta jawo masa rigima yau,da bai san yarda zaiyi solving d’inta ba. ya dur’kusa ya gaida su Dada sannan ya ‘karasa gefen hajja ya zauna, Da kyar take amsa gaisuwar da yake mata tana gama amsa gaisuwar ta d’ora da “meye gaskiyar labarin da naji game da aure biyu da akace an d’aurawa Imrana,wacece yarinyar da har ni ban isa kayi shawara dani ba?” Manga waigawa Yayi yaga Dijah bata wajen don haka ya ciro wayarsa ya kira ta yana kallon hararar da Hajja take masa ya cigaba da kiran Imran shima a waya,so yake su hallara duk ayi komai a gabansu. Tsawon mintuna mommah ta shigo da su Hajiya mama, sai ga Imran shima ya shigo jikinsa a sanyaye, ya zauna a gefen mommah, haka nan zainab da su shaheedah su hameedah suma duk suka bayyana.
Sannan manga ya gyara zama ya fara da “kamar yarda kuka saka Imran da shaheedah soyayya har suka amince da junansu suka ‘kaunar junansu haka ita ma Dijah mahaifiyarsa ta bu’kaci son a had’a Auren Imran da shatu yarinyar wajenta………

Idanu waje kowa yake kallonsa cikin tsananin mamaki.Imran kuwa zama yayi kamar statue yayi masa ‘kuri da ido kawai yana tunani shatu shi aka aura ma Shatu,shatun dai da ya sani ‘kazama shi kuwa mai zai yi da ita a yanzu ba sai anjima ba zai saketa wallahi yaushe zai iya wannan abin kunyar mai zai cewa mutanen da yake cikawa baki yana fad’in mai zai yi da ita? Ita kuwa shaheeda tuni ta zube a jikin hameedah ta ma kasa kuka sai sakin ajiyar zuciya take.
Imran murya na rawa ya fara ro’kon Dahda “please dahda wallahi bana sonta ko kad’an kada kuyi min haka zaku sa min attack wallahi don Allah ka amince Na sake ta.” “Wallahi Imran ka sake Na saki shatu sai dai ka sake uwa don wallahi sai na zare ka daga cikin ‘ya’yana Na gaya maka kada ma ka fara attempting zancen saki idan kuwa haka ta faru zan nuna wa kowa bad side d’ina wallahi an kaini ‘karshe” sosai kuwa yake kallonta saboda yarda take maganar da gaske take daga ‘kasan zuciyarta take fitowa, ranta a ‘bace idanunta kuwa yayi jajir.
Sai ji su kayi Hajja ta saki dariya muryarta a sama tace “Ai kuwa ba ki isa ba dijah ni kuma zan nuna miki nice uwar manga ko ki amince ya sake ta ko kuma ni na saka manga ya sake ki…….

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-21

ELEGANT ONLINE WRITERS……

Mommah ta kalli saratu “mai za tayi masa da yake nemanta?je ki ce ba zata zo ba idan ya matsu da son ganin ta shi ya shigo ya ganta a gaba na.” “Auzubillahi Wannan wace maganar wauta ce mutum da matar sa kice ba zai ganta ba wani yace ki d’aura musu Auren ?a’a ni ba za’a yi wannan d’iban albarkar dani ba tashi maza kije kafin in kai miki mangara da ido ‘kwala-‘kwala a wajen.” Shatu ta mi’ke tana duban dada da tace sai taje kanta ko d’ankwali babu ga rigar tata armless ce sai wani skinny jeans. Bayan saratu ta bi tana ta mita da zuciyarta wallahi ya gaya min ba’ka sai na gaya masa ‘kirin ai nima ba son auren nake ba.corridor d’in da ke hanyar kitchen saratu ta nuna mata ta wuce tana dariya ‘kasa-‘kasa. Shatu ta girgiza kai alamar zamu gamu. Tana shiga ta gan shi zaune a kan kujerar da take gaban working space na kitchen d’in mommah. Ya had’e rai sosai yayi folding hannayensa a ‘kirji kayan da suke jikinsa sun amsheshi sosai three quater black jeans da white T.shirt Kansa ya cukurkud’e kamar Na buzaye alamar bai samu gyara ba. tsaye tayi a gefe tana ta’be baki duk da ta san bai yi wanka ba amma gaba d’aya mayen ‘Kamshin turrensa ya game kitchen d’in.Ganin yayi mata banza yana mata kallon up and down yasa ta juya zata fice.murya a cunkushe yace “wallahi kika fita ba tare da na gama abinda Yasa nace ki zo ba zaki gane baki da wayo” juyowar tayi itama tana masa irin kallon da yake mata “to ka fad’i abinda zaka fad’a I have something to do.” Tsaki yayi yace “bar d’an guntun english d’inki ki je kiyiwa wad’anda basu sanki ba ba su san yarda kika zo ba burga dashi wai ni ban ga dalilin da yasa mommah ta ma’kala min ke ba ban ga komai tare dake ba banda ‘kwala-‘kwalan idonki kamar me”
Waro ido tayi tana dubansa dariya take sosai har ya ‘kulu kafin tace “exactly like your’s”bud’e idanunsa yayi sai kuma yayi tsaki “Ba wannan yasa na kira ki ba warning d’inki zanyi dama kada ki sake naga ‘kafafunki wajen dinner wallahi kika kika saka ran habibteey ya ‘baci zaki gane baki da wayo a wajen zanyi disgracing d’inki kina ji ai? Kuma ki san yarda kika yi ki ka sa mommah ta raba wannan auren ko ta yaya ma kuwa idan ba haka ba duk wula’kancin da kika tarar a gida na ke kika siya na gaya miki.” Sake kallonsa tayi ta turo baki “To ni ina ruwa na na gaya maka nima ina sonka ne kawai biyayya zan yiwa mommah idan kai kaga ba zaka yi musu biyayya kaje ka gaya mata baka so na sai me? Kuma wajen dinner sai naje sai dai kai da matarka muciya da zani ku ha’kura.” A zafafe ya taso zai kai mata cafka ta san kuma mai zai faru idan ta bari ya cafketa don haka tayi saurin fita a guje tana tuntsira dariya ta lura baya son ace muciya da zani ita kuwa ta samu nayi. Babu wanda tayi wa maganar ya hana ta dinner tana komawa d’aki Hafsa ta fara mata make up don ta iya make up sosai,kafin su tafi turkey karatu ma tana yin na kud’i a Abuja don haka ta fara tsantsara mata.
Shi kuwa Imran yana can yana ta faman kiran mommah ta’ki receiving so yake ya gaya mata bai amince shatu taje dinner ba tunda shaheedah bata so kuma yaga dai dinnerr ta Shaheeda ce.yayi mata missed calls ya kai goma bata d’aga ba,ita kuwa mommah tana ganin kiransa ta’ki d’agawa tana gaban Dahda da yake sanar da ita kawu sa’idu yace lallai-lallai shatu ta tare a gidanta ta zaro ido “amma why Dahda she is too young fa ba zata iya facinga marriage issue ba wallahi don Allah ka bashi ha’kuri bayan haka ma ga karatunta abin zai yi mata yawa.” Dahda ya ja ajiyar zuciya “kin san dai halin kawu sa’idu wallahi ba zan iya fuskantar fad’ansa ba,ki bar ta tare d’in idan yaso shi sai ya kula da harkar karatunta a kuma ja masa kunne kada ya sake yayi wata mu’amalar auratayya da ita.
Gaba d’aya mommah jikinta ne yayi sanyi, har sai da Dahda ya ri’ko hannunta yana matsawa a hankali “Don’t worry ba fa abinda
Zai faru insha Allah sai yanzu nake ganin wautar mu daga nia har ke da muka had’a aurennan zuwa nextweek ayi mata kamu da walima kawai a kaita Allah ya basu zaman lafiya zan tura miki 10million a account a siya mata komai da zata bu’kata a kaita d’akin mijinta haka Allah ya tsara kuma zanyi warning d’in Imran d’in dama ya barta tayi karatunta. Tashi kije ana ta kiranki.”
A sanyaye ta mi’ke kamar jira ake wayar Imran ta sake shugowa, a zafafe ta danna “wai Imran meye haka ne tunda ka kira kaji ban d’aga ba ai ka san a busy nake amma ka wani dameni da kira. Nace menene kayi shiru wallahi zan cutting wayar.”
Sakin ajiyar zuciya yayi murya a ciki yace “Am sorry mommah wai me nayi miki da zafi haka kullum kike min fad’a?” Tausayinsa ya kamata amma madadin ta nuna masa sai tayi tsaki “ina jin ka menene nace?” “Mommah favour d’aya zaki yi min don Allah yarinyar nan kada taje dinner.” Tsaki mommah tayi jin ko sunan ta baya iya fad’a saboda tsana “wacece yarinyar nan?” Shiru Imran yayi har mommah ta ‘kulu tace “duk sanda ka tuno sunanta ka kira ni muyi magana.” Ta kashe wayar.Imran ya dafe kai yana tsaki shi wallahi ko sunanta baya son furtawa. Amma ya zaiyi dole ya sake kira.tana d’agawa ya runtse idonsa “please mommah Aysha nake nufi.” “Oho saboda kada shatu villager ta ‘bata maka taro ko kuma a dinga nuna ta ana ga second wife d’inka ko to sai taje idan yaso idan tace ka tashi a gaban mutane da mic kace baka sonta shashasha kawai. ‘Dif tayi switching phone d’in off gaba d’aya ma. Imran ya cillar da wayar yana tunanin wata mafitar ran sa duk a ‘bace.Samu mafita ya saka shi sakin murmushi idan an san wata ai ba’a san wata ba shi yasan tsiyar da zaiyi mata.

Tsaf shatu ta fito tayi masifar kyau cikin makeup d’in da dressing d’in da aka yi mata pink lace ne da touches d’in maroum a jiki hakn yasa aka saka mata head maroum dinkin ya zaunu daram a jikinta duk da dai ‘kwailace inji Imran amma fa
Komai yaji don tafi waccen matar tasa muciya da zani 😂. Tafiyar da za tayi ma sai da Nahna ta koya mata sai zabga’kamshin turare take. Suka fita da su Hafsa don mommah da Hajiya mama dama ba zuwa za suyi ba. Ta windown bedroom d’insa ya hangosu, don haka da sauri ya ajiye babbar rigarsa da hularsa a saman gado ya fice da key d’in mota a hannunsa. A tsaye ya tarar dasu murmushin dole yayi yana duban Hafsa don ya san Nahna bala’i ce da wayonta sarai ba zata yarda da rainin hankalinsa ba. “small mom mu d’anyi magana ma na” bin sa tayi tana murmushi ganin yarda yake kallon shatu ita tunaninta mamakin kyan da tayi yake. “Waye zai kaiku ne?” Ya fad’a yana kallon Hafsa “wallahi Ammar muke jira wai ya tafi shiryawa” “okey ita wannan ku bani aronta zan kawo ta da kaina” Hafsa ta kalleshi “mhmn mhnn faof Big son kada ka jefa ni a trouble don Na sanka trouble maker ne”. Dariya yayi sosai “nothing will happen insha Allah kada kiji komai wannan jaririyar ma kawai dai kin sanni da kishi apart from that ma yanzu duka responsibility d’inta yana kaina tunda an shafa ko ba haka ba?” Hafsa ta ta’be baki “ni dai da ka barta” zuwa yayi yaja hannun shatu yana murmushi “muje ke” shatu tayi ‘ko’karin janye hannunta ta kasa ya matse shi gam ya kuma yi mamakin jin wani irin taushi a hannun kamar audiga. “Alhamdulillah” ya furta bayan ya shiga part d’insa ya tarar gayyar abokansa sun fita, turjewa shatu ta fara yi ya jata da sauri har suna had’e jikinsu ya tura ta bedroom dinsa jin ana bud’e bedroom d’in Ammar.suna shiga ya tura ta saman kujera yana murmushi “ba dai nace ba zaki ba ance sai kin je yanzu ai sai naga ta yarda zaki.” Turo baki tayi alamar zata yi shagwa’bar da ta saba, ya matsa kusa daf da daf da ita yana mata kallon cikin ido “wallahi kika fara min kuka anan sai kin gane kurenki ba dai ba kya jin magana ba? Sai in ga mai fita dake ai har da wani zuwa ayi miki shafe-shafe kayan haushi kawai in dai don ni kika yi to ba kiyi kyau ba look at your mouth kamar gidan tsutsa.” Shiru tayi masa zuciyarta Na ‘kuna yanzu duk wannan kwalliyar a banza aka yi kenan? Nocking d’in da ake ne Yasa shi saurin zira rigarsa don ya san shaheedah ce ya gyara hula yana fesa turare Ta mudubi yake yi mata dariyar mugunta ganin yarda ta ‘bata fuska ‘kiris take jira ta fashe amma taurin kai ba zai bari tayi kuka ba. Tana kallo ya bud’e bedroom d’in ya zare key d’in da sauri ya fita ya kulle ya rufe ta baya da key yana murmushin mugunta. Shaheedah da take tsaye ta zata ita yakewa murmushin ganin kyan da ta zuba.
Tayi kyau sosai cikin black dressing ya kama hannunta suka fita.to su shatu za’ayi dinner a d’aki kenan,yana fita shatu tasa kuka ta tuge d’an kwalin da sar’kar kuka take sosai kamar me gashi tana ta buga ‘kofa amma ba wanda ya jita hakan yasa ta zauna gefen gado,ga mararta ta fara ciwo ta kuma san period ne tunda tun last month dama ta fara,Allah yasa dama da pant d’inta da pad a jaka don mommah ta gaya mata in dai ta ga date d’inta yazo to ta dinga fita da shirinta,tana ji mararta na ta motsi ta zuba tagumi kawai.

Gurin dinner ya had’u an cika kamar me kowa yayi kyau an ci kuma an sha ana ta spray d’in kud’i, Hafsa da Nahna kuwa sai neman shatu suke ba ita ba labarinta, haka yasa hafsa taje kusa da Imran tana tambayarsa,murmushi yayi yace tace fa ba zata iya zuwa ba bata jin dad’i tana d’aki na.” Hafsa bata kawo komai ba ta juya jikinta a sanyaye tana tantamar zancen Imran a zuciyarta.

Ita kuwa shatu tana can ri’ke da mara ba tayi aune ba ta fara bleeding tana mi’kewq taga tayi masa staining bed sheet waro ido tayi a hankali tace “Na shiga uku” sai kuma ta ‘kyal’kyale da dariya “Allah ya ‘kara ni nace ya kulleni kuma wallahi ba zan wanke ba” kuma sosai yayi staining. Ta shiga toilet ta zame pant da under skirt d’inta ta yar a wajen sannan ta wanke jikinta a toilet seat d’in shima ko flurshing ba tayi ba ta gyara jikinta tsaf Ta fito tana dariyar mugunta.”Alhamdulillah nagode maka period da kazo yanzu.”
Ta koma saman bed d’in tayi kwanciyar ta daga d’ayan side d’in ‘kamshin turarensa da sanyin a.c ya gauraye ta lumshe ido barci tuni ya fara fisgarta.

Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shiga d’akin da suka sauka tayi shirin

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-21

ELEGANT ONLINE WRITERS……

Mommah ta kalli saratu “mai za tayi masa da yake nemanta?je ki ce ba zata zo ba idan ya matsu da son ganin ta shi ya shigo ya ganta a gaba na.” “Auzubillahi Wannan wace maganar wauta ce mutum da matar sa kice ba zai ganta ba wani yace ki d’aura musu Auren ?a’a ni ba za’a yi wannan d’iban albarkar dani ba tashi maza kije kafin in kai miki mangara da ido ‘kwala-‘kwala a wajen.” Shatu ta mi’ke tana duban dada da tace sai taje kanta ko d’ankwali babu ga rigar tata armless ce sai wani skinny jeans. Bayan saratu ta bi tana ta mita da zuciyarta wallahi ya gaya min ba’ka sai na gaya masa ‘kirin ai nima ba son auren nake ba.corridor d’in da ke hanyar kitchen saratu ta nuna mata ta wuce tana dariya ‘kasa-‘kasa. Shatu ta girgiza kai alamar zamu gamu. Tana shiga ta gan shi zaune a kan kujerar da take gaban working space na kitchen d’in mommah. Ya had’e rai sosai yayi folding hannayensa a ‘kirji kayan da suke jikinsa sun amsheshi sosai three quater black jeans da white T.shirt Kansa ya cukurkud’e kamar Na buzaye alamar bai samu gyara ba. tsaye tayi a gefe tana ta’be baki duk da ta san bai yi wanka ba amma gaba d’aya mayen ‘Kamshin turrensa ya game kitchen d’in.Ganin yayi mata banza yana mata kallon up and down yasa ta juya zata fice.murya a cunkushe yace “wallahi kika fita ba tare da na gama abinda Yasa nace ki zo ba zaki gane baki da wayo” juyowar tayi itama tana masa irin kallon da yake mata “to ka fad’i abinda zaka fad’a I have something to do.” Tsaki yayi yace “bar d’an guntun english d’inki ki je kiyiwa wad’anda basu sanki ba ba su san yarda kika zo ba burga dashi wai ni ban ga dalilin da yasa mommah ta ma’kala min ke ba ban ga komai tare dake ba banda ‘kwala-‘kwalan idonki kamar me”
Waro ido tayi tana dubansa dariya take sosai har ya ‘kulu kafin tace “exactly like your’s”bud’e idanunsa yayi sai kuma yayi tsaki “Ba wannan yasa na kira ki ba warning d’inki zanyi dama kada ki sake naga ‘kafafunki wajen dinner wallahi kika kika saka ran habibteey ya ‘baci zaki gane baki da wayo a wajen zanyi disgracing d’inki kina ji ai? Kuma ki san yarda kika yi ki ka sa mommah ta raba wannan auren ko ta yaya ma kuwa idan ba haka ba duk wula’kancin da kika tarar a gida na ke kika siya na gaya miki.” Sake kallonsa tayi ta turo baki “To ni ina ruwa na na gaya maka nima ina sonka ne kawai biyayya zan yiwa mommah idan kai kaga ba zaka yi musu biyayya kaje ka gaya mata baka so na sai me? Kuma wajen dinner sai naje sai dai kai da matarka muciya da zani ku ha’kura.” A zafafe ya taso zai kai mata cafka ta san kuma mai zai faru idan ta bari ya cafketa don haka tayi saurin fita a guje tana tuntsira dariya ta lura baya son ace muciya da zani ita kuwa ta samu nayi. Babu wanda tayi wa maganar ya hana ta dinner tana komawa d’aki Hafsa ta fara mata make up don ta iya make up sosai,kafin su tafi turkey karatu ma tana yin na kud’i a Abuja don haka ta fara tsantsara mata.
Shi kuwa Imran yana can yana ta faman kiran mommah ta’ki receiving so yake ya gaya mata bai amince shatu taje dinner ba tunda shaheedah bata so kuma yaga dai dinnerr ta Shaheeda ce.yayi mata missed calls ya kai goma bata d’aga ba,ita kuwa mommah tana ganin kiransa ta’ki d’agawa tana gaban Dahda da yake sanar da ita kawu sa’idu yace lallai-lallai shatu ta tare a gidanta ta zaro ido “amma why Dahda she is too young fa ba zata iya facinga marriage issue ba wallahi don Allah ka bashi ha’kuri bayan haka ma ga karatunta abin zai yi mata yawa.” Dahda ya ja ajiyar zuciya “kin san dai halin kawu sa’idu wallahi ba zan iya fuskantar fad’ansa ba,ki bar ta tare d’in idan yaso shi sai ya kula da harkar karatunta a kuma ja masa kunne kada ya sake yayi wata mu’amalar auratayya da ita.
Gaba d’aya mommah jikinta ne yayi sanyi, har sai da Dahda ya ri’ko hannunta yana matsawa a hankali “Don’t worry ba fa abinda
Zai faru insha Allah sai yanzu nake ganin wautar mu daga nia har ke da muka had’a aurennan zuwa nextweek ayi mata kamu da walima kawai a kaita Allah ya basu zaman lafiya zan tura miki 10million a account a siya mata komai da zata bu’kata a kaita d’akin mijinta haka Allah ya tsara kuma zanyi warning d’in Imran d’in dama ya barta tayi karatunta. Tashi kije ana ta kiranki.”
A sanyaye ta mi’ke kamar jira ake wayar Imran ta sake shugowa, a zafafe ta danna “wai Imran meye haka ne tunda ka kira kaji ban d’aga ba ai ka san a busy nake amma ka wani dameni da kira. Nace menene kayi shiru wallahi zan cutting wayar.”
Sakin ajiyar zuciya yayi murya a ciki yace “Am sorry mommah wai me nayi miki da zafi haka kullum kike min fad’a?” Tausayinsa ya kamata amma madadin ta nuna masa sai tayi tsaki “ina jin ka menene nace?” “Mommah favour d’aya zaki yi min don Allah yarinyar nan kada taje dinner.” Tsaki mommah tayi jin ko sunan ta baya iya fad’a saboda tsana “wacece yarinyar nan?” Shiru Imran yayi har mommah ta ‘kulu tace “duk sanda ka tuno sunanta ka kira ni muyi magana.” Ta kashe wayar.Imran ya dafe kai yana tsaki shi wallahi ko sunanta baya son furtawa. Amma ya zaiyi dole ya sake kira.tana d’agawa ya runtse idonsa “please mommah Aysha nake nufi.” “Oho saboda kada shatu villager ta ‘bata maka taro ko kuma a dinga nuna ta ana ga second wife d’inka ko to sai taje idan yaso idan tace ka tashi a gaban mutane da mic kace baka sonta shashasha kawai. ‘Dif tayi switching phone d’in off gaba d’aya ma. Imran ya cillar da wayar yana tunanin wata mafitar ran sa duk a ‘bace.Samu mafita ya saka shi sakin murmushi idan an san wata ai ba’a san wata ba shi yasan tsiyar da zaiyi mata.

Tsaf shatu ta fito tayi masifar kyau cikin makeup d’in da dressing d’in da aka yi mata pink lace ne da touches d’in maroum a jiki hakn yasa aka saka mata head maroum dinkin ya zaunu daram a jikinta duk da dai ‘kwailace inji Imran amma fa
Komai yaji don tafi waccen matar tasa muciya da zani 😂. Tafiyar da za tayi ma sai da Nahna ta koya mata sai zabga’kamshin turare take. Suka fita da su Hafsa don mommah da Hajiya mama dama ba zuwa za suyi ba. Ta windown bedroom d’insa ya hangosu, don haka da sauri ya ajiye babbar rigarsa da hularsa a saman gado ya fice da key d’in mota a hannunsa. A tsaye ya tarar dasu murmushin dole yayi yana duban Hafsa don ya san Nahna bala’i ce da wayonta sarai ba zata yarda da rainin hankalinsa ba. “small mom mu d’anyi magana ma na” bin sa tayi tana murmushi ganin yarda yake kallon shatu ita tunaninta mamakin kyan da tayi yake. “Waye zai kaiku ne?” Ya fad’a yana kallon Hafsa “wallahi Ammar muke jira wai ya tafi shiryawa” “okey ita wannan ku bani aronta zan kawo ta da kaina” Hafsa ta kalleshi “mhmn mhnn faof Big son kada ka jefa ni a trouble don Na sanka trouble maker ne”. Dariya yayi sosai “nothing will happen insha Allah kada kiji komai wannan jaririyar ma kawai dai kin sanni da kishi apart from that ma yanzu duka responsibility d’inta yana kaina tunda an shafa ko ba haka ba?” Hafsa ta ta’be baki “ni dai da ka barta” zuwa yayi yaja hannun shatu yana murmushi “muje ke” shatu tayi ‘ko’karin janye hannunta ta kasa ya matse shi gam ya kuma yi mamakin jin wani irin taushi a hannun kamar audiga. “Alhamdulillah” ya furta bayan ya shiga part d’insa ya tarar gayyar abokansa sun fita, turjewa shatu ta fara yi ya jata da sauri har suna had’e jikinsu ya tura ta bedroom dinsa jin ana bud’e bedroom d’in Ammar.suna shiga ya tura ta saman kujera yana murmushi “ba dai nace ba zaki ba ance sai kin je yanzu ai sai naga ta yarda zaki.” Turo baki tayi alamar zata yi shagwa’bar da ta saba, ya matsa kusa daf da daf da ita yana mata kallon cikin ido “wallahi kika fara min kuka anan sai kin gane kurenki ba dai ba kya jin magana ba? Sai in ga mai fita dake ai har da wani zuwa ayi miki shafe-shafe kayan haushi kawai in dai don ni kika yi to ba kiyi kyau ba look at your mouth kamar gidan tsutsa.” Shiru tayi masa zuciyarta Na ‘kuna yanzu duk wannan kwalliyar a banza aka yi kenan? Nocking d’in da ake ne Yasa shi saurin zira rigarsa don ya san shaheedah ce ya gyara hula yana fesa turare Ta mudubi yake yi mata dariyar mugunta ganin yarda ta ‘bata fuska ‘kiris take jira ta fashe amma taurin kai ba zai bari tayi kuka ba. Tana kallo ya bud’e bedroom d’in ya zare key d’in da sauri ya fita ya kulle ya rufe ta baya da key yana murmushin mugunta. Shaheedah da take tsaye ta zata ita yakewa murmushin ganin kyan da ta zuba.
Tayi kyau sosai cikin black dressing ya kama hannunta suka fita.to su shatu za’ayi dinner a d’aki kenan,yana fita shatu tasa kuka ta tuge d’an kwalin da sar’kar kuka take sosai kamar me gashi tana ta buga ‘kofa amma ba wanda ya jita hakan yasa ta zauna gefen gado,ga mararta ta fara ciwo ta kuma san period ne tunda tun last month dama ta fara,Allah yasa dama da pant d’inta da pad a jaka don mommah ta gaya mata in dai ta ga date d’inta yazo to ta dinga fita da shirinta,tana ji mararta na ta motsi ta zuba tagumi kawai.

Gurin dinner ya had’u an cika kamar me kowa yayi kyau an ci kuma an sha ana ta spray d’in kud’i, Hafsa da Nahna kuwa sai neman shatu suke ba ita ba labarinta, haka yasa hafsa taje kusa da Imran tana tambayarsa,murmushi yayi yace tace fa ba zata iya zuwa ba bata jin dad’i tana d’aki na.” Hafsa bata kawo komai ba ta juya jikinta a sanyaye tana tantamar zancen Imran a zuciyarta.

Ita kuwa shatu tana can ri’ke da mara ba tayi aune ba ta fara bleeding tana mi’kewq taga tayi masa staining bed sheet waro ido tayi a hankali tace “Na shiga uku” sai kuma ta ‘kyal’kyale da dariya “Allah ya ‘kara ni nace ya kulleni kuma wallahi ba zan wanke ba” kuma sosai yayi staining. Ta shiga toilet ta zame pant da under skirt d’inta ta yar a wajen sannan ta wanke jikinta a toilet seat d’in shima ko flurshing ba tayi ba ta gyara jikinta tsaf Ta fito tana dariyar mugunta.”Alhamdulillah nagode maka period da kazo yanzu.”
Ta koma saman bed d’in tayi kwanciyar ta daga d’ayan side d’in ‘kamshin turarensa da sanyin a.c ya gauraye ta lumshe ido barci tuni ya fara fisgarta.

Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shiga d’akin da suka sauka tayi shirin

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-22

Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shige masaukinta tayi shirin barci ta kwanta sannan Ta samu Hajiya mama da zancen tariyar shatu kamar yarda su kawu sa’idu suka bu’kata “Hajiya mama kin ji bu’katar da suka zo da ita na son shatu ta tare nan da one week.” Hajiya mama da sauri ta kalleta “wani irin zance ne wannan ina ce dake mu kayi zancen nan kika tabbatar min baki saka nan da sahekara biyar ma zata tare ba,su waye suka zo da wannan batun nifa bana son mutane su ga muna tauyewa yarinyar nan ha’kkinta a fara zaton don marainiyace don haka ni ban amince ba na tabbata kuma Babanku ma ba zai amince ba.” mommah tayi ‘kasa da kai tace “wallahi Hajiya mama nima yanzu na fiki da na sanin aurennan ji nake kamar na warwareshi ban da kawu sa’idu ne ma yazo da maganar da tuni na gama solving d’in problem d’in to shi mutum ne kaifi d’aya da baya canja magana, shi ya gayawa Dahda yace a gaya min a bisa umarninsa yarinya ta tare ko nan da one week ne ba na son yaga kamar na nuna masa bai isa da yarinyar ba.” Hajiya mama ta girgiza kai kafin taja ajiyar numfashi tace “Tir’kashi ana wata ga wata yanzu shatu mai zata je ta aiwatar a gidan auren shekara sha hud’u da watanni ai an daina yayin wannan auren,wallahi dama da kinyi shawara dani tun a farkon fari ma ba za’a yi wannan auren ba yanzu mai gari ya waya? Kin san dai babu dalilin da zamu bad’awa wannan dattijon arzikin ‘kasa a ido dole mu amince da abinda yace tunda dai kina gani ranar shi yazo ya siya miki ‘yanci a gidannan dole mu amince Allah yasa haka shi yafi zama alheri a gareta,ikon Allah kenan idan banda haka ga iyayenta nan su hafsa ko maganar aurar dasu ba’a fara ba sai ita jaririya a kansu to Allah ne kad’ai ya san lamarin da ya ‘boye a bayan hakan sai mu bita da fatan alheri,amma ko nan gaba idan zaki aiwatar da abu ki dinga neman shawara don aikin mai shawara baya ‘baci kuma ko bakomai ba za’a zo ana dana sani ba Allah ya shige musu gaba yasa ace gwara da aka yi.” Murya can ‘kasa mommah tace “ameen ai insha Allahu ma zan ja kunnensa kada ya sake ya d’ora mata nauyin auratayya har zuwa san da za ta gama ko da secondary ne” murmushi mama tayi a zuciyarta tace “kayya ban da yaran zamani duk da dai aure ne aka yi shi ba da son junansu ba.” momma ta gyara zama tace”kuma da dada zan had’a ta su tare har zuwa san da
Zamu ga kamun ludayin zamannasu,Sannan ga babansu ua bada ten million yace a siya mata kayan d’aki suna cikin account d’ina.” “Kash ai da bai wahalar da kansa ba addarsu,kuma tabbas Na san Babanku fad’a zaiyi amma shikkenan kiyi masa godiya ai hannun ba zai ‘ki dad’i ba mu ma za muyi namu ‘ko’karin don Babanku yace kallon shatu yake kamar maryam gatan da maryam ba ta samu ba shi zai mayar kan shatu, zan kira shi nima da safe nayi masa godiya gobe sai ku fara shiga kasuwa da ‘yan uwanki ku siya mata kaya Na gani Na fad’a kayan da ko gidan waye za’a kai ba’a ji kunya ba zan wa Babanku waya anjima kad’an shima ya bada abin da zai bayar.” Momma tayi godiya ta mi’ke ta tafi wajen dahda don shima bai je dinner ba yace ba zai iya wannan rashin kunyar ta ‘ya’yan zamani ba. Hajiya mama kuwa d’an kwanciya tayi da niyyar cikin dare za ta tashi tayi nafiloli Ta sake ro’ka musu zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba don ita macece mai ibada kuma kullum addu’arta akan zuri’arta take.

Sai ‘karfe d’ayan dare dinner ta tashi duk da ango ya gaji amma kasancewar amarya tana ta girgizar rawa yasa dole ba’a tashi ba.rawa ce ta rashin kunya take ta yinta kamar yarda amaren zamani suke yi abin har mamaki ya dinga bawa jama’a musamman ango da abokansa. Da ya gaji ne ma ya mi’ke ransa a ‘bace ya fisgi Hannunta suka fice daga hall d’in dinnerr.zuciyarsa a cunkunshe da ba’kin ciki kasancewarsa mutum mai kishi, bai san ba abinda mutane suke kallo a jikinta ba.
Tun a mota kuwa ya dire mata kwandon masifa kamar zaici babu. Ita dai tayi shiru don ta san ta ‘bata masa rai. Yana packing kuma kallonta bai yi ba ya bud’e motar ya fita.jikinta a salu’be ita ma ta fito daga motar tana kallo ya shige part d’insu ta san ko ta bishi ba zai saurareta ba don haka ta wuce cikin gida da niyyar ta kira shi a waya ta bashi ha’kuri,tunda dai ta lura har lokacin aikin su bai kammalu ba.

Shi kuwa sauri kawai yake ya isa part d’insu ya fitar da shatu kafin friends d’inss suzo su same ta. Yana bud’e d’akin mamaki ya kamashi ganinta tana barcinta peacefully ya zata zai zo ya sameta tana kuka. Gashinta a baje a saman pillow. Ya tsaya yana kallonta kafin ya daddage ya d’aka mata duka. Da sauri ta tashi da addu’ar farkawa daga barci a bakinta kamar yarda mommah ta koya mata. Ta tsaya tana kallonsa ranta a ‘bace. Tsaki yayi “da halla mi’ke ki fice Min a d’aki kafin wani yazo ya ganki kin wani baje min a bed kina barci salon ki saka min virus,saura kuma Idan kin shiga ki gayawa mommah ni na hanaki zuwa wallahi sai na miki rashin mutunci dama tana tambayrki kice barci ne ya kwasheki kuma kanki Na ciwo shi yasa ba kije ba.” ta’be baki tayi kafin tayi magana ya ja hannunta cikin mita yake cewa “wuce muje na lura so kike sarakan maganar nan su ganki anan to ta Allah ba taki…..” sak yayi yana kallon abokansa da suke zaune a parlourn idanunsu a kansa a zuciyarsa yayi tsaki yace mayu kawai ya juya d’akinsa ya rufe gam da key. Dariya suka tuntsire da ita Ali da Abdul suka bi bayansa don tsokana sai dai suna zuwa suka tarar ya rufe bedroom d’in gam.Ali ya tuntsire da dariya “Bar magulmaci dama wa zai ce baya son wannan zu’ke’kiyar da gaba ma ba’a son kyan da za tayi ba.

Shi kuwa Imran dama ya san idan ya bar ‘kofa a bud’e yaga ta kansa don haka ya rufe. ‘Ko’karin cire kayan sa yake yana cire babbar rigar zai d’aura akan gado idonsa yayi masa kyakykyawan gamo da sauri ya ware ido yana kallon stain d’in da yake gadon sa da d’an ‘karfi yace “what?”lallai ma yarinyar nan ta gama raina ni ‘bata gurin nan tayi haka Allah yaso wani bai shigo ya gani ba, balle a zata disvirgining d’inta yayi.ya dafa kan sa zuciyarsa na tashi “wallahi yau shatu kin gama dani ina zan kai wannan kayan ‘kazantar ko masu aiki na bawa fassarar da zasu yi min kenan kai ya Allah wace irin yarinya ce wannan?” Tsaki ya sake ja ya fara ‘ko’karin yaye dubet d’in da bed cover d’in ya d’aga can dole yaje toilet ko idonsa ne ya rufe ya wanke ga shi bashi da hand gloves.iya gurin ya kama yana runtse idonsa, bud’e toilet d’in ke da wuya ya sake yin wani gamon da sauri yayi cilli da bed sheet d’in cikin sink amai na taso masa wannan wace irin ‘kazama ce yanzu kuma ita aka aura masa? Wallahi ba zai iya wannan ‘kazantar ba, idonsa a runtse yay flurshing toilet d’in yana yi yana ja
Mata Allah ya isa kamar wani ya sa shi. Ya saka harpic, yana sakin ajiyar zuciya a zatonsa ya gama amma ina juyawar sa ke da wuya ya ga undies d’inta zube a ‘kasa da sauri ya ja baya,kamar ba zai yi ba sai kuma yayi tsaki ba dolena nayi ba duk wanda na kira kamar na tarawa kaina jama’a ne kowa kuma da fassarar da zai yi masa.idanunsa a runtse shima undies d’in ya d’auke shi ya saka a toilet bin kafin da safe ya kira ta wallahi sai ta wanke masa toilet tsaf duk dama gobe zai bar gidan sai ta ci kanta ita kad’ai, da kyar ya wanke bed sheet d’in kawai don baya son yin wani cikin friends d’insa by mistake ya shiga ya gani wallahi da shima barin sa zai yi ta zo ta wanke to yana gudun ‘bacin rana kada ayi zaton wani abu yayi da ita shi kuwa Allah kada ya nuna masa wannan ranar da wani ido zai kalli jama’a bayan tarin cika bakin da yayi akan cewa MAI ZAI YI DA ITA. Yana gama wankewa ya cilla shi cikin washing machine sai sannan zuciyarsa ta dinga tashi ai kuwa ba ji ba gani ya dinga kwara amai sai da ya gama aman yayi brush yana gamawa ya fice da sauri murya a cunkushe yace wallahi ban yafe ba banza ‘kazama.😂 ya gyara gadonsa tsaf ya bad’e bedroom da turaren wuta da room freshner. Sannan ya fice parlour baya tunanin zai iya wanka a toilet d’in wallahi dole key ya d’auka a daren gwara yaje gidansa yayi wanka. Yana had’e rai ya fito, ai kuwa suna ganinsa Ali da shegantaka ya taso”wai ya aka yi ne yalla’bai mai amarya tazo yi part d’inka ko dai har ka fara sonta ne?”harara ya zabga masa “matseni in gaya maka” Abdul yace “ai abin bai kai na matsewa ba in dai wannan ne ai baya ‘buya abinda zamu gani ‘kunshe a mahaifarta muzo mu sha suna.” “Mtsww God forbid wallahi sai kace irin ku ai ni tunda nace muku ba abinda zanyi da yarinyar nan to kuwa zaku sha mamaki ba ku san waye Imran ba.” Dariya su kayi sosai suna kallo ya fice Ali yace “mhmn a dai juri zuwa rafi yalla’bai wata rana tulun zai fashe” Abdul ta tuntsire da dariya yace “d’an iska ranar mayar da martani ba.” Yana jin su murmushi kawai yayi ko don tanadin iskanci da suka yi masa ai ba zai kusanci yarinyar nan ba haka zai saketa wallahi da zarar shirinsa ya kammala. (To kowane shiri ne wannan mhmmn wani abin sai d’an gidan manga)

Ita kuwa tana bedroom d’inta bayan tayi wanka Night gown a jikinta da cup d’in tea a hannunta tana sipping a hankali so take ciwon marar da yake d’an damunta ya lafa mata. Hafsa ta shigo d’akin idanunta a kanta ta zauna a gefen gadon “wai ina kika shiga ne? Ban ganki wajen dinner ba?” Hafsa ta fad’a tana shafa kanta.
Murmushi shatu ta saki a karo na farko taji tana son rufa masa asiri saboda sam bata son haushinsa da mommah take ji tace “wallahi period pain ya hanani fita d’azu fa kamar na mutu dole kuwa nayi kwanciyata side d’in su Ya Imran.” Hafsa ta girgiza kai “ashe da gaske yake wallahi na zata ‘karya yake har na had’a shi da mommah sai kije ki wanke sa a wajen mommah don wallahi ta kunnu da yawa cewa take zai zo ya sameta don ma Hajiya mama tana hanata tace ba huruminta bane da tuni ta kira shi ta sulle shi sai kije ki wankeshi.” Shatu ta mi’ke ta tafi wajen mommah. Tsaf ta wanke shi kuwa mommah ta jata jikinta “oh am sorry daughter to da kika yi zamanki a can hope ba abinda yayi miki kuma kin sha magani?” Daga kai tayi tana kwanciya a cinyar mommah da take feeling d’inta kamar Innaji she really love mommahnta to the extent.

Da safe Dahda ya shiga wajen hajja gaishe ta da kyar take amsa gaisuwar. Sister’s d’insa ma duk suka gaisheshi anan yake sanar da Hajja tariyar shatu ita ma kamar yarda kawu sa’idu ya tsara sati mai zuwa Hajja ta ta’be baki”To ni yanzu ina ruwa na nayi magana kaje ka yayata ni a bakin duniya ai ba abinda zance maka manga aje Allah yayi albarka gobe-gobe ma zamu tattara komatsanmu muyi gaba ba kuma zamu sake dawowa ba kamar yarda ka bu’kata kuma ina son ka jini da kyau dama ka samu fili ka siya ka fara yi min gini anan kano duk san da na tashi zuwa na dinga zuwa can na sauka na san mallakina ne. Shashasha ana yi maka gata baka san gata ake maka ba duk an mallakeka da
Surkullen fulani.” Murya can ‘kasa Dahda yake amsa mata “Insha Allah Hajja za’a Gina,amma tafiyar da kun bari wani satin idan shatun ta tare.” Hameedah mai son ganin ‘kwaf ta gaban Hajiya ta saka baki “eeh Hajiya mu bar shi wani satin idan ta tare sai mu tafi cab amma za’a ga ‘kwailar amarya ai ni na zata ba yanzu zata tareba. Dahda ya zabga mata harara don sam basa shiri da hameedah baya son halayenta gaba d’aya.ya mi’ke yana yiwa Hajiya godiya bayan ya ajiye mata ma’kudan kud’i da niyyar yi mata toshiyar baki. Bakin Hajja kam yana mutuwa tsaf saboda kud’i.nan ta shiga jera masa albarka. Yana fita hameedah ta shige part din zainab ta bata labarin tariyar. Hankalin zainab ya tashi don basu kawo tariyar nan kusa ba sun zata sai ‘yar su ta riga ta mallake gida tukunna sai ga sabon labari ya bayyana a zuciyarta tace ashe kuwa sai na tashi tsaye kafin kwa’bata tayi ruwa.

Tsaf yayi wankansa ya shirya cikin shigarsa ta musamma farin filtex d’insa da hula damanga takalmi bartozzi ya d’ora agogon rolex d’insa a damtsen hannunsa kana ganinsa kamar ka sureshi ka sace. Sai zabga ‘kamshin turarensa da yake mix yake different colours ‘kamshinsa daban yake.
Direct part d’in mommah ya nufa cikin tafiyar izza kamar Kuma ‘kasaita kamar yarda ya saba yi kullum. So yake yaje ya dam’ki ‘yar gidan mommah ta wanke masa toilet duk da yasa an wanke amma sai ya wahalar da ita.

Cak tayi da tea cup a hannunta tana ‘kare masa kallo cikin shigar doguwar rigar ta ta shadda as usual yanzu ma kanta ba d’ankwali. Sarai yaji idonta a kansa yayi mata banza yana dur’kushe a gefe yana gaida su dada da Hajiya mama da momma. Dada ta dubi shatu tsaki tayi “kiji min ‘yar banzar yarinya ba zaki gaida mijinnaki ba.” Da sauri yace “ta bar gaisuwarta jeki bedrroom d’ina da toilet ki gyara min” ya fad’a yana tsareta da ido tsaki momma tayi “akan me duk ina house helpers d’in gidan da sai ita zata gyara maka don wani sabon iyayi gidan ma da yau zaka barshi.” Dada ta zabura tace “Auzubillahi kuji min mata tana neman jawo mana masifa da ranar nan ruguzu ta fad’o mana aikin mijinnata ne ba za tayi ba to kuma idan bu’katar ta yake fa ba iya sharar za tayi ba tashi ki fice kafin na kai miki mangara a’a wallahi ba ruwana idan rashin kunya zaki saka ta dinga yi masa ba kuwa zanje zaman d’akin nan ba ki hana a raya sunnahr muhammaduna rasulillahi d’an Abdullahi. Kai tashi ka bi matarka kaji.” Mommah gaba d’aya ran ta ya ‘baci har ya mi’ke a zafafe tabi bayansa suna zuwa corridor tace “kai ji mana kuma wallahi ko hannu ka ri’ke mata ban
Yafe ba.” Tana fad’a ta juya Imran shi dariya ma ta bashi ya juya kawai a zuciyarsa yace “kin san kina tsoron hakan kika yi mata aure kash ina ma bana gudun ayi min dariya da ayau zan mayar miki da shalelen taki cikakkiyar mace.”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-23

ELEGANT ONLINE WRITERS……..

Suna shiga bed room d’in ya ja ‘kofa ya rufe, fuska a d’aure yake kallonta,ya tsareta da ido sosai kafin yace,”sakonki na jiya ya isar min, wai ke ki nuna min kin cika mace ko?har kin fara period, amma ban san ke wawuya bace sai yanzu,wa yace miki mace tana bari ma a gane tana period? Baki san abin kunya bane hakan?” Turo baki tayi kawai tana kallonsa,sai kuma a lokacin wata shahararriyar kunyarsa ta kamata,ta ji sam bata kyauta ba yanzu shikkenan ya gane mata sirrin ta? Sirrin da mommah tayi ta jan kunnenta akan kada ta bari a gani, da sauri ta runtse idonta.
Tsaki ya ja “Dama kafin na dawo ki tabbata kin fitar da ‘kazantarki daga toilet d’in ki kuma wanke min bin d’ina,and then lastly ki tabbatar kin wanke anything dake toilet d’in ya dawo kamar sabo, wawuyan yarinya kawai.” Ya fad’a yana kai mata ran’kwashi, daga haka ya fice ya kuma kulleta da key ta baya.

Sai sannan shatu ta bud’e idonta, tana sakin ajiyar zuciya, a hankali tace “Wai ni Shatu mai na aikata mutuminnan yanzu zai sake min kallon ‘kazama.” Tsaki ta ja ta shige toilet d’in, very neat ta samu toilet d’in,amma haka nan ta ‘kara wankeshi.

Momma jin shirun yayi yawa, da sauri ta danna kiransa a waya don hankalinta sam ya gaza kwanciya. Tsawon lokaci wayar tana ringing shi kuwa yana kallo yana driving ya’ki receiving call d’in sai murmushi yake, ya san mai take yiwa bata san ko bindiga aka saka masa ba zai iya aikata abinda take tunani ba.

Ji yayi text message ya shigo, ya bud’e yana murmushi had’e da ware ido kamar yarda hakan ya zame masa jiki. “Wallahi ka aikatawa yarinyar nan wani abin sai ka sani.” Dariya yayi sosai har da dukan sitiyari. A zuciyarsa yace “Ai kuwa yanzu wasan zai fara Mommah.”


Cikin kuka da tashin hankali take kallon mahaifiyrta, “Yanzu Anty duk burin da naci ya tafi a banza kenan? Yarinyar nan tarewa za tayi? Kuma ana nufin itama Imran mallakinta ne kamar yarda yake mallakina? Tana da right da komai a kansa, zata had’a jiki dashi? Komai da zaiyi min zai mata?” Cikin tashin hankali ta sake rintse ido. “Na shiga uku Anty pls kiyi wani abu mana, wallahi ji nake kamar zuciyata zata buga.” Tsaki Zainab tayi kafin tace “Ke bana son shashancin banza ki tsaya ki saurari abinda zan ce miki,ko jiya munyi waya da shuwa ta tabbatar min da ta koma gurin mutuminnan abinda ya sake ce mata kenan dole ki san yarda kika yi kika bashi maganinnan yaci a nama, a kuma ranar da yaci ake so lallai ya had’a shimfid’a da ita, yace min wallahi da zarar anyi haka kashegari zai sake ta kuma ba zai sake waiwayarta ba.” Kukan ta sake saki “Ni fa anty a sake wata shawarar wallahi ba zan amince ya shafi jikinta ba,balle har su had’a shimfid’a Imran nawa ne ni kad’ai.” Tsaki Anty tayi ta mi’ke a zuciye tace “Sai ki shirya zama da ita din-din-din a matsayin kishiya,ni dai abinda naga zan iya yi kenan shashasha ko meye abin damuwa?abin rana d’aya lokaci d’aya, kuma wallahi kika sa nayi asarar kud’ina ranki ne idan yayi dubu zai ‘baci,kin san nawa na kashe? Ban da tafiya cikin jeji da shuwa ta kwana tana yi a garinsu, to kije kiyi yarda kike so, ki bari suyi surkullensu na fulani su su mallakeshi,kin san dai yarinyar nan ta fiki komai da komai.” Runtse idonta shaheeda tayi murya na rawa tace “zan gwada Anty Allah ya bani iko.” Antyn ta dafa ta yauwa “ko ke fa idan kika yi hakan shine zaki samu kansa,ki ci karanki babu babbaka.” Shaheedah ta saki ajiyar zuciya tana dafa hannun mamanta tace “Amma Anty ta yaya zai amince ya kusanceta bayan kin san ba son auren yake ba.” Anty tayi murmushi “Yaro-Yaro ne ai ba yanzu zakiyi ba sai lokacin da muka so ta bar gidan,a lokacin dama kin tsara tafiya Abuja sai ki bashi a nama yaci,to kafin ki tafi ki tabbatar kin bashi desire tablet a cikin tea da safe mai ‘karfin gaske,idan ya bu’kace ki kice period kike ko kuma kafin maganin ya fara aiki kiyi sauri ki tafi shikkenan fa fa’kat, burinmu na farko zai cika.” Dariya shaheedah tayi ta rungume Antyn ta cikin tsananin farin ciki,hankalinta kam yanzu hundred percent ya kwanta.

Da yamma kafin a kai amarya Momma ta kira Imran, ba ‘bata lokaci yazo, tana kallonsa su biyu a
Parlourn tace “Nasiha zan maka Imran a matsayina na mahaifiyarka duk runtsi duk wuya ka kula da iyalinka,amana ce ubangiji ya dan’ka maka a hannunka, kayi adalci a tsakaninsu Imran kada kaga ita wannan yarinya ce ka cuceta ko ka zalunceta,zata tare nan da kwana shidda….” da sauri Imran ya zaro ido yace “kwana shidda Mommah ai naga tayi ‘karama.” Mommah tsaki tayi”Ni kaina ba’a son raina hakan zata faru ba ba yarda zanyi ne, sai dai ina son in ja kunnenka hakan ba yana nufin na baka lasisin kula ta bane, wallahi ban amince ba kada wata mu’amala ta had’aku,
Ka bar ta tayi karatunta please Imran.”

Ransa a ‘bace ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mai zai kaishi kusantarta ko shi ya kawo maita duniya, gaskiya bai ji dad’in lamarin tariyar nan ba, har hakan ya gaza ‘boyuwa a
Fuskarsa,sai dai bai ce komai ba ya mi’ke ya tafi bayan ya zaro key d’in part d’in shatu na gidansa ya mi’kawa mommah kamar yarda ta bu’kata.

Tunda ya koma bedroom d’insa ya zubawa kayan da abokansa suka had’a masa na komawa gidansa kallo,idan ka ganshi zaka yi zaton kayan yake kallo,Sai dai tuni zuciyarsa ta tafi tunanin neman mafitar yarda zaiyi da auren Shatu, tunani iri-iri ya shigeshi wata zuciyar tace kawai ya saketa ya gudu da matarsa su bar ‘kasar, a duk shawarwarin wannan ce tafi tsaya masa.

Tsaf Amarya Shaheedah ta fito a cikin shigar laffaya sai zabga ‘kamshi take kai kace anyi ‘barin turare a jikinta,sanye take cikin pink d’in laffaya, ta dai rufe kanta amma idonta ko alamar kuka babu,
Burinta a yau ya cika na auran Imran, kamar yarda ta dad’e tana mafarki,yau dai ga ta a matsayin matarsa,don haka take jin kamar taje ta kai kanta ganin su masu kaiwar basa sauri sun tsaya sai zagaye suke da ita wajen ‘yan uwa.

Gida yayi kyau ya sha kayan alfarma na gani a fad’a,sai zabga ‘kamshi yake. Amarya tun daga haraba take sakin murmushi cikin laffaya.

Kowa ya yaba sannan masu kawota suka tattara suka tafi, ‘yan mata zuciyarsu cike da burin samun irin gidan ko makwafinsa.

Ango dai tunda abokansa suka fara siyan baki yake sakin tsaki,burinsa suyi su tattara su tafi,tunda ya dad’e yana jiran wannan ranar a matsayinsa na kamilin saurayi.

Abubuwan da suka faru a daren abubuwane da baza su manta su ba a kaf tarihin rayuwarsu,ango dai ya riski matarsa sabuwa dal a leda sai muce Allah ya kawo ‘kazantar d’aki.


Tsaf tayi shirin makarantar ta ta fito, tana isa parlour taji ‘kamshin turarensa a parlourn, tayi mamakin ganinsa a yau d’in don rabonsa da zuwa gidan kwana hudu kenan cif tun bayan da amaryarsa ta tare. Yayi kyau sosai cikin black blue d’in yard d’inkinsa na kullum ne a jikinsa,gajeriyar riga mai gajeren hannu kan sa ba hula, hakan kuma sai yayi masa kyau. Har zata wuce da sauri Dada ta ‘kwalo mata kira “zo nan ‘yar nema baki ga mijin ki bane?” Bakin ta ta turo murya a cunkushe tace “Dada na makara fa.” Tsaki Dada ta ja cikin masifa tace “Allah dai wadaran naka ya lalace uwarki ce ta d’aure miki wani abu can, an ce wani sai kin yi tsinanniyar boko matar da za’a kai d’akin miji jibi ace tana yawo a gantale don wauta ko ‘yan magungunan gyara na daka ban ga ana baki ba,balle aje ga batun gyaran jiki,sai anje an cuce shi an kai masa ke salam kamar kazar da ba maggi ba gishiri,ko da yake ina ruwa na ke da uwarki ku zaku yi da na sani,ki wuce ki koma ciki yau ba zuwa wata makarnta idan kika tare idan ya zama dole kya je.” ‘Kwalla ce ta kawo idon ta,murya a cunkushe tace “Test ce fa dani zaki ce wani ba zan je school ba.”Mommah ran ta a ‘bace tace “Dada ki bar ta taje idan yaso goben sai ta ha’kura insha Allah ai kema dai zaki so ace ‘yar jikar ki ta zama likita.” Dada ta gyara zama cikin masifa tace”To kuwa idan har zata je makarantar nan sai dai wannan ‘katon banzan ya kaita ba Ammaru ba da kullum za’a dinga tashin sa da sassafe kai ta makaranta don an gan shi salihin bawa.” Ko kallon in da Dada take bai yi ba,ya mi’ke yana yiwa Shatu kallon sama da ‘kasa a
Zuciyarsa yace “Ai dama Ammar d’in aka aura wa ita.” “Ki nemi mai kai ki school ba abinda nazo yi ba kenan.” Cikin ‘bacin rai Mommah tace “Wuce kije ya kai ki idan yaso ya zubar da ke a titi,saboda ka ga na kyale ka? Kwanan ka nawa rabon ka da gidannan sai kace a kanka aka fara aure to kai zaka kai ta daga yau kuma kai zaka cigaba da kaita, wuce ku tafi Shatu kada kiyi late ai ha’kkin ta akan ka yake.” Dada tace “‘kwarai kuwa.” A ran sa yace yau zaku ga ha’k’ki wallahi sai nayi mata abinda ba zata sake shiga mota ta ba.

Tafiya suka yi sosai kafin su isa d’an ‘karamin building d’in mai tsananin kyau a ido,ginin kuma bungalow ne,gurin sam ba hayaniya. Da sauri Shatu ta kalleshi murya a cunkushe da tayi al’kawarin ba zata yi magana ba tunda taga ba hanyar makaranta yayi ba, ta san wata muguntar ya shirya mata saboda ance ya kaita makaranta.”please Yaya Imran ka mayar dani gida idan ma ba zaka kai ni school d’in ba.” Ko kallon inda take bai yi ba, ya zare seat belt d’insa yace “wuce muje malam ba dai sunce ha’k’kinki yana kai na ba,to yau zan sauke babban ha’k’kin kafin ‘kananan su biyo baya.”
Jikin Shatu ne ya d’au rawa don tun tana ‘kauyensu ta san menene aure tunda da friends d’inta da yawa da aka yiwa Aure. Ta kalleshi da sauri ta ga ya had’e rai, tuni idonta ya kawo ‘kwalla ta san matan. ‘Kauyensu suna bata labarin wahalar da suke sha har ruwan zafi ake saka su.”Don Allah Ya Imran kayi ha’kur.” Ba tare da ya kalleta ba yace “fita muje malama you are wasting my time,ai kin girma zaki iya d’aukan nauyin auratayya zaki kuma iya d’aukan duk wani abu da matan aure suke iya d’auka,tunda Babar ki ta aurar dake,ko baki san aure ba?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba Yaya Imran.” “To me yasa kika tsorata har da kuka? Kada kiyi min ‘karya fad’a min gaskiya kin san aure ne?wallahi kika yi min ‘karya kika bari na gane ‘karya kike min a yau zamu goge raini tsakanin ni dake don ba zan bar mana wajenan ba sai na mayar dake cikakkiyar mace mai amsa sunan matar aure,gaya min nace.” Da sauri ta fara wasa da hannunta jikin ta yayi sanyi sosai kamar ba Shatu Danger ba, ta sunkuyar da kai sosai hawaye sai zirara yake.
Shi kuwa dariya ce take son kama shi ganin tun ba aje ko ina ba ta razana alamar ta san duk abinda ake a aure,ya matse dariyar kafin yace “oya tell me ina jin ki mai ake a Aure?” “Iskanci” shatu ta fad’a murya na rawa sai kuma ta fashe da kuka “Don Allah kada kayi min kaji Yaya Imran wallahi Dijen gidan maigari tace da mijin ta yayi mata shine ta samu ciki.”
Still idon ta a ‘kasa take magana ta ma kasa kallonsa.shi kuwa dariya ce kawai take cin sa amma ya kasa yi,sai murmushi yake yana kallon yarda duk ta gigice. “Kin san meye iskancin Kenan?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba wallahi amma dai tace min cire kaya….” “yi min shiru fita muje ashe ma kin san komai yau kuwa zaki san menene iskanci,shashasha kuma Idan baka da aure idan kayi shine ake ce masa iskanci idan kuwa kana da aure raya sunna ake ce masa,Fita muje nace.” Ganin ba alamar wasa a fuskar sa yasa ta fita ‘kafarta na rawa al’amarin ya gigita ta sai kace ba Shatun Mommah danger ba. ‘kafar ta ta kasa d’aukanta a zafafe yace “ko sai nazo mun fara daga nan.” Da sauri tabi bayansa hankalinta a tashe,ta san yau kashin ta ya gama Yawo.”

Yana knocking Gate man ya bud’e gidan da sauri yana kai masa gaisuwa.gidansa ne da ya gina yake saukar guest d’insa turawa idan sun zo harkar business Nigeria. Ya tsaru iya tsaruwa yanayinsa tsarin turawa. Yayi kyau sosai parlor ne guda d’aya babba sai kitchen da toilet a parlourn sai 2 bedrooms.
Raku’bewa tayi a one seater tana chewing hand finger d’inta a tsorace take sosai tana kallo ya shiga bedroom ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando da sauri ta runtse idon ta ganin ya nufo ta ta mi’ke a guje tayi hanyar bedroom.murmushi yayi yace “shikkenan kin hutar dani kin
Kai kan ki.” Tana shiga ta rufo ‘kofar sai dai abin takaici babu key a Jiki. Tana kallo ya shigo fuskarsa a had’e, ta dinga ja da baya tana ro’konsa “please Ya Imran!” “wuce toilet kiyi brush sosai malama.” ta bud’e toilet d’in shima abin takaici babu key a jiki. Shatu ta zaro ido a hankali tace “Na shiga uku.” Idanunta duk sun firgice, tana ji ya turo ‘kofar ya shigo idanun sa a kanta “Ba zaki yi sauri ba?” “Ni fa nayi brush d’ina a gida.” “Na sani ai wannan na musamman ne ba na son naje kissing d’inki naji bakinki ba daidai ba.” Ai da sauri ta zube a ‘kasa hawaye sha’be-sha’be.”Don daraja da girman iyayenkaw Ya Imran kayi ha’kuri.” “Idan na ha’kura za kiyi min abinda nake so?” Da sauri ta d’aga kai,murmushi yayi “okey taso ki fito mu d’aura al’kawari.” Da sauri ta mi’ke ta fito tana sakin ajiyar zuciya, sai kuma ta kalleshi tayi saurin d’auke kai “please amma ka fara mayar da kayan ka tukun.” Yayi mata wani kallo “Meye a jikin nawa? Ko naked kika ganni?” Da sauri ta girgiza kai “To kina feelinga sha’awa ta ne? In d’auke miki ita yanzun nan?” Da sauri nan ma ta girgiza kai ba tare da ta san menene ma sha’awar ba.
Ya ta’be baki “Oya zauna maza na fad’a miki sharad’ina.” Ta kuwa zauna ta ra’be a gefe kamar ace kyat ta gudu.”Zan kyale ki idan kin amince da sharad’ina,kije gida ki sawa Mommah rigima kice mata ba kya son auren idan kuma ta ‘ki kice mata ba kya son ki tare yanzu,kiyi ta kuka idan ba haka ba wallahi kika bari aka kawo ki gida na sai kin gaya wa aya za’kin ta zuwa zan miki abinda ake yiwa masu aure,kina ji na ko?” Ta d’aga kai da sauri. “Yauwa idan kika yi haka kin zama good girl kuma zaki yi karatu sosai,idan kuwa kika ‘ki ana kai ki zan miki ciki ki haihu kuma ba karatu kina jina?” Da sauri ta d’aga kai, yayi tsaki “Ba kai zaki d’aga min ba kice na amince da sharad’inka Ya Imran.” Da sauri tace “Na amince da sharad’inka Ya Imran.” Ya gyad’a kai yana mi’kewa had’e fad’in “Good Girl.”

‘Daya bedroom d’in ya shige yayi kwanciyrsa, don ba zai mayar da ita yanzu ba sai ya kad’a ‘yan hanjin Mommah tukunna. Murmushi yayi a zuciyarsa yana tunanin halin da Mommah zata shiga.

Mommah lokacin d’auko ta yana yi ta tura driver, sai dai me? Driver ya kira ta yace ai ance shatu ba ta zo makaranta ba.Mommah bata san san da ta zauna da’bas a kujera ‘kirjin ta yana bugu bata so ace hasashenta ya zama gaskiya ace Imran yaje ya aikatawa Shatu wani abun da kan ta ba zai iya d’auka ba. wayarsa ta dinga kira,kusan missed call biyar kafin ya d’aga murya a dashe tamkar yana cikin wani hali yace “Hello Mommah.” Bata san san da ta ‘kunduma zagi ba.”Gidan uban wa ka kai ta?” Dariya ta so kubce masa yace “Ba ko ina fa Mommah gamu nan muna tare.” Mommah ta saki salati “kuna tare a gidan uban wa?” “Haba Mommah ki kwantar da hankalinki ni fa mijinta ne ku da kanku ku ka fad’a to me ye na……..” a zafafe ta katseshi “Wallahi Imran ka jini da kyau idan ka sake ka bud’ewa yarinyar nan sirrin da yake cikin aure zaka gamu dani nawa Shatun take?” Cikin dakiya yace “Amma ku kayi mata aure Mommah ku fa kuka ce duk hakkinta a wuya na yake..” “Uban ka nace Imran, kaci uban ka ka dawo min da yarinyar nan yanzunnan wallahi ko ranka ya ‘baci.” Ta kashe wayar tana jan salati “Na shige su nima wa ya aike ni?”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-24
Elegant Online Writers..

Masu son Littafin MIJIN MALAMA suyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾
https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Bai Tashi mayar da ita gida ba sai da yaga 3:00pm sharp, lokacin yunwa ta ci ta cinyeta. Ranta duk ya gama ɓaci da wannan mulkin mallakar, ta na kallo ya fito fuskar shi fresh da alama wanka ya yi ya fito. Ita ɗin ma watsa mata kallo ya yi “Tashi Malama kije kiyi wanka ban son ƙazanta, ba za ki shigar min mota ba sai kin yi wanka tun safe har 3:00pm” Marairaice fuska ta yi, idanunta yana shirin kawo ƙwalla ta ce “Don Allah Ya Imran ka bari idan naje gida zan yi” Ya girgiza kai ya ce “Ba zan iya ba kusan 7 hours rabonki da wanka, sannnan ki shigar min mota? yi sauri I have something to do kina wasting time ɗina” Miƙewa ta yi bisa tilas ta shige cikin ɗakin don yin wankan.

Suna parking ya watso mata kallo “kada ki manta da alƙawarinmu, idan kuma kin ƙi ki shirya karɓar haƙƙin ki na aure,don in dai na gan ki a gidana na san kin zaɓi zama cikakkiyar House wife” Ta ɗaga kan ta kawai,ta fice daga motar cikin azama. Imran ya bita da murmushin mugunta, ko ba komai ya san yau ya kaɗar da hanjin Mommah.

Tana shiga gida ta tarar da su Hajja a main parlour na gidan, bisa tilas ta durƙusa ta gaishesu, ko ba komai dole ne ta bi umarnin Mommah, sai dai ko kallo bata ishe su ba, har da masu harara da zabga tsaki, tana ji Hameedah tace “shegiya mai siffar jinnu” Girgiza kai tayi a zuciyarta tace zamu haɗu wallahi kafin ki tafi.

Ba kowa a parlourn Mommah, hakan yasa tayi saurin shigewa bedroom ɗinta, sai dai tuni Mommah taji motsin ƙofarta hakan yasa ta fito da sauri har tana yi kamar zata faɗi
A bakin Gado ta tarar da shatu tana zaune ta zabga uban tagumi,idanunta ya ɗan kaɗa alamar yunwa da barci ne a cikinsu,sai dai ita Mommah tuni tayi wa hakan wata fassarar ta daban.
Da sauri ta dafa ta tana zama a gefenta tace “Shatu hope ba abinda yayi miki? Ko ya miki wani abin?” Girgiza kai tayi hawaye na zuba a idon ta, ta rungume Mommah,hankalin Mommah idan yayi dubu ya tashi,ta
dinga salati tana tafa hannu “Tashi mu gani muje toilet.” Shatu ta riƙe hannunta tana girgiza kai “Mommah ba komai ni dai don Allah bana son auren yanzu bana son na tare please Mommah.” Kuka take sosai hankalin Mommah ya tashi,saboda bata tabua ganin Shatu a wannan halin ba.

“Kin tabbatar ba abinda ya yi miki?” Ta ɗaga kai kawai,tana ci-gaba da share hawayen fuskarta.Mommah ta girgiza kai “To me yasa ba kya son ki tare?” Kuka ta sake saki kafin tace “Mommah bana son na haihu yanzu,ya ce kuma idan na bari na tare yanzu sai ya buɗe min duk da wani sirri na aure” Mommah ta saka salati kafin tace “Amma Imran ya iya tsiya, bai dai yi miki komai ba bayan hakan ko?” Shatu ta ɗaga kai “Shi ke nan ki barni da shi ai ba ke kaɗai zaki tare ba da Dada zan haɗa ku,kuma ɗaki ɗaya zaku dinga kwana, ki rabu dashi tsokanarki yake ba abinda zai iya yi miki. Yanzu ki tashi kije ki ci abinci ko kin ci?” Tana share hawayenta tace “Ban ci ba tun breakfast” Mommah ta miƙe tana cewa “okey maza kije ki ci abinci,ni ma kasuwa zan je yanzu zan dawo.” Daga haka ta fice ita kuwa Shatu kwanciya tayi idanunta a lumshe tana tariyo moment ɗin da ya gaba ta. Gaba ɗaya jikinta Ƙamshin turarensa yake duk da tayi wanka. Ƙamshin da take masifar so,don haka ta kasa cire kayan.

Babu wani gyaran jiki da aka yi mata,duk da Dada tana ta maganar gyaran jikin, Mommah kuwa tace ba yanzu ba tunda yanzu ba zaman Aure za taje yi ba. Ita kuwa Dada da kanta ta bawa mai gadi kud’i yaje kasuwa ya siyo mata kayan magunguna tace suna tarewa zata fara banka mata.
Masifa take tana ‘karawa “Ni ban ga dalilin wannan tsiya ba ace wai Auren da aka yi ba yanzu miji zai tare da matarsa ba, to ba dani za’a yi wannan shirmen ba.”

Imran gani yayi kawai ana ta shiga da kaya na gani na fad’a, bugun turkey, ‘bangaren Amarya ya fara d’aukan harami kamar a ‘kasashen ‘ketare. Ransa ya gama ‘baci ya tabbatar shatu bata ji jan kunnen da yayi mata ba kenan. ‘Karshe don takaici ficewa yayi ya bar gidan zuciyarsa a hassale, musammman ganin yarda shaheedah ta hassala,sai kuka take masa.

Kashegarin Ranar Mommah ta shirya walima gagaruma, a kuma ranar aka yi kamun Amarya Shatu. An ci an sha an kuma yi wa’azi sannan Mommah tasa aka yi saukar Al’kur’ani, da niyyar Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka a auren. Ango dai ko gidan bai zo ba.
Mutane da dama walimar ta burgesu, har suka gaza shiru suke fad’an dama haka aka dawo ake yi a kowane aure, aka rage bidi’a ko don samun albarka a Aure.

Tsirarun mutane ne suke fad’ar haka, yayinda majority abin bai burgesu ba, musamman dangin Dahda da suke ta’be baki suke fad’in Iyayi ne da son a sani, ta kuma nunawa mutane wai ita mai tsoron Allah ce. Bata ce komai ba duk da zancen yaje har kunnenta tace “Allah ne kad’ai ya san zuciyar bayin sa.” Don haka sam surutun jama’a baya damunta.

Rabuwar Mommah da Shatu, abu ne da girgiza zuciyarka in dai kana wajen, Shatu kuka take kamar ranta zai fita, musamman idan ta tuna al’kawarin Imran na aikata mata irin abinda aka yi wa ‘yar gidan maigari matu’kar bata saka Mommah ta janye auren ba,haka ne yake sake tunzura zuciyar Shatu take kuka kamar zata mutu.
Mommah ma kukan take, tana ji kamar ta saka Imran ya saki Shatu tausayinta yana sake tsirga mata.Ta rungumeta sosai a jikinta, tana rad’a mata kalamai masu dad’i, wanda duk uwa ta gari ya kamata ta gayawa d’iyarta,yayin sallamar Aure. Tabbas rabuwa da gida abu ne mai ciwo Shatu,sai dai fatan dacewa a gidan Aure.

Haka tana ji tana gani aka raba ta da jikin Mommah, su Anty Nahna suka jata jikinsu.

Kamar yarda ake a al’adance dole sai an kai ka wajen dangin miji, itama Shatu haka aka dangana ta da na ta dangin mijin. Sai dai ba wanda yayi musu kar’ba ta mutunci musamman Hajja da tace ba zata kar’bi amana ba,haka nan cikin yaranta bata amince wani ya kar’ba ba. Ta ‘kara da cewa “Ai ita ‘yar gata ce sai a mi’ka ta gurin uwar mijinta kuma uwar ri’konta mai zai dame ta?” Ba wanda ya tanka su kamar yarda Hajiya Mama ta ro’kesu, kada suyi abinda za’a tafi dasu a baki.

——————————————-
Gefe guda kuwa Imran yana can zaune a part d’insa, yana kallon Shaheeda da tabi ta nad’e masa a jiki,tana kukan shagwa’ba, zuciyarsa har ta fara tunzira da rashin ha’kurinta.
A zafafe ya janye jikinsa cikin kaurara murya yace “Wai Shaheedah ya kike so nayi ne? For Goodness sake, nace miki nima ba a son raina aka yi aurennan ba, ba kuma a son raina ta tare ba, ki barni mana kiga hukuncin da zan d’auka.” Cikin Muryar kuka tace “To kada ka kula ta please!” Tsaki yaja yana zabga mata harara “In kula ta ince mata me? Wannan yarinyar ‘karama kada ki sa wa zuciyarki ma banzan tunanin nan, ki barni na san yarda zan ‘bullowa lamarin.” Shaheedah ta shafa gemunsa tana murmushi, Hankalinta kam yanzu ya kwanta.

Duk bugun da dangin amarya su kayi, a ‘bangaren uwargida ba’a bud’e ba, hakan yasa aka sadata da nata ‘bangaren ko bakomai dai sun fita ha’k’kinta.

Masha Allah Aljannar Duniya. Haka kowa yake cewa idan ya shiga part d’in Shatun Mommah, yayi matu’kar kyau iya kyau. parlour ‘karami daga farko da bedroom d’aya da suka ji turkish furniture, sai kuma ka shiga wani Babban parlourn shima mai d’auke da Royal furnitures complete set da dinning set duka iri d’aya Golden and Milk colour,curtains d’in parlourn da kujerun irin d’aya. Ga manyan turkish carpets malale a kowacce kusurwa. Bedroom d’in irin kayan parlourn ne da alama haka suka zo a set. Sai kitchen shima Babba ne sosai da store a cikinsa,komai na kitchen d’in black and white ne, hatta tiles da wall tiles da cabinet d’in. Kai su Mommah sun yi ‘ko’kari sai dai muce Allah ya ‘kara zumunci.
Yarda ‘kasa yake haka sama yake sai dai shi sama bed roon uku ne da kuma terrace a saman gidan, saman ma ya sha turkish furnitures da Royal furnitures, adon Blue and Golden, d’ayan parlourn kuma Black and white.
Ko makaho ya shafa ya san part d’in Shatu yafi na Shaheedah komai da komai, babu ma had’i.

Duk ‘yan kai amarya suka watsa ya rage daga Dada ‘yar zaman d’aki sai Shatu. Babu abinda ya dameta tana zaune tana ‘karewa d’akin kallo, wani farin ciki yana ratsa ta, a zuciyarta tana tunanin wai ita dai Shatu, Shatun ‘kauye Shatu mai idon mujiya ta ‘kauyensu itace Allah yayi wa Gam da katar da alheri haka, kuka d’aya take na rabuwa da Mommah da kuma tunanin kada Imran yayi mata irin abinda aka yiwa ‘yar gidan mai gari da ba abinda zai dameta.

Dada tun tana mitar rashin shigowar ango har ta gaji ta fara gyangyad’i, ita kuwa Shatu ba abinda ya dameta ya shekara ma bai shigo ba matsalarsa ce. Ta shige had’ad’d’en toilet d’in ta tayi wanka tayi brush, sannan ta fito tayi shirin barci dama tayi sallahr ta. Ta you kwanta a gefen da Dada take kwance a gadon.

Cikin barci taji Dada ta d’aka mata duka “Ke tashi lusarar banza la’ilahailallahu mai zan gani haka? Don ubanki ina mijinna ki kika zo nan kika baje kina barci, ko kazar baki je kin kar’bo ba Muhammaurrasulillahi.
Shatu dai ranta a ‘bace take kallon Dada tace “Don Allah ki ‘kyaleni nayi barci na.” “Wallahi kuwa ba dai anan ba, ba zaki saka mu kwana mala’iku suna tsine mana ba, maza tashi muje shi kuma inji dalilinsa na ‘kin zuwa siyan baki,ko kuma kazar yaka mana ba’kin cikin muci?” Shatu ta mi’ke tana zira Hijabinta. Murya a cunkushe tace “Ni fa Ina da test kuma Mommah tace kada na sake na shiga d’akinsa.” Dada ta zuba mata dundu “Mommo nace ba Mommah ba ka ji min ja’irar yarinya, ita Mommahn zata ceceki a kabari ne idan ana jibgarki? Wuce muje.”
Dole ta bita suka fita babban parlourn da zai sada su da ‘bangarensa kamar yarda Anty Hafsa ta nuna mata.

Da hannu ta nunawa Dada ‘kofar murya na rawa tace “Ga ‘kofar nan sai ki buga ya baki kazar muje mu kwanta.” Dada kuwa ta hau bugu.
Cikin barci yaji bugun yayi yawa da kyar ya janye Shaheedah da take barci peacefully, ba tare da tunanin satar kwana su kayi ba. Ya fito yana kallon Agogo ‘karfe 2:45pm. Ya ware ido yana tunanin waye da tsohon daren nan?

Yana bud’ewa idanunsa ya sauka a kanta ita da Dada. Fuska a d’aure yace “Lafiya?”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-25

Dada ta masa kallon she’ke’ke kafin ta furta “Lafiya tana gidan ubanka Manga,tunda nan ban ga ana zaman lafiyar ba, ba ma wannan , mai kake nufi da ka barmu muke barci she’ke’ke kamar shi aka kawo mu muyi ko siyan baki baka zo ba,balle ka ja amarya ku tafi turakarka.” Fuska ya d’aure sosai yana kallon Shatu yace “Ba yanzu na shirya kar’bar aurenta ba duk san da na shirya zan zo siyan bakin yanzu dai ku tafi don Allah.” Dada salati ta saka tana fad’in “Ni jikar fad’imatu wallahi Dijah dai ba tayi sa’ar haifoka ba, wallahi shashasha ta haifa idan ban da dolo waye zai zubar da wannan indiyar dajin ya kama mai suffar turawa,mace a ‘kanjame to ai shikkenan ke wuce muje shi yasa mai za’a yi da auren cushe.” Fuska a d’aure Shatu tace “Ai sai da nace miki kar muzo kika ‘ki.” “Ki wuce nace muje ai wallahi yayi da ‘yar halak Moddibo uban Dijah ya wula’kanta bani ba da na haife kakansa shi kuma ya haifi uban Dijah, ita kuma ta haifo mana jaraba.” Bai yi magana ba ya mayar da ‘kofa ya rufe yana jin zuciyarsa na sake tsanar auren alamar aikin su Zainab ya fara ci.

Suna komawa d’aki,Shatu ta saka masifa tana jan pillow zata mayar da kai ta kwanta, Dada ta kwad’a mata duka “Tashi shashasha wannan mijin naki sai kin dage masa da addu’a da alama mutanen ‘boye sun shafeshi. Nima nan yau ba zan runtsa ba,yarda ya wula’kantamu d’in nan alfarmar manzo sai yazo yana binki.” Shatu mi’kewa tayi ta shiga toilet d’in don ta tuna a nasihun Mommah har da sallahr dare da tace ta ri’keta gam-gam itace makamin ‘kare dangi.

Da sassafe wayar Mommah ce ta tashe shi, lokacin bai fi 30mints da komawa barci ba,idon sa a rufe ya jawo wayar had’e da sata a kunnensa. Cikin muryar barci yace “Hello” Mommah tace “kana jina Shatu ta shirya ka kaita school kada tayi late.” Daga haka ta kashe Imran ya mi’ke zaune yana dafe kansa a ransa yace “Kai oh my God wannan Shatu wannan Shatu wallahi Mommah ko don haka dole na koma turkey gurin harkar company na dama can nafi wayo ba sai an ganni ba balle a d’ora min wata hidimar Shatu.”
Shaheedah ta mi’ke tana kallonsa, kafin ta yi tsaki ta furta “Wai lafiya naji kana ta magana kai kad’ai?” Mi’kewa yayi ya fice yana ce mata “Am coming.”

Yana murd’a ‘kofar bedroom d’in ya jita a bud’e, da sauri ya shiga ciki, idanunsa akan Shatu da take barci, santala-santalan cinyoyinta farare sol a waje, ya saka hannu ya d’aka mata duka a cinyarta. Da sauri Shatu ta mi’ke tana murtsika idanunta, ta ware idonta a kansa fuska a had’e tace “Lafiya?” Ya girgiza kai “Ni kike tambaya lafiya? Ki tashi ki wuce ki yi shirin school kafin in murtsike bakinki, kuma daga yau ki san yarda zaki dinga tashin kanki ki tafi school ba zan juri tashinki ba.” Daga haka yasa kai ya fice. Tilas Shatu ta mi’ke ta shige toilet, kafin tayi wankan sai da ta and wanke toilet d’in tas kamar yarda Mommah ta ja kunnenta. Ta kuma fito ta koma parlour ta gyara duk yarda yake son gyara. Duk da Mommah tace zata saka a samo mata mai aiki. Ta kunna burnerr turaren wuta gidan gaba d’aya ya d’auki ‘kamshi. A kitchen ake yinta don ba abinda ta iya dafawa sai indomie ita d’in ma ba wani ‘kwarewa tayi ba. Haka dai ta zauna ta cacca’ba musu indomien sai dai tayi ruwa jingim.

Da sauri ta fito taje tayi wankan,ta zura uniform d’inta, sannan ta tashi Dada ta sanar mata ta tafi school. Dada ta zaro ido “Makaranta kuma? Kai Allah wadaran naka ya lalace,jiya a kawo ki gidan miji yau ki tafi makaranta, sai kace makarantar ganin Annabi.” Shatu dai mi’kewa tayi da sauri ta fice, tana jin Dadan na ta mita ita kad’ai.
Turus tayi a kitchen bayan ta bud’e indomie d’in taga ta ca’be kamar me? Haka dole ta fice daga kitchen d’in kamar tayi kuka,saboda bala’in yunwar da taje ji.

A parlourn ta ta gan shi zaune yana danna waya,sai zabga ‘kamshin turarensa yake. Ta tsaya tana matsar ‘kwalla, jin idanu a kansa ya tabbatar ta shigo parlourn ba tare da ya kalleta ba yace “wuce muje.” Murya na rawa tace “Yunwa fa nake ji.” A harzu’ke ya d’ago yana kallonta,sai kuma yaja tsaki “ Maza ki mayar dani abinci ki ci.” Yayi tsaki ya fice don dole ta d’au school bag d’inta ta bi shi.

Suna fitowa Main parlour d’in suka tarar da Shaheedah Zaune,ta ci kwalliyar ta cikin lace fuskar nan ta sha makeup, colour d’in lace d’in ya amshi fatarta sosai. Tana ganin Shatu ta had’e rai har da jan tsaki, Shatu kuwa murmushi tayi a hankali tace “Ni da Aljana a cupboard.” Da sauri Shaheedah ta juyo tana kallonta sai kuma tayi tsaki “Ni ba zan kula ki ba,saboda takaici d’aya da na bar miki ya isheki, daren farko Miji ya kwana a d’akin kishiyarki alamar duk da kyannaki bai damu dake ba. Ta shige jikinsa murya can ‘kasa tace “Ko Habibi?” Shima d’in jan ta yayi jikinsa duk don su turawa Shatu haushi.
Shatu kuwa ko a jikinta sai ma dariya da tayi tace a fili “Na bar miki shi har abada in dai wannan ne kece ya ke gabanki, ni miji na yana nan zuwa.” Da sauri Imran ya juyo yana kallonta “Rashin kunya zaki yi mana? Ko mu sa’anninki ne?” Shatu turo baki tayi kafin tace “ita me yasa ba kayi mata magana ba sai ni?” Da sauri ya murd’e bakinta suka zama so close har tana jin hucin numfashinsa a fuskarta. Tayi saurin runtse Idonta “ Sa’arki ce ita?” Bud’e idanunta tayi a cikin nasa kafin tace “Ba sa’a ta bace Allah ya kiyaye ta zama sa’a ta, wannan tsohuwar.”Shaheedah a zafafe ta yun’kuro zata mare ta, Shatu ta kauce fuskarta “Wallahi kada ki fara fuska ta tafi gaban mari idan kuwa kika aikata wallahi zaki yi dana sani.” Daga haka ta fice ran ta a
‘bace. Ta fara tunanin Ina ma ta san hanya da wallahi ba zata bi motarsa ba.

Bayan ya gama lalla’ba Shaheedan ya fito ya sameta a bakin Motar, fuskarta a d’aure.
Bud’e Motar yayi ya shiga, sannan cikin masifa yace “Malama ko na tafi ne?” Ta shiga motar tana tunanin muguntar da zata shuka musu idan ta dawo.

Shaheedah na koma wa ciki ta shige d’aki, mahaifiyarta ta kira murya na rawa tace “Anty ko dai nayi usinga maganinnan?” Anty t zabga salati tace”baki da hankali ne zaki yi amfani dashi yanzu, ina zaki ‘buya idan ya nufeki da bu’katarsa? To kada ma ki fara wallahi sai nan da one month.” Shaheedah tace “Ni fa wallahi Anty na tsani yarinyar nan so nake kawai ta bar gidannan.” Anty taja tsaki “dad’ina dake rashin ha’kuri har yaushe tayi zaman da zaki ce kin gaji da ita, kada ma ki fara ‘bata min aiki na gaya miki.” Da kyar dai Shaheedah ta amince da shawarar Antyn ta.

Suna tafe a motar ya juyo yana kallonta, ita kuwa d’auke fuska tayi tana kallon waje. Imran ya girgiza kai kafin yace “Kin shirya kar’bar ha’k’kinki kenan shi yasa kika amince da tariyar? To ki shirya dama yau da daddare zaki san mai ma’anar kalmar aure take nufi, tunda sai da naja kunnenki akan hakan kin ga bani da laifi.” Ta’be bakinta tayi ba tare da ko kallonsa tayi ba. Parking d’in motar yayi dai-dai lokacin da suka zo makarantar ta su yasa luck ya kulle ‘kofar, ganin har lokacin bata kalleshi ba yasa cikin masifa ya juyo fuskarta,tayi saurin runtse idonta.Tsam yayi yana kallonta shi kansa ya amince Shatu kyakykyawa ce irin kyan da ake nufi zallar kyau, Gashin idonta kansa abin kallo, balle gashin gira da haka-yalan gashin da yake kwance gaban goshin ta. Dogon hancinta da idan tayi dariya yake pointing daga ‘kasa wajen tsinin hancin. Da ‘karamin bakin ta da yayi kyau da zagayayyiyar fuskarta da ta dace da dogon wuyanta. Bayan ya gama ‘kare mata kallon ya saki tsaki “Raini ne yasa ina miki magana kika yi min banza?” Shirun ta sake masa had’e da bud’e ido tana kallonsa. Ya girgiza kai “Anjima zamu goge raini fita min daga mota.” Murya a ciki tace masa “ina jin yunwa.” Tsaki yaja kafin ya zaro kud’i a aljihunsa ya d’ora mata a cinya “Sadaka na baki don bani nace ki fito da yunwa ba.” Ta d’auke kud’in had’e da saurin ficewa daga motar.

A makaranta kuwa bata da matsala kasancewar tana da sharp brain sosai,nan da nan take gane karatu don haka nan da nan ta kamo abokan karatunnata.

Dada da ta tashi rasa abincin da zata ci tayi, hakan yasa ta fita parlour, tana ‘kwalawa Imran kira don rashin sanin ‘kofar da zata shiga. Jin shirun yayi yawa yasa ta buga ‘kofar Shaheedah. A zafafe Shaheedah ta fito don tana jin ta sarai don a ‘karamin parlournta take. She’ke’ke ta tsaya tana kallon Dadan kafin cikin tsaki tace “Lafiya?” Dada ta girgiza kai kafin tace “Ba shakka Imrana ya auro dai-dai dashi, to wallahi kuwa ba dani za’ayi wannan iya shegen ba yau-yau zan bar gidannan ina dalili gida kamar gidan Aljannu a bar mutum da yunwa, don fitsara kuma ana tambayarsa lafiya.” Daidai lokacin Imran ya shigo. “Dada lafiya?” Ya fad’a yana kallon Dadan. Cikin masifa tace “Lafiyar kenan ita ta kawo haka, juya muje maza-maza muje ka mayar dani can inda na fi wayo zaman d’aki aka kawo ni ko zaman hora mutum da yunwa.” Imran yace “Baki cida abinci ba?” Dada ta juya “Ni daida muje ka kaini can wajen uwarku wallahi ba zanyi zaman d’akin ba dama ban da tsiya wata gemai-gemai dani za’a kawo zaman d’aki.” Imran ya bita a baya, shi hakan ma yafi masa, Dada Allah ya raka taki Gona.

Ko a mota mita Dadan take yi tana ‘karawa can kuma tace “Haka kawai a aura maka yarinya ace wani kada ka kusanceta sai ta girma, to wallahi ahir kada ka bi wannan layin halaliyarka ce
Ina dalili? Irin wad’annan yaran ai sun fi dad’in mu’amalar Aure.” Imran had’e fuska yayi kafin yace “Ni dai ban tambayeki ba.” yana ji ta cigaba da mita.

A ‘kofar gida ya sauketa ya ‘kara gaba don baya son ma had’uwa da Mommah.

Mommah da take sallamar su Hajja zasu wuce maiduguri ta bi Dada da kallo cikin mamakin ganinta.
Dada cikin fara’a take yiwa mutanen mai dugurin sallama, sai dai ba wanda ta samu kallon arziki daga wajensa.
Hajja ta sake kallon Mommah a karo na uku, tun bayan fitowarsu tace “Burinki ya cika kin had’a aure da Shatu da Imran, sai dai ki bud’e kunnenki da kyau kiji hakan ba yana nufin zan saka miki ido kiyi abinda kika ga dama ba, wallahi duk wani motsinki akan ido na yake, shima Mangan da kika gama dashi kwana kwanannan zan warware kaf sihirinki da yake kansa.” Mommah sunkuyar da kai tayi kafin cikin murmushi tace “Allah ya sauke ku lafiya, Hameeda Allah ya ‘kaddara saduwarmu.” Daga haka ta wuce tana kallon yarda Hameedan ta bita da kallon banza har da tsaki.

A bakin Gado ta tarar da Dada tana cin abinci hannu baka hannu ‘kwarya, tana yi tana bawa Hajiya Mama labari “Wallahi ni naga tsana da gaske Imrana yake baya son yarinyar nan don ko kazar amarci bai kai mana ba, kuma ya tsallake santaleliyar yarinyar nan zubin larabawa ya tafi wajen waccen ‘kashi da ran, ba ma fa wannan bane abin haushi ita kuma ‘yar taku Shatu bata iya girki ba a hakan zata ‘kwace miji, Wallahi Dija dai tayi asara, to gwara ma tazo ta san yarda tayi ta koya mata girki, don baki ga abincin da tayi yau ba wallahi ina tabbatar miki da naci sai nayi amai, yaushe kuwa Imran zai ci and wannan kwamacalar.”
Mommah zama tayi tana murmushi tace “Wai Dada ya naga kin taho?” Dada ta sake kai loma bakinta kafin tace “Ba dole in taho ba gidan Imran ba abinci, kuma wallahi ba zan koma ba, ‘kafa ta ‘kafar uwarki Habuja zan koma.”Hafsa ta mi’ke daga kwancen da take tace “Ai Adda zata dinga kai muku abinci.” Dada tace “Wallahi ba inda zan koma dama mijin na sonta ne ma ga abin arziki amma gida ‘Kayan-‘kayau haka, Allah ya kaimu Ammar yayi aure na tare gidansa.”

Tunda ta dawo ba taga Dada ba hankalin ta ya tashi gashi bata da waya balle ta kira Mommah ga ‘yar banzar yunwa da take ji.

Da sauri ta fito main parlour sai ta tarar Ammar d’in baya nan, har ya tafi kenan yana ajiyeta, kamar wanda ake kora. Dama shi ya kawota shi Imran d’in wai yaje Abuja a ranar amma zai dawo da daddare.
Wuni guda tana cikin bedroom yunwa kamar ta kasheta, ga shi bata iya shan tea mai madara ba, dole ruwan lipton take ta sha. Tana juyo ‘kamshin girkin Shaheeda amma ko yunwa zata kasheta ba zata ce ta sammata ba.

Vest ce kad’ai a jikinta, sai Gashinta da tayi gammo da shi, ta fito main parlour ta zauna ta kasa ta tsare tana jiran Imran. Don bata son ya dawo bata sani ba,
Kuka ta keyi sosai saboda zuwa lokacin ta galabaita, dama tun asali bata iya ri’ke yunwa ba.
Yana bud’e ‘kofar parlourn ta taso a galabaice take tafiya har ta isa wajensa. Idanunta yana luuuu alamar lumshewa ta nuna masa cikinta, kafin kace mai tuni jiri ya d’ebeta ta zube a wajen. Da sauri ya tarota kafin ta kai ‘kasa a rud’e yake kiran sunanta yana jijjigata, amma ina Shatu an ji yunwa ta suma. Dai dai lokacin da ya d’ora bakinsa yana son hura mata iska don ceto numfashinta dai-dai lokacin Shaheedah ta bud’e ‘kofar sashenta take idon ta yayi kyakykyawan gani bakin Imran cikin na Shatu………..

Ps🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-26

Elegant Online Writers……

Da sauri ta zaro ido had’e da sakin kaskon turaren wutar da yake hannunta. ‘Karar abinneyasa Imran saurin d’agowa idanunsa cikin na Shaheedah da yake hango tsan-tsar bala’i a cikinsu. Cikin azama ya mi’ke yana gyara zaman Shatu a jikinsa, har a lokacin hankalinsa a tashe yake ganin bata dawo dai-dai ba. Da sauri ya d’aga ta cak rungume a jikinsa ya shimfid’eta kan kujera. Shaheeda kuwa ‘kara ware ido take tana kallon abinda yake wakana, yarda Imran yake wani lalla’ba Shatu. Da sauri ta ‘karasa wajen cikin masifa ta janye shi, ganin yana ‘ko’karin d’aga rigarta, duk hankalinta ya tashi gani take wani abin yake shirin yi, bata san Shatun bace bata da lafiya. Tayi saurin janyeshi tana furta “Wai Imran mai ye haka, a gabana kake nani’karta, a haka kake kwana gaya min Mai zaka yi da ita?” Tsaki ya ja, ya tureta gefe “Bari in gama ceton rayuwarta tukun sai kiyi duk abinda za kiyi.” Ta mayar idon ta kan Shatu,
Sai kuma ta saki tsaki “Munafurcin banza Wallahi ‘karya take yi, lafiyarta ‘kalau, karuwanci ne kawai.” Imran bai bi ta kanta ba sai d’aukan Shatu da yayi da sauri ya shige da ita part d’inta. A gadon ta ya kwantar da ita sannan ya shiga bathroom ya d’ebo ruwa ya watsa mata a fuska, sai a lokacin ta kawo ajiyar zuciya, numfashinta yana fita sama-sama. Ta bud’e idonta akan Imran da yake tsaye a gefenta. “Ruwa” tace masa a cikin wata galabaitacciyar murya.

Da sauri ya fice a kitchen d’in ta ya samu ruwan, sai kuma yayi tunanin ruwan zai iya ‘kulle mata ciki musamman kasancewar cikin bakomai. Da sauri ya jona kettle, ya koma d’akinta kafin Ruwan ya tafasa. Sam a tsorace yake baya son wani abu ya sameta ya san Mommah ba zata ta’ba yafe masa ba.
A jingine ya sameta jikin Gadon a ‘kasa, idanunta a lumshe da alama tana jin jiki. “Kiyi ha’kuri yanzu Ruwan zai tafasa kin ji” karo na farko da yayi mata magana da muryar tausasawa, wanda har yasa ta d’ago ta kalleshi, kallon da ya jawo abubuwa da yawa, kallon da ya jawo mata tsananin ‘kaunarsa har taji zuciyarta na bugawa tamkar ta fasa ‘kirjinta ya fito,
Yanayin yarda yake mata magana abu ne abin so a wajenta, ba ta’ki su dawwama a haka ba yana nuna mata kulawa. A hankali tace “Ruwa fa nake son sha.” Ya girgiza kai “Idan kika sha ruwa cikin ki zai yi ciwo saboda bakomai a ciki, ina zuwa.” Da sauri ya fita daga d’akin.

Tea ya kawo mata mai zafi, sai dai yana saka shi a bakinta tayi saurin girgiza kai. “Why?” Ya furta a hankali. Muryar da ta tsarga mata har zuciyarta taji tsigar jikinta ta tashi abinda bata ta’ba ji ba,wani yanayi take jin kanta a ciki, yanayin son kusantar d’a Namiji. Duk da bata banbance yanayin ba tunda ba sanin menene sha’awa tayi ba,Ganin ya ‘kura mata ido yasa tace “Ba na shan madara.” Dafe kai yayi “Oh God mai zaki sha yanzu?” ‘Kara lumshe ido tayi tace “ka kaini wajen Mommah ita kad’ai nake son Gani.” Ware ido yayi kamar yarda ya zame masa al’ada yace “Ganin Mommah a wannan lokacin ai masifa ce a wajena don tsaf zata iya yi min baki.”
Murmushi ta saki bayan ta ga ya fita, ta bi bayansa da kallo, tunani sosai ya shiga zuciyarta ina ma su zauna a haka dimin da’imun cikin farin ciki da walwala, kamar yarda Burin Mommah da fatan ta yake kullum.
Yana fita part d’in Shaheedah ya bud’e, tana zaune cikin tashin hankali idanunta yayi ja alamar ta ci kuka sosai. Zama yayi a gefen hannun kujerar da take, ya rungumeta ta gefe, murya a cunkushe yace “Please Habibteey I need a help.” Kallon banza ta watsa masa, kallon da ya bashi mamaki har bai san sanda yace “Ni kike wa wannan kallon?” Tsaki taja ta mi’ke “Ai wallahi Imran zaka san ni ka wula’kanta akan waccen ‘kwailar yarinyar kullum zancenka mai zaka ya da ita? Gashi yau Allah ya toni asirinka na ga zahirin abinda zaka yi da ita. Shame on you wallahi.” Ransa ne ya ‘baci har bai san sanda yace “Haram na aikata? duk da ba abinda kike tunani bane kuma idan shi d’in ne ma ai halak d’ina ce sadaki na biya aka d’aura aure, kawai ina ganin yarinya unconscious sai in tsallake na barta saboda ina tsoronki sai na bari Allah ya kama ni ko?”
Yana fad’in haka ya wuce Dinning da niyyar ya d’ibarwa Shatu abinci, ya bar Shaheedah a tsaye baki a sake tana kallonsa, cikin tsananin mamaki har murza ido take don ta tabbatar, zahiran ta ga Imran ne dai tsaye, Imran da Antyn ta da su Hameedah su kayi Al’kawarin ko za suyi yawo tsirara sai sun mallaka mata shi. Shine yau a tsaye yake Gasa mata magana son ransa, lallai dole su tashi tsaye aikin Mommah yafi na su ‘karfi. Har ya d’ebi abincin yana shirin fita ta yi saurin daka tsalle ta fisgo shi da ‘karfi ta baya. Da sauri ya juyo ransa a ‘bace yace “Me ye haka?cika ni.” “Ba zan cika ka ba sai ka bani abinci idan yaso kaje kaci na Shatun tunda ka riga ka raba mana kwana.” Ran sa a ‘bace ya mi’ka mata plate d’in abincin, ya fita da sauri tunanin halin da Shatu take ciki.

A toilet ya same ta tana ta kelaya amai ta galabaita sosai, ya tsaya daga bakin ‘kofa yana yi mata sannu. Jiri ne yake d’ibarta haka ta fito tana yin kamar ta fad’i. Da sauri ya ri’keta ya rungumota jikinsa. Hankali tashe yake mata sannu. Ta bi shi da kallo ita ba tayi tsammanin ma zai dawoba. Kwantar da ita yayi da sauri ya shiga kitchen d’inta, Allah yasa ya iya girki ya fara ‘ko’karin soya mata ‘kwai mai kauri.

Cikin mintuna kad’an ya gama suyar ya had’a mata tea mai Milo zalla yayi shi da kauri sosai. Yau dai su Imran anyi abin arziki.

Yana ajiye abincin yayi ‘ko’karin mi’kar da ita zaune, rabin jikinta duk a jikinsa yana jin yanayin yarda jikinta ya d’au zafi hakan yasa d’imin jikinnata yake shigarsa sosai, daurewa kawai yake amma lamarin ya fara fin ‘karfinsa. Sharewa yake a zuciyarsa yana yakicewa yana sanyawa a ransa ba sha’awa bace, ina ai bata kai munzalin da zaiyi sha’awarta ba,Mai ma zai yi da ita? shi har kullum kallon ‘kanwarsa yake mata. Zame ta yayi daga jikinsa don abin ya soma fin ‘karfinsa, ya jinginata da bed d’in, ita kanta hakan yafi mata kwanciyar hankali saboda yarda turarensa ya ke sanya ta cikin wani ba’kon lamari. A hankali yake bata tea d’in wani sa’in cikin rashin sa’a idanunsa su sar’kewa cikin nata. Da sauri yake d’auke kai baya son al’amarin yayi tasiri mai girma a zuciyarsa.

——————

Dai-dai lokacin da hakan take waka na a tsakaninsu, a lokacin Shaheedah hankalinta yana can a tashe,ta rasa yarda zata sanya kanta taji dad’i. Tabbas ya zama dole a daren yau ta yi amfani da maganin nan ta kuma kulle ‘kofarta idan yaso yaje ya sauke bu’katarsa akan Shatu. Sam ba zata jure ba, ba zata jure zama da Shatu a matsayin kishiyarta ba, tabbas idan hakan ta kasance zuciyarta zata buga. Ta kai Mari ta kai gwauro tana tunanin yarda zata soma. Da sauri ta d’auki ‘kullin maganin ta isa part d’in Imran cikin ikon Allah kuwa ta tarar da baya nan.
Da sauri ta bud’e heaterr da ke gefen gadonsa, da yake ajiye da ita saboda kullum cikin dare sai ya sha tea kamar buzu, ko da yake gida da irin heaterr a side bed drawer d’insa. Ta kunce ‘kullin maganin da sauri ta zazzaga, ta mayar ta rufe. Cikin azama ta koma side d’inta. Sai da ta shiga bedroom sannan ta saki ajiyar zuciya gani take kamar burin ta ya cika an gama, gobe da sassafe Shatu zata jewa da Mommah Mummnan labari, wanda ita zai zamewa mahaifiyarta da su Hajja labari mai tagomashin dad’i. Ta kwanta flat a kan gado tana sakin murmushi, duk da ta wani gefen zuciyarta na zafi ta san yau Imran zai kusanci Shatu, kusancin da zai zamo masa tamkar d’and’ane first and last a rayuwa, don boka ya tabbatar mata matu’kar ya sha maganinnan to kuwa ba zai gushe a rayuwa ba sai da tsananin ‘kiyayyar Shatu.

———— Gefe d’aya Imran yana can yana fama da Shatu, da ta sake narke masa, bayan gama cin abincin ma amai tayi. Hakan yasa dole ya kira Doctor ya gaya masa. Doctorn yayi masa prescribing magani yace ya siyo ya bata. Hakan yasa dole ya tafi siyowa. Ko da ya dawo Shatu ta sake galabaita, da kyar ta sha maganin ta sha kuma lucozade d’in da ya siyo mata. Sannan ya shiga ya had’a mata ruwan wanka mai zafi. Yana fitowa ya mi’kar da ita tsaye sai sannan ya kula da ‘yar ‘bingilar rigar da take jikinta, wanda da ita da babu duk d’aya. Idanunsa suka sauka kan matasan boobs d’inta da sauri ya d’auke kai, zuciyarsa tana bugu al’amarin da har mamaki ya bashi, yayi saurin juyawa ya fice daga bedroom d’in yana fad’in “Please ki daure kiyi wanka ki sha magani zaki samu sau’ki insha Allah.” Yana shiga bedroom d’insa ya kulle da key ya bar key d’in a jiki don ma baya so Shaheeda tazo ta saka masa ciwon Kai.

Sai sannan ya saki ajiyar zuciya tabbas shi kansa ya san ya wahala kuma ba don komai yayi ba,fad’an Mommah ne baya so. Ga shi a week d’innan yake saka ran shirin sa na komawa turkey da Shaheedah ya tabbata,baya son yayi abinda zai sosa zuciyar Mommah ta hana shi tafiya. Gwara ya lalla’ba ya tafi ya bar mata ‘yarta idan yaso idan ta girma idan yana da ra’ayi ya tare da ita.

Toilet ya shiga yayi showering kan sa sannan ya fito d’aure da toilet a Jikinsa, kafin yayi shirin saka kaya sai da ya kunna heater d’insa, sannan ya shafe jinkinsa da lotion jergens sannan ya sa turarensa a jikin pyjamas d’insa farare tas dasu jikinsu kamar auduga, ‘kafarsa sanye cikin room sleepers wani mai gashi a jikinsa, zama yayi a gefen gadonsa yana kunna babbar plasma tv d’in dake jikin bangon bedroom d’in, yayi mamakin da Shaheedah bata biyo shi ba,
A zuciyasa yace “Kishi kumallon mata ban da abin Shaheedah mai zanyi da ‘kwailar yarinyar nan? Duk da yau da na ganta ta bani mamaki yarda ta fi Shaheedan cika ta ko ina duk da ‘kan’kantar shekarunta. Ya lumshe ido yana sake kallo surar Shatu a cikin ‘yar ‘bingilar rigarta. Da sauri ya kawar da wannan tunanin had’e da cewa “God forbid idan ba so nake su Ali da sauran mutane su saka ni a wa’ka ba” ya ware ido yana tunanin yarda zai shiga tashin hankali idan hakan ta faru ina zai ‘boye kansa?” Murmushi ya saki yana tunanin yarda lamarin zai kasance. Da sauri ya mi’ke had’e da cewa Allah ya kiyaye yana ‘ko’karin yakice tunanin daga zuciyarsa.”

Tea ya had’a mai zafi yana sha yana kallon series na korean film,har ya shanye ya ‘kara zuba wani, shima ya shanye sannan ya mi’ke ya kashe t.v d’in ya kwanta. Ba zai kira Shaheedah ba don ya san ko ya kira ta wula’kanta shi zata sake yi yau dai kam zai bar ta sai ya koya mata hankali.

Amma mai? Sam ya kasa barci surar Shatu tsaf ta mamaye idanunsa da zarar ya rufe ido ita yake gani, wata zazzafar sha’awa Na ratsa duk sassan jikinsa, tun daga kansa har zuwa babban d’an yatsan sa tun yana d’aukar lamarin wasa har abin ya fara gagararsa. Da sauri ya mi’ke a daddafe ya fita direct sashen Shaheeda ya nufa……

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-27

Elegant Online Writers…….

Cikin rashin sa’a bayan ya murd’a ‘kofar d’akin ya tarar da ita a rufe. Nocking ya shiga yi tun yana yi a hankali har ya koma yi da ‘karfi amma Shaheedah bata bud’e ba. Cikin tashin hankali ya koma part d’insa ya samo spare key na part d’in nata sai dai ya tarar da d’akin ya ‘ki bud’uwa alamar da key a cikinsa ta baya. Jikinsa a sanyaye ya koma bedroom d’insa. Cikin yanayin da shi kansa ba zai iya misaltawa ba, yanayin da ko yana saurayi bai ta’ba shiga irinsa ba.

Kwanciya yayi ruf da ciki a kan gadon sa yana runtse ido da addu’ar Allah ya lafar masa da
Abinda yake damunsa, amma abin ka da yanayi na sihiri abin ‘kara gaba yake masa. Ganin yana neman hallaka yasa ya mi’ke yana tunanin samun fita, ji yake kamar yaje waje ko karuwa ya nema duk da bai ta’ba aikata zina ba. Sai dai take zuciyarsa ta hasasho masa halalinsa Shatu, tsoron Allah ya shige shi yaga gwara yaje ya kusanci Shatun domin ita halaliyarsa ce, da yaje yana bin matan banza a titi. Da sauri ya mi’ke bayan zuciyarsa ta gama hasasho masa Shatu ce mafitarsa.

Ya dad’e a tsaye a ‘kofar d’akin yana sa’kawa da warwara tsawon mintuna talatin yana shawarar shiga ko ya koma, amma jin lamarin yake kamar zai iya rasa ransa matu’kar bai kusanci mace ba. Ransa a ‘bace yana jawa Shaheedah Allah ya isa ya bud’e d’akin Shatu ya shiga.
Kwance ya sameta tana barcinta peacefully alamar lafiya ta samu,
Ya dad’e yana ‘karewa kyakykyawar surarta da kyan fuskar ta kallo, zuciyarsa tana ayyana masa tabbas idan ya kusancetan zai ajiye komai ya rungumi matarsa su zauna lafiya, ya kuma nuna mata soyayya sosai zahiran wa bad’inan ko da hakan yana nufin abokannasa za su tara mutane suyi masa dariya. Yanzu kam ya amince yana son Shatu So kuwa ba na wasa ba, yanzu ne ya fahimci yana da abinda zai yi da ita, ya ‘kalubalanci furucinsa na Me Zan yi da ita? Ashe wannan lokacin zai zo da zai ji son Shatu? Ya runtse idanunsa yana switching light d’in d’akin, zuciyarsa na harba masa da ‘karfi wai yau shine yazo Gadon Shatu da niyyar sauke bu’katarsa ta aure, tabbas Allah Alhakamu mai juya lamari yarda ya so ya kuma tsara shi a lokacin da yaga dama.

Kyakykyawar rungumar da yayi mata da ‘kamshin turarensa da ya ziyarci hancinta shi ya farkar da ita daga barcin wahalar da ya d’auketa,cike da tunani da tsananin ‘kaunarsa a ranta, don bata sam ma ta yi barcin ba, saboda yanayi tunanin da ta lula.

Gaba d’aya ta ji ya lula ta wata duniya, duniyar da bata ta’ba mafarkin shiga nan kusa ba.yanayi mai wuyar fassaruwa, yanayin da zata so ta dawwama a cikinsa dimun da’iman, ko da ace mafarki ne ba zata so ta farka ko a tashe ta ba, balle ta tabbatar zahiran ne abinda yake aiwatarwa a jikinta. Imran mutum ne na daban da ya iya nunawa mace zallar soyayya tattali da shagaltar da gangar jikinta a wani al’amari can daban da ya zama sirrinsu ne. Sirri ne mai wuyar fallasuwa ga ma’aurata masi koyi da sunnar manzon Allah da yace a ‘boye hakan kada a fallasashi. Mai fallasa shi kuwa ya zama daga cikin mutane mafiya shashanci a duniya.

Shi kansa Imran ya lula wata duniyar, duniyar da bai ta’ba tsintar kansa a cikinta ba a lokacin da yake mu’amalantar Shaheedah, akwai banbanci mai tarin tazarar gaske, banbancin yana yin taushin fata santsinta da laushinta, da wani kuma al’amari daban da bai ta’ba jin sa a baki da sassan jikin Shaheedah ba. Tabbas yanzu ya yarda mata ma suna suka tara ya yarda ko wace mace da baiwarta. Ya samu Shatu a yanayin da yake so matarsa ta kasance kuma ko a aljannah aka bashi za’bi akan Shatu da hurulaini zai yi fatan kasancewa da Shatunsa. A kunnenta yake ta jera Alhamdulillah ala ni’imatihi, sai wasu zantuttuka da ya dinga fad’a mata tun kafin ya kai ga sanin ta d’iya mace, wanda zantuttukan kad’ai sun isa sanya ta ‘kololuwar alfahari idan kuwa ta tuna dasu ko da nan gaba ne sun isa su saka ta nishad’i ta kuma san tabbas Imran ya kai ‘kololuwa a cikin. ‘Kaunarta.

Komai ya kammala cikin hukuncin ubangiji ya kuma samu Shatun sa fiye da tsammaninsa ciki da waje sai dai yace Alhamdulillah.
Ita kuwa duk da tsananin azaba da taje ji bata saki baki tayi masa kuka ba, kamar yarda Shaheedah tayi shi kansa ya san Shatu akwai dauriya kamar yarda yake son matarsa ta kasance.

A cikin daren ya had’a mata ruwa mai zafi, ta gasa jikinta sosai tana yi tana daurewa don ba ‘karamar azaba ta sha ba. A gefen Gado ta zauna shi kuma ya fita da sauri cikin azama ya had’o mata tea mai zafi ya kawo mata sannan ya bata pain reliever ta sha, yana yi yana kallon fuskarta yana sakar mata murmushi alamar lamarin yafi gaban furtawa a baki. Ita kuwa tsananin kunyarsace take d’awainiya da ita don haka ta mi’ke da sauri ta zira hijab. “Muyi Sallah” ta fad’a a hankali murmushi ya sakar mata “zaki iya” ta d’aga kai kawai tana wasa da yatsunta. Saboda Shatu akwai Ibada kuma malamanta na Islamiyya sun gaya mata kada tayi wasa da ‘kiyamallaili itace makamin ‘kare dangi.

Sun yi salloli duk da ita a zaune tayi don ba zata iya yi a tsaye ba ya kama kanta ya dinga zubo addu’oi har abin ya bata mamaki ashe yana da ilimin addini haka, sam a haka sai ka zata bai damu da ibada ba. Yana shafawa ita ma ta shafa, tana shirin mi’kewa ya kama hannunta “Gwara da kika tuna min dama na shigo a wani yanayi shi yasa ba muyi sallahr ba amma yanzu ma da mukayi lokaci bai ‘kure mana ba.” Ya ja ajiyar numfashi sannan ya mi’ke yana kama ta ta mi’ke tsaye a kunne ya rad’a mata “ubangiji Allah yayi miki abarka ya bani ikon kyautata miki sannan kuma don Allah ki manta abinda ya faru.” Ta d’aga kai tana murmushi, da kansa ya zare mata hijab d’in ya d’auketa cak sai kan Gado, su kayi kwanciyarsu cikin yanayi na matu’kar jin dad’i, ya kuma rungumeta tsaf a jikinsa kamar wani zai ‘kwace masa ita.”

——————-
Shaheedah kasa runtsawa tayi cikin daren, kuka kuwa ita kanta ba zata iya irga adadin da tayi shi ba, kukan take ba ‘ka’k’kautawa tana dana sanin bata zuba masa maganin ba. Bayan ya gama buga ‘kofar tana le’kensa ta ga kuma san da ya fito daga bedroon d’insa ya shiga d’akin Shatu. Hankalinta tashe ta shiga buga kanta a jikin wardrobe tana kuka, ga numberr Antynta ta ‘ki shiga. A zuciyarta ta dinga ayyana shikkenan yau Imran ya d’and’ana wata macen duk da dai ta san i gobe aure ya mutu murus. Tunaninta ne ya tsaya cak lokacin da ta tuna iya zallar maganin na zubawa a shayi ta bashi ya sha bata bashi na naman ba. Ta zaro ido da sauri tana mi’kewa bata son a samu matsala, zuciyarta ta shiga harbawa ya akayi ta manta? Bayan mutumin ya ja kunnenta akan kada tayi kuskure yanzu tsoronta d’aya akan mai zai faru? Bata son lamarin ya juye kanta. Da sauri ta sake buga wayar Antynta cikin sa’a a lokacin ta shiga. Hankali tashe ba tare da gaisuwa ba tace “Na shiga uku Anty.” Da sauri Antyn tace “Da aka yi me? Kin kuwa duba time Shaheedah past 3:00am fa.” Cikin kuka ta shiga bata labari. Antyn ta zabga salati “lallai kuwa Shaheedah dole kice kin shiga uku ba ke kad’ai ba ma har ni. Wace irin wauta ce wannan? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna sai fa da na ja kunnenki akan kada ki bada maganin ba tare da mahad’insa ba saboda shiriritarki yasa nace duk sanda zaki bayar ki nemi shawarata saboda in tuna miki yanzu ga shi kinje kin ji’ka mana aiki. Sai ki jira zuwa wayewar gari muga abinda zai faru. Yanzu na san ko na kira Shuwa wayarta ba shiga zata yi ba tana can tana yawon banza.” Kuka Shaheedah ta saka kalmar Na shiga uku kuwa ba ta bar bakinta ba.

Ai kuwa Shaheedah yarda ta ga rana haka ta ga dare gashi taje ta ga Imran bai dawo d’akinsa ba. Ta tabbatar har a lokacin yana tare da Shatu, hakan ya dad’a d’imauta zuciyarta, ta tabbatar da maganin yayi aiki da yanzu wani zancen ake ba da ba wannan ba.

Har Asuba tana jiran wayar Antynta. Sai da aka idar da sallah sannan Antyn ta kira, duk da ita Shaheedahn ko sallahr ta gagara yi. Da azama ta d’aga wayar cikin murmushi Antyn tace “ki kwantar da hankalinki boka yace wa Shuwa bakomai tunda har ya sha na shayin, sakin zai yiwu ‘kiyayyar ce nan gaba zata iya gushewa amma kafin lokacin za’a san abin yi in dai sakin ya yiyu za’a yi musu farra’ku. Yace na tsananin tsanar a cikin naman yake.” Shaheedah da sauri ta saki dariya cikin zakwad’i tace “Har naji dad’i da wallahi hankalina a tashe yake. Ina godiya Anty na samun kamarki sai an tona really proud of you yanzu shegiya yau zata je musu da black news.” Ta she’ke da dariya Allah dai ya bar mana Anty shuwa” Anty tace ameen ai ta cika aminiyar ‘kwarai.”

(Masoya na kuyi ha’kuri da jinkirin da aka samu yau biki muke wallahi shi yasa ma zaku ga typing d’in kad’an ba haka na so ba. Sannan gobe insha Allah ba typing ina da babban uzurin da zai ri’keni zuwa jibi dai insha Allah zaku ga typing mai yawa. Wallahi ina sonku sosai kamar yarda kuke son books d’ina domin da bazarku nake taka rawa💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿)

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-28

Elegant Online Writers.

Cikin daren ya farka yaji kansa yayi nauyi yana wani irin sara masa tamkar zai rabe gida biyu. Zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai ta’ba jin kwatankwacin wannan ciwon kan ba. Idanunsa har dishi-dishi suke ga ni. Da kyar ya mi’ke yana ture Shatu daga jikinsa ‘ko’kari yayi sosai ya kai kansa bakin ‘kofa, zuciyarsa na hassala da bugawa da ‘karfi ya fice daga d’akin, burinsa dama ya fita don sam baya son ganin Shatu da take kwance a gefensa, tsanarta sosai ta d’arsu cikin zuciyarsa, fiye da
Kwanakin baya. Da azama ya isa part d’insa. Turus ya zauna a gefen resting chair da take bedroom d’in nasa Kansa yana cigaba da sara masa. Duk ‘ko’karinsa na son furta addu’a sai dai harshensa ya ‘ki ba shi had’in Kai. Tsawon lokacin da shi kansa ba zai iya ‘kayyadewa ba yana zaune a bakin gadon sai d’aga kai yayi ya ga gari ya fara haske. Da kyar ya mi’ke ya shige toilet. Sai da ya fara sakar kan sa shower ko zaiji sau’kin rad’ad’in da kansa da zuciyarsa ta ke yi, kafin ya d’auro alwala ya fito.
Sallahr ma yayi tane kawai ba tare da nutsuwa ba al’amarin da zai tabbatar maka tabbas da sihiri. Imran mai ‘ko’karin Ibada musamman Azkar na bayan sallahr Asuba, yau shine da mi’kewa da sauri bayan ya idar da sallah. Burin sa kawai ya aiwatar da abinda zuciyarsa take so na sakin Shatu, yana ji tabbas idan ba hakan ya aikata ba zai samu lislama cikin ‘kirjinsa da kwanyar kan sa ba.

Biro kawai ya d’auko da jotter ya kuma rubuta abinda zuciyarsa ke son ya aiwatar. Ya nad’e takardar had’e da mi’kewa. Direct part d’in Shatu ya nufa.

Shatu tun da Imran ya farka itama ta farka sai dai rad’ad’in da take ji a ‘kasanta shi ya hana ta mi’kewa, har zuwa san da ya fice daga bedroom d’innata tana jinsa.
Ba ta jima sosai ba ta mi’ke da
‘Kyar don duk jikinta ya d’au tsami, sai dai ta dake ta shiga toilet d’in a hankali. Yarda ta ga yayi mata da daddaren haka itama ta had’a ruwan ta zauna a ciki. Tsawon
Mintuna sannnan tayi wanka Ta d’aura Alwala ta fito.

Tana zaune saman daddumar da carbi a hannunta kan ta akam gwiwarta. Idanununta a lumshe da alama barci take ji, amma da yake ta saba sai tayi azkar d’in dole haka ta zauna tana son ta ‘karashe ta kwanta, don bata jin ko school zata iya zuwa yau.

Motsin bud’e ‘kofar ne yasa ta d’ago idanunta suka sauka cikin nasa, Gabanta ya fad’i ganin yarda idanunsa suka nuna tsananin ‘bacin rai haka nan fuskarsa babu annuri ko mis’kala zarratin, tamkar dai fuskar mutumin da aka yiwa mutuwa mai tsananin d’aga hankali, mutuwar iyaye d’a ko miji haka fuskarsa ta nuna. Da sauri ta d’auke kai don kuwa ba zata juri kallon da taga yana antaya mata ba, sai ya tuna mata da kallon da yake mata lokutan baya da ya shud’e sai dai wannan har ya fishi muni. Zuciyarta ta shiga sa’ke-sa’ke da son hasasho mata ma’anar kallon tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta ita da zuciyarta. Laifin mai nayi masa? Ko dai ya taraddani ba budurci? Da sauri ta kawar da wannan tunanin don ba zata mance zafafan kalmomi da yabo da godiya da ya dinga mata da ya sameta a cikakkiyar budurwa da ta kai mutuncinta d’akin miji. Ba wannan bane zuciyarta ta bata amsa. Bai bari ta sar’ke da wani tunanin ba ya mi’ka mata takarda, ba tare da ya jira ta bud’e ba yayi azamar barin d’akin.

Hannunta na rawa ta shiga bud’e takardar, fatan ta taga yabo da godiya kamar yarda take karantawa a littafi sai dai tuni idanunta suka ga sa’banin haka kan kace kwabo hawaye sun ji’kar takardar sharkaf, ta sake ware idanunta akan rubutun da suka koma mata dishi-dishi “Ni Imran na saki mata ta Shatu…..
Daga haka ta yarda takardar ta fara gurshe’ken kuka “Tabbas nayi ganganci Imran da na mallaka maka kaina na manta ma’kiyi baya ta’ba zama masoyi, abinda kake sha’awa a jiki na kenan kuma ka same shi, dole ka sake ni don ka sha fad’a dama abin kunya ne a ganni tare da kai ace matarka ce mai zaka yi dani? Ni Shatu ‘yar ‘kauye Shatu da na taso a daji.” Hawayen ya cigaba da gangaro mata. Tana ji zuciyarta na bugawa na tsananin ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya.

Da kyar ta mi’ke ta koma bakin Gado ta zauna, tana sake saka maza a layin mutane marasa tabbas dubi dai kalaman da ya dinga gaya mata jiya dubi sakayyar kuma da yayi mata yau, sakin aure a ranar da ta kwana uku da tarewa a gidan miji ya mayar da ita ‘karamar bazawara a shekarunta da ko shekaru sha shidda bata rufa ba. Wallahi ya cuce ta kuma ba zata ta’ba yafe masa ba har gaban abada ta kuma tsane shi tsana mafi muni, da bata ta’ba yiwa wani mahaluki ba.

Shi kuwa yana komawa d’akin sa ya ji duk wani ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya sun kau daga ransa ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya. Shi dama ya san ba zai ta’ba son Shatu bada jiyan ma bai san me yasa har yaje ya kusanceta ba yana kuma dana sani da ba’kin cikin aikata hakan, ya tabbatar yanzu raini zai shiga tsakaninsu ba zai kuma bar ‘kofar rainin ba. Don ko dariya ba zai yi mata ba balle ta raina shi. Mommah da ya tuna shine gaban sa ya fad’i ya sani sarai a wannan ga’bar ba zata yi masa sassauci ba, yayi zugum yana tunani zuwa lokacin da wayarsa taand hauand ringing.
Da sauri ya d’auka ganin mai nemarwa Shaheedah visar zama a turkey ne, nan yake sanar masa visa ta kammala kuma ko gobe suke so zasu iya tafiya akwai jirgi da zai tashi daga Abuja. Cikin farin ciki da son gujewa fad’an Mommah Imran yace yayi masa booking. Da sauri ya mi’ke ya shiga shirya kayansa, yau zasu wuce Abuja idan yaso gobe jirginsu ya d’aga zuwa turkey shikkenan ba shi ba fad’an Mommah.

Ita kuwa Shaheedah tana can zaune jiran tsammani tun asuba take saka ran ganin Imran sai dai bai shigo ba, hankalinta a tashe yake bata da tabbacin maganin yayi aiki ko baiyi ba. Duk da dai bata haufi game da shu’umancin Shuwa. Ko sleeping dress bata cire ba balle aje ga babin wanka, idanunnnan yayi ‘kozai-‘kozai tunda ranar ba makeup gashi na kwana ana kuka. Tana cikin wannan yanayin Imran ya shigo. Gabanta ya fad’i ganin fuskarsa a had’e ba dai abu bai tafi yarda suke so suke fata ba. Ba kamar yarda hasashenta yake ba shi Imran haushinta yake ji tunaninsa duk ita taja masa yaje ya saukewa ‘karamar yarinya bu’katarsa ta jawo masa raini, da bata kulle ‘kofa ba ai da duk hakan bata faru ba. Fuskar nan a had’e yake dubanta, ya ja tsaki ganin duk tayi Jeme-jeme da ita zai iya cewa tunda yake bai ta’ba ganinta ba makeup ba, don haka yau yaga fuskarta ta kamar an tsamo kaza a
Salu’be daga ruwan zafi. “Ki tattara duk wani komatsanki…..” da sauri ya kalleta ba tare da ya ‘karasa ba ganin ta d’ora hannu a ka tana shirin runtuma ihu ido a waje take cewa “Don Allah kayi ha’kuri.” Tsaki ya ja “meye haka? Ai ba kiga hukuncin da zan miki ba sai nan gaba kad’an wallahi don na lura kin raina ni sosai. Kiyi sauri malama kada mu rasa jirgin tafiya Abuja gobe zamu wuce turkey sai kiyi waya ki sallama da duk wanda ya dace nan da 30mint jirgin Abuja zai tashi.” Daga haka ya juya ya fice Shaheedah ta saki wata wawuyar ajiyar zuciya, idanu a lumshe take fad’in Alhamdulillah wallahi har na tsorata. Na zata saki na zai yi. Sai kuma ta fara taka rawa jin turkey zasu wuce. Murnar ta ta tsaya cak tana tunanin ina labarin sakin Shatu? Ko har ya sake tan bata sani ba? Ture zancen tayi a gefe ta tashi da azama tana tattara kayan da zata tafi dasu. Tana yi tana danna kiran Antyn ta, sai dai bata d’aga ba da alama tana can tana hidimar Dahda.

Shatu ta dad’e a zaune ta rasa abin yi ita ba waya ba balle ta kira Mommah. Gaba d’aya jin ta take kamar mara lafiya, da kuma zata iya dama da fita zata yi tada shiga motar haya to sam ba zata iya tafiya ba. A hakan dai ta lalla’ba ta tattare iya abinda zata iya zuciyarta na tururi, ta fara tunanin ashe haka mata suke ji idan aka ce an sake su. Tabbas abin da ciwo ba kad’an ba wallahi ta tausaya musu ta kuma tausayawa kan ta.
Tana ganin takwas tayi ta shige toilet don tayi alwalar sallahr walaha kamar yarda Mommah ta koyar da ita.

Dai-dai lokacin shi kuma Imran ya fito daga part d’insa d’auke da trolley d’insa guda biyu. Cikin shigarsa ta kullum ta yard d’inkin African Attire. Da sauri ya isa sashen Shaheedah ta gama shirinta tsaf sai zanga ‘kamshi take, tayi kyau kuma sosai kamar ba ita ya tarar wata iri d’azun ba. Murmushi ta sakar masa tana bashi side hug “Haba my Habibi afuwa mana kada mu shiga flight kana had’e min rai a zata auren dole aka yi mana.” Bai yi mata magana ba yaja trolley d’inta d’aya ya fice. Don haka dole ta bi bayansa da sauri tana kulle part d’inta. Har ya wuce part d’in Shatu sai ya jiyo ya kalli ‘kofar sai kuma ya saki tsaki, ya juya da sauri, yaa jin tsanarta na sake shiga zuciyarsa.

Sun shiga mota kenan ya gaya kiran Mommah ya sake shigowa wayarsa a karo na biyar, gaban sa ya sake fad’uwa duk da ya tabbatar har zuwa lokacin bata san da sakin ba, don ya san Shatun ba ta da waya. Hakan yasa dole ya d’aga kiran, murya ‘kasa yada gaisheta “Sannu isashshe kaga damar d’aga wayar kenan? Allah yasa dai ka kai min yarinya makaranta.” Da sauri yace “ Bata je ba.” Mommah cikin zafin rai tace “Saboda me?” Imran ya d’an ‘bata fuska kafin yace “Ba ta da lafiya ni kuma tafiya ta kama ni, dama ina shirin bugowa na sanar miki mun wuce da Shaheedah ita kuma a tura driver ya d’aukota kiyi ha’kuri Mommah.” Ya fad’a murya a sanyaye had’e da sauri switching wayar off, yaja motar da sauri. Da motar zai wuce airport sai ya yiwa Ammar waya yazo ya d’auki motar.

Mommah sakar baki tayi tana kallon wayar cikin tsananin takaicin Imran d’in Shatu bata da lafiya shi kuma shi da matar sa ta Gold tafiya ta kama su, bai kuma yi hankalin yada kawo min Shatu gida
ba saboda bai damu da ita ba cabd’i ai kuwa ido na idon Imran wallahi sai ya gane kuren sa.” (Allah sarki Mommah baki san ma mai gaba d’ayan Imran yayi ba.)

Ran ta a ‘bace ta ‘kwalawa Nahna kira, su suna nan basu tafi ba sai wani satin. Da sauri Nahna ta shiga. Key kawai Mommah ta mi’ka mata “kije gidan Imran ki taho da Shatu bata da lafiya.” Ganin ranta a ‘bace yasa Nahna bata ce komai ba taand kar’ba ta wuce.

Tana isa mai gadi yawas bud’e mata, ta ci sa’a ‘kofar main entrance d’in gidan ba a rufe take ba da Shatu ba zata ji bugun ba. A ‘kuryar d’aki tais sameta tana karatun suratul mulk da alamar sallahr walaha ta idar. Don sun mayar da ita kamar compulsory in dai kai jinin Hajiya Mama ne. Shatu ta sakar mata murmushin da zamu iya kiransa na ya’ke kafin tace sannu da zuwa Anty Nahna, idanunta na zubar da hawaye duk da ‘ko’karin ‘boyesu da take. Nahna cikin tausayinta ta zauna a gefenta tana dafa ta “wani ciwo nea yasa idanunki suka yi haka Shatu kin gasan idon ki kuwa?” Shatu ta lumshe idanunta tana jin azabar suyar da zuciyarta take kafin tace…..

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-29

Elegant Online Writers…..
“Wani ciwo ne yasa idanunki suka yi haka Shatu? Kin ga kuwa idanunki?” Nahna ta sake maimaita mata tambayar a karo na biyu, ganin Shatun ta runtse idanunta tana kwararar hawaye Ta ‘ki magana. Hankalin Nahna a tashe ta dafa ta “kiyi magana nace mai ya same ki?” “Wani abu yayi miki?” Girgiza kai tayi ta mi’ke, gaban dressing mirror taje ta d’auko ba’kar takardar sakin ta mi’ka mata, sannan ta sake zubewa a gabanta tana kuka.
Hankalin Nahna ne yayi bala’in tashi, a wani irin yanayi na fad’uwar gaba ta bud’e takardar, idanunta suka hasasho mata abinda zuciyarta take hange, ta san tabbas ba zai wuce hakan ba. “Na saki Mata ta Shatu saki d’aya.” Rintse takardar tayi a hannunta, ita kanta zuciyarta suya take hawaye na zuba a kwarmin idon ta. Tabbas Imran bai kyauta ba, ya bar musu abin fad’a a cikin dangi bata san kuma ya mutane za su kalli abin ba. Tausayin Mommah ya kama ta,mace mai son zumunci Allah ya bata d’a da ya taso da soyayyarta da son zumunci,sai dai gaba d’aya rashin tsoron Allah yasa an birkita mata shi. Kamar ba Imran d’in ta Na da ba,da ba ta saka kara ya tsallake. Ganin kukan da Shatu take, hakan yasa tayi saurin share hawayenta ta rungumeta “Kiyi ha’kuri Shatu Na san mutuwar aure da ciwo amma ina son ki d’auki hakan a matsayin ‘kaddara, haka dama Allah ya tsara I ya ‘kayyadaddun kwanakin da za kiyi da auren Imran kenan, wani mahalu’ki bai isa ya juya hakan ba, hakan kuma ba yana nufin gushewar farin cikinkiba
insha Allah soon Allah zai kawo miki madadinsa ai ba shine autan maza ba. yanzu ki tashi mu tafi kuma don Allah bana son ki nunawa Mommah damuwa balle ki ‘kara sanya ta a wani yanayi, ki daure ki ‘karfafa mata gwiwa. Ko kina son wani ciwon ya kama ta?” Da sauri Shatu ta girgiza kai “Yauwa to ki nuna mata bakomai bana son ganin hawayennan a fuskarki.” Da sauri ta goge ta mi’ke ta bi bayan Nahna da sauri, tana jin abinda ya cunkushe mata a ‘kirji yana raguwa kad’an-kad’an.

Har suka shiga Mota Nahna bata sake cewa komai ba, da alama bata ta’ba shiga ‘bacin rai kamar irin na yanzu ba.
Shatu ta juya ta yiwa gidan kallon ‘karshe a matsayinta na matar aure a gidan,tuni zuciyarta ta sake karyewa ko bakomai wallahi ta tabbatarwa zuciyarta tana son Imran, amma ko son sa zai yi ajalinta a yanzu kam ta cire shi fit daga ranta. Bata muradinsa a rayuwarta kamar yarda ya tozar ta ta iya tozarci.

Suna yin parking Nahna ta sake kallonta tace “ki tabbata al’kawarin da kika d’aukar min kin cika shi kada ki sanya Mommah ‘bacin rai.” Shatu ta d’aga kai, har a zuciyarta tana fatan ta iya danne ‘bacin ran ta amma gani take abin da kamar wuya. Kafad’ar Mommah nanne wajen da take sauke duk wani ‘bacin ranta burinta yanzu ta jita jikin Mommah tana sauke mata damiyoyinta. Ta kuma sanar da ita Imran ya ‘kwace mata budurcinta sannan ya dan’kara mata saki. Amma anya kuwa zata Iya? Zuciyarta ta tambayeta da sauri ta girgiza kai “No I can’t ai da kunya wallahi ba zan iya ba.”
Suna bud’e ‘kofar main parlourn, da Anty Amarya suka fara had’a ido tana zaune ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya. Nahna ta ja hannun Shatu da take ‘k’karin gaishe ta suka wuce part d’in Mommah. Anty Amarya tsaki ta ja.
Sai dai tayi farin cikin ganin Shatun don ‘kila ha’karsu ce ta cimma ruwa kamar yarda suke fata.

A zaune suka samu Mommah ran ta duk a ‘bace tun ma ba ta ji maganar sakin ba, wannan ‘bacin ran na tafiyar da yayi ya barta ne ba ta da lafiya alhali sarai ya sani. Shatu na ganinta ta ji zuciyarta ta narke duk ‘ko’karin da take na son cikawa Anty Nahna al’kawarinta hakan ya gaza cimma faruwa, tuni ta fad’a jikin Mommahn ta saki kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro. Momma ranta a ‘bace ta shiga shafa bayanta. Cikin muryar lallashi ta fara mata magana “kiyi ha’kuri Shatu bai kyauta ba, kuma ni da ya sanar dani baki da lafiya da tuni ban tura an d’aukoki ba, tun da ni na damu dake.” Nahna ji tayi ita ma zuciyarta ta karye da sauri ta sunkuyar da kanta. Hawaye wani na bin Wani. Sai a lokacin Mommah ta lura da Nahna da take hawaye, tun kafin ta kai ga tambayarta menene? Gabanta ya yanke ya fad’i, dama dauriya take gaba d’aya ranar bata jin dad’in yanayin jikinta. Da sauri tace “Wai menene kun bar ni a cikin duhu.” Nahna a hankali ta mi’ke tare da mi’kawa Hafsa takardar, sam ba zata iya tsayawa ba, ba zata iya jure ganin Yanayin Mommah a lokacin da ta ankare da abinda yake cikin takardar ba. Tana mi’ka mata ta fice da Sauri. Hafsa ma gabanta ne ya fara dukan uku-uku hannunta na rawa ta fara ‘ko’karin mi’kawa Mommah takardar, sai dai cak da Mommah tayi bata kar’bi takardar ba yasa Hafsa kai idon ta kan Mommah, sai lokacin ta lura Mommahn a tsaye idanunta suke cak, yanayin da yake nuna ta shiga shock sosai. Da sauri Hafsa ta mi’ke tana girgizata, sai a Lokacin Mommah Ta saki ajiyar zuciya ta runtse idanunta kawai ba tare da ta ce komai ba, ko ba a fad’a ba ta san meye a cikin takardar ba ta bu’katar ‘karin bayani. Imran ya kasa bin umarninta ya saki Shatu. Ba tare da ta karanta takardar ba tace “Saki nawa ne?” Hafsa tace “‘Daya ne Mommah amma please kada ki d’aga hankalinki.” Ganin shirun da Mommah tayi yawa yasa Hafsa d’aukan wayar ta ta kira Dahda sannan ta kira Hajiya Mama duk ta sanar dasu halin da ake ciki. Hajiya Mama sakin ajiyar zuciya tayi kafin tace “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, ina Addar ta ku?” Hafsa cikin sauri ta kama Mommah da take shirin zubewa ‘kasa, vedio call ta shiga ta kira Hajiya Mama. Hajiya Mamar tayi mata umarni ta saka wa Mommahn wayar a kunne. Da sauri ta kara mata. Muryarta cikin nutsuwa ta fara mata magana “Rashin yarda da ‘kaddara a lokacin da ta sameka alamune na tawayar wani sashe daga cikin imanin mutum, idan masifa ta sameka kuma cewa aka yi kace Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Don haka ina umaratar ki da ki fad’a yanzunnan.”cikin rawar murya alamar kuka yana son cin ‘karfinta ta furta Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna Hajiya Mama Imran ya cuc…” cikin daka tsawa Hajiya Mama tace “akul kada na soma ji kada na soma jin kin yi masa baki ko kin fad’i mummunar kalma a kansa, duk uwa ta gari bata furuci akan d’anta a lokacin da ranta yake ‘bace, an fiso kiyi shiru ko kiyi musu addu’ar shiriya idan Imran ya lalace sai kin fi kowa shiga tashin hankali a rayuwa don haka tsakaninki dashi addu’a. Aure dai Allah ne yake ‘kaddarashi haka nan saki shi yake zartar dashi da so ko ba so duk wannan a hannun rabbul izzati yake, babu wani mahaluki da zai aikata abu face dama yana rubuce a cikin Kundin ‘kaddararsa, don haka ki yawaita yi masa addu’a da fatan Allah yasa hakan ya zame musu alheri gaba d’ayansu dama Allah (s.w.a)ya fad’a zaka ga kana tsananin son abu a zuciyarka baka san sharri bane a wajenka, kamar yarda zaka ‘ki abu tsananin ‘kiyayya ba ka san alheri bane a wajenka shi yasa a koda yaushe ake son mi’ka lamari ga ubangiji fiye da za’bin rai ko son zuciya.” Zuciyar Mommah ta d’an huce daga kumburin fushin da take sai dai hakan bai hana ta furta “Hajiya Mama a karo na ba adadi mutanennan suna samun nasara a kaina wannan karan ma sune da nasara a kaina. Ni na tabbata ba haka suka bar Imran ba.” Cikin tsananin fushi Hajiya Mama tace “Baki yarda da abinda nace miki ba kenan? Baki yarda Allah ke hukuntawa ba saboda kin saka a ranki zasu iya yi miki abinda Allah bai miki ba, ki cire wannan tunanin a ranki ki kama Allah, duk abinda ya samu bawa ko zai sameshi daga gareshi yake, idan ma su d’inne to muje a cewar sun ci Nasara a duniya to ki kwana da sanin cewa fad’uwa da madawwamiyar asara ta tabbata a garesu ranar al’kiyama. Bana son ki sanya damuwa a ranki har tayi tasiri a lafiyarki. Kiyi ha’kuri mai ha’kuri yana tare da samu, ita kanta ‘yar taki idan ta ganki cikin damuwa zaki raunatar da zuciyarta, alhali ke ake so ki ‘karfafa mata gwiwa.”

Sosai zuciyar Mommah tayi sanyi daga tu’ku’kin ba’kin cikin da take, tabbas duk wanda ya rasa mahaifiya yayi kuka. Ta d’aga mata kai alamar ta aminta da duk abinda tace “Yauwa Allah yayi miki albarka ki tashi kiyi sallah kiyi addu’a Allah yasa mu dace. Su Nahna kuma suyi shirin tahowa don sun kusa komawa makaranta.” Mommah tace “To insha Allah.” Ta fad’a tana sakin ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar, tabbas ta samu rangwame sosai kashi talatin cikin d’ari tuni ya zagwanye ta d’ora hannunta bayan Shatu da take kwance lamo a jikinta. Ta windownta ta ga alamar giftawar mutum ta tabbatar la’be aka yi mata. Ta saki murmushi a zuciyarta tace kuyi murna kuyi farin ciki a karo na barkatai burinku ya sake cika.

Kamar yarda tayi hasashe kuwa Zainab ce jikin windown ta kuma ji duk abinda yake wanka na, don tsananin farin ciki har rawa da juyi tayi a cikin parlournta burinta ya cika wannan karon ma suke da nasara. A fili ta furta haba Dijah muje zuwa ni daku d’an halak ka fasa in dai ina da Shuwa ai na tabbata bani ba kuka. Yarda na zauna da ba’kin cikin ki shekara da shekaru kema yanzu zaki fara d’and’ana nawa. Don Imran dai haihuwarsa kawai kika yi sai na dawo ni nake iko dashi kamar ra’kumi da akala.
Ta sake lalubar numberr Shuwa wannan karan ma dai switch off da alama har zuwa lokacin bata isa wajen mutumin ba. Tsaki ta ja labari take son bata amma ba dama. Ta juya akalar kirannata a layin Shaheedah ita ma still switch off. Kawai sai ta dangwarar da wayar tana sakin dariya.sai muce Allah ya shirya.

Dahda kuwa hankalinsa a tashe ya baro office ya taho gidan jin wannan tashin hankali, shi kansa ya tausayawa Dijah a yanayin da ya ganta. Sam Imran bai kyauta ba wallahi gashi yayi ta kiran wayarsa a kashe burinsa dama yaji idan da damar sulhuntawa a sulhunta tun kafin labari ya baza dangi. Shi kansa yaga wautar Imran da ya saki Shatu yarinya son kowa ‘kin wanda ya rasa. Rashin samun wayar yasa ya taho gidan jikinsa a salu’be.

A parlour ya tarar dasu kan kujera, har Shatu da take kwance kanta a saman cinyar Mommahn, ita kad’ai ta san azabar da take cinta a ‘kar’kashinta sai dai ba damar furtawa. Ina kunya ba zata barta furtawar ba don haka take ta nu’ku-nu’ku da abinta, su kuma zatonsu duk damuwar sakin da aka yi mata ce. Dahda yayi sallama ya shigo wanda ya sa Shatu saurin mi’kewa, Dahda ya kai dubansa kanta tausayinta gaba d’aya ya sake rufeshi. Ta gaida shi ya amsa cikin kulawa. Tare da shiga ciki yana duban Mommah “Muje ina son ganin Ki.” Mommah ta mi’ke ta bi bayansa bayan ya shige bedroom d’inta. Tana shiga ta saki ‘yan ragowar hawayen da take ta ‘ko’karin dannewa. “Kaji abinda d’anka yayi min ko?” Dahda ya saki d’an murmushin da bai kai zuci ba. “Shine abinda yasa kike ‘bata ranki a banza, shin sakin ba d’aya bane? Idan kuwa haka ne ai Kin ga za’a iya mayar da auren kafin ma wani yaji.” Wani kallo Mommah tayi masa kafin ta saki murmushi mai ciwo tace “Ai Dahda ko Imran ne autan maza a duniya Shatu ba zata sake komawa aurensa ba, anyi an gama kenan wallahi.” Dahda ya girgiza kai “kada kice haka Dija na ba’a yiwa aure wannan cin alwashin baki san abinda Allah zai zaratar ana gaba ba.” Ranta ne ya sake ‘baci “Don Allah Dahda mu bar wannan maganar ni ko zancen Imran ma a yanzu bana son ji, aure kuma tsakaninsa da Shatu ko bayan raina na haramta masa shi har abada kuwa, kuma daga yanzu na kulle wannan chapterr Shatu karatu zata cigaba da yi har zuwa sanda zata siyawa kanta ‘kima da mutunci a gurin kowa, a daina kallonta a matsayin fulanin daji bagidajiya har ayi mata sakin wula’kanci, farin ciki na d’aya da bai riga ya d’ebe mata albarkatun jiki ba, bai kuma kawar mata da budurci ba da ya cuce ni wallahi, saboda haka ni yanzu ba ya gaba na yaje ya cigaba da matar so har gaban abada.” Dahda ya saki ajiyar zuciya “A daiyi ha’kuri kada ayi masa baki idan rai ya ‘baci ba’a sob hankali ya gushe Dija na. Amma ya aka yi kika san bai kawar mata da budurci ba kin tambayeta ne?” Momma ta girgiza kai “kwananta nawa a gidan uku fa dama Dahda tace ko kallon arziki bai yi musu ba, yarda ya tsaneta bana jin zata tsole masa idon da har zai aikata wani abin da ita, ba ma zan tambayeta ba balle na sa ta jin kunya ‘karshenta ma bata san abinda zan tambaya d’in ba inje in bud’e mata wani sirrin da ya girmi kwanyar kanta in jefa mata tunani da ‘kananan shekarunta.” Dahda ya girgiza Kai “kafin yace Ai shikkenan zan dai cigaba da kiransa har zuwa sanda zan sameshi ban san inda ya tafi bane.” Momma ta ta’be baki kawai ba tace komai ba.

Dada tsohuwa tana fitowa daga d’akin da take taga Shatu zaune da su Hafsa. Baki ta kama tana taunar goro kafin tace “Muhammdu d’an Abdallah mai zan gani haka ke kuma wa yace ki fito wirjanjan haka ko yunwar ya sake barinki da ita?” “Cab Dada ai gwara yunwa akan abinda yayi mata sakinta fa yayi.” Momma ta fad’a tana fitowa daga bedroom d’inta. Sai gani su kayi Dada ta zauna da’bas akan kujera “menene saki? ko dad’in ji babu ke dai wallahi Dijah kiyi ta instingifari don bakinki ba ya fad’ar Alheri sai sharri, sharrin ma Ki rasa wa zaki yiwa sai d’anki Na cikinki auzubillahi wallahi uwarki bata yi sa’ar haihuwarki ba.” Mommah cikin takaici ta shige d’aki, tana ji Nahna na sake tabbatarwa da Dada sakin. Ji tayi ta saki kuka tana fad’in “Wallahi Dijah kin haifi tanbad’adde tunda muke a danginmu ba’a ta’ba bazawara ba sai yanzu…”.

Zainab Amarya da sauri ta sallame sallahr, ta d’au wayarta da take ta faman ringing, kamar yarda tayi hasashe kuwa Shuwa ce. Don haka cikin azama ta saka wayar a kunne tace “ke kuwa Shuwa ina kika shiga? Tun safe nake nemanki da daddad’an labari saki dai ya tabbata.” Shuwa tace “ Kai har naji dad’i, hankalina ya kwanta. Sai dai fa da wata a ‘kasa don kuwa yanzu daga wajen sa nake ya bani wani magani yace lallai a saka masa a abinci, shine ‘kiyayyarta zata dawwamawa zuciyarsa idan ba haka ba nan da lokaci kad’an komai zai iya canjawa kuma yauyau ake son a saka masa kafin wancan na jikinsa ya sake shi. Don haka ga maganin yanzu zan taho dashi.” Anty Amarya ta zaro ido “Yau kuma Shuwa ba sa fa gari, ya za’a yi yanzu?” Shuwa ta zaro ido “ki aika mata mana sai ta tura tasha a kar’ba” Zainab tace “kin san ina kuwa suka tafi? Turkey fa.” Wayar da take hannun Shuwa ce ta fad’i cikin tashin hankali tace “Wallahi to zainab akwai gagarumar matsala matu’kar wancan maganin ya sakeshi kiyi sauri ki kirata idan jirginsu bai d’aga ba ta san yarda tayi ta hana tafiyar a yau har sai ta amshi maganinnan..” zainab hannunta na rawa ta shiga danna kiran Shaheedah….

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-30

Elegant Online Writers……

Cikin hukuncin ubangiji bugu d’aya wayar ta shiga, Shaheeda tayi saurin picking call tamkar jira take dama a kira. Anty Amarya ta saki ajiyar zuciya. Shaheeda da hannunta yake sar’ke da na Imran taji Antynta tace “Hello Shaheedah ki san yarda kika yi kika ruguza tafiyar nan dan akwai babbar matsala, auren dai ya mutu amma komai zai iya faruwa Idan ba kiyi amfani da wannan maganin da Shuwa ta kawo yanzu ba.” Shaheedah da ta saki baki cikin tsananin razana tace “Ai muna cikin jirgi har mun d’aura belt, ina shirin switching wayar Off fa kika kira ni.” Zainab tace “shikkenan Shuwa kin ji sun tafi.” Shuwa ta dafe kai, sun jima zaune cikin hali na tashin hankali, kafin Shuwa ta saki ajiyar zuciya ta dubi Zainab tana mi’kewa “Shikkenan ni bari na wuce zama bai ganni ba, tunani na d’aya shiga kwazazzabonnan sam hanyar bata da kyau, shima nace masa yayi ‘ko’kari ya samu waya yace min wani baya bu’kata, yana da babbar hanyar sadarwa daga aljannu. Kema kiyi ‘ko’kari ki san hanya da kanki ki dinga zuwa kin bi kin li’ke a gida uwa a kanki aka fara aure, daga anyi magana kice kina shakkar mijinki tattabara uwar aure. Kin zauna kamar wata sokuwa har yau kin kasa kame miji.” Anty Amarya jiki a sanyaye tace “Ke dai kiyi ha’kuri Shuwa Manga waccar matar ta riga ta shanye zuciyarsa tsaf, wallahi duk asirina ta fini, don duk zaman da nayi a gidannan da asirce-asircen da nake baya tasiri a zuciyar manga, kallon arziki wannan ba yi min shi yake ba,a wajen danginmu kad’ai nake samun sau’ki don Hajja da kanta ma bani abu take tace na zuba masa a abinci, don mu had’u muyi maganin makira Dijah,amma wallahi kamar ‘kara masa ‘kaunarta ma nake yi.” Shuwa tayi tsaki “ Dai na ga ya min kayan haushi don Allah da kinje kin yiwa mutumin can bayani ai da ba haka ba, kin zauna kina jira na inyi hidimarki in yi Ta ‘yarki, shi yasa sam ni ban yarda da lamarin zaman aure ba a wani kulle ka a gida sai san da a kaso zaka fita. Idan zaki tashi tsaye ki tashi idan kuwa ba haka ba kina ji kina gani burinki zai bi iska.” Daga haka ta fice kamar guguwa ta tafi. Duk takaicin zainab na cika ta shi ys sam bata so tayi wannan auren na jaraba ba, da tun tana yarinya ta ‘kidirce sai ta auri Manga shi yasa ma ta taimaka mata, don sosai take ji da ita ta d’auketa tamkar uwa d’aya uba d’aya suke.

Ita kuwa Shaheedah tana cikin jirgi abin duniya ya isheta, tunaninta mai zaije ya dawo. Burinta na farko dai ya cika da taji an saki Shatu. Amma fargabar ta d’aya yarda lamarin zai juya, duk da ba ta haufi a al’amarin Shuwa ta san tabbas zata taimaka mata. Ta sake kwantar da kanta a kafad’ar Imran, da har I zuwa lokacin ya kasa walwala fuskar sa a had’e take kamar hadarin kaji. Ji yake kamar bai kyauta ba kamar Allah zai tambayeshi akan tsakaninsa da Mommah. Ya lumshe ido sakamakon wata ‘yar ‘kwalla da ta tarar masa. Yana ji jirgin ya lula dasu sararin samaniya alamar ya daidaita. Zuciyar Imran tayi nauyi, har wani bugu take na tashin hankali. Fatansa da burinsa Allah ya huci zuciyar Mommah, amma fa sam bai yi dana sanin sakin Shatu da yayi ba. Zuciyarsa ce ma take ‘karfafarsa akan hakan da yayi shine abinda ya dace.

—————————-
Shatu a kwance kan Gadon ta na ainahi na gidansu, idanunta kulle kamar mai barci sai dai ba barcin take ba, sa’banin haka tunani ne ya cika zuciyarta fal, tunanin Imran da moment d’in da suka yi spending a first Night d’insu na daren jiya, shine abinda ya hana ta sukuni, ya kuma yi tsaye a zuciyarta kamar me. Da zarar ta lumshe ido hakan take gani. Imran dai Imran dai, kunnuwanta kuwa sun kasa toshewa da jiyo tarin za’ka’kan kalaman da yake furta mata a kunnuwanta cikin zallar so da alfahari da kasancewarta matarsa. Ashe hakan duk sun wani salon yaudara ne na maza da suke aiwatar wa idan suna bu’katar matansu, tabbas Imran ya bar mata tabon da ba zai ta’ba gogewa ba, ya d’arsa mata ‘kaunarsa a zuciyarta ta yarda ko nan gaba bata jin zata samu wanda zai maye gurbin tarin ‘kaunarsa a cikin ran Ta. Ya cuce ta tun daga ran da ta samu kanta a matsayin matarsa take jin dad’i da farincikin samun miji kamar sa. Ashe lamarin zai zama tamkar dangwaliliya ne a wajenta. Ta share ‘yar guntuwar ‘kwallar da ta taru a saman idonta, kafin ta mi’ke ta shige toilet, gwara tayi alwala ta fuskanci rabbil hikimati ko zai yaye mata damuwarta.

Da safe tsaf ta tashi, ‘kasanta ma da yake mata ciwo tuni ta nemi ciwon ta rasa, ras take jin kanta duk Wani ‘bacin rai ma ya gushe daga ‘kirjinta har wani annashuwa da walwala ne suka ‘karar mata. Wannan yana daga cikin sirrin ‘kiyamallaili in dai zaka lazimci yin ta to fa cikin hikimar ubangiji kun yi hannun riga da ‘bacin rai. Allah ka bamu iko. Tayi shirin ta tsaf cikin uniform d’in ta tana ji a yanzu ne za ta d’aura d’amarar karatu. Sai ta bawa Imran mamaki da yake mata kallon bagidajiya.

A kitchen ta tarar da Mommah tana aiki, ta baya ta rungume Mommah cike da Nishad’i take furta. “Morning sweety” cikin farin ciki Mommah ta rungumeta ita ma, ta ji dad’i sosai da yarda Shatu ta saki jikinta, itace dai ko barci ba ta samu ta rintsa ba, saboda tunanin da yayi mata dabaibayi.
Hannunta akan Shatu tana shafawa tace “Masha Allah daughter na, hope everything is alright?” Shatu ta d’aga kai tana kar’bar wu’kar da Mommah take yanka cake da ta gasa mata a oven. Saboda ita tayi wannan sammakon idan ban da haka ba itace da girki ba. ba abinda zai fito da ita da Asuba haka. Suna aiki Mommah tana sake yi mata nasiha a fakaice “Ki dage da karatu kin ji daughter na both ilimi nake nufi boko da islamiyya, ina so kuma ki ajiye wauta da shiririta you are now a matured ki zama ‘yar gayun da za’a dinga kwatance dake, kin ji?” Shatu ta d’aga kai, alamar amsawa duk da dama ko Mommah bata fad’a ba ta ci burin hakan a cikin ranta. So take ta zama so silent irin mutanennan da magana ma sai a dole suke yin ta. Wanda dai ake kira masu aji.

Tana zaune a dinning tana break-fast, Ammar ya shigo fuskarsa da alamun rashin walwala a tare dashi. Tun jiya da Dahda ya sanar dashi ko runtsawa bai yi ba tunaninsa d’aya da ya tsaya masa, shine mai ya shiga yan yayannasa? Da yake son saka mahaifiyarsu a matsala, kullum ba shi da buri sai saka mata ‘bacin rai, sai ya jawo mata wani ciwon ya cucesu. Da wannan tunanin ya shigo don a jiyan bai samu ganin Mommahn ba, ba zai iya ba tasirin da tausayinta yayi a cikin ransa mai girma ne, don ya dad’e bai samu abinda yasa shi zubar da hawaye ba sai jiyan da ya riski wannan ba’kin labarin.
Shatu cikin fara’a ta d’ago tana kallonsa, kafin tace “ Yaya Ammar ina kwana?” Murmushin ‘karfin hali ya sakar mata sannan yace “lafiya Shatu, irin wannan loda abinci haka ina zaki kai shi?” Murmushi ta sakar masa tana nuna cikinta. Ya gyad’a kai “maza kije ki zama lutiya, wallahi ba kyau za kiyi ba.” Ya zauna gefen Mommah yana gaisheta, hankalinsa ya kwanta ganin Shatun Ta saki ranta. Mommah ta amsa masa cike da kulawa “Yaushe ka dawo daga kadunan? Don jiya har na kwanta baka shigo ba, hope tafiya tayi nasara an samu abinda aka je nema?” Murmushi ya sakar mata “Wallahi Mommah Alhamdulillah” yayi saurin fad’a yana mi’kewa “Bari na sauketa a school na dawo.” Mommah ta bi bayansu da kallo, tana ji da ta sani ma da Ammar ta had’a Shatun ta san da zai yi mata kyakkyawan ri’ko. Ba ka tara sani ga Allah, sannan lamarin ubangiji ya wuce nan ba mamaki shine dalilin da yasa bai sanya mata wannan tunaninba sai yanzu da lokaci ya riga ya shige.

Sai da ya sauketa a school ya sake dawowa wajen Mommah, so yake ya taushi zuciyarta sannan ya sanar da ita abinda ya kwana dashi a zuciyarsa. Har sannan Mommah tana saka turaren wuta a sashennata da yake ta bad’a ‘kamshin turare da ‘kamshin Girki kasancewar Mommahn ‘kwararriyar chef ce ta ainahi kuma karatun da tayi kenan. Ya zauna yana had’a tea. Mommahn ma sai da ta ‘karasa sannan ta dawo ta zauna kusa da kujerar da yake a saman dinning d’in. “Gwara da ka dawo dama ina son nace ka yiwa su Nahna booking flight na Abuja, har Dada ma tun jiya take tijarar ba zata zauna gidansu Imran ba tunda ba shi da zuciyar musulunci. Kuka fa ta dinga yi a gidannan.”
Ammar ya tsayar da zuba peppe soup d’in da yake yi, yace “Mommah ai bai kyauta ba wallahi nima Dahda da ya fad’a min kasa barci nayi wallahi, na ji zafin abin sosai a raina.” Momma ta saki ajiyar zuciya kafin tace “ai lamarin Hammanka sai addu’a, Allah ya shiryeshi.” Ta fad’a tana ‘ko’karin kawar da ‘bacin ran da yake son dabaibayarta. Ammar ya ajiye cokalin yana fuskantar ta, cikin muryar lallashi da ‘ko’karin kwantar mata da hankali yace “Addu’ar da za muyi tayi masa Kenan, ki kuma cire abin a ranki kada damuwa ta kama mana ke, sannan insha Allah ni zan share miki hawaye idan Shatu ta gama karatu zan maye gurbin Ya Imran.” Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Mommah cikin murmushi take cewa “Idan kayi min haka Imran ka share min ba’kin ciki Allah yayi maka albarka ya nuna mana lokacin.” Shima yana murmushin ya mi’ke, ko yanzu burinsa ya cika da yaga murmushin farin ciki a fuskar Mommah. Ya bata side hug ya fice. Bin shi tayi da kallo tana tuno Imran d’inta na da mai son farin cikinta da walwalarta amma gaba d’aya ya juye mata tamkar an canza mata zuciyarsa.

‘Karfe 5:00 dai-dai Na asuba jirgin mutanen turkey yayi landing a yotel air international airport. Istanbul suka Isa, dama tuni yayi musu booking a five star hotel. Suna zuwa motar da zata d’aukesu zuwa hotel d’in ta iso. Gaba d’aya Shaheedah Ta ru’kun’kumeshi saboda sanyin da taji yana ratsa mata ga’bo’bin jikinta. Har suka isa zuciyar Imran a cunkushe take ji yake tamkarma ya koma Nigeria.

Suna shiga apartment d’in da ya kama a hotel d’in, toilet kawai ya shiga, burinsa kawai ya watsa ruwa yayi wanka yayi sallah. Har ya fito ya tarar da Shaheedah zaune ta zabga tagumi, sai ya ji tausayinta ya kama shi don tunda suka taho bai bi ta kanta ba. ya zauna a gefenta, cikin cunkushasshiyat murya yace “kije kiyi wanka madam.” Ta saki ajiyar zuciya tana mi’kewa, ko bakomai yanzu hankalinta ya d’an kwanta da taji yayi mata magana cikin Kulawa.
Har ya shafa mai ya zira kaya, bata fito ba hakan yasa ya zauna a gefen gado yana jiran ta fito suyi jam’i. Wayar Shaheedan ya bud’e da yake ya san password d’inta. Kamar jira ake text d’in Anty nta ya shigo “Shaheedah ki saurare ni da kyau…..,,,”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-31

Elegant Online Writers…..

Tsaki kawai ya ja, yayi keeping wayar a side, ba ya son duba sirrin mutum sam, hakan ba d’abiarsa bace. Yana zaune har ta gama shiryawa kafin ya mi’ke su tada jam’in sallar.

——————————-
Bayan wata uku..

Kafin nan abububuwa sun fara da dama, wasu masa dad’i wasu sa’banin hakan. Shatu ta koma school kuma sosai ta mayar da hankalinta akan karatunta, gayu kam iya gayu yanzu Shatu ta zama ‘yar gayu bugawa a jarida. Momma ta mayar da ita classic baby, koman ta mai tsada ake siya mata kayan cosmetics da kayan sawa duka masu tsada sosai take using. Girki ma Mommah ta dage sosai waken koya mata, tana kuma dagewa sosai da yake ta saka abin a ranta. Tuni suka manta da Batun Imran, da tun bayan tafiyarsa ya kasa kiran Mommahn, sau tari yana son kiranta sai dai yana tsoron fad’anta. Hakan yasa sai dai yawan turo mata text messages akai-akai, ita kuma ko ta karanta bata bashi amsa.wani lokacin ma ba ta karantawa take barinsa.

A yanzu kam Imran suna yawan samun sa’bani da Shaheeda, don haka kawai wata rana sai yaji ya tsaneta baya ko san ganinta. Wata rana kuma sai yaji ba wacce zai iya so bayanta. Sau tari tunanin Shatu yana damun zuciyarsa, har yaji ya d’okantu da son ganinta, amma kuma sai yaji take ya ‘kara tsanarta. Don haka Shaheedah suka ‘kara dagewa duk da ba su samu wanda zai kai mata sa’kon ba, suna matu’kar ‘ko’kari wajen kawar da hankalinsa, ko da na lokaci kad’an ne. Suka kuma kawar da hankalinsa daga tunanin zuwa Nigeria yaji sam ya tsani zuwa Nigerian sosai kuwa, lamarin dai sai addu’a.

Gefe d’aya Ammar yana ta dakon jiran lokacin da Shatu zata gama idda don ya bayyana mata abinda yake ransa, ya kuma kafa kansa a zuciyarta. Duk da Mommah tace ya bari ta gama karatu amma yarda soyayyarta tayi ‘karfi a zuciyarta baya zaton zai iya hakan. Don haka duk san da yayi tafiya tsarabarta daban take daga kayan sawa har kayan makeup ya d’aukewa Mommah su shi yake yi mata, har waya ya siyo mata Iphone 13 ya kuma koya mata yarda ake amfani da ita. Zuwa lokacin yana ta lissafi ta gama iddar ya fayyace mata sirrin zuciyarsa.

Yauma da wuri ta dawo daga Islamiyya saboda ciwon mara da ya addabeta. Tana shigowa direct bedroom d’inta ta wuce ta cire uniform ta fad’a toilet. Kamar yarda tayi hasashe period d’inta ne yazo wanda daga shi ta gama idda. Bayan tayi wanka ta kintsa kan ta sannan ta fice parlour.

A kitchen Ta samu Mommah, sakwara take da mitar egusi, gefe d’aya baseerah mai aiki tana wanke kwanu kan daga aka ‘bata. A sanyaye ta shiga kitchen d’in ta zauna a d’aya daga cikin kujerun da suke working space na kichen d’in. Mommah cikin kulawa ta kai kallonta kanta tana murmushi “Ya aka yi lazyn Mommah gajiya ko yunwa? Don na san yanzu kin zama acici.” Mommah ta fad’a tana murmushi. Basirah tayi dariya tace “Wallahi kuwa Mommah har cikin dare fa tashi take cin abinci.” Mommah tace “Mhmn basira rabu da ita ai gashi nan sai uwar ‘kiba take ta bud’e ko ta ina girmanta ya wuce shekarunta, yanzu fa idan tace shekarunta sha takwas ba sha biyar ba ba wanda ba zai yarda ba, yarinya ta zama uwar mata, wallahi ki rage cin nan, duk halittunki sun bud’e.” Shatu ta turo baki kamar za tayi kuka, ta hau buga ‘kafa tana kallon Basirah da take mata dariya. Cikin muryar shagwa’ba tace “Mommah wallahi kiyi mata magana ba ta fini ‘kiba bama ni fa ba ‘kiba nake ba cinyoyina ne suke ‘kara girma don duk wanduna na sun yi min kad’an, sai kuma riguna na daga ‘kirji wallahi duk sun matse ni.” Mommah tayi dariya tace “Ai dama ba ‘kiba kike ba bud’ewarce take bani mamaki, sai dai na godewa Allah da ya bani yarinya mai cikakken diri son kowa ‘kin wanda ya rasa masha Allah.” Shatu tana murmushi tace “Amma to me yasa Ya Imran ba ya so na?” Tuni annurin fuskar Mommah ya ‘bace ‘bat, sai kuma ta kalli Shatu tace “Ya period ya zo kuwa don a lissafina yau ko gobe ne.” Shatu ta d’aga kai “Wallahi yazo shine abinda yasa ma na gudo gida da wuri, wannan zuwan ma sai da na samu pain.” Mommah tace “Allah yasa kin gama a sa’a ubangiji ya tsare min mutuncinki ‘yar albarka.” Shatu tace “Ameen” jikinta a sanyaye.

A tsawon sati d’aya Shatu ta sake bud’ewa lamarin da ya dinga bawa Mommah mamaki ga cin abinci babu iyaka, har Mommah ta fara tunanin ko ba ‘kalau ba. Ta kuma yi jajir da ita kamar ka dangwali fatarta jini ya fito, ga she’ki da shinning da take abin sai dai ace tubarakallah. Sam Mommah bata kawo komaiba a ranta tafi danganta hakan da kwanciyar hankalin da Shatun Ta samu da mayukan da take using masu tsada.

Yau aka yi musu hutu, aka kuma yi speech and price giving day, Shatu ta fita zakka a cikin classmates d’inta, don tayi ‘ko’kari sosai duk da tafi ‘yan ajin girma, hakan yasa principal tace zata iya joining ‘yan S.S one tunda yanzu ba karatun da bata ganewa. Zata karanta kuma zata fahimta, sai a samar mata lesson teacher da zai dinga sake koya mata a gida. Mommah taji dad’i sosai har farin cikinta ya kasa ‘boyuwa, tana hasashen tabbas Shatu zata cika mata burinta. Gashi ta samu farin jini gurin malamai da student duk inda ta zaga zaka ji ana Shatu Mujittafa.

A ranar cikin dare cikinta ya fara ‘kugin yunwa da sauri ta tashi neman abinci. Ta shiga kitchen Ta lodo abinci a plate, don yanzu an saba ma dole ake ajiye mata abincin saboda yunwar dare. Tana fara cin abincin ta ji cikinta yana harbawa alamar motsi sosai ta zaro ido, ta kai hannu ta dafa wajen da taji motsin sai taji ya sake harbawa. Da sauri ta mi’ke cikin matu’kar tashin hankali a fili tace na shiga uku meye a ciki na,
Sosai kuwa ya cigaba da harbawa kamar tana tunzira shi, ai ba shiri ta zunduma da gudu sai ‘kofar d’akin Mommah, ta shiga nocking tana ‘kwala kiran sunan Mommah.

A razane Mommah ta farka cikin barci, jin Shatun na kiran sunanta da sauri ta sauko daga Gadon, ta nufi ‘kofa don bud’ewa.

Ganin Shatu a firgice yasa ‘kirjin Mommah ya buga da ‘karfi tana kallonta, tana nan waige-waigen ganin ko wani mugun abinne ya samu Shatun. Da sauri ta ri’ke hannunta suka shige bedroom d’in Mommahn. Bayan ta zaunar da ita a gefen Gado ta kalleta tace “Menene?” Shatu hawaye sha’be-sha’be tace “Mommah cikina wallahi ina jin micijin ciki ne ya girma har ya fara motsi a cikina tun d’azu yake watsalniya.” Mommah ta ware ido tana sake ‘karewa Shatun kallo banda ita shaida ce tayi period har uku, a gobe ko jibi suke saka ran na hud’u da sai tace ciki ne da ita don duk alamomin juna biyu sun bayyana ga Shatun. Mommah tagumi kawai ta zuba bayan ta rasa tudun dafawa. Fatan ta Allah yasa ba wani mugun ciwon bane zai kama Shatun.

Da kyar ta bari Asuba tayi, ta tayar da Shatu da take kwance saman gadon ta tana barcinta hankali kwance, ba abinda ya dameta, duk da cikin yana ta harbawa.
Sai da suka yi Sallah, sannan Mommah ta kira wayar Ammar don ya kaisu asibiti. Ta turawa Dahda text msg. Suka fice da sauri duk hankalinta ya gaza kwanciya.

Suna zuwa asibitin, bayan tambayoyi likita ya tabbatar ta ta’ba aure, sannan ya rubuta musu gwale-gwajen da zata je ayi mata a laboratory. Zaman jugum su kayi kafin result ya fito aka kaiwa Doctor d’in.

Murmushin da Mommah taga ya saki ne hankalinta ya kwanta ta san tabbas da wani mummunan ciwo me, da ba zai yi murmushi ba. Ya d’ago yana sake kallon Shatu, a ganin farko dama da yayi mata ya san hakan ce zata faru. “Alhamdulillah ba wani abin damuwa bane, she is pregnant.” Da sauri Mommah ta d’ago tana kallonsa “Ciki fa kace Doctor?” Ya d’aga kai “Yes off course akwai abin damuwa ne ko bata da aure ne?” Mommah ta saki ajiyar zuciya tare da cewa “Bakomai, amma abin da mamaki duba da ko last month tayi period.” Doctor ya girgiza kai “wannan ba abin damuwa bane, ba kowace bace don tana da ciki take daina period, wasu sai cikin ma ya girma suke dainawa, wasu kuwa har su isa haihuwa ma, ya danganta ga yanayin mahaifar mace, amma yanzu for confirmation bari muyi mata scan don mu san tsawon lokacin cikin.” Ita dai Mommah jin sa kawai take, amma hankalinta kam a tashe yake Allah yasa dai cikin nan na Imran ne shine fatanta.

Ana yin scanning kuwa ciki ya tabbata sati goma sha shidda wata hud’u cif-cif, watannin cikin watannin aurenta, hakan ya kwantr da hankalin Mommah tunaninta d’aya yanzu, ko dai Imran ba virgin ya sameta ba shi yasa ya saketa idan kuwa ba haka ba mai yasa zai sakar mata ‘ya bayan ya tare da ita. Ta shiga addu’ar kada Allah ya tabbatar da tunaninta, lamarin fa sosai ya d’aurewa Mommah kai har ta kai bata wani fahimtar dogon bayanin da likitan yake mata.
Ya rubuta mata magunguna suka mi’ke suka fito. A reception suka samu Ammar yana zaman jiran su, fuskarsa na bayyanar da damuwar da yake ciki. Yanzu kam ya ha’kka’kewa kansa ba ‘karamin son Shatu bane ya kama shi. Tunda ta taho idanunsa yake zube a kanta.
Da sauri ya mi’ke yana tambayar Mommahn ya ake ciki? Mai likitan yace? Mommah ba tayi masa magana ba illa jan ajiyar zuciya da take yi akai-akai. Tsaf tunani ya cunkushe mata zuciya burinta suje gida ta titsiye Shatu ta ji gaskiyar batun.

Ammar hankalinsa a tashe yake driving, don haka tu’kinnasa ya zama rough sosai, bai san me ya canja Mommah, burinsa d’aya Allah yasa ba wani mugun ciwo bane ya kama Shatunsa, da lamarin ya gigita hankalin Mommah. Suna parking Mommah ta fice da sauri, ta kuma tasa ‘keyar Shatu zuwa cikin gida. Basu tsaya ko ina ba sai cikin bedroom d’inta. Ammar duk da bai iya la’be ba ranar kam ya koya. Suna shiga Mommah ta mayar da ‘kofa ta rufe. Idanunta ta zuba cikin na Shatu “Gaya min Kun had’a shimfid’a da Imran ne kafin ya sake ki?” Gaba d’aya kunya tayi wa Shatu dabaibayi ta shiga wasa da yatsun hannunta bata ta’ba jin kunyar wani mahaluki ba kamar yarda ta Mommah yau tayi mata dirar mikiya “Ki fito fili ki gaya min, ki ture batun ni mahaifiyar Imran ce ya saka ni a mizanin mahaifiyarki, ki d’ago ki gaya min kun had’a shimfid’a nace.” Idanun Shatu a runtse, cikin wani yanayi ta d’aga kai. Mommah ta saka salati kafin tace “Shatu bud’e idonki kiyi mini bayani idan ba so kike zuciyata ta buga ba, shin bai sameki cikakkiyar budurwa bane shi yasa ya sake ki a kashe gari ko ya aka yi? Don ni dai abin ya bani mamaki ganin tafiyarki ko canjawa ba tayi ba, bai same ki a budurwa bane?” Da sauri ta girgiza kai kafin ta sake runtse ido murya na rawa tace “Wallahi Mommah ya sameni don zanin gadon ma ya ‘baci da jini, kuma naji a ‘kauyenmu ance idan aka ga haka shine mace ta kai budurcinta. Don yar gidan maigari ma da akayi mata aure sai da ta bamu labari.” Mommah ta saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya hankalinta kam yanzu ya kwanta. Ta tabbatar rashin mutunci ne kawai ya sa Imran ya ketawa ‘yarta haddi ya kuma tsallake ta barta. Ai kuwa wallahi sai ta shayar dashi ruwan mamaki. Ta sake jin haushin Imran ya dabaibayeta sosai.
“Zan ja kunnenki kada ki sake ki gaya wa kowa kina da ciki, kafin na san shawarar da zan yanke akan cikin naki, don bana son karatun ki ya samu tasgaro.”

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-32

Elegant Online Writers…..

Momma ta sake gyara zamanta, tana kallon Shatu “Kada ko da wasa ki gayawa kowa kina da ciki, idan nace kowa ina nufin kowa, yanzu tunda hutu kuke jibi insha Allah zan wuce dake Abuja a can zaki haihu, idan yaso a samo miki malamin addini da wanda zai dinga koya miki karatun boko, kafin ki haihu mu san mai za’a yi.” Shatu ta d’aga kai cikin ‘karfin hali jikinta duk a sanyaye yake, ta mi’ke ta fita bayan Mommahn tayi mata umarni.

Ko da ta isa d’aki tsayawa tayi cak a gaban mudubi, ta d’aga rigarta hannunta akan shafaffan cikin da ko alamar da nuna zaunuwar ciki bai yi ba.sai dai motsin da cikinnata yake yi ne ya tabbatar mata da akwai cikin, lokaci d’aya ta saki hawaye sai kuma murmushi kamar wata zautacciya, a fili ta furta oh ni Shatu nice zan zama Mama”. Ta saka tsalle cikin tsananin murna saboda dama Allah ya sawa Shatu jarabar son yarinya. Tayi sak kuma cikin tsoro tana tunanin Innaji kada dai itama ta mutu kamar yarda Innaji ta mutu. Zama tayi gefen gadon hannu bibbiyu tayi tagumi tana tunanin Innajinta. Take hawaye ya gauraye idanunta cikin tsananin kewar Innajinta.

———————————-
Ammar tunda ya shiga d’akinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai struggling a d’akin zuciyarsa cike da tunanin abubuwan da yaji suna tattaunawa. Shatu da ciki? Kuma cikin Imran, hankalinsa kam ya tashi duk d’okinsa na Shatu ta gama idda ya sanar da ita abinda yake kwana yake tashi dashi, da gaske yake son Shatu, zai iya cewa tun ba yanzu ba ya fara sonta, tun kafin ayi bikinsu da Imran, lokacin da aka yi auren hankalinsa ya tashi sosai, sai dai da ya tuna Imran ba sonta yake ba hankalinsa ya kwanta, ya tabbatar ko mu dad’e ko mu jima zai rabu da ita a taurin kai irin na Imran ya san ba zai zauna da ita ba, sai dai kash burinsa bai cika ba ashe Imran ya gama da Shatu. Amma duk da hakan ba zai fasa ba, ba zai daina jumirin Jiran Shatu ba har zuwa sanda zata haife ta gama idda. Idan ya so tana haihuwar sai ya fitar da abinda yake cikin ransa a d’aura musu aure. Da wannan tunanin ya mi’ke ya nufi d’akin Mommah.

A zaune ya samu Mommah da alama tayi zurfi a tunani, jin sallamarsa ne ya sata saurin d’agowa tana amsa masa sallamarsa bayan sakin gwauron ajiyar zuciya.
Ammar ya ‘karasa ya zaune a gefenta, hannunta ya kama a hankali yace “Mommah kiyi ha’kuri kada ki dinga d’aga hankalinki akan Imran addu’a kawai zaki yi masa nima kuma zan taya ki, sannan cikin Shatu ba zai hana ni aurenta ba idan ta haihu.” Da sauri Mommah ta d’ago tana kallonsa, kafin tace “ya aka yi kasan tana da ciki?” Murmushi Ammar yayi kafin yace “Duk naji hirarku d’azu, Na biyo ku da magungunanta da kuka manta a mota na samu kuna zancen.” Mommah ta saki ajiyar zuciya kafin ta kalleshi tace “Ammar ina son wannan ya zama sirri tsakanina da kai pls, bana son kowa ya san da zaman cikin nan, hankalina ya fi kwanciya da hakan ina son na bawa mutane da dama mamaki, ka kuma kwantar da hankalinka Shatu tamkar ka aureta ka gama in dai ina raye, saboda na lura da abubuwa da dama tun farko da kai Shatu ta dace ba da Imran ba, saboda haka a ranar da ta haihu ranar suna za’a d’aura aurenku, saboda bana son yaron ko yarinyar suyi maraicin uba, sannan bana son su ri’ki Imran a matsayin Babansu.” Ammar farin ciki ya cika zuciyarsa, burinsa zai cika a lokacin da ya cire tsammani da tabbatuwar hakan. Shatu burin ran sa zata zamo matarsa, ai ji yayi kamar Mommah ta tsundumashi a aljannah, ya shiga furta “Nagode Mommah ubangiji ya ‘kara girma, amma kuma ya za’a yi da karatunta?” Mommah tace “Idan mu kaje Abuja zan samar mata fitattun malamai zan kuma basu ko nawa ne su dinga yi mata lesson a gida, tana haihuwa sai ta zana S.S.C.E, burina a yanzu bai wuce ayi auren ba, ko don na cusawa Imran ba’kin cikin da ya cusa min, Na san tabbas nan gaba sai yayi da na sani in dai dangin Abbanku ne.” Ammar ya mi’ke farin ciki fal zuciyarsa tare da tunanin Shatu ta zama tasa confirmed.

—————
Da daddare kuwa bayan Dahda ya dawo ya ci abinci ya gama duk wasu al’adu da yake yi kafin ya kwanta, Mommah ta kawo masa zancen son tafiyarta Abuja, sai dai ta ‘boye masa musabbabin tafiyar tata ta dai sanar dashi tana son zuwa kai Shatu hutu. Bai kawo komai a ransa ba yace “Allah ya kaimu gobe zan saka Ammar yayi muku booking flight, hakan yayi kyau ko bakomai ai sunyi miki kara kuma na tabbata suna son ganin jikarsu.” Murmushi kawai Mommah tayi alamar ta jin dad’in barinta da yayi.

Kashegari kuwa wuni guda su kayi cur suna ta shirye-shriyen tafiya, duk wasu kayan da zata bu’kata Ammar ya siyo mata irinsu turare bulgari da mayukanta na Neutrogena zuwa ‘yan dogayen riguna sakakku da zasu yiwa masu cikin dad’in sawa, kaya dai cikin Akwati babba tamkar shine uban d’an duk da ba kayan babies bane, sai dai kayan babies d’in ma tuni yace Mommah tayi masa list akwai tafiyar da zai yi zuwa Qatar zai siyo su a can. Mommah tace “Don zumud’i Baban Baby” yayi murmushi yana jin dad’in sunan da aka kira shi dashi. Jin d’an yake kamar nasa.

——————-
Flight d’in Azman Air na 7:30am suka bi zuwa Abuja, su Shatu an maze wai ita a dole ba za ta nuna lokacin ta fara hawa jirgi ba. sai dai lokacin da jirgin ya fara tashi ta ji wani iri ga kunnuwanta sun toshe tuni ta ru’kun’kume Mommah cikin tashin hankali, tana kiran sunan Allah idanunta a runtse, Mommah a hankali ta rungumeta tana murmushi tace “A’a Shatu ya da haka Kuma? Ai da kin cigaba da mazewar.” Shatu ina bata nutsu ba duk jikinta rawa yake har sai da taga jirgin ya daidaita ya daina jirkitawa. Sannan ta bud’e ido tana kallon Mommah, ita kanta dariya abin ya bata. Ta shafa cikinta da taji yana mata ‘kugi sannan ta kalli Mommah tace “Mommah cikina wallahi kamar zan yi bayan gida.” Mommah tace “To tashi ga toilet can ki shiga.” Da sauri ta zaro ido tace “In mi’ke tsaye anan? Ai wallahi ba zan iya ba.” Mommah ta ‘kunshe dariyar da take cinta tace “Sai ki ri’ke abinki kafin mu isa, minti nawa ne.”

——————
Suna isa airport d’in na Abuja, suka tarar Drivern Hajiya Mama yana jiransu.

‘Karfe 🕤 kuwa a ‘kofar gidan su Mommah tayi musu dake unguwar Gwarimfa a Garin na Abuja. Gidane mai girman gaske wanda da ka ganshi zaka san mazauna cikinsa ba ‘karamin kud’i suka tara ba, wanda za kayi mamaki ‘kwarai Idan aka ce maka ahalinsu Mommah ne a ciki saboda mutanene da basu d’au duniya da zafi ba, ba su da girman kai ko kad’an kuma, ba kamar yarda wasu masu kud’in suke ba.

Duk girman gidan Hajiya Mama ce kad’ai, sai masu mata aiki su biyu mata da biyu maza da ta ajiye. Su Nahna da Hafsa tuni suka koma karatu, shi kuma Hisham ba kasafai yake zaman Nigeria ya fi zama a uk a can yawancin business d’insa yake, sai dai yana yawan zuwa akai-akai.

Hajiya Mama cikin farin ciki da murnar ganinsu ta taresu, musamman Shatu da bata ta’ba kawo mata ziyara ba.

Sai da suka ci abinci suka huta sannan Mommah ta dubi Shatu “sai ki shiga ciki da bedroom d’in su Hafsa kiyi amfani dashi yafi kusa da na Hajiya Maman.” Shatu ta mi’ke da sauri don dama ta gaji burinta kawai ta mi’ke ta kwanta.

Sai da ta shige sannan Mommah tace da Hajiya Mama “Sai ki ganmu kwatsam.” Hajiya Mama tace “Hutu na san kika kawota.” Mommah ta girgiza kai “Hutu ba Hutu ba, Shatu dai ciki ne da ita.” Wata irin fad’uwar gaba ce lokaci d’aya ta riski Hajiya Mama tace “Ciki Kuma? Wani irin ciki ko dad’in ji babu cikin na wanene?” Mommah ta saki murmushin takaici tana girgiza kai tace “cikin Imran, Mama ashe sai da ya riga ya kusanci ‘yar nan sannan ya tsallake ya bar ta.” Hawaye ya kawo idon Mommah alamar ita kad’ai ta san rad’ad’in da take ji. Hajiya Mama tayi salati ta sanar da ubangiji kafin tace “cab wannan fa shine ana wata ga wata, yanzu ya za’ayi shekaru sha biyar yarinyar nan ta iya haife cikinnan ina tsoron lamarinnan in dai ba tiyata za’a yi mata ba,kuma shi Imran d’in ya san da cikin?” Mommah ta girgiza kai “Bai sani ba, don ba ma zan gaya masa ba, don ni tunda ya tafi magana ma ta fatat baki bata had’a ni dashi ba, kuma kema Hajiya Mama please bana son ki fad’awa kowa zancennan shi yasa ma na tattara na dawo da ita Nan,don haka ma tun jiya kika ji ina tambayar ki Dada tana nan kikace ta tafi, don bana son surutunta, kin san mutanennan ba hankali ne da tunani dasu ba sai abin su ya koma kan cikin don haka zan ‘boye zancen Baba kawai na yarda ki gayawa.” Hajiya Mama ta saki ajiyar zuciya kafin tace “Eeh to kema kin kawo shawara abar dubawa, yanzu mutum kam abin tsoro ne sai kana takatsantsan da addu’oi da azkar, Allah yasa mu dace ya kuma raba ta da cikin lafiya amma tabbas kam sai dai ayi mata c.s, kuma ya za’a yi da zancen karatunta?” Mommah tace “Ai kafin na tafi zan saka a samo mata ‘kwararrun malamai Insha Allah ldan ta haihu kuma lokacin ta dad’a gogewa sai ta jarraba zana ssce, saboda Shatu akwai sharp brain masha Allah.” Hajiya Mama tace “sai ‘kiriniya kuma ba da rashin iya girki.” Mommah dariya kawai tayi tana duban Hajiya Mama da tace “Maganar ba kwa waya da Imran ba mafita bace, duk da ba’ace idan d’a yayi wa uwa laifi laifi ne ta ‘kaurace masa ba, amma a gareni ni ban ga fa’ida a cikin haka ba. Fushin uwa ga d’anta ba ‘karamar masifa bace gareshi, idan har ya kira ki nan gaba ki amsa idan ba haka ba kina sake nisanta soyayya da sha’kuwar da take tsakaninku, su yaran yanzu addu’a suka fi bu’kata fiye da fushi, da yawa iyaye su suke lalata yaransu da bakunansu, idan yaro yayi maka laifi madadin addu’ar shiriya sai zagi da masifa iri-iri, don haka ki jajirce da yi masa addu’a nima kuma ina kanyi ba zan kuma fasa ba har sai naga abinda ya turewa buzu nad’i Allah yayi muku albarka da ku da zuri’arku baki d’aya.” Mommah tace “Ameen insha Allah zan sake dagewa Hajiya Mama.”

Koda Babansu ya dawo Hajiya Mama ta sanar masa ba ‘karamin dad’i yaji da samuwar cikin ba, saboda ko bakomai suna son ‘karin yara a cikin zuri’arsu kasancewar ba su da yawa.

—————————————
Mutanen turkey, zamannasu ya zamo ba yabo ba fallasa wata rana a sha zuma wata rana a sha mad’aci, kamar yarda dai hausawa kance zo mu zauna zo mu sa’ba.

Yau ma kamar kullum ya dawo daga office a gajiye, sai dai yana shigowa yaga gidan kaca-kaca kamar yarda ya barshi, mamaki ya kama shi don ya san Shaheeda dai ba ‘kazama bace tana da tsaftar ta iya iyawarta. Ya ‘karasa cikin bedroom d’in kamar yarda yayi hasashe kuwa ya sameta du’kun’kune a gado sai rawar d’ari take. Da sauri ya ‘karasa ya yaye blanket d’in yana furta “Me ya sameki haka?” Murya a cunkushe tace “Bani da lafiya” ya mi’ka mata hannu “oya tashi mu tafi Asibiti.”

Tun a hanya take kwara amai, duk da hankalisa a tashe yake amma farin ciki bai bar zuciyarsa ba. burinsa yaje hospital a tabbatar da zarginsa na cewa Shaheedahn ciki ne da ita saboda Allah ya saka masa son yara.

Suna zuwa kuwa aka yi test da scanning bayan likitan ya tambayeta yanayin da take ji. Da murmushi Doctorn ya dubeshi “Congratulations she is pregnant.” Wani sanyin dad’i ya ratsa zuciyar Imran, yayin da Shaheedah taji labarin yazo mata kamar dirar mikiya take annurin da yake fuskarta ya ‘bace ‘bat.

Am sorry for the late posting..

🤍ME ZAN YI DA ITA?🤍

  NAZEEFAH SABO NASHE

FREE📚
08033748387
-33

Elegant Online Writers.

Mamaki ya cika zuciyar Imran har bai san sanda yace mata “Madam Lafiya?” Ba tare da ta amsa ba ta mi’ke tayi hanyar fita, hakan yasa shima dole ya mi’ke yabi bayanta.

Tun a mota yake jero mata tambayoyi amma tayi d’if da ita, ‘karshe ma runtse ido tayi tana tunanin zuci, har bata san zancen da take d’arsawa a zuciyarta ya fito fili ba “Ina ni ina ciki yanzu, wallahi ban shirya ba, ban shirya wata haihuwa yanzu ba, shikkenan duk na bi na lalace jikina ya susuce, bayan yanzu ne na san na fara sanin dad’in duniya sannan wani baby can ya rusa min shi, ban shirya haihuwa ba gaskiya, don haka kayi ha’kuri cire cikinnan zanyi.” Wani kallon da bai shirya ba ya watsa mata, saboda yarda ta ha’ki’kance take magana ba ko shayin idanunsa yaga alamar kuma zancen nata daga ‘kasan zuciyarta yake. Bai mata magana ba har suka isa gida.

Sai da suka zo kwanciyar barci yace mata, bayan ya gaji da kuka da ro’kon da take masa akan a zubda cikin. “Meye dalilinki na rashin son haihuwa yanzu?” Ta mi’ke tana sake murza idonta da share hawayenta tace “Kai kanka idan kaji hujja ta sai kafi ni son a zubar da cikin, na farko dai na san baka son mace mai ‘kiba ka sha kuma fad’a min hakan, to wallahi haihuwa da wuri shi yake saka mace ta bud’e ta zama kamar uwar mata. Sannan duk wata ni’imar ta raguwa za tayi breast, hips d’ina da komai ma sai nayi loosing d’insu, don haka please Habibi mu bari nan da ten years haka sai muyi shirin haihuwa, kana ga dai yarda matar khalil abokinka ta zama lutiya, to wallahi haka zan zama.” Shiru Imran yayi ya fad’a dogon nazari a hankali yace “Idan haka ne zan bi ra’ayinki on one condition amma idan likita yace ba matsala idan aka cire cikin, ba kuma matsala tattare da yin planning d’in.” Cikin farin ciki ta rungumeshi “Insha Allah Habibi bakomai ma.” Yayi smilling yana lakuce mata hanci “kin ci sa’a bana son ‘katuwar mace kuma kince saurin haihuwa na sa mace ta bud’e, idan ban da haka da ba zan yarda ba wallahi, to ni d’in ma dai bana son zama Daddy soon, amma fa ina da son yara.”

———————————
Kwanan Mommah uku a Abuja ta tattara ta tafi ta bar Shatu da tsananin kewarta, don da kuwa gaba d’ayansu suka tafi, har abin yada dinga bawa Hajiya Mama tausayi ta jinjinawa girman sha’kuwar Shatu da Mommanta.
Amma haka suna ji suna gani suka rabu da juna.

Bayan tafiyar Mommah Hajiya Mama gaba d’aya ta mayar da kulawarta akan Shatu da abinda yake cikinta. Cima mai kyau da Abin sha mai kyau da zai ‘kara mata lafiya da ta jaririn da yake cikinta. Tayi ‘bul’bul da ita gwanin sha’awa kamar ka ta’ba jini yada fito. Kullum Ammar sai ya kira ta yaji lafiyarta ya kuma tambayeta bata da wata matsala? Kiran nan uku a rana ya zame masa tamkar tilas a gareshi, ita bata kawo komai sam a ranta ba har a yanzu a matsayin d’an uwa mafi kusanci ta ajiye shi. Kullum Mommah tana kiranta taji ya yanayin jikinta da karatunta? Tana jin dad’in ganin yarda take samun Improvement a karatun, both islamic da boko ta san ba zata bata kunya ba.

Ko da aka koma school Dahda ya ishi Mommah da zancen dawowar Shatu, direct tace Hajiya Mama ta ri’keta zuwa shekara d’aya zata dawo. Dahda sam bai kawo komai a ransa ba, yace Allah ya nuna mana amma dai ba fishi su kayi da sakin da Imran yayi mata ba ko?” Mommah ta girgiza kai “Ko d’aya ai sun yarda da ‘kaddara.” Bayan haka da kwana biyu Mommah tasa Shatu ta dinga kiran Dahdan tana gaisheshi.

Sanda tafiya ta kama Ammar zuwa Qatar a can yaof siyo duk wani kayan baby da za’a bu’kata, komai unisex duk da a lokacin cikinnata bai fi wata shidda ba.

———————
Bikin ‘yar gidan falamata ‘kanwar Dahda, hakan yasa su Mommah suka fara shirin tafiya bikin, duk da bata son zuwa amma Hajiya Mama tace taje duk kuma abinda aka yi mata kada ta tanka ta kawo ido ta zuba. Kada tace ‘kala. Hakan yasa dole ta shirya ta bi Dahda da zai tafi. Don ita zainab sune ‘kirjin biki tuni na ta tafi.

Dahda yana da gida a maiduguri don haka a can suka sauka, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta tafi gidan Hajjan. Mota cike da kayan gudumawa.
Gidan dan’kam da jama’a ta samu. Babu mai yi mata kallon arziki kowa wani irin duba yake mata, ‘kalilan ne masu murmushin da bai kai ciki ba. Gefe ta samu ta zauna ita da Basirah mai aikinta kasancewar Hajjan na cikin bedroom d’inta, kuma bata bata fuskar shigar mata d’aki ba. Tsawon lokaci tana zaune Hajja bata fito ba, jama’ar wajen kuwa ba wanda yake ta tata, hakan yasa ta zauna tana dannan wayarta.

Tafi Awa d’aya da zuwa kafin Hajja ta fito daga d’akin ‘yan koranta na bayanta alamar an san da zuwanta, don duk fuska ba walwala suka fito. Mommah na ganinta ta dur’kusa har ‘kasa ta gaisheta, tamkar ba zata amsa sai kuma ta amsa cikin ginshira.
Basirah ta jawo babbar ghana must go ta kayan da suka kawo ta dire a gaban Hajjan, daga haka ta fice daga parlourn ranta a ‘bace da kallon rainin da ake yiwa uwar d’akinta, matar da take mata kallon mahaifiya don kuwa Mommah tayi musu ri’ko na fisabilillah da ko a gidajen iyayensu ba zasu samu irn kular da take ba su ba.

She’ke’ke Hajja ta dubi kayan, ba Ta kuma ko bud’e ba tace “An Gode.” “Hajja ai ba ita zaki godewa ba Ya manga za’a godewa don na tabbatar shi ya bada kud’in.” Mommah ta zuba mata hameedah da tayi maganar ido saboda yarda ranta ya ‘baci don kosun ficikar Dahda babu a cikin kayannan, amma da yake ba sa sonta balle ace tayi alheri dole suce Haka, wannan ta guda tace ba zata zo bikin ba gashinan tunda ga yanzu ta fara riskar takaici. Hajja ta gyara zama “Alhamdulillah dama ina ta son ganinki, ya kika ji da ‘bacin ran sakamakonki tun yanzu kuma ashe kin fara girbar abinda kika shuka, Imran kuma ya saki ‘yar taki, ko bakomai ya nuna miki baki isa ba, ina isar taki da kike tin’kaho da ita? Ai dama Na san ko mu dad’e ko mu jima sai tarihi ya maimaita kansa, yarda kika hana d’ana yi min biyayya kema sai kin riski sakamakonki gashi nan kuwa dahir kin gani. Kwana uku da aure ya sako miki ita.” Gaba d’aya gurin suka saka dariya Idanun Mommah suka kawo ‘kwalla, har zata tanka musu sai kuma taa tuna umarnin Hajiya Mama, don haka dole tayi shiru tana jan addu’oi a zuciyarta, ko bakomai Imran ne ya jawo mata, mi’kewa kawai tayi ta fice daga gidan don bata son zubar da hawaye a gabansu. Hannun Basirah ta ja suka bar gidan tana sake jiyo sanda Hameedah tace “Aikin banza gayyar tsiya kawai ta bi ta mallake mana d’an uwa.”

Ko da ta shiga motarr driving d’in kawai take ba cikin nutsuwa ba, yarda zuciyarta take tafarfasa tamkar ta fasa ‘kirjinta ta fito hakan yasa ta samu gefen titi tayi parking hannunta dafe da ‘kirjinta ta shiga kiran layin Dahda don ba zata iya cigaba da driving d’in ba, da kyar ta sameshi ta gaya masa halin da take ciki. Basirah kuwa hankali tashe take tofa mata duk addu’ar da tazo bakin Ta.

Cikin mintuna ‘kalilan Dahda ya bayyana a wajen cikin tashin hankali ya d’aukota cak daga cikin motar numfashinta yana fisga da ‘karfi, da sauri ya sata a seat d’in baya kanta saman cinyar Basirah yaja motar da wani irin mahaukacin speed. Suna isa asibitin dama tuni yayi waya don haka suka tarar da wheel bed aka yi saurin d’orata akai aka turata a guje don numfashinnata gaba d’aya yana shirin d’aukewa.

—————
Wani irin mugun mafarki da Shatu tayi sakamakon kwanciyar da tayi barcin rana shi ya farkar da ita a razane, cikin firgita take kiran “please Mommah kada ki mutu bana son na rasa uwa a karo na
Biyu.” Da sauri Hajiya Mama ta kamata don itama tun safe gabanta yake fad’uwa ba wai tana jin dad’in jikinta bane. Idan kuwa ta shiga irin wannan yanayin zahiran mutuwa ce babu tantama. “Kiyi addu’a ba’a son tashin hankalin mai ciki.” Hajiya Mama ta fad’a cikin ‘karfin hali da dauriya. Da sauri Shatu ta rungumeta “Hajiya Mama don Allah ki kaini wajen Mommah. Mafarki nayi ta mutu.” Wani irin tashin hankali ya riski Hajiya Mama don bata san sanda ta dafe ‘kirjinta da yake bugawa ba ta kama Shatu ta rungume kawai ba tare da tayi magana ba, ‘kirjinta yana bugu fat-fat.

———————

Dai-dai wannan lokacin shi kuma Imran suna gaban Doctor shi da Shaheedah. Bayan rattabawa Doctor bu’katar su ta zubda ciki da kuma son tsarin iyali Doctor ya tabbatar musu ba wata matsala. Har ya sake ‘karfafa musu gwiwa abinda ya dace kenan it’s too early ace sunyi aure ko shekara ba ayi ba su haihu, zai zubar mata da cikin tunda bai wuce 3months ba tablet kawai zai bata, cikin zai fice. Maganin tsarin iyali kuwa zai d’orata akan methoe d’in da zaiyi dai-dai da tsarin jikinta, har zuwa sanda zasu bu’kaci haihuwar, idan ma bata son d’aukar ciki da haihuwa zasu iya yi mata dashen kwalba ko a samu wata macen a dasa mata cikin ta haihu ta yarda halittarta ba zata canja ba, tunda bata so. Hakan yayiwa Shaheedah sosai ta kuma raya a ranta idan time d’in yayi abinda zata yi kenan.

———————-

Doctors sosai suke ‘ko’karin ceto ran Mommah, duk da hankalinsu suma a tashe yake don har zuwa lokacin numfahsinta gaba d’aya ya d’auke sunyi-sunyi ya’ki ya dawo.

Dahda hankalinsa a tashe yake zirga-zirga yake kawai bakin emergency d’in zuwa lokacin da
Yaga fitowar Doctor d’in daga d’akin. Yanayin yarda yaga fuskar Doctor d’in yasa zuciyarsa matu’kar bugawa da ‘karfi…..

ME ZANYI DA ITA?

34

Dahda yayi saurin dafe ‘kirjinsa yana ambaton addu’oin da duk suka zo bakinsa, a zahirin gaskiya shi kansa bai san abinda bakinsa yake furtawa ba.
Har zuwa sanda likitan ya iso wajensa. Ya dubeshi kafin yace sai dai kuyi ha’kuri mun yi ‘ko’karin ganin ta dawo hayyacinta, sai dai still she is unconscious, amma dai muna saka rai za’a samu nasara insha Allah. Dahda ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya, ji yake a rayuwarsa bai ta’ba samun kyakykyawan labarin da ya zarce wannan ba. Alhamdulillah ya furta a hankali har yana sakin d’an guntun murmushi yace “Doctor Allah ya baku nasara, ni kuma nayi al’kawarin yi muku kwaskwarimar asibitin nan cikinsa da bai. Amma Doctor kana ganin meye musabbabin ciwon nan?” Doctor yace “Gaskiya ba zan ‘boye maka ba,musabbabinsa ‘bacin raine mai tsananin gaske da ya cunkushe zuciyarta ya hanata functioning yarda ya kamata.” Dahda yace “Na san za’a rina, Dijah da na sani ban amince da zuwanki bikinnan ba, amma wallahi sunyi na farko sunyi na ‘karshe yau zan nuna musu bad side d’ina da za suyi mamaki, in dai na tabbatar su d’inne silar ciwon Dijah.” Duka wannan zancen Dahda a zuciyarsa yake yinsa, sam bai san ma Doctor d’in tuni ya wuce da sauri ba ya koma ‘dakin da Mommah take dama abu yazo ‘dauka.
Basirah ya kalla ransa a ‘bace ya shiga rattabo mata tambayoyi, tamkar dai ‘dan jarida.
Basirah kuwa bata ‘boye masa ba, ta bashi labarin zahirin abinda ta sani. Dahda ransa ya shiga ‘kunci da tunanin anya Hajja tana sonsa kuwa? Tabbas da tana sonsa, da ta so farin cikinsa Dijah, su ba su san Dijah zai iya fad’a kansa tsaye itace rayuwarsa ba. Uwa-Uwa ce dole ya ‘daga mata ‘kafa, amma Hameedah kam tabbas yau zata san waye shi, zai je mata a zahirinsa na Ahmad ba Mangan Hajja da suka sani ba.

———————

Hajiya Mama hankalinta a tashe, ta shiga kiran wayar Manga, bayan ta gwada ta Mommah sau shurin masa’ki ana sanar mata is switch off. Bugu biyu ta ci nasarar Mangan ya ‘dau wayar. Bayan gasiheta cikin girmamawa, ta tambayeshi isarsu lafiya sannan ta d’ora da tambayar Dijah. “Na kira Addar tasu ya fi sau nawa bana samunta, Allah dai yasa lafiya?” Manga ya saki ajiyar zuciya Uwa kenan, ita ce mafi kusanci da zuciyar ‘ya’yanta, gashi dai har taji a jikinta Dijan ba lallai ta zama tana lafiya ba. “Bakomai Hajiya Mama, sai dai tana bu’katar addu’a don tana kwance anyi admitting d’inta a hospital, amma dai Alhamdulillah cikin hukuncin ubangiji da sauki.” Maimakon ta shiga ru’dani kamar yarda Manga ya yi hasashe sai yaji tace “Ubangiji Allah ya bata lafiya, yasa kaffara ne, zuwa gobe idan yanayin jikinnata ba afuwa insha Allah zan biyo flight, a kuma cigaba da addu’a ba’a ja da hukuncin ubangiji, cuta da mutuwa duka lamarin ubangiji ne, shi ya saukar da cuta ya kuma samar da maganinta.” Manga ya saki ajiyar zuciya yana gasgata ‘karfin Imani na surikar tasa a zuciyarsa, shi yake ganin girmanta a ko da yaushe. A hankali yace “Nagode Hajiya Mama, idan ta farka zan ha’daku a wayar.” “Allah ya farkar da ita lafiya yasa muji alheri. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” “Ameen” Manga ya furta. Yana disconnecting wayar.

Sai da ta kashe wayar sannan ta dubi Shatu da duk nutsuwarta ta tattara ta akan Hajiya Maman tana jiran ‘karin bayani. “Ki kwantar da hankalinki, Mommah ba mutuwa tayi ba, tana dai kwance bata da lafiya, mafarkinki kuma insha Allah ba zai zama gaskiya ba.” Shatu hawayene ya sake zubo mata gaba ‘daya hankalinta yafi ‘dazu tashi tunda taji Mommah ba lafiya hankalinta ba zai ta’ba kwanciya ba har sai Mommah ta samu lafiya.
Hajiya Mama cikin zafi ta katseta “Bana son sakarci kin ji ko? Menene abin kuka wa yace miki a yanzu kukanki take bu’kata? Idan kika cigaba da yi min kuka tafiyata zanyi wajenta Na barki, dama dalilinki zan zauna ban tafi ba sai Na ji yarda ta kaya gobe tukunna.
Kuma ki tashi ki je ki nemi abinci ki ci, kafin kisa mu wani tashin hakalin, ayi haihuwar guzuma ‘ya kwance uwa kwance.”

——————————-

Tablet ‘din abortion ‘din da ta sha, bai tashi yi mata aiki ba sai cikin dare. A mugun razane ta farka hannunta dam’ke da mararta da take jin tamkar zata dare. Cikin tashin hankali ta fara dukansa tana kiran sunansa. Shima a ‘dimauce
ya farka yana duban yarda take mur’kususu. “Imran help please!” Ta fad’a da ‘karaji, yayi saurin mi’kewa yana tayar da ita, ganin shegiyar rigar barcin da take jikinta ya sashi sauri zaunar da ita, ta mi’ke da sauri don ta ma kasa zaman, shi kuwa ‘ko’kari yake ya suturce mata jikinta, ganin duk ta ru’de ya sa shi zira mata hijabi kawai ya sunkuceta cak a guje suka fita compound ‘din gidan.

An sha gwagwarmaya sosai a asibitin kafin cikin ya fita, sannan aka yi mata wankin ciki aka bata hospital Gown tasa, don rigarta tayi kaca-kaca da jini.

Tana kwance akan gadon ya shiga ‘dakin, idanunsa akanta, yana mamakin yarda ta zabge lokaci ‘daya, sai ga shi yau dai yaga zallar muninta, don bai ta’ba ganinta ba makeup ba sai sau ‘daya shima bata kai haka lalalcewa ba.” Ya zauna a gefenta, yana kallon asalin gashinta, ashe wanda da yake gani duk gashin doki ne, sai yau yaga nata na ainahi wanda ba zai fi nasa da kad’an ba. Ya dai ta’be baki yana zama a gefe yace “Ya jikin?” Cikin kunyar kanta da yanayin da ya sameta yanzun na bayyanar ainahin halittarta ta shiga kau da kai. “Mu tafi gida Habibi wallahi ina son hutawa.” Ya girgiza kai “sun ce ba yau ba, ba ma wannan ba za suyi miki planning d’in da kike so sunce a tambayeki za’bin wanda kike so.” Zura masa ido tayi kafin a zuciyarta tace “Ina? Ai wallahi gida zan tafi ba zan zauna ka dinga ‘kare min kallo ba a haka har sai ka hango muni na.” Murya a sar’ke tace “planning daga baya ai sai muzo ayi ni nafi son su saka min inplan.” Ya ta’be bakinsa. Ta lura sosai da wani irin kallo da yake jifanta dashi, abinda yake dake ‘daga mata hankali.

——————————————-

Cikin Iko da izzar khali’ku, Mommah ta farka, idanunta akan dandazon likitocin da suke tsaye a kanta su kusan goma. Tana ganin sanda suka fara fa’din Alhamdulillah, suna mamakin yarda suka samu nasara haka, don da har sun cire rai. Ni kuwa nace Allah ai maji ro’kon bawa ne Hajiya Mama da Shatu da duk wani da yake da kyakkyawar ala’ka da Mommah ranar baiyi barci ba, addu’a suka kwana suna yiwa Mommah da fatan samun lafiya. Tabbas naga tasirin addua da girman ubangiji.

Bayan an gama kimtsata, sannan suka tura ta zuwa ‘dakin da zata huta. Sai lokacin Manga da Basirah suka san ta farka. Da sauri Manga ya ‘karasa wajen idanunsa cikin na Mommah da take sakar masa kyakkyawan murmushi, wanda kana ganinsa ka san na tsagwaron ‘karfin hali ne. Kawai likitoci da malaman jinya sai gani su kayi Manga ya dur’kushe ya kai goshinsa ‘kasa yayi sujjada. Gaba ‘daya wurin sun gasgata da girman soyayyar Manga da Matarsa. Dariya kawai ake masa, musamman ganin yarda yake hawaye hannayensa a sama ya mi’ka godiyarsa ga Jalla wa Azza.

A Amenity aka ajiyeta, hannayenta cikin na mijinta, nurses suka zo zasu ‘da gata, da sauri ya tsayar dasu da kansa ya zaunar da ita ya jinginar da ita a jikinsa, yana shafa bayanta. Ita kuwa tayi lamo a jikinsa cikin shau’ki da tsananin son Mijinta. Suna fita Basirah itama Ta bisu bayan ya mi’ka mata key d’in gidansa na maiduguri “Kije ki yiyo break-fast, sannan ki ha’do mata kayan da zata bu’kata.” A kunyace ta amshi key ‘din ganin yarda ya rungume Mommah da tsam tamkar wani zai ‘kwace masa ita. Suna fita ya ra’da mata a kunnenta “I love you Dija na, tabbas da wani abu ya sameki, ban san ya rayuwata zata kasance ba, dole nayi azimi uku na godiya ga rabbil izzah.” Murmushi tayi tana wasa da fingers ‘dinsa, shi kuma ya ciro waya yana kiran layin Hajiya Mama. Bugu ‘daya ta ‘dauka alamar dama a ‘kage take ya kira ta. Ba tare da yayi magana ba ya kangawa Mommah wayar a kunne, cikin kasalalliyar muryar ta tace “Assalamu Alaikum.” Hajiya Mama bata san sanda murmushi ya su’buce mata ba tace “Alhamdulillah ala ni’imatihi tatummussalihati Addarsu ya jikinnaki?” Mommah tayi murmushi cikin kasalalliyar murya tace “Alhamdulillah, wallahi naji sau’ki Mama, ina Shatu?” Hajiya Mama ta mi’kawa Shatu wayar da take jin tamkar ta fisge. Tana sawa a kunne cikin dariya tace “Mommah kin warke?” Dariya tayi tace “Insha Allah Shatu, Allah yasa dai baki saka damuwa a ranki ba kin san…” sai kuma tayi saurin katse maganar ganin idanun Dahda a kanta. Ta ‘karasa da “komai na Allah ne.” Shatu tace “To Mommah na har naji da’di Allah ya baki lafiya idan Hajiya Mama zasu taho anjima zan biyosu.” Da sauri Mommah tace “A’a kada ma ki fara, kin manta abinda nace miki?” Kamar tayi kuka taji Mommah tace “Mi’kawa Hajiya Mama wayar, tana bata Shatu ta fice tana hawaye ita haka kawai dalilin wani ciki a hanata ganin Mommah, cikin jin haushi ta kaiwa cikin duka “ladan janyowa da kai ka hanani ganin uwata, da ‘katon kanka kamar na Babanka.” Sai kuma ta ri’ke baki Oh kuji shashanci na ko a ina naga kanna sa?” Ta saki murmushi kawai tana shigewa kitchen jin zaburar da cikin yayi “Acici na san yunwa yake ji, ko kuma don na masa ‘dan wannan dukan ne, yaro baka sha duka ba sai kazo duniya tukun in rama duk abinda ubanka yayi min a kanka.”

————

Tana gani su Hajiya Mama suka tafi, ita kuma aka barta da Iya shugabar ma’aikatan cikin gidan, Haushi ne ya kama Shatu ta le’ka ta windown motar tace “kuma wallahi Hajiya Mama kafin ki dawo sai na shanye duka kayan za’kin gidannan ba dai kin hanani ba.” Hajiya Mama ta ware ido kafin tace “Au ta’bargazar da zakiyi kenan! To na san maganinki muje cikin gidan.” Shatu ya wuce tana tura ciki, da har mamaki girman cikin yake bawa Hajiya Mama kamar ba cikin fari ba, yayi girma sosai ga Shatun ta sake bud’ewa. Hajiya Mama tace “Allah ya raba lafiya.” Sai da ta kwashe kaf kayan za’kin gidan tas, ta kuma kira masu aiki ta basu dokar kada wanda yaba Shatu kayan za’ki, sannan ta tafi. Alhaji Babba Babnsu Mommahn da zasu tafi tare sai dariya yake mata ita da Shatun da take ta sake tunzira Hajiya Maman. Kuka ta zauna ta dinga yi a parlourn kamar yarinya sai watsi take da throw pillow d’in parlourn. Masu aiki sai dariya suke mata suna fad’in SHATU DANGER kamar yarda suka ji Hisham yana gaya mata.

Isar su Airport ‘din ke da wuya suka tari taxi suka nufi asibitn bayan sun gayawa drivern sunan Hospital ‘din.

Dahda ne ya fito harabar Hospital ‘din bayan sun sanar da isowarsu ta cikin waya.

Sun tarar jikin nata da sau’ki, sai dai har yanzu numfashinta bai koma normal ba, tana yi tana hutawa. Hajiya Mama da Alhaji Baba sun tausayawa ‘diyar tasu sosai, musamman ganin duk juriyarta an wayi gari zuciyarta ta kasa, dama duk cikin ‘ya’yansu ta fi kowa ha’kuri. Alhaji Baba ya dubi Manga bayan sun fita yace “ina son ganin Doctors d’in nata domin naji ainahin abinda yake damunta, idan kuma ba matsala zan fitar da ita waje ko egypt haka ko Germany.” Dahda ya girgiza kai “ Bakomai Alhaji Baba amma kamar hakan nauyi nane kuma ko baka fa’da ba nayi niyyar aikata hakan. Sannan matsalar dangina ce musabbabin wannan ciwo nata ba zan ‘boye maka ba.” Nan ya shiga bawa Alhaji Baba labari.

Kafin a gama bashi labarin gaba ‘daya ransa ya ‘baci cikin wani yanayi yace “Ashe har yanzu jahilcin nan ba zai kau daga zuciyar malam bahaushe ba, me ye laifin yarinyar da ta auri ‘danki ko ‘dan uwanki? Sannan kuma mai yake jawo wannan muguwar tsanar da gaba ta dangin miji? Da suke tsangwamar mutum bai ji ba bai gani ba a nawa tunanin jahilci ne da hassada, da kuma jayayya da lamarin ubangiji, haka ne mana kina ganin Allah bai iya ba da ya bawa ‘danki mata wance, ko kuma bai iya ba da ya bawa ‘dan uwanki mata wance, a wannan zamaninfa ba dama aga mace tana zama da mijinta lafiya sai ace ai ta mallakeshi ta asirceshi alhalin ba a san mizanin ha’kurinta akan shi mijin ba, ya kamata mutene su farka a daina jayayya da hukuncin ubangiji. Sannan kayi ha’kuri Manga an zo ga’bar da ya kamata ‘yan uwanka su san Dijah tana da gata, sannan karamci da kawaici na mahaifiyarta yasa nake ‘dauke kai nake ha’kura kamar yarda taso idan banda haka da tuni na nunawa danginka ina son yarinyata, don duk cikin ‘ya’yana ba na biyunta a biyayya, zan ‘dauke Dijah zuwa gida na har sai ta samu lafiya sannan kuma sai maza daga zuri’arku sun zo an zauna, don bana fata na wayi gari ace zuciyar Dijah ta buga dalilin kyara da tsangwamar danginka. Ba kuma don komai zanyi haka ba sai don kanku kai da Dijan su sakar muku mara su barku ku sha’kata ina dalili shekara da shekaru ayi tayin abu kamar cin ‘kwan makauniya.” Manga shiru yayi ba don zuciyarsa ta amince a tafi masa da Dijah ba sai don
Baya son jayayya da surikinsa dattijon arziki, da duk abinda ake bai ta’ba magana ba sai yanzu da tura ta kai bango. Alhaji Baba ya dafa shi yana murmushi yace “kada ka damu ba rabaka zanyi da Dijah ba, asali ma sashe guda zan baku a gidana kafin mu ga abinda hali zaiyi. Sannan kuma ka gayawa su Imran bata da lafiya?” Dahda ya girgiza kai, Alhaji Baba yace “Hakan bai dace ba kayi ‘ko’karin sanar dasu su zo su dubata, ko bakomai uwa-uwa ce, kuma ita kanta zata so ta gansu yanzu. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” Ameen manga yace, hankalinsa ko yanzu ya kwanta jin sashe guda zai basu da Dijah.

Basu bar gurin ba sai da kuwa Dahda ya kira Ammar ya sanar dashi, cikin tashin hankali Ammar yace yana nan tafe ko zuwa dare idan ya samu jirgi. Ya kira Imran ya gaya masa Imran sak yayi zuciyarsa Na bugu yace “Please don’t hide the truth ka gaya min idan Mommah mutuwa Tayi? Na shiga uku ya zanyi…” cikin tsawa Dahda yace “idan mutuwar ma tayi kai kana da asara ne ba dai ka za’bi farincikin wasu ba fiye da Na mahaifiyarka. To Na baka 24hours duk abinda kake kazo ka ganta ba ta da lafiya kuma umarni Na Baka.” Daga haka ya yanke kiran ya bar Imran da waya a hannu hawaye Na bin ‘kuncinsa zuciyarsa Na wani irin bugu da ‘karfin gaske tamkar Zara bud’e ‘kirjin ta fito. Da azama ya mi’ke yana kallon Shaheedah da take kwance a gadon asibiti ya ‘dau car key ‘dinsa tare da furta “Nigeria is calling……! Shaheeda ta waro ido tana kallonsa.

(Ku fito mu tattauna, shin me yake kawo ‘kiyayyar dangin miji da matar ‘dan uwansu? Me yake kawo rashin jituwa tsakanin uwar miji da surikarta? Kowa dai ya san abubuwan da suke yawan faruwa kenan a duniyar mu ta yanzu. Mecece Mafita? Sannan laifin wanene?”)

Jikar Nashe ‘yar mutan makwarari mai ta’kama da ikon Rabbi. Sai naji daga gareku!
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi Da ita?

35

Cikin ‘bacin rai ta kamo hannunsa, idanunta cikin nasa kafin ta furta “Haba Habibi yanzu Nigeria zaka tafi? Ka bari na samu sau’ki mana sai mu tafi tare, wai shin mai ma ake yi a Nigerian?” Zame hannunsa yayi kafin yace “Zuwa ta Nigeria ba shi zai hanaki samun lafiya ba, Mommah ce ba lafiya kuma Dahda yayi min umarnin lallai na tafi. Ko da ma baiyi min ba ya zama tilas naje na ga jikin Mommah.” Har ya kai ‘kofa ya jiyo yace “zan sanar da grace tazo ta zauna dake.” Yana fita ta saki ajiyar zuciya, ‘kirjinta yana matu’kar suya da saboda tsananin ‘bacin rai. Da sauri ta lalibi numberr Anty Amarya ta shiga danna mata kira ba ji ba gani.

‘Daga wayar ke da wuya, Shaheeeda ta sa mata kuka “Ki taimakeni Anty, wallahi kamar komai ya warware ina hango tsanata a idanun Imran, duk da bai furta ba ina jin tsoro Anty. Yanzu ma fa Nigeria zai taho wai Mommah ba lafiya.” Anty ya ri’ke kanta, ga shi time ‘din tana cikin dangin su, ana ta sha’anin biki ba damar tayi wani abin. “Kiyi ha’kuri, zan san abin yi, ba dai Nigeria zai zo ba Allah ya kawo shi lafiya.” Shaheedah ta kashe wayar ranta a ‘bace don ba haka Ta so ta ji ba, so tayi Antyn ta san yarda aka yi ta hanashi zuwa Nigerian gaba ‘daya.

—————-
Bayan fitar Dahda daga hospital ‘din direct Family House ‘dinsu ya tafi ransa a ‘bace matu’ka, dama rashin mai zama da Mommah ya hana shi zuwa yayi musu maganar.

Tun daga corridor ‘din sashen Hajiya yake jiyo ihunsu da shewarsu, yana jiyo Anty Amarya tana cewa “Ai cewa yayi bata da lafiya, shi yasa bai zo ba tun jiya.”
Hameedah tayi zumbur tace “Shegiya ina ma mutuwa tayi muka huta da gayyar tsiya.” Hajja tace “Wallahi kuwa, wannan masifa har ina? Ni na rasa yarda zanyi na datse wannan auren, amma kam na tsani yarinyar nan.” Zuciyarsa ce ta sake dugunzuma kamar mai? A zafafe ya danna ‘kofar ‘dakin da ‘karfin gaske,da yasa su saurin ‘dagowa suna kallonsa. Gaba ‘daya suka firgita har Hajja, musamman ganin yarda idanunsa suka ka’da su kayi jazur, ya kalli Zainab sai kuma ya mayar da kallonsa kan ‘yan uwansa mata, “Duk abinda kuke fa’da ina jinku, a yau kuma na sake tabbatar da al’amarin tsanarku da Dijah mai girma ne, ba tare da sanin wani laifin Dijah tayi muku ba, laifinta ‘daya da ta aureni take tattalina da nuna min soyayya, ku kuma abinda ba kwa so kenan kun fi son ku ganni da macen da zata dinga ‘daga min hankali, don haka ayau ba sai gobe ba zan tabbatar muku mahaifiyata kawai nake shakka, kuma ita ka’daice wacce ba zan iya rabuwa da ita ba, kun saka mata a gaba gata can a gadon asibiti zuciya ta cunkushe da ‘bacin rai, ku ko kunyar yaranta ba kwa ji? To daga yau na yanke ala’kata daku matu’kar ba zaku zauna da matata ‘kalau ba, ke kuma zainab kije na sakeki saki ‘daya.” Gaba ‘daya wajen ihu aka saka da salati, Zainab kuwa cikin tashin hankali take kallon Hajja tace.” Hajja please kice wani abu mana, kina ji yace ya sake ni.” Cikin takaici Hajja tace “Ince mai Zainab? Ina da mutunci ne a idonsa? Kina jin irin maganganun da yake fa’da a gaba na saboda baya gani na da mutunci, zuciyar Manga gaba ‘daya an canja ta, ni kuma yarda ya rabu da ‘yan uwansa akan Dijah ya kuma sake ki, ina tabbatar masa nima na zare hannuna daga lamarinsa, yaje dangin Dijah su zame masa uwa da uba. Na sallama musu shi wallahi.” Hawaye ne taf a Idonta, don lamarin Manga ya kere tunaninta. Cikin wata irin karayar zuciya Manga ya zube idanunsa cikin na Hajja ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta ihu, ba tare da yayi magana ba ya juya ya fice, da sauri tamkar tashin iska.

———————
A ranar aka sallami Mommah, cikin hukuncin ubangiji jikinnata da sau’ki sosai. Fargabar ta ‘daya komawa Abuja da aka ce zata yi bata so ta koma saboda bata son a san Shatunta na da juna biyu.

A ranar kuwa suka bi Flight zuwa Abuja, bayan Hajja ta sanar da ita ba matsala, suna da c.c.t.v camera yanzu a gidan, suna ganin mai shiga da fita a gidan duk wanda yazo zata saka Shatun Ta shige bedroom. Hakanne ya kwantar da hankalin Mommah, ita ma kam wannan ciwon ya razana ta kuma yanzu tana bu’katar a kar’bar mata ha’kkinta bata son ta rasa rayuwarta a garin kawaicin ta na banza.

Tun safe Shatu ta shiga gyaran gidan, bayan Hajiya Mama ta sanar da ita da Mommah za’a taho, tsananin murna yasa ta fara shiryawa Mommahn girkuna masu da’di burinta Mommahnta ta san a yanzu itama ta fara zama ‘kwararriya a ‘bangaren Girki-Girke na mu na gargajiya da na ‘kasashen ‘ketare. Mandi Rice tayi mata, sai chines Rice aka kuma Gasa mata kaji Gashin larabawan Oman, sannan aka yi mata Gizdodo, da kunun aya da Dinger drink sun kuwa yi da’di sosai, ‘bangaren snacks kuwa had’addiyar pizza tayi mata da fish roll don ta san tana matu’kar sonsu sosai. Ta gyare mata ‘daki tsaf, inda ta saba sauka sam Shatu yau ko nauyin cikinta bata ji burinta ta kyautatawa Mommahnta.

——————————

‘Karfe 6:00 jirginsu yayi landing, a Nnamdi azikwe International airport, kamar ha’din baki dai-dai lokacin da jirgin su Imran yayi landing kenan, tsakaninsu mintuna ‘kalilan ne. Sai dai basu had’u ba don su Mommah sun riga shi fita saboda nasu jirgin na gida ne.

Wayar Dahda ya shiga kira don ya gaya masa isowarsa Abuja da safe kuma zai biyo jirgin Kano. Dahdan ya sanar dashi Suna Abuja suma a yanzu hakan gidan su Mommahn. Gaban Imran ya fa’di, addu’a ya dinga yi Allah kada ya tabbatar da Hasashensa ace Mommah mutuwa tayi, idan banda haka mai zai dawo da ita Abuja.

Gwiwoyinsa a salu’be ya samu taxi don tafiya gidansu Mommahn da yake unguwar Gwarinfa. Zuciyarsa cike da fargaba.

—————

Tunda su Mommah suka isa take bin Shatu da kallo, ganin yarda take ta hidima da ita ko nauyin jikinta bata ji, ga cikin yayi mata wani turtsetse, sai jansa take yi, kuma Shatun tayi duhu ka’dan ta kuma kumbura ka’dan. Sai da ta gaji da zirga-zirgar sannan ta zauna a hankali tana furta wash. Mommah ta jata jikinta tana matsa mata yatsun hannunta, murya a ‘kasa alamar ta marasa lafiya tace “Shatu haka kika canja? Mai Hajiya Mama take baki? Naga cikin yayi girma sosai kamar ya wuce watanninsa.” Murmushi Shatu tayi tana duban Hajiya Mama da take cewa “Yo wannan uban ci da Shatun taki take yi ai dole kiga Haka, ban da likita yace is better ayi mata aiki ai da ta gane kurenta wajen haihuwa yarinya kullum hannu a Kwano.” Basirah da take gefe ta tuntsire da dariya, Shatu ta hurgeta da pillow tana ‘dora kan ta a cinyar Mommah tace “Mommah kin ganta ko? Zata fara zolaya ta.” Mommah ta harari Basirah tace “Allah ya ha’daku zaku fara ko? To ki bari ta haihu sai ku cigaba don yanzu ba ita ka’dai bace.” Kamar ance Hajiya Mama ta ‘daga kanta ta hango Imran yana shigowa ta jikin t.v ‘din dake hasko camerar gidan. Da sauri tace Shatu ta shige ‘dakinta don basa son Imran ya ganta.

Ba’a fi mintuna biyar ba kuwa suka ji knocking ‘dinsa a bakin parlourn. Basirah ce ta bu’de masa ‘kofar, ‘kamshin turarensa tuni ta baza parlourn, jikinsa a sanyaye hannunsa janye da ‘Yar ‘karamar trolley da ba zata gaza ‘daukan kayan da suka fi 2set ba. idanunsa ya sauka cikin na Mommah, ya saki wata ‘kakkarfar ajiyar zuciya, ‘kirjinsa ya samu salama don bai ta’ba zaton zai zo ya risketa da rai ba, ya ‘dauka gawarta zaiyi arba da ita kamar yarda yake ta hasashe a cikin jirgi. Mommah idanunsa a cikin nata, duk da tana fushi dashi tayi farin cikin ganinsa cikin ‘koshin lafiya ta tabbatar yana cikin kwanciyar hankali tunda gashi har ‘yar ‘kiba yayi, ya kuma ‘kara haske akan nasa Na da duk da haskennasa disashshen haske ne, ba mai irin fau ‘dinnan bane.

Hawaye ya fara ‘kokarin kwaranyo masa a idonsa, da sassarfa ya ‘karasa wajen su ya dur’kushe a gabanta cikin wani yanayi ya dam’ki hannayenta yasa fuskarsa a ciki, sai a lokacin ya samu sukunin kwararrar da hawayensa, wanda yake nuni da zallar farin cikinsa Na riskar Mommah cikin ‘koshin lafiya. Hannayenta kawai akan bayansa ba tare da furta komai ba. zuciyarta a cunkushe tana tunano mata girman laififfukan da ya aikata mata musamman sakin Shatu da yafi tsaya mata a rai. Hajiya Mama sa’ke tayi tana kallonsu zuciyarta cike da tausayinsu duka tana addu’ar Allah ubangiji ya daidaita lamarinsu ya kawar da dukkan lamarin da yake lullu’be.
Kamar ‘kiftawar ido suka ga Mommah ta mi’ke a zafafe ta shige ‘daki ta kullo ha’de da murza key, sai sannan kukan yazo mata duk ‘kokarin da tayi Na danneshi. Imran da sauri ya bi bayanta sai dai kafin isarsa ya tarar ta datse da key. Jikinsa a salu’be ya dawo gaban Hajiya Mama ya zauna idanunusa kawai ya ke aikin murzawa. Yana duban Hajiya Maman kafin ya saki wani huci da zallar tururi ya fito daga bakinsa, ya gaishe da Hajiya Maman. Ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace “Ai ta samu sau’ki sosai ma kuwa,kwana uku da suka shige tuni muka cire rai da ita, duk da Allah yace Latakna’du min rahmatillah.” Imran yace “Alhamdulillah,amma Hajiya Mama menene musabbabin ciwon?” “Musabbabin ciwo Imran ya wuceka? Kai da dangin mahaifinka da ka biyewa kuke ‘ko’karin kai mahaifiyarka ‘kasa, saboda baka san ciwon kanka ba, Idan ta mutu wallahi kune kuke da asara ba ruwan danginka, in Banda sakarci ya za’ayi ka saki Shatu kasan ‘yar uwarka ce kuma itace za’bin Ta, amma ka zubawa idonka toka ka saketa ka bamu mamaki wallahi, kuma Alhaji Baba ma yana nan yana jiranka.” Shiru Imran yayi yana jin tsanar Shatu tana sake hauhawa a zuciyarsa, sa’banin da yake turkey da kullum yake kwana da tunaninta har yayi Al’kawarin duk ran da yazo Nigeria zai saka a mayar da aurensu, amma yanzu duk wannan soyayyar da begen ya kau, gani yake duk itace musabbabin sake samun sa’bani tsakaninsa da mahaifiyarsa, ban da haka kafin zuwan ta ‘kalau suke zaune. Ransa a ‘bace ya mi’ke yayi hanyar waje bayan ya amshi key ‘din part ‘din Hisham a wajen Hajiya Mama.

Hajiya Mama kuwa binsa tayi da kallo zuciyarta Na sake girmama ‘kiyayyar da Imran yake yiwa Shatu da ko sunanta baya son a ambata, tabbas al’amarin sai ta tashi tsaye da addu’a don alamar sihiri maigirma a tare dashi.

Mi’kewa tayi ta isa bedroom ‘din Mommah bayan tasa Yaseerah ta kai masa abinci, duk da ta san bai ci zaiyi ba.
bugu ‘daya tayi tace da Mommah “Bu’de, nice nan Addarsu.” Da sauri Mommah ta bu’de Hajiya Mama ta mayar da ‘kofar ta rufe.

A gefen Gado ta zauna, Idanunta akan Mommah da yayi jazur dashi. “Sau nawa zan gaya miki ki daina wannan fushin akan Imran? Addu’a ta kamaceshi don na gano tabbas akwai sihiri a tare dashi.” Murmushi Mommah tayi tace “Mai kika gani Hajiya Mama? Kada ki sawa kanki wannan tunanin, ke fa kike cewa mu daina beleiving da asiri.” Hajiya Mama ta girgiza Kai “Tabbas da asiri a jikin Imran, saboda yau zancen Shatu kawai nayi masa amma kamar na sanar dashi ranar mutuwarsa, ban ta’ba yarda a zuciyata Imran Zai yiwa Shatu wannan ‘kiyayyar da ba gaira ba sabab ba.” Mommah ta saki murmushi” “Hajiya Mama baki san Imran bane, tun a farkon fari ya tsani Shatu shine ma dalilin da yasa na ha’dasu aure, amma ya nuna min ban isa ba saboda yana tunanin ya fi ‘karfin Shatu da tazo daga Daji yana yi mata kallon bata waye ba. don haka ki cirewa zuciyarki wannan tunanin, ni yanzu ko Shatun ma bana son ya ha’du da ita wallahi.” Hajiya Mam cewa tayi “Allah ya kyauta” ba tare da ta amince da maganar Addarsu ba.

———————————
Ran kawu sa’idu a ‘bace yake kallon Alhaji Babba yace “lamarin mutane ya zama abin tsoro, duk jan kunnen da nayi mata sai da aka sake kwantantawa shikkenan ka barni dasu Insha Allah Na san maganinsu.” Alhaji Babba yayi masa sallama suka rabu cikin farin ciki da fahimtar Juna.

——————-
Da safe Imran ya shiga gidan, Hajiya Mama na ganinsa ta fara addu’oi a cikin ranta, Mommah kuwa fuskarta ta ha’de tana godiya ga Allah da baiga Shatu ba. Ha’kuri ya shiga bata ta ta’be baki kafin tace “Bakomai ni mai kayi min? Aure ai a hannunka yake tun da ka riga ka saketa kuma ai shikkenan Allah yasa hakan shi yafi alheri.” Jikinsa a sanyaye ya mi’ke Hajiya Mama tace “Ina zaka? Ba zaka tsaya ka karya ba?” Lumshe idanunsa yayi yace a kawo min garden can zanje…” ya nufi garden ‘din da sassarfa, gaban Mommah ya fa’di sanin Shatu a can take lesson kafin tayi ‘ko’karin hanashi har ya Tura ‘kofar da zata sada shi da Garden ‘din…….. Mommah ta ware ido ita kanta Hajiya Maman bata son had’uwar Shatu da Imran a yanzu sai dai kana taka Allah Na tasa, Zahiran kuma ta Allah ce Gaskiya…..
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

36

Kiran da Alhaji Baba yayi masa ne yasa sh jiyowa, hakan yasa shi fasa shiga garden ‘din. Alhaji Baba ya yafito shi da hannu alamar yazo. Hakan ya saka shi nufar kakannasa.

A parlourn sa ya zaunar dashi, yana dubansa zuciyarsa cike da begen jikannasa. “Ka shigo jiya bamu ha’du ba? Ko da yake ni na hana Hajiya taso ka, Na san baka samu isashsshen barci ba anyi tafiyar da ba shiri, ya iyalinna ka?”
“Suna lafiya” “Masha Allah” nan ya zaunar dashi suka karya, yana ta tambayarsa cigaban da ake samu a business ‘dinsa.

Mommah da Hajiya Mama suka saki ajiyar zuciya a kusan tare, ganin Imran bai shiga ba. Mommah tace “Alhamdulillah, ke basirah maza kije kice ta koma sitroom da karatun nan.” Basira ta mi’ke ta fita isar da sa’ko, ita kanta mamakin yarda taga Shatu da ciki take yi.

——————————

Cikin masifa Kawu Sa’idu ya kalli Hajja, sannan ya dubi Manga “Tunda ya sake ta ba mahalu’kin da ya isa yasa ya dawo da ita, ai ni tun farko ban san da wata manufa kika ha’dashi aure da zainabun ba da ba zan amince ba wallahi, kuma yafiya dole ki yafe masa matu’kar ba kina so nima na janye hannuna a kanki ba, ban ta’ba ganin shashanci da zubar da mutunci ba irin naki, amma an zo ‘karshe tun da gashi iyayenta sun ‘dauketa, to ina dalili yarinya da gatan ta da komai ku saka ta a gaba har ciwon zuciya na neman hallakata, magana ta ta ‘karshe kenan tsakani na dake ki bar Manga da Iyalinsa su huta, kafin ubangiji ya nuna miki Ishara, kuma ya zama dole ki bi ni Abuja ki duba yarinyar nan ki kuma bawa iyayenta ha’kuri ke da marasa kunyar ‘ya’yanki.”
Hawaye ne ya ‘balle mata jin yace sai taje Abuja ta basu ha’kuri, gaskiya abinda ba zata iya ba kenan, a dai sake wata mafitar. “Don Allah kawu ayi ha’kuri ba sai naje ba, na amince ba zan sake shiga hurumin gidan sa ba.” A harzu’ke Kawu Sa’idu yace “Baki isa ba dole kije wallahi kuma ‘kafa ta ‘kafarki, dake da fitsararrun yaranki.” Daga haka ya mi’ke ya fice.

Yana fita Anty Amarya ta sakawa Hajja kuka “Don girman Allah Hajja ki bawa Manga ha’kuri na koma ‘daki na. Hajja hannu bibbiyu kawai ta zuba tagumi ta rasa ma mai yake mata da’di. Wai kamar ita ace zata je ta bada ha’kuri tayi ‘kwafa a fili tace “Ai kuwa Dijah idona idonki Allah ya dawo dake lafiya, ke kuma Zainab ki sha kuruminki komawa ‘dakinki kamar kin koma indai nice uwar da ta haifi Manga. Sai sannan hankalin Zainab ya kwanta, Hameedah kuwa ta cika ta tumbatsa jira kawai take ta fashe.

——————————
Kwanan Imran biyu yayi shirin komawa, Ammar Kuwa Dahda yace ya zauna ba sai yazo ba tunda yaga jikinnata da afuwa.

Ranar da zai tafin da sassafe ya shigo cikin gidan, direct kitchen ya nufa, dai-dai lokacin Shatu tana kitchen ‘din Burger take ‘ko’karin ha’dawa, don tana son ta birge Mommah. Basirah kuma na gefe tana hidimar ha’da Alkubus da miyar taushe. Ji suka yi kawai an turo ‘kofar, da sauri Shatu ta juya ta kuma ja mayafi ta rufe fuskarta da shi. Tuni ‘kamshin turarensa ya baje kitchen wanda hakan yasa bugun ‘kirjin Shatu ya tsananta. Gaisuwar Basirah ya amsa yana bu’de fridge. Har ya juya zai fita sai kuma ya waigo yana Mallon Shatu ba tare da ya san wacece ba ya dai yi mamakin rashin gaisheshi da ba tayi ba. Ta’be baki yana mur’de murfin ruwan ya kai bakinsa, da sauri ya fice.

A parlour yayi wa su Mommah sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Tana saurarar Hajiya Mama da take mi’ka masa takardu “Addu’oi ne na tsarin jiki ka dage da yinsu saboda rayuwar nan ta zama abin tsoro ba’a zama haka. Allah ya tsare ya kiyaye ka gaishe mana da iyalinnaka.” A gaggauce ya amsa mata yana ficewa da sauri don gudun rasa flight.

——————

Tunda ya tafi gaba ‘daya walwalar Shatu ta tafi gaba ‘daya, tunaninsa ya sake bun’kasa a zuciyarta, a le’kensa da tayi tana hango tsananin kyau da ya ‘kara alamar ba abinda yake damunsa sai zallar nutsuwa da kwanciyar hankali. ‘Kamshinsa yana nan ya kama gidan ra’dam tamkar lokacin ya bar gidan. Ita kanta ta amince Soyayyar Imran a jininta yake, idan ban da haka ya za’a yi ta kasa manta shi duk da butulcin da yayi mata, amma ina madadin raguwar lamarin kullum sabunta abin yake musamman yau da taji turarensa gaba ‘daya ta sake tunowa da first Night ‘dinsu, duk da soyayyar tasa bata jin zata sake komawa gidansa ko da ya bu’kaci hakan, gwara ta tsira da mutuncinta bakin da ya furta ‘ki baya ta’ba dawowa ya furta so.

———
Kashegarin ranar su Hajja da Kawu Sa’idu suka zo, Hajiya Mama tayi musu tarba ta mutunci da girmamawa, fuskarta fal da fara’a tasa aka jere musu abinci iri-iri, amma haka suka dubi abincin a wula’kance ba tare da sun ci ba, duk da kajin da suke ta zaginsu. Hajiya Mama tana fita Kawu Sa’idu yasa musu fa’dan da dole suka ‘debi abincin suka fara ci, sai dai suna ta jan addu’oi a zuciyarsu wai kar Asiri ya kama su. Kawu Sa’idu yace “Aikin banza ai shi mai yin abu shi yake tunanin wani ma irin abinsa yake. Ku dai daga ganin gidannan kun san sun fi ‘karfin su tsaya yi muku Asiri shashashai kawai da babu Allah a ranku, wani yayi min abin rashin kyautawa a gidannan yaga yarda zan yaga mutuncinsa, kun samu mutane masu mutunci da karamci ma wallahi idan banda haka da wasu ne ya za’a yi su kalleku da ko ruwan sha balle su ha’da muku wannan daular.” Tsit suka yi baka jin sautin komai sai na cokula sai kuma gashi sun cinye abinci tas ragowar shinkafa kawai suka bari. Kawu Sa’idu yace “Aikin banza kuna so kuna kaiwa kasuwa.”

Bayan gama cin abincinnasu Alhaji Baba da ‘kannensa biyu suka shigo, sannan Hajiya Mama da Mommah suka shigo. Har ‘kasa kuma Mommah ta dur’kusa ta gaida Hajja ba tare da ko canjin fuska ba balle fitsara. Jikin Hajja yayi sanyi a karo na farko ta ji kunyar Mommah ita kanta ta shaida Mommah mai ha’kuri ce, don koda wasa bata ta’ba nuna mata ba’kin hali ba, kullum a cikin yi musu uzuri take. Ba yabo ba fallasa ta shiga amsa gaisuwar tare da tambayarta jikinta. Fa’da sosai Kawu Sa’idu yayi, ya kuma bada ha’kuri tare da cewa insha Allah anyi na farko an yi na ‘karshe.” Ya saka su Hameedah ma da ‘yanuwanta suka bada ha’kuri, haka dole suka bayar ba da son ransu ba.
Sannan ya koma da yi musu nasiha sai dai gaba ‘daya ba jin nasihar suke ba, musamman Hameedah da take gani kamar an zubar mata da ajinta. Alhaji Baba yace “Ni kuma tunda ka gama ina da magana, kayi ha’kuri yaronnan ya mayar da matarsa Zainab alfarma na nema. Kawu Sa’idu yace “Sun ci albarkacinka dattijon arziki na amince masa ya mayar da ita, amma a bisa shara’di ko kallon banza ban yarda ta sake jifan Dijah dashiba balle zagi, don iya shege saboda ta Samu ‘daurin gindin uwar miji.” Alhaji Baba yace “Godiya nake, Allah ya basu zaman lafiya ya ka’de duk fitina.” Ameen suka amsa wasu a fili wasu a zuci. Taro ya watse, wasu sun kar’bi nasiha irinsu Fanna da Falmata wasu kuwa anan suka zubar tare da ‘daura ‘damarar sabon shiri.

A ranar suka juya maiduguri a jirgi. Su Mommah kuwa kashe gari ta bi Dahda suka koma. Wannan karan ma da kuka Shatu ta rabu da Mommah.

——————-
Bayan Wata biyu, lokacin cikin Shatu ya isa haihuwa, a asibiti kuma suka bada shawarar ayi mata c.s duk da dai zata iya haihuwa amma suna gudun faruwar matsala, saboda cikin yayi girma sosai ita kuma ga ‘kan’kantar shekaru.

Ana saura kwana biyu ayi mata aiki Ammar ya samu labari don haka yayi shirin tahowa daga Qatar yafi so ayi a gabansa, ji yake tamkar Shatu shi zata haifawa babyn. Siyayyar da ya jibgo kuwa har da ta banza, kaya ne akwatina kusan biyar duka unisex na haihuwar.

Cikin murna Shatu ta tare shi, da abinci kala-kala tana girmama Ammar sosai tana ganin mutuncinsa musamman ganin yarda yake ‘dawainiya da ita da aljihunsa da jikinsa.

A ranar ma Mommah ta iso tare da Basirah, bayan tayi wa Dahda ‘karyar Shatu ce ba lafiya. Ammar ne ya saka hannu a madadin uban ‘da aka shiga da Shatu theatre….
Shatu sai muce a fito lafiya..

Kuyi hakuri ba yawa yau ciwon kai nake, wallahi.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi da ita?

37

Nimcyluv ubangiji ya baki lafiya, Allah yasa kaffara. Ku saka marubuciyar Zain abeed a addu’a da bakunanku masu albarka.

Alhamdulillah nagode sosai da wa’danda suka kira ni ko text messages domin yi min fatan samun lafiya, nagode ‘kwarai da ba zarku nake taka rawa, Alhamdulillah ala kulli halin, wa astagfirullah min kulli zanbin.

Tsawon lokaci suka ‘dauka a cikin theatre Room ‘din. Kafin lokacin fitowar tasu su Mommah addu’oi kawai suke zubawa domin samun nasara.

Da sauri wata nurse ta iso wajensu, idanunta cikin na Hajiya Mama tace “Alhamdulillah, an yi aiki successfully, an ciro Baby Boy yanzu za’a fito da ita.” Gaba ‘daya wajen suka ha’da bakin fa’din “Masha Allah.” Hajiya Mama ta bu’de jakarta ta ciro ku’din da bata san adadinsu ba ta dam’kawa matar. Ita kuma ta juya da sauri ta koma dama tukwuicin take yiwa.

Juyawarta kenan, suka ga ta dawo da sauri tace “Hajjaju ashe biyu ne, tukwuicina yafi haka duk da yanzu kishiya aka zanka’do miki.” Wani tarin farin ciki ne ya wanzu a zuciyarsu, wannan karan Ammar ne ya zura hannu a aljihunsa ya ciro dalolin Amurka guda uka ya dam’kawa matar. Mommah kuwa burinta taga Shatu domin ta gama biyanta a duniyar nan ta khali’ku.

Bayan mintuna Goma aka fito da yaran, Tubarakallah shine abinda su Mommah suke cewa kawai yayin da su kayi arba da zanka’da-zanka’dan yaran tamkar ‘diyoyin larabawa. Hannu bibbiyu Mommah ta saka ta rungumesu tama manta da wata kunya balle ta tuna Hajiya Mama a wajen, zallar farin ciki ya sata shatatar hawaye cikin wani rin shau’ki take bawa yaran sumbata a kumatukan su, tana jin tsananin ‘kaunarsu na ratsa dukka sassan jikinta, fiye da lokacin da ta haifi Imran da Ammar, tabbas ta yarda da maganar malam bahaushe da yace Abin cikin ‘kwai yafi ‘kwan da’di.

Hajiya Mama kuwa sai kallon Mommah take fuskarta cike da murmushi a zuciyarta tace “Dijah dole ne kiyi farinciki ni kaina da aka haifi Imran nayi fin haka balle ke da aka yiwa biyu lokaci ‘daya, kuma tuwo na maina don kuwa Shatu ‘yar Mommah ce halak malak.

Dai-dai lokacin aka fito da Shatu a wheel bed idanunta a lumshe hawaye yana zirara ta cikin su, hannu ta mi’kawa Mommah, da sauri kuwa Mommah ta mi’kawa Ammar Babies ‘din ta nufi ‘yarta. Da ita aka tura ta har zuwa Amenity1 ‘dakin da zata huta.

Ammar farin ciki ne ya baibaye zuciyarsa, yana ayyana ko yanzu kallon Shatu take kamar ta zama tasa domin dai kuwa yau ta gama idda. Babu shamakin da zai katange shi da furta mata zahirin abinda yake zuciyarsa, da zarar sun isa gida an sallamesu, tunda Mommah ce tayi masa al’kawarin ko ranar suna za’a iya yi musu aure.

Idanunta a lumshe alamar barci yana son ‘daukarta, Mommah ta haska mata fuskokin yaran tana cewa “Shatu na bu’de idonki kiga ‘kurrati ainun. Shatu ta ware idonta tar tana kallonsu tare da girmama hikimar ubangiji ta yarda yaron yayi kama da Imran kwabo da Kwabo, ita kuma jaririyar tayi kama da ita sak kamar tayi kaki ta zubar. Cikin zuciyarta tace tabbas ‘kudirar ubangiji girma gareta ubangiji yayi muku albarka, ko a tunani ban ta’ba tunanin haihuwar biyu ba. Sai ta lumshe ido sai kuwa ga hawaye ya sake zubo mata na tsantsar farinciki da godiya da ni’imar Azza wa Jallah.

Bayan sun nutsu Hajiya Mama ta kalli Mommah “Ai sai a fara sanar da dangi haihuwar.” Mommah ta girgiza kai “Wallahi Hajiya bana son kowa ya san da haihuwar nan…” “Ai kuwa gan-gan kenan zancen banza zancen wofi a na wani dalilin zaki ce ba za’a sanar dasu ba, shikkenan sai a ‘boye ciki haihuwar ma a ‘boye, sai kace an haifi shegu to ba dani za’a yi wannan iya shegen ba. Ki ‘dau waya ki kira mijinki ki fa’da masa, sannan a gayawa duk wanda ya dace.” Cikin takaici Mommah ta shiga bin umarni Hajiya Mama don taga ta hau da yawa.

Dahda ta fara kira ta sanar dashi, kasa’ke yayi da wayar ba tare da ya iya furta komai ba. Ransa ya kai ‘kololuwar ‘baci. Jin yayi shiru yasa Mommah fa’din hello!hello! Mamaki ya kamata jin ya saki ajiyar zuciya alamar yana jinta.

A sanyaye tace “Dahda kaji kuwa mai nace?”
“Naji mana” ya amsa a ginshire
Mommah cikin sanyin jiki tace “Naji ba kace komai ba, ko ba kayi farinciki da abinda nace ba?” “Farin cikin me zanyi? Tunda ni baki mayar dani komai ba a rayuwar Aishatu, babu abinda zance sai Allah ya raya, haihuwa ai ke aka yiwa tunda ke kika san da Cikin…”
Daga haka ya kashe wayar da sauri, ran sa yana matu’kar suya duk da yayi farinciki da haihuwar amma yayi mamakin dalilin da yasa Dijah ta ‘boye masa samuwar Cikin.

Hankalin Mommah ba ‘karamin tashi yayi ba, hawaye ya fara tsere a fuskarta. Cikin tashin hankali Hajiya Mama tace “Lafiya? Ko bai yarda da ‘ya’yan na Imran bane?”

Mommah Ta ‘daga kai “Hajiya Mama, ai gwara yace bai yarda ba, akan fushin da yayi yanzu, haushi yaji bai san da cikin ba sai haihuwar yaji…..”

“Au kina nufin shima ‘boye masa cikin kika yi? Inna lillahi wa inna ilaihirraji’una Addarsu wani irin shirme kika aikata?” Kuka ta fashe dashi “Hajiya Mama idona ne ya rufe wallahi sai yanzu na gano kuskure na na san fushin Manga ba abune mai kyau ba balle naga ya hau da yawa yanzu ya zanyi?” Hajiya Mama ta ja tsaki “Ni yanzu mai zan ce miki? Sai kiyi maza ki kira Hajja ki fa’da mata haihuwar kafin ki ‘karawa kanki wani laifin, na rasa irinki Addarsu kina girma amma tunaninki baya girma.”

Mommah Ta ‘dau waya ta fara kiran Hajja, ta da’de tana kira kafin Ta ‘daga.
Kwmar bata so haka ta dinga amsa gaisuwar Mommah, zuwa lokacin da Mommahn tace “Dama kira nayi na sanar miki Shatu ta sauka.” Da rawar murya Hajja tace “Shatu kuma wata ce Shatun?”
Ran Mommah a ‘bace tace “Matar Imran nake nufi.” Hajja ta ta’be baki kafin tace “Au har kun sake mata wani aure kenan, bayan rabuewarta da Imran? To Allah ya raya, meye nawa a ciki? Da
Baki wahalar da kanki wajen gaya min ba.”
Daga haka ta kashe wayarta ta bar Mommah da waya a hannu cikin tsananin ‘kunar zuciya.

Hajiya Mama ta kalleta ta ta’be baki.. “Tsun-Tsun da ya ja ruwa dai shi ruwa kan doka ita kuma me tace miki?”
Mommah tana hawaye ta sanar mata. Hajiya Mama tsaki tayi kafin tace “Ai ba kuka za kiyi ba sai ki kirata ni nayi mata bayani, cikin Imran ne aka haife, idan kuma sunce basu yarda ba sai Na ‘kyalesu suje da halinsu. Kai ni wannan masifa ta dangin mijinki Addarsu ta fara isa ta wallahi.”

Hannu na rawa Mommah ta sake kiran Hajja. Wannan karan a zafafe Hajja Ta ‘dauka. “Wai Dijah lafiya? Kin sanar dani haihuwa nace Allah ya raya to meye Na ‘kara kira na?”

“Ba Ita bace, uwarta ce kuma kira nayi na sanar miki haihuwa dai ta jikan ki Imran ce an haifa masa ‘yan biyu sai ki sanar da Dangi.” Daga haka ta kashe wayar ranta yana hassala da ‘bacin rai da ba’kin cikin surikar Mommah, ta ayyana idan bata fito musu a mutum ba ba zasu barsu su sha’ki iskar ‘yanci ba.

Hajja kuwa gabanta ne ya shiga dukan Tara-tara tana sake jin amon sautin uwar Dijah da take sanar da ita haihuwar Imran aka yi mata. Bata yi murna sam da samuwar ‘ya’yan nan ta tsatson Shatu ba, ina ma ta jikin Shaheedha suka fito da ba mamaki rabin burinsu ya cika, yanzu kuwa ta sani Dijah aka haifawa su dole dai wannan karan ma Dijah ce ke da riba. Wa zaga gayawa wannan abin takaicin su raba ba’kin cikin tare? Hameedah ta fara kira kafin ta kira Zainab uwar Shaheeda. Gaba ‘dayansu babu wanda bai girgiza da lamarin ba don kuka kawai suka Saka zuciyarsu a hassale, burikan rashin alheri kuwa sun ci alwashin tabbatar dasu akan ‘yan biyun Shatu.

Hajiya Mama sai da zuciyarta ta huta da ‘bacin ran sannan ta danna kiran Imran, dai-dai lokacin yana wanka, sai Shaheedah ce tayi saurin ‘dauka ba tare da tayi maganaba taji Hajiya Mama tace “Albishirinka Imrana! Matar ‘ki ta haifa maka ‘yan biyu mace da namiji.” Gaban Shaheedah yayi wani mummunan fa’duwa, tana ji Hajiya Mama tana fa’din hello! Hello! Shaheedah tayi saurin datse kiran.

Kafin wani kiran ya shigo Shaheedah tayi saurin rubuta text kamar haka.

Naji da’di da haihuwar da tayi Allah ya raya su, sai dai ba zan ‘boye muku ba nayi ba’kin ciki da suka fito daga jikin Shatu har yau ina kan baka na. Yara idan na samu lokaci zan zo na gansu idan kuma ban samu ba ku saka musu duk sunan da kuka ga dama fatan alheri.” Daga d’anku Imran.

Da sauri ta danna send ta kuma yi deleting, tare da bin contacts tayi blocking duk wata number da ta danganci family ba ta so ko ka’dan ya samu labarin haihuwar nan. Kafin ta gama ta ji’ke da gumi sharkaf. Hawaye ya fara bin idanunta, sautin amon muryar Hajiya Mama kuwa bai bar kunnuwanta sun zauna sa’kat ba.

Hajiya Mama ta duba wayar taga dai tabbas yayi receiving, to me zai saka shi yin shiru, “Bai yi farin ciki da haihuwar ba ko? Na san za’a rina.” Direct Hajiya Mama ta kalli Mommah tabbas ta samo mata amsar tambayar ta Imran kam baiyi farin ciki da labarin ba, asalima ba mamaki tu’kukin zuciya ne ya saka shi yin tsit da bakinsa.

Bata sake ‘ko’karin kiransa ba taji message ya shigo wayar, da sauri ta kai idanunta kan message ‘din kafin kace kwabo Hajiya Mama ta fara zurarar da hawaye ta kwarmin idanunta, lamarin da ya girgiza zuciyar Mommah ta tabbatar ba alheri a cikin sa’kon da ya shigo cikin wayar yanzu. Da sauri ta sa hannu ta ‘dau wayar. Tsaf ta karance abinda ke ciki, zuciyarta ta cika da ‘bacin rai kafin ta saki murmushi “Hajiya Mama ki kwantar da hankalinki Imran zai yi abinda yafi wannan amma bakomai kansa ya cuta, yara kuma Allah ya shirya su ya bawa uwarsu lafiya shayar dasu, Insha Allah rana ita yau za’a ‘daura aurenta da Ammar shi zai maye musu gurbin uba na tabbata Ammar zai kula min dasu ko bayan raina fiye da Imran. Ta shanye hawayen tas ba tare da ta bari sun zuba ba,
Don tayi al’kawari ta daina zubar da hawayenta akan Imran, ta lura ba abinda yafi so irin wanzuwar ‘bacin ranta. Murtar Hajiya Mama a sanyaye tace “Allah ya shiryeshi, hukuncin da kika yi kuma shine abinda ya dace ubangiji ya bawa Ammar wuyan ‘dauka. Farin ciki ta cika zuciyar Ammar yaji tamkr ya tashi ya buga tsalle.

Saduwar alheri love you all. Ana tare.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi Da Ita?

38

Tsawon awoyi takwas Shatu Ta ‘dauka a kwance, kafin su shigo don ‘daga ta ayi mata wanka.

Mommah da kanta tayi mata wankar bayan nurse ‘din ta nuna mata yarda zata yi, sosai ta gasa mata jikinta da towel. Shatu ta fito da ‘kwarinta, duk da tana jin iska kamar ta ‘dauketa, ba mamaki saboda an cire abin da yake cikin.

Kafin a mayar mata da drip ‘din, Doctor ta bu’kaci a bata yaran su ‘dan zu’ki Maman saboda hakan yana da amfani a wajen jariri. Kunya ce gaba ‘daya ta dabaibaye Shatu tana jin tamkar ‘kasa ta dare ta shiga.
Mursisi tayi, tamkar bata fahimci abinda Momma ta ke gaya mata ba. sai da Mommah ta fahimci kunya take ji, sannan ta shiga lalla’bata “Haba Shatu, daure ki ba su kowa daga haka ya fara kuma kina ji aka ce hakan yana da matu’kar amfani ga lafiyar su, ko ba kya son su zamo masu kuzari?” Hawaye ne ya fara ambaliya a idanun Shatu, a zuciyarta ta raya yau fa ake yinta! Yanzu ta ya zata iya shayar da su? Wallahi kunya ba zata barta ba. musamman ga Ammar yana zaune ya tasa baby girl ‘din da kallo, ji yake tamkar ya lasheta ko don ganin tana kama da Shatu ne. Mommah ta kalli sashen da take kallo, tace “Au Ammar dama kana nan maza to ka bamu waje.” Yana murmushi ya fice a zuciyarsa yace “Kwana nawa ne zasu zama mallakina a daina yi min rowarsu.”
Yana fita Momma ta zura hannu da kanta ta zaro Maman ta ri’ko Baby ta manna maman a Bakinsa, da sauri Shatu ta runtse ido na tsananin jin kunya. Duk da babu ruwa a ciki sosai haka ya dinga zu’ka tamkar zai cire kan, da alama nan gaba Good sucker za’a yi.

Hajiya Mama dariya tayi ganin yarda Shatu take ta kawar da kai idanunta kuwa a rufe ta kasa bu’de su. “Addarsu da kin bar masa haka, kada ya kwankwa’de ita kuma ya barta, duk da ni zan fi son haka kada ta ture min gwamnati wajen Alhajina.”
Mommah tana murmushi ta mi’kawa Hajiya Mama shi kafin tace “Tun yaushe kuma kina ganin yarinya Balarabiya. Bari Alhajin ya zo ki ji mai zai ce.” Tana ri’ke da ‘yar ta sake ciro ‘daya maman ta manna mata a baki. Wani karan Kuka Shatu ta saka da ita kanta bata san dalilin kukan ba sai dai na fassara shi a na farin ciki.

Sun dai sha abinda suka sha amma ba don sun ‘koshi ba, hakan yasa da Ammar ya shigo Momma tace yaje ya tambayo Doctor ko za’a iya basu madara? Take Doctorn ya rubuta musu madarar da za’a iya basu mai kyau ta S.M.A ya siyo musu carton guda a pharmacy ‘din asibitin, sai da aka dama musu suka sha sannan suka samu barci mai nauyi ya ‘daukesu. Shatu kuwa tsananin yunwa take jin musamman jin cikinta yayi fa yau.

Sai dare Dahda ya koma gida. Da azama Zainab ta tare shi cikin kwalliya ta gani a yaba. Ga ‘kamshin humra da ta sha surkulle kala-kala da ta ba’de jikinta da ita. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar da take masa, da
Azama kuma ta rungumeshi tsaf a ‘ko’karinta na son ya sha’ki sihirtacciyar humrar.

Abin mamaki Dahda janyeta yayi gefe, tabbacin sa’kon nata bai isa in da take so yaje ba. Fuskarsa a ha’de tamau ya shige ‘daki.

Zainab ji tayi kamar ta ‘dora hannu a kai tayi ta zunduma ihu, ta rasa wani irin mutum ne Dahda da duk ‘karfin asiri baya cinsa, duk da ta sani abin a bayyane yake Dahda baya wasa da ibada musamman sallolin dare da azimin litinin da alhamis, sallahr walaha da azkar na safe da yamma duk basa wuce shi. Sannan duk sanda zai yi barci sai ya karanta suratul mulk da suratul kafirun bayan azkar ‘din barci. Amma duk ta jingine hakan ta ‘dora laifin akan Mommah Dijah baiwar Allah gani take sihirin da take masa ne yafi nata ‘karfi.
Hawayen idonta ta ‘dauke tana tunanin Shikkenan ita kuma ta tabbata mara nasara a rayuwa, Dijah ce kullum take rinjaye a kanta. Abin ba’kin ciki haihuwar da Shatu tayi yau na ‘yan biyu, ita tata ‘yar bata jin ko ‘batan wata ta ta’ba yi.

Kamar an zungureta ta zaro wayarta ta shiga dannan kiran Shaheedah, ji take idan bata sauke duk wani takaicin ta akan ta ba yau ba zata samu salama a zuciyarta ba.

Shaheedah da ta ji kiran daga sama, a zabure Ta ‘dau wayar gabanta yana sake duka, don tun da aka sanar da ita haihuwar ta rasa sukunin zuciya. Ganin Antynta ce ta ‘daga a sanyaye. Kawai kuka ta saka mata. Zainab tayi tsaki “Ke da halla saurara min ki ji tambayar da zan miki, kina da ciki ko baki da shi?” A shagwa’be tace “Haba Anty Allah ya tsareni da haihuwa yanzu, ban shirya kwararra’bewa ba.” Wani zagi Zainab ta ‘kunduma mata kafin tace “Fahimtar dani ban gane mai kike nufi ba? Zuwa kika yi kika yi tsarin iyali ko me?” “Ni wallahi kwanaki ma na samu cikin ni nace masa bana so muka je muka cire shi.” Zainab ta zabga salati “Shikkenan Shaheedah kin kashe ni amma kuwa ke dai nayi jakar yarinya da babu tunani ko ka’dan a zuciyarki, don ubanki to ga Shatu nan ta haifa masa twins, kin ga ko yanzu ta ci gida, ke sai ki zauna kiyi ta adana jikinki shashashar banza.”
Cikin takaici ta ajiye wayar tana sake tsaki da la’antar shashashancin Shaheedah.

Ita kuwa Shaheedah ta’be baki Tayi, cikin ranta ta ce “To ni ina ruwa na ta haifi duniya ma, ko da na ‘boyewa Imran haihuwar ba don komai bane sai don kada yace lallai sai ya tafi Nigeria yanzu, idan ban da haka ni bana ba’kin cikin ta haifi ‘dari ma.

Zainab kuwa da takaicin ya gama cinta, wanka Ta ‘karawa she’kawa ta sake ambula sihirtacciyar humra, tayi shigarta cikin wata shara-sharan rigar barci ita a dole sai ta ja hankalin Dahda a wannan Daren. Ta fice bayan ta cilla chewingum a bakinta.

Taci sa’a kuwa ta samu ‘kofar a bu’de, cikin farin ciki ta danna kai bedroom muryarta cike da kwainane tayi Sallama. Kamar wata zararriya ta saki zani da hijabin da ta shigo dasu tana jifan Manga da wani shu’umin murmushi, idanununta cikin nasa. Shi kuwa sak yayi yana yi mata kallon mamaki da tunanin ko ta fara samun motsuwar kwanya. Farinciki ya cika zuciyarta a tunaninta kallon tsananin bu’kata yake jifanta da shi. Ganin bai ta’ba tsayawa yayi mata wannan kallon.
Takaici ya gume Dahda, da sauri ya mi’ke idanunta zube Cikin shamulallen ‘kirjinta da kyautatuwa yayi a ‘boyesu saboda rashin kyan ganinsu, ba a bayyana ba. ko Mommah da nata suke cas gwanin sha’awa bata tayyara su haka a fili.

Tsaki ya zabga ganin tana tunkaro shi yayi saurin dakatar da ita da hannunsa fuska a ha’de yace “Saurara am not in the mood, kuma Abuja zan tafi da sassafe na san ai kina da labarin kinyi Jikoki ko?” Ranta ya ‘baci da salon wula’kancinsa, tunda aka yi aurensu bai ta’ba bu’katar ta ba kullum ita take kawo kanta idan bu’katar hakan ta ciyota, murya a sha’ke tace “Tabbas naji labari, amma ina tantama idan jikokin namu ne, kwananta uku da tarewa fa ya saketa, yaushe har ya sadu da ita ta samu ciki…..” “Ke! Dakata bana son sakarcin banza kada ki sake ki sheganta min jikoki, ko kwana ‘daya tayi ya saketa,
Hakan ba yana nufin ba zai kasa tarawa da ita ba, kuma ‘ya’ya na sane don haka kada na sake jin wannan banzar maganar mara kan gado.” Daga haka ya ja duvet ya rufe jikinsa idanunsa a lumshe yace “Idan kin tashi fita pls off the light asuba ta gari.” Tsananin takaici ne ya rufe Zainab bata san sanda ta kai kanta bakin ‘kofa tana takaicin asarar ku’din humra da tayi. (Haka lamarin yake wanda bai ji bari ba zai ji hoho!)

—————

Takwas na safe a cikin asibitin tayi wa Dahda, tuni y kira Ammar ya tambayi ‘dakin da suke, don fushi yake da Mommah ba zai iya kiranta ba, duk da tun jiya yake ganin kiran ta amma yayi burus ya ‘ki ‘Dauka, so yake ya nuna mata abin da tayi ‘din zahiran bai ji da’di ba kuma bata kyauta ba.

Bayan Knocking na minti ‘daya ya tura ‘kofar bakinsa ‘dauke da sallama ya shiga. Momma cikin farinciki ta amsa masa, ya ‘dauke kai kamar bai ganta ba direct ‘bangaren da Hajiya Mama ya isa har ‘kasa ya dur’kusa ya gaisheta. Cikin kunyar surukuta take amsawa tare da yi masa murnar haihuwar da aka yi masa. Ya amsa shima ‘din idanunsa a ‘kasa, yana wasa da hannunsa, ya dubi Shatu da take ‘ko’karin mi’kewa zaune yace “A’a Shatu yi kwanciyarki ke da baki da lafiya.” A kwancen ta saki murmushin kunya ta gaida shi, ya amsa fuskarsa ‘dauke da tausayinta yarinya ‘karama ‘yar shekara sha shidda da haihuwar ‘yan biyu, gani yake kamar lamarin yayi mata girma. A hankali yace “Ya jikin naki?” “Da sau’ki Dahda” ta fa’da murya a sanyaye. Yace Masha Allah” yana kar’bar baby boy ‘din da Mommah take mi’ka masa tana gaisheshi. Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Mamaki ya kama shi ganin yaron a hannunsa yana tuno sanda aka haifi Imran haka yake kwabo da kwabo kamar yayi kaki. “Masha Allah ubangiji ya raya ka. Amma ba kai ya kamata na fara ‘dauka ba amaryata ya kamata na fara ‘dauka.” Ya fa’da yana ajiye shi a makwancinsa, ya ‘dauki Baby Girl ‘din yana bin Hajiya Mama da kallo da ta kama Shatu “Mi’ke maza muje ki tattaka, sun ce ki dinga tattakawa kada wajen yayi tsami.” Daga haka ta kama ta tana takawa a hankali suka fita. Dahda yayi murmushi don ya san hakan wata dabara ce ta dattijan mutane masu nagarta irin dai surukarsa Hajiya Mama. Suna fita Mommah ta kama shi suka zauna, kanta ta ‘dora a kafa’darsa suna kallon babies ‘din tare. Muryarta ta kwantar sosai kafin tace “Yalla’bai am very sorry please naga fushi kake dani sosai, Don Allah ka yafe min, wallahi jiya ko kyakykyawan barci ban yi ba tunda nayi ta kiran wayarka ka’ki ‘dagawa hankalina ya tashi please ka yafe min!” Cikin sauyin muryar da ta san tana narkar da zuciyarsa ta fa’da, tuni kuwa ya lumshe idonsa cikin sake godiya ga rabbi da ya azurta shi da mata ta gari mai amsa laifinta, ba kuma ta girman kai wajen bashi ha’kuri. Cikin wasa ya shafa kumatunta “Na yafe miki Deejah na, da kam nayi fushi sosai tunanina ba ki mayar dani wata tsiya ba, amma yanzu da naga zanka’de’diyar amarya ta duk wani ‘bacin rai ya tafi. An gayawa Imran ni na kira wayarsa bana samun sa I don’t know why?” Mommah wani murmushin takaici tayi kafin tace na gaya masa ga kuma amsar da ya bayar.” Ta mi’ka masa wayar bayan ta bu’de text ‘din da Imran ‘din ya turo. Dahda cikin ‘bacin rai ya ke mi’ka mata wayar cikin fushi yace Allah ya kyauta amma kuwa zai sha mamaki na a lokacin da yazo zaiyi iko da ‘ya’yan nan.” Mommah ta kama hannunsa tana matsawa a hankali tace “Ai ni na riga na yanke hukunci, hukuncin da na tabbata sai ya kusa buga zuciyarsa daga Shatu har ‘ya’yan na mallakawa Ammar rana ita yau za’a ‘daura musu aure……”
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

39

‘Kuri dahda yayi mata ido cike da mamakin furucinta fuskarsa a ‘daure yace “Allah ya sanya alheri.” Ya dire mata yaran a gefe yayi hanyar fita. Da sauri ta sha gabansa ta ri’ke duka hannayensa biyu idanunta cikin nasa race “Dahda Why? Me yasa na hango tamkar ba kayi farin ciki da abinda na yanke ba?” Matsar da fuskarsa yayi gefe, ya ‘ki cewa komai sai jan numfashi yake, tabbas ko a mafarki bai yi zaton Dijansa zata riki’de ta koma haka ba. Zartar da hukunci a duk lokacin da taga dama sa’banin da da sai ta nemi yardarsa Kafin aiwatar da komai. “Please yalla’bai say something mana bana jin da’din wannan fuskar da kake arowa ka sawa kanka.” “Kamar yarda bana jin da’din wannan Dijahn mai yanke hukunci bisa son zuciyarta ba tare da tunani ko tsinkaye ba.” Ya furta fuskarsa na sake tamkewa. Gaba ‘daya ta ha’de hannunta ta dun’kule kafin tace “Am sorry ba nufina zartar da hukunci ba, da ma yanzun ma shawararka na nema kuma duk abinda kace dashi za’a yi aiki, don haka please zauna, ka kwantar da hankalinka ina nan a Dijanka ta da mai bin umarninka cikin son rai ko akasin haka.” Ya zauna ‘din kamar yarda ta bu’kata, sai dai bai saki fuskar ba yace “Me yasa tunaninki ya baki wannan abin da zaki ha’da ya dace? Ban hana Ammar auren Shatu ba amma not now it’s too early ki sake aurar da Aysha, Na zata ko wani kika ga zai aurar da ita a yanzu sai inda ‘kardinki ya ‘kare wajen ganin kin hana shi sai gashi da kanki kike son aurar da ita sati guda kacal da haihuwa tamkar kina neman kai da ita. Bance lallai sai kin mayarwa da Imran ita ba, ko ka’dan bai cancanta da Shatu ba tunda baya sonta kada a koma ‘yar gidan jiya, Amman ‘din ya dace da ita amma shima ba yanzu ba sai ta goge ta yi karatu ta yarda zata iya fafatawa da kowace matsala a rayuwar aure, ta kuma solver ta ba tare da ta tunkari wani da zancen ba. Da C.s a jikinta sati guda ko gama farfa’dowa ba tayi ba taji za’a yi mata aure, ai sai ki jefa zargi a zuciyarta, ta zata kin fi son farin cikin ‘ya’yanki fiye da nata marainiya. Don haka ki sake tunani.”

Mommah tayi shiru tana gasgata zantuttukan Dahda a zuciyarta, tabbas zancensa dutse zata iya kam jefa tunani a zuciyar Shatu Allah ya sota Dahda ya ankarar da ita kuskuren da taso tafkawa. Da sauri ta dinga yi masa godiya,
Dahda murmushi yayi kawai ya ja hancinta “Sarauniyar ‘yan gaggawa, ki ri’ke a kanki duk mai gaggawa yana cikin aikin dana sani kullu yaumin, kina girma tunaninki na yara. Bari in yi sauri in tafi kada Hajiya Mama taga rashin hankali na na san saboda ni ta fita.” Mommah murmushi kawai tayi tana masa rakiya zuwa ba’kin ‘kofa.

Koda Hajiya Mama ta Shigo, Mommah tayi mata bayani akan maganar da suka yi da Dahda. Hajiya Mama murmushi tayi kafin tace “Nagode Allah da ya fahimtar dake kika gane, Allah ya nuna mana lokacin, ya ha’da kawunansu” Mommah ta amsa da ameen. Yayin da Shatu ta lumshe ido, zuciyarta na dakan uku-uku tunani take yi a zuciyarta, shin da gaske ne zancen auren ta ake yi da Ammar, hawaye ne yake shirin fito mata zuciyarta cike da fargaba tace wannan fa shine ana wata ga wata, tabbas ba za ta iya yiwa ammar butulci ba, mutumin da ya tsaya mata tsayin daka yake nuna mata ‘kauna ta fisabilillah. Idan ban da haka sam bata da burin sake aure anan kusa ta fiso ta zurfafa iliminta, bata sa a ranta ko nan da shekaru goma zata sake aure ba, da so samu ne da sai ta rufa shekaru talatin cif, amma kana taka Allah na tasa ga yarda lamarin ubangiji ya juya, ba zata iya bijerewa muradin Momma ba na aure Ammar.

——————————-
Kwanan su hu’du aka sallamesu, cike da ‘koshin lafiya yara sai ‘kara kyau sukeyi kamar ka suresu ka sace. Kaf dangin Imran babu wanda yayi waya yayi barka, balle Allah ya raya, abinda ya hassala zuciyar Mommah, musamman Imran ‘din da bai sake kiran ta a waya ba, hakan yass cikin fushi tayi blocking ‘dinsa a wayarta, da wayoyoyin su Hajiya Mama.

A ranar kuma su Nahna da Hafsa jirginsu ya dirga Nigeria sun zo hutu. Zuciyarsu fal da farin cikin ‘karuwar da suka samu. Har rige-rigen shiga gidan suke. Suka ‘dauki yaran suna sakin Murmushi, su ‘dinma bayan sun ci abinci suka tambayeta Imran ya sani? Take Mimmah ta basu amsa ta kuma sanar dasu cin mutuncin da ya turo, “Don haka ina ro’kon ku kuma kuyi blocking ‘dinsa in dai na isa daku. Cikin matu’kar jinjina girman lamarin suka dinga jajantawa da fa’din bai kyauta ba. A take kuma suka cikawa Mommah burinta na blocking ‘dinsa.

Ammar ya fahimci Dahda bayan yayi masa bayani, ya amince tabbas Shatu yanzu tana bu’katar nutsuwa, da kula da yaranta sannnan da gamsashshen ilimi, hakan yasa dole ya fara shirin kokawarsa Qatar, yanda yake kasuwancinsa. Bayan ya bu’dewa Shatu account, ya samar mata makarantar da zata zana waec

Ranar suna da kansa ya ro’ki Dahda da Alhaji Baba akan cewa a saka sunan iyayen Shatu. Maryama da Mujittaba haka kuwa aka yi, har ila yau da kansa yayi musu inkiya da Ikram da Akram.

——————
A daren ranar da zai tafi ya shiga bedroom ‘din Shatu don suyi sallama ya kuma fallasa mata sirrin zuciyarsa.

Yaci sa’a kuwa Ba kowa sai ita ka’dai Ikram da Akaram suna wajen
Mommah dama shan Nono ne yake ha’da ta dasu saboda matu’kar kunyar su take ji.

Kasancewar sanyi ake bedroom ‘din ya ‘dau ‘dumin heater sosai, Shatu na zaune ta sha wanka sai zabga ‘kamshi take. Kallo take a t.v taji sallamarsa da sha’kar dadda’dan turarensa na companyn lulu. Yayi dressing mai matu’kar burgewa, shi dama ya fi saka ‘kananan kaya sa’banin Imran da ya fi son African Attire. Idanunsa a cikin nata ya isa side bed drawer ya zauna. Gaban Shatu ne ya dinga bugawa ras-ras wanda da mutum zai zuba ido zai hango yarda yake ‘dagawa. Tsoro take ji sosai bata son ya furta abinda yake ransa, don ba zata iya musa masa zata ji matu’kar kunya.

Yana murmushi yake amsa gaisuwarta, tana yi tana wasa da yatsun hannnunta, idanunta a ‘kasa. Cikin wata irin murya yace “Shatun Mommah ya jikin?” “Da sau’ki” ta furta bakinta ne kawai ya motsa ban da haka da ba zai ji muryarta Ba.

Ya ja fasali kafin yace “kin san abinda ya kawo ni?” Tayi saurin girgiza kai bugun zuciyarta na ‘karuwa. “ yauwa ina son ki gaya min gaskiya Idan kin amince to Idan ma baki amince ba duk ina son ji, kin yarda?” Da sauri ta ‘daga kai, cikin zullumi da abinda zai fito daga bakinsa. “Shatu so nake na maye gurnin Yaya na idan kin amince, duk da dai ba yanzu za’ayi ba, amma dai hausawa na cewa a bari ya huce shi yake kawo rabon wani, zan tafi Qatar yau jirgin dare zan bi, mai kika ce kin Amince?” Da sauri ta ‘daga kai bayan ta runtse idanunta tana ji zuciyarta na wani irin bugu. Hawaye yana son zubo mata tayi saurin mayar dasu. Ya zama dole duk soyayyar da take yiwa Imran ta mayar dashi akan Ammar ko don ta saka halacci da halacci. Murmushi ya saki a hankali yace “Alhamdulillah nagode sosai, yau kuma na san zanyi kwanan farin cikin samun amsarki, buri na ya cika.” Ya zaro waya a aljihunsa sabuwa ‘kal ‘kirar Iphone 12 ya fara nuna mata yarda za tayi amfani da ita. Sannan ya ciro atm card ya bata “Na saka miki ku’di a ciki ina yi miki addu’ar samun nasara a karatunki and I really love you.” Da sauri ta rufe idanunta tana sake jaddada masa kalaman godiya.

Tana gani ya fice suna waving juna, ji yake tamkar ya dawo ya rungumeta. Yana tunanin yarda zai jure tsawon lokaci bai ganta ba.

———After One year( Bayan shekara ‘daya…….)

Cikin shekarar al’amura da dama sun faru wasu masu da’di wasu akasin haka.
Cikin masu da’din har da fara karatun Shatu a jami’a, da gogewarta sosai ta zama ‘yar gayu ta bugawa a jarida, duk inda ta wuce dole idanuwa su bi kanta. Fatarta ta murje sosai kamar larabawan Habasha ga diri cikakken hips da tsukakken ciki, uwa uba cikowar mamanta da suke cas dasu a cikin Riga. Hatta da idanunsa sun ‘kara haske tamkar madara.

Har wannan lokacin Imran bai zo ba, saboda al’amura sun caku’de masa, yana yawan kiran Wayoyinsu baya samunsu. Sai dai ya kira maigadi ya ce ya kaiwa Mommah. Sosai take receiving sai dai ko sau ‘daya bai ta’ba tambayar ‘ya’yansa da bai san da su ba. Haka nan ita ma bata ta’ba cewa mai yasa bai tambayesu ba. Addu’a ce dai bata fasa yin ta ba.

Sosai tunanin Shatu ya bun’kasa a zuciyarsa, wata irin soyayyarta ce mai zafi take huda dukka sassan jikinsa, burinsa ya gan ta, sai dai yana jin kunyar tunkarar Mommah da zancen, ya san abin da kunya. Don haka yake dauriyar shanye abin a cikin ransa. Yana niyyar ya samu hutu yaje yayi ya’ki a bashi matarsa.

Tuni asirin ya fara barin jikin sa an kai tajallin da yake zama ya dinga tuna moment ‘dinsu da Shatu.
Wani al’amari da Ba zai iya mantawa da shi ba. Zuciyarsa tana jin zafin sakin da yayi mata, ashe zai zo yayi da na sani, ashe da wannan halin da yake ciki har gwara ace ya zauna da ita yaji kunyar abokannasa, da duk wanda ma zai masa dariya.

——————-

Gabatowar bikin su Hafsa da Nahna ne ya sa Ammar dawowa Nigeria, don ya ro’ki alfarmar a ha’da da na shi da na Shatu.

Ranar da ya iso ya samu Mommah da maganar, tayi na’am da maganar sai dai tana tsoron zartar da hukunci kai tsaye tace ya bari zata samu Dahda da umarninsa zata yi aiki.

Da daddare kuwa ta Samu Dahda da zancen, ya dubi kyawawan jikokinsa da suke gefensa suna wasa tamkar ba ‘yan shekara ‘daya Ba, sun yi girma na ban mamaki kamar Akram ta sake bayyana sosai da mahaifinsa, haka nan macen da Shatu take kama sak da sak. Dudubniyarsu suke akan kakannasu da ‘ko’karin son ‘kwace alawar da yake ba su. Tunani ya shiga yi sosai kusan duk burin Shatu yanzu ya cika yarannan kuma dama bata saba dasu ba Mommah ce take hidima da su, ko anyi auren kuma Ba bata su za’ayi ba. Ga shi ta fara karatunta, tunda bikin su Hafsan sai nan da wata biyu zai iya amincewa ayi. Musamman da na Hisham za’a ha’da, shi yin wancan da yake ta dakon dawowarsa bai dawo ba balle ayi tunanin kome. Don haka direct yace “Shikkenan yayi shirye-shiryennasa ayi bikin dashi amma anan zai barta sai ta gama school.”
Farin ciki ya cika zuciyar Mommah burinta a karo na biyu zai cika. Da murna ta fita ta sanar da Ammar amincewar Dahdan.

Ammar yayi murna da farin cikin da har ba zan iya fasalta muku shi Ba. Yayi sujudusshukur ha’de da sake godiya ga Mommah sannan da sauri ya nufi ‘dakin Shatu.

—————————
Jirgin ‘karfe 8:00 na dare ne ya sauke su Hisham a airport. Ya kira wayar Imran ya sanar masa ya zo ya ‘dauke shi.

Farin ciki ya cika zuciyar Imran na ganin Hisham ya san ba mamaki ‘karshen matsalolinsa sun zo.

Tun a hanya Hisham yake son tambayar sa ko ya san da haihuwar yaransa amma ya kasa zuwa ya gansu tsawon shekara guda? Sai dai yaja bakinsa yayi shiru tunda Mommah ta garga’desu da yi masa zancen. Sai dai ya kalleshi yayi masa magana ta hanyar lislama “Ni kuwa Imran mai ya hanaka zuwa gida tsawon shekara da wani abin?” Imran jim yayi kafin yace “Ina son zuwa amma dai akwai dalilin da yasa ban je ‘din ba.” Hisham yayi tsaki “Wani dalili ne zai hanaka zuwa ganin iyayenka? Amma shikkenan ka san da cewa saura 2 months bikin mu da su Hafsa?” Da sauri Imran yace “Kai masha Allah, a kace zuwa Nigeria ya kama ni, ni I don’t know why? Duk wanda na kira daga family baya shiga, ko kaima ka san sai a dubai na Sameka? Wa ka samo mana?” Hisham cikin murmushi yace masa fine girl idan kaje zaka ganta.”

Suna isa gida suka tarar da Shaheedah zaune ta sake ramewa kamar mai cutar ‘kanjamau, don tsananin rama, ‘kirjinnan ya shafe kamar na tsofaffi. Cikin wani irin kallo Hisham yace “Lafiya Shaheedah me ya sameki haka?” Tsaki tayi ta ma ‘dauke kai kamar ba da ita yake ba. Imran yana dariya yace “Kai ma dai ka fa’da ance family planning ‘din da tayi ne ya sata wannan uwar ramar, kuma ta cire fa amma har yanzu bata ciko ba ji don Allah ni kaina bana son ko kallonta wallahi saboda ramar tayi yawa.” Cikin masifa Shaheedah ta kalleshi “Kaji da munafurcinka ina ce kai da kan ka kace baka son ‘kiba amma yanzu da kinibibi kace wani wai baka son kallona saboda rama.” Cikin bala’i shima ya kalleta “Da nace miki bana son ‘kiba ce miki nayi ki ‘kanjame ji be kifa bakomai a jikinki sai ‘kashi……” ai kuwa ta mi’ke “amma dai kasan ko lalacewar nayi a gidanka na lalace don ba haka ka aure ni Ba.” A zafafe shima yace “A ya na aureki?dama can duk ciko ne kada ki manta a daren farko na gane komai ciko kike yi, komai na jikin ki Ba ki da ‘kirar mace ko ka’dan komai ciko…” hawaye ne kawai ya fara zubar wa Shaheedah ganin cin mutuncin da yayi mata a gaban Hisham taji kamar ta ‘dora hannu a kai ta saka ihu….

Saduwar alheri ku yiwa ‘kanwata addu’a An yi mata c.s ta samu ‘karuwa Baby Boy. Nagode
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Hajja ae gidan kamsh
Turaren wuta
Turaren gashi
Turaren kaya
Turaren wanka
Kulaccan
Kurkur oil
Humran
Kabbasa
and more
Whatsapp number 09120958937

In dai turare mai nagarta kuke nema to kun dace, ku nemeta domin ku kwashi gara’basa.

Me Zan Yi Da Ita?

Kai Alhamdulillah Masha Allah jiya sister ta ta sha addu’a am really appreciated wallahi. Jazakumullah bil jannatil Aaliyah.

ME ZAN YI DA ITA?

40….

Da wata irin zabura ta mi’ke cikin matsanancin ‘bacin rai tace “Wallahi Imran ka yi da ‘yar halak you will pay for it.” Daga haka ta shige ‘dakin ta cikin tashin hankali, tabbas dole ta kira Antyn ta ta gaya mata kalar iskancin da Imran ya tsiro da shi. Alamar duk wani shiri na su ya ruguje ko yana daf da rugujewa.

Imran tsaki yayi yana kaolin Hisham da duk ransa ya ‘baci, da abinda ya aikata. Zai yi magana Hisham ya dakatar dashi. “Am highly disappointed wallahi au Imran gaskiya ban ji da’din abinda ka aikata ba da alama yarinyar nan ba ta jin da’din zama da Kai, me yasa ka canja ne completely kamar ba Imran ‘din da na sani ba?” Tsaki Imran yaja yana zama saman kujera kansa kawai ya dafe yana murza goshinsa, kafin ya ‘dago idanunsa sun burkice sunyi jajur “Ba zaka gane ba Hisham gaba ‘daya yarinyar nan ta fice min a Zuciya, ga takaici da dana sani da nake na sakin waccen Yarinyar.” Da sauri Hisham ya ware ido “What! Tsaya wai wa kake nufi? Kada kace min Shatun Mommah?” Direct Imran ya amsa masa “Yes exactly ko ina da wacce na saka ne bayanta?” Wata dariya ce ta ‘kwacewa Hisham “Ashe kuwa ka sha giyar wake in dai Shatu ce, kada ka manta Shatu fa Fulanin Daji da kace ko an ‘daura maka ita a ‘kafa sai ka kunce, yarinyar da Mommah ta za’ba maka ka saketa within three days da aure ita kake gaya min kana da na sanin sakinta? To me zaka yi da ita? Kada kace min dawo da ita zaka yi domin kuwa tayi maka nisa tuni ta yi aure ta haifi twins.” Wata irin zabura Imran yayi hankalinsa a tashe ya mi’ke yana kallon Hisham, kafin ya ji wani jiri na ‘dibansa “Kace min wasa kake Hisham? Please!” Hisham yayi tsaki akan me zan yi mk ‘karya gaskiya na gaya maka.”
Daga haka ya zauna yana kallonsa “Ba abinci ne a Gidannan? Naga tun da na shigo ko ruwa baka bani ba..” Imran bai ko kalleshi ba ya zauna dafe da kansa. Zuciyarsa take wani irin tu’ku’ki tamkar ya mutu, da gaske ne Shatu tayi aure? Shatun da yake da niyyar mayar da aurensu, Shatun da ta mamaye duk wani gurbi da tunani na zuciyarsa, Shatunsa da yake tuno da duk wasu ni’imominta da Allah ya bata a lokacin da ya tara da ita, itace wani banza can ya aureta har ya ‘dan’dani ni’imarta yaji taushi da santsin fatarta, yaji za’kin ba’kinta ya ‘dan’dani da’di da gar’dinta har da albarkar zuria a tsakaninsu. Da sauri ya hau yamutsa sumar kansa yana fa’din No No No! Da ‘karfin sa. Hisham tsayawa yayi cak yana kallonsa tsananin mamakin lamarin yake yi. Kafin ya ja tsaki yace “Tunda baka yarda ba kaje Nigeria ‘din ka gani. Ai gani ya kori ji, kuma idan babu Abinci a gidannan ni zan kama gaba na.” Mi’kewa kawai Imran yayi hannayensa zube a aljihu ya hau struggling a parlourn kafin ya juyo cikin kyakykyawan kallo ya tsare Hisham da idanunsa cikin zafin rai yace “Wani mai gangancin ne ya aure min mata?” Tsaki Hisham ya ja kfin yace “Kayi Istigfari ka daina kiran matar wani da sunan matarka, mutumin da ya aureta har da albarkacin zuri’a tashi guda twins ta haifo masa alamar an sha soyayya kafin a haifo su don sosai yaron yayi kama da ubansa..” flower verse ‘din dake gefensa yayi cilli da ita ji kake wani taratsatsa bai damu ba ya tashi ya bi ta cikin glasses ‘din ya isa inda Hisham yake. Wuyansa ya da’kuma a wani irin yanayi ya furta “Don’t tell me rubbish, ya ishe ni Hisham, ka gaya min sunansa nace kawai!” Hisham ya ta’be baki ha’de da mi’kewa yace “Sunansa Muhammad, malam zaka bani abinci ko na kama gabana na gaji da wa’dannan silly Questions ‘din naka kana nufin don ka saketa sai a rasa mai aurenta duk da tsananin kyan ta?” Idanunsa akan jinin ya ke masa magana “Idan ban da hauka ji yarda ka jiwa kanka ciwuka tun ma ba kayi arba da yarda ta goge ta zama kyakykyawa ba, da kuma santala-santalan yaranta ina ji da sai zuciyarka ta buga don tsananin takaici, ga shi wanda ta aura ‘din yana tsananin sonta ya kuma fi ka komai ku’di kyau uwa uba dukiya……” da ‘karfi Imran yace “Hisham! I’m tired of you nonsense zo ka fice min a gida kuma bikin naku ma ba zan zo ba, sai me don tayi aure ina ce dai ba gwauro ka ganni ba da matata.” Hisham yana dariya yace “Fankon? Ko ba kai da bakinka kace duk ciko bane yanzu ne zaka kirata mata? Gida kuma kar kazo amma ka sani ko yanzu ka mutu, da kyar rahmar ubangiji ta sameka saboda rashin biyayya ga iyaye, Na barka lafiya dama sada zumunci nazo muyi tunda kuwa kayi min korar kare sai nace saduwar alheri.” Daga haka yayi saurin ficewa daga gidan saboda dariyar da take shirin fallasa shi. Sai da ya bar harabar gidan sannan ya shiga tuntsira dariya tamkar mahaukaci sabon Kamu.

———————————-

Tana kuka sosai ta shiga kiran mahaifiyarta, zuciyarta tamkar ta tsinke don tsananin ‘bacin rai. Da kyar ta samu kiran yayi connecting, Antyn ta ta ta ‘daga wayar “Shaheedah ya aka yi?” Fashewa da kuka Shaheedah tayi kuka mai cin rai da saka tashin hankali a zuciyar mai sauraro “Anty wallahi na mutu, yanzu Imran ya tsane ni ya tsani surar jikina tsana mafi muni….” Tsaki zainab tayi kafin tace “To ba dole ya juya miki baya ba Shaheedah, kin zauna kin ‘kanjame ke ‘yan magungunannan na ‘karin ‘kiba da hips ba shan su kike ba balle ki ciko ki yi dumimi irin na ‘ya’ya mata, me nace miki rannan da kika turo min pic ‘dinki ban ce miki ki nemi magani ba kin zauna kin ‘kanjame kin bushe kin lalace wai ke miji baya son ‘kiba, sai ranar da ya auro mai ‘kibar sannan zaki san dama yaudararki yake.” Kuka ta sake fashewa, sam bata son jin kalmar kishiya. “Ba zaki min shiru ba ki saurari abinda zance miki? Ko kin ji nace kishiyar za’a yi miki? Ki san yarda kika yi kika dawo Nigeria zan baki supplement Na ‘karin ‘kiba kuma ki saki jiki ki dinga cin fats ko kya tayar da koma’dar da ta kwanta, duk namijin da kika ji yace baya son mace mai ‘kiba ‘karya yake bai samu bane, sai kin murje jikinki sannan za mu san abin yi.” Tayi shiru tana jinjina lamarin komawa gidan a zuciyarta, ba don komai ba sai don bata son ha’duwar Imran da Shatu, don haka tace “To amma Anty kina ganin dawowa gidan ba matsala? Bana son Habibi ya ha’du da Shatu wallahi.” Antyn ta zabga tsaki “Ke kike ta wata Shatu tun taushe muka yi musu farra’ku ko kin ga ko zancenta yana yi? Ina ji ma Ammar ne zai aureta haka dai Manga yace ban ce kuma ki sanar da Imran ba kin ji na gaya miki. Kuma kin je kin cire abin hannunnan ko yana nan ma’kale a hannunki?” Ta ja ajiyar zuciya kafin tace “Tun yaushe na cire nima yanzu buri na ai na haihun, tun da naga kamar yana son yara, har yanzu fa bai sanma ta haihu ba fa.” Anty ta tuntsire da dariya “Ai dabararki tayi Shaheedah ban ta’ba zata ni kika biyo ba sai da kika aikata hakan naji da’di sosai, ko da takaicin wannan aka barsu ai ya ishe su, ka haihu uban yara ya’ki zuwa ganinsu kuma ko hoto bai ce a tura masa ba, ai kin sha’ka musu aikinki yayi kyau wallahi.” Haka dai suka yi sallama suna sake ha’da ‘kulle-‘kullensu da makircin su ubangiji ka raba mu da sharrin zuciya.

—————————-

‘Kwala kiran da Mommah take mata ne ya sata fitowa da mugun sauri, hannunta ‘dauke da Spoon da take aiki dashi a kitchen. A hanzarce ta isa ‘dakin Mommah don jin kiran kamar ba na lafiya ba.

A tsaye ta samu Mommah Ikram a bayanta da alama barci takeyi don ta tashi da ‘dan Zazza’bi. Hawayen da ta gani a fuskar Mommahn yasa gabanta matu’kar fa’duwa ta isa da sauri tana tambayar “Lafiya?” Mommah ta runtse ido tace “Shatu sai dai muyi ha’kuri Dada tazo sa’i lokaci yayi yanzu Hajiya Mama take gaya min.” Hawaye ne sosai ya mamaye fuskar Shatu tace “Innalillahi wa innailaihirrajiuna! Ashe ha’duwarmu da ita ta ‘karshe kenan da muka je kai mata yara.” Mommah ta saki ajiyar zuciya tace “Eeh, Baiwar Allah kenan Dada mai matu’kar ri’ko da addini, mai son zumunci da fa’dar gaskiya komai ‘dacinta Ubangiji Allah ya gafarta miki Dada.” Hawaye ya sake wanke idanunta tana tuna drammerr da suka sha lokacin da suka kai mata su Ikeey, ta dinga rungumesu tana cewa “Ubanku yayi asara yana ma kan yi ‘dan banza mai idon gwal ai zai zo ya sameni ne, shine ya ‘dirkawa ‘yar ciki har cikin ‘yan biyu sannan ya saketa duk don kada ayi masa dariya bayan ga abin dariyar nan ya bari tun da gashi nan wannan mai faskareren kan shi ya ‘dauko, da an yi magana sai yace me zai yi da ita? Yau dai ga abinda zai yi da ita nan ya fito ‘dan jakar Uba.”
Hawaye ya sake zubowa Mommah ta share su, tace “Allahumma gafir zunubiha jami’an. Maza Shatu kije ki duba girkin ki, ba mu da lokaci jirgin asuba zamu bi insha Allah,idan mun sauka a
Bauchi sai wani ya tare mu a mota.

Da sauri Shatu ta juya dai-dai lokacin da taji Knocking tana bu’dewa taga mai gadi, waya ya mi’ka mata yace “Don Allah kaiwa Hajiya Chairman ne ke magana.” Ta shige da sauri takaiwa Mommah.

Mommah ta san wayar waye, don haka ta ‘daga bayan gaisuwa ta sanar dashi mutuwar Dada. Salati ya saka da wayar a kunnensa, kafin ya dawo daga shock ‘din Mommah ta katse wayar.

Yana ta Hello! Yaji ‘dif hakan yasa ya ri’ke wayar zuciyarsa cike da wani irin tsoro ya shiga kwararowa Dada addu’oi a zuciyarsa. Kafin da azama ya fara booking flight ta internet. Ya shiga kiran wayar Hisham da kamar ba zai ‘dauka ba sai kuma ya ‘dauka a zafafe yace “Ka gama kora ta daga gidanka meye kuma na kira Na?” Imran yace “Allah ya baka ha’kuri ni mutuwar Dada na bugo na sanar maka.” Hisham ya ja salati shima kafin ya ri’ke kansa ba ‘dan ka’danba yaji mutuwar Dada kakarsa. Imran ne ya gaji da shirun yace “Kana ina ne?” “Ina ruwanka da inda nake? Ina airport gida zan koma yanzu haka ina cikin flight.” Imran yace “Shikkenan ma ha’du gobe a Nigeria nima na yi booking gobe zamu taho, and thanks for the visit kayi ha’kuri da rashin kyauta ta maka da ban yi ba temper tace ta hau da yawa. Ni kaina I don’t know what am going through amma insha Allah zanyi ta addu’a safe flight sai mun ha’du.” Jikin Hisham ne yayi sanyi yana jin kamar wani abu mai kama da tausayin Imran yana tsirga masa amma Ammar fa? Ya ri’ke kai Allah ya kiyaye samuwar tashin hankali a zuri’ar su.

Gefe ‘daya Imran da sauri ya isa ‘dakin Shaheedah, a gaban dressing mirror ya tarar da ita sai tsara kwalliya take tamkar zata shiga gasar sarauniyar kyau, sai dai maimakon ya ga kyan muninta ya gani saboda wasu ‘kasusuwa da suka bayyana a fuskarta, ya dai daure don tilas ya sakar mata murmushi “Kin yi kyau” ya furta a hankali wanda da Shaheeda da za ta tsaya ta kalleshi sosai zata tarar furucin iya bakinsa ne bai kai zuciyarsa ba, amma ina idanunta ya rufe wani farinciki ya baibayeta har bata san sanda ta taso da azama da rungumeshi ba hawayen farinciki na zurara a fuskarta “Nagode Habibi.” Tausayinta ne ya kama shi ya ‘dan bubbuga bayanta “Is Okey ki shirya maza zamu bi jirgin safe gobe, Dada is death.” Cikin tsananin farincikin zuwa Nigeria da bayyana a fuskarta ‘Baro-‘baro tace “Okey Habibi.” Ya tsaya sak yana kallonta ganin ko ka’dan mutuwar Dadan bata girgiza bata mamaki ya cika shi, sai kawai ya girgiza kai ya juya zai fita. Ji yayi da sauri tace “What should I cook for you?” Ransa a ‘bace yace “Nothing.” Jikinta ne yayi sanyi kuma ganin yarda yayin bai wani yi ‘dokin son kasancewa da ita ba balle yayi tunanin bata ha’k’kinta. Ta ta’be baki a zuciyarta tace “Mu je dai Nigeria ai matsalata ta kusa zuwa ‘Karshe sai ka zo kana bina, wallahi sai na mayar da kai abin kwatance mijin kafin tace ma ba tace ba.” ta tuge hular gashin da tasa ta cilla akan Gado.

—————-

‘Karfe 9:00 Na safiyar asabar aka sada Dada da makwancinta, ‘daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar baiwar Allah Dada kuma kowa yazo fa’dar alhairinta yake musamman maigidanta Moddibo da shima yana nan tsoho mai ran ‘karfe, ‘ya’yanta su lami’do da su Alhaji Baba ba ‘karamin girgiza suma su ka yi da mutuwar ba, haka nan jikoki da ‘ya’yan jikoki su Shatu, tabbas Dada tayi tsahon rai ta kuma tara zuri’a mai amfani sai dai fatan saduwa da Rahmar Jalla.

Ta mutu daren juma’a an kuma birneta asabar Allah ya gafartawa iyayenmu. Duk inda Shatu tayi idanun mutane ne a kanta ganin yarda tayi wani irin kyau ta kuma cika ko ina mulmul da ita ta ko ina idan ka ganta ba zaka bata shekaru sha bakwai da rabi ba sai dai ka lulata ashirin saboda cikar da tayi, su Akram dama tuni ta yayesu, ba kuma a taho dasu ba suna can gidan Alhaji Baban da ya ‘kera anan liman katagum ‘din.

—————————

‘Karfe takwas jirginsu ya sauka a airport ‘din Nnamdi azikwe da ke Abuja. Mutanen turkey an bayyana a Nigeria bayan tsawon shekara ‘daya da rabi. Kasancewar ba su samu jirgi ba hakan yasa dole gidan Dahda suka nufa da niyyar gobe suyi asubanci su nufi garin Bauchi by flight.

Da murna Anty Amarya ta tare su kamar ta goya su, shi dai Imran sassan Mommah ya tafi da sauri ba tare da ya tsaya rawar jiki wajen Antyn ba. takaici ya kama ta sai dai bata nunaba burinta ya ci abincin da ta riga ta ba’deshi da sihirtaccen Maganin da Shuwa ta kawo mata.

Yana knocking Basirah da Yasirah da suke aiki a parlourn suka kalli juna, suna tunanin bu’dewa, ‘kara knocking ‘din da suka ji an ‘kara yi ne yasa su cewa waye? Ya amsa da “Bu’de” jin muryarsa yasa su bu’de ido, da sauri Basirah ta bu’de. Ya shiga cikin takunsa na ginshira idanunsa zube a kansu, yana amsa sannu da zuwan da suke masa, sai da ya zauna sannan yace musu “Ku nutsu tambaya zan muku,kuna ji na?” Gaba ‘daya suka nutsuwa suka dur’kushe idanunsu a ‘kasa “Tambayar ku zan yi Da gaske Shatu tayi Aure?” Da sauri suka zare ido suna kallon juna ga shi ba daman su yi masa ‘karya hakan ya sa suka sunkuyar da Kai…… ya buga table ‘din da ‘karfi yace “Ba kwa ji ne malamai?” Basirah ce Ta ‘dago idanunta a kansa tace……….

Saduwar alheri ina ji daku mutanena.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan Yi Da Ita?

41

“Eeh tayi aure…” Yasirah ta zuba mata ido da sauri kafin ta mayar da kallonta akan Imran da ya runtse idonsa gam yana furta “Oh shit!” Yana buga hannunsa a table, sai kuma ya mi’ke hannunsa saye cikin aljihu ya bu’de ainahin ‘dakin Shatu, fes dashi ‘dakin ga wani ‘kamshi da ya kamashi ram na ainahin turaren da take amfani dashi. Idanunsa ya sauka akan wangamemen pic ‘din twins suna babies, zuciyarsa na dukan Tara-tara ya ‘karasa gurin pic ‘din… cikin takaici yake shafa hoton kishi ya cika zuciyarsa fal. Ya shiga tunanin da tuni zuri’arsa ce wannan ‘din. Ji yayi har jiri na neman kada shi hakan yasa ya kwanta flat a saman gadon Shatun, tunaninta ya dinga bijiro masa a yanayin da ba zai fasaltu ba. Da sauri ya dinga jan istigfari tunawa da yayi a yanzu Shatun matar wani ce. Jikinsa a sanyaye ya bar bedroom ‘din nata bayan yaji a yanzu ba abinda yake bu’kata irin yara.

Ko da ya fito Anty Amarya ba yarda ba tayi dashi ba ya tsaya ya ci abinci amma ya girgiza kai “Alhamdulillah nagode” ya yi furucin yana ficewa da sauri. Motar Mommah ya hau ya bar gidan.
Takaici ya cika zuciyar Anty Amarya da Shaheedah da suke jin tamkar su saka kuka.

———————————

‘Karfe 9:00 dai-dai suka isa garin katagum. Gidan a cike yake dan’kam nan ido gaba ‘daya ya koma kan Shaheedah kowa mamakin ramarta yake yi. Wai don ma a haka Hijabi ta sako har ‘kafa.

Lokacin Mommah da Shatu basu iso ba suna gidan su Mommahn, Hajiya Mama ce kawai ta taho amma har su Hafsa da Nahna suna can Gidan ba su taho ba, haka nan Hisham da Ammar.
Dalilin hakan bayan ya gaida jama’ar da suke dam’kar a gidan ya fice da sauri burinsa yaga Mommah. Ita kuwa Shaheedah Hajiya Mama da farinciki ta tare ta, ta sa aka kawo mata kayan breakfast.

Drivern Alhaji Baban yana parking Imran ya fito, cikin takunsa na ginshira, kayan sun amsheshi sun masa kyau sosai ba’kin yard ne a jikinsa ‘dinkinsa na kullum gajeriyar riga da gajeran hannu, wannan karan dai anyi abin arziki ya saka hula a kansa, kuma hular ta amsheshi sosai da sai ‘kamshin turare yake yi.

Ya da’de yana Knocking kafin Shatu da take kitchen tayi saurin fitowa kanta ko ‘dankwali babu, Gashinta gaba ‘daya ya zuba har gadon bayanta. Doguwar riga ce a jikinta mai jikin robber da tabi ta kwanta a jikinta ta kuma lafe ta fidda duk surar jikinta. Fitowar Hisham da Ammar ce ya sata jin wata matsananciyar kunya tayi saurin bu’de ‘kofar kafin ta juya ta shige kitchen ya danno kai cikin parlourn ha’de da ‘kamshin turarensa da ya baibaiye parlourn, wani shock da bugawar zuciya ne ya samu Shatu a lokaci guda, haka nan Imran da Ammar da yake gefe. Da sauri ta juya ta shiga kitchen ba tare da tayi masa second look ba.

Ko a kitchen ‘din ma tsayawa tayi hannayenta dafe da ‘kirjinta tana saurarar yarda bugawar zuciyarta ke ‘karuwa, idanunta na sake hango mata fuskar Ammar da ya sake ‘kawata ta da kyakkyawan saje, yayi fresh sosai alamar Naira ta zauna masa. Wani danshi taji a saman fuskarta, da hakan ya sata saka hannayenta ta ji ko menene mamaki ya kamata da taji wai ashe hawaye ne yake zuba daga idaniyarta ta, hawayen da za ta kira na takaicin ganinsa, ba ta so ganinsa ba a lokacin da komai ya ‘kure. Mutumin da take kwana take tashi dashi, zuciyarta kullum bata fasa tunanoshi ba, in dai za tayi sallah sai ta Ro’ki ubangiji ya zare mata son shi daga zuciyarta, amma abin al’ajabi kullum soyayyar nan ninkuwa take, musamman idan tana ganin Akram da yake tsananin kama da shi. Idan tace bata son Imran ta yiwa kanta ‘karya shine first love ‘dinta da kuma shi ta so tayi rayuwar aure na dindindin, rayuwar da babu tasgaro a cikinta, sai dai tuni ‘kaddara ta riga fata a yanzu dai kam ba zata ta’ba iya kallon idon Ammar tace bata sonsa ba, ko ba zata iya aurensa ba ya riga yayi mata halarcin da bai kamata ta bar shi ba a cikin ko wane hali. Sai kuma ta tuna da jan kunnenta da Hisham yayi akan ko da Imran yazo ta gaya masa tayi aure ‘ya’yan bana sa bane, haka ma ya ro’ki Mommah, hakan ya sa ta sakin murmushi a zuciyarta tace “Za’a buga drammer domin a jikinta ta ji kallon da Imran yake jifanta dashi, ta shafa kanta da ko head tie babu, idanunta akan ‘kirjinta da hips ‘dinta da suka cika fam a cikin rigarta, wata kunya ta kamata ta san dole ko ba so duk namijin da ya ganta a wannan shigar ya baibayeta da kallo, wanda ba zai kasance na komai ba sai na zallar sha’awa. A hankali tace “Astagfirullah! Don kuwa sarai ta san ba muharramanta bane Hisham ne kawai muharrimanta. Ba tayi aune ba ta fara jiyo ‘kauri, da sauri ta kai dubanta ga naman da take tafasawa za tayi shawarma, tuni ta waro ido ganin naman yana shirin ‘konewa saboda tunanin da ya aureta na ba gaira ba dalili, tunda dai bata san da wacce Imran yazo ba. Duk da Uncle Hisham ya fara bata labari.

—————————-

Mommah da take shirya ‘yan jikallenta ta jiyo sallamarsa a bakin ‘kofa, sak tayi tana amsa sallamar cikin wata irin fa’duwar gaba da ita kanta bata san ta mececeba, ganinshi a gabanta ya sa zuciyarta ta karye, ‘kwalla ta baibaye idanunta, tsawon shekara ‘daya da rabi sai yanzu ya tuna da gida? Ta lumshe idanunta tana kallonsa ido cikin ido ‘kwalla ta shiga gangaro mata. Da azama Akram ya shiga share mata cikin salon maganarsu ta gwaranci yake fa’din “Sowi Mommah.” Ya kuma rungumeta, yana fasa kuka shima. Sosai memory ‘din da ya dawo mata yarda Imran ‘dinta yake mata a duk lokacin da ya ganta a
Damuwa, jikinsa kamar an zare laka haka ya shiga takowa inda take idanunsa akan Akram da tun bayan ganinsu yake jin wata fa’duwar gaba.
A gabanta ya dur’kushe ya kama duk hannayenta ya damtse su kamar yarda yake yi a lokutan baya idan yayi mata laifi ya rasa yarda zai yi ya nemi afuwa. Shiru tayi idanunsa cikin na ta kafin ta zare hannunta cikin dakiya da ‘karfin hali tace “Maraba lale da mutanen turkey dirar yaushe kuma?” ‘Ko’kari yayi sosai wajen mayar da dukkan damuwarsa ya saki murmushin ‘krfin hali kafin yace “Jiya muka iso muna Abuja, ya ha’kurin Dada?” Mommah ta gya’da kai kafin tace “Kun kyauta, Dada kuma anzo sa’i sai dai Allah ya gafarta mata yasa kuma can ta fi mata nan. Ina Hakimar take?” “Allah yaji ‘kanta ya bamu ha’kurin rashinta.”
Ya amsa mata yana bagarar da waccen tambayar ba don ya rasa amsarta ba, sai don ba ita bace a gabansa. Mommah ta bi shi da kallo tana kallon yarda yake kallon yaran ta san tambaya ce fal a bakinsa, amma ya rasa ta yarda zai fara, hakan yasa tace “Akram ku gaida uncle ‘din ku.” Yaran suka zuba masa ido kafin su fara gwarancinsu, yana murmushi yake amsa zuciyrsa fal da mamakin yarda Akram ‘din ya ‘dauko zahirin kamanninsa “Mommah yaran wanene?” “Na Shatu” Direct ta ba shi amsa tana mamakin tambayar tasa wato da gaskiyar Hisham da yace bai san an yi haihuwar ba, idan kuwa haka ne waye ya turo wannan message ‘din, akwai alamar tambaya akan hakan sai dai ba yanzu za tayi masa ba sai nan gaba. Ta mi’ke ta fice daga ‘dakin ba tare da ta sake waiwayarsa ba. Shi kuwa flat ya kwanta akan bed zuciyarsa cike da tunaninnika da dama Musamman Shatu yau da ya gani ta zama Hamsha’kiyar mace ta ko ina ta amsa sunanta na mai kyau.”

Mommah na shiga kitchen ta ga Shatu na aikin abincinta duk da ta kammala tana juye su a wammers, ga ikeey a gefenta da take ta kukan noodles zata ci. Mommah ta ja Ikeeyn tana rarrashi kafin ta kalli Shatu tace “Ko ka’dan kada ki bashi fuska ba ruwanki da shi, tunda dai kinga an riga an saka ranar ku da Ammar bana son wani abu yasa a fasa Ammar ne abin a tausayawa yanzu tunda shi ba shi da mata shi kuwa ya rasa ki yana da inda zai je yaji sanyi, yara kuma alamu sun nuna bai san da su ba, don haka kada ki nuna masa nasa ne. Ni da kaina idan ta tunkareni da zancenki zan sanar dashi Ammar zan bawa ke ko ma na riga bashi. Ki kula sosai bana son zubar da aji.” Shatu ta sunkuyar da kai a hankali tace “To Mommah.” “Yauwa ki kiyaye don yanzu haka ya zata kina da aure kamar yarda Hisham ya sanar masa, sai dai a yau idan na dawo a gaban Hajiya Mama zan sanar da shi yaransa ne, aure kuma ba ki dashi sai dai Ammar za ki aura kin ji me na gaya miki?” Shatu ta ‘daga kai kawai a zuciyarta tace ma “duk zancenku kuke ba ni bace a gabansa.”

A gurguje tayi wankan Ta ‘dauko set ‘din mayukanta na makari ta fura mutstsika wa a fatarta da take walainiya kamar ta tarwa’da, ko powder bata saka ba kasancewar gidan mutuwa za suje, ta zira tight trozer ‘din ta da half gown, sannan ta kawo after dress bugun Larabawan Oman ta saka sea blue mai touches ‘din maroum don haka ta yane kan ta da mayafi maroum. Sosai tayi kyau kamar ka sure ka gudu musamma da ta saka medical Glass ‘dinta fari tas da shi da zagayen ba’ki sai ta fito zam kamar Bahabashiya. Duk da ba wata kwalliya ta fesa ba illa lip gloss da ta goga a le’benta.

Takalmi flat ne a ‘kafarta amma yanayin yarda take tafiya sai ka zata hill shoe ne, taku take gaba ‘daya’kugunta da sassan jikinta na rausaya kamar ganyen bishiya. Yarda ya kafa mata ido har bai san san da ya kur’bi tea ya ‘kwareshi ba, hakan yasa duk gurin suka kai duba ga yarda yake kallo. Mommah ta’be baki tayi kawai ta cigaba da shan shayinta. Ita kuwa Shatu tana ‘karasowa ta ha’de rai shi sai ya ga ma kamar harararsa take, ganin yarda suka zuba masa ido sai abin ya bashi kunya da sauri ya mayar da idonsa kan tea cup ‘din da yake hannunsa, amma ‘kasa-‘kasa kallon fresh fingers ‘din Shatu yake yi da suka sha zanen lalle. Tunda yake bai ta’ba yarda lalle abin kwalliya bane sai yau da ya gan shi a hannun Shatu. Tamkar ya sa hannu ya dam’ko su yayi ta shafar su, gaba ‘daya yaji zaman cin abincin ya gundireshi da sauri ya mi’ke ya kai hannu zai zari tissue kamar ha’din baki ita ma Shatu ta kai hannu zata ‘dauka hannayensu suka ha’de just like magnet, wani yarr Shatu ta ji a jiknta tayi saurin ‘dauke nata hannun tana kallonsa, “Sowie” yace wanda muryar sa ba ta fito ba illa la’b’ban bakinsa da suka motsa. Shatu ta ‘dauke idonta tana sakin wata ajiyar zuciya.
Yana juya baya ya ji Akram yace “Mommah uncle waye wannan?” Ya fa’da cikin gwarin hausar sa, da sauri Mommah tace “Go and ask him.” Cikin takaicin wai bai san ‘ya’yansa ba. Yaron yana zuwa ya ‘daneshi, yana cewa “uncle wa?” Imran da sauri ya rungumeshi yana kallon cikin eyes ‘din yaron irinnasa sak ba banbanci, har zai wuce sai wani tunani ya shige shi da sauri ya koma dinning area ‘din idanunsa cikin na Mommah yace “Mommah idan dai har Shatu tayi aure to da cikina tayi aure saboda wannan yaron da ni yayi kama, don haka auren ta bai halarta ba ina da damar maka shi court ya sakar min matata!” Gaba ‘daya gurin suka zuba masa ido…

Kuyi manage da wannan ina gidan mai jego.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

Wannan ne complete wancan mistake ne

42

Hafsa da Nahna dariya ta so ku’buce musu sai dai suka gimtse kawai. Yayin da Ammar gabansa ya shiga dukan uku-uku, yaji ganinsa na neman ‘daukewa, tashin hankalinsa ‘daya kada dai ace Imran kome ya zo yayi da Shatu, tabbas kuwa da zuciyarsa ta buga. Da kuma ya sanya hakan a mizani na rashin halarci matu’kar iyayensu za su sake yarda da Auren Imran da Shatu shi kuma ya tashi a tutar babu da ba’a yi masa adalci ba.

Mommah ta’be baki tayi a fusace tace “Sai ka ‘daura himma.” Ta mi’ke ma ta bar table ‘din gaba ‘daya tana ‘ko’karin yakice ‘bacin ran da ya taso mata, na abubuwan da duk suka faru a lokutan baya. Imran kuwa wucewa yayi da Akram aka fa’darsa zuciyarsa fes da samun mafita don ko ba’a yi DNA ba ya tabbatar wannan ‘dan nasa ne ko makaho ya shafa zai yarda da hakan.

A ranar su Hajja su kazo gaisuwa bisa tilastawar Kawu Sa’idu. Har da Zainab aka taho. Lokacin da su Mommah suka zo suka tarar dasu. Zuciyarsu gaba ‘daya sai da ta kusan bugawa da suka ga yarda Shatu da twins ‘dinta suka Koma. Yara kamar ‘diyoyin larabawa jajur dasu ga suma ba’ka si’dik kwantacciya a kansu ga shi jikinsu dumimi a murje gwanin sha’awa. Idanuwan kowa a kansu yake don ma Mommah tana tofe su da addu’oi kafin su shiga taro.

Gaba ‘dayansu da kyar suke amsa gaisuwar Shatu ita kuwa ba abinda ya dame ta bayan ta gaishe su mi’kewa tayi ta fice daga sashen gaba ‘daya tana mamakin yarda Shaheedah ta koma kamar mai cutar ‘kanjamau.” A gefe can daga tsakar gida suka zauna ita da Hafsa da Nahna sai suka zamo tamkar wasu fitulu masu haskawa.

Suna zaune su Imran suka shigo, Idanunsa suka fa’da cikin na Shatu tayi saurin ‘dauke nata ta mayar kan nasu Akram da suka mi’ke da guru, suka nufesu direct Akram wajen Babansa ya nufa ita kuwa Ikram wajen Uncle Ammar ta nufa. Har sun wuce yaron yace “Uncle caya na amco ciweet a wajen Mimi na.” Imran yace okey bari na kai ka, har gurinsu ya ‘karasa dashi yaron ya mi’ka mata hannu “Mimi na ciweet.” Harara ta zabga masa tace “Ka sauka daga gurinsa ko sai na makeka, ka san shi ne?” Da sauri Imran ya watsa mata idanu yana kallon ‘dan ‘karamin bakinta da yaji tamkar ya kai mata sumbata a zuciyarsa yace “Sai tsiwar tsiya.” Shi kuwa Akram kuka ya saka jin fa’dan da Miminnasa take masa. Cikin zafin rai Imran yace mata “Zaki ba shi ko sai na ‘bata miki rai? Ni kike cewa kuma bai sanni ba ko? Daga ke har mijinnaki ku saurari sammaci zan ji dalilin da yasa kika yi aure da cikina a jikin ki.” Murgu’da masa baki tayi har da ‘dan guntun tsakin ta. Imran ya wara ido kafin yace “Ni kike yiwa tsaki?” Ta sake zuba masa harara ta ‘dauke Kai. A zafafe ya juya da yaran a hannunsa ya ma fasa shiga gidan mutuwar sai yaje asibiti anyi DNA test ‘dinnan. Idan kuwa ya tabbatar da yaron nan ‘dan sa ne wallahi sai yaci uban mijinta, sai kuma yayi shari’a da wanda ya ‘daura mata aure da cikinsa a jikinta. Tunanin da ya dinga yi kenan yana driving a motar da ya kar’bi key ‘dinta wajen drivern Alhaji Baba.

Sun da’de a asibitin kafin result ya Fito, a hakan ma don ya sakar musu ku’dine kuma private hospital ne. Sakamako dai ya nuna yaro nasa ne. Likitan cikin tsokana yace “Ai ba sai kayi DNA ba kamanninka da yaron kamar kayi kaki ka zubar ya isa a shaida ‘dannan naka ne ko tantama babu.” Imran murmushi yayi yana kar’bar takardar as evidence zuciyarsa a dugunzume da ‘bacin ran da wani banza can ya aurar masa mata, ya raya a ransa wallahi sai ya ‘daureshi kuma shari’a zasu zuma da shi har kotun ‘Koli.

A zafafe ya koma gidan mutuwar, ya tarar su Hajja har sun fito zasu tafi, don haka antsaitsaye suka gaishe shi har zai wuce Hajja tace cikin ‘bacin rai “Imrana idan ka sami lokaci ka zo ina son ganinka in ji dalilin wannan rama ta tashin hankali da Shaheeda tayi.” Wani kallo ya jefi Shaheedan dashi kafin yace “Ai bani zaki tambaya ba ita zaki tambaya dalili tunda ni dai ina bata ci da sha, ina kuma sauke mata duk wani hakkinta na aure.” Daga haka yasa kai ya shige gidan a ransa yake fa’din “Ke ce wannan yake a gabanki ni ba shi bane a gabana.” Gaba ‘daya sak su kayi suna kallonsa tare da tsananin mamakin sauyawarsa kamar ba Imran ba da suke juyawa son ran su. Hawayen takaici ya zubowa Shaheeda tace “Hajja kun ga abinda nake gaya muku ko?” Hajja ta girgiza kai “Na gani ba shakka wannan karan Dijah da ‘karfinta take, to wallahi gidan ta tarar mu zuba ni da ita shege ka fasa jar uba! Ban ga ta zama ba. Zainab ma da falmata da ran su ya gama dugunzuma ya ‘baci suka dinga sakin maganganu da alwashi iri-iri na son rai da ba’kin hali a zuciyarsu.

Ko da ya shiga gidan bai tarar da su ba sai su Mommah da Hajiya Mama, hakan yasa ya shiga rarraba ido yana son yaga ta inda zai hango ta rigima ce take cin sa sosai a ransa. Mommah ta kalleshi ta hango rigimar da take zuciyarsa a zafafe tace lafiya? Shima cikin dakiya da jarumtar da ya aro yace “Uwar yaronnan nake nema.” Ba Mommah ka’dai ba harta Hajiya Mama sai da gabanta ya fa’di lokaci guda kuma dariya ta kusan ku’buce mata. Mommah ta mi’ka hannu “Bani shi nan, ai ba ce maka yayi dole sai a hannun uwarsa zai zauna ba.” Yaro kuwa ya ma’ke kafa’da alamu sun nuna ba ya son zuwa wajenta, a zafafe ta ja hannunsa ya kuwa saka kuka. Hajiya Mama tace “Kema sarai kin san ba zai zo ba, yarda baya son mutane ba zama zaiyi ba ya tafi dashi ya kaishi can gida gurin uwarsa, tunda su ma sun gudu saboda mutane ni ban ta’ba ganin masu tsoron mutane irin Shatu da iyayenta ba sai kace wasu kuraye.” Mommah harara ta zabgawa Akram tace “Zan dawo gidanne zaka ha’du dani ne.” Imran ya mi’ke da shi a kafa’darsa zuciyarsa fes jin Shatu ta koma gida zai je ayita ta ‘kare ta gaya masa wani shegen bunsurun ne mijinta. Shi ka’dai yake tunani a zuciyarsa.

Tun a mota ya tasa Akram da tambaya, tamkar yaron zai fahimci mai yake cewa. “Kai ya sunan mijin uwar ka?” Akram dariya kawai ya ‘bangala masa Imran yayi tsaki idona idon mutuminnan sai sha’keshi ya mutu har lahira idan bai yi wasa ba shege mai ‘katon kai.” Sumbatun da yake yi shi da kansa ya saka kan sa dariya cikin ‘bacin rai kuma yace “Just like I know him.” Ya furzar da hucin ‘bacin rai mai zafi a bakinsa.

Da masifar gudu yayi parking kamar zai tashi sama, har hakan ya ja hankalin masu hidimar gidan suna kallonsa. Ya fito da ‘dan hanzari Akram a kafa’darsa.

A parlour duk ya samu su Hafsa Shatu ce kawai bata nan tana kitchen ya lura masoyiyar kitchen ce ta gasken gaske. Kowa yayi masa magana banda Ikram da tayi kamar bata san Allah yayi ruwansa anan, ya zuba mata wani kallo a ransa yace “Ja’ira mai kama da uwarta.” Sannan ya kalli Hafsa kasancewar ya san tafi Nahna sau’kin kai yace “Ina uwar yarannan?” Da hannu Hafsa tayi masa poiting kitchen cikin mamakin neman da yake mata, kuma wai wani uwar yarannan kamar bai san sunan ta ba. Nahna kuwa tsaki ta ja a zuciyarta tace “Ai kuwa in dai Shatu ce kai tsaye zan ce maka ‘kwalelenka.” Ta tuno a ranar da ta ‘dauko Shatu bayan ya ‘dauke mata budurcinta ya kuma zabga mata saki saboda rashin tausayi, ya zama dole ta ja kunnen Shatu ta kama kanta da wani Imran Allah na tuba meye wani Imran ragowar Shaheedah ga Ammar gallelen saurayin da yake matu’kar san Ta. Ta sake bin bayansa da kallo ganin gadan-gadan ya shiga kitchen ‘din, tabbas ta yarda maza ba su da kunya ko ka’dan wallahi.

—————————————-

Tun a Mota su Hajja bakinsu bai huta da zancen ba har sanda suka isa gida. Nan ma sallah kawai suka yi suka ‘dora daga inda suka tsaya.
Hajja ta shiga kiran malamai tana basu ku’din sadaka tana ayiwa ‘danta da jikanta addu’a suna cikin wani yanayi. Sannan ta kira malamin duba ta gaya masa matsalolin ta, al’kawari yayi mata akan insha Allah zai duba mata kuma duk abinda ake ciki zai sanar mata.

Gefe guda kuwa Hameedah ce da Zainab har da Shuwa suke sake ‘kulla-‘kullarsu. Hameedah ta gyara zama cikin masifa tace “Amma Shaheedah an yi shashasha yanzu cikin kika je kika zubar? Don wauta kuma kika gar’kama abin planning a hannunki gashi nan ya zu’ke ki tas kin dawo sai kace sillar kara, yo ba dole miji ya wula’kanta kiba, saboda babu mamora a jikinki.” Ta sake zabga tsaki “Ko mace ba za tayi sha’awar sake miki second look ba bayan tayi na farkon. Ke kuma zainab wannan karan zancen asiri ya kau a canja wata dabarar ki koma kissa da sharri ki ‘kwace mijin ki.” Shuwa ta zabura tace “Ai kuwa wannan malamin aikinsa kamar yankan wu’ka yake wallahi duk taurin kan Manga wannan karan sai yazo hannu.” Hameedah ta mi’ke a zafafe tace “Wallahi ba wani asiri da zai ci manga a yanzu dai idan da ya cishi yanzu ba zai ci shi ba domin kuwa Hajja tuni tasa aka yi masa dafa’i. Don haka ni dai ina gaya muku ku canja shawara ke kuma ki nemi sha ka fashe ki sha, kafin a fara ‘dora miki cutar ‘kanjamau.” Daga haka ta fice da sauri. Shuwa ta bi bayanta da harara kafin tace “Alhamdulillah na samo bakin zaren.. haba No wonder muyi ta asiri baya cin bawan Allahnnan ashe shegiyar uwarsa ce tayi Kane-Kane. Tabbas yanzu abin zai sauya salo sai mun yi farra’ku tsakanin uwar da ‘dan sannan mu zo mu asirceshi. Allah mun gode maka da ka fitar damu cikin duhu shi yasa fa ni dama matar nan sam ba tayi min ba hushinta nake ji, don daga ganinta fuska biyu ne da ita.”
Ta bu’de jakarta ta ciro conrainers na ‘kwayoyin magani ta cillawa Shaheedah tana fa’din “Saura ki yiwa uwarki asara dubu maitan kenan ta bayar aka sissiyo miki duk na waje ne hips kam da boobs har sai kin gaji dasu, duk su ‘yan mata suke sha yanzu ki gansu tumbul-tumbul dasu idan kika jure da sha duk wannan ramar sai ta zama labari, ki kuma zage ki samu ciki shine zai zauna dake ko ya’ki ko ya so.” Haka ta saka su a gaba da fa’da tamkar uwar da ta kawo su duniya. Har yamma tana gidan suna sake koya wa Shaheedad tsagerancin yarda zata mallake mininta ta mallake dukiyarsa har suma ta ‘yan musu tunda ance yanzu har yafi ubansa ku’di.

————————
Imran kuwa yana shiga kitchen ‘din ya mayar da ‘kofar ya rufe, har da murza key, hakan yasa Shatu saurin juyowa idanunta suka fa’da cikinnasa, da yayi kicin-kicin da fuska, ya matsa daf da daf da ita, har tana iya juyo hucin numfashinsa, idanunsa akan ‘kirjinta da suke ‘dagawa ta cikin riga saboda fargabar da ta risketa a lokaci ‘daya, Ta yi ‘ko’karin matsawa fuskarta a ha’de tace “Ka bari it is prohibited in Islam!” Bakinta ta zubawa ido duka sassan jikinsa na tashi musamman jin hucin numfashinta a fuskarsa duk da ba rungumeta yayi ba, amma tuni yaji wani zazzafan feelings ya mamaye ilahirin sassan jikinsa, lumshe idanunsa yayi yana jin ‘dacin furucin da ba zai fa’da “Ya sunan uban wanda aka ce an ‘daura miki aure dashi? Don ni da ubansa zanyi shari’a ba dashi ba.” Shatu ta ware idonta a kansa kafin ta ta’be baki tace “A dalilin sun maka me?” ‘Kuri yayi mata da ido cikin ‘bacin rai, kansa tsaye kuma yace “Fashin mata mana.” dariyace ta so kamata sai dai ta gintse ta ha’de rai a zafafe tace “sai ka ‘daura himma.” “Zan kuwa ‘daura kema kuma sai na kaiki ‘kara dan ban san me yasa kika yi aure alhali kin san nayi miki ciki ba.” da sauri ta janye jikinta har tudun ‘kirjinta na shafar sa ya kuwa runtse ido don jin shi yayi ya afka wata duniya bai san san da ya sa hannu ya ri’ko tausassan hannunta ba. tana shirin zamewa ya ri’ke su gam kafin yace “Mijin naki ma Aldayyus da zai bar ki ki dinga irin wannan zanen a hannu shashasha ne na ajin ‘karshe, ji irin kayan da kike sawa.” murgu’da masa baki tayi tace “Ina ruwanka, shari’a kuma muna jiran sammaci.” ta fice daga cikin kitchen ‘din cikin azama ta barshi a tsaye zuciyarsa na sake han’koron ‘bacin rai. Burinsa ya san wanene mijinnan nata a fili ya furta wanene kuwa idan ban da ri’ka’k’ken jahili kayi aure mace da ciki baka sani ba wallahi sai yaci ubansa. Ya fice daga kitchen ‘din da azamarsa

Da daddare suna zaune duk za su fara cin abinci, Imran ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya nufo inda suke baje akan dadduma suna shirin fara cin abinci. Zama yayi kusa da Alhaji Baba idanunsa cikin na Shatu kawai sai ji suka yi yace “Ke mijin naki bai zo ya ‘daukeki bane?” Alhaji Baba sai yaji maganar wata iri don bai san da zancen za’a wahalar dashi kafin a gaya masa bata da aure ba, ya dubi Imran yace “Tana da wani miji ne bayan ‘dan uwanka Ammar…..” Gaba ‘daya Imran ya fito da idanunsa cikin wata irin fa’duwar gaba idanunsa suka sauka kan Ammar sannan ya dinga bin mutane da kallo ‘daya bayan ‘daya kafin ya mi’ke cikin sarewar gwiwa da kasala ya shige ‘dakin da ya fito daga cikinsa…….

Saduwar alheri, amma don Allah ku daina damuna in ‘kara yawan pages ba ku san da yaya nake typing ‘dinnan ba, ba fa biyana kuka yi ba free book ne.

Ina godiya da wasu daga cikin group ‘din jiddatul khair da suka saka min ku’din data nagode sosai don haka ba zan gaza ba wajen fa’dar sunanku. Wasu kuma mu tara a wani pages ‘din, gaba ‘daya na sadaukar da wannan page ‘din gareku

Sakina Ibrahim Dayyab
Aisha sa’ad Abdullahi
Bilkisu ubaid
Zara Musa
Aisha Dan toro
Fatima Sunusi
Baraka usman
Aysher
Tees cuisine
Ummin khadija
Maman mubarak.

Thanks so much I really appreciated ❤️❤️
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

43

Tun bayan shigarsa bedroom ‘din ya zauna gefen gado hannayensa ri’ke da kansa da yake matu’kar sara masa, yana fata abinda yaji ya kasance mafarki ne, ba zahiri ba. Ammar ne ya auri matar da ya saki? Kafin yayi aune ya ji zubar hawaye akan fuskarsa, da gaske zuciyarsa ‘kuna take tamkar ta fito daga ‘kirjinsa don tsananin bugu, lokaci guda zuciyarsa Ta dinga hasasho masa rashin adalcin da aka yi masa. Gaba ‘daya wutar tsanar Ammar ta bijirowa zuciyarsa.

Kamar an mintsineshi ya mi’ke da sauri hannunsa ri’ke da takardar gwajin ‘kwayar halitta da aka yi masa, zuciyarsa na sake ‘karfafa masa gwiwar hasashensa gaskiya ne ko da ace Ammar ne mijinta to tabbas wannan yaron nasa ne hakan yana nuni da cikinsa Shatu ta auri Ammar. Tashin hankali! Ya fa’da a fili. Da sauri ya fita parlourn.

Ya kuwa ci sa’a har a lokacin ba su gama cin abincin ba. Ganinsa kawai suka yi ya shigo da hanzarinsa tamkar zai kifa ya kalli Ammar a zafafe yace “Duk wanda ya ‘daura maka aure da ita ka sanar dashi ya aikata haramun domin da ciki na ka aureta, kuma wannan yaron tun ‘dazu na kaishi hospital aka tabbatar min ‘kwayoyin halittarsa irin nawa ne.” Alhaji Baba sak yayi cikin mamakin furucinsa kafin yace. “Waye ya sanar da kai an yi masa aure da ita? ba ayi auren ba amma ana shirin yi nan kusa.” Wani abu ne ya fa’da masa wanda da ya tokare zuciyarsa, har sakin ajiyar zuciya yayi kafin cikin sanyin jiki ya dur’kushe murya a raunane yace “To don girman zatin ubangiji ku yi ha’kuri ku yafe min abinda na aikata na sakin da nayi mata wallahi sharrin shai’dan ne da na zuciya.. kuyi ha’kuri ku mayar min da matata.” Wani kallo Mommah ta watsa masa wanda ya ka’da ‘yan hanjinsa. Cikin matu’kar ‘bacin rai tace “Wallahi idan kaga Shatu ta komawa aurenka sai dai idan bana raye.” Wata irin razana da fa’duwar gaba Ta riske shi ya runtse idonsa gam, yana sake jiyo amon sautin Mommah, da ta cigaba da magana a zafafe “Shatun da ka wula’kanta ka tozarta, ka tsallake ka barta cikin ra’da’di da zafin rashin budurcinta, a ranar da ka hai’ke mata ka saketa sakin tozarci, ka ‘dauke matar so kuka shilla uwa duniya, Bayan ta haihu Hajiya Mama da kanta ta kira ka a waya ta sanar da kai haihuwar amma saboda kai isashshe ne ko magana ba ka yiwa Hajiya Maman ba sai message ‘din banza da ka turo..” Imran da sauri yace “Ni Mommah!” “Kai ‘din fa, ko ‘karya zan maka? Dama saboda irin wannan na ajiye evidence.” Ta ‘dauko wayarta ta bu’de message ‘din a ma’adanar ta ta sirri da ta ajiye shi. “Ko ba kai bane? sannan saboda ma kada a dameka sai ka kama duk numbobinmu kayi blocking, shima ba kai bane?” Wata irin zufa ce ta fara zubo masa bayan ya karanta message ‘din hawaye kuwa tuni ya fara tsere a fuskarsa, tunani yake yi ko dai an zuba masa wani abu ya sha da har ya yi wannan rubutun don dai wallahi ba shi bane itama Mommah da za tayi masa adalci ta san ba zai aikata ba. Amma zai tsaurara bincike akan hakan matu’kar kuwa ya samu Shaheedah ce da aikata irin wannan abun wallahi shi ka’dai ya san hukuncin da zai yi mata. Mommah ta cigaba da magana a zafafe “Saboda haka in dai ni na haifi Shatu na haramta maka aurenta, kuma don in ‘kunsa maka takaicin da ka ‘kunsa mana,Ammar zan aurawa ita.” Wannan karan ba Imran kawai ba har ta Shatu ‘kirjinta dakan uku-uku yake yi.

Idanunsa sun ka’da sun yi ja sosai ya ‘dago ya kalli Alhaji Baba murya a raunane yace “Don Allah ka bata ha’kuri na rantse da girman Allah ban san wa ya aikata haka ba, kuma wallahi ban san Shatu ta haihuba, kuma ba ni nayi blocking ‘din numbers ‘dinku ba hasalima nima ina yawan kira bana samunku.” Mommah tace “Ai na gama magana, su da kan su sun san nayi ha’kuri da abubuwan da ka dinga yi min, wanda har hawan jini suka saka ni, na san kuma iyayena masu adalci ne wannan abinda kayi ba zai sa su su sani janye furucina ba, ko bayan raina Shatu Ammar na yarda ta aura. Don haka ga sadakinsa.” Ta bu’de jaka ta ciro dubu maitan ta ajiye gaban Alhaji Baba. Cikin tu’ku’kin zuciya Imran ya mi’ke ko ganin gabansa baya yi. Ita kanta Shatu ‘ko’kari take sosai wajen danne damuwarta da tuni ta saka kuka gani take kamar abin yayi masa yawa. Kuma ta amince da gaske Imran bai san da haihuwar nan ba. Jikinta a salu’be ita ma ta mi’ke ta shige bedroom, Mommah ta bita da kallon mamaki.

Alhaji Baba ya saki ajiyar zuciya shi kansa yana cikin wani hali da bai san yarda zai warware cukurku’dewar al’amurannan ba, ya zubawa sadakin da Mommah ta ajiye idanu, a fili ya furta “Tir’kashi! Amma Dijah da zaki fahaimceni da kin bari anyi abubuwannan a hankali.” Da sauri ya kalleta ganin ta saka masa kuka “Don Allah kada ku goyi bayansa, alhali yayi abinda bai kamata a goyi bayannasa ba, sai yanzu da yaga matarsa ta kwara’be ita kuma wannan ya ga ta goge sannan zai lalla’bo yace yana sonta, ni na tabbatar son sha’awa yake mata Ammar ne yake mata zahirin so, please ko bayan raina Ammar na amince ta aura.” Daga Alhaji Baban har Hajiya Maman shiru suka yi sun ma rasa tudun dafawa.

Shatu kuwa tana shiga ‘daki ta sulale akan gado, tausayin Imran ne gaba ‘daya ya cika zuciyarta duk da ba tana nufin ta komawa aurensa bane, amma bata son Mommah ta cigaba da zafafa masa. Turowar ‘kofar da aka yi ne da ‘karfi ya sata ‘dagowa. Anty Nahna ta gani sam fuskarta ba rahma, ta ‘karaso a ‘dakin a zafafe tace “Mi’ke zaune Shatu.” A sanyaye ta mi’ke tana goge ‘kwallar da ta kwanta mata cikin idonta.
“Kada kice min kukan rasa Imran kike? Ko kuma kukan mutuncinki da Mommah ta kare? Cab da kuwa kin bani kunya na zata da ke za’a zage a ‘kwaci martabarki da mutuncinki, shine kika zauna kina kuka? Ba dai zuciyarki har yanzu tana son mutumin da ya gallaza miki a rayuwa ba? Da nace kuwa zuciyarki ba tayi miki halacci ba da kuma na kira ki da wacce ta rako mata duniya. Ki bu’de kunnenki ki ji abinda zan gaya miki da kyau, a yanzu ne zaki nuna wa Imran kuskurensa, a yanzu ne zaki ‘dandana masa guba irin wacce ya cusa miki, ki shayar dashi mamaki ki nuna masa kema mace ce Hamsha’kiya yanzu da ko ya sameki zai san mutuncinki da darajarki ba zai ce ya sameki a ‘bagas ba. ki nuna masa kin cika kin ri’ka kin tumbasa samun ki sai wanda ya shiryi. A zahirance ki nuna masa Ammar ne za’binki ko da a ba’dinance ba hakan bane. Kiyi gogayya da shi ki jashi a ‘kasa kada kuma ki sake ki bujirewa umarnin Mommah duk da ‘ko’karin kare martabarki da tayi, kiyi watsi da Imran ki kama Ammar shine ya dace dake. Kin ji mai na gaya Miki?” Shatu Ta ‘daga kai tana jin duk abinda Anty Nahna ta gaya mata shine gaskiya dole ta yakice soyayyar Imran ta yi wulli da ita matu’kar tana son siyawa kanta mutunci. Ta rungume Antyn ta Nahna tana sakin hawaye Na zallar samun nutsuwa.

Ammar kuwa tun da ya shige ‘daki ya kulle kansa ya da’de zaune dafe da kansa, yana jin zuciyarsa na suya, ina ma zai iya da ya sahalewa Imran matarsa, amma ina zuciyarsa ta kasa yi masa lamini soyayyar Shatu sake gauraye duk ilahirin sassan jikin sa take, baya jin zai iya rayuwa idan ba Shatu a tare dashi.

————
Lamarin Imran kuwa babu da’din ji, domin ya rasa mafita ya kuma rasa waye ya turo wannan sa’kon, zuciyarsa sunan Shaheedah ta ke Ta nana ta masa, hakan yasa a zafafe ya mi’ke. Dole ne ya nemo Shaheedah duk da sun koma barci amma asubanci zaiyi yaje ya tambayeta dalilin da yasa ta aikata haka.
Jirin da yaji yana ‘dibansa ne yasa ya tuna rabonsa da abinci tun tea ‘din da ya sha da safe, don haka ya mi’ke a hankali cike da ‘karfin hali ya nufi hanyar fita daga bedroom ‘din.

A kitchen ‘din take a tsaye tana ‘ko’karin dafawa Akram noodles da ya dameta da kuka. Jikinta sanye da Hijabin da tayi sallah da shi, fuskarta fayau ko powder babu, hakan ya saka idanunta fita dar dasu, dama ita tafi kyau ba makeup.

Jin ‘kamshin turarensa ya tabbatar mata shine ya shigo kitchen ‘din, don haka ta aro fuskar jarumta ta saka akan fuskarta, domin kuwa kicin-kicin tayi da fuska, tana zubawa Akram da ya isa wajensa harara tare da jawo shi da ‘karfi “Don gidanku matsa daga jikinsa saninka ma yayi da kake ‘ko’karin li’ke masa shashashan yaro kawai.” Kuka Akram ya fara yi yana ‘ko’karin ‘kwace hannunsa daga jikinta. Shi kuwa Imran sak yayi yana kallonta, yana son yi mata masifa amma yana shakkar kada ya sake cusa tsanarsa a zuciyarta. “Kiyi ha’kuri sabida ya zo wajena kika masa wannan fa’dan?” Wani tsaki taja kafin ta harareshi tace “Anyi masa ‘din ko kai ka haifa min shi?” Jikinta ya matsa sosai tamkar za su ha’de yana jifanta da wani irin kallo mai narka zuciya, cikin wata iriyar murya da tasa gaba ‘daya tsigar jikinta tashi yace “Idan ba ni na haifa miki shi ba amma ni na yi miki cikinsa, kuma cikin son ran ki da shau’ki.” Ta ja baya ha’de da ‘bata rai tace “Sai me don kai ka yi min cikinsa? Ai abu ne mai sau’ki kuma ko yanzu na yi aure wani ma zai min ciki na haihu.” Bai san lokacin da ya dam’ko ta ba cikin ‘bacin rai yana kallon cikin ‘kwayar idon ta da tayi saurin rintsesu saboda bata son idaninsa su yi mata tasirin da za ta kasa yi masa rashin kunya. “Ka cika ni.” Ta fa’da tana kicinyar ‘kwacewa saboda gaba ‘daya yayi kusa da ita tamkar ma rungumeta yayi “An ‘ki a cika kin sai kin sake fa’dar abinda kika ce yanzu, say it again.” Shiru tayi masa, hakan yasa ya samu wannan damar ya cugaba da magana cikin husky voice ‘dinsa. “Ba zaki Ta’ba auren wanda ya jiyar dake da’din da Na jiyar dake ba a first night ‘din mu, kada ki mance zafafan kiss da kika dinga aika min kamar dama ma jira kike Na zo, twins ka’dai sun isa ki shaida cewa ni ‘din gwarzon namiji ne, don haka ki taimaki kan ki kije ki sanar da Mommah ‘dakin mijinki zaki Koma, ni kuma in cigaba da jiyar dake da’di fiye da na wancan daren da ya gabata, Ayshatu na wallahi ina son ki, son da ni kaina bana yiwa kaina shi.” Tsaki ta ja duk da yanayin da ta tsinci kanta bai hanata yin furuci a zafafe ba “Kana so na? Yanzu da Na tashi daga fulanin daji Na tashi daga ‘kazama mai wari, wacce kake ‘kyama har kake gudun a kai ta gidanku, yaushe ka fara so na yanzu da Na zama educated da zaka iya shiga taro dani ba kuma zaka ji kunyar nunawa kowa ni ba a matsayin matarka, yaushe ka fara so na? Yaushe ka daina tunanin me zaka yi da ni? Lokacin da ka ‘dan’dani zumata ka gauraya da ni’imar da Allah yayi min shine kake ba’kin cikin Ammar shima ya ‘dan’dana ya ji ni’imata, ya samu tarin nutsuwa da baiwowin da Allah yayi min…” Da sauri ya sa tafin hannunsa ya rufe bakinta ruf cikin tsananin kishi yake furta “Ki fa’da min komai zaki fa’da amma please kada ki sake danganta kan ki da wani please Ayshatu forgive and Forget wallahi ina matu’kar son ki sai yanzu na fahimci dalilina na takura miki.” Hawaye ne kawai yake sauka daga idanunta, dalilin tuno wa’dannan abubuwan ashe Allah zai amshi addu’oin da take yi akan Imran? Dama bata haufi Ta san ubangiji mujibuddu’ai ne, amma yanzu lokaci ya ‘kure Mommah ta riga ta gindaya katanga mai ‘karfi tsakaninsu. Hannayensa masu tsananin taushi kawai ta ji a fuskarta suna goge mata hawaye, wani sanyi da nutsuwa suka zo mata ta lumshe ido, kafin a zafafe ta bu’de su ta kuma janye fuskarta, dole ta cusawa Imran tsanarta matu’kar tana so ya rabu da mahaifiyarsa lafiya tunda dai tace ko bayan ran ta bata amince su yi aure ba, cikin zafin rai ta shiga furta masa maganganu “Na tsaneka Imran, har abada kuma ba zan sake son ka ba ka riga ka cusa min tsanarka a zuciyata, ka fita a rayuwa ta Ammar nake so shi nake muradin Aure.” Sam bai san sanda ya jata jikinsa ba kamar magnet Lokaci ‘daya ya saki ajiyar zuciya yana furta “Ni kuma ina tsananin son ki ba mamaki son ki shine Ajalina I love you Ayshatu na and I really mean it…”

Turo ‘kofar kitchen ‘din da akayi ne yasa Shatu saurin zame jikinta, sai dai tuni idanunta suka sauka cikin na Ammar bata haufi ya riga ya gansu. A hankali ta furta ya salam!

Saduwar alheri.

Kamar yarda wasu daga cikinku suka bu’kaci a bu’de vip group, Alhamdulillah ‘korafinku ya kar’bu na bu’deshi akan farashin ku’di mafi ‘karanci daga 500 to above. Zaku dinga samun posting 2 times a day. Normal group kuma posting ba kullum ba. nagode da ha’din kan da kuka bani.

Da bazarku muke taka rawa!

[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

44

Da sauri Ammar ya ‘dauke idon sa ‘kirjinsa yana dukan uku-uku, tabbas ya yi mummunan gani da kuma ace ya san hakan zai ganin da bai shigo kitchen ‘din ba. Ya runtse idon sa yana jin tamkar zuciyarsa za ta buga.

Shatu kuwa a zafafe ta kalli Imran “Burin ka ya cika, ya ganni tare da kai, wanda direct zai iya zargin wani abu wallahi ban yafe ‘batawa masoyi na rai da kayi ba.”

Shi ‘dinma wannan karan takaici ya gume shi da sauri yace “Na ji da’di da ya gani, wa ya aike shi shiga gonar da ba tasa ba, ko an gaya masa bakin rijiya wajen wasan makaho ne, ai wallahi ka’dan ma ya gani matu’kar bai janyeba wata rana sai yaga abinda zai saka idon sa makancewa. Kuma wallahi duk ran da kika sake kiransa masoyinki ko mijinki a gabana sai na kusa cinye bakinki saboda sumbata, shine purnishment ‘din ki.” Daga haka ya juya da sassarfa ya bar kitchen ‘din, saboda matu’kar zai cigaba da ganinta a hakan zai iya wuce gona da iri. Wani irin feeling yake ji na tashin hankali, wanda ya da’de bai samu kansa a wannan yanayin ba.

Shatu ta bi bayansa da kallo, ita kanta gaba ‘daya jikinta a mace yake, rungumar da ya kai mata a bazata ta haifar mata da kasala, ta tayar mata da duk wata kwantacciyar sha’awarta, ta runtse ido tana sake sha’kar ‘kamshin turarensa da ya gauraye jikinta gaba ‘daya.

Ammar da Ta tuna ya sata fita da sauri, da nufin taje ta fahimtar dashi kada ya ‘dora zuciyarsa a bigiren zargi.

Ta da’de tana knocking a ‘kofar bedroom ‘din kafin ya amsa murya can ‘kasa “Yes come in, a bu’de take. Ya fa’da yana mi’kewa da ‘kyar daga kwanciyar da yake, idanunsa sun ka’da sun yi jazur.

Jikinta a sanyaye ta shiga cikin ‘dakin, idanunta a ‘kasa tana wasa da fingers ‘din ta. Ammar kuwa idanunsa a kanta yana tuno a yanayin da ya ganta a jikin Imran, ga ‘kamshin turarensa nan ya baibaye jikinta don daga shigowarta bedroom ‘din ya na’de ‘kamshin turarensa, duk da zuciyarsa a zafafe take cike take da kishi, hakan bai hana shi sakar mata murmushi ba, yana yi yana kawar da ‘bacin ran da yake fuskarsa. “Welcome Amarya ta, shigo mana ki zauna.” Ya nuna mata kujera. Babu kuzari sam ta zauna har a lokacin idanunta a ‘kasa. Kula da ya yi ta kasa sakewa ya sa shi cewa “Ko baki zo ba dama ina da niyyar kiran ki, maganar lefe ki ba ni sizes ‘din ki idan kuma kin fi son ki siyo da kanki then sai na baki ku’din under wears ‘din ku siyo da su Hafsa, tunda na ji sun ce kanon za su bi mu.” Da sauri ta girgiza kai “Ka siyo kawai, zan turo maka sizes ‘din ta whatsapp, amma don Allah kayi ha’kuri da abinda ka gani ba wani abu muke ba….” Da sauri ya dakatar da ita “Ban shirya jin komai ba, na fahimci abin da yake nufi shi yasa ma zan fara shirin bikin gadan-gadan, don ya fahimci da gaske nake ba gudu ba ja da baya, idan ma tunaninsa zan ha’kura na bar masa ke, ba zai yiwu ba.”

Shatu kasa cewa komai tayi illa cigaba da jan zaren mayafinta da Tayi, har a zuciyarta ba haka ta so ba so tayi Ammar ya janye ya ha’kura. Amma ba yarda ta iya dole ta mi’ke ta fita daga bedroom ‘din Ammar ya bita da kallo yana sakin ajiyar zuciya.

——————-

A ranar Imran ya juya zuwa kano so yake ya je ya think tsiye Shaheedah ya gano gaskiyar lamari, idan kuwa ya tabbatar ita ce ta ha’da kitimurmurar nan tabbas zai gwada mata zahirinsa. Ta jirgi yabi kuma tare da Akram da ya ma’kale masa ya tafi, ita kuwa Ikram ko kallonsa ba ta yi.

Ba tare da ya sanar mata zai dawo ba, zuwan da ake kira zuwan ba zata. Suna zaune ba je da kayayyakin da Shuwa ta kar’bo musu wajen yawon bin malamansu, ya tura ‘kofar side ‘din Anty Amaryar ya shiga. Ganin yarda suka razana ne daga ganinsa ya tabbatar masa akwai wani abu da basa so ya gani. Yana shigowa idanunsa ya sauka akan wata laya da aka gar’kamawa kwa’do (padlock). Gabansa ya fa’di, yayi excusing ‘din su bai kuma fasa shiga ba.

Zama yayi akan kujerar da take fuskantar Anty Amarya, idanunsa cikin na shuwa da take shirin juya tunaninsa “Kina ji ko Shaheedah dole sai an tashi tsaye, wannan ramar taki akwai mutanen ‘boye don haka na kar’bo miki magungunan nan kada ki sake ki yi wasa dasu.” Imran cikin mamakin matar ya zura hannu a aljihu yana mi’kewa kamar zai wuce sai kuma ya saka hannu ya ‘debe tarkacen da suke gaban Shuwa. Gaba ‘daya ji su kayi kamar su zunduma ihu, yana murmushin rainin hankali yace “Bari ni zan adana mata su,
na san ta sarai da wasa da magani ni kaina ramar tata tana damuna ashe mutanen ‘boye ne?” Daga haka yasa kai ya fice ‘dauke da Akram a kafa’da.

Ba Anty Amarya ba har ta Shuwa sai da ‘yan hanjinta suka ka’da saboda gaba ‘daya magungunan da bayaninsu a ciki, gudun kada ta manta yasa ta rubuta, da kuma sunayen mutanen da maganin zai yiwa aiki, hakan yana nufin Imran yana gani zai san inda maganin ya nufa. Shaheedah kawai hawaye ta ji yana zubo mata ta tabbata ta ta ta ‘kare.

Shuwa da sauri ta dubeta “Ki mi’ke kije tun kafin ya bu’de ki san dabarar da kika yi masa kika kwashe. Ai kuwa ba shiri Shaheedah ta mi’ke har da gudunta.

Sai dai ina addu’arta bata amsu ba, wannan ranar, yau dai kam Allah ya toni asirin su.

A parlourn ta tarar dashi hannunsa ‘dauke da layar nan da sunanta da nasa ya fito ‘baro-‘baro. A takardar kuma an rubuta yarda za tayi amfani dashi ta mallaki zuciyarsa. Saura duk kayan ‘kazanta ne har da wanda da jinin haila zata ha’da. Wata irin tsanarta ta ziyarci Imran fiye da wacce yake mata. Ya runtse idanunsa yana son ‘daukar action amma yana tunanin gwara ya bari ya gama ‘kunsa musu takaici, bari ya nuna musu bai fahimci komai ba, ya ga iya gudun ruwansu. Ajiye kayan yayi a gefe yana jifan ta da murmushin da na dole ne ya aro ya yafa a fuskarsa. Ya tura mata kayan yana ta’be baki “Zo nan ki kwashi kayannan ki adana su amma please kada kiyi wasa dasu kin ji ance maganin jinnu ne.”

Wata kyakkyawar ajiyar zuciya Shaheedah ta saki tana hamdala a zuciyarta da bai gane ko meye ba da sauri ta ‘debe kayan, ta kai su ta adana su. Sannan ta dawo gefensa ta samu ta zauna, ya ji kamar ta jona masa wuta, amma haka nan ya daure yana kallon Akram da ya fara alamar barci ko yunwa. Itama ido ta zubawa Akram ‘din kafin tace “Wai a ina ka samo mana yaro mai kama da kai?” Mamaki ya kusa kashe Imran daga zaune, na zallar rainin hankalin Shaheedah nufinta bata son ‘Dansa bane ko me? Direct ya amsa mata da “Jikan Mommah ne.” Jikin ta ne ya sanyi, tsoron kada ya jefo mata tambaya ya sata saurin mi’kewa “Allah ya raya shi, bari in je in samo maka abinci.” Har ta kai ‘kofa ta ji yace “Ki bar abincin nan za muje eatery mu ci nagode.” Jikinta a salu’be ta fita jin yace ba zai ci abincin ba, ta fara tunanin ko dai ya ganeta ne ya bagarar da zancen, amma anya kuwa da ya ganeta ai ba zai ‘kyaleta ba, da tuni ya ‘dau mummunar hukunci.

Tana shiga Shuwa ta tarbeta “Yaya? Allah yasa dai bai gane ba.” Shaheedah ta ta’be baki “Gaulan babu abinda ya gane. Ya ma bani magungunan na kwashe abi na, kuma a yau zan fara amfani da su.” Suka saki ajiyar zuciya gaba ‘daya. Shuwa ta ‘dauko ‘dayan maganin Ta mi’kawa Zainab “Kin ga wannan maganin shi ake kira manta uwa, na farra’ku ne tsakanin Hajja da ‘danta don kuwa mutumin nan ya tabbatar min matu’kar ba farra’ku aka yi musu ba aikin da ake son ya kama manga ba zai kama shi ba,
Sai an cusa wa Hajja tsanar Manga ta daina tunawa da shi a addu’a sannan zai ci shi. Don haka ki kula, cikin dare ake so ki fita da ‘daurin ‘kirji ki yi ha’ka ki birne kina yi kina ambatan sunan mijinnaki da na uwarsa.” Zainab cikin farin ciki ta amsa tana zabgawa Shuwa godiya, gani take ko uwar da ta kawo ta duniya bata sonta kamar yarda shuwa take son ta, ta yarda da hakan har cikin ranta.

——————————

Kashe garin sadakar bakwai suka dawo, nan fa Ammar ya fara sakin ku’di ana ha’dawa Shatu lefe, a tsukun wannan lokacin sam Imran hankalinsa ba a kwance yake ba, dauriya kawai yake da ‘karfin hali, ga shi ya tsaurara bincike akan Shaheedah da iyayenta musamman Shuwa, duk wani takun ta ya sani, burinsa ya samu hanyar da za su tonawa junansu asiri da kansu, ba tare da wani ya shiga cikin lamarin ba.

Yau ma bai gaji ba a bedroom ya samu Mommah, da niyyar sake bata ha’kuri kamar yarda ya ‘kwallafawa kan sa kullum. Mommah Ta ‘dago ido tana kallonsa “Ba zan gaji da ce maka na ha’kura ba, amma batun na sake aure maka shatu ne babu shi, Shatu bata da miji sai Ammar don haka kada ka sake zuwa min da wannan zancen na gaya maka.”

Idanunsa jazir ya mi’ke ya tafi ‘d’aki zuciyarsa cike da ‘kunci ya zauna dafe da kansa yana tunanin mafita, idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kai shi dare, a yarda ya ji suna shirye-shirye auren ba zai fi sati uku ba, hakan na nufin yana ji yana gani Ammar zai yi winning a kansa. Ina! Ba zai yiwu ba.

Da sauri ya ‘dau wayarsa ya shiga danna kiran Ammar, murya a cunkushe yace “Kana ina?” Ammar sai da yayi jim sannan yace “Ina tare da Shatu, wani abu ne?” “Ka sameni a bedroom ‘dina akwai maganar da za mu yi da Kai.” Ammar shima murya a cunkushe yace “Okey” ya ja gwauron numfashi yana duban Shatu “Ina zuwa ki shiga gida idan na dawo za muyi magana.”

A tsaye ya sameshi yana struggling a bedroom ‘din nasa. Ammar yayi sallama a karo na uku kafin ya amsa da alama yayi nisan kiwo a tunani.

Fuskar Ammar a ‘daure yace “Ga ni.” Imran ya ja numfashi kafin yace “Na gan ka, yanzu Ammar kana tunanin abinda kayi, kayi min adalci a matsayi na na brother ‘din ka ciki ‘daya? We are siblings fa.” Ammar ransa a ‘bace yace “Me nayi na rashin adalci?” “Auren matar da ‘dan uwanka ya saki.” Ya ba shi amsa a zafafe. Shima a masifen yace “Hakan ya haramta ne?” Cikin takaici da kallon baka da hankali Imran yace “Idan bai haramta ba, ka san dai ana barin halak don kunya, kai yanzu ba zaka ji kunyar su Akram su girma suga ka aurewa uban su mata ba, da wani ido zaka kallesu? Ina raye ka aure min mata saboda son zuciya. To I warn you for the last time ka fita daga harkar mata ta.” “Idan na ‘ki fa?” Wani murmushin takaici Imran yayi kafin yace “Dole ma zaka yi ko da tsiya ko da arziki, ka bawa Mommah shawara kada ta ‘kulla gabar da ba’a san ‘karshenta ba. Me Za ku sanar da ‘ya’yan da zaku haifa, na baka shawara idan kunne ya ji jiki ya tsira.” Ammar ya ta’be baki kafin yace “Sai dai idan kashe ni zaka saka ayi, amma ba zan bar ta ba ni na saka ka sake ta?”
“Okey kada ka sake ta je ka ka aureta.” Ya fa’da yana sakin murmushin takaici.
Ammar ya juya ya fice a zafafe.

————————-

‘Karfe 3:00 na daren ta mi’ke daga gadonta, bayan ta yi ‘daurin ‘kirji ta fito a hankali daga ‘d’akinta. Ta bu’de ‘kofar da zata sada ka da baya ta cikin parlournta.

Tana isa wajen da sauri ta hau waige-waige, ganin ba wanda ya ganta ya sata ‘ko’karin ha’ka ramin da zata burne layar, tana gama ha’kawa ta ciro layar tana ambata suna da ‘dan ‘karfi ta zura layar a ramin. Dai-dai lokacin da hasken flasherr waya ya dallareta da sauri ta juyo, lokaci ‘daya ta razana zata saka ihu. Cikin wata irin murya yace “Kada ki fara Zainab, Yau Allah ya toni asirinki, ha’ko abinda kika birne…….

Ga masu son biyan ku’din vip group inda za ku dinga samun posting biyu a rana ga account number.

2118666253 U B A

Sai tura shaidar biya ta wannan layin

08033748387

Nagode da ‘kaunar da kuka nuna min jiya kam na ga masoya na!
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me zan yi da ita?

45

Gabanta ya shiga dukan Tara-tara, bayan Ta d’ago ta yi arba da Dahda a tsaye idanunsa cikin nata, ran sa a matu’kar ‘bace yana mata wani irin Kallo. Ya zura wayarsa a aljihu bayan ya yi saving vedionta da ya d’auka. Bai ce mata komai ba ya juya ya bar wajen.

Ji ta yi kamar ta dur’kushe a wajen ta saka ihu, shikkenan dubunta ta cika bata da wata hujja da zata kare kanta.

Dahda kuwa tunda ya koma bedroom ya kasa barci,hakan ya saka shi tashin Mommah ya ce ta d’auro alwala su yi sallah. Mommah ba tare da ta san dalili ba ta cika umarninsa kasancewar dama ta saba irin wannan lokacin sallahr ta ke yi.

Dahda ya da’de a sujjada ya na godiya ga Allah da ya bayyana masa wacece Zainab. A kuma daren ya rubuta mata takardar saki cikotan guda biyun da suka rage, ya tura vedion cikin system ‘dinsa saboda ya zama shaida a wajen Hajja, duk da ba yanzu zai gaya mata ba sai ya sake ‘kwakkwaran bincike akan lamarin Zainab.

Tun a daren Zainab ta ke kuka, ta shiga kiran Shuwa domin ta sanar mata aiki ya riga ya kwa’be, amma Shuwa bata d’aga ba tana can ta na sharholiyarta, duk da ta ga kiran tsaki ma ta ja ta kife wayar ta na cigaba da aikata bad’ala, a zuciyarta fad’i take na gaji da matsalarki zainab ba akan ki zan ‘kare ba, ina ga ma yanzu na daina miki wani aiki kud’inki zan fara ci haba ina dalili?

———————————

Mommah ganin Dahda sukuku ya tashi hankalinta, hakan yasa ta sak shi a gaba da tambaya, jan ajiyar numfashi ya ke yana fad’in bakomai ki bari akwai lokacin da za ki ji, tabbas Lamarin d’an adam abin tsoro ne a dai tsukun lokacinnan ki dage da addu’a da azkar kawai shine abinda zan ce miki.” Shiru ta yi tana kallon cikin ‘kwayar idonsa tace “Allah ya jishshemu alheri, dama zancen gidan Ammar zan maka ya ce muje mu gani an kammala gini. Kuma ka ga bikin ‘karatowa ya ke ya kamata na shiga Abuja akwai shirye-shiryen da za mu yi, Hajiya Mama ta ce na mayar da Shatun can saboda a had’ata da ‘yan uwanta a fara musu gyaran aure.” Dahda ya ce “Ni kuwa da ina son mu yi shawara, ko dai Ammar zai jan ye ya barwa d’an uwansa matarsa wallahi Dijah bana son rabuwar kan yarannan su biyu fa kad’ai Allah ya bamu.” Mommah ta girgiza kai “Kada mu yi haka da kai Dahda, ka bari na koyawa Imran hankali, idan za ku yi la’akari da abubuwan da ya aikata bai fa kamata ku goyi bayansa ba, kun ce gaba ma ya sake yi kenan, yara kuwa ba su kad’ai Allah ya bamu ba ga Ikram da Akram nan an haifa mana.” Dahda ya girgiza kai “Allah ya sanya alheri yasa kuma za’a yi damu, kin tabbatar ita yarinyar ta amince da za’bin na ki?” Momma ta jinjina kai “Ta amince tuni shine ma dalilin da yasa na zo maka da zancen ka yi musu addu’ar fatan alheri kawai.” “Allah ya tabbatar da alheri.” Dahda yace yana mi’kewa da key a hannunsa “Bari na je na ga gidannasa, idan akwai abin da bai yi ba a gyara tun wuri, sai ki yi wa masu furniture d’inta da aka bawa su siyar da nata na gidan Imran magana, su samo mata latest design idan da ciko sai ayi musu.” Cikin farin ciki Mommah ta ce Allah ya saka da alheri Dahda ya ‘kara arziki.” Ya amsa da ameen yana ficewa da sauri.

A bakin part d’in ta ya ganta a tsaye da sauri ta sha gabansa ta dad’e ta na dakon jiran fitowarsa. Yana ganinta ya d’aure fuska tamau ya ce “Zainab matsa na wuce ba na son rashin arziki.” Kuka sosai ta sakar masa ta na jan hannunsa zuwa cikin part d’insa.

Gaba d’aya ta zube a gabansa “please Dahda ka yi ha’kuri wallahi sharrin shaid’an ne.” Cikin masifa ya ce “Shi shaid’an dama kullum a cikin sharri ya ke ai, ki tashi tsaye in dai nine ba abinda zan miki na bar ki da duniya ta koya miki hankali.” Wani fariciki ya ratsa ta ashe dai da gaske Shuwa ta ke da ta ce ba da abinda zai iya yi, an riga an kulle bakinsa. Farin ciki ya sata su’butar baki da cewa “Aikin ki ya na kyau Shuwa.” Da sauri ta toshe bakinta ta na kallon Alhajin da sarai ta san ya ji abinda ta ce, amma ga mamakinta sai bai ce komai ba, alamar ya zama mijin ta ce d’in dai da gaske.
Juyawa ya yi ya fice a ransa ya na mata dariyar mugunta saboda shi kad’ai ya san gadar da ya shirya mata. Ita kuwa tsalle ta sa ka har da juyi cikin ‘karaji ta ke kiran Shuwa ta na fad’in “Alherin ubangiji ya kai miki aminiya ta gari.” (Allah ya shiryi ma su hali irin na wad’annan bayin Allahn, Rabbi ya kare mu daga tarkon su)

———————-

Bayan kwana biyu, da zancen da Mommah su ka yi da Dahda, tuni ta shirya tafiya da Shatu Abuja ita da su Nahna da suka gama hutun su.

Imran bai san da tafiyar ba ya na zaune a parlour abin duniya yayi masa zafi ya rasa yarda zai yi, ya ji Mommah na yiwa Ammar magana ya samo musu ticket na Abuja a kashegarin ranar za su tafi.

Lumshe idonsa ya yi ya na jin sautin bugawar zuciyarsa yana sauyawa, da gaske dai idan bai yi wasa ba wankin hula ya na nema ya kai shi dare, Shatu na neman kufce masa. Tunda a kwana biyunnan Mommah ta hana ta ma ganinsa, kullum ta na ma’kale da ita, ya sha aika Akram da short note amma yaron ya dawo cikin gwarancinsa ya ce Mommah ta yaga.

Da kyar ya mi’ke yana layi ya nufi d’akinsa. A can d’in ma ba ta sauya zani ba mafitar dai ya ke nema, zuciyarsa ta yi cak tare da tunani, ba ‘bata lokaci ya amince da shawarar da zuciyarsa ta ba shi, idan ba hakan ya yi ba, Mommah ba zata san annabi ya fakuba.

Cikin daren ya mi’ke, bayan ya tabbatar zuwa wannan lokacin kowa yayi barci, ya nufi bedroom d’in Shatu, ya kuwa ci sa’a ‘kofar a bud’e take. Da sauri Shatu Ta d’ago ta na kallonsa dama kasa barci ta yi tunaninsa ya bun’kasa a zuciyarta. Ware ido ta yi ta na
Masa kallon mamaki “Ya Imran mai ka zo yi min cikin darennan? Past 2:00 fa?” Wani kallo ya hurgeta da shi Allah yasa da hijab a jikinta don kuwa daga ita sai satin sleeping dress, muryarsa a cunkushe ya ce “Sace ki na zo yi.” Ya hau gadon gadan-gadan cikin wani irin yanayi Shatu ta so saka ‘kara, tuni ya dam’keta “Wallahi ki ka yi min ‘kara anan zan aikata koma me na yi niyya. Kina ji kina gani ana shirin raba mu alhali na san kema kina so na kunya da kawaici ya hanaki fad’a kika bar bi ni kad’ai ina ya’ki, to ki bud’e kunnenki ki ji, sharad’i zan baki guda uku! Na d’aya ki amince mu je wani wajen a d’aura mana aure mu gudu mu bar gida, ko kuma a yanzu na aikata zina dake idan ya so naga uban da zai d’aura miki aure ba ki yi istibra’i ba……..” wata irin fad’uwar gaba ta riski Shatu a zafafe tace “Idan na ‘ki fa?” “Dole ma ki amince don a shirye na zo ba ta yarda za’a yi ina ji ina gani a d’aura miki aure da wani ba ni ba za’bi ya rage na ki….”

Saduwar alheri lahadi insha Allah kun san bana typing asabar ina godiya mutanena na vip. Allah ya bar so da amana.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita

46.

Wata irin bugawa zuciya ce ta risketa, lokacin da ta ji ana buga ‘kofar d’akin, shi kansa bai san sanda ya bud’e ido ba, da azama ya mi’ke yana neman wajen ‘buya.

Shatu da sauri ta ja hannunsa jin ana sake buga ‘kofar wannan karan da d’an ‘karfi, toilet ta tura shi ta jawo ‘kofar da sauri, zuwa lokacin har wani gumi ya yanko mata duk da sanyin a’cn da yake d’akin.

Tana bud’ewa taga Hafsa a tsaye ri’ke da kanta, Ta d’an matsar da ita gefe “Matsa Shatu barci nake ji kamar na kifa, waccan ‘yar rainin hankalin ta hanani barci, wallahi Nahna akwai ba’kar muguwa.” Cikin wata iriyar razana Shatu tace “Tashin hankali anan za ki kwana?” Da sauri Hafsa ta kalleta, tana nazarinta sai ta lura kamar tana ‘boye wani abu saboda yanayin yarda fuskarta ta nuna, Hafsa ta ce “Anan zan kwana is there any thing wrong?” Da sauri Shatu ta girgiza kai cikin matu’kar firgita, ta bata hanya ta wuce.

Jikinta a sanyaye ita ma ta bi bayanta hantar cikinta na kad’awa da kuma fargaba da tsoron kada Hafsa tayi katari da shi bata san wace iriyar amsa za ta bata.

Allah-Allah ta ke barci ya kwashe Hafsa ta samu ta bud’eshi ya fito,
Sai dai har zuwa lokacin Hafsan ba tayi barci ba tana dai kwance kanta yana sara mata.

Shi kansa da yake cikin toilet d’in hankalinsa a tashe ya ke, duk wani sound d’in maganarsu a kunnensa suka yi shi, it means kenan kwanan toilet ya kama shi, ya juya ya dubi toilet d’in duk da neat yake and clean ba ya jin zai iya kwana sur a cikinsa. Idanunsa ya kai kan windown toilet d’in ya ga ‘karami ne sosai ba ta yarda za’ayi ya iya fita ta cikinsa. Tsaki ya ja sosai ya tabbatar da maganar hausawa da suka ce idan ba ka iya mugunta ba ba ka yiwa kanka ba yanzu ya zai yi ya ku’buta daga tarkon da ya tsunduma kansa. Tur’kashi! Ace Mommah ta wayi gari a ganshi a bedroom d’in Shatu ai shikkenan kashinsa ya bushe ya kad’e kuma har ganyen sa.

Hafsa na daga kwancen ta zaro waya ta duba lokaci past 2:00 am, ido ta zubawa Shatu kafin ta ce “Ke me ya hanaki barci?” Shatu da ta lula duniyar tunani bata ji me Hafsan ta ce ba har sai da ta ta’bo ta kuma ta sake maimaita mata, a murya a d’ashe ta ce “Dama ina samun sleepless ban san me yasa Ba.” Hafsa ta ta’be baki kafin ta ce “Saboda kina tunanin Imran mana kin kuma kasa fitowa ki gayawa Mommah gaskiya, ke mijin ki kike so kin bari kuna wahala da soyayyar juna, ni wallahi ban ga dalilin wannan kwamacala da Mommah ta ke shirin had’awa ba na yi mata magana ta kasa fahinmta, na kuma lura Nahna ce ta ke zuga Ta.” Shatu shiru ta yi mata kawai, saboda ita ba wannan zancen ta ke so ba, so ta ke Hafsan ta yi barci Imran ya samu ya fito daga toilet. “Ta shi ki yi light off bana iya barci da haske, kema kuma ki kwanta ki runtse idon ki kina karatu a zuciyarki za kiyi barci.” Shatu ta bi yarda tace ta kwanta ta runtse idon ta tana saurarar karatun da Hafsan ta saka mata, cikin hukuncin ubangiji barcin mai nauyi ya d’auketa. Hafsa ta bita da kallo zuciyarta cike da tausayinta ta tabbatar soyayyyar Imran ce ta ke d’awainiya da ita. Har ta rufe ido za ta yi barcin sai ta ga kuma gwara ta yi alwala ta yi sallah ta ro’ka musu Allah sassauci a zuciyar Mommah.

Direct toilet d’in ta nufa, Ba tare da wani sound na tafiya ba, saboda kada ta tashi Shatu, shi yasa Imran bai ji tahowarta ba balle ya yi locking toilet d’in. Ta murd’a da sauri kawai ta afka kanta ciki.

A tare wata irin fad’uwar gaba ta riskesu, Hafsa da Imran, har Shatu da ta farka jin sound d’in bud’e toilet, da sauri ta d’ora hannu a kai, shi kuwa Imran runtse idanunsa ya yi cikin wani irin takaici da dana sanin biyewa son zuciyarsa. Yanzu mai zai cewa Hafsa ta fahimci ba abinda ta ke zargi suke aikatawa ba? Babu! Direct zuciyarsa ta bashi amsa.

Hafsa kuwa wani irin sanyin jikine ya rufeta da tashin hankali lokaci guda. Kafin ta ja jiki ta jingina da bango sabods jirin da ta ji yana neman kada ita, cikin wata iriyar murya tace “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna! Imran mai zan gani haka?”

Hannunsa na rawa ya kama hannunta cikin ‘karfin hali ya ce “Look Hafsa Ba abinda ki ke tunani bane, wallahi ba abinda mu ke aikatawa.” Cikin takaicinsa ta watsa masa kallon banza kafin ta ce “Kada ka gaya min maganar banza Imran, ban gane ba abinda ku ke aikatawa ba, me ka ke yi a toilet d’inta? Kuma tun wani lokaci ku ke aikata bad’alar?” “Hafsa kada ki saka zato a ran ki, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ne, wallahi ki yarda ba abinda mu ke aikatawa.” Tsaki ta ja “Ko Qur’ani za ka bani na dafa ba zan yarda da wannan tatsuniyar ba, wallahi ka bani mamaki Shatu ce fa ‘kanwarka marainyar Allah ita kake lalata da ita a cikin gidanku, matar da d’an uwan ka ya ke shirin aura shin ka yi masa adalci? Dole Mommah ta sani saboda dole sai ta yi istibra’i kafin a d’aura mata aure.” Ganin Shatu kawai ta yi a gabanta “Don Allah Anty Hafsa ki rufa mana asiri wallahi ba abinda ki ke zato bane magana muke da ya ji knocking mun zata Mommah ce shine ya shige toilet.” “Rufe min baki kafin na doke bakin ki, magana ku ke? Magana cikin tsakiyar dare kuma a d’akin ki? To maganar me kuke, ko ‘karamar yarinya ce ta ganku a haka ba zata yarda da wad’annan tatsuniyoyinnaku ba, ina shigowa na ga alamar rashin gaskiya a tare da ke, dama ance rana dubu ta ‘barawo, Yau Allah ya toni asirinku, kuma wallahi ba zan rufa muku asiri ba.” Hawaye ne ya ‘ballewa Shatu bata san sanda ta kalli Imran ba cikin kuka ta ce “Ka cuce ni Ya Imran.” ‘Bacin ran sa ya bayyana ‘karara da har kana iya gani akan fuskarsa, ya zubawa Hafsa wani kallo kafin ya fice da sauri daga d’akin.

Ai kuwa yana fita Hafsa ta juya kan Shatu ta shiga surfe ta “Namijin ki ka bawa yarda har haka, kin cuci kanki Shatu, Shi duk abinda ya yi ado ne sa’banin ke da zai goga miki ba’kin paint, ki sanar da ni gaskiya me ya yi miki da ya shigo?” Kuka ta ke sosai tace “Bakomai Anty Hafsa.” Wani banzan kallo ta yi mata tace tatsuniya kenan kada ki fad’a bari na tara muku jama’a tukunna sai ki magantu Allah ya kaimu safe.” Zubewa Shatu kawai ta yi akan tiles d’in da yake toilet d’in ta ri’ke kanta da ya ke matu’kar sara mata ta rasa dalilin da yasa Hafsa ta kasa mata uzuri ta kuma yarda da cewar ba abinda suke aikatawa. Yanzu gobe mai zata ce da Mommah da sauran mutanen da Hafsa ta ke i’kirarin sai ta gayawa? Take zuciyarta ta bata amsa fa Babu! Ba wanda zai yarda ba abinda suka aikata, a fili ta furta “Hasbunallah!”

Har asuba barci ya gagare su ba ita ba Hafsa ba ba shi kansa Imran da yake d’akinsa ba, zuciyarsa cike da matsanancin tashin hankali, shi ba ya jin takansa mutuncin Shatu kawai yake yi wa, don ta shi bai ‘ki hakan ya faru ba idan ya so ayi uwar watsi dole a bashi matarsa idan Mommah ta ji yana bin d’akinta cikin dare. Don shi kam a nasa tunanin gaba ta kaishi matu’kar wannan ne dalilin da za’a dawo masa da matarsa.

Da sassafe suka yi shirin tafiya Abuja, Shatu wanka ta yi kawai ta zira riga idanunta sun kumbura alamar bata samu barci ba, ga kuma kukan da ta sha.

A dinning suka zauna don su yi breakfast su wuce, tana fitowa Mommah ta zuba mata ido tana mata kallon tuhuma “Shatu lafiyarki kuwa? Kin kalli idonki a mudubi?” Ammar ya d’ago yana dubanta, cikin tashin hankali yace “Me ya same ki?” Hawayen da ya zubo mata ta saka handkerchief ta d’auke, ta amsa musu da muryar ta da ta dashe “Bakomai bana jin dad’i ne.” Mommah ta girgiza kai tana mamakin zuciya irin ta Shatu
Da ta ke manta sharri ta sani sarai soyayyar Imran ce ke wahalar da ita, sai dai ita ba zata amince ta komawa Imran ba tunda ita bata san ciwon kanta ba ita Ta sani. “Allah yasa bakomai d’in, sai ki hanzarta ki sha tea kada muyi missing flight.” A hankali tace “Azimi nake” idanunta akan Hafsa da tayi kicin-kicin da Fuska. Mommah murmushi ta saki tace “Allah ya bada ladan azimi ya sanya a mizani, amma shi azimin na menene? Da ake yinsa ranar talata.” Hafsa tace “Kika sani ko zunubi ta tafka ta ke neman yafiyar ubangiji, wani zunubin ai saboda girmansa sai an had’a da azimi domin neman yafiyar ubangiji.” Wayar da ta ke hannun Shatu ce ta zame ta fad’i, dalilin yanayi jikinta da ya hau ‘bari jin Hafsa na niyyar tona musu asiri. Fitowa Imran ce yasa suka yi shiru. Mommah ta dubeshi shima dai idanunnasa irin na Shatun duk sun kumbura dalilin rashin barci. Ta amsa gaisuwarsa tana ta’be baki, a zuciyarta tace kad’an ma ka gani sai kaji ana gud’a ana an d’aura sannan ne zaka san ka yi rashi kaje ka ji da ‘kanjamammiyar matarka. “Ku tashi mu je Imran ya saukemu tunda ya fito.” Ta fad’a tana kallon Ammar don dashi za’a tafi. Suka mi’ke kuwa gaba d’aya sai ji tayi Imran yace “Ni ma Abujar za ni.” Mommah ta juyo tana masa wani duba kamar ta yi dariya sai kuma tace “Ni fa bana son shashanci shikkenan ita kuma matar taka sai ka tsallake ka barta, dama yau-yau ku shirya ku koma gidan ku, ban ga dalilin da zaku tare mana a gida ba, tunda kun bar turkeyn.” Mommah ta fad’a a zafafe. “Aiki an je yi.” Ya fad’a yana jan trolley. Har ya kai ‘kofa Mommah tace sai ka tsaya ka sha ko tea ai.” Direct yace “Azimi nake.” Dariya ta kama Mommah ta guntse ta tace “Allah ya bada lada.” Nahna kuwa dariyar ta tayi sosai ta ce “To ko dai yau d’in wani special day ne a islam da ake azimi mu ba mu sani ba.” Ji suka yi kawai Ammar ya saki wani dogon tsaki.

—————————-

A parlour duk suka zube bayan isarsu Abujan,banda Imran da ya shige part d’in Hisham saboda kansa da yaji yana sarawa, musamman ganin an fito da lefe ana ta kallo ciki har dana Shatu da na Ammar, alamar da gaske dai an yi masa fashin mata ‘kiri-‘kiri, ya zama dole ya nemi malamin musulunci ya kai ‘kara.
Nan aka shiga tsare-tsaren Biki, banda Hafsa da ta ja gefe cikin tashin hankali, tana tunanin ta yarda zata fara gayawa iyayenta abin da ta ci karo da shi a daren jiya, tabbas gwara ta gaya musu don a san abin yi.

‘Karfe takwas na dare suke zaman cin abince har da Alhaji Baba, Imran ma ya fito, don burinsa yaga Shatu ko zuciyarsa za tayi sanyi daga tafasar da take masa.

Fuskarsa ba annuri ya zauna a gefen Alhaji Baba.

Sai da aka gama cin abincin sannan Hafsa Ta d’ago kanta ta gyara zama tace “Assalamu alaikum, don Allah ina son ku bani hankalinku akwai maganar da zan yi dangane da abinda ya faru a daren jiya………
Shatu da Imran suka zubawa juna ido cikin tsananin bugun zuciya.

Saduwar alheri

Masu son vip group inda nake posting safe da dare su biya 500 kacal ta wannan account d’in….

2118666253 U B A

Idan an saka sai a tura shaidar biya ta wannan numberr

08033748387.

Nagode biya ka huta takaicin ka samun postin akan kari safe da dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button