Hausa Novels

MARYAMA HAUSA NOVELS COMPLETE

💫MARYAMA💫

Related Articles
        BY

ASMA’U A.I MAI ANGUWA

(Ummu Fadeela)

Typing.📲

         EPISODE 01.

Bismillahi Rahmanir-Raheem, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin sammai da kassai,tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba ja gaba Annabi Muhammad S A W.Da iyalan gidansa da sahabbansa baki daya.

Alhamdulillah, fanss na dawo muku da sabon littafina mai suna a sama👆bayan gama book din AUREN FANSA,ina rokon Allah SWT da ya bani ikon rubuta abunda zai amfani al’umman annabi ,ya kaucar da ni daga rubuta abunda zai sabawa addinina da al’adata…Duk wani marubuci da ya daura alkalaminsa bisa takarda to tabbas da akwai wani sakon da ya ke son isar wa,idan aka bi karatun cikin nutsuwa za a fahimci inda alkalamin ya dosa,Ina tabbatar muku da insha Allah zakuji dadin wannan labarin, and I believe kuma baza ku bani kunya ba Insha Allah.Allah ya bar kauna ummu fadeela heart you all guys😍…..

KHALEEFA BIN ZAYED AL NAHYAN STREET ABU DHABI CITY (DUBAI).

Katafaren anguwa ne da ke cikin babban birnin hadaddiyar daular larabawa wanda aka fi sani da dubai, anguwa ce mai dauke da rukunin gidaje masu kama da aljannar duniya,…

Lumshe kyawawan fararen idanu na nayi, na dade ina jin yadda ake yabon kyawun zubin hallitar idanuna mutane da dama idan sun tashi yabon kyan hallita ta su kan kirani da mai idon madara tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya bani, amma a halin da na ke ciki yanzu sabanin kasancewar su launin milk idanun sunyi jajur kai kace attaruhu aka daka aka watsa cikin su ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaita wa ba, saidai ba ko daya daga ciki tsabar tashin hankalin da na ke ciki ne ya haddasa min canzawar launin ido.

A hankali na juya na kuma kallon shi zuciya ta na bugawa da karfi karfi yayinda nauyin da kaina yayi ya haddasa min ganin dishi dishi,…yana durkushe gaban gadon da nake zaune ya bani baya yana ta daddaure hodar iblis (COCAINE) cikin wasu kananan leda nylon, da sauri sauri yake aikin wanda duk bayan second daya sai ya daga kai ya kalli kofa.

Rumtse idanu na kuma yi, zuciya ta na tsananta bugu tuna cewa wai nice zan hadiye gaba daya wannan hodar iblis din a cikin cikina inyi safararta zuwa Nigeria.Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un na furta cikin raina kana nabi dogayen kafafuna farare sol da kallo daure suke cikin chains sakamakon yunkurin guduwar da nayi hakan yasa suka daure ni.Zuwa yanzu na tabbatar roko da magiya bazai min amfani ba,.

“You have to be brave” zuciya ta ta fada min, tabbas dabara ne kawai zanyi da taimakon ubangiji inbar wurin nan, if not rayuwata ta kare, safarar cocaine ba karamar risky bane ga rayuwata, cikina ne ya hautsine gami da bada sautin kululululu sakamakon tunawa da nayi wai hadiyar wadannan ledodin zanyi cikin cikina. duk da ya sanar min da hanyoyin da za’abi a fitar dasu idan mun isa nigeria hakan bai rage koda kaso daya cikin dari na irin tsoratar da nayi ba.

A hankali na fara bin dakin da kallo ko zan dace, aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa dani ga kuma wani tangaran mai dauke da rose flower duk a wuri daya, cikin dabara nakai hannuna duk biyun na dau lamp din da kuma flower vase din,…ya dukufa sai aiki yake a gaggauce hakan yasa bai maida hankali kaina ba, rumtse idanu nayi ina tabbatar wa kaina abunda zan aikata shine daidai, baiyi aune ba yaji saukar tangaran a keyarsa ji kake garammm cikin azama ya juyo jin abin unexpected, yana juyowa na kuma rotsa masa bedside lamp din at the same point, take yayi baya baya ya kwala wani irin ihun kiran suna na “MARYAMAAAA” ya fadi kasa jini ya fara malala a wurin, da gaggawa na fara kokarin kwance chains din da ya daure min a kafata, sai a lokacin na kula da cewa tunda ya fadi bai kara motsi ba, ga jini dake tartsuwa ta keyanshi da baki harda hanci.Zuciya ta ce ta kuma bugawa da karfi dan matsowa nayi kusa da shi a hankali nace “ABDALLAH” amma shiru ko motsi baiyi ba, na daga hannunshi ina sakewa hannun ya dawo, mikewa nayi ina ja da baya baya yayinda wani irin jiri ke kwasata, “ya mutu!” na furta da karfi a lokaci daya kuma wani irin bell yayi ring cikin kwakwalwata na kashe shi, idan aka kamani shikenan ba mai kara jin labarina a duniyar nan,…without second though na janyo bedside drawer na cire passport nawa da kuma credit card sai wayoyina guda biyu da kuma tab nawa da sauri sauri na kuma zuge wata doguwar durowa mai dauke da kayayyakina jere reras ba tare da na bi ta kansu ba na janyo wata yar akwati na bude American dollars ne shimfide dauri dauri, duk kaunata ga kudi duk irin wuyar da nasha da irin hadarurrukan da na shiga wurin tarasu amma na kasa daukansu, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban wani,dauri biyu kawai na dauka shida sauran tarkacen wayoyina da na sa su a flight mode, gyalen bakar abayata na yafa da hanzari kana na bi gefen abdallah na fice daga dakin,.

“Act smart maryama this is dubai not abuja nigeria” zuciyata ke bani shawara sai dai duk yadda naso bin shawaran na zuciyata na kasa jikina sai rawa yake, yayinda launin idanuna ke kara sauyawa zuwa tsananin tashin hankali,cikin sa’a na fita daga gidan ba tare da mai gadi ya tuhume ni ba sanin matsayina da yayi a gun mai gidan, cab na tsayar na shige hade da cemasa “Airport,” ina daidaita zamana cikin cab din wani irin kuka mai masifar karfi ya taho min amma haka na dinga dannewa wanda ya haddasa min rawar jiki hadi da takurewar fuska.

ABU DHABI INTERNATIONAL AIRPORT UAE.

“I need ticket to nigeria” na fada muryata ta na rawa, dago kai mutumin yayi yana kallona jin yanayin muryata sannan ya mayar da kanshi yace “your passport ma’am” ciro dan karamin takardar paspo dina nayi jiki na rawa na mika mishi ya karba yadan dudduba kana ya miko min yace “ohk give me a moment to check ma’am” ya maida hankali kan computer dake gabanshi ya danyi danne danne na dan lokaci kana ya dago yace “The earliest flight is emirate airlines but the economy is full, would you like to opt for business class? ko zanyi schedulling naki zuwa gobe”. “Gobe”? na maimata no bayadda za ‘ayi inkai gobe a kasar nan wannan ba mai yiwuwa bane, pleadingly nace plss sir ka kara duba min economy din maybe a dace.

Kafun ya bani amsa kamar ance in juya na hango su suna ta baza ido cikin airport din sun kai su biyar,katti ne sosai mara sa kyan gani idan sun damke ka saidai uwarka ta haifi wani ba dai kai ba,boys na Abdallah ne mun kwashe lokaci sosai muna aiki tare dasu, zaro ido nayi yayinda wani irin zufa ya karyo min har yana diga a kasa, jiki na na rawa na zaro credit card nawa na mika masa nace “a bani business class din” kallo na yayi da mamaki ganin yadda nake ta jan mayafi na don ya rufe min fuska, yayinda na ke jin rawar da kafafuna ke yi yana gab da kayar dani kasa…Kaina a sunkuye nake tafiya bayan na gama da batun ticket mutumin ya sanar min da naje na duba information panel domin sanin exact time da zamu tashi da kuma seat no dina, dan dago kai nayi kadan na kalli gefen da na hango su dazu, aiko karap muka hada ido da john wanda shine babban yaron abdallah, muna hada ido naga ya tunkaro inda nake, nasan bazaiyi gigin da za’a kamashi ba ganin a airport muke hakan yasa nima na dan saisaita nutsuwata amma deep down saura kadan zuciyata ta shige cikin cikina, tafiya nake amma gaba daya hankali na yana kansu ganin bina suke bil hakki, without thinking twice na kwasa a guje domin duk kokarina na ganin banyi gudun ba kasawa nayi,ga uban zufan da ya gama min wanka.

Gudu na dinga yi irin na ceton rai cikin ikon Allah ban hadu da security ba…,garapp naji na bugi wani abu mai kauri kuma mai laushi kana mai sanyayyen kamshi,a lokaci daya kuma wani irin zafi ya ziyarci hannuna hade da watsewar wasu takardu a kasa,jikina na mazari na sunkuya da sauri sauri na shiga tattare takardun da suka zube a kasa cikin second daya na mike na kamo tafin hannunshi ba tare da na daga kai naganshi ba na damka mishi takardun hadi da furta sorry sorry is not intentionally, ban yarda na hada ido dashi ba na ci gaba da gudu na.

Juyawa yayi yana kallona da madaukakin mamaki kafun yabi tsadadden suit nashi da na bata masa da coffeen dake hannunsa…wani dan lungu nabi na ga wani babban dustbin ba tare da dogon tunani ba na shige cikin dustbin din mai cike da tarkacen datti ina sauke numfashi da zare idanu kamar bera cikin bokitin gari, da addu’ar Allah ya tseratar dani,

Wani lokaci can baya

GOMBI L. G. A, ADAMAWA STATE.

Wasu kyawawan yan mata ne su biyu sanye da uniform na makaranta riga da wando da kuma hijabi, wandon dark green yayinda riga da hijab din ya kasance farare tas, kafafunsu sanye cikin takalma sau ciki bakake kirar toms,hannunsu rike da wasu dogayen papers wanda yafi kama da question paper,fuskar dayar cike yake da murmushi da annuri yayinda dayar duk tsiyarka baza ka fahimci expression dake saman face nata ba, tafiya suke cike da nutsuwa irin na yan matan da suka san kansu, yayinda mai fara’ar take dan magana kadan kadan, dayar kuma amsarta daga uhm, sai um um.

A haka suke ketara hanyar da suka shigo kasancewar wurin kasuwa ce sosai irin dai kasuwar bakin hanyar nan babu abunda zaka nema a wurin na siyarwa ka rasa, so wurin cike yake da jama’a anata hada hada, wasu cikin shaguna, wasu kuwa tebura suka kakkafa wasu kuma tampol tampol, don haka ko da yaushe wurin cike yake, mutanen unguwar basu da kewa ko kadan unguwar KASUWAN BUTU Kenan dake garin gombi na jihar adamawa,,tsallake kwaltar da ta raba kasuwar da kuma cikin anguwar sukayi suna ci gaba da tafiya suna ratsa gidajen dake cikin anguwar wanda galibinsu tsofaffin gidaje ne irin na masu karamin karfi,…dan taba ta mai maganar tayi tace “Pretty kinga mutumin ki tunda ga wurin fulani masu saida nonon can nake hango shi ya kafe ki da idanu sai murmushi yake zabgawa kamar mai tallan close up,ni tsorona ma kar ya yanke hannunshi da zarton nan mu shiga uku” ta fada cikin sigar zolaya,.

Wacce aka kira da Pretty ta kara daure fuska tamau kamar bata san me dariya ba cikin muryarta mai dadin sauraro tace “kinga UMAIMAH, Rabani da jarabarki banson tashin hankali da tsakar ranar nan, ki barni inji da abunda ke damuna plsss,.”…Hakan kuwa yayi daidai da isowar su kusa da wani wuri da ake aikin kera gado da kujeru da dai sauran kayan katako, wani saurayine tsaye rike da zarto yana kokarin tsaga katako,kakkarfa ne sosai a kalla zai yi shekara 27 zuwa 28 a duniya, kallon fari zaka dauka shidin baki ne amma zahiri fari ne sol tsabar tsayuwa cikin rana ne ya kodar dashi, dogo ne mai kiran mazantaka, saidai kallo daya zaka masa ka fahimci talauci ya samu lasisi a jikinsa,duban wacce aka ambata da Pretty kawai yake without blinking, yana dan murmushi kadan kadan wanda zahiri daga can cikin zuciyar shi smile din ke fitowa.

Dan rusunawa umaimah tayi tace “barka da aiki HAMMA JABEER”. murmushin sa ya kuma fadadawa looking direct into Pretty eyes yace “barkanku dai, ya jarabawar hope dai bai ba gimbiyata wahala ba?.” ko uffan bata ce ba,sai umaimah ne ta kuma cewa”Alhamdulillah final exam yayi dadi hamma jabeer sai ku taya mu da addu’a kawai”. Kafun ta karasa maganar ta hango Pretty tayi nisa, da dan sassarfa tabi bayanta, murmushi jabeer yayi yace “my drama queen”.

Umaimah tace “wani irin busashshen walakanci ne wannan Maryama, ya zaki yi tafiyar ki ki barshi ko gaisuwa baki mishi ba bayan kinsan domin ki yake tsaye a wannan uban ranar, haba mana Maryama atleast you show some concern mana” tsaki maryama Pretty taja, amma bata ce komai ba, umaimah ta kuma cewa “wannan dai ba halin kwarai bane wallahi ki gyara, gidanshi zaki je a matsayin mata ko ba ma wannan ba yayan kine jini daya ai ba wasa ba may be ma yanxu haka gadon aurenki yake ta fafutukan kerawa amma ko sannu kin gaza ce mashi.” dum dum dum kirjin maryama ya bada sauti jin furucin umaimah na karshe, “may be ma gadon aurenki yake fafutukar kerawa” ta kara maimata maganar a zuciyarta, da sauri tace “impossible, ni nafi karfin a mere kafinta ya kera min gadon aure na, kamar ni ta fada tana nuna kanta, impossible wllh,.” bude baki umaimah tayi da nufin yin magana,….Maryama tayi saurin katseta ta hanyar dago dara daran idanunta ta zuba mata hadi da fadin “look umaimah dan girman Allah ki kyaleni in samu sawaba, rayuwata daban taki daban, dan kina matsayin aminiyata bashi zai sa rayuwar mu ta zamo daya ba, you know me, and you know all my dream and my desire so leave me along plsss, ta juya hadi da shigewa dan tsurkukin gidansu wanda yafi kowanne lalacewa a unguwar, girgiza kai umaimah tayi kana itama ta shiga gidansu wanda yake katanga daya da nasu maryama.

Wani irin takaici ne ya turnuke zuciyar ta lokacin da ta shiga cikin dan madaidaicin gidan nasu sakamakon arba da tayi da wani katon bokiti cike tap da ruwan da aka wanke kalwar yin daddawa ga kudaje sai yarindo suke yi a kai, gefe guda kuma innarta ce ke ta faman kirba kalwa a wani katon turmi.Yamutsa fuska tayi tace “kai innarmu yanzu bazaki daina wannan abun ba, duk gida ya cika da wari ta ko ina, ni shiyasa fa banson kawo kawayena gidan nan salon su rena ni,” daquwa inna ta mata tace “ungo naki maryama, ja’ira da idanu kamar dan farin alade, wannan shine sallama ko haka aka koya maki,” turo baki tayi tace “kai innarmu dan kawai na fadi gaskiya duk sana’ar duniyar nan ki rasa wanda zakiyi sai daddawa,Allah duk sanda nayi kudi zaki huta da wannan wahalar” tana fadin haka ta daga labulen dakinsu ta shige ciki tana kunkuni…Dafe kumatu inna tayi sannan ta ce “Allahu ya shirya min ke maryama” kana ta ci gaba da kirba daddawanta………
💫MARYAMA💫

EPISODE 02.

Dukkansu suna zaune a dan madaidacin tsakar gidan bayan sallan isha, shimfide da babban tabarma kamar yadda suka saba, Baffanmu, innarmu, sai maryama da kuma kannenta Fatima mai shekara goma sha biyu sai salima mai shekara tara,kana daga gefe hamma jabeer shima yana zaune a bakin kofar dakinshi, yayi wanka ya sauya kayan aikin shi na dazu zuwa wasu black jeans da black shirt mai gajeren hannu wanda ya bayyana hasken fatarsa,hakan yasa yayi kyan gani ba kamar dazun ba

Kowa ya sa abincin sa na dare gaba yana aikawa cikinsa hakkinsa amma banda maryama wacce ta kafe kwanon gabanta da ido ko kiftawa batayi kuma ta kasa kai ko loma daya zuwa bakinta,tukekken tuwon masara ne fari sol wanda ya samu tuki irin na kwararriyar hannu yayi sumul sumul gwanin sha’awa sai miyar kuka wanda yasha attarugu da daddawa sai kamshin man shanu yake.

Duk abunda take innarmu tana ganinta amma ba abunda tace mata, saima girgiza kai da tayi taci gaba da cin abincinta, lokaci lokaci hamma jabeer kan dago kai ya kalleta ganin sai yamutsa fuska take yi,yasan abunda ke damunta hakan yasa shi daukar wayarshi ya tura mata dan gajeren sako.

Karar shigowar message wayarta ne yasata dawowa hayyacinta gami da daukar wayar da sauri tana dubawa.Tun wayewar gari sai a lokacin maryama tayi murmushi bayan ta gama karanta content din, cikin dabara ta daga kai suka hada ido dashi, dage gira yayi yana kanne mata ido.A hankali ta janyo marfin dake kusa da ita tayi tana kokarin rufe kwanon tuwon baffa da ya gama cin nashi abincin yana kuskure baki da butan dake kusa dashi ya kalleta gami da fadin.

“Uwata har kin gama cin naki abincin ne?” da sauri tace “eh baffanmu” yayi kyau cewar baffa, to ya jarabarwar taku yau kuka gama ko?.

Sunkuyar da kai maryama tayi tace “eh baffanmu, yau muka gama”. Yace to Allah ya bada sa’ar samun sakamako mai kyau,”duk suka amsa da ameen, gyara zama baffa yayi yace “dama da akwai wani fom da na sai miki jiya, ko zuwa safiya saiki yi kokari ki cike shi, fom ne na koyan dinki shagon M.BELLO FASHION DESIGNER suka fara siyarwa.

Dum dum kirjinta ya bada sauti a ranta tana maimata koyon dinki kuma? amma don karta sacewa baffan nata guiwa cikin sanyin murya tace “na gode baffanmu Allah ya kara girma”. yace “ba komai uwata saiki maida hankali.

Kana ya juya yana kallon hamma jabeer wanda ya mike yana dan shafa suman kanshi zuwa yalwataccen sajensa yace “ya naga ka tashi jabeeru”? yana dan murmushi yace nan bakin hanya zanje amso sako ba dadewa zan ba,” baffa yace “ku ringa kula dai kunsan yadda duniyar ta lalace, ba abar mai kudi ba ba abar talaka ba,jabeer yace insha Allah baffa ya juya ya fita.

Hira suke yi sama sama kasancewar akwai farin wata tarwai, bayan wani lokaci kadan baffa ya daura alwala ya shige daya daga cikin dakuna hudun dake gidan,wani irin ajiyar zuciya maryama ta sauke tana Allah Allah innarmu ma ta tashi, ganin bata da niyyar tashi lokacin ne yasa maryama mikewa ta fara tattara tsakar gidan nasu da bai wani cika da tarkace ba da kuma kwanukan da suka ci abinci,bayan ta gama ta zo ta ciccibi salma wacce tayi bacci a wurin ta kaita bayi tayi fitsari sannan ta shigar da ita dakin da yake mallakinsu ita da kannenta, tazo ta daga fatima ma ta shigar da ita,sai a sannan inna ta mike tana dan hamma tace “bansan me ya tsaida hammanku a waje ba har yanzu bai shigo gida ba, shiyasa banison fitanshi na daren nan sam hankalina baya kwanciya.

Tsagal maryama tayi tace “innarmu bari in leka shi,yanzu haka ma baiyi nisa ba kinsan baya wuce kofar gida inba ya kama dole ba”. Inna tace ki hanzarta to, amma karki wuce kofar gidan kema kinsan baffanku zaiyi fada”.

Da sassarfa ta figi mayafinta tayi hanyar waje,dan dakatawa yayi daga kokarin shigowa gidan jin footstep kuma yasan itace, saida ta kusa isoshi ya fito da sauri gami da fadin.

      "kamata!"

Tsabar irin tsoratar da tayi maimakon ta koma baya sai kawai ta sa kai da niyyan fita waje a guje, hakan yasa suka yi karo da jabeer wanda ya bayyana a gabanta yana murmushi, dafe goshi tayi tana fadin ouchhhh.Allah hamma Jay ka tsoratani,” cikin shagwabar da batasan ma tanayi ba wanda kusan yanayin halittar ta ce hakan.Jabeer da yaji wani abu na mishi yawo a tsakar kai har zuwa kan dan yatsanshi yayi karfin halin kwaikwayan muryarta yana fadin “kai dai prettyn hamma jay karki zama raguwa mana,.

Kamar yace ta kara nan ta fara dire kafafu a kasa tana kukan shagwaba wai ya buge ta da kanshi mai kamar kwakwa, tuni ta kara turning nashi on, jabeer ya dade da sanin baida control when it comes to maryama. Wayar shi ya ciro daga aljihun jeans nashi yana haska fuskarta dukda cewa akwai hasken farin wata, shagala yayi da kallon baby face nata fari sol mai dauke da kyawawan idanu masu kirar kwai farare tas, da zara zaran lashes wanda yanzu suka jike sharkaf da hawayen ta, kana yabi dogon karan hancinta wanda tamkar ita ta zana wa kanta, a hankali ya sauko kan bakinta dan madaidaici mai dauke da siraran pink lips that look sexiest, kana gefe da gefen kumatunta da duk sanda ta motsa fuskarta sai sun loba balle idan tai murmushi ko dariya.Daga kai yayi sama zuwa kan goshinta inda take ta aikin murzawa yabi kyawawan kwantattun gashin dake gaban goshin nata da kallo wanda saura kadan ya hade da dogayen cikakkun girarta.

Maryama is just a definition of beauty, kama hannunta dake kan goshin yayi yana kallon wurin ba shakka kuwa taji ciwo saidai baikai wanda zata yi raki har haka ba, wurin ya danyi ja kadan kasancewarta fara, goga mata wurin ya fara yi, sakar mishi jiki tayi kamar mage, a bangaren jabeer kuwa jin yanayin sa ya fara sauyawa ne yayi saurin sakin goshin nata ya dau ledan da ya shigo dashi ya mika mata cikin shakakkiyar murya yace “maryama shiga gida dare yayi sosai”.

Karbar ledan tayi dama abunda take ta jira kenan ta juya ba tare da ta mishi godiya ba, taku biyu tayi taji ya kira sunanta a hankali kamar mai yin rada “maryama”.Cakkk ta tsaya taku daya yayi ya iso kusa da ita har suna jin numfashin juna, lumshe idanu yayi ya dan matsa baya kadan yana kallon cikin idonta yace.

“I love you maryama, i love yhu with all my heart,plsss don’t betrayed me no matter how situation goes,dan Allah ki soni koda kaso daya cikin darin sonda nake miki,.na roke ki maryama ina miki son da idan kika gujeni zan iya rasa raina, Ko uffan bata ce ba sai aikin murza ledan dake hannunta take yi, shima yasan bazata ce dinba don wannan hali nata shike kara bashi tsoro,yana ganin kamar wata rana zai rasata duk da cewa ita din tashice lokaci kawai ake jira ta kare sakandire gashi kuma ta kare din.

Cikin sanyin murya ba tare da yayi tsammanin zata ce wani abuba yaji tace “hamma jabeer zan shiga gida dare nayi,” murmushin karfin hali yayi yace “to bazamuci tare ba, tunda baki son tuwon innarmu,ware mishi kyawawan idonta tayi tace “kai hamma jay. taya zamu ci tare kuma”. Ware ido yayi shima yace “ta haka mana prettyn hamma jay.”

Da sauri ta juya ta karisa shiga gidan,jabeer kuma cusa hannunshi yayi cikin aljihun wandonshi yana binta da kallo gami da lallausan murmushi,….baje ledan maryama tayi a tsakar dakinsu tana addu’ar kar su fatima su tashi, hollandia yoghurt ne mai dan karen sanyi sai ledan cake guda biyu da wani kunshi wanda ko bata kunce ba tasan kaza ce a ciki, da murmushi take bin rabin kazan dake cikin takarda an yayanka an barbade shi da yaji, lumshe idanu tayi ta bude tana jinjina irin kulawar da hamma jabeer ke bata, koda bata furta ba daga yanayinta yake fahimtar me take so da kuma halin da take ciki,yanzu haka may be dan kudin aikin da ya samu yau gaba daya ya kashe mata anan. tunda shima ba wai gurinshi bane mai gida gare su,idan sunyi aiki a san musu wani abu.

Ita dai bata jin komai na soyayyan aure a zuciyarta kan jabeer, amma tana tsananin kaunar irin kulawar da yake bata da kuma uwa uba irin sadaukarwar da yayi akanta,wanda babu wani mahaluki da ya mata kwatankwacin sadaukarwar da hamma jay yayi kanta a baya..saidai kash ba irinshi take burin aure ba duk da iyaye sun hada amma tana ji lokaci ya kusa da zasu wargaza shirin da sukayi.

Kofi ta dauko ta tsiyayi yoghurt din ta kurba tana jin sanyin shi na ratsa makoshinta, kana ta dau tsokar kaza ta fara figa cikin kwarewa da murna irin na andade ba’a haduba, taci fiye da rabin kazar kana taci cake daya hollandiar kuwa tasha fiye da rabi, wani irin gyatsa tayi tana jin komai ya mata daidai hakan yasa ta daure sauran hadi da ture su gefe a cewarta da safe zata bawa su salima,.

Muryarshi ce ta dawo mata a rai,.

“baza muci tare ba?,

Turo baki tayi gaba sai kuma ta mike ta zura dogon hijab har kasa ta dauki sauran naman da cake din ta hada da yoghurt din cikin sanda ta fita tana taku a hankali dan karta janyo hankalinsu inna da baffa, taje jikin dakinshi cikin sa’a tana tura kofar ya budu, ba tare da sallama ba duk don kar ta janyo hankalinsu ta sa kai cikin dakin, still tayi rike da leda a hannunta ita bata fita ba ita bata shiga ba kuma ta kasa dago idanunta ta ganshi tun bayan kallon farko da ta mishi da halin da ta ganshi a ciki…..
💫MARYAMA💫

    by 

UMMU FADEELA.

EPISODE 03.

…. Yana kwance kan katifar shi yayi rub da ciki daga shi sai boxer, ya cusa kanshi a cikin katifar,still tayi a wurin rike da ledan da ta kawo masa na yan sakwanni kafun ta turo baki ta juya da nufin barin dakin, juyi daya tayi taji ya damko hannunta, cikin muryar da ba tashi ba yace.

“Ina kuma zaki je? koba wurina kika zo ba”?.

Dago kai tayi da sauri suka hada idanu jin yadda muryar shi ya shake,cikin sauri kuma ta maida fuskarta kasa sakamakon arba da tayi da kakkarfan jikinsa fari kal da zara zaran gashi kwance lib lib, bazaka taba dauka cikin jikinsa zai kasance haka ba kasancewar yadda fuskar sa ke kode da aiki cikin rana,.

Kame kame ta fara cikin rawar harshe tace. “am emm dama,..dama na rage maka ne,kuma bansan har ka yi bacci ba,tana fadin haka ta kwace hannunta ta ajiye ledan ba tare da ta yadda sun hada ido ba ta fita a dakin,.

“Maryama”

Ya fada a kasan makoshinsa,amma bata juyo ba,shafa kanshi yayi ya koma bakin katifar ya zauna.

Washe gari da asuba hamma jabeer ya fito kamar yadda ya saba kafun ya tafi masjid sai yayi wanka,sanyi ko ruwan sama basa hanashi yin wannan wanka sanye yake da wando three quater jikinsa ba riga sai towel nashi da ya rataye a wuya hannunshi daya rike da kwandon wanka daya hannun kuma rike da bocket,cika bocket din yayi da ruwan rijiya mai dan dumi kana ya wuce bayinsu dake hanyar fita,saida ya gabatar da uzurinsa kafun yayi wanka a gaggauce jin ana kokarin tada sallar asuba, doguwar jallabiya fara kal ya zura wanda ya ajiyeshi musamman dan zuwa masallaci…

Anan masallacin ya zauna ya gabatar da atkhar nashi har wurin karfe shida kafun ya fito zuwa gida inda yabar baffa acan, zare jallabiyar yayi bayan ya shigo dakinshi ya kuma shiryawa cikin wani katon wando three quarter wanda girman wandon ya kusa buhun siminti yasa da wata riga armless daka gani kasan a gwanjo ya siyesu ya fito ya nufi wata tsohuwar karfen mota mai girman gaske da alamar kuma zatayi nauyi wurin dauka,nan ya hau daga karfen da sauri sauri niko nace bayajin nauyinta ne ko dai kawai tsabar jarumta ce.

Duk tsananin sanyin da ake kwadawa na hunturu take jabeer ya fara hada wani irin zufa mai bada mamaki gaba daya jikinsa ya jike da zufar tsawon lokaci yana motsa jikinshi kafun innarmu ta fito hannunta rike da carbi zata shiga madafa,ajiye karfen yayi yace “barka da safiya innarmu”.

Da murmushi tace, “barka ka dai jabeeru har an soma ibadar ne?”

Dariya yayi yace “ibada kuma innarmu”?

Tace “yo inba ibada ba me zance, ka maida daga wannan karfe kamar sallar farilla,ni tsorona ma kar wataran ya fadi maka a kirji mu shiga uku,kwata kwata na kasa fahimtar ma’anar wannan dage dagen da kake kullum ta Allah.”

“Wannan shine mazantakan ai dijah”.

Suka jiyo muryar baffa dake shigowa daga masallaci.Innarmu tace “to Allah ya kyauta amma dubi yadda daga karfen nan ya maida mishi jiki kamar irin na yan danben nan da ake haskowa a talabijin suna laftar junansu,dukkansu dariya sukayi kafun inna ta shige madafa jabeer kuwa ya gaida baffa wanda yasa kai cikin dakinsa shima.

“Ina kwana baffanmu”.

Ya jiyo Daddadan muryarta cikin kunnuwanshi.lumshe idanu jabeer yayi kafun ya bude, cikin kasala wanda yake halittarta ta sunkuya ta fara sharar dan tsakar gidan nasu ba tare da ta ga inda jabeer yake ba duk da cewa tasan yana wurin a irin wannan lokacin…”Morning pretty!” ya fada lokacin da ta iso kusa da shi a sharar tata.

“Ina kwana” ta mayar masa ba tare da ta yadda sun hada ido ba, murya kasa kasa yace “kawo tsintsiyar in tayaki,maqe kafada tayi hadi da turo baki gaba,…Gudar dari biyu ya zaro daga aljihun shi murya kasa kasa yace “ga wannan ki tura salima ta siyo miki kosai da madara kisha da tea nasan yau innarmu dumamen tuwon jiya zata yi.”

Da sauri ta dago kanta suka hada ido tayi saurin sauke nata idanun ,tana mamakin yadda jabeer ya haddace duk wani motsinta na rayuwa.Koda shike ba abun mamaki bane duba da labarin da innarmu ke bata a kullum cewa jabeer ne ya rene ta tun tana cikin tsumma shiyai yayenta lokacin da aka cire ta a nono,duk inda zashi tana makale a kafadar sa inka cire makaranta shima dan yasan baza’a barshi bane,innarmu tana yawan cewa jabeer ya ci kashi na da fitsari na, a kaina ya koyi yiwa yaro wanka da saka napkin,so ba abun mamaki bane kenan idan yasan fassarar duk wani motsi na.

Sauke ajiyar zuciya nayi kafun na miko hannu zan karba muka hada ido yamin wani kyakyawan murmushi mai shiga zuciya,amma ni iya bakin zuciyar ta tsaya baikai ga shiga ciki ba.

“Mayar mishi kudin nan kafun in fito in sare hannun nan naki da wuka”.

Duk muka juyo sakamakon jin muryar innarmu dake tsaye bakin madafa,fuskarta ba alamar wasa tace “idan bazata ci abunda duk gidan zamu ci ba sai ta zauna haka kokuma ta dau azumi, amma wannan iskancin nata ya isheni haka,kai kuma da shike solobiyo ne sabulalle sai kake biye mata, to duk kujini da kyau ba a gidan nan za’ayi haka ba, duk ina lure daku ai kai ka daure mata kugu take zuba mana isakanci son ranta,ita yar uban waye da bazata ci tuwo ba,?.

Shiru sukayi dukkansu basu motsa ba, da masifa mai dauke da fushi innarmu ta kuma tambayar ta “ke yar ubanwa nace, waye ubanki a garin nan da bazaki ci tuwo ba,?”.

To ku bari randa kuka tare a gidanku sai ku yi duk tsiyar da zakuyi idan ma kafar ka take so sai ka guntule ka dafa mata parpesu dashi kaji ko ROMEO.

Murmushi jabeer yayi yace “ayi hakuri innarmu, ko kallonshi batayi ba maryama kuwa na tsaye gefe ko uffan ba ta ce ba,wani kallon zaki shiga hannuna inna ta mata kana ta koma madafa tana ta sababi.

Bakin rijiya jabeer ya nufa yana shafa lallausan sumar shi,bokiti ya janyo hadi da jefa guga ya fara diban ruwa, jin karar juye ruwa cikin randa yasa innarmu fitowa harta na tuntube tasan jabeer ne ke jan ruwan bayan yasan aikin maryama ne, kullum aikin kenan ko ya taya ta shara ko diban ruwa kai har wanke wanke yana mata idan ya paki idon innarmu, baki a bude tace, “anya jabeeru kanka kalau yake kuwa,anya kana son ganin daidai nan gaba kuwa, ajiye botikin nan kafun in haure ka.bansan yaushe ka zama sauna ba, idan anyi auren naku haka zaka je ka shashance a rasa waye matar waye mijin,to wllh tun wuri kayiwa kanka fada, kayi wa kanka karatun ta nutsu.

Yana sosa kanshi yace “innarmu aikin ya mata yawa ita kadai gashi zata tafi islamiyya shisa nake taimaka wa.Zuwa yanzu innarmu ta tabbatar da maryama bazata taba samun miji irin jabeer ba,duk kuwa da ta lura da irin take taken ita yar tata.

Fatima jabeer ya kwalawa kira, jiki na rawa ta fito dan baya musu da sauki ya mika mata bokitin yace “ki cika randunan can gaba daya yanzun nan,and daga yau ke zaki ringa diban ruwa a gidan nan right? ya fada yana kallonta gyada kai tayi ya kira salima ma yace ita zata ringa yin wanke wanke…Komai innarmu bata ce ba ta shige kitchen ta barsu.Maryama kuwa shararta taci gaba dayi happingly.

Bayan ta gama share tsakar gidan wanka tayi ta shirya cikin uniform na islamiyyarsu tasa hijabi har kasa ta dau litattafanta ta fito,zuwa lokacin karfe takwas ya kusa tuni jabeer da baffa suka fita jabeer ya tafi wurin aikinsa baffa kuwa ya tafi kasuwa inda yake saida danyen kayan miya.

A tatstsaye maryama tasha kunu rabin kofi shima saida innarmu ta matsa mata,shigowar umaima itama shirye cikin uniform ne yasa maryama ajiye kofin hannunta ba tare da inna ta kula ba dan tana amsa gaisuwan umaima ne gami da tambayarta lafiyar yan gidansu, “duk suna lafiya cewar umaima”.

Maryama tace “innarmu sai mun dawo karmuyi latti,” tace “Allah ya baku sa’a ku kula da kanku,idan kun dawo ba lallai ki same ni gida ba,zan dafa farar shinkafa da wake in zuba a kula sai ki aika su salima idan sun dawo makaranta su amso ganyen salad wurin baffanku ki yanka mana,” cikin fara’a ta amsa da “to innarmu, sai in mana harda miyar ma ko?.

Ungo naki” cewar inna ja’ira shiyasa naga kina fara’a to da mai da yaji za’a ci, turo baki maryama tayi suka fice daga gidan.

Sannu a hankali suke tafiya, umaima na mata hirar saurayin ta yusuf…Juyo dara daran idanunta tayi wanda suka dan sauya kala sakamakon ciwon marar dake dan damunta kadan kadan amma take dannewa ta sauke akan ta kafun cikin sanyin muryarta mara hayaniya tace “kinsan Allah umaima kina bani mamaki,ni banga abun so a wurin yusuf ba wanda har kike rawan kai haka, mutum aljihu duk annakiya amma kin like masa kamar wani gwamna,ko kuma dan gwamna, nifa har yau banga talakan saurayin da zan yiwa so irin na hauka kamar yadda kike wa wannan yusuf din ba, dan juya ido tayi taci gaba da fadin, babban gida mai bene, manyan motoci na hawa, zuwa honeymoon a kasashen turawa, saudi duk shekara uwa uba inyi karatu mai zurfi, wanda ya mallaka min wannan ne kawai zanyi wa so na hauka, kai ko taka ni yake kullum bazan damu ba, amma bazan yadda iyayena talakawa sannan in kare a auren miji talaka ba ina impossible.”

Uhmmm kece kike ganin saida arziki ake soyayya maryama, amma for me arziki ba itace soyayya ba,mata dubu nawa ne suke cikin irin daular da kika lissafo koma fiye da wanda kika lissafa amma basu da farin ciki da walwala?kiyiwa kanki fada tun lokaci bai kure miki ba maryama,ki dena yadda kyale kyalen duniya da kyan da ake fada kina dashi su rude ki,wllh zakiyi nadama idan baki sauka akan wannan jirgin takardan da kika hau ba, ki kama hamma jay, dan wallahil azeem baki da mai sonki kamar sa kuma bazaki taba samun mai sonki kamar shiba, karki manta sadaukarwar da,yayi akanki can baya kim… …Da sauri maryama ta katse ta ta hanyar fadin kinga karki bata min mood dina, na rasa meyasa mutane suke son alakanta ni da hamma jay. Bayan ko da wasa bamu dace ba, nidin matar manya ce ba matar kafinta ba mai aiki a karkashin wani, wannan sadaukarwar da kike magana kuma dama can Allah ya nufa ta dalilinshi zan samu, so ku sarara min inshaki iskar duniya dan Allah.

Ko uffan umaima batace mata ba domin idan maryama tana irin maganganun nan duk abunda zaka fada mata bazata fahimta ba, mutane sun riga da sun saka mata virus a kwakwalwa tun tana yarinya cewa ita matar manya ce dan ta kasance kyakyawa gashi abun ya bita har zuwa girmanta, da haka suka iso islamiyya…Wurin misalin karfe goma ciwon marar da maryama take ji ya tsananta dan har wani rawa jikinta keyi ga idanunta da suka kada sukayi jawur sai zufa take sharcewa ganin hakan ne yasa mu’allim nasu yace taje gida tasha magani….Tun daga nesa ya hango ta tana tahowa, daga yanayin tafiyarta yasan ba lafiya, kureta yayi da ido har ta shiga gida kafun ya dauke idonshi cikin dakiya ya nufi ogansu don yasan innarmu bata nan, gashi yaga yanayin maryama akwai damuwa yace “oga zubairu minti daya zan dau abu a cikin gida”

Ba tare da tunanin komai ba ogan su yace ba damuwa…Da kyar maryama ta kai kanta daki ta ajiye jakar litattafanta kana ta zare hijabinta da rigar ta,daga ita sai farar vest da dogon wandon islamiyyarta, kwanciya tayi rub da ciki tasa filo daidai cikin nata yanda zai matse mata shi dan sosai yake mata azaba yayinda dogon sumarta ya bazu saman gadon, duk da ta cire kaya hakan bai hana zufa jike ta sharkaf ba…

Kamar yadda duk muka sani ba wanda bai son ci gaba a rayuwa, nima ta bangare na haka ne…I know ina da solid fans da za su patronizing dina a littafin maryama koda naira nawa nace, kuma ina alfahari da ku…Littafin MARYAMA na kudi ne zaku biya naira 300# kacal ta wnn acc. Din👉0056115042….Asma’u Isa…Unity bank. then show your evidence of payment via 08104875999.

Patronize me and read happily, thank you all😘.
💫MARYAMA💫

EPISODE 04.

   ELEGANT ONLINE WRITER'S.

….Hankali a tashe ya shigo gidan bai zarce ko ina ba sai dakinta,zuwa lokacin ciwon da ta keji ya karu sai birgima take yi a kan gadon tana rike da cikinta tana kiran wayyo innarmu wayyo baffanmu,baisan yadda akayi ba sai ganinshi yayi bakin gadon rike da hannunta.

Jin hannun mutum cikin nata yasa ta rike wa gam tana sakin wani marayan kuka. murya cike da damuwa yana jin kamar ya maida ciwon jikinsa yace “maryama!ciwon cikin ne?gyada mishi kai tayi tana kara murkususu akan gadon,rumtse idanu yayi gaba daya basirar sa ya gudu ya rasa me zai mata. Wani irin yunkura tayi da karfi ta mike zata fita waje saidai kafun takai wajen nan tsakar dakin ta durkushe ta dinga kwarara amai tamkar zata amayar da yan hanjinta,jabeer da ya rasa abunyi shima durkuson yayi gefenta pitiefully yake mata sannu.

Mikewa tayi tana jin jiri na kwasarta ta koma kan gadon ta kwanta, gaba daya jikinta ya baci da aman da tayi.lamo tayi kan gadon tana sauke numfashi a hanakali domin aman da tayi yasa taji saukin kartawar da mararta ke mata.

Shafa gashin kansa yayi yana lumshe ido kafun ya mike ya fita waje, ruwa ya deba a bocket hadi da janyo tsummar da innarmu ke goge goge ya dawo dakin….Tas jabeer ya kwashe aman da tayi kana ya goge wurin da ruwa da omo,dan matsowa yayi kusa da ita yace “pretty, tashi ki canja kayan nan kar sanyi ya kama ki kinga sun baci gaba daya.”

Ko uffan bata ce ba sakamakon sabon ciwon cikin da ya taso mata, haka maryama take fama da wannan jarababben ciwon ciki da marar duk sanda lokacin period nata yayi sai kowa ya sani, ga amai ga ciwon cinyoyi ga gudawa duk ita kadai kuma every month sai tayi hakan.

Jin bata motsa ba yasa jabeer kamota yana fadin “pretty ki tashi ki sauya kaya sai ki sha magani ki kwanta kinji?.”

Bata musa masa ba ta tashi tana jin duniyar na juya mata,bin shafaffen cikinta dake cikin vest yayi da kallo wanda aman da tayi ya taimaka wurin kara lafewar vest din a jikinta, ga kuma wani sabon lamarin dake jikin vest din, bin jikinta tayi da kallo ganin yanda ya kureta da ido, da sauri ta juya mishi baya tana turo baki gaba ganin gaba daya farar vest nata ya baci da jini, arba tayi da bedsheet dake saman gadon wanda gaba daya shima yayi staining da jinin thats mean bayanta ma ya baci kenan,wani irin juyi ta kuma yi ta durkushe a wurin tana takurewa wuri daya gami da fadin Hamma j. Banaso

Murmushinsa mai kyau yayi yana shafa kanshi wanda ya zamo dabiar sa yace, baki son me prettyn hamma j.”?

Ko motsi batayi ba hakan yasa qya fita a dakin, kitchen ya shiga dan yadda ta bacin nan tana bukatan wanka,cikin sa’a kuwa ya samu ruwan zafi akan wuta ba tare da wani tunani ba ya dauko bocket ya juye ruwan ya fito ya sirka saida ya tabbatar yayi daidai kafun ya shigar mata bayi,lokacinda ya dawo dakin maryama tana kokarin cire wandonta tuni ta cire vest din dama,wani irin ihu tayi gami da dirkusawa a wurin,cikin shagwababbiyar muryar da ya saukewa jabeer kasala tace.

“Ni banaso kuma ka fita a nan” dariya ta basa ganin yadda ta takure amma baiyi ba yace “ohk zan fita, kiyi sauri ga ruwan ,zafi a toilet kije kiyi wanka kar ya huce.”…Da zani daure sai babban hijab da ta zura ta fito dauke da kwandon wanka zata wuce bayin,jabeer yayi kasa da murya yace “kindau PAD naki? ko ya kare in kawo miki wani.”

Da kamar baza tace komai ba, sai kuma ta rufe fuskarta da hijab din jikinta tace “ya kare”.

Baice komai ba ya wuce dakinsa bayan kamar minti biyu ya fito rike da ledan always ya mika mata, karba tayi ta wuce toilet din shikuma ya shige dakinta,…Kallon kayan dake kan gadon yayi nadan wani lokaci kamar mai nazarin su a hankali ya lumshe kyawawan idanunshi kana yasa hannu a kanshi yana shafa lallausan gashinsa, bude idanun yayi ya kwashi kayan da bedsheet din ya fita dasu waje, wurin da suke wanke kaya ya ajiye su kafun ya dauko bokitai da omo nan ya dara wanke kayan jinin maryama….Tas ya wanke su ya shanya ya koma dakin ya shimfida mata wani zanin gado ya fita. Lokacin da ta fito wanka da mamaki ta tsaya tana kallon kayan dake shanye bisa igiya, ba yau hamma j. Ya fara yi mata dauraya ba, amma na yau din yafi bata mamaki,…Haka ta shiga daki ta kimtsa jikinta ta hau gado ta kwanta domin kwanciyar take bukata a lokacin.

Jabeer da ya kasa komawa wurin aikinsa sakamakon halin da ta ke ciki ya shiga dakin yafi sau a kirga amma ganin ta samu bacci ya dauke ta sai bai tayar da ita ba,jin shirun yayi yawa yasa ogansa kiran wayarsa don ya bar aikin da ya fara a walakance,…Daga karshe dai innarmu jabeer ya kira awaya ya sanar mata maryama ba lafiya.

“Me ya ke damunta.”?, Cewar innarmu,kame kame ya fara kafun yayi gathering courage yace “ciwon cikinta ne ya motsa mata,” dan jim tayi sannan tace “to Allah ya sauwake ganinan tahowa gidan yanzu”.

Saida innarmu ta dawo jabeer ya koma wurin aiki wanda ko kadan hankalinsa baya kai, ya karkata ga tunanin halin da ta ke ciki.

Tsawon kwanaki biyar maryama ta kwashe tana fama da cramps before ta ci gaba da harkokinta zuwa islamiyya da kuma koyon dinkin da baffa ya samar mata wanda ko kadan hankalin jabeer bai kwanta da zuwanta shagon ba ganin duk shagon maza ne, a bangaren maryama ma bata son zuwa amma dan karta bata ran baffanta yasa ta fara zuwa da niyyar idan result nasu na SSCE ya fito zata dena zuwa…

  -----------------------------------------------

Tafe suke cikin murna,yan mata ne kusan su biyar ko wacce ka gani baki har kunne tsabar farin ciki fitowar su daga cafe kenan inda suka yi browsing result nasu na kammala sakandire,duk murnan da sukeyi ya kamata ace maryama ta fisu dan duk tafisu samun sakamako mai kyau, inda ta samu 7credit da 2 distinction a both waec and neco dinta,wannan ba karamar nasara bace saidai ga maryama ba alamun annuri saman face. nata kwata kwata ma bata tare dasu hankalinta ya karkata ga wani tunani na daban.

Tun ina karama na taso da wani buri a rayuwata, burin yin karatu mai zurfin gaske da zamowa hamshakiyar mace wacce za’ake kwatance da ita,sannan in auri miji hadadde mai ilimi mai arziki wanda zai mallaka min duk abunda na bukata,kana ina da burin rayuwa da mijin da zan aura a manyan biranen duniya,duk sanda naga mace a cikin mota tana tukawa nakan ji inama ace nice,wani lokacin har hawaye nake zubarwa amma nakan lallashi kaina da ba kaina tabbacin idan na girma zan mallaki duk wadannan.

As I grew older,the likelihood of my dreams becoming true,kasancewar zallar madarar kyau dake bayyana a gareni irin na buzayen asali,duk ta inda nabi sai mutane sun tanka akan hallita ta yaayinda wasu da dama ke kirana da maryama matar manya,ga wani irin farin jini da Allah ya bani baga maza kawai ba hatta mata jinsi na kaunata suke yi manya da yara,wannan ne ya kara min karasashi wurin neman cikar burina, domin a gani na duk wani mutum mai kyau to ya mallaki makaman samun abunda yake muradi a rayuwarshi.

Saidai iyayena sun katse min hanzari tun ban fara nisa ba,inda suka shirya hadani aure da tilon dan uwana ba tare da sun nemi jin ra’ayi na ba,…Wannan sakamakon jarabawar ssce dake hannuna yanzu shine chance dina na cikar buri a yanzu,idan iyayena da suka kasance talakawa tibisss da abincin da za’aci ma sai an nema wataran ma rasawa ake,idan sun amince na ci gaba da karatu zuwa matakin jami’a xanfi kowa farin ciki,idan ko sabanin hakan na samu lallai zan kare rayuwata cikin dauwamammiyar kunci marar gushewa.

Ni maryama ina cikin shekara ta goma sha bakwai ne a yanzu,saidai idan ba baby face nawa ka karewa kallo ba,zaka dauka nidin cikakkiyar budurwa mai shekaru ashirin da biyu ne domin irin kirar da Allah ya min na dirarriyar mace, ina da tsawo da murjejjen jiki,bani da kiba amma ina da cikakkun kirji masu daukan hankali a kallon farko kana inada wadatattun mazaunai da kuma shimfidaddiyar hips,wanda ke bayyana asirin shafaffen cikina,skin nawa fari ne kal irin na matan indiya,yayinda fuskata ta kasance oval shape mai dauke da dara daran idanu masu haske da kuma yalwar lashes masu tsawo saman su kuwa eyebrow ne da yake so thick bakikkirin,daga saman goshina akwai kwantattun gashi wanda zai tabbatar maka inada arzikin gashi a cikin kaina, hancina dogo ne sosai ta bakin hamma j. kamar ni na zana wa kaina,kana bakina zagayayye ne mai dauke da pink lips masu sheki koda bansa musu lip gloss ba,ta ciki kuwa suna dauke da set white teeth a jere reras gwanin sha’awa yayinda a tsakiyar guda biyu na gaba dake sama akwai dan tsaga siriri wanda yake kawata murmushi na, a duk sanda bakina ya motsa kuwa gefe da gefen kumatuna sukan loba ciki abun so masha Allah……”Wai tunanin me kike yi haka ne?, gasu safeena suna miki sallama amma har suka shiga gida baki tanka musu ba,kodai yauma kin hau jirgin takardar ne ya lula dake wata nahiyar maryama?.”cewar umaima da ke karkadawa mata papers din dake hannunta a saman fuskanta ganin tayi nisa cikin tunanin da take har sauran yan mata ukun suka shige gida bata ma sani ba.

Dago dara daran idanunta tayi that look very restless ta zuba su kan umaima cikin sanyin muryar ta tace.” kinyi magana ne umaima?”.

Cike da tausayawa rayuwar da ta daurawa kanta umaima ta kalli aminiyar tata tace “cewa nayi gasu feena suna maki sai anjuma baki tanka su ba,yanzu haka sai su zaci girman kai kike nuna masu maryama,plsss kina rage yawan tunani kinsan yawan tunani is not good for health barin ma wannan tunanin rayuwar da ke kika daurawa kanki wllh ki canja maryama if not zaki sha wahala a nan gaba.”

Fuska a cunkushe ta kalli umaimah cikin sanyin voice nata tace “I regret telling you what’s in ma heart umaimah,idan baki bani kwarin guiwa ba bai kamata ki dinga discouraging dina ba haba mana for God Sake ke baki da aiki kullum saidai ki bata min rai ? ni ban isa inyi tunani yadda rayuwata zata kasance ba, inace ke kullum sai kinyi planing yadda zakuyi rayuwa da yusuf,ki barni dan Allah this is my life dole inyi yadda nakeso dashi” bata jira jin abunda zata fada ba ta shige gida ta bar umaima da baki agape…

Kamar kullum yauma a tsakar gidan aka shimfida tabarma din cin abincin dare, yau da fara’a maryama ta ke cin abincinta domin favourite nata a ka dafa,white rice da stew da yaji nama zuku zuku hamma jabeer ne ya sai musu shinkafar da nama don anbiya ogansu kudin wasu funitures da suka yi shikuma ya rabawa ma’aikatan hakkinsu,ganin hakane yasa shi masu cefanen abinci, innarmu tasa baffa ya kawo kayan miya da ganyen salad aka zuba girki tamkar ranar salla.yayinda hamma j. Yake jin wani irin dadi a zuciyar shi ganin masoyiyar tashi tana cin abincin happily.

Bayan an gama fatima ta tattara wurin,baffanmu ya kishingida cikin dan hiran da suke yi ya tambayi maryama “uwata ya maganan sakamakon naku? ina fatan dai yayi kyawu ko?”

Mikewa tayi fara’a fal fuskarta tace “eh baffanmu yayi kyau sosai bari in kawo maka dama ina jira ka gama abunda kake ne”.

Daki ta shige hamma j. ya bita da ido, ba jimawa ta fito dauke da takardun ta durkusa cike da ladabi ta mika masa.

Karba yayi yana dariya yace “uwata ni me na sani anan, banda dai fararen takardu da na gani, maza jabeeru zoka duba min, ya fada yana kallon hamma j.”

Duk dariya sukayi banda jabeer da ya taso daga inda yake zaune, salima dake tattare da yarinta tace baffanmu lokacinda kuke zuwa makaranta ku ba malamai ne?” dariya yayi yace “salima ta baffanku bai yi boko ba,kune dai kika dace kuna bokon yanzu,dakuwa innarmu ta mata tace “banason banzan tambayoyin nan marasa kan gado salima,”.

Still laughing baffanmu yace “kayya dijah barta tayi tambayarta mana ai tambaya yana bude kwakwalwar yaro kuma yana nuna yaro mai kaifin basira ne”.

Karbar takardar jabeer yayi ya dudduba kafun yace “baffanmu sakamakon yayi kyau, ina ganin ba wanda ya samu result irin nata a shekarar nan”.

“Madallah” cewar shi “amma anya jabeeru baka karawa sakamakon armashi ba kuwa, ya fada cikin barkwanci. nan ma duk dariya suka yi banda maryama da ta sha murr, gyara zama baffanmu yayi kafun ya koma serious yana kallonsu dukansu, yace “to alhamdulillah, wannan lokacin muke jira dama dukkanmu gashi ubangiji ya nuna mana uwata ta kare sakandire yanzu menene shirinku akan maganar aure?,domin a namu bangaren nida mahaifiyar ku dama mutanen nijar mun gama namu shirin lokaci kawai dama muke jira”.

Yana kallon jabeer da ya sunkuyar da kai kasa kana maryama ma tana durkushe gabanshi kamar wacce ke neman gafara saidai sabanin jabeer da kanshi ke kasa, ita ta kafe jabeer dinne da manyan idanunta kirjinta na tsalle kamar zai fito waje yayinda jikinta ke dan rawa kadan kadan tana jiran jin me zai fada….
💫MARYAMA💫

By

Asma’u Mai Anguwa

      (Ummu Fadeela).

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Kafun yanzu littafin MARYAMA,na kudi ne.amma due to some reason na mayar dashi kyauta,dalilin kuwa shine,duk yadda naso yin posting a group nawa na facebook abun ya gagara dole na hakura, so yanzu maryama FREE BOOK ne, abunda kawai nake son ku saka man dashi shine sharhi da sharing,dan Allah ku dinga share duk wani group da kuke ciki,iya shrhinku da share din ku iya yawan posting din da zaku samu😍Thank you All…

EPISODE 05.

…..Cikin nutsuwa jabeer yace “duk yadda kuka tsara shine daidai ranka shi dade mu namu bin umarni ne idan kunce ayi yanzu sai nafi kowa farin ciki da hakan …,zaro idanu tayi tana jin gabanta na tsananta bugu,jabeer ne yaci gaba da fadin “amma tunda kunce ra’ayinmu kuke son ji to nidai a bangare na dama ina planing ta zana jarabawar neman gurbin shiga jami’a by then na samu aiki watakila abubuwa zasufi yi mana sauki,amma wannan tunanina ne baffanmu,idan tayi jarabawar gaba kadan za’a fara deban sabbin dalibai kunga sai ta jona kawai koda tana dakinta.duk maganan da yake kanshi yana kasa bai yadda sun hada idanu da kowa ba, ba karamin kokari yayi ba kafun yayi wannan jawabin Allah ya sani yana son auren cikin lokaci kadan kodon fargabar da ya ke ciki na barazanar rasata da yake yawan fado mashi a rai,amma dole ne ya cikawa maryama burinta koda ko shi zai take nashi burin, Wannan shine hakikanin soyayya.ka take naka kaso abunda wanda kake so ya so.

Tunda maryama take bata taba sanin wani abu wai shi relieve ba sai yanzu,wani irin ajiyan zuciya ta sauke wanda yasa gaba dayansu dagowa suka ganta,…Dan daburcewa tayi ta fara kame kamen fadin “eh baffanmu kaga yanzu an fara saida fom din jamb kawai sai…” shiru tayi sakamakon wani kallon da innarmu ta aika mata.

Dan gyara zama yayi yana kallon su both yace, “cikin ku wa ya tsara wannan maganar?….ba tare da ya jira sun bashi amsa ba yaci gaba da fadin “sannu mongo park mai kankat kenan a boko,nace sannu mongo park mai kashin ABCD,kai da kayi digiri din me ya tsinana maka?cikin fada baffa yake tambayar jabeer da ya tsunkui da kai kasa,ba magana nake bane jabeeru,nace amfanin me digirin da kayi ya maka kaida kake namiji ma balle ita mace, ina ce duk wuyan da kasha da kudin da aka kona akan digiri din karshe filo kayi da sakamakon da ka samu ba aikin yi,aiki a kasar nan sai dan wane da wane sai yayan masu hannu da kumbar susa,dan talaka saidai yayi kallo ko ya rike sana’ar da ya sauwaka.

“Ayi hakuri baffanmu” cewar jabeer yana shafa sumar kanshi.

Sassauta murya baffa yayi yace “jabeeru karatun diya mace yana da kyau bance bashi da amfani ba amma ana sara ana duba bakin gatari, maryama ta samu ilimi iya abunda ya sauwaqa na matakin sakandire ta sauke alqur’ani yanzu tana haddanshi da na wasu litattafai,dama ana son mace tayi ilimi ne dan a samu al’umma masu aminci tunda uwa itace matakin tarbiya na farko, ina da tabbacin uwata bazata bani kunya ba a wannan bangare, nasan tunaninka shine inda zaka ajiyeta da kuma sauran abubuwan al’ada,mun rigada mun yanke shawara da innarku gidan da yake kasan layi na dada can zaku zauna farar kasa da penti kawai za’a samu a goga,tunda akwai komai ciki da bayi da madafa madafar ne kawai yake bukatan gyara, tunda dada ta koma nijar sai ku zauna ciki har muga abunda Allah zaiyi zuwa gaba,batun lefe kuma ko zuwa gaban bazai hana ka mata ba idan Allah ya hore maka,” innarmu da tunda suka fara maganar bata ce komai ba tace “oh oh Allah ita maryaman ce maku tayi bata da kayan sawa ne?”.
Baffa yace “ah ah amma al’ada ce ai dole zai mata”, wani irin hautsinawa cikina yayi da gudu na mike kafun in iso kwararo na fara kela amai kamar yan hanjina zasu fito,innarmu ne ta tashi zuwa kaina da fadin sannu,kinci abincin nan dayawa ko maryama? daga can kuwa ba karamin jarumta jabeer yayi ba wurin hana kanshi tashi ganin idon baffa amma jikinshi har rawa yake yi, baffanmu dake lure dashi yana mamakin irin son da jabeer yake wa maryama tamkar dai labarin laila da majnoon,yana iya sadaukar da komai domin farin cikinta,kamar dai yadda ya sadaukar da…..

Katsewa tunaninshi yayi sakamakon “Subhanallah” da innarmu ta ambata tana kokarin rike maryama dake shirin faduwa kasa,a tamanin jabeer ya nufe su baisan ya akayi ba sai ganin shi yayi rike da maryama wacce jiri ke kwasarta sakamakon aman da tayi mai yawan gaske,ruwa innarmu ta kawo domin wanke mata baki jabeer ya amshi ruwan hadi da tsugunar da ita kasa a hankali ya fara zuba mata ruwan tana kurkure bakinta da wanke fuska,gaba daya maryama ta galabaita kamar mai jinya gyara wurin da ta bata innarmu ta fara shikuma ya kama ta da nufin shigar da ita daki, “sannu uwata Allah ya kiyaye gaba” cewar baffanmu daga kai kawai ta iya yi su salma ma sannu suka mata duk tabisu da daga kai haka jabeer ya kaita har cikin daki kan gado rike da hannunta ba tare da ya yi la’akari da idanun da iyayen nasu suka bisu dashi ba.

Kwantar da ita yayi saman gadon calmly yace “bazaki canza kaya ba?naga wadannan sun baci, gyada mishi kai kawai tayi bata ce uffan ba, hakan yasa ya bude mazubin kayanta ya fitar da wankakken bedsheet ya rufa mata har kan kirjinta, cikin nutsuwa yace “sleep tight pretty,don’t stress your self with thinking, anything will be alright, okay? ya kare da daga mata gira daya, jin batace komai ba kuma yasan zaiyi wuya tace din yasa shi juyawa don fita karsu baffa suga ya dade a dakin, jin lallausan hannunta mai kama da garin fulawa yayi cikin nasa, rumtse idanu jabeer yayi kafun ya juyo a hankali yana kallonta da gajiyayyun idanunshi,.

Cikin marayan murya mai cike da alamu na rashi maryama tace “do something hamma jay. Plsss na rokeka kar ka bari su baffanmu su hanani yin jamb dinnan kaga idan nayi missing yanzu sai next year, and i don’t want t….Shhhhht ya katseta ta hanyar sa dan yatsanshi a saman lebenshi ya kafe ta da ido wanda ya tilasta mata janye nata idanun domin wasu irin bama bamai take hangowa cikin nashi idon wanda anytime zasu iya tarwatsewa,yace cikin sanyin murya “you don’t worry pretty zaki jana jamb Insha Allah zanyi kokari ganin nayi convincying baffanmu idan ya amince nasan innarmu ma zata amince,kedai keep praying idan Alkhairi ne Allah ya tabbatar idan kuma sabanin haka ne Allah ya musanya mana da mafi alkhairi”

Turo baki tayi gaba tace “kai hamma jay, ka taba ganin inda neman ilimi ya zama ba alkhairi ba, nidai alkhairi ne Allah, yadda take maganan ba karamin yamutsa jinin jikin jabeer take yi ba, da shakakkiyar murya yace “da gaske pretty ba komai mutum kanso ba a rayuwa ya zame masa alkhairi,….Shigowar innarmu dauke da ruwa da magani ne ya katse masa maganar da ya fara.

Tace “to bawan mace saika bamu wuri haka nan, ni naga yadda za’ayi auren ai kana nuna mata rawar kafa tun yanzu ba dole ta rena ka ba ta ringa wahalar da kai, murmushi yayi yana shafa sumar shi as usual kana simi simi ya fice a dakin, juyowa innarmu tayi tana banka mata harara ganin yadda ta turo baki gaba tace “kin tashi kinsha maganin ko yaya?…..Misalin karfe sha biyu dare ya tsala amma barci ya kauracewa idanun jabeer dake kwance rungume da filo, hakama maryama dake ta faman juyi saman gadonta tunanin duniya ya isheta na yadda zata raba kanta da auren jabeer ba tare da ta bata ran iyayensu ba da shi kanshi jay din don yana da wani matsayi na musamman a zuciyarta amma bangaren yan uwantaka na jini ba soyayyan aure ba, a gefe guda kuma zuciyarta na batan shawaran gobe da safe ta kira kawarta siyama ta tabbata zata taimaka mata. Da wannan tunanin ta tsaida matsaya.

Lumshe idanu yayi ya kuma budewa cikin mutuwar jiki ya janyo wayarshi gallery dinshi ya shiga ya fiddo wani hotonshi da maryama wanda suka dauka a asibiti lokacin bata da lafiya tana zaune kan gadon hospital din fuskarta tayi fayau kamar ba jini a ciki, bakinta ya bushe sosai shikuma yana gafenta ta kwantar da kanta a kafadunshi, ya dade yana kallon hoton yana saka abubuwa dayawa a ranshi kafun ya rufe ya nufi messages ya fara rubuta mata kamar haka,

“This is for you my life.”

Yadda kunne yaji haka zuciya ke aunawa.
Inda raina da rabo na zaki yi ganewa.
Nida ke sirrin juna zamu yi boyewa.
Ra’ayina kece kikka zamanto tawa.
Ki kula min da kaina ma’ajin sirrina.
Hakan shine zai sanyaya ruhina.
Wa’adina yazo indai bakya sona.
Tunda naji wadansu akanki suke zagina.
Kinga tauna sam ba’ayi saida hakora.
Kiyi kirana gefenki nazo na sarara.
Ko a dan aiki daukeni na kore kura.
Nifa ba komai kanki koda anmin kyara.
Ni kawai sonki nake dan zuciya ta harbu.
Da’ace zakiyi shagawaba ni zan miki bambu.
Fadamar sanyi kika so na hada miki lambu.
Kanki zan iya dambe koda hannu ba kambu.
Tausaya min agaza min kada kiyi min bore.
Na aiko sakonnin so karda ki share.
Na rasa ki masoyiyata a dole na zare.
Shi dafin so naki da wuya taya zan jure.
Kalmomin da kike min nake yin hadda.
A kwakwalwata na aje su zamar mini shaida.
Bani in baka sone ba ya yin tsada.
Nai sabo dake sonki zuciya ya huda.
Ki tuna ni dake kowa tare ya ganmu.
Hanta da jini tilas sai an barmu.
Nayi kuka kwakwalwa sonki yake damu.
Nazarina aure naki a taya zan samu.
Babu laifi dan ni ke dai nayiwa kishi.
Ko kallon ki naga wani yanai sai na tsaneshi.
So ya danne ni a sa’in da kyar zanai nishi.
Kinji sakona ina fatan zaki karbeshi.
mKarki bari ya zamanna inayin kuka.
Ni masoyine kanki kamar zan hauka.
Ki gina min sharuddai naki kawai na dauka.
Tunda kaunarki nake babu dare ba rana.
Ajikina na ke jin kina saurarena.
Abar kaunata kin tsaurata alwashina.
Mafakar ruhi kaunarki tana ta gudana kanki ni na zaqu daure ki zamo gatana.
Ina fatan wataran ki kirani habeebi.
Zanji dadi mai sona ko bayan raina.
Koda ace a duniya ba numfashina.
Da kin tuna wanda kike so ya zamo ni daina.
Lyrics by hameesu breaker.

Lokacin da sakon ya shigo wayar maryama tana kwance sai faman juyi da kulla wasikar jaki take yi ita kadai, janyo wayar tayi cike da kasala,ganin sunan hamma jay yasata bude sakon…Maryama ta karanta content din yafi sau goma ta karanta ta sake yayinda take jin kanta kamar tana yawo cikin gajimare tsabar yadda kalaman suka shiga har cikin zuciyarta, ayyanawa take a ranta wannan kalaman daga bakin attajirin mai kudi ya fito ma’ana dream husband dinta wayyo dadi kan dadi kenan dan turo baki tayi gaba duka ita kadai tunowa da hamma jay ne ya turo mata ba wannan mai kudin ba, rungume wayar tayi a kirjinta ta sake fadawa duniyar tunanin da ta saba, da haka bacci ya kwasheta, a bangaren jabeer ma yayi ta jiran ganin ko zata mishi reply amma shiru har dare ya raba haka ya saduda ya rungumi pillow yayi baccin wahala.

Washegari da ya kasance alhamis maryama ta gama aikace aikacenta da ta saba dan ma yanzu aikin ya ragu mata tun randa hamma jabeer yayi magana su fatima suke wanke wanke da diban ruwa, itako yawanci daga sharar tsakar gida da gyaran dakuna wataran da wanke bayi shikenan aikinta.dakin su ta nufa da sauri dan ta riga da ta gama yanke hukunci jiya da dare jiran wayewar gari kawai take yi ta aiwatar,wayar ta ta janyo mai kyawun gaske kirar samsung wanda hamma jay ya siya mata koshi wayar dake hannunshi bata kai girman nata ba,contact ta shiga ta fara laluben lambar siyama.

Siyama kawata ce amma ba sosai ba dan ta girme ni da akalla shekaru shida zuwa bakwai, farin jinin mutane da nake dashi ne ya hadani da ita saidai ko kadan innarmu da hamma jay basason alakata da ita a cewarsu idonta ya bude da yawa kuma gidan su ba gidan mutunci ne ba,wannan ne yasa na dan fara jan baya da ita,siyama tana yawan fada min idan ina neman taimakonta akan komai kar inyi shakka in tambayeta kawai,ba laifi tana da budaddun idanu kam dan yanzu haka ma babban shago take dashi na saida suturu irin na mata kala kala mutane da dama ganin karuwa suke mata dimin kowa yasan iyayenta talakawa ne gashi ita kuma tana juya miliyoyin kudi cikin lokaci kadan….Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na iso kan lambarta ina tunanin anya abunda zan aikata daidai ne kuwa? da sauri na kauda tunanin daga raina na danna mata kira na kara a kunne na,…Muryar matar nan ta mtn ce ke sanar dani bani da kati a wayata,wani dogon tsaki naja da zan kama matar nan ta mtn Allah ne kadai yasan abunda zan mata,kwata kwata na manta banida da kati, to dama wa garen da zai samin kati duk wanda yazo da dan maikon shi sai baffanmu yace anmin miji shikuma mijin da ake hankoron anmin din sai yayi leburanci an sammishi before ya zo ya sanmin, kaico na! ni maryama.

Bani da zabi fache in turawa siyama ‘please call me,’hakan kuwa nayi in the hopes that she will respond, tagumi nayi ina jiran kiranta patiently, it was only a few minutes,but it was the longest waiting in my life,wani irin zabura nayi lokacin da naji karar wayata alamar kira yana shigowa…

By

Ummu Fadeela.

EPISODE O6

…..Da hanzari na daga wayar na kara a kunnena hadi da fadin “hello”

Daga daya bangaren siyama tana murmushi tace “yau wace rana maryama ta tuna da ni, dan dariya nayi nace “haka zaki ce kenan? dariyan tayi itama tace “what’s up babe? naji muryarki wani iri,ajiyan zuciya na sauke nace nothing much siyama,i really want to see you,”….hope all is fyn kina cikin damuwa ko”cewar ta, yake nayi nace all of the above yanzu dai kina ina, dan fasali taja kafun tace “ina boutique nawa,” ohk ina zuwa nan da 30 minutes insha Allah.

Kiran da naji innarmu na kwalo min ne ya tsaida ni daga shirin da na fara na fita da sauri abun karin kumallo ta nuna min banyi musu ba na dauki plate mai dauke da dafaffiyar doya da kuli kuli ko arzikin mai bai samu ba sai kofin bakin shayi na juya, sosai hakan ya ba innar mu mamaki ganin yau ban turo baki ba amma sai bata ce komai ba… A daddafe na tura doyar rabin yanka daya kana sauran na tura shi kasan gado, gwara shayin shikam na shanye tas dan innarmu ta iya dafa bakin shayi irin na yan nijar, doguwar rigar material kalan milk na saka kana na dauko jilbab dina shima har kasa na zura na dan feffesa turare sama sama na fito ina tunanin karyar da zanyiwa innarmu kamun in fita, da sallama na shiga dakinta nadan durkusa nace “innarmu zan shiga wurin umaimah da akwai wani littafi da zamu duba tare da ita,”

Ba tare da tunanin komai ba tace “ki gaida mun da ummar ta su.” da ” to” na amsa ina jin dadin yadda ban samu matsala ba wurin fitar.Saidai ina sako kaina kofar gida idanun hamma jay ya shige cikin nawa tamkar dama jiran fitowa ta yake.wani irin faduwa gabana yayi amma sai na dake na shige gidansu umaimah badan raina ya so ba…Mintuna ishirin na kwashe a wurin umaimah da na same ta babu lafiya tana kwance ribb,amma duk da haka ummar su ta jibga mata uban wanke wanke wai sai ta wanke su tsabar rashin tsoron Allah, zan iya cewa tunda nake ban taba ganin azzalumar kishiyar uwa irin ummar su umaima ba,duk saurin da nake haka na tattare jilbab nawa na fara wanke kwanukan yayinda ummar ta ke ta banka min harara da fadin gwara da kika taimaka mata don ko uban ta ne yau bai isa ya hanata wanke wadanan kwanukan ba” ko kala bance ba don nasan halinta ba Allah a ranta, da sauri sauri na ke aikin don in samu in tafi.Haka na fito bayan na gama wanke wanken badan na soba sai dan kar in makara zuwa wurin siyama,koda na fito maimakon inbi kudu wanda zai kaini har boutique nata sai kawai nabi arewa duk don in gujewa hamma jabeer saidai banyi taku goma lafiyayyu ba call nashi ya shigo wayata, tsaki naja a raina nace ko kafi kuda naci bazan dau kiran nan ba,aiko kamar yaji abunda na fada ya ringa kira ba tsayawa wani na yankewa wani na shigowa keke napep na tsayar ba tare da nabi takan kiran da ya ke ta shigowa ba saida na zauna mai kyau na sanar da mai keken inda zai kaini kamun na daga kiran na kara a kunnena.

Wani irin ajiyan zuciyar da naji shi har cikin kwanyata hamma jabeer ya sauke, da breaking voice yace “damn it!baby ina kika yarda wayarki?”.

Ina hararar wayar nace “sorry hamma jay wayar tana silent ne shiyasa ban ga kiranka ba”.

“Ina kika tafi yanzu”

“Zan karbarwa umaimah magani a pharmacy ne yanzu bata jin dadi”

“Ohk ki kula min da kanki plsss kar wani ya gane min ke, ko inzo in rakaki”?

Na yi saurin fadin “a’a kayi aikinka ai babu ma nisa nan nan nefa, concentrate on your work plss ko so kake oga zubairu yayi fushi, yanzu zan dawo ma ai,”na fada da saurin da inda a gabanshi nake sai ya fahimci karya nake mishi tsabar yadda jikina ke rawa.

Jabeer ya shafa kanshi yana lumshe idanu murya kasa kasa yace “I love you pretty”.

“Uhhmm” nace kana na katse kiran ina hararar wayar tamkar shi yai min laifi,…Lokacinda na iso na iske siyama tana tare da costumers suna siyan kaya, dan haka na ja gefe na samu plastic chair na zauna har ta sallamesu kafun ta juyo gare ni cikin fara’a ta kama hannuna zuwa wani dan corner dake cikin shagon mai dauke da kujeru guda biyu masu kyau sai center table a a tsakiyar kujerun bissmillah zauna ta fada tana wucewa jikin wani karamin fridge dake wurin, zama nayi ina karewa haduwar shagon siyama kallo,yanzu duk wannan uwar dukiyar nata ne babu mai kwace mata Ya Rabbi ka dubeni.

Maganarta ne ya katse min tunani na ba tare da nasan ta iso wurin ba,”hey girl,you look so worried and tensed me ya ke faruwa ne?.

Ta fada tana tsiyaya fanta mai sanyin gaske cikin glass cup wanda take raba ya cika har bayan cup din,turo min tayi gabana tare da wani bowl shima na glass mai dauke da crispies mai dan yawa a ciki, duk da yadda yawuna ya tsinke hakan bai hana ni kauda kai ba ina kallonta nace “nagode,” na cigaba da fadin “siyama ina cikin damuwa matuka kinsan burina na son yin karatu mai zurfi alhmdullillah I passed my WAEC in flying colours,saidai kinsan iyayena are not financially enough dazasu iya daukan nauyin karatuna.

Rumtse idanu nayi ina jin ciwon abunda zan fada cikin zuciya ta, na daure naci gaba da fadin, “would you believe wai aure za’amin da hamma jay? hakan na nufin gaba daya mafarkina ya zama zero,siyama bazan boye maki ba,zamana ina ganin mahaifana cikin talauci ba karamin kona raina yake ba,haka kuma bazan amince in taso cikin talauci kuma inyi aure cikin talauci ba, can you imagine kwanakin baya baffanmu fom na tailoring school ya kawo min? plsss siyama i need help, i want you to help me da babbar sana’ar da zanyi inbar garin nan inje inyi karatu in zama successful woman abun kwatance.”

Ajiyar zuciya siyama da tayi tagumi tana kallona pitiefully ta sauke sannan tace,”kwarai na tausaya maki maryama I feel your pain also, talauci babu kyau babe,…”Dan numfashi taja kafun ta cigaba da cewa,”Mutane da yawa kallon karuwa suke min, wacce take saidawa maza jikinta domin ta samu kudi,ganin wannan dan shagon da motar da nake hawa da gidan dana ginawa iyayena,saidai sam ba haka bane maryama.”

Duk da ban yarda da maganarta ba amma hakan bai hanani gyada kai na ba alamar gamsuwa,…

Taci gaba da fadin, “akwai wani mai gidanmu wanda saurayi na ke aiki a karkashinsa nima ta dalilin saurayin nawa na saba dashi, yana aiki ne a yankin naija delta……Sai kuma ta matso kusa dani sosai ta min maganar a kunne sannan ta matsa baya tana dan murmushi da fadin aikin baida wani hatsari in kin amince yanzu zan kirashi nasan zai taimaka miki.”

Without thinking twice na gyada mata kaina dan a wannan lokacin tamkar a cikin teku nake duk abunda aka mika min domin ya ceto ni kamawa zanyi koda ko wuka ce mai kaifin gaske…..Dariya tayi tace “that’s my girl,just give me a moment bari inyi magana dashi”.

Mikewa tayi tana taku daidai domin matsawa daga kusa dani, yayinda nabi bayanta da kallo cike da sha’awar hadaddun kayan dake jikinta,…Daga inda nake ina iya hango yadda bakinta yake motsawa tana magana cike da yanga,haka kawai na tsinci kaina da son jin me take fade cikin wayar saidai duk yadda naso hakan ya gagara domin kasa kasa take maganar,after like ten minutes ta katse wayar ta dawo kusa dani tana fara’a hannuna da suka sha jan kunshi ta kamo tace,” You are a lucky girl maryama, munyi magana dashi yace zai shigo adamawa ran friday kuma sunday zai koma,so all what we have to do now shine muyi kokari ku hadu ran saturday kuma zai sauka ne a 10 STAR HOTEL a jimeta,yanzu bansan ya za’ayi kije jimeta daga nan ba? kina ganin za’a barki a gida?.”

“Ba wannan maganar siyama,wa kike ganin zai barni in tafi jimeta a gida, ai saidai kawai in sati hanya inje ba tare da sanin kowa ba.”

“Anyway, ki fito da wuri ranar asabar din sai ki biyo ta nan muga yadda za’ayi daga nan in baki contact nashi, and abu mai muhimmancin daya kamata in sanar miki shine,don’t tell him your real age, idan ya tambayeki shekarun ki kice masa 23, ohk?.

“Meye ma’anar hakan?, na tambaye ta sounding confused…Just do as i say maryama” gyada mata kai nayi na tafi zuciyata na ta tsalle wani sashi na zuciyar na gargadina yayinda wani sashi yake karfafa mini guiwa.

Allah ya taimakeni lokacin da na dawo gida ban tarda hamma jay a waje ba a gida ma Innarmu tana bayi haka na shige kamar munafuka…Na kwashe yinin ranar ina tunanin yadda zan tafi yola ba tare da kowa ya sani ba a gida a bangare daya kuma na kagu asabar tayi domin ina ji a jikina mafarkina na rayuwa mai inganci ya kusa tabbata. “Shin zaki bijirewa iyayenki ne da kuma wanda ya sadaukar da rayuwarshi akanki saboda duniya ne maryama?anya kinyi tunani mai kyau kuwa? zuciyata ce ta tuna min hakan, rumtse idanu nayi da karfi hadi da matse pillown dake hannuna, ji nayi kaina na sarawa da karfi karfi…

Misalin bakwai na dare bayan nayi sallan isha na sake tambayar innarmu zuwa duba jikin umaima dan tana tsaye min a rai…Koda na shiga jikin nata da dan sauki saidai still tana kwance.

Kwance na sameta har lokacin tana fama da zazzabi,

“to uwar iya yi me kuma ya kawo ki cikin daren nan?,muryar umma ya katse min hanzari daga kokarin zama da nake yi, na bude baki da niyyar bata amsa umaimah ta girgiza min kanta cike da tausayi saman fuskanta, tunda umaima ta taso take shan gallazawar kishiyar uwa sakamakon rasuwar mahaifiyarta ita kuma umma bata taba haihuwa ba don haka take zuba mulki a gidan son ranta ko baban umaima idan taga dama sashi aiki take yi kuma bai isa ya tanka ba.Sallamar da kanwar ta basira tayi ne yasa ta juyawa da fara’a suka shige daki da kanwar tata.

Kwafa nayi na zauna hadi da tagumi, abubuwa sun min yawa a yan kwanakinnan,.

Kallon tsaff umaimah ta min tace cikin muryar marasa lafiya, “pretty meke damunki? you look so dull.” numfashi na sauke,banyi mamaki da umaimah ta fahimci akwai damuwa tattare dani ba,dan bama boyewa juna komai amma yau kam dole in boyewa umaimah sirrin dake raina don ko giyar wake nasha bazanyi gigin fadi mata decision dana dauka ba.

“Uhmmm ina jinki,karki ji shakkan fadi mani komai don na saba jin abubuwan mamaki kala kala a wurin ki maryama”cewar umaimah da ta kureni da idanu tana jiran jin abunda zan ce.

Yaken dole nayi nace “wai me kika gani ne? nifa ba abunda ke damuna, its just a mood swing, sai kuma halin da kike ciki da wannan uwar taki mai bakin halin tsiya, Allah dai ya kaimu ki yi aurenki ki huta da wannan rayuwar na kunci da takaici,kana gidan ubanka amma ka kasa rawar gaban hantsi” na fada ina dan dariyar da iya karshi saman lips nawa.

Umaimah tace “da dai bansanki bane saikice mood swing amma indai maryamar dana sani ne,then there most be something fishy, sannan halin da nake ciki kuma ai wannan ya riga da ya zama jiki maryama ni har abun ya daina damuna yanzu, nasan komai lokaci ne with time zata chanza insha Allah, ta fada da rauni cikin muryar ta…duk bama wannan ba,dazu karyar me kika bankawa hamma jay dan ya shigo,zaro ido nayi hadi da mikewa ina buga kirjin da bansan ma na aikata ba,cikin zaro ido nace” ya shigo umaimah?me kika ce masa to?.”

“Relax mana yan mata, yace kince masa umma ta aike ki karbo min magani a pharmacy”.

Da sauri nace “eheemm me kikace masa ke kuma”?

“Cemasa nayi karya ne ba wanda ya aike ki, kuma ma ai shima ya san umma dai bazata ce a siyo man magani ba”.

Hannu na daura aka nace “shikenan kin kashe ni umaimah,yanzu idan hamma jay ya tutsiyeni da tambaya sai ya gano gaskiya, innalillahi wa’inna ilaihiraji’un nake ta maimaita wa….Nasiha sosai umaimah tamin kamar dai yadda ta saba kullum,zuwa yanzu kaina ya dade da yin haddar nasihohinta sai dai bana amfani dasu duk da cewa wataran ina ji a jikina cewar gaskiya take fadamin,shigowar innarmu ne yasata katse maganar da take yi, innarmu ta mata sannu da jiki sannan tace mu koma gida dare yayi,har nakai kofar fita umaimah ta kira sunana cikin sanyin murya, a natse na juyo muka hada idanu fuskata dauke da tashin hankali,tace “ban fadi masa komai ba”.

Wani irin ajiyan zuciya na sauke na bi bayan innarmu da sauri….Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi asabar tayi,kwana biyun nan na kwashe sune cike da zullumin abunda zai faru da yadda zanyi in tafi yola ba tare da kowa ya ankare ba,aikace aikacen dana saba nayi hamma jay kuwa na gefe sai faman daga karfen mota yake tamkar Allah ne ya aikoshi ya jike sharkaf da zufa…Dan satan kallon shi nayi ina mamakin yadda lafiyayyen jikinshi ke ta shekin daukan ido ga gargasa kwance gwanin sha’awa amma sabanin fuskarshi da yayi bakikkirin,kanne min ido daya yayi gami da dage gira bayan mun hada ido, kasa kasa yace “morning my pretty angel, ki kalleni yadda kike so am all yours”

Wani irin kunya ne ya lullubeni kenan hamma jay yasan ina kallonshi, hooo what a shame….Wanka nayi bayan na gama share sharen da na saba,na shigo daki na goge jikina da xani na musamman dana adana dan goge jiki bayan na fito daga wanka, lotion dina na jergens mai dadin kamshi na mulke ilahirin jikina dashi kana na shafa roll on a armpit dina na dauki body spray na vivelle da kuma bakhour na feshe jikiina dasu suma, take dakin ya bade da kamshi Na nufin gaban akwatuna na dake jere na bude daya ina tunanin kayan da zan saka,fitar na musamman ne don haka dole kayan da zan saka ya zama na musamman.

Karshe dai bayan na gama ruwan ido wasu riga da siket na atamfa na fitar mai kalan dark pink and brown touches na bude akwatin inners dina na dau pant bra da under wear su na fara sakawa sannan na saka atamfata da ta zauna min dasss tamkar a jikina aka dinka, gaban mirrow na na koma ni ba mai cika kwalliya bace a fuska,dan haka dan farar hoda na murza a hannuna na goge face nawa dashi sai chapette dana gogawa lips nawa nadan gyara eyebrow da eyelashes dina da mascara, nan na fito gwanin sha’awa turaren rasasi na fesawa jikina kana na ajiye kwalbar ina karewa kaina kallo jikin mirrow ba karamin kyau nayi ba…Wani tunani ne ya fado min cikin kaina yanzu duk abunda nayi amfani dashi kama daga sabulun wanka har zuwa sutara da kayan kwalliya da dangin perfumes dana shafa duk hamma jay ne ya siyamin fa, kai hatta wannan mirrown da nake ganin kaina a ciki shi ya buga min a wurin sana’arshi, “anya maryama”

Da sauri na kawar da tunanin ina barin wajen,jakar islamiyyata na sauke na cusa gogaggen gyale na pink colour a ciki kana na dau hijab din islamiyyata da ya kasance har kasa na zura a jikina na dauko nikab na daurawa fuskata flat shoe bakake na sanya na rataya jakata na fito kirjina na dukan tara tara.

Wani kallon da ya haddasa min kadawar yan hanji innarmu ta banka min, tace “ina kika nufa da wannan farar safiyar dan nasan dai lokacin islamiyyar taku baiyi ba, ko yau kuma sabon salo kika bullo dashi?”

Agogon dake daure tsintsiyar hannuna na duba,inna lillahi na furta a kasan makoshina, ashe bakwai ma yanzu ta cika,what i have done ni maryama?.

Amm…emm…In. Innarmu “rufe man baki cewar innarmu ganin sai kame kame nake yi”kin shige kin jira abun karin kumallo ko sai na make ki jai’ra kawai,nasan don ki gujewa dumamen tuwon ne yasaki shiryawa da wuri, to sai ki fadan gidan uban da zakije ki karya da asubahin nan,”

Nannauyan ajiyar zuciya na sauke ina barin wurin ganin inda innarmu ta dosa…A daddafe naci dumame yanka daya nasha koko inajin tamkar zanyi amai,amma don kar in makara yasa naci na fito ina dan kame kame nace da innarmu “zan wuce”.

A tsanake ta dubeni tace “wai saurin na meye haka yau?.”

Cikin saisaita nutsuwata nace “ina so in shiga wajen umaimah ne inga ya ta kwana da jiki, kuma kinsan zata rike ni innarmu gashi banson yin latti”.

Bayan na fito ko kallon kofar gidan su umaima banyi ba, na sake nikab nawa na tsaida keke napep na shiga ban zame ko ina ba sai boutique na siyama, zaune na tarda ita tana jiran isowata,

“Wow babe!you look just a pretty you are,cewar siyama lokacinda na zame nikab da hijab dake jikina, da hanzari na yafa gyale na wanda ya rufe min har kan mazaunaina,ina blushing nace “stop whining me abeg,” dariya siyama tayi tace “serious kinyi kyau sosai,act classy acan maryama plsss koda shike bani da damuwa da wannan na sani”turaren bondage ta dauka ta kuma fesheni da shi sannan ta dau wani jaka samfurin gucci dake rataye jikin rack na jakankunan siyarwarta ta jefa turare da lipbalm sai chewing gum da kudi 5k a ciki ta rataya min a kafadata,tace manage with this”.

With much suprise nake kallonta kafun inyi karfin halin cewa “amma banida kudin da zan biyaki wannan siyama”.

‘”Karki damu ba sayar miki nayi ba kyauta na baki”cewar ta.

Ita tamin rakiya har inda na hau mota kafin ta koma, kirjina ne keta tsalle lokacinda na gyara zama cikin motar, wannan shine first time da zan tafi wani gari ba tare da sanin iyayena ba, shin anya nayi daidai kuwa? anya ban kauce hanya ba? sai karfe sha biyu na rana muka iso yola wani napep na kuma tsayarwa na mika masa papern da siyama ta rubuta min address na bako na.

Bakin wani tangamemen hotel dan sahun ya tsaida ni, daga kai nayi naga an rubuta 10STAR hotel jikin wani allo, jikina ba kwari yayinda kafafuna ke rawa na nufi hanyar shiga hotel din,ya salam wannan shine karo na farko a tarihin rayuwata da ni maryama zan shiga hotel koda ko wani iri ne,duk inda nabi idanun mutane ne ke yawo akaina kamar sunga bakuwar hallita, da kyar na kai kaina reception na samu wuri na zauna ina sauke numfashi kamar wacce tayi gudun famfalaki.dama siyama ta fadi man cewa idan nazo in sanar da ita sai ta sanar dashi, hakan kuwa nayi na sanar mata isowata.

Daya daga cikin waitress dake wurin ne ta matso hadi da tambayata,”first time here ma’am?.”

Daga mata kai nayi kafun nace “yes”.

Tace “kina bukatar oda ne kodai jiran wani zakiyi”?

Nace mata “jira zanyi,amma ina bukatar ruwa mai dan sanyi”.

Yess ma’am” cewarta kafun ta juya ta kawo min ruwan gora mai sanyi da kuma glass cup akan tray godiya na mata ta juya ta tafi, gyara zama nayi na tsiyaya ruwan kadan cikin cup dan am very thirsty,sipping ruwan na fara kadan kadan kamar bana so…,I waited patiently is not too long amma a wurina ji nake tamkar nayi awanni zaune wurin. kamar ance in daga idanu na na hango shi ya shigo wurin,wani irin bugawa zuciyata yayi take ruwan dake bakina ya kauce hanya ya nemi fita ta cikin hancina…..
💫MARYAMA💫

  By

Ummu fadeela.

      FREE  BOOK📚

Episode 07.

……Walking slowly ya nufo inda nake ba tare da ya daina kallona ba, da sauri na tsugunnar da kaina kasa ina kokari saisaita nutsuwata da yake shirin kubce min yayinda kirjina ke bugun tara tara,siyama bata ce man haka yake ba na dauka zanganshi katon gaske bakikkirin mai katon ciki tunda tace mai gidan sairayin ta ne, saidai sabanin tunanina,…Babba ne akalla zai kai shekaru talatin da biyar ko ma fiye da hakan, shi ba baki ba kuma baza’a ce masa fari ba,dogo ne kadan amma hamma jay ya fishi tsayi da kuma fadi kodon hamma jay yana daga karafuna ne?.sanye yake cikin wasu tsadaddun suit black colour kallon farko idan ka mishi zaka fahimci arziki ya zauna a jikinsa kyakkyawan sajensa zuwa kan dan karamin gemunsa na gayu ya taimaka wurin fitar da kyawun bakar fuskarsa….lokacinda ya matso gab da ni zuciyata ce ta nemi shigewa cikin cikina hannunshi duka biyu ya daura saman teburin dake gabana ya dan rankwafo kadan yana leka fuskata kamar mai son gano wani abu..,da kallo few mutanen dake reception din suka bimu.

Cikin low voice yace “maryama i guess!”.

Dago kaina nayi karaf idanuna suka shiga cikin nashi da hanzari na janye nawa idanun na mayar dasu kasa ina jijjiga masa kai kamar kadangaruwa.

Dariyar shi mai kyau yayi yace “ai ni legend ne wurin guessing abu” hannunshi daya ya miko min yana kokarin zama yace “I am Sadeeq.

Matse nawa hannayen nayi a tsakanin cinyoyina ba tare da na dago kaiba nace “nice name”….Thank you yace yana maida hannunshi ganin banda niyyan bashi nawa hannun, zama yayi a kujerar dake fuskantar tawa ya daura hannayenshi bisa kumatunsa yana min kallon kurilla,murya kasa kasa yace “wani ya taba fada miki cewa you’re beautifull?”.

Gabana ne ya fadi dan ba wanda ya fado man a rai a lokacin sai hamma jay, kusan kullum sai yace min ” ke kyakkyawa ce maryama”.

Kawar da kaina nayi daga kallon da yake min kamar sabon maye nace “i heard that for a million times”.

Jinjina kai yayi yace “add with mine,you’re very very beautifull”. Na gode na fada jikina yana yin sanyin da ban san dalili ba.

“Anyway,siyama ta fadamin dalilin zuwanki, but you look younger than i expect, shekarunki nawa? ya tambayeni,siyama tace min kar in fada mishi ainihin shekaruna but me amfanin karyar shekarun? me hakan zai kare ni dashi? cikin rawan harshe nace mishi 17 almost 18.

“You are young,too young.Kinsan dalilin zuwanki nan? sam wannan business din bai dace dake ba kinyi kankanta sosai, bazan iya dealing da childinesh and drama da zaki min ba while working “

Wani irin bugawa kirjina da gabana sukayi lokaci guda, take wasu hawaye masu zafin gaske suka cika man idanu suna kokarin saukowa, da dabara na maida su ina jin duniyar tana juyamin tamkar ina cikin gajimare.

Waitress Sadeeq ya yafito ba tare da ya kula da halin da na shiga ba,da hanzari ta taho hadi da ajiye mishi menun dake hannunta, kallon menu din yayi for few second kana yace “table water for me, and fried rice with pepper chicken and soft drink for bakuwata.

Juyawa tayi tana fadin “yes sir”.

“Banajin yunwa” na fada cikin muryar da ya bayyana halin da zuciyata ke ciki.

Kallona yayi kadan yace “duk wanda yazo wuri domin ni ki tabbata baya tafiya haka ba tare da yaci wani abu daga gareni ba, hope you get it pretty?.”

Wani irin dagowa nayi jin sunan daya kirani da “pretty”oh Ya Rabb.Save me.” na fada domin sak ya koma min hamma jabeer.

Bayan kamar minti biyar saiga ta ta dawo dauke da wani dogon tray tazo ta ajiye a gabanmu plate mai dauke da hadadden fried rice da yaji vegetables ta ajiye gabana sai wasu bowls guda biyu daya cowslow ne ciki dayan kuma pepper chicken ne da kallo daya na mishi na ji ya tono min yunwata na kusan shekara daya spoons ta ajiye bisa wani dan kyalle mai daukar hankali,sai drink din ta jere hadi da bottle water sai tissuen dake tsakiyar teburin da ta gyarawa zama, tana murmushi tace min “enjoy your meal ma’am ta juya ta bar wurin.

Tsiyaya ruwan da ta ajiye masa yayi yakai baki ba tare da ya daina kallona ba yace “kici abinci ki koma gida zan sanar da siyama cewa you are too young for me,bazaki iya aikin nan ba”.

Hawayen da nake ta kokarin boyewa ne suka samu nasarar gangarowa bisa kumatuna, duk sanda yace nayi karama nakanji tamkar guduma ya buga min a kahon zuciya ta,shikenan dama shine last hope dina to shima na rasa shi, ban ankara ba ashe kuka nake yi sosai yayinda sadeeq kuwa yayi tagumi yana kallon ikon Allah. A ranshi yace “you see,wannan shine abunda nake gudu dama tayi karama sosai gashi nan yanzu daga magana dai harta fara min kuka.”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “yanzu me na kuka?kodai so kike ki tara min jama’a?”

Goge fuskata nayi cikin sheshshekar kuka nace “nothing sir, ina kuka ne dan na rasa damata,.”

“Wani irin dama kenan?”.

Ya tambayeni sounding so pissed off.cikin nutsuwa na fara bashi labarin yadda na gama candy na da sakamako mai kyau, kana na daura da labarin burina na son ci gaba da karatu zuwa matakin jami’a…Ina goge hawaye na nace “sir sai dai iyayena basu da karfin daukan nauyin karatu na zuwa gaba,dan haka suka fara shirin aurar dani ga dan uwana shiyasa na yiwa siyama hirar ita kuma tace akwai wadda ta sani da zai taimakamin da haka ne ta hada ni da kai, gashi kaikuma kace bazan iya business din ba so dole inyi kuka, dama kai ne last hope dina yanzu idan na koma aure za’ai min and thats the end of my hobbie,my dream,my passion,my ambition. And the end of me also”.na fada ina fashewa da kukan da ya kara janyo hankalin mutane zuwa kanmu.

Tunda na fara magana yake kallona with much interest a labarin da nake bashi, saida na kai karshe sannan ya dau hankerchief ya goge goshinsa duk da ba zufa yayi ba,bude baki yayi cikin maturity yace “Sad, very sad, na tausaya miki matuka,amma yanzu gogen hawayen haka nan crying moody gal”

Cike da zolaya ya fadi hakan yana mika man hankin dake gabanshi,amsa nayi na goge fuskata.

Dan fasali yaja sannan yace “a matsayin yata ko kanwata zan taimake ki, for now kije kiyi magana da parents dinki duk yadda kuka yi you let me know ni kuma i will help you daga kan naira daya har zuwa million goma matukar zakiyi karatu ki amfani al’umma,shi karatun ya mace ai yana canza al’umma ne domin itace tarbiya matakin farko, so kije ku tattauna saiki sanar dani duk yadda kuka yi.”

Wani irin farin ciki nake ji marar misaltuwa, ji nake kamar in tashi inyi ta tsalle a wurin tsabar farin ciki,ina kuka ina dariya duk ni kadai “cikin zumudi da tatin farin ciki nace “na gode sir, Allah ya sa farin ciki a rayuwar ka kwatankwacin yadda kasa ni a ciki,na gode Allah ya kara budi mai albarka”.

Sadeeq dai ya tallabi chin nashi sai kallonta yake, da alama kallon yarinyar yana bashi nishadi don ta iya drama sosai, murmushi yayi yace “ba godiya a tsakaninmu dukda cewa yau na fara ganinki, ina respecting mace mai son yin ilimi a kowanne bangare na rayuwa,and don’t call me sir again, call me sadeeq ohk?

Jinjina kai nayi nace “thank you sir, aww sorry am ehhhm..Yayaaa.”

Dariya yayi yace “das you, yanzu kici abinci sai ki koma gida kar dare yayi, now bari inje masjid don azahar yayi, har ya mike sai kuma ya juyo ya kalleni yace “ko inzo muci tare”?

Da hanzari na kalleshi dan yanayin maganganunshi suna min yanayi da na hamma jabeer, dariya ya kuma yi wanda na fahimci shi ma’abocin dariya ne , yace “Iam just kidding pretty”.

Tafiya yayi ya barni da sakakken baki, tsabar excitement kasa shan ko da ruwa nayi a wurin dukda yadda raina ya biya da abincin dake zube gabana… A haka ya dawo ya same ni ina ta kulla wa da kwancewa na yadda wannan al’amari zai kasance ba tare da iyayena sun gane ba.

Duk yadda yaso inci wani abu ki nayi daga karshe dai waitress din yasa tamin takeaway na abincin.ta mika min badon na so ba na amsa nace “na gode”.k

Ya amshi wayata yasaka nomba dinshi yayi saving sannan yayi dialing zuwa wayarshi yayi saving tawa,yana kallona yace “idan kin iso gida we will talk,.Jakata na dauka da kuma fancy ledan da aka samin takeaway a ciki nace ‘most grateful sir, ahh sorry yayaa”.

Murmushi yayi yace “nice meetig you maryama hannu ya miko min wai muyi musabaha na noke kafada ina turo baki” a daidai lokacin kuma wayata tayi kara, da sauri na fitar daga jaka naga hamma jabeer ke kira gabana ne ya fadi ganin karfe uku saura minti biyar, inna lillahi na furta gami da sa wayar a silent, karfe uku ai lokacin tashi islamiyya yayi gaba daya na sha’afa gashi ko sallan azahar banyi ba, ganin mood dina ya sauya sadeeq yace “yaya dai ko daga gida ake kiranki?”

Nace “eh, sunga na dade ne bari inzo in wuce”.

Jakata ya kama ya cusa min wani abu a ciki yace “take care sai na jiki a waya”.

Tsunkuyar da kai nayi inajin bugun kirjina yana sauya wa,…har na kai bakin get na fita daga hotel din ban daina jin idanunshi a kaina ba, hakan yasa na juyo ilai kuwa yana tsaye ya kafe ni da ido, murmushi ya min bayan mun hada ido ya daga min yatsunshi guda biyu yana karkada su,murmushin na mayar masa na fita da sauri, saida na tabbatar na bar area din sannan na bude jakata dan ganin abunda ya jefa man a ciki, ,…Zaro ido nayi gami da dafe kirji na shiga uku ni maryama note na yan dubu dubu na gani a ciki, “dubu dari” na fada ina kara fiddo idanu na waje, da sauri na tare keke napep jikina yana karkarwa na shige nace ya kaini tasha,ya zanyi da kudi har dubu dari? nasan tawa ta kare idan innarmu ta kamani da kudin nan, ya zanyi dasu yanzu? siyama ce ta fado man a rai dan haka na danyi ajiyar zuciyar samun relief, wayata na kuma dubawa naga miss call na hamma jay kusan goma, “dan wahala” na furta a bayyane har mai napep din ya juyo yana kallona…A park din nayi sallar zuhr da asr kafun motar dana shiga ta cika muka dauki hanya ina ta addu’ar Allah yasa mu iso kafun a tashi islamiyya.

Munyi nisa a tafiya amma gani nake kamar dreban baya sauri yayinda agogon hannuna ya nuna min karfe hudu da rabi, saura mintuna talatin a tashi a islamiya… inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, gaba daya mutanen cikin motar suka furta ciki kuwa harda ni,lokacinda tayar motar mu tayi wani irin kara dukkan mu mun rude Allah ya taimaka motar ta tsaya cak ba tare da ta fadi ba,cikin hanzari muka fito daga motar kowa yana gode wa Allah daya takaita mana bamu fadi ba.

Tayar ta pashe cewar direba, na duba gaba na duba baya gabas da yamma kudu da arewa ba alamar gari muna tsakiyar jejin Allah, na shiga tara yanzu kam dan yafi uku ga wani uban yunwan da nake ji kuma na kasa cin abincin daje hannuna kamar wacce aka hanata, kiran hamma jabeer ne ke ta rige rigen shigowa wayata shima n kasa dauka dan kar ya gane akan hanya nake, muna ta tsaye har karfe biyar ya cika mai motar mu bai dawo daga gari na gaba da ya jr neman mai gyaran taya ba, kamar hadin baki kuwa duk motar da ya zo wucewa a cike yake da pasinjoji.

Zuwa lokacin tashin hankalin da na ke ciki baya misaltuwa, idanuna sunyi jawur har wani zazzabi nake ji yana neman rufeni, sai bayan wasu minti talatin din direban ya dawo yana ta bamu hakuri akan dadewar da yayi, nan suka hau gyaran da ya kara kaimu wasu minti talatin din wanda yayi daidai da karfe shida da minti uku.

Duruwa mukayi a motar bayan ya tashi muka miki hanya, kiran umaimah ne ya shigo, jikina yana rawa nake kallon kiran amma na kasa dauka, wani kiran ya kuma shigowa wannan karon daga innarmu still na kasa dagawa sai hamma jabeer again sai kuma innarmu wani da layin baffanmu sai kuma layin umaimah, Inna lillahi, shikenan yau tawa ta kare ni maryama Alla ka dubeni, shine kawai abunda nake maimaitawa a raina har muka iso gombi wurin karfe bakwai na dare a lokacin an fito sallar isha shagon siyama na nufa bayan mun sauka ina jin kafafuna kamar zasu kada ni,still nayi a wajen na daura hannu aka ganin shagon a rufe, wayata na daga na shiga neman layinta unfortunately a rufe,” kin kashe ni siyama” na fada hawaye na gangarowa bisa face dina yanzu ya zanyi in koma gida da gyale da jakar nan da kuma wannan uban kudin? bayan ansan da hijab na fito har da nikab da kuma jakar islamiyya.,ganin ina kara bata lokaci yasa jiki na rawa na tsaida wani napep din na shiga, a kofar gidanmu ya sauke ni na shigo hawaye yana bin fuskata yayinda karkarwar da jikina keyi ya tsananta, da kyar na sa kai tsakar gidanmu, ina tattare siket nawa gami da damke jakar dake hannuna kamar kace kyet in zura da gudu.

Da hamma jabeer muka fara hada ido, sai safa da marwa yake a tsakr gida hannayeshi goye a bayanshi,duk da dare ne hakan bai hanani ganin yadda fuskar shi ta sauya kamanni ba idnaunshi sunyi jawur, daga gefe kuma innarmu ce zaune tayi tagumi sai su salima da fatima jaune suma sunyi jugum jugum,kana baffanmu yana kishingide bisa tabarma sai umaimah da ta hada kai da guiwa tana sheshshsekar kuka.

Cikin wani irin takun da ya sa cikin juyawa hamma jabeer ya nufo ni gami da fadin “pretty” da karfin da ya janyo hankalin sauran mutanen gaba daya suka mike tsaye har baffanmu dake kishingide….
💫MARYAMA💫

Free Book.

Na

Ummu Fadeela

Episode 08.

“Maryamaaa!”ya fada da karfin da ya janyo hankalin sauran mutanen zuwa kaina, tashi baffanmu yayi daga kishingiden da yake, innarmu ma ta mike ta nufo inda nake yayinda salima da fatima suka zo suka rungume ni da gudu,tsananta rawa jikina yayi sakamakon kallon da innarmu ta ke min kamar yau ta fara sani na, a hankali ta juya ba tare da tace min komai ba tana share hawayen da ya gangaro mata da bakin zani.

Salima tace “antinmu ina kika je kikasa innarmu tana ta kuka ita da anti umaimah, gashi anje islamiyyarku bakya nan, fatima tace “ehh anje islamiyyarku mu’allim yace bakije ba yau, shine hamma jabeer da baffanmu sukayi ta yawo ba a ganki ba, kuma ana ta kiran wayanki yana shiga baki dauka, salima ta kara amshe zancen da fadin “kuma hamma jabeer ya kara fita nemanki shine ya dawo da hijab naki da kuma nikab da jakar islamiyarki,sai kawai anti umaima ta fadawa innarmu wani magana shine suka kama kuka dukkansu”.

Wani irin zufa ne ya shiga karyo min cikin jikina, yayinda idanu na suka zazzaro waje kamar wacce ta hadiye kunama,damke yaran nayi sosai ina jin kamar zan bar duniyar ne, banyi aune ba naji tarwatsewan ledan dake hannuna,gaba daya abincin dake ciki yayi pieces a kasa yayinda bottle watern dake ciki yayi wani irin gangarawa ya tsaya dab da kafar hamma jay dake tsaye ya goya hannuwanshi a baya,duk tsiyarka bazaka karanci expression dake kan fuskar shi ba,goran yabi da kallo kana daga bisani ya dago kai yabi fried rice da kuma naman kazar da ya yi dai dai a kasa, sai kuma ya maida kallonshi kan fuskata zuwa jikina dake makyarkyata kamar an jika dan akuya kana jakar dana damke da iya karfina dan kar shima ya tarwatse.

Kamo umaima dake kuka innarmu tayi cikin sanyin muryar da ban taba sanin ta da irin shi ba tace “umaima tashi kije gida hakanan kinga ai ta dawo ko? kuma lafiya kalau ta dawo ba abunda ya same ta, kinga harda abincin yan gayu sabbin iyayenta masu kudin suka sai mata,wanda mu bama bata ir….Kasa karasawa tayi sakamakon rawar da muryarta ya fara, umaima dake rawar ,zazzabin da tashin hankalin batan maryama ya tsananta mata shi tace “kiyi hakuri innarmu,kuskure ne kuma ba wanda baya kuskure, zata gyara Insha Allah, don Alla kiyi hakuri innarmu”.

Ta fada tana hada hannayenta wuri daya,juyawa tayi ta shige daki ta barsu a wurin, baffanmu ma baice komai ba ya tashi ya shige dakinsa saidai da ka ganshi kasan yana cikin matsanancin damuwa.

Taku umaima tayi zuwa wurinta tace “why maryama,?why,why? meyasa kika aikata haka,?kina ganin wannan shine rayuwar da zai fishsheki? meyasa meyasa? ta fada da karfi tana hawaye,ba tare da na bata amsa ba itama ta juya ta fita daga gidan.

Hannu na daura aka zan zunduma ihu amma nayi saurin toshe baki na,”meyasa suka min shiru?meyasa kowa yake shigewa daki ya barni,? hamma jabeer ne ya matso kusa damu har na fara jin dadin cewa zai min magana amma sabanin tunani na cewa yayi yana kallon fatima “fati samo tsintsiya ki kwashe wannan ki kai bola,”ya nuna mata abincin da ya zube nan kasa kama hanyan dakinshi yayi shima ya barni nan tsaye,da sassarfa nabi bayanshi jikina na rawa nace “Ham..mm.ma j..ay plssss”

Wani irin juyowa yayi idanunshi sunyi jajur kamar garwashin wuta,na kuma gathering courage nace “hamma jay ba y….Wani irin dunkule hannu yayi da karfin gaske yace “bullshiiiiit”.

Hannuwa biyu nasa na toshe kunnuwa ta kana na tsugunna da sauri ina jiran jin saukan duka dan na gama sadakarwa, amma sai naji ya kaiwa randar innarmu na kasa wanda ke kusa damu bugu da kafarshi, take kuwa randar ta bule ruwan ciki ya fara zuba a kasa, cike da mazantaka ya juya ya shige dakinsa ya barni nan durkushe.

Da rarrafe na shiga dakinmu ina jin tamkar duniya ta juya min baya, tamkar kowa ya tsaneni,me yasa baza su duba burina ba,me yasa bazasu yi la’akari da abunda nake so ba, (niko nace anya kuwa maryama?.)

Ajiye jakar danake damke dashi tun dazun nayi ina bin hijab da nikab dina dake ajiye kan gado da kallo, waya dauko su daga shagon siyama? me ya faru? banida mai bani wannan amsar,zama nayi bakin gadon na zuba tagumi ina jin wani irin yunwa tana azalzalata gashi banyi sallan maghrib da isha’i ba.

Dago labulen dakin akayi innarmu ta shigo fuskar nan tata ba alamun annuri, wani irin juyi nayi sai ganina nayi tsaye karshen dakin ina zare idanu,calmly tace “dawo nan ki zauna” ta na nuna min inda na tashi,jiki na yana karkarwa nace “don girman Allah innarmu kiyi hakuri wllh b..”dawo nan ki zauna nace” ta fada wannan karon a dan fusace,

Ko motsi banyi daga inda nake ba sai mazari da jikina keyi yayinda zufa ya gama yimin wanka.

A fusace innarmu ta finciki jakar dana dawo dashi tana kokarin balle hannun jakar wanda ya kasance chains ne,hannu na daura akai na kurma ihun da yayi daidai da watsewar gaba daya kudin dake cikin jakar yayiwa innarmu wanka daga sama har kasa.

Bin kudin da ya watse daidai ya cika dakin tayi da kallo gabanta na faduwa sannan ta dago ta kalleni tace “maryama,karuwanci kika fara?”

Da sauri na durkusa kasa still holding my hand on my head nace “wllh innarmu bana karuwanci wallahi Allah kenan, shine ya samin cikin jakar”.

Shi wa? inji ta.

Sai lokacin na tuna baran baramar da nayi na fara zare ido bance komai ba.

Fita a dakin innarmu tayi bayan kamar minti daya saigata ta dawo da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu,tuni na saki fitsarin da na ke ta faman matsewa, without thinking twice tayo kaina gadan gadan ba abunda nake yi sai ihun neman agaji tun dorinar bai sauka jikina ba,sai dai duk ihun da nake ba wanda ya kawo min agajin.

Zabga min dorinar tayi a gadon bayana wani ihun na kuma yi da wannan karon nayi imanin cewa duk anguwar mu ba wanda baiji ba sakamakon wani azabar da ya ziyarci kwakwalwata,…duka na take yi duk inda ta samu bata ji bata gani a take na fita haiyacina ina kiran sunan baffanmu hamma jabeer suzo su taimakeni,.

Mikewa jay dake kwance rub da ciki yayi ya fito ya shiga dakin da gudu,wani irin sufa yayi ya kamo dorinar dake hannun innarmu ya rike gam kana yayi kneeling a wurin yana bata hakuri ganin yadda jikin maryama ya parpashe sai digan jini yake yi, a fusace tace “Ka sake bulalar nan ko sai na hadaku duka na zane lusari kawai”.

Ba tare da ya sake ba yace “kiyi hakuri innarmu for the sake of Allah kiyi hakuri dan Allah kiyi hakuri” rokonta yake amma bakin shi rawa yake yi ga hawaye har ya cika idanunshi abunda innarmu bata taba gani ba”.

Fisge bulalan tayi tace barni in kashe ta kafun ta kashe mu gaba daya ci gaba da labtar maryama da zuwa lokacin ko motsin kirki bata iya yi, kukan ma ta fara kasawa,ganin da gaske innarmu zata kashe ta ne yasa jabeer fadawa kan maryama dake kwance ranga ranga ya kankameta tsam a kirjinsa,yana fadin Ah ah ah innarmu bazata kara ba kiyi hakuri bazata kuma ba, idanunta ya rufe bata ganin gabanta sai zabgawa jabeer dake rungume da maryama dorinar take tana cewa “ka matsa ko in hada da kai”.

Rike bulalar akayi ta baya innarmu ta juyo da sauri ganin wanda ya rike dorinar yasa ta durkushewa kan kafafunta tana tsiyayar da hawaye,calmly baffanmu yace “dijah duka would not be a solution to kangararrun yara saidai ma ya kara lalatasu,ki bar dukanta haka nan”.daga haka ya fita ba tare da ya kara cewa komai ba,duk da azabar da na ke ciki hakan bai hana kalaman baffa dukan kirjina ba so yanzu na zama kangararriyar yarinya kenan, inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Bin bayan baffa tayi zuwa dakinshi ta same shi zaune bakin gadonshi hannunshi daya dafe da goshinsa daya kuma yana rike da wayar dake kare kunnensa bayan dan lokaci kadan ya fara magana a wayar “barka da dare dada,ya mutan gidan da kowa,dama ina son sanar muku ne na yanke auren yaran nan zuwa sati biyu masu zuwa,sai a sanar ma sauran yan uwa.

Daga haka ya yanke wayar ba tare da ya jira jin abunda dada zata fadi ba.wani irin sayi innarmu taji a bayyane ta furta “Alhamdulillah”.

Karar da wayata tayi na shigowar kira ne ya sa hamma jabeer sassauta rikon da ya min kamar zai maida ni cikinsa duk da tsananin azabar da na ke ciki bai hana ni jin yadda zuciyar sa ke bugawa kamar zai balle ya fado kasa ba kana makwogoronsa sai hawa da sauka yake da sauri sauri…tashi yayi yana rike da hannuna ya ajiye ni bakin gado, sai a lokacin ya kula da kudaden dake watse tsakar dakin juyowa yayi zaiyi magana wayata ta kara daukan tsuwwa,daukar wayar dake yashe gefe yayi sakamakon faduwar dayayi lokacin da innarmu ta balla jakar.

“Sadeeq?” ya furta yana kallon screen na wayar, tabbas da ina da iko da na karbe wayata jin sunan daya ambata amma inda nake ko yatsata bazan iya motsawa ni kadai ba,Picking call din yayi ya kara a kunnenshi a hankali na lumshe idanu na ina jiran bomb din ta pashe,dan nasan yau kam ta kasance bakar rana a cikin rayuwata,…Daga daya bangaren sadeeq relaxing yayi kan makeken gadonshi dake dakin hotel din cikin low voice jin anyi picking call din yace,

“Hii pretty, fatan kinje gida lafiya? nayi ta kiranki baki dauka ba duk kin tayar min da hankali hope all is fyn? naji dadin yinin yau tare dake matuka.”

Jabeer baisan sanda wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa ba,bin wayar yayi ya durkushe bisa guiwarsa,kana ya dunkule hannunsa biyu ya naushi kasan carpet din,jan da idanunsa sukayi yana karuwa tamkar zaiyi tartsatsin wuta, jijiyon wuyansa suka fito rado rado, da karfi yace “Noo maryama,nooooooo don’t do this to me,nooooooooo.Wani kiran ne ya kuma shigowa a harzuke ya daga wayar ya maka ta da bangon dakin take ta rabe biyu,yace “what the heck?”

Ficewa yayi daga dakin da sassarfa ba tare da ya juyo ba, gaba daya ahalin wannan gida yadda suka ga rana haka suka ga dare idan ka cire salima da fati, bacci kauracewa idanun jabeer sukayi yayinda yake jin ciwo a zuciyarsa don sautin bugunta ma ya sauya haka kuma yana yawan jin faduwar gaba cikin lokaci kadan zazzabi mai zafi ya rufe shi amma yayi ta karfin hali da jarumta, a bangaren maryama ma zazzabi mai zafin gaske ne ya lullube ta sai rawar sanyi takeyi daga inda take zaune, da kyar na iya kwanciya a gefe guda tsabar yadda jikina yayi tsami duk yadda naso lulluba kasawa nayi sai shivering nake yi.


Washe gari da kyar jabeer ya fita sallar asubahi ana idarwa kuwa ya dawo ko azkar bai tsaya yi ba, duk kaunar shi ga daga karfe kuwa yau ko inda karfen yake bai gani ba ya shige daki ya kudundune a bargo…,kafun karfe bakwai jikin maryama ya rikice ba shiri aka kwasheta sai asibiti dan ba karamin tsanani jikinta yayi ba, tuni jabeer ya wartsake ganin abar kaunar sa tana halin mutuwa ko rayuwa.

Emergency aka karbe ta likitoci suka rufu a kanta don ceto rayuwar ta sakamakon daukewar da numfashinta yayi,saida suka kwashe akalla awanni uku a kanta kana daga bisani aka makala mata oxygen tube dan taimakawa numfashinta da kuma karin ruwa kana aka kaita female ward akayi admitting nata,.

*.

Zare siririn farin gilashin dake makale saman fuskar sa likitan yayi yana kallon baffanmu da kuma hamma jabeer dake zaune gabanshi tsananin tashin hankali kwance saman fuskar su, dan goge zufar dake tsatstsafo mashi yayi sannan yace yana kallon baffa,

“Sakamakon binciken da muka gudanar,mun gano cewa patient namu tana fama ne da…..”

Shiru yayi yana kallon su daya bayan daya, cikin kaguwa hamma jabeer da idanunsa suka yi jajawur kamar gautar da ya sha rana yace,

“Kamana bayani mana dacta ka tayar mana hankali fa”

Karkada kai likitan yayi sannan yace,”kuyi hakuri ba wata cuta da ta sauka duniyar nan face da maganinta, ita jinya jarabawace idan akayi hakuri aka ci jarabawar za’a samu result mai kyau, patient nawa dai tana fama ne da kidney diaseas, duka kodar ta biyu sun kamu da cutar dole tana bukatar dashen koda wadda ya zama wajibi a mata cikin lokaci kadan idan ba haka ba komai na iya kasancewa”.

Wani irin zabura hamma jay yayi ya mike tsaye yana kallon likitan bakin shi na rawa yace,

“Dr. You mean…Maryama…Kana nufin..Maryama ta ce kidney dinta ya samu damuwa?…

💫MARYAMA💫

        By
   Ummu fadeela.

Episode 09.

….Janyo shi baffa yayi zuwa kan kujerar da ya tashi, shima cikin rudanin yace,

“Jabeeru kwantar da hankalinka mana dan ya mana karin bayani”.

Likitan yace,” ku kwantar da hankalin ku baba, matukar aka mata dashe cikin gaggawa zata tashi lafiya kalau kamar ma bata taba ciwo ba, da ace daya ne ya samu damuwa zamu iya cire shi, a bar mata daya domin dan adam yana iya rayuwa da koda guda tamkar kowa amma duka biyu sun tabu so dole yanzu muna bukatar cire su duka cikin gaggawa a dasa mata wani, hakan kuma zai faru ne ta hanyar samun wani ko wata da zai sadaukar mata da kodar shi guda daya,karku manta kuma muna bukatar shine cikin gaggawa dan tana cikin hadari matuka.”

Rike kai baffa yayi da hannu biyu sakamakon wani irin sarawa da kan nashi yayi,cikin nutsuwa irin ta dattijai masu mutunci yace,

“Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allahumma ajjirni fi musibati wa akhlifni khairan minha,ya rabbi ka dubi baiwar ka”.

“Ni zan bata nawa kodar”.

Da sauri baffa ya dago kai ya kalli inda maganar ta fito,jabeer ne zaune idanunshi sun kada jajir jijiyar kanshi sai harbawa take yi dil,dil,dil.

“Kwarai kuwa zan bata,zamu raba nawa kodar da ita baffanmu” Jabeer ya kuma fada yana kallon baffa da ya tsare shi da idanu.

Gyaran murya likitan yayi yace,

“Baba kuna bukatar yin shawara a tsanake irin na family, amma karku dauki lokaci mai tsawo”

Fitowa sukayi daga ofishin suka durfafi inda innarmu da daada ke zaune dukkansu sun rabka uban tagumi,daada ne ta fara ganinsu dan haka ta mike har tana tuntube tace,

“Ya ake ciki? Me dactan yace game da jikin takwarata? duk kunmin shiru kuna kallona,cewar daada ganin baffanmu da jabeer sun sadda kai kasa.

“Wai ba magana nake bane kuka min shiru,wato ga sabuwar yar iska ko,…Shiru tayi tana kallonsu sai kuma ta daura hannu aka ta rusa ihu tana fadin mun shiga uku Alhassan kodai mutuwa takwara tayi.? inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un,cikin tashin hankali ta kuma fadin,”wai ba magana nake yi bane?.

Da kyar baffa yayi karfin halin cewa,”kiyi hakuri daada, bata mutu ba amma……Nan ya kwashe duk yadda sukayi da likitan ya fadi mata, a rikice innarmu da tunda suka fara maganar take binsu da ido kawai ta mike duk yadda taso yin magana ta kasa sai rawar da jikinta keyi da bakinta tana nuna hanyar ward din da maryama ke kwance da hannu.

“Saidai jabeer yace zai bada nashi daya a sanya mata” cewar baffa da ya ci gaba da magana.

Sassauta wa daga kukan da take risga kamar babu gobe daada tayi,baki galala take kallon baffa kafun tace,

“Ban fahimta ba,me jabeeru zai bayar alhassan?.

Baffa yace, “cewa yayi shi zai bada tasa kodar guda daya a dasa mata”.

“Karku maida ni sakarai shashasha mana, ina sam ba wannan maganar, so kuke in rasa jikokin nawa duka biyu lokaci guda? ko baku da hankali ne ne kam banda labari, jabeeru shi kadai Allah ya mallakawa abokin tagwaicinka alhussain kafun Allah ya dauki abunsa kuma shidinma dana ke gani inji dadi a raina saiku salwantar min dashi? ina sam ba Allah a ranka,ni na taba ganin inda aka cire kayan cikin mutum kuma ace ya rayu? ah ah wllh tunda uwata ta haifeni ban taba gani ko ji ba sai yau” Daada ta fada tana fyace majina da bakin zaninta dake kokarin faduwa.

“Ko da ace bazan rayu ba matukar maryama zata tashi nizan sadaukar da tawa rayuwar domin ceto tata,zan iya bada rayuwa ta dominta daada”.cewar jabeer da kallo daya zaka masa ka fahimci alamun fitar haiyaci a tattare dashi.

Baki galala daada ke kallonsa cike da madaukakin mamaki, yayinda innarmu da kafafunta suka rasa garkuwar su nan take tayi baya baya kana tayi zaman dirshan a wurin, saidai kafun daada ta samu zarafin cewa wani abu suka hango wata nurse ta fito daga dakin da aka kwantar da maryama a guje ta nufi ofishin dr.

“Your attention dr.” Cewar nurse din bayan ta shiga office din…A dari da tamanin su daada suka bi bayan likitan da kuma nurse din ganin sun shige dakin da maryama ke kwance.

Juyi take ta faman yi hadi da murkususu akan gadon rike da gefen cikinta tana fadin,

“Wayyo innarmu zan mutu, baffanmu cikina, hamma jay!mutuwa zanyi wayyo cikina,”…duk inda imaninka yake idan kaga yadda maryama take yi sai ka zubar mata hawaye a lokacin.

Yan dube dube dactan yayi sannan ya dago ya dubi su baffa yace, “lallai ana bukatar yi mata aikin cikin gaggawa”.

Ya juya da niyyar barin dakin, daada ta kamo hannun farar labcoat nashi gami da fadin, “ah ah naga ikon Allah, dannan ba kai ne zaka shuka mata kodar ba?ai baka ga ta tafiya ba,gadai dan uwanta yace shi zai bada tasa a yanke a shuka mata,in gaya maka da uban shi da uban ta ciki daya suka zauna mahaifa daya suka fito dashi duniya, to ai kaga dan ya taimaka ya bata nashi ba laifi yayi ba ahto, zuciyar uban garesa, gashi shi kadai Allah yaba uban har ya bar duniya bai samu wani ba, sai kuma ta fashe da kuka cikin kuka take fadin Allah sarki sukuma haka tasu kaddarar tazo na rayuwa da koda daya daya,tana kallon jabeer tace maza jabeeru jeka a ciro a zo a shuka mata kaga dai halin da take ciki,kai kuma ubangiji ne kadai yasan da me zai saka maka wllh dan kayi shahadar da ba ko wanne mahaluki ne zai yi ba, yanda dai zumunci yayi karanci a zamanin nan yan uwa duk sun zama yan banza kamar ana ganin hanjin juna”

Murmushi likitan yayi yace, mama ba shuka wa ake fada ba,dashe zaki ce”.

“A haap kaji zancen kawai”cewar daada, yo me marabar dambe da fada yaro?”

Jabeer da yake jin wani irin farin ciki ya matso likitan yace, dr muje a duba abunda ya kamata dan kamar muna kara wasting time ne a nan”. Hakane muje a maka gwaje gwajen da ya kamata.”


Hamma jay zan mutu wayyo hamma jay cikina, karka tafi karka tafii karka tafiii,shine kawai abinda maryama ke maimaitawa tana ta faman murkususu ta jike jagab da zufa.

Jabeer dake zaune a kan farar kujerar robar dake gaban gadon da ta ke kwance baisan sanda bacci ya kwashe shi ba sakamakon baccin da bai samu ba daren jiya, kamar a mafarki kamar a gaske yake jin sautin muryar maryama cike da galabaita tana kiran sunanshi da fadin zata mutu karya tafi.Da sauri ya bude idanunshi da suka rine saboda dan baccin da yayi da kuma tashin hankalin da ya ke ciki suka haddasa masa,Tashinsa yayi daidai da wani irin kara da maryama ta saki kana ta mike zaune daga kwancen da take tana fadin hamma jayyy.

Babu shiri ya kamota ganin yadda ta rude, ya sassauta murya yace, “pretty gani nan kusa dake mi ne ne?.

Murya can kasan makoshi tace, “hamma jay zan sha ruwa.”

Da azama ya cika ta ya nufi inda bag na pure water yake cikin kayan da ya koma gida ya taho dasu hospital din,.

Binshi nayi da idanu mafarkin da nayi yana dawo min sabo,…shekara tara kenan cifff yanzu da hamma jay ya sadaukar da kodar shi guda a gare ni sakamakon rashin lafiyar da nayi fama dashi lokacin ina yar shekara tara a duniya inda likita ya tabbatar da kidney dina duka biyu sun harbu da cuta dole sai an cire min an min dashen wata,.

A lokacin ba abunda bai faru ba,amma daga karshe anyi aikin cikin nasara,ma’ana yanzu koda daya hamma jay keda shi ta sila ta,saidai sam moment din yaki gogewa daga kwakwalwata,its always fresh as new saidai idan ban kwanta ba sai nayi mafarkin abunda ya faru a baya.

Ruwar da yake kokarin bani a baki ne ya dawar dani daga duniyar tunanin da na fada, hannunshi daya yasa ya tallabi keya ta daya hannun kuma ya sa min ruwa a bakina dashi,banyi musu ba na amsa na sha kadan gami da janye kaina gefe.

“Ki kara kadan” ya fada da shakakkiyar muryarsa da ya sani dagowa muka hada ido,he look so worried and tensed amma hakan bai hana shi sakar min murmushi ba ya na kokarin gyara min kwanciyata sannan ya koma kan kujerar da ya tashi ya kuma lumshe madaidaitan idanunshi cike da tarin damuwar da ke kwance saman fuskar sa.

Kure shi da kallo nayi gami da tilastawa kwakwalwata son nemo min hujja da dalilin da ya sa zuciyata bata son auren hamma jay,saidai duk iya nazari na na kasa fahimtar komai,jabeer saurayine son kowa kin wanda ya rasa, bawai iya kasancewar sa cikakken namiji ba,yana dauke da wani baiwar da ba kowanne namiji ke dashi ba,gashi dan gayu duk da talaucin da ya masa tarnaki hakan bazai hana ka fahimtar cewa jabeer ya iya gayu ba da son kamshi.

Shafa gefen cikina na yi bangaren da kidney dina yake, take sadeeq ya fado min a rai, wani irin murmushi ne ya kubce min,jay ya fishi kyau da kuma kuruciya,amma shi kuma yafi h.Jay dukiya that’s what I want,turo baki nayi gaba cikin kunkuni nace
“To me ya sa shi h.Jay din bazai nemi kudin ba ya tara su kamar na sadeeq mai kyautar dubu dari daga haduwar farko?”.
(Hmmmm,maryama kowa yana rayuwa ne akan tubalin kaddararshi.)

Kallon shi na kuma yi still idanun shi a rufe yayi matashin da kan kujerar da ya ke a kai,cikin murya kasa kasa da banyi zaton zai ji ba nace,

   "Hamma jay!".

Ga mamakina dagowa yayi ya daura min jajayen idanunshi mai tattare da rudani cikin nawa idanun,…Daburcewa nayi na fara inda inda da kyar na iya cewa “hamma jay, abunda ya faru jiya b…..Hannu ya daga min cikin tsananin fushin da bai kasance dabi’ar shi ba yace,

“Plsss maryama not here, you’re sick I don’t want….Sai kuma yayi shiru ya kara maida kanshi yayi relaxing hadi da rufe idanunshi yana jin zuciyar shi na mishi zafi, baison tuna abunda ya faru jiya, he could’nt believe prettyn shi ce taje wurin wani kato har wani gari,its hurt.It really hurt him to the extent da ko tunawa yayi sai kirjinshi ya harba.

Binshi na yi da kallo,wannan ba hamma jay din da na sani bane ba,wannan is something else dake tattare da fushi da kuma damuwa mai tsanani saidai duk da fushin da ya ke dani hakan bai hanashi zama dani a asibiti ba yana bani kulawa,

“Is this what pure love means?”

Bude baki na kuma yi nace, “innarmu bata zo ba ko?.Har muryata ta fara rawa.

Ba tare da ya dago ba ya daura yatsarshi manuniya saman labbanshi gami da furta,

    "Shshsht".


   **********************

Cike da dumbin mamaki sadeeq yabi wayar tashi da kallo bayan ya sauke daga kunnenshi,kamar muryar namiji yaji yana magana,sake kiranta yayi yana fara ringing ya katse ya kuma kira wannan karon a kashe yaji wayar sakamakon rotsa wayar da jabeer yayi a jikin bango.

Juya akalar kiran yayi zuwa ga siyama, bugu daya ta dauka tamkar dai wacce take jiran kiranshi dama da hanzari tace,

“Hello yallabai” ba tare da ta jira amsawar shi ba ta ci gaba da magana muryar ta cike da tashin hankali, “ina fatan dai maryama ta dawo? dan yau naga tashin hanakali a rayuwa ta badon Allah ya takaita ba da yau a hannun yan sanda zan kwana”.

Yamutsa fuska sadeeq yayi yana shafa gefen fuskarshi yace,

“I don’t get you lady”.

Tace, “dazu bayan sallan azahar kwatsam yayanta yazo shagona wai ana neman maryama ba’a ganta ba, kuma anje islamiyyarsu duk bata nan,ina kokarin cewa bata zo wurina ba kawai yaga jakan islamiyyarta a wurin shine fa ya tayar man da hankali wai sai na fito da ita kai baka ga haukan da yayi a wurin ba da kyar na gudu.”

Mikewa daga kwancen da yake sadeeq yayi yana ci gaba da yamutsa fuska kamar mai magana da abun kyama cikin dan fada fada yace,

“Mi ki ke nufi ne? dama iyayenta basu san ta fito bane?.”

Sai a lokacin siyama ta ankare da baram baramar da tayi amma sai ta waske tace,

“No, yallabai, kawai dai dan uwan nata ne baisan bata nan ba amma iyayenta sun sani.”

Duk da bai amince da maganar ta ba amma sai ya basar cike da bada umarni yace,

“Ohk go check her now, ta bar wurina tun da dadewa and make sure kin hada ni da ita a waya da zaran kin iso”.

Jiki na rawa siyama ta amsa da “to yallabai”.Sannan ta yi tagumi tana kokarin auna maganganun sadeeq,koma dai menene bazata iya zuwa gidan su maryama yanzu ba dan abunda jabeer yayi a shagon ta dazu daidai yake da abunda mayunwacin zaki zai aikata idan ya hadu da dabbar dawa….Kiran layin maryama ta yi saidai switch off matar mtn take ta maimaita mata, daga karshe shawaran da zuciyar ta ke bata tabi, inda ta bada tazaran mintuna talatin sannan ta kira sadeeq.

Yana zaune tsakiyar gadon shi dake hotel room din ya tisa wayar shi gaba yana kallo amma a zahiri ba kallon wayar yake ba yayi nisa cikin tunanin da yake, murmushi yayi mai dan fadi har hakoranshi suka bayyana sakamakon tunawa da kukan da maryama ta sakar mishi dazu cike da yarinta, “Yarinya ce” ya fada yana kara fadada murmushinsa,sai kuma ya shafi gefen fuskar sa kana ya dan bugi kanshi da karfi a zahiri yace,

“Why are you care sadeeq?” still shi kadai ya kuma cewa, “Yes why am I even worried?”.

“Musamman dan kai tazo”,wani sashe dake zuciyar shi ya sanar dashi, kiran siyama ne ya katse masa zancen zucin da yake yi, bai jira yayi bugu biyu ba ya daga da hanzari ya kara a kunnenshi,murya kasa kasa kamar sabuwar munafuka tace,

“Yallabai naje gidan nasu yanzu kuma na samu ta dawo, wani irin ajiyar zuciya sadeeq ya sauke da yasa siyama matsar da wayar daga kunnenta ba shiri,

“Hang the phone to her”

Shine abunda taji ya fada, da sauri ta mayar da wayar kunnenta tace,

“Yallabai akwai matsala bazai yiwu tayi magana yanzu ba dan yayan nata ya kasa ya tsare yanzu ma makewayi na shiga”.

“Ohk ki sanar mata lallai lallai ta kira ni anjuma”

“Insha Allah sir, ta fada tana sauke numfashi bayan ya katse wayar shi…Tunanin yadda za’ai tayi reaching maryama take amma ta rasa mafita Dan ba wanda ta sani a anguwar tasu sai wannan kawar maryama mai idanu zubin na munafukai umaimah.

     *************

A ranar aka sallamo maryama daga asibiti dan jikinta da sauki dama zazzabi ne da dukar da innarmu ta mata ya haddasa mata,har aka sallameta innarmu bata zo ba hamma jay kuma bai kara mata magana ba duk da bai matsa daga kusa da ita ba har ruwan da aka daura mata ya kare. Adaidaita ya tare masu suka koma gida amma ko ci kanki innarmu bata ce mata ba, sai ma hararar hamma jay da take yi da fadin ka juri wulakanci ai”.

Bayan da baffanmu ya dawo kasuwa ne yayi kiran jabeer ya sanar dashi ya fara shiri nan da sati biyu za’a daura auren shi da maryama,..

Tsunkuyar da kai jabeer yayi yana jin zafi cikin zuciyar shi yayinda wani daci ke biyo makwogoranshi zuwa kan harshen shi yace, baffanmu ina gan…..
💫MARYAMA💫

               by

      ummu fadeela

typing📲

EPISODE 10.

  FREE BOOK.

Yayi kasa da kai yace, “baffanmu ina ganin…”

Dakatar dashi baffa yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin fada yace,

“Mu muka haife ku, ba ku kuka haifemu ba, dan haka wannan umarni ne nake baka ba shawara ba,kaje ka fara duk wani shiri da zaka yi nanda sati biyu za’a daura muku aure dan bazan zuba idanu ku bata min zumunci ba, na riga da na sanar ma daada ita kuma zata sanar da mutan nijar gaba daya, tashi ka bani waje mutumin kawai.”

Tunda baffa ya fara magana jabeer yake jin kanshi kamar yana yawo a sararin samaniya, ya rasa farin ciki zaiyi ko akasin hakan,maryama ta riga da ta zama wani bangare na rayuwar shi,ta zama jinin dake gudana cikin jijiyoyin jikinshi,rasata daidai yake da faduwar bangon da ya ke jingine da, amma abunda ta aikata jiya yasa ya fara tunanin an…..

“Tashi ka bani wuri” muryar baffa ya katse mashi tunanin da yake yi.mikewa yayi har ya nufi hanyar fita sai kuma ya dawo ya shiga dakin shi,girgiza kai kawai baffa yayi tare da fadin “Allah ya kyauta.”

TUSHEN LABARI....

Alhassan da Alhussain tagwaye ne kuma kyawawan buzaye yan asalin jamhuriyar nijar cikin gundumar kancha, garin da jama’ar cikinta suka yi kaurin suna wurin fita ci rani zuwa kasashe daban-daban cikin afirika,musamman nigeria,algeria,senegal da kuma libiya.

Alhassan da alhussain sun taso ne cikin maraichi domin mahaifinsu mal.Amadou ya rasu tun suna yan shekara daya a duniya, sai mahaifiyar su maryamou wacce suke kira daada, sunsha gwagwarmayar rayuwa sosai dan mal. Amadou bai bar musu komai ba face gona guda daya da shima gadon sa yayi wajen mahaifinsa,… ganin wahala ya masu yawa ne yasa daada bin ayarin mata masu fita ci rani inda suka yada zango a kasar libiya, ba karamar wahala suka sha ba cikin sahara kafun su iso saidai basu wani jima a can ba suna bara gwamnatin libiya tasa aka kwaso su zuwa gida nijar, wannan kalubale yasa daada bata kara bin ayarin masu fita ci rani ba ta rungumi yayanta hadi da kama kananan sana’o’i da noma gonan su na gado,ba laifi tana samun na rufawa kai asiri da haka yan biyunta suka taso har suma suka fara fita neman na kai.

A lokacin da suka kai shekaru goma sha biyar ne suka nemi izinin daada dan fita ci rani! bata musa mu su ba tace, “kuje Allah ya bada sa’a” da wannan suka shigo nigeria inda kaddara ta hankado su zuwa adamawa suka fara neman na kai.Alhassan ya fara saida ruwan jarka, shiko Alhussain wankin takalma yake wani lokaci yana hadawa da yankan farce, ance mai nema yana tare da samu. cikin dan lokaci Allah ya sawa sana’ar tasu albarka, suna samun na rufawa kai asiri suna kuma turawa daada mahaifiyar su wani abu,idan damuna ta kankama ko sukan koma nijar ne suyi noma.

Da haka har suka zama samari sosai masu zafin nema ilai kuwa suna samu.daga baya suka fara sana’ar saida danyen kayan miya kasancewar inda suke kayan miya yana wucewa sosai,.

A wani zuwa da sukayi noma a nijar ne Allah ya hada jinin Alhussain da wata cousin dinshi ramatou suka fara soyayya mai cike da tsafta,nan daada ta rasa inda zata jefa kanta tsabar dadi da farin ciki, zaunar da su tayi ta nuna wa Alhassan ma ya zama wajibi ya fitar da mata a hada su duka rana daya tunda dan uwanshi ya samu, Baiyi gardama ba amma ya barwa daada zabi, a cewar shi ta zaba mashi duk wacce ta mata.

Sosai daada taji dadin wannan karramawa da dan nata yai mata,ta zabo mashi wata zukekiyar budurwa itama dai buzuwance dijah diyar wanta duk dai na gida dinne, da ya ke gaba daya talakawa ne kuma dangi daya ba,asamu sabanin fahimta ba,cikin lokaci kadan aka sha shagali angwaye suka tare da amaren su cikin dakuna falle daddaya da aka shafawa farar kasa a cikin gidansu, da alkawarin idan damuna ya kare zasu dawo nigeria da matayen su.

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah.bayan watanni uku da biki matar Alhussain ta fara laulayin ciki,a kayi rashin sa’a kuwa cikin yana bata wahala sosai dan ba abunda take iya yi sai kwanciya wannan dalilinne yasa da suka tashi dawowa nigeria daada tace a barta sai cikin yayi kwari saboda wahalan hanya.

Hakan ko akayi alhassan da matar shi dijah da kuma alhussain suka tattara suka dawo, nan gidan da suke hayan dai basu chanza wani ba,…a can nijar kuwa ramatou tayi fama da jinya har dai cikin yayi wata bakwai sannan ta dan fara gane kanta, yayin da dijah matar Alhassan kuma har zuwa lokacin ko ɓatan wata bata taba yi ba, kusan kullum sai daada tayi korafi har ma ƙorafin nata ya zame wa dijah jiki…

Lokacin da cikin ramatou ya kai wattani tara, wani dare ta fara nakuda mai matuƙar wahala wanda ya dauke ta awanni masu yawa har wayewar gari ana abu guda gaba daya ta fita a hayyacinta harta kai ta kawo ba ta gane wanda ke kanta, duk wata ungozoma dake wannan ƙauye tazo ta gwada dabararta amma haihuwa ya gagara ga kuma naƙuda na zuwar mata da wuta wuta, daga ƙarshe dai aka yanke shawarar kaita asibiti a garin da ke kusa da su kasancewar basu da asibiti a wancan lokacin.

Da taimakon Allah da dabarun likitoci ramatou ta haifo santalelen danta kyakyawan gaske jinin buzayen asali,kallo daya zaka mashi kaji ya shiga ranka.sai dai ko juyawa bata yi ta kalli wannan yaro ba Allah ya amshi ranta sakamakon jijjiga da ɓallewar jini da ta samu, drs din sunyi iya kokarin su amma sun kasa ceto ta dan kwana ya kare…ba karamin tashin hankli alhussain da dan uwanshi suka shiga ba yayinda labarin ya riske su hakanan suka dau hanyar nijar cike da tarin alhini mai tsayawa a zuciya,wani ikon ubangiji kuma shine suna akan hanya suka yi hatsari inda mutane da dama suka jikkata wasu kuwa suka rasa ransu, cikin wadanda suka rasu harda alhussain…Allahu Akbar.daada taga zallan tashin hankali lokacin da aka shimfide mata gawar Alhussain a gaban ta,tayi kuka har hawayen ta suka kafe.daga karshe ta fauwalawa mai duka, wanda yake bamu ba tare da yayi shawara damu ba, kana ya kan dauki abunsa duk lokacin da ya so ba tare da yayi shawara da mu ba.

Alhassan shima ya shiga dimuwa da tashin hankali mai yawa na rabuwa da wani sashi wanda suka rayu a mahaifa guda daya,amma haka ya daure ya nuna mazantaka ya rungumi dan da aka haifawa alhussain yayi masa huduba da suna JABEER.

Da ya ke duk dangi daya ne sai daada ta ce a bar mata jabeer ta rike shi hakan zai ke tuna mata da danta da kuma matar shi, da wannan rikon jabeer ya dawo hannun daada inda Allah ya rayashi da kunu da madarar shanu,…lokacin da ya kai shekaru uku a duniya ne alhassan ya roki daada ta biyoshi nigeria dama sun dade dayin plan da dan uwanshi kafun Allah ya dauki ranshi har sun sayi fili da niyyar gina mata,.Dukda kasa ya rufe idanun alhussain alhassan baiyi kasa a guiwa ba wurin cika masu wannan buri,inda ya ginawa daada dakuna biyu da sauran abun bukata a wannan fili da suka siya tare.

Daada batayi gardama ba ta biyoshi zuwa nigeria,a bangaren dijah matar alhassan kam shiru har lokacin ko batan wata bata taba yi ba,amma suna zaune lafiya da mijinta a cewar shi komai lokaci ne, daga wurin daada ne take samun yan matsaloli nan da can da baza’a rasa ba.

Lokacin da jabeer ya kai shiga matakin primary baffanmu baiyi kasa a guiwa ba ya sashi a wata makaranta ta gwamnati dama tuni ya dade da shiga karatu da islamiyya a lokacin ne kuma daada ta tayar wa baffanmu hankali zata koma nijar a cewar ta ta gaji da zama ba wurin zuwa ita ko ta bar danginta a cike a can anzo nan an yarda ita kamar marar galihu,wannan shine silar dawowar jabeer hannun alhassan ya ci gaba da karatu, kuma baffanmu da innarmu suka mishi riko na amana,riko irinna iyayen kwarai, duk da babun dake tattare da rayuwar su, jabeer bai taba kukan rashin mahaifa ba, daada kuma ta koma nijar saidai lokaci lokaci suje ko ita tazo,wannan kenan….

     **********

A kwana a tashi asarar mai rai,jabeer yana da shekaru goma sha daya cibb a duniya ciki ya bayyana a jikin dijah,.

“Godiya ta tabbata ga Allah buwayi gagara misali mai kyautar da bata yankewa” .

Wannan shine kalmar da daada ta ambata cike da farin ciki lokacin da labarin cikin dijah ya risketa,.Duk yadda taso su koma nijar suyi rainon cikin a can ki alhassan yyi saboda gargadan hanya,ba don daada ta so ba ta hau hada itatuwa da ganyayyaki na wanka da na turarawa ta aikowa dijah tun daga nijar har nan a cewar ta maganin ido ne da bakin makiya tunda ta dade bata samu rabo ba.Farin cikin da alhassan da dijah suke ciki baya misaltuwa,hakama jabeer tunda ya fahimci innarshi nada ciki yake murna.

Cikin ya zowa dijah da laulayi dan haka kusan komai na aikin gidan jabeer ke yi…Saida dijah ta kwashe wata biyar sannan laulayin ya lafar mata.Haka suka ci gaba da renon cikinsu cike da kulawa da soyayya,..bayan cikin ya shiga wata tara, wataranar litinin da safiya,dijah ta tashi da nakuda Allah yasa jabeer na gidan bai riga da ya bi baffa kasuwa ba,ba bata lokaci ya gudu kasuwa ya yi kiran baffa nan suka dungumo gida hankali tashe, dan ba abunda alhassan yake tunawa sai mutuwar mahaifiyar jabeer da na dan uwansa alhussain,…A gaggauce suka tafi asibiti da ita cikin kasa da awa daya dijah ta santalo kyakkyawar diyar ta fara kal.

Kimtsa su ungozomar tayi kana ta tura su dakin hutu,. Tunda jabeer ya kyallara idanu yaga jaririyar nan yaki ba wa baffa ita, baffa yana dariya yace “jabeeru kodai yar gida za’ayi ne? tuwona maina ince wa daada ta fara shirin karban kishiya?.

Dariya dijah dake kwance tayi, a nashi bangaren shi kuwa hade rai yayi sannan yace, “Baffa nifa ba wani son daadan nan nake bafa dama, me zan yi da tsohuwa? kaga innarmu ta samo min amarya mai kyau ni ita nake SO, ya fada yana kure jaririyar dake hannunshi cikin tsumma da idanu…Wnn shine mafarin lamarin.

Murmushin manya baffa yayi yana kallon jabeer yace, “ni kuma nayi alkawarin aura maka wannan jaririya matukar ranmu yakai lokacin girman ku….😭(alkawari kaya ne baffa).

Ranar suna jaririya taci sunan daada wato MARYAMA, dijah ta sa mata alkunya Arwat amma daada ta fitittike idanu tace ba mai canza mata suna, Maryama nta za’a kira ta.

Jabeer dake rike da jaririyar suna zaune gefen Innarmu, ya shafa saman girar babyn dake ta baccin ta,a hankali ya furta,
MARYAMAAA…

Jumma’at Moufida, Allah Ya Karbi Ibadunmu.

💫 MARYAMA 💫

Story And Writing
by
Ummu Fadeela.

Typing📲

Episode 11 / 12.

Ina kuke ma’abota yanar gizo gizo? shin ko kunsan sai da DATA mai aminci ake zagaye duniya da tafin hannu? maza ku garzayo mu gwangwaje ku da DATA mai rahusa wanda zaku shafe tsawon lokaci kuna amfani dashi. DATAr mu ba irin sauran bane ba yana da aminci da kuma kargo.Me ku ke jira yi kokarin ka/ki mallaki na ka/ki a kan farashi mai saukin gaske, muna maraba da masu sari ko sayan dai-dai zaku iya sara kuma ku siyar ku samu riba kana wayar ku bazata rabu da DATA ba. RAHUSA DATA HUB duniya a tafin hannun ku😍. ga mai bukata sai ya tuntube mu akan lambar waya👉….08069501245. Aminci shine tambarin mu.

_________Shekara kwana,tun daga wannan lokaci jabeer ya sanya wa ranshi soyayyar maryama da niyyar auren ta idan lokaci yayi.Duk wani abu da ya danganci maryama a gidan shike yi, wankin kayan ta kuwa ya mayar dashi wajibin sa,tun tana da wattani jabeer ya iya mata wanka, tun innarmu na fada dan tsoron kar ya sheka mata ruwa a hanci har ta hakura,wata rana idan ya dauki maryama shan nono ne kawai ke sa shi mikata ga inna,kana duk wani abun da ya samu ko mai yawanshi komai kankantarshi a kan maryama yake karewa, idan a ka bashi kudin break na makaranta kuwa,gaba daya maryama yake kwasowa su tarkacen sweets da chocolates, tun bata iya sha har ta koya.

       **************

A hankali wani irin shakuwa ya shiga tsakaninsu, har ya kasance da maryama ta ga jabeer zata fara daga hannu alamar ya dauketa yana daukar ta ko zata ringa babbaka ma sa dariya,idan ta fara kuka kuwa ba wanda yake iya rarrashin ta sai jabeer.Lokacin da ta fara koyan magana sunan shi ne abu na farko da ta fara fada jay jay jay wannan sunan ya bishi har girma a wurin maryama dan sosai sunan ke mashi dadi idan ta ambace shi da hakan.

Ranar da aka yaye ta kuwa kwana sukayi suna kuka tare da jabeer wai sai innarmu ta tsammata nono kadan in yaso gobe a yi yayen, murmushi kawai inna tayi ta juya abunta, haka jabeer ya dauki maryama zuwa dakinshi ya dinga lallashin ta.a ranar dai a kan kirjinshi ta kwana yanda suka ga rana haka suka ga dare..Life goes on,abubuwa da ya wa sukan zo su shude wani ya kan wuce a manta dashi, yayin da wani ke wucewa da barin tambari a zuciya na har abada…hakan ce ta kasance a gidan su maryama,yayinda take girma sirrin kyawun da Allah ya bata yana kara bayyana,tamkar ita ta hallici kanta.
(Fatabarakallahu Ahsanul Khaliqeen)

Time da ta kai shiga makaranta aka sanyata a nursery, kullum jabeer ke dorata a kafadunshi ya kaita ya kuma dawor da ita,kowa kaunar maryama yake tun tana karamar ta,,irin yaran nanne da idan ka kalle su dole saika daga su.Kyawun fuskarta mai fusgar hankali da kuma yalwataccen gashin kanta da ya bayyana har saman goshinta shike kara fadada kaunar ta ga mutane,,jabeer ma yana ci gaba da karatunshi sannu a hankali,kana ya na bin baffanmu kasuwa inda suke sana’ar kayan miya, saidai kaso casa’in cikin dari na kudin da ya ke samu a kan maryama yake kashe su, kama daga kayan kwalam zuwa kan kayan kwalliya da kuma sutura,inna tayi fada akan ya dinga tara wa shima yayi abu mai amfani amma a banza, dan yana samun kudi zai siyowa maryama wani abun…

Rayuwa tana tafiya, soyyayar maryama a zuciyar jabeer tana kara yaduwa da kyawawan yabanya,kana alkawain baffa yana ta kara kusanto su, duk wani numfashi da jabeer zai shaka, yana shaka ne da zunzurutun kaunar ta da kuma taraddadin mai gobe zata haifar sakamakon farin jinin da ta ke dashi, ba ga yara ba baga samari ba kana har tsofaffi son ta suke,saidai duk wanda yazo baffanmu kance maryama dai an mata miji.Da wannan jabeer ke samun nutsuwa kadan amma duk da haka cike yake da fargaba,innarmu ta kara haihuwar yaya biyu bayan maryama, fatima da kuma salima…Maryama tayi fama da kidney diasease lokacin tana yar shekara tara domin har an cire rai ga rayuwar ta amma jabeer ya sadaukar da nashi kidney din guda a gare ta inda yake rayuwa da koda daya duk a dalilin ta…Daga time din da ta fara zama yan mata komai na cikar hallita ya bayyana a jikinta duk da kasancewar ta mai kananan shekaru, amma tana da kira irin na manyan mata da wani irin kwarjini da aji da Allah ya bata hakan yasa mutane da yawa suke kiranta maryama matar manya.

Ire iren wadannan maganganu sunyi tasiri matuka wajen jirkita tunani da zuciyar ta, tana son hamma jay irin so wanda kanwa take yiwa yayanta amma bata mishi so irin na aure a ganinta bai mallaki abubuwan da zai inganta rayuwar ta dashi ba sai dai bata taba nunawa ko a fuska ba, a gefe guda kuma ga zugar da mutane ke mata na cewa bata dace da talaka ba, ita din matar hutu ce.kana muradin ta na karatu mai zurfi shima yana kara taka rawa wurin gurbacewar tunaninta.

Jabeer yayi karatu har zuwa matakin jami’a ya karanci law, amma yanayin rayuwa ya hanashi tafiya ci gaba da karatu a school of law, wannan dinma da kyar da sudin goshi aka gama shi, duk kuwa da cewa ya fito da sakamako mai inganci amma samun aiki ya gagara kasancewar kasar tamu ta zama wa ka sani, wa ya sanka ne yanzu…Dama jabeer bai mai mataccen zuciya bane, yasan zafin nema, dan baffa yayi iya kokarin shi na ganin dan nashi bai zama cima zaune ba masu dogaro da kwalin boko, dan tun yana zuwa makaranta yake aiki tukuru wajen ganin ya share wa iyayen shi da kuma masiyiyar shi hawaye ta hanyar neman na halak karkashin oga zubairu mai gadaje, zuwa yanzu babu irin nau’in gado da kujeru da jabeer bai iya bugawa ba.saidai karancin jari yasa shi ci gaba da zama a karkashin ogansu.

Maryama tana da kawa daya ko muce aminiya wacce ita kadai ce ke fada mata gaskiya a duniya kuma ita kadai ce tasan sirrinta, umaimah kenan kullum cikin fada suke kuma basa batawa basa jimrar fushin junansu, suna yiwa juna soyayya na fisabilillah duk da bambancin halayya dake tsakanin su, umaima yarinya ce mai fara’ar gaske wacce ke shan musgunawar kishiyar uwa, dan mahaifiyarta ta rasu da jimawa inda rikon ta ya koma hannun ummar su matar babanta, ita ko tayi amfani da wannan damar tana gana mata azaba son ranta.Umaimah tana yawan nusar da ita akan rayuwa, sau tari tasan gaskiya umaimah ke fadi mata amma sai tayi biriss da maganar,tamkar ba da ita ake magana ba…..Rashin jin shawarar umaimah da kuma rudin shaidan ya kaita ga ziyarar shagon siyama tsohuwar kawar ta da iyayenta suka raba su da jimawa dan sanin bata samu tarbiya mai kyau ba, har kaddara ya kaita inda sadeeq yake shi kuma ya…..Wannan kenan.

    *******************

    CI GABAN LABARI.

*.

Har jabeer ya kama hanyar fita waje sai kuma ya dawo baya ya shige dakinshi,kada kai baffanmu yayi ya ce, “Allah ya kyauta”.

Rigar jikinsa ya zame take farar fatar sa mai cike da gargasa da kuma murdewa irin na mai gymin wacce ko kadan bata yi kama da fuskar saba ta bayyana, kwanciya yayi ruf da ciki bisa katifar sa dake kwance bisa leda carpet da ta malale dakin, a hankali ya lumshe idanunsa yana sauke wani irin nimfashi mai nauyin gaske da zafi kana yana jin kanshi yana mashi wani irin kara gim gimm gimmm kamar ana buga karfe da karfe, ba abunda ke mishi yawo a kwakwalwa sai sautin muryar sadeeq inda yake fadin, “pretty naji dadin wunin yau tare da ke,.”

Rumtse idanu da karfi ya kuma yi yana kokarin hana kanshi tunanin amma ya kasa, “why pretty? why?.” shine abinda ya furta yana danne kanshi cikin katifar.

   ******************

Tunda ya sanar da siyama lallai ta fadi wa maryama ta kirashi yake zaune yana jiran tsammanin kiranta, wasa wasa har karfe goma shiru, goma da minti arba’in shiru,goya hannayen shi yayi a baya yana zagaye hotel room din kamar mai gadi,ya kasa tsaye balle zaune, dialing layin siyama ya kuma yi amma switch off, damn it! ya fada a harzuke kana yayi cilli da wayar kan gadon shi, saukar wayar yayi dai-dai da shivowar wani kira, a tamanin ya bi wayan saidai sabanin tunaninshi bai maryama bace kamar yadda yaya zato. Kara wayar yayi a kunne yayi magana na tsawon minti biyar kafun ya yanke kiran yana sauke numfashi, a na bukatar shi da gaggawa wurin aiki, and bayajin zai iya komawa ba tare da ya kara kallon fuskar maryama ba.

Mikewa yayi ya dauki wata yar karamar jaka ya dura abubuwan da yake da bukata kana ya zuge zip din ya ajiye gefen gado da alkawarin gobe zai je garinsu maryama ya ganta kafun time na tashin jirginsu yayi….

Kuyi manage da wannan ba yawa da babu dai gwara ba dadi…..Gobe idan Allah ya kaimu baza’a samu update ba dan ina da wasu uzurin da zan gabatar,
💫MARYAMA💫

 By.

Ummu Fadeela

Typing📲

Episode 13/14.

  ELEGANT ONLINE WRITER'S...

__________Yan abubuwan bukata kadan ya hada cikin jakar ya ajiye gefe da niyyar washe gari zai je garin su maryama before time na tashin jirginsu….Cikin nutsuwa da ya kasance dabi’arsa ya koma bakin gadonshi ya zauna ya dafe hannayensa duka biyu bisa gadon.

“Sadeeq me zai kai ka garin su yarinyar nan?”.

Zuciyar shi ta tambayeshi.Shafa beard nashi zuwa kan gemunshi na yan gayu yayi,wani bangaren na zuciyar shi ta bashi amsa da, “Dan in san ya ta koma gida,tunda dan ni tazo garin nan”.

“Dan kai ta zo, amma bukatar ta ne ya kawo ta, this is madness Sadeeq,actually madness. Is better ka farka daga nannauyan baccin nan da ya dauke ka lokaci daya”.

Sashin zuciyar shi ya kara gargadinsa, kamar wadda aka mintsina ya mike tsaye ya goya hannayensa a baya ya ci gaba da zagayen dakin…Shi kanshi ya san abunda kwakwalwarshi ke ankarar da zuciyar shi gaskiya ne, amma why ita zuciyar ta ke ingiza shi ga son zuwa taga fuskar maryama, wacce a kallo daya ta yi haddar fuskar ta? ko me ya tuna?. Da sauri ya girgiza kai shi kadai yana murmushi a zahiri yace “She’s too young”.

Tayi karama da yawa, ina zan kaita?…Haka sadeeq yai ta sambatu shi kadai ya saka ya warware har around 11pm Sannan ya kwanta ba tare da ya tsaida takamaiman abunda zai aiwatar ba…

Washe gari kiran waya ne ya farkar da sadeeq daga bacci, inda mai kiran yake kara jaddada masa muhimmancin zuwan sa a kan lokaci dan wani Important meeting suke dashi, kana kasancewar sa a wajen yana da matukar amfani,don ya je ya ba da bayanan da ya zo ya tattara a nan adamawar….Badon ya so ba haka ya tattara ya tafi saidai jirgin su natashi ya ji kamar ya yi tsuntsuwa ya sauko,yana jin kamar ya bar wani sashi mai girma na jikin shi a kasa…

     **************************

Maryama….Tunda muka dawo asibiti babu wanda ya leko ni haka kuma babu wanda yace man sannu da jiki, innarmu sai harkokinta take yi,baffanmu ko yana kasuwa,hamma jay da nake sa ran samun sassauci a gareshi, shima ko keyar sa ban gani ba…Haka na kasance a daki ni kadai tamkar mayya, ina zaune ina ta sakawa da kwancewa aka daga labulen dakin,innarmu ta shigo fuskar ta daure babu alamun fara’a a tattare dashi,kwanon abincin dake hannunta ta ajiye gefe ba tare da ta kalle ni ba ta ce, “Idan kinga dama ki ci,idan kin ga dama kuwa ki zubar duk yadda kika yi daidai ne, ta sa kai zata fice a dakin.

Bansan ya aka yi ba sai tsintan kaina nayi bakin kofa rike da bakin zanin innarmu. Ina durkushe hawaye na shatata a idanu na na ce,

“Don girman Allah kiyi hakuri Innarmu, wllh Allah daya kenan bazan sake ba, dan Allah kiyi hakuri ki bawa baffanmu hakuri bazan sake ba innarmu ku daina fushi dani Don Allah”.

Na fada ina kara fashewa da wani irin kuka mai ratsa zuciya.

Duk yadda inna taso kwace zaninta daga rikon da maryama ta mata kasawa tayi sakamakon zuciya irin ta uwa. A hankali ta kamo kafadu na ta mikar da ni tsaye, rungume ta na yi na kuma fashewa da kuka, cikin kukan na ce,”Sorry mother! I fail you,amma bazan sake ba sharrin shaidan ne Allah bazan sakr ba ” baya na innarmu ta ke shafawa cikin lallashi sannan ta tafi dani har bakin gado na ta ajiye ni gefe itama ta zauna ta zuba tagumi tana kallona ina ta sauke ajiyar zuciya da numfashi sama sama,hannayena duka biyu ta kamo ta rike su gam ta na fuskan tata. ta ce.

“Maryama ita duniya a sannu ake binta, lallabata ake sai a samu rayuwa mai inganci,maryama duniya idanunta a tsakar ka take, sau tari zata yunkoro ta dauki mutum sai ta daga shi sama sai ta ga ashe bashi ta ke son dauka ba,maimakon ta saukar da kai a hankali, a’a hajijiya zata yi da kai sannan ta wantsalo ka zuwa kasa kana ta dauki waninka idan bakayi sa’a ba sai ka karya wuyarka garin saukowa.” dan jimmm innarmu tayi sannan ta ci gaba da cewa, “Maryama kowa yana tafiya ne bisa tsarin kaddarar da Allah ya rubuta masa tun yana cikin mahaifiyar sa, kina da ilimi Alhmdllhi kin karanta hadisi na hudu cikin arba’unanawwawi, ka da ki bari kyale kyalen duniya su rude ki, ki zo kina nadama a lokacin da wuri ya kure maki, Maryama a matsayina na wacce ta haifeki ina tabbatar maki har abada bazaki taba samun miji mai kaunar ki da zuciya daya kamar jabeer ba,…..Jabeer ya so ki tun baisan menene so ba, dan haka ki nutsu ki mai da hankalin ki jikin ki, arziki bai taba zama dauwamammiyar jin dadi da farin ciki ba,kamar yadda talauci bai zama bakin ciki na har abada, duk da cewa manzon Allah S A W ya hore mu da neman tsari da talauci mai tozartarwa, wasu ma arzikin su shine musabbabin shigar su fitinar duniya da ta kiyama, Allah ya ki ya shemu,wasu ko talaucin su shike masu tsani har zuwa gidan aljannah idan sun yi hakuri,sau tari abunda kake hange daga nesa ya na walkiya kamar gwal maryama sai ka iso shi ne zaka fahimci ashe rana ne ya haske shi, amma zahirin bakin karfe ne kirin,.” dan fasali innarmu ta ja sannan ta kara duban fuskata da ya yi jage jage da hawaye da majina ta ce, “yanzu ki tashi ki je ki baiwa hammanki hakuri akwai aikin da na ke yi zan dawo ki ban dalilinki na abunda kika aikata”.Sake hannuna ta yi ta fice ba tare da ta bani damar cewa ko uffan ba.

Mikewa nayi don cika umarnin inna, hijabi na saka jiki na ba kwari kana yayi tsami sakamakon dukan mutuwar da na ci wurin innarmu,dakin shi na shiga ina ta sakawa da warwarewa.

Yana kwance sambal ba riga a jikinsa ya cusa kanshi cikin katifa ba ka ganin alamun numfashi tattare dashi, wani irin sauti kirjina ya bada dammmm, da sassarfa na iso gareshi ba tare da shirya wa hakan ba, durkushewa nayi bakin katifar nace “hamma jay,hamma jay, amma shiru ko motsi bai yi ba,hannu na sa na kama nashi hannun ina jijjigashi da ci gaba da kiran sunanshi amma bai motsa ba,….Tun shigowar ta dakin yana ji kuma yasan ita ce, dan ita kadai ke shigo masa daki gaba gadi haka ba tare da sallama ba,mikewa nayi cikin tashin hankali dan zuwa kiran innarmu ta zo ta ganshi ban yi aune ba naji ya janyo hannu na saura kadan in fada kanshi yayi azamar matsawa baya sosai na fada bisa katifar, cikin sakwan daya na mike da iya karfi na na juya baya ina turo baki,cikin gunguni na ce ,

“Dama idanka biyu shine ka bani tsoro ko?”.

Bansan ya taso ba sai maganar shi na ji a gefe na, “Uhmmm da ma za ki ji tsoron mutuwa ta ne pretty? na dauka farin ciki za ki yi da hakan,?”

Ya fada ya na bayyana a gabana. Da sauri na sa hannuwa na duka biyu na rufe fuskta da su,

“tambayarki na ke yi,” make kafada na kara juya masa baya nace, “ni dai ka sa rigar ka tukunna”. “why”? ya tambaye ni, kara turo baki nayi nace,” ni dai Allah tsoro kake bani a haka,”…Shafa kai yayi yana dan karamin murmushi wanda rabonsa da yi kusan kwana biyu da yini kenan.

Bayan kamar second biyar yace “to bude idon haka tunda ni na zama abun tsoro” make kafada na kuma yi nace “ni dai kasa riga”, na sa rigar ai pretty bude idon ki gani mana,”

Still ba bude ba nace ,”kace wallahi ka saka”, sosai ta bashi dariya amma sai ya fuske yace,”eh nace”.

Ta tsakanin yatsun hanuna na dan leko shi kadan dan tabbatar da ya sa rigar, dan tsakani da Allah jikin hamma jay yanda ya mummurde din nan yana bani tsoro.

Sosai dariya ke cinsa amma ya maze, ….ganin da gaske ya saka rigar ne ya sani matsowa kusa dashi na durkusa a hankali nace “Hamma jay kayi hakuri da abunda ya faru bazan sake ba insha Allah”. wani abu ya ji ya soki zuciyar shi saida ya rumtse idanu da karfi, abubuwa da yawa suna dawo mishi cikin kwakwalwa.

“Ka ce wani abu mana plssss, ” na fada ganin ya yi shiru idanun sa a rufe.

Bude idanun yayi wanda dama tun shigowa ta suke rine cikin kwantar da murya yace, “Pretty kaunar ki ce JARABTATA kana watakila shi zai zamo AJALI NA. amma idan hakan ta kasance ina farin ciki da cewa kinsan ni ma’abocin sonki ne da nake fatan rayuwa da ke har gaba da abada wato a gidan aljannah. Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya da fitar da wani huci mai zafi da alama duk abunda zai furta yanzu yana mashi zafi cikin kirjinsa, yana kallo na yace “Maryama son da nake miki bazai barni in cutar dake ba, zan iya sadaukar da soyayyata matukar ke din zakiyi farin ciki,na zabi jinyar zuciyata duk da ina da yakinin bazai warke ba saidai ya kaini kabari, akan ke kiyi jinyar taki zuciyar, abunda kike so shine farin cikina maryama ina sonki har zuwa karshen numfashi na, abunda ya faru shekaran jiya ya haska man wata hanya mai cike da duhu da kuma karangiya,nayi kokarin fahimtar da baffanmu amma yaki bani listening ears, shin maryama zaki iya zama dani a matsayin miji ko akwai wanda zuciyar ki ke muradi?karki ji shakka na ki fada min zallar gaskiyar dake ranki koda ko in naji zanyi collapsing a nan ne ki fadan preety,

Shin zaki iya aure na? Za ki iya zama da ni a matsayin mijinki?….

Banyi editing ba,kuyi hakuri da typos

💫MARYAMA💫

By

Ummu Fadeela.

Typing📲

Episode 15/16.

ELEGANT ONLINE WRITER’S📚.

_ Kafun Maryama da ta yi mutuwar zaune a wajen ta samu zarafin furta wani abu, aka bude labulen dakin, duk dagowa suka yi suna kallon bakin kofar,Salima ce ta shigo da sallama ta tsugunna ta ce, “Anty Maryama kinyi ba’ki wai kizo in ji Innarmu”. Wani irin sanyi na ji ya ratsa daga tsakar kaina har kan babban yatsar kafata. Amma sai na daure na ce.

“Ba’ki kuma?” na tambaya cike da madaukakin mamaki, gyada kai ta yi ta ce “ehh wai kawar ki ne tazo duba ki da jiki.Da sauri na mike ina jin farin ciki na mafitar da Allah ya bani don gujewa amsa wannan tambaya ta hamma Jay mai cike da sarƙaƙiya.Lumshe idanunsa ya yi sakamakon sarawar da kanshi ke yi,ya so ta ce wani abu,ya so ta amsa mashi wadannan tambayoyin,amma hakan bai samu ba.

Koda na fito wata ƴar dattijuwar mata na gani zaune a tabarma ita da innarmu suna gaisawa, gefenta wata ƴarinya ce da bazata haura shekaru na ba.Lallausan murmushi ƴarinyar ta sakar min lokacin da muka hada ido da ita tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, “Ah Masha Allah,hajiya kin warke ashe?” ya jikin naki yo?”.

Kafun ince wani abu, dattijuwar matar ta katse min hanzari tare da hararar budurwar ta na fadin, “To uwar zuba kya bari ta isar dake ɗaki tukunna ai, ba ki tare ta da surutu ba,” ba don na so ba na gaida matar kana ina kallon budurwar da ke ta kallona tana murmushi na ce mata, “sannunku da zuwa mu isa ciki”.

Ko da yaushe dakinmu tsab ya ke shiya sa bana shakkan shigar da mutum ciki,dan dofanuwa ta yi bakin gado na tana ci gaba da murmushi ta ce, “ya karfin jiki kuma?”.

“Alhamdulillah” na amsa ma ta kana na ci gaba da faɗin “sai dai ban gane ku ba,ko dai ɓatan kai ku ka yi ne?”.

    "Ko ɗaya," cewar ta.

“Sunana Laurat kuma Siyama ce ta aiko ni wajenki,ɗan waige waige ta fara kamar munafuka sannan ta gyara zamanta da kyau ta ce, “Ana ta kiran wayarki a rufe me ya ke faruwa?”…Tunda ta ambaci Siyama na ji gaba ɗaya miyau din baki na sun kafe, da kyar na tattaro jarumta da niyyan magana wayar ta ta ɗauki tsuwwa.

“Yauwa ƴar halak”,cewarta tana ƙoƙarin miƙo min wayar haɗi da faɗin “Ga shi kuyi magana da ita”…Jikina ne ya tsananta rawa har wayar tana faɗuwa ƙasa, amma na yi azamar tarota na kara a kunne na.

“Ina kika jefa wayar ki ne haka pretty?”.

Tambayar Siyama ta doki kunne na,..Cikin in ina na ce, “Siyama abubuwa da yawa sun faru, har na kwanta a hospital ma,wayata kuwa hamma jay ya fasata,siyama ya aka yi yasan na je wajenki? ya akayi hijab da jakata suka dawo gida kafun in dawo?”.

Nan siyama ta bawa maryama labarin yadda Jabeer da Baffanmu suka je shop nata har bala’in da h,jay yai mata. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama bata labarin sannan ta ce, “duk ba ma wannan ba,sadeeq ya ce lallai lallai ki kirashi yanzun nan.Wai Maryama me ki ka yiwa bawan Allahn nan haka ne gaba daya ya fita a hayyacinsa?” Siyama ta fada cikin zolaya.

“Me zan mashi ni ko?kinsan sanadiyyar kiran da yai min ne hamma Jay ya fasa min wayata?. yanzu bani da wayar da zan kira shi da, plssss Siyama ki bashi hakuri dan Allah.”

Ba wannan maganar, yanda ya dau zafin nan ban isa in tunkareshi da wannan zance ba….Abunda za’ayi yanzu zan sanar da laurat ta baki karamar wayar ta dake hannunta zan miki sending na contact nashi sai ki ƙirashi yanzu nan, yanzu nan faa,” ta ƙara maimaitawa dan in tabbatar. da “to” na amsa nima a raina na ƙagu in yi magana dashi. haka ko akayi Laurat ta bani ƙaramar wayar dake hannunta bayan ta sa ta a silent mode suka mana sallama ita da wannan matar da suke ta hira da Innarmu tamkar sun san juna. bayan kamar minti biyu sai ga massage na Siyama da layin Sadeeq. kallo daya na yiwa namban na haddace shi, take na loda cikin wayar na fara tunanin yadda zanyi in ƙirashi ba tare da an kama ni ba,…..

     ABUNDA YA FARU.

Tunda Sadeeq ya iso porthacourt ya ka sa samun nutsuwar zuciya da ta gangar jiki, da kyar ya iya presenting Data ɗin da ya zo ya tattara a wajen meeting din na su, ya koma gida ya kwanta, duk yadda ya so daina tunanin ta kasawa yayi, ya yo trying layin Siyama ya fi sau curin masaki amma switch off ake sanar mishi.wata idea ce ta fado mishi na ƙiran saurayin ita Siyamar wato Huzaifa wanda ta dalilinshi ne suka haɗu da ita,…cikin nasara kuwa ya same shi, ta ke ya bashi umarnin ya je ya hada shi da Siyama.Huzaifa bai bata lokaci ba wajen cika umarnin uban gidan nashi, ko da ya kai mata wayar ma still maganar daya ce wato ta je ta hada shi da Maryama. Huzaifa ne ya kawo musu shawarar nemo wa Maryama kawa ta karya taje gidan tunda shi ko ita Siyamar ba bu wanda zai iya tunkarar gidan, bayan yan binciken da suka gudanar na sirri suka gano ai maryamar ma bata da lafiya har ta kwanta a asibiti wannan ne ya karawa tafiyar tasu armashi har suka nemo da uwar karya suka hada laurat da shi wacce itama biyan ta kudi suka yi kuma a kayi sa’a suka gama mission din nasu sucessfully….Wannan kenan.

Ina zaune sai tunanin yadda zan kira shi nake yi, daya barin na zuciyata kuwa cike ta ke fal da tunanin hamma jay da kuma tambayar da yai man da zu….Haske wayar dake hannun ta yi kasancewar ta na silent, sai da zuciya ta ta kusan shigewa cikin cikina sakamakon arba da na yi da nambobin Sadeeq suna yawo bisa allon wayar,duk da zuciya ta tana rawa da tsoron kar wani ya shigo ya kamani,haka na kama call din ba tare da na jira ya katse ba.

“Ohh Damn It! Pretty ina kika shige ne haka?”.

Abunda Sadeeq ya fara fada kenan lokacin da ya ji an dau kiran, lumshe idanu nayi amma bance komai ba sai numfashi na da ke tseren gudu.

“Assalamu Alaiki”. Are you there baby?” ya kuma fada jin an kama kiran amma ba’ace komai ba.

“Barka da warhaka ranka ya dade” na fada cikin sanyin murya dan kar innarmu ta jiyo ni.Maimakon ya amsa sai tambayat da ya jefo min. “Lafiyar ki kuwa?”

“Hmmmmm” na bashi amsa. Gami da fadin, “ina wuni, ya ka koma ?”

“Alhmdllh na koma lafiya qalau Maryama, sai kewar ki da ya addabeni kamar zanyi karamar hauka.Na kasa sukuni tun isowa ta har saida na nemo wanda zai hada ni da ke a waya sannan na fara dawowa normal.”

Dafe kirji na yi hadi da zaro idanu waje na ce, “kewata ku ma?”.

“Kwarai kuwa kewar ki maryama. At first na dauka abun wasa ne,sai daga baya na fahimci kinmin kamu irin na kazar kuku”.

“Ban fahimta ba,” na fada cike da rudani….Da ma banson ki fahimta tun yanzu sai zuwa gaba by then kin kara girma”. Gaba daya maganganunshi sun daure min kai amma haka na hakura ba don na fahimci komai ba,sai don yadda na ke jin dadin hira dashi, duk sanda yayi magana sai inji wani abu ya na tasowa tun daga tafin kafata har zuwa cikin cikina, sannan gaba na ya na faduwa ban san dalili ba, mun dau tsawon lokaci muna magana dashi kafun ya yanke wayar,da sauri na cusa wayar cikin rigata jin footsteps…..Tun daga wannan lokaci kullum sai munyi waya da shi a kalla sau hudu a rana luckily ba wanda ya ankara cewa da waya a hannuna, dan kullum a silent ta ke,cikin sati daya munyi wani irin shakuwa da sadeeq na ban mamakin da idan lokacin da ya saba kirana ya wuce bai bai kira ni ba na kanji tamkar bani da lafiya,Sadeeq mutum ne mai barkwanci da iya kalamai masu taushi da sanyaya rai wannan ya taka rawa matuka ga ya wajen kara dankon shakuwar mu da shi.

A bangaren hamma Jay kuwa,tun randa ya min waccan tambayar bamu sake zama dashi ba har tsawon one week din, Iyaka ta da shi hange daga nesa shima ba kullum ba, dan kwannan nan ya zama tamkar mace kullum yana kwance a daki ba ya fita aikin shi ma ya daina zuwa, ko daga karfen da ya mayar tamkar ibada shima ya daina yanzu,sai wani rama da ya ke yi a tsaye tamkar mai jinya. …Saidai abunda ba wanda ya sani tabbas Jabeer jinya ya ke yi a tsaye wani irin ciwon kai da ciwon kirji ya ke fama dashi these days musamman ya fi tasar masa cikin dare tamkar zai mutu…

Yau saura sati daya lokacin da Baffanmu ya dibar na bikin Maryama da Jabeer ya cika, saidai ba bu abunda ango ko amaryar suka fara na shirin biki, a yau ne kuma daada za ta zo daga nijar.

Daga labulen dakin Jabeer baffa ya yi ya leka kanshi ciki,cike da karfin hali jabeer ya mike daga kwancen da ya ke ya ce, “Sannu da shigowa Baffanmu”.

“Yauwa Jabeeru, biyo ni daki akwai abunda za mu tattauna” cewar baffa yana sakin labulen da barin wajen.

Da sallama ya shigo dakin sanye da jallabiya fara kal ya samu gefe ya zauna gaisawa suka kara yi da baffa sannan yayi gyaran murya ya ce, “Jabeeru lokaci ya na kara matsowa banji kayi wani motsi ba har yanzu, ko akwai wani damuwa ne?”

Girgiza kai ya yi yace, ” ba bu wani damuwa Allah ya nuna mana lokacin”.

Dan jimm baffa ya yi sannan ya fara yi mashi nasiha mai ratsa jiki yawanci a kan hakuri da rayuwa ne. Sosai Jabeer ya ji dadin nasihar da baffa ya yi mashi har ya dan sake, ko da dai ciwon da ya ke ji a zuciyar shi ya tabbata ya na bukatar ganin likita.

Wasu damin kudi yan dubu dubu da suka gaji da rayuwa kamar kana kamawa za su tsage baffa ya fitar da ga cikin wani akwatin karfe, yana kallon Jabeer ya ce, “ungo wannan ka ka ra kayi wani abun da shi, nasan basu da yawa amma ka yi hakuri ba bu ce ta sa hakan Jabeer, na san da dan uwa na yana raye ba karamar farin ciki zai shiga ba a irin wannan lokacin,” ya fada cike da alhini.

Ta ke idanun Jabeer suka kada jajur, ya yi karfin halin cewa, “ka bar wannan a wajenka baffa,ni ne ya kamata in baka ba wai kai ka bani ba”.

“Ka rena abunda na maka ko Jabeer?”

“A’a ranka ya dade a yi min afuwa ba nufi na kenan ba, ganin abubuwa za su ma ka yawa ne shiya sa ka a yi hakuri” cewar Jabeer.

Baffa ya ce, “matukar ba raina wa ka yi ba yi maza ka amsa “

Hannu biyu jay ya sa ya amshi kudin ga mi da fadin, “Allah ya kara girma baffanmu”.

Koda ya fito dakin baffa, da sallama ya shiga dakin Inna, tana zaune bakin gado da wani banki na katako a kusa da ita ta bude sai aikin shirya kudi take yi yan dubu dubu da dari biyar biyar masu yawan gaske, da alama an dade ana tara su….Da hannu ta mishi alamar ya matso kusa da ita, ba bu musu a tsakaninsu dan haka ya karasa shigowa ya zauna a bakin gadon ta kasa.Kusan minti goma suna a haka kafun Inna ta gama shirya kudin inda ta raba su gida biyu ta dago ta na kallon shi da dan murmushi fuskar ta ta ce, “ango ya aka yi ne”.

Lallausan murmushi ya yi shima ya na shafa gashin kanshi ya ce, “Ba bu komai Innarmu,” kudin da ke hannun shi ya ajiye kusa da ita ya ce, “Baffa ya bani su yanzu wai in yi wani abin dasu,sai dai Inna kamar……”

“Shiiit” inna ta fada tana sa dan ya tsanta a saman bakinta. Shirun ya yi kuwa, inna tace, “Ka rena abinda ya baka ko?”.

Da sauri ya dago yace, “wllh ba haka bane innarmu kawai ganin shima abubuwa za su mashi yawa ta bangarenshi ne ga shi ba bu mai taimako, ni da ya kamata in taimake ku din kuma b….Ka sa karasa maganar ya yi sakamakon harbawa da kirjinsa ke yi.

Sassauta murya inna ta yi, sarai ta fahimci abunda ke damun dan nata, din haka itama nasihar ta shiga yi ma shi har saida ta ga ya saki jikinshi tukunna, kudin da ya ajiye ta dauka ta duba su, naira dubu dari uku ne cifff, mika masa su ta yi,kana ta kuma daukan kaso daya cikin wanda ta shirya ta ce, “Ga wannan ta bangare na, na dade ina tarasu domin lokaci irin ta yanzu, ga shi Allah ya kawo mu, ka hada da na wurin baffanku ka nemi ma’aikata ku je kuga gyaran da za kuyi wa gidan naku, sai batun lefe kuma kar ka damu kanka, dama ba addini ba ne, idan mun fita sayan kayan kitchen zan duba mata yan zannuwa ko guda uku ta samu na fitar bikin.. A yi ta hakuri da rayuwa dai wata rana sai labari,Allah ya rufa mana asiri ya yi maku albarka, ya kuma albarkaci auren naku”.

Duk yanda Jabeer ya so daurewa kasa wa ya yi baisan sanda ya kama kafafun inna ya durkushe a kansu ba,wasu hawaye masu zafi suka gangaro ma shi a ido daya.

Dafe bango Maryama dake tsaye bakin kofat inna ta yi, da ma ta zo shiga ne ta ji suna magana hakan ya sa ta tsaya. “Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un.” ta ke ta maimaitawa a ranta, ba dai ita za’ayi wa aure nan da sati daya ba, iyayenta da ta ke ganin talakawa sune masu taimakon mijin da za ta aura?…….
💫MARYAMA💫

By

Ummu Fadeela

Typing📲

Episode 17/18

  ELEGANT ONLINE WRITER'S.

Assalam alaikum Sunana Zee arts Graphic Designer ce ba muna graphics ba atoh 😂😂😂
Ina yan kasuwa, marabuta, amare, kai har ma yan siyasa da Sauransu wann naku ne , kuzo ayi muku kayataccen design na abubuwa kamar haka 👇🏻👇🏻👇🏻

 • BRAND LOGO – LOGO DESIGN
  -FLYER DESIGN -INVITATION CARDS
  -BANNER -POSTER DESIGN
  -BOOK COVER -STICKER
  -WATERMARKS -BUSINESS CARD
 • CERTIFICATE -POLITICAL POSTER
 • INSTAGRAM HIGHLIGHTS
  Da ma wasu abubuwan da dama akan farashi mai sauki🥰🥰, kuyi min mgn ta wnn lambar idan kun shirya domin ganin samples sai kunzo 👇🏻👇🏻
  What’s app number: 07011988593.

……Iyayena da na ke yiwa kallon talakawa sune masu taimakon mijin da zan aura da kuɗin aurena?.” Ya Rabb save me”. na fada underneath breath.

Da bin bango na koma ɗaki na faɗa saman gado wasu hawaye da ban san daga ina ba suka fara shatata saman fuskata,…ina cikin rera kuka wayar da na ɓoye cikin bra di na ya fara vibrate,sanin wanda ke kirana na yi saurin goge hawayena na yi picking call din.”Hiii pretty,” Sadeeq dake kwance cikin luntsumemiyar kujera ta alfarma dake cikin kayataccen falonshi ya faɗa.duk sanda ya ƙira ni da pretty sai zuciya ta ta buga kana gabana ya dinga faɗuwa,duk yadda na yi ƙoƙarin saisaita murya ta dan kar ya fahimci wani abu amma sai da ya gane, ɗan jim yayi bayan na gaishe shi.

“What happened pretty” ?cewar shi….”Babu komai” na faɗa murya ƙasa ƙasa,

“No don’t lie to me, ga shi na ji muryar ki kina kuka then ki ce man nothing”.

“Da gaske babu komai faaaa” na faɗa cike da shagwaba ina turo ba ki gaba.

Ta ke sadeeq ya ɗauke wuta sakamakon wani irin yarrr da ya ji a jikinsa, da sauri ya ce,”ohk to shikenan….munyi hira dashi na lokaci mai tsawo, har saida naji su Salima sun nufo ɗakin sannan na mishi sallama ba don na so ba na kashe wayar.

Riƙe kafafun Inna ya yi wasu hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mishi a ido guda ɗaya. Shafa kanshi inna ta hau yi cikin lallashi ta ce, “Ba kuka zaka yi ba Jabeer, Allah zaka godewa da ya bar maka mu a raye, na san abin da kake ji cikin ranka baya misaltuwa amma haka zaka daure…idan muna dashi ko da duniyar nan ce zamu iya mallaka maka kamar yadda mukayi imanin kaima zaka iya mallaka mana duk wani abin da ka ke taƙama dashi a rayuwa, yanzu ka tashi ka nemo mai gyara sai ku ke ku duba abin da za’a fara a gidan,hanzarta ka tashi mana angon maryama,kuka ba na angwaye bane fa kar ka yadda ka zamo ragon maza masu kuka akan shirme.” ta faɗa cike da zolaya. ɗago kanshi ya yi yana ɗan murmushi kaɗan, “yauwa ko kaifa,yanzu ka yi kama da ango”cewar inna cikin salon karfafa gwuiwa.

“Na gode Innarmu Allah ya ƙara girma,bansan da wanne irin kalma zanyi amfani wajen gode maku ba Allah ya……”

“Ya isa haka, ta shi kaje ku fara abun da ya kamata” cewar Inna ganin Jabeer zai fara dogon jawabi.

Kamar yadda inna ta ba da shawara hakan akayi ya samo masu gyara suka duba aiyukan daza’ayi haɗi da yin estimend,….aiyukan sun haɗa da ɓamɓare zinc dake saman ɗakunan haɗi da yin sabon roofing, sai hade ɗakuna biyun su zama room and parlor, kana a sa ceiling kasanvewar babu, za’ayi tailing parlor da dogon varendar dake gaban ɗakunan,sai germain floor da za suyi a tsakar gida da toilet kana a buga kanta a cikin kitchen, daga karshe a yi paint….(Mai karatu ya ka hango gidan gimbiya maryama?)….😍….

Sosai hamma Jay ya fitar da kuɗi dan a yi aikin yadda ya ke so kuma akan lokaci,.bai cika tarkacen abokai ba,amma jama’a abokan hulɗar yau da kullum sun shirya meeting na auren, kuɗin da ya daɗe yana tarawa ya fitar shima don haɗawa maryama lefe na bajinta😀.sosai ake shirin wannan aure, aɓangaren amarya kuwa kamar wacce aka cirewa ruhi haka ta zama bata uhm bata umum sai ido.

Umaima innarmu ta ƙira a ranar ta bata cimgam da minti dan rabawa ƙawayen su.a ranar da ya rage kwanaki shida ɗaurin aure daada da tawagar ta suka iso daga nijar, da gudu maryama ta je ta rungume daada ta fashe da kuka. sake baki daada tayi kana ta ce,

“Aniyar ki ta biki takwara, ya zaki zo ki tarbe ni da kuka da farar daren nan bayan uwar doguwar tafiyar da nasha, shima angon na ganshi ya ƙare tas kamar mayu sunyi guzuri da shi, anya lafiya kuwa”? bance mata komai ba sai ƙara rungumeta da nayi na ci gaba da kuka na……..

Washe gari daada ta fitar da wasu kayayyaki ɗauri ɗauri wai za’a fara min gyaran amare, duk yadda na so gujewa hakan bai samu ba,…..

Asuba ta gari team jaymar ya kamata ku fidda anko kafun team sadmar su riga ku.😁😌

💫MARYAMA💫

By

Ummu Fadeela.

Assalam alaikum Sunana Zee arts Graphic Designer ce ba muna graphics ba atoh 😂😂😂
Ina yan kasuwa, marabuta, amare, kai har ma yan siyasa da Sauransu wann naku ne , kuzo ayi muku kayataccen design na abubuwa kamar haka 👇🏻👇🏻👇🏻

 • BRAND LOGO – LOGO DESIGN
  -FLYER DESIGN -INVITATION CARDS
  -BANNER -POSTER DESIGN
  -BOOK COVER -STICKER
  -WATERMARKS -BUSINESS CARD
 • CERTIFICATE -POLITICAL POSTER
 • INSTAGRAM HIGHLIGHTS
  Da ma wasu abubuwan da dama akan farashi mai sauki🥰🥰, kuyi min mgn ta wnn lambar idan kun shirya domin ganin samples sai kunzo 👇🏻👇🏻
  What’s app number: 07011988593 ELEGANT ONLINE WRITER’S.

Typing📲

Episode19/20.

_“Ince ko akwai abun da ke damun yaran nan Dijah?,duk na gan su sukuku sukuku kamar an jiƙa ƴaƴan kyanwa”.cewar daada ta na kallon innarmu, gefe da gefenta jabeer ne da maryama a zaune.ta ci gaba da faɗin, “duk ba irin ɗokin nan na aure a fuskokinsu ko kaɗan hala dai lafiya gashi ɗannan ya sanar dani auren haka bagatatan.”

Kafun Innarmu ta ce wani abu,hamma jay ya riga ta faɗin, “ke dai faɗi gaskiya tsohuwa,ki ce kawai kishi ke ɗawainiya dake kinga wata zata ƙwace maki miji,to kwantar da hankalinki ko anyi auren ma bazan manta da ke ba ai da tsohuwar zuma ake magani”.ya ƙare da dariya saman fuskar shi.dariya sauran ma suka yi.

Daada ta ce, “yo Allah na tuba ina abun da zanyi kishi anan, duk inda kaje na zaka dawo ne ka same ni daram dam.”

Jabeer ya na murmushi ya miƙe haɗi da zura hannu cikin aljihu ya ce,”ni nasan zancen zai fito ai dama kawai yar tsohuwa ki ce kishi na kike” kafun daada ta ce wani abu ya kalli maryama dake ta cika tana batsewa ya ce, “meet me outside pretty”. kana ya juya ya ce da daada yana zuwa yanzun nan, da kallo su dukka uku suka bishi har ya fice daga ɗakin Innar,ɗakin maryama ya shiga a zatonshi ba kowa saidai saɓanin tunaninshi ɗakin cike yake da mutanen da suka zo bikin da ga nijar tare da daada, ƙannen mamarshi biyu sai yayar innarmu da kannenta biyu sai da daada, iya mutum shida ne suka zo daga nijar saboda yanayin hanya….tsugunnawa ya yi ya gaishe su kana ya juya a gurguje ya fice daga ɗakin…

“Ba jiranki ake ba ne?” cewar inna tana kallon maryama wacce ke ƙara gyara zama jikin daada,turo baki ta yi sannan ta miƙe ta fita, daada ta taɓe baki ta ce,”yaran zamani ba su san yadda ake riƙe miji ba ko kaɗan,amma Dijah me kika yiwa yar nan na gyara don ban ga wani alamar kin fara mata gyara ba, kamar dai ba ƴan nijar buzaye ba?”

Murmushi Inna ta yi ta ce, “gani na yi budurwa ce ai daada shi sa”

“Amma kin iya sa kai a uku Dijah, yaran yanzu da suka gama zubar da budurci a waje da tsalle tsalle da ɗaga abu mai nauyi, yanzu ko ƴan gyara mai sauki sauki baza ki mata ba, duk rawar kan da yaron nan yake yi da yaje yaga ba abin da yake tunani ba sai ki ga yanayi ya canza.” ke dai ki ji tsoron Allah Dijah, amma ke da ba’ai miki gyaran ba ai da yanzu wani labarin ake”.

Inna dai bata ce komai ba dan tasan halin daada na mita,…wata katuwar ghana must go daada ta janyo ta fara fitar da wasu itatuwa da dakan gari kulli kulli, ta ce, “to bude idanunki da kyau dijah, haka ta fara lissafa mata daga na tafasawa zuwa na jiƙawa da na sha da nono, ta ƙare da cewa “kuma ki tashi ki fara tun yanzu.”

A bayan kitchen ɗin Inna na sameshi tsaye ya harɗe hannu a kirji,gaskiyar daada ne cewa hamma jay ya rame ya ƙara baƙi sosai, kafe shi na yi da ido,bansan sanda maganar ya fito ba sai ji nayi na ce, me ke damunka hamma jay,baka da lafiya ne?.”

Ɗan matsowa ya yi kaɗan kana ya rankwafo saitin kunnena har inajin sautin numfashinsa ga kamshin turarensa na oud essential da ya cika man hanci, ya ce, “ke ce damuwa ta pretty,”…..”ni kuma?” na faɗa innocently.

“Yes ke ce,amma na kusa warkewa in six days masu zuwa insha Allah”, ya faɗa ya na ɗan murmushi, ” ko ba haka ba amaryata?.”

Turo baki na yi gaba bance komai ba…jingina yayi da bangon kitchen ɗin ya ce, me ne shirye shiryen ki,ganin yadda komai ya zo mana a kurarren lokaci?”.

Da’ace zan iya, cemasa zanyi ni bana son auren,amma nasan furta wannan kalma daidai ya ke da ɗaukewar numfashin hamma jabeer a yanzu. …don haka sai na tsungunnar da kai kawai bance komai ba.

 "Say something mana pretty." 

“Ni bani da wani shiri” na faɗa ina jin wani irin zafi a raina,a tsarina big wedding na ke so a aure na,amma sai gashi ….

“No dole akwai plan ɗin da kuke dashi ke da frnds naki pretty,ki daure ki sanar da ni,plsss wife.”

“Da gaske babu fa,sai dai ko ka nemi umaimah,.ni zan koma ciki”ban jira ya ce wani abu ba na juya na koma cikin gida,…dafe saitin zuciyar sa jabeer dake jingine da bango yayi kana ya rufe idanunsa a hankali yana jin wani irin zogi a wajen,”sonki ya min illa maryama,da’ace nasan inda yake tabbas zan ciroshi ko zan samu nutsuwar zuciya,saidai kash shi so ba ya shawara kafun ya shiga haka kuma ba ya jin rarrashi bayan ya shiga sannan ba ya sanin kan wanda ya ke sauka, wannan shine soyayyata”.

Kamar yadda daada ta umarci innarmu hakan ta yi,take ta haɗa wuta ta fara dafa tsumin yar nijar da daada ta kawo na sha da nono kuwa ta tura fati ta siyo mata nonon,….Da yammacin ranar aka fara bata tsumin kasancewar yana da daɗi tas maryama ta shanye abinta ba tare da tasan minene ba, bayan kamar minti biyu Inna lami ƙanwar innarmu ta shigo da wani abu a kwano ta ce maza tuɓe kayan nan na jikinki zamu fara dirje maki jiki,bansan wani irin sakaci ne wannan adda dijah tayi ba, ace biki saura kwana shida amma ba’a fara gyara ki ba, wannan sam ba dabi’ar zuriyar mu bace ba can ta samo shi wallah,…”ganin ban motsa ba ne ya sata daka min wani tsawan da ya kaɗa min yan hanji don Inna lami ba sauƙi tana da zafin gaske,ko lokacin da muke zuwa nijar bana yadda in kwana gidan ta dan tsananinta.

“Kin ta shi ne ko sai na ma ke ki?” jiki na yana rawa na ta shi na tuɓe kayana sai dan zani da na ɗaura zuwa kirji, haɗin dilkar gargajiya ta fara ɗeba tana dirzar jikina dashi kamar zata canja mani fata…..sosai ta dirje ni sannan ta barni for one hour abun ya bushe sannan ta zo ta kamani zuwa toilet wai zata min wanka, ni abin ma dariya ya bani shirgegiya dani wai za’a min wanka,amma ba yadda na iya don ina turjewa na tabbata ba karamin aikin inna lami bane ta min duka a wajen.Ruwan wankan ma na musamman ne, ga wani kamshi da ya ke tashi aciki kamar gonar turare, nan ta wanke ni tas da wani sabulu na musamman amma ban cire ɗan kampai ba, idan ka kalle ni a lokacin zaka rantse da Allah a inji aka sani aka canja man fata, hmmm wannan ma sau ɗaya kawai akayi.wani mai shima na musamman ta bani mai ɗan karen kamshi da santsi na mulke jikina dashi, take skin ɗina ya ɗau wani irin glowing..ni da kaina na kasa daina kallon kai na a madubi.nan ta fita ta barni tana ta sababin mu yaran zamani bamu san sirrin gyara ba sai iyayi da kauɗi…

UWAR GIDA KEMA KI GWADA WANNAN DILKAR ZAKI GODEMIN 👇

.Lalle

.Kurkur

.Jar dilka

.Madarar ruwa

.Man zaitun

.Kwai guda uku amma kwaiduwar

.Manja

.Lipton

Ki samu ki zuba lallenki, ki juye kurkur akai,dama kin jiƙa jar dilkar ki da ruwan zafi idan ya kumburo sai ki juye akan lallen ki diga manja kaman table spoon ɗaya, shima lipton dama kin jiƙa guda ɗaya da ruwa dan kadan sai ki juye a cikin lallen,ki ɗauko kwaiduwar kwanki ki kada ki juye a kai, sai man zaitun kamar table spoon biyar,sai madara ta ruwa idan lallen dayawa ne zaki juye duka idan kaɗan ne, sai ki sa rabin gwangwani,ki hada ki kwaba su sosai har sai sun hade jikin su, datauri ake so kar yayi ruwa ko kadan, and ba’a samashi ruwa a kwabin iya haɗin kawai ya isa,idan kina so zaki iya ɗiga lemon tsami dan kashe karnin kwan ,sai ki samu container dinki mai murfi ki zuba ki rufe,duk sanda zaki yi amfani dashi sai ki ɗeba ki kara mashi ruwa ki dirje jikinki dashi idan ya bushe ki bambare ki shiga wanka,hmmmm uwar gida har ma da yan mata, idan ku kafara wannan kin huta da kashe kudinki wajen sayan man bleaching……

Daga baya zamu yi bayanin hadin mai da sabulu ɗin…..

Da dare Inna lami ta kuma kawoman wata dafaffiyar kaza haɗe da itatuwa a cikinta waibin cinye ni kaɗai, wayyo duniya ina sonki zan barki,duk da rashin taste da ke tattare da naman kazar gaka na ringa figar ta cin huce takaici, ni maryama na san indai nama ne to ko da ruwan batir aka dafa ta sai na ci,musamman a ce namar ta kaza ce.ina cikin figar kazar da sometimes na kan manta da aure za’a min sai wani abu ya faru ko na ga yan biki nake tuna hakan, ko me yasa hakan?, oho.Kamar daga sama na jiyo muryar innarmu tana ta bambamin faɗa.

“Wato Jabeer ban isa in hanaka abu ba ko, da na ce ka bari ko daga baya kayi shi ne ka ƙi jin magana ta ko”?, faɗa ta ke ta inda ta shiga bata nan ta ke fita ba.

Daada dake fitowa daga bayi har zaninta na ƙoƙarin faɗuwa ƙasa,”ta ce kai wai wa ya ke mana jaraba da farar magaribar nan ne haka?, ɗan shiru tayi bayan an gama mata jawabin abin da ke faruwa, wani irin salati ta saka da ya sa gaba ɗaya jama’ar wajen kamewa ta ce, “amma kedai Dijah ba tsoron Allah a ranki, wallahi kin cika sa kai a uku, ke ba’ayin lefen aka maki? na ce ba’a yin lefe aka maki tun duniya ba ta waye bama balle yanzu da aka waye,?ahah yau naga jaraba ni mero,ki fa fita a idona dijah, yo Allah na tuba mazan nan na yanzu da suka zama yan banza gaba dayansu sun sha bakar wahala sunyi lefen ma ya aka kaya balle an kai masu ƴa hakanan ziƙau uwa marar gata, to ki fitar da kanki a harkar nan, jabeer da mairamu dai kece bare a tsakaninsu.”.

Tsokar da ke baki na na tofar sakamakon maƙalewa da ya yi, na miƙe cikin sanɗa na leƙa tsakar gidan ta gefen labule, hamma jay da ke tsaye kanshi a ƙasa ya goya hannunshi a baya na ke hangowa, sai wasu akwatuna guda uku red colour masu kyau dake ajiye gefe.

“Ke lami maza ɗauko mana tabarma mu baje kaya mu kalla,ni ina can ina tausaya masa ashe ja’irin kuɗi gareshi”cewar daada ta na janyo akwati guda,shimfiɗa babbar tabarma inna lami tayi duk mutanen dake wurin suka zazzauna suka fara buɗe boxes ɗin,fittt na fito tamkar wacce aka turo na tsaya a kansu ina zare ido da rashin sanin takamaiman abin da zanyi.wani mugun hararar da Innarmu ta banka min ya sa ni juyawa ba shiri, daada da ta ganni ta ce “Ina kuma zaki takwara?zo zauna ki ga kayan da aka maki mana, gasunan wallahi duk ba na yarwa a ciki, yo ba dole ya kashe kanshi ya zaɓo maki kaya na gani na faɗa ba, tunda ya samu mata kamar ba hindiya.”cewar ta lokacin da ta ke ɗaga kyawawan zannuwan dake cijin akwatin.

Ban gama jin abin da zata ce ba na faɗa ɗaki wani kuka mai cin rai yana taho min.

Jabeer ya yi ƙoƙari wajen sayan kayan akwatin nan, la’akari da cewa tsakanin jiya da yau kawai ya siye su, kaf kudin da ya ke tarawa dan auren ya kashe akansu, a ganinshi idan da duka duniyar nan ya mallaka zai iya bawa maryama matuƙar zata yi farin ciki. kayane na gani na fada unique one ya zuba cikin akwati guda uku, duk wani abin da ake bukata a lefen masu karamar karfi jabeer ya saka wa Maryama, sosai Innarmu taji daɗi dama tana faɗa ne ganin bai da shi kuma komai na gida ne.bayan an gama kallon kayan aka shigar dasu ɗakin baffanmu aka ajiye su, Daada kuwa ta fitar da nata guzurin da suka yo daga nijar, tabbas duk da rashin wadata da suke ciki yan uwan sun fitar da juna a kunya, ba karamar kudi suka tarawa jabeer ba, ita ko maryama kayan kitchen sosai suka mata both dangin innarmu da na mamar Jabeer da shike duk family ɗaya ne dama….ƙin karbar kudin jay ya yi yace a bawa Innarmu, har saida inna ta nuna mashi bacin ranta sannan ya karba ya na ta godiya ga Allah da yake ta sauƙaƙa masa abubuwa.

Yan da naga rana haka naga dare banyi bacci ba tsabar tashin hankali, yanzu shikenan da gaske aure za’amin aure da hamma jay, shikenan mafarkina da burina ya tashi a banza kenan?…koda na tashi da safiya fuskata ta kumbura suntum, gashi gida ya fara daukar harami dan sai shirye shiryensu suke yi, ina kwance a ɗaki baifi minti biyar ba da fitar inna lami ta zo ta ƙara dirje min jiki da wannan haɗin nata na jaraba, na jiyo sallamar umaimah labulen ta ɗaga ta shigo da fara’arta ta ce, “amarsu ta ango, amarya a gidan hamma jay,” wuri ta samu ta zauna ko kallon inda ta ke banyi ba, ta ce, “pretty ki godewa Allah, yanzu innarmu ta nuna min kayan lefenki, a gaskiya hamma jabeer yayi ƙoƙari matuka gaya, wayyo Allah na inama my yusuf ya min ko da rabin wannan ne,oh Ya Rabb, ta faɗa tana kwanciya saman gadona.

Dogon tsakin da na ja ne ya sa ta miƙewa da sauri, na ce, “yanzu umaima fisabilillahi wannan har lefene da mutum zaiyi alfahari da fatan samun kamanshi? akwati uku fa for God sake, haba mana dan Allah,wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro min.wannan karon saukowa ta yi zuwa gabana cike da tausayawa kawar tata umaima ta kama hannun maryama duka biyu ta riƙe su gam, a ranta tana tunanin anya kan maryama daidai yake kuwa? abun ya fara bata tsoro gaskiya.

Cikin sassauta murya tace, “Maryama ina ji maki tsoron ranar da zakiyi nadama marar amfani, ina ji miki tsoron ranar da zaki fara sharar kasuwa a maimakon ta masallaci,Maryama irin son da hamma jay ya ke maki zai iya mallaka miki komai kamar yadda ya mallaka miki wani sashi na jikinsa a baya,ki yi tunani mana pretty, yanzu da bai da shi ma yana fafutuka a kanki duk don kiyi farin ciki, me kike tsamanni zai faru idan yayi arziki, karki manta kuma dare ɗaya Allah kanyi bature, plssss Maryama kar ki zama butulu karki bar hamma jabeer da tabon da bazai warke ba a rayuwar shi, ke yanzu a tunaninki arziki shine farin ciki? mutane nawa ke rayuwa da arziki amma ya kasa basu farin ciki? wasu ga dukiyar amma ba ƴaƴa, wasu ko ba bu lafiya kuma dukiyar ya kasa samar musu da lafiyar,..babbar arziki maryama shine lafiya, kina ji kina gani kina magana kina tafiya, ko ina ajikinki yana motsi, Maryama wasu da dukiyar amma sun rasa wannan,…kuka ne ya ci karfin umaimah tilas tayi shiru, gaba ɗaya jikin maryama ya yi sanyi kalau hannu ta sa tana sharewa aminiyar tata hawaye,…ɗan murmushi tayi tacigaba da cewa hamma jay ya tambaye ni me shirinmu wai ke kince babu abin da zaki yi, so mun yanke da ke cewa zamuyi walima kawai ya isa tunda ga halin da ake ciki…tsawon awa ɗaya umaimah ta yi a gidanmu tana ta tsara min yadda abubuwa zasu kasance sannan ta tafi…yauma inna lami ce tamin wanka ba shakka ina dirjuwa dan sau biyu kawai aka min amma ni da kaina nasan na canja….bayan na fito wanka na fitar da wayar da siyama ta bani dama boyeta na keyi kullum, missed calls na sadeeq na gani kusan goma, kafun in kira shi kiran siyama ya shigo wayata….”Maryama me nake ji haka? da gaske aure za’a miki nan da five days?”

Fashewa na yi da kuka nace, “wai siyama”

Wani irin ashar siyama ta labta saanan tace ,”kuma kina zaune baki ce komai ba? gashi sadeeq ya ƙirani har ya turo min ƙudin jamb naki wai yana ta kiranki tun jiya baki dauka”, dage kirji nayi nace, “da gaske siyama? yaushe ya turo? kinsan dama nace, masa su innarmu sun amince da maganar makarantar,yanzu yaushe zamu haɗu?” duka a hankali nake maganar dan kar in janyo hanklin mutane zuwa kaina…munyi magana ya kai na minti bakwai ni da siyama kafun muka ajiye waya,kwakwalwata ta fara nazarin maganganunta,anya zan iya abin da ta sani kuwa,anya?.

A bangaren siyama kuma tana ajiye wayar wani irin tsalle ta yi tana dariya ta ce, yarinya bazan taɓa bari kiyi auren nan ba ki toshe min hanyan samu na sai na ɓamɓari rabo na, wayar ta ta ɗauka ta kara kallon alert na 500k da sadeeq ya turo mata wai ta bawa maryama ta zana jamb.hmmmm lallai boss ya shiga da yawa, yasin nima sai na ci rabona.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah cikin kwana huɗun da suka biyo baya abubuwa dayawa sun faru, jabeer ya gama gyaran gidanshi wanda ya fito sak na amarya, su innarmu sun gama haɗa kayan kitchen da na gado har anje anyi jere an kuma yi kayan fulawa irin su cincin da sauran su.wayar mu da sadeeq kuwa sai abinda ya qaru dan ma gidan a cike ya ke yanzu, umaima kuwa ta yi kokarin haɗa kan ƙawayen mu gaba daya, yayinda maganar da muka yi da siyama ya ke cigaba da yawo a kwnayata, hamma jay kuwa duk yadda ya so inje inga gida ƙi nayi thou kwana biyun nan ya shiga busy shima.yau alhamis akayi walima kamar yadda umaimah suka tsara abun ya tafi cikin tsari gwanin sha’awa, malamar da suka gayyato tayi wa’azi mai shiga zuciya sosai,saidai ko kaɗan banji ba, duk da cewa dan ni akayi amma hankali na ya tafi wata duniyar na tunanin maganganun siyama.

Karfe shida aka tashi walimar kowa ya kama gabanshi sai kuma gobe ɗaurin aure, kawayen inmarmu da suka dawo gidanmu sai an gama biki kuwa suka hau gyaran gida da shirin abincin liyafar bayan ɗaurin aure. bayan sallar isha na ji alamar ana kiran wayar da na ke ta boyewa cikin bra dina, dan haka na zari buta na shige bayi na buya siyama ce, dan haka da sauri na kama na kara a kunne na.”Pretty baki manta ba ai ko? ina nan jiranki a kasan layi karki manta basai kin ɗauki kaya ba kinji ai ko,cikin mutuwar jiki nace, “amma siyama bakya ganin…” katseni ta yida sauri ta hanyar fadin, “haba mana ba min gama wannan maganar ba? karki maida mu baya mana, duk fa ina wannan ne dan taimakonki.”

“Shikenan zan yi ƙoƙari insha Allah.”

Dare yayi misalin sha ɗaya da rabi lokacin kowa yayi bacci, masu girkin ɗaurin aure ma sun girka tukwane kowa ya shiga saboda yanayin sanyi da ake ciki, ɗakin mu ma cike yake da ƙawaye na waɗanda zasu kwana ciki har da umaimah, a hankali na buɗe idanuna kana na sauƙe kafata cikin sanɗa na fita daga ɗakin ba tare da making any sound ba, ba abin da na ɗauka kamar yadda siyama ta ce sai zumbulelen hijab dake jikina.A tsakar gidan na tsaya ina karewa ko ina kallo, hawayen da nake ta riƙewa suka silalo min saman fuskata, da sauri na juya na nufi kofar fita zuciya ta tana bugun tara tara………
💫MARYAMA💫

Typing📲

Episode 21/22

By

(Ummu Fadeela).

__________Tsayawa na yi ina ƙarewa gidan namu kallo wasu zafafan hawaye su na gangarowa saman fuskata,a hankali na juya na nufi hanyar fita…..Taku ɗaya na biyu na ji an riƙe hijabi na ta baya,dum dum dum haka kirjina ke bada sound kamar zai faɗo ƙasa.

“Ina za ki je da dare haka ba ki tada ni na raka ki ba?,ke bakya jin tsoron dare ne?”.

Muryar umaimah ta da ki dodon kunne na,Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un,na ke ta nanatawa a raina,” umaimah why now?”. Da kyar na yi gathering courage na juyo ina ɗaura fake smile saman fuskata, muryata ta na makyarkayata na ce, “ehmm ammm ehhh umaimah toilet zanje me ya hanaki bacci,? da ba ki fito ba ai”.gaba ɗaya na birkice kallo ɗaya zaka min ka fahimci zallar rashin gaskiyar dake tattare dani.

Bacci ne ba bu a idona thats why”cewar umaimah tana kamo hannuna, kamar raƙumi da akala haka na bita har bakin randunan Innarmu ta tsugunna ta ɗauki buta kana ta miƙamin ta na ɗan murmushi ta ce, “Kin manta ba ki ɗauki buta ba amarya,and can ne hanyar bayin ba inda kika nufa ba, kodai duk fargabar haɗuwar ku da hamma jay gobe ne ya fara rikita ki tun yanzu?” ta faɗa ta na ɗan sakin karamar dariyar da iyakarshi leɓenta.

Girgiza kai na yi cikin rashin sanin abin yi na karbi butar na shiga bayi…kasan hijab nata umaimah ta kama tana share wasu hawayen da suka silalo mata a ranta ta na mamaki halin Maryama,ba dan ta gano take-takenta ta ƙi yin bacci ba da yanzu shikenan tafiya fa zata yi,Hasbunallahu wani’imal wakeel…jin shirun ya yi kamar an tsikare ta umaimah ta kwasa a tamanin ta nufi toilet ɗin tunawa da ta yi kar fa ta kama katanga ta gudu.kicibis suka yi bakin kofar umaimah ta na sa kai ita kuma ta na fitowa, a razane ta koma baya ta na zaro ido ga mi da faɗin mene ne umaimah?.

“Babu komai fa, kamar kyankyaso ne ya hau min ƙafa shisa na tsorata”….”Allah har kin tsorata ni nima,”

“To a yi hakuri amaryar gobe,zo mu koma ɗaki kinsan ba’a barin amare su kaɗai, still na yi a wajen ban motsa ba saidai idanu na dake karewa umaimah kallo duk da cewa dare ne yayinda kirjina ke luguden bugu, a mamaki na kuwa na kasa yin ko wani irin tunani,ji na ke kamar ƙwaƙwalwata ta zama blank…ganin na tsaya kamar statue ya sa Umaimah kamo hannuna yanzu ma ta jani har cikin ɗakinmu ta maida ni kan gado inda na tashi tunda farko, ina zama na ji wayar da ke jikina ta ɗau vibrate,rumtse idanu na yi da karfin gaske dan na san Siyama ke kira na.

A ɓangaren Siyama kuwa tun tana tsaye ta na jiran Maryama har ta nemi waje ta zauna,ga sanyin da ake tabkawa ga tsoron da ke shigar ta na dare bata jin motsin komai sai kukan dabbobi da tsuntsaye mabanbata sauti.sa ke ƙiran layin Maryama ta yi a karo na barkatai amma no answer, “Me yarinyar nan ta ke nufi ne?,…ai wallahi ba ki isa ki ja min asarar dubu ɗari biyar ba a na zaman lafiya,yanda na ƙwallafa rai a kan kuɗin nan sai na cisu wallahi, kuma na san wannan so min taɓi ne yadda oga ya kwallafa rai a kankin nan,”.Sake gwada layin ta yi wannan karon matar mtn ce ke sanar da ita layin a kashe yake.”What the f**k”cewar Siyama ta na kallon screen na wayar ta, da hanzari ta miƙe ta kama hanyar gidan su Maryama. (niko na ce ayye karfin hali, ko mai zata je ta yi gidansu pretty da tsohon daren nan?).

Baifi ta ku goma ta yi ba ta ji haushin kare a bayanta,a zabure ta juya za ta gudu ta ji wani haushin ta gabanta kamun ta ankara ta fara jin haushin karnuka ta ko ina kamar ta shigo kejinsu, a ɗari da tamanin siyama ta fara gudun ceton rai, karnukan ma ba su yi ƙasa a guiwa ba suka rufa mata baya.Gudu Siyama ke yi kamar na famfalaƙi ga dare ga duhu ga tsoro da fargaba,garabb ta ji ta bugi wani katon dutsi sama sama ta yi ta faɗo ribbb a ƙasa hakan ya ba karnukan daman wuceta,wani irin marayan kuka ta sake jin wani irin azaba ya ziyarci kwanyar ta, ta ke hakorinta na gaba guda ɗaya ya faɗi ƙasa duk da azabar da ta ke ji haka ta miƙe ta ƙara ƙaimin gudunta ba ta yi aune ba ta ji ta afka cikin wani ƙaton rami dake gabanta,wani irin wari ne ya ziyarci hancin ta,kana wani kalar ruwa ya cika mata baki, ashe lambatu ne mai cike da ruwan dauɗa hajiya siyama ta faɗa a ciki lokacin da ta ke gudu. wannan karon ma da kyar ta fitar da kanta daga lambatun tana tafiya cikin dingishi sai sa’a ma idan bata samu dislocation a guiwar kafa ba tsabar azabar da ta ke ciki, da kyar Siyama ta kai kanta gida, da ya ke ita ke mulkar iyayen su kuma bayinta, kamar yadda ba wanda ya san fitan ta, haka ba wanda ya san dawowar ta, tana shiga ɗakin ta ta faɗa bathroom ta haɗa ruwan zafi cikin dauriya ta gasa jikinta mai kyau, madubi ta kalla ganin ba hakorinta guda tayi saurin rumtse idanunta ta na jin wani irin tsanar kanta, a gefe guda kuma ta na tunanin irin sakamakon da zata tanadarwa Maryama.kafun wani lokaci zazzabi mai zafi ya rufe siyama sai makyarkyata ta ke akan gado ita kaɗai, ta yi kokarin laluben wayarta amma bata gane ba, ta na ma tunanin ta yar da ita a hanya ne…..

………………+++++………………..

Yadda na ga rana haka naga wannan daren ba tare da na rintsa ba nayi kukan zuci da na bayyane marar sauti, kukan da na kwana yi shi ya haddasa min ciwon kai mai tsananin gaske da har bana iya ganin abu mai kyau sai dishi dishi.ga wani irin nauyi da kaina da kirjina suka yi tamkar an danne su da dala da gwauron dutse, da wannan yanayin na wayi gari da asuba ma a zaune na yi sallah shima ina idarwa na kwanta a nan saman abun sallar. a hankali na ke jin duniyar ta na sauya min wani irin sanyi yana shiga duk wata hudar gashi dake jikina, ko wacce second na bugawar agogo tana bugawa ne ta re da tunanina na kubcewar wata dama da nake da ita, kana ko wacce second tana wucewa ne tare da kusantowar wani al’amari mai girma a rayuwata, ya kamata mai karatu ya sani, ba wai hamma jay ne a karan kanshi bana so ba,a’a yanayin talaucin da ya ke ciki ne ba naso. haba mana na taso cikin talauci sannan in yi aure cikin talauci duk da kyau da na ke dashi? Inna lami ce ta zo ta tada ni daga kwancen da na ke,sama sama nake jin abin da ta ke faɗa kamar daga nesa ta ke min magana,jijjigani ta yi tana faɗin, “Lafiya kike kuwa maryama,? ga ruwan wanka can an haɗa wuce muje a miki wanka”.Umaimah ce ta shigo ɗakin sai warin hayaƙi ta ke yi, tun asuba dama suka shiga cikin masu aikin girki su na ta aikace aikace, ta na murmushi da salon tsokana ta ce, “ta zama ta zama ta zama woo ta zama ɗauko rig,….” kafun ta gama na fashe da wani matsanancin kuka, dama mai neman kuka ne aka harbeshi da kashin awaki.

Inna lami ce ta ce, “ke umaimah ba ni son tsokana yaushe ta zama wani abu,”maza wuce ki fitar mata kayan da zata saka idan mun fito wankan sannan ki haɗo mata abun breakfast da wuri kinga lokaci yana tafiya ga mutane sun fara taruwa amarya bata yi wanka ba.”

Ƙeyata inna lami ta tisa gaba muka fito, aikam gidan namu danƙam yake da mutane ta ko ina sai hada hada ake yi Innarmu dai ban ganta ba, kodan dishi dishin da nake ganin kowa ne ban sani ba, kaina a kasa muka shiga bayin yauma ita ta min wanka ta sille ni tas, na dawo ɗaki,duk yadda umaimah ta so yiman light makeup ƙi na yi, da ace ta san irin haushin da take bani ko inda na ke bazata matso ba, amma ita ba ruwanta sai wani rawar kai ta ke yi.kaya kawai na sanya na kwanta ko mai ban shafa ba, sanyi na ke ji sosai yana shiga jikina, duk magiyar da umaimah ta ke min na in tashi inci abinci ƙi na yi, ba don bana jin yinwa ba sai don jirin da ke kwasata, ina daga kwance bansan ta fita ba sai shigowar su ita da daada na ji,rarrashina daada ta dinga yi har na tashi nasha ruwan shayi kadan da shinkafar da aka dafa shima baifi spoon uku na ci ba na fara kwarara amai a wajen…….Ina kwance har kusan sha daya na safe, aman da nayi ɗazu ya ƙara bada gudunmawa wajen rashin kuzarin da na ke tatyare dashi a yanzu, jikina yayi zafi zau kamar ana hura wuta ta ciki.

    .....................................

A massalacin dake anguwar mu za’a ɗaura auren dan haka anguwar a cike take danƙam da mutane matasa sa’annin hamma jay da dattijai da kuma yara, can na hango Jabeer cikin wani rantsatstsen getzner fara sol sai maiƙo ta ke yi, babbar riga da yar ciki da wando, ya murza hular dara sai walkiya take yi, ba shakka Jabeer ya yi kyau a wannan rana fuskarshi ta yi fayau ya dan faɗa kaɗan sai fara’a ya ke yi tamkar mai tallan closeup…zagaye da shi abokanshi ne da sauran yan uwa da abokan arziki da suka hallara don shaida wannan daurin auren dake cike da soyayya mai daɗaɗɗen tarihi,can gefe kuwa baffanmu ne da abokanshi su baban umaimah sai liman da sauran dattawan anguwa.baffanmu ne wakilin Jabeer, sai liman da ya zama waliyyin Maryama.

Bugawar agogo karfe sha ɗaya ya yi daidai da bugawar zuciyata da karfin gaske wanda ya sanya ni mikewa da sauri daga kwance da na ke zuwa tsaye, a lokacinne kuma na jiyo muryar wani maroƙi ya ratsa loudspeaker zuwa cikin kunnena, ” Alfatihaaaa,an ɗaura auren Jabeer da amaryarsa Maryama akan sadaki…….laƙadan ba ajalan ba, mu ƙara yiwa Annabi salati, (S A W).

Take na fara jin ɗakin yana juya min, sautin guɗar da mata keyi a tsakar gidan na fara jiyo shi kamar ihu, a hankali ji na ya fara ɗaukewa, duhu ya fara mamaye gani na cikin ƙasa da second biyar na sulale ƙasa sumammiya…….. ..
💫MARYAMA💫

   BY

Ummu Fadeela.

Typing📲

Episode,23/24.

________A hankali na buɗe idanuna waɗanda na ke jin su tamkar bishiyar da ta kakkafa rassa,ɗakin na fara bi da kallo duk da kamar dare ne hakan bai hana idanuna sauƙa a kanshi ba,yana zaune bisa farar kujera sanye da kayan da ya je ɗaurin aure da su, saidai babu babbar rigar yar ciki ce kawai da wando hannunshi riƙe da hula kanshi ya ɗan karkace kaɗan bisa kafaɗunshi,idanunshi rufe da alama bacci ne ya ɗauke shi ba ta re da ya shiryawa hakan ba, fuskarshi ta faɗa ta yi fayau sosai sai wani haske da ya yi.a can gefe kuwa Inna lami ce ƙanwar Innarmu ta ke sallah sai baaba fa’iza yayar mamar su hamma jay ta na zaune bisa wani gado dake ɗaya bangaren ɗakin ta yi tagumi da hannu biyu.

Dogayen hannayena da ke ɗauke da canulla na bi da kallo, a hankali na ke jin tafiyar ruwar da aka maƙala min yana bin jijiyoyina zuwa cikin jikina wanda ke alamta min cewa asibiti na ke,ta ke abubuwan da suka faru har ya haddasa min ɗaukewar numfashi ya shiga rige rigen dawo min cikin ƙwaƙwalwata,gefen yatsa ta na sa na share wasu hawaye da suka gangaro min cikin idanuna zuwa kan filon da na ke kwance a kai…Ɗan motsin da ta yi ne ya farkar da jabeer da dama baccin nasa bai je ko ina ba tsabar stress,suna wajen reception da za suyi na ɗaurin aure ya samu mummunar labarin cewa pretty ta faɗi a sume a na ta yayyafa mata ruwa amma ko motsi batai ba,ai bai jira ya gama jin labarin ba ya nufo gida hankali a tashe, isowar shi kuwa ya zare babbar rigar shi ya cicciɓi maryama sai asibiti inda inna lami da baaba fa’iza suka rufa masa baya, da gaggawa likitoci suka amshe ta a ka fara bata taimakon gaggawa da kyar suka yi nasarar janyo numfashin maryama da yayi nisan zango saida aka tabbatar da ta zama normal sannan suka mata allurar bacci daga bisani aka turata daƙin marasa lafiya, tunda suka zo jabeer ke tsaye bisa kafafunsa ya kasa zaune, dole ka tausaya masa yadda ya zama shima kamar mara lafiya har yanzu da ya kasance karfe bakwai na dare sallah kawai ke matsar da jabeer daga kusa da maryama, ba yadda su inna lami da sauran yan bikin da suka biyosu daga baya basu yi ba akan ya je gida amma jabeer ya kasa tafiya, yana ganin kamar idan ya matsa wani abu zai faru da maryamar shi.

“Pretty kin ta shi?.me kike so kici yanzu?akwai inda ke maki ciwo ne? ko in kira likita ya zo ya ganki?.”

Waɗannan sune jerin gwanon tambayoyin da hamma jay ke jero min fuskarshi ɗauke da tsananin kulawa da tausayawa kana da zallar soyayya mara algus, har cikin raina ya bani tausayi dan haka bansan sadda na fashe da kukan da ni kaina bansan dalilin yinshi ba….Kuma rikicewa ya yi yana faɗin “ina ke maki ciwo pretty?ko in kira likita? ki daina kuka mana karki ƙara wa kanki wani ciwon kuma,gaba ɗaya ya fice a cikin nutsuwarshi,ji yake kamar ya maida ciwon jikinsa a gefe ɗaya kuma kukanta na ƙara tayar masa da hankali.

Dafa goshina baba fa’iza ta yi tun maganar da hamma jay ya yi da farko ta taso ta matso garemu. “Sannu yata, ki daina kukan haka, jabeer maza kirawo likitan dan ya shigo ɗazu ta na bacci” ta faɗa ta na kallon jay,bai jira ya gama jin abin da ta ke faɗa ba ya nufi waje da hanzari.kicibis suka yi da likitan yana shigowa don haka jabeer ya koma baya ya ba shi hanya, da fara’a irin nasu na likitoci cike da barkwanci ya ce, “a’a kaga ango, bada kanka a sare kaje gida kacewa amarya ya faɗi, amaryar ta mu ta farka ne?.”

Murmushi ne ya kubcewa jabeer ba tare da ya shirya ba, haka kuma baice komai ba, dan shi kaɗai yasan abin da ke damunshi a jiki da zuciya…

Ƙarasawa gaban gadon dr.ya yi, ya ɗan dudduba maryama abun gwada bp ya fitar ya gwada ta ya na kallonta ya ce, amarya a dinga rage damuwa Allah ya ƙara sauƙi, da hannu ya yiwa jabeer alamar ya biyoshi zuwa office,suna fita inna lami ta idar da sallah ko addu’a batai ba ta taso gareni tana jeramin sannu itama.

Da kai na amsa mata sannan cikin dabara na kai hannuna cikin bra ɗina,dan wannan tunani ke man yawo tun ɗazu… wani irin ajiyar zuciya na sauƙe jin na taɓa wayar Alhmdllh tana inda na maƙala ta bata faɗi ba.

Bayan shiru na kimanin minti biyu likitan na ƴan rubuce rubuce cikin wani takarda ya ɗago ya kalli jabeer ya ce, “ku kwantar da hankalinku jikinnata da sauƙi sosai,sai dai jininta ya na ƙoƙarin hawa kuma hakan ya bani mamaki matuƙa because ta yi ƙanƙanta dayawa dan haka ku dinga kiyaye bacin ranta,zuwa gobe za’a iya baku sallama Insha Allah…”Ƙuri jabeer ya ma likitan da idanu ba tare da ya samu zarafin cewa komai ba,zuwa can ya yi karfin halin cewa, “dr. nima inaso ka duba min nawa bp ɗin”.

Kallonshi likitan ya yi ya ce, “akwai wasu alamomim da kake ji ne?”

Jinjina mishi kai ya yi, janyo abin gwajin dr yayi ya ɗaure a tsintsiyar hannun jay ya fara gwada shi,bayan wasu ƴan mintuna ya cire haɗi da dafe kumatunshi da hannaye biyu sannan ya ce,”meke damunku ne kaida amaryar taka? gashi nan kaima jininka ya hau fiye da ƙima and your condition is not encouraging karka manta da halin da kake a ciki, kuma na ga kana wasa da karɓar magani akan lokaci jabeer ki…..” Katse shi jabeer ya yi da sauri ta hanyar faɗin, “Na gode dr, what next yanzu?

Rubutu ya yi kaɗan saman wani paper ya miƙa mishi yana gyara zaman glasses na shi ya ce, “kaje pharmacy a baka wannan, kuma ka dinga ƙoƙarin ganin ka ragewa kanka damuwa karka manta da health status naka, tun bayan da aka cire maka kidney guda ɗaya, ga ɗayar ta fara bushewa and kana wasa da magani jabeer ka dinga kulawa shi rai guda ɗaya ne fa, idan ya fita shikenan”.

Hannu jabeer ya miƙawa dr bayan ya miƙe sukayi musabaha ya fita.Tun bayan da jabeer ya donating wa maryama ƙodar shi guda bai daɗe ba ya fara wani irin rashin lafiya a tsaye amma bai faɗiwa kowa ba lokacin yana university abun ya ci karfin shi saida aka kaishi asibiti a hannu nan likitoci suka tabbatar da ƙadar shi ɗaya ce kuma ta fara samun matsala, an laura shi akan medication ba laifi ya ji daɗin amfani da su har dawowar shi gida idan abun ya tashi mishi yakan je ya ga likita ba tare da kowa ya sani ba. …Lokacin da ya dawo ɗakin ina zaune kan gado da pillow a bayana hannuna riƙe da kofin shayin da inna lami ta haɗa ta kuma tilasta min sha, haɗa idanu muka yi dashi ya sakar min lallausan murmushi, gabana ne ya wani irin faduwa har na kusa sakin kofin dake hannuna, amma na yi saurin damƙewa.

“How you feeling now pretty?.”

Ya tambaye ni lokacin da ya iso saitin gadon da nake kai.” da sauƙi na faɗa ba tare da na yadda mun haɗa idanu ba dan wani irin kwarjini na ga ya min yau ɗin,juyawa ya yi yaiwa su inna da baaba sannu sannan ya janyo kujera ya zauna ya jinginar da bayanshi gami da lumshe idanu, samun kaina na yi da kasa barin kallonshi, tabbas akwai abinda ke damunshi dan ba ɗabi’ar hamma jay ba ne zama shiru musamman in ya kasance ina wajen…yana zaune ɗakin har wajajen 11 na dare sannan inna lami ta sa baki ya koma gida.

Washe gari aka sallamo ni muka dawo gida, yawancin yan biki sun watse sai ɗaiɗaiku da kuma tawagar daada, faɗa baffanmu ya dinga yi wai me aka kawo ni inmasa a gida,? gidana za’a wuce dani ai, saida daada ta sanya baki sannan ya haƙura a miƙani zuwa dare,…duk abun da aka sanyawa lokaci tabbas zai zo saidai mune bamu da tabbacin kaiwa lokacin…ko motsin kirki banyi ba naji har isha ta yi, ana idar da sallah kuwa aka sani ƙara yin wanka na shirya cikin wani haɗaɗɗen leshi coffee colour mai touches na cream colour cikin kayan da inmarmu ta dinka man na fitar biki, riga da zani sai ɗankwali da umaima ta ɗaura min nidai binta kawai nake yi duk ta yadda ta juya ni kamar mutum mutumi, su uku ne suka rage cikin ƙawayena da zasu min rakiya,ba shakka na yi kyau matuƙa tamkar ka sace ni ka gudu, ga wani irin walƙiyar da jikina keyi na gyaran da yasha hannu da ƙafafuna zane suke da lalle ja da baki mai ɗaukan hankalin mai kallo kasnacewar ya samu farar fata, wani zani aka ɗaura min saman gyalen da na lulluɓa dashi ya rufe min fuskata ruff wannan karon daada ce ta riƙe ni muka fito, kukan dana ke ta riƙewa ne yayi nasarar kibce min, kuka nake yi kamar zan mutu, “dole ki koka yannan, aure yaƙin mata kana zaman zamanka da iyayenka rana tsaka a dauke ka a damƙawa wani ƙato idan ba Allah ya haɗaka da mai hankali ba duk sai ka firgice a take ka zama kamar mai shekaru ɗari a duniya, to dai bance ki raga masa ba idan ya taka ki ki takasa kema dan yanzu maza duk sun zama yan banza sai kin nuna musu kema yar iska ce zaku daidaita”. cewar daada tana gyara zaman mayafinta tamkar ma ba abun da tace,.

Ɗakin Innarmu ta fara kaini, tana zaune a bakin gadonta, daada ta ce, gata nan dai Dijah sai ki mata nasiha, koda dai babu abun da ya rage ban faɗa mata ba, amma saboda haƙƙin zama tare gata ki faɗi wani abu a girguje kar mu makara,” murmushi inna ta yi tace , ai daada tunda kin mata nasiha basai na ƙara cewa komai ba, maryama dai ba yarinya bace, she know what’s right from wrong, dan haka kiyi amfani da iliminki, shi aure dai ibada ne, shi ibada kuma sai an dage an jure an sanya haƙuri kamun ake yinshi yadda ya kamata, basai na tuna maki waye jabeer a wajenki ba,duk sanda kika so sanin waye shi a wajenki, ki dubi bangaren cikinki na dama, idan kinyi da kyau kanki idan akasin hakanma kanki, je ki Allah ya maku albarka ya sanya farin ciki da zuriya na gari a cikin rayuwar aurenku…wani kukan da ya fi na farko karfi na saki na tashi na rungume innarmu, da kyar aka bambare ni a jikinta, baffanmu ma ya min nasiha sosai mai ratsa jiki da ɓargo…haka inaji ina gani aka fita dani zuwa gidan hamma jay dake kasan layinmu, yan rakiyar basu fi minti talatin ba kowa ya kama gabanshi, riƙe rigar umaimah na yi ina kuka da faɗin, “umaimah kema tafiya zakiyi ki barni,?dan Allah karki barni ni kaɗai a gidan nan tsoro nake ji”.

“Ba tafiya zan yi ba pretty rakasu zan yi in dawo ki jirani yanzun nan” cewar umaimah, sakinta na yi ba don na so ba sai don yarda da ita da na yi, na koma saman doguwar kujera na zauna,..tashin hankalin da na ke ciki bai barni na ga irin kayan da iyaye na suka kashe kuɗi wajen sai min ba…tun ina irga mintuna har na gaji ba umaimah ba alamunta, wani irin tsoro ne ya fara mamaye ni…haka na daure na ci gaba da zama ni kaɗai tamkar mayya…

A kofar gida jabeer ya ja ya tsaya,yana kallon abokanshi da sukayo gayya zuga guda wai zasu sayan baki ya ce, “to duk na gode muku da rakiya kowa ya koma gidanshi mai mata yaje ya rungumi abarshi gwauro kuwa ya rungumi pillow ya haɗa da istigfari”. ta ke wajen ya kaure da hayaniya har kowa baijin abinda ɗan uwanshi ke faɗa,masu zolayanshi wai kishi ya ke nayi, masu rama gorin da ya musu suna yi daga karshe dai suka rabu a wajen shikuma ya shige gida haɗe da garkame kofar da sakata fuskarshi cike da farin ciki yai gashi ga pretty zasu kwana gida ɗaya a matsayin ma’aurata shiko mai zaiyi ya tabbatar da godiyar shi ga ubangiji?.

Da murmushi ya iso bakin kofar palon dake ta kamshin sabon fenti da sababbin furnitures…Ina zaune saman doguwar kujerar har lokacin gabana sai dukan tara tara yake yi ba tare da wani dalili ba, ban yi aune ba naji wayar dake maƙale cikin jikina ya fara vibrate,da sauri na fitar da shi zaro ido nayi kirjina na luguden daka ganin mai kirana, “SADEEQ?”Na faɗa da ɗan sound kaɗan ina ci gaba da zare idanu hakan kuwa yayi daidai da shigowar hamma jay hannunshi ɗauke da wani katon leda baƙa,wani irin hantsilowa nayi daga saman kujerar na koma edge na ɗakin ina ɓoye hannuna dake riƙe da wayar a bayana jikina yana rawa kar kar kamar naga dodo,ajiye ledar jay yayi sannan a hankali ya fara takowa zuwa inda na ke……..
💫MARYAMA💫

EPISODE 25/26…

ELEGANT VERIFIED WRITER’S

__________Kowane taku idan ya yi sai zuciya ta ta harba da karfin da ya ke sanya gabana faɗuwa,cike da izza ya ke takowa gare ni fuskar shi ɗauke da mixed expression,saura baifi taku biyu ya riske ni ba nima na fara ja baya yana matsowa ina matsawa har na iso bakin kofar bedroom, kamar walƙiya na shige cikin bedroom ɗin na turo kofa da ƙarfin gaske haɗi da murza makulli, jingina na yi da jikin kofar ina sauke wani irin tagwayen numfashi.

A palo ma jingina da kofar jabeer ya yi ya na sauke numfashi gami da shafa lallausan gashin kanshi a zuciya ya furta “drama queen”.A fili kuwa cewa ya yi a hankali, “pretty yau kuma ni kike gudu ko? Am I a stranger?.” Shiru na yi bance komai ba sai turo baki da na yi gaba.jin na yi shiru yasa shi ƙarayin ƙasa ƙasa da murya ya ce, “ohk to ki fito ba bu abunda zan maki fito kiga wani abu.” still bance komai ba sai ma godiya ga Allah da nakeyi da ya kasance baiga wayar da na ke riƙe da ita ba, gashi sai kuma ƙira Sadeeq ke yi ina ta matse wayar jikin cinya ta.lallashin duniyan nanba wanda hamma jay bai yi ba amma naƙi buɗe kofar, daga karshe saman kujera ya koma ya zauna gami da rufe fuskarshi da hular da ya cire a kanshi….sau huɗu Sadeeq ya na ƙira duk yanda zuciyata ta ke kwaɗayin jin muryar shi kunnuwa ta ke muradin jin kalamanshi amma gangar jikina ya kasa bani haɗin kai wajen amsa kiran, sako ne ya shigo wayar jikina yana rawa na buɗe…..

“Ahhh baby girl, ina kika yarda wayarki ne ina ta ƙira, idan kinga sakona call me imediately i want to hear your sweet voice, byeeee” na karanta content ɗin ya fi sau goma a hankali na fara zamewa har na kai kasa na yi zaman dirshan a wajen ina jin sanyin da jikina ya yi yana ƙaruwa.na shafe a ƙalla mintuna talatin zaune a wajen ba tare da na iya yin tunanin komau ba, daga karshe na miƙe na zauna bakin haɗaɗɗen gadona dake ɗakin, ba ƙarya su innarmu sunyi ƙoƙari wajen saya min kayan ɗaki masu inganci.kamar an tsikare ni na tashi da sauri na kashe wayar na ɗaga kasan katifa na jefa ta a ciki yadda zan iya ɗauka da safe.

Jabeer ya daɗe zaune wajen yana ta sakawa da kwancewa, ya daɗe da sanin cewar soyayyar maryama tana ɗaya daga cikin manya manya jarabawarshi na rayuwa wacce ya ke fatan Allah ya bashi ikon cinyewa…tashi yayi daga karshe ya fara rage kayan dake jikinshi, daga shi sai boxer da singlet ya rage ya nufi hanyan fita,wani irin wawan birki ya ci sakamakon karo da ya yi da ledan da ya shigo da shi mai ɗauke da gasashshiyar kaza, da fresh milk sai kayan tea da tarkacen su choculate wanda yasan mutuniyar tashi ta na so tun duniyar su na zaune qalau…Murmushi ya yi yana cusa hannunshi cikin gashin kanshi, ya ce, “Wannan shi ne daren farkon ka Jabeer, “wani murmushin ya kuma yi ga mamaki na ba alamun fushi a fuskarshi. kitchen nasu ya shiga dake cike da kayan amfani ya ɗauki bocket ya fito ya debi ruwan dake cike a randar roba ya shiga bayi don yin wanka..kasancewar dare ya fara nisa ga kuma sanyin da ake tabkawa irin na damuna sai bai jima a bayin ba ya fito ya ɗaura alwala kana ya haɗa buta da bokitin ya mayar kitchen ya fito saida ya tabbata ko ina a rufe,ya shige palon kulle kofar palon ya yi sannan ya zauna ya fara tunanin mafita,ɗan murmushi ya kuma yi a karo na barkatai kana ya shafa kanshi zuwa beard nashi cikin kamala jabeer ya tada sallah bayan ya maida rigar da ya cire,nafila ya yi inda ya daɗe a raka’ar karshe ya na godiya da jinjina ga ubangijin talikai mai kowa mai komai da ya mallaka mashi burin ranshi, yau gashi ga Maryama za su kwana the same roof same bed and the same……..tsawon lokaci ya ɗauka yana miƙa godiyar shi ga Allah.

   ..................*******...................

Zazzaɓi sosai ne ya rufe Siyama cikin dare, kar kar kar jikinta ke rawa gashi ta yarda wayar ta a gudun famfalaƙin da tai.haka tayi ta fama har asuba da mamanta ta shigo tashin ta ta yi sallah, “Subhanallah!Siyama me ya sa me ki?wa ya miki haka?”.cewar mamanta ganin halin da ta ke ciki…ko kanta Siyama bata iya ɗagawa.

Kamota uwar tayi tana ihu da faɗin wa ya miki haka,jin muryar ta ta na kuka ne ya janyo hankalin babansu dake shigowa daga masallaci,da hanzari ya faɗa ɗakin.

“Kaga abun da nake faɗa maka ko malam?ni daman na daɗe da sanin mutane sun sa min ƴa a bakin duniya ganin ta na samun kuɗi ta rufa mana asiri mun fi karfin neman taimako a wajen mutane,dubi abin da aka shigo har gida a ka mata wannan cin zalin har ina?kuma wallahi bazamu ya fe ba, sai mun yi shari’ah da koma waye ya aikata wa siyama wannan ɗanyen aikin.” ta faɗa tana ƙoƙarin kamo Siyama da hargagin uwar tata ma ƙara mata ciwo yake yi.a ranar dai a asibiti ta wuni inda aka mata dressing na ciwukan da taji gami da ƙarin ruwa….
(Yan uwa mata ya kamata mu ringa sa’ido akan harkokin shige da fice na ƴaƴanmu,kar mu bari son zuciya ya sa mu ringa rufe idanunmu da ƙin amsan gaskiya,kamar uwar Siyama yanzu bata nemi jin ba’asin me ua samu yarta ba, a’a a take ta ɗaura laifi akan wasu wai maƙiya sun sawa yarta idanu dama,…masu iya magana dai sunce kaso naka duniya ta ƙishi, ka ƙi naka duniya ta soshi.)

Wannan ya sa Siyama bata nemi Maryama ba hasalima babu waya a hannunta har dare suna asibitin ba’a sallamosu ba….

…………..**

Zaune suke kusan su goma sha biyu akan kujerun da ke zagaye da wani babban teburi,ko wannensu da abin magana a gabanshi da kuma computer, gefe kaɗan kuma bottle water ne da soft drink,ko wannensu ya ci gayu cikin haɗaɗɗun kayan da kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba karamar arziki ya lakume ba wajen sayanshi,yawancinsu matasa ne da bazasu gaza shekaru arba’in ba zuwa ƙasa.Sadeeq na zaune a tsakiya kuma yana daga cikin masu karancin shekaru a click ɗin kana yana cikin jerin waɗanda ake ji dasu dan cigaban da ya ke kawo masu….Sanye yake cikin wani black jean trouser da red polo shirt mai ɗan girma,kana kanshi ɗauke da p,cap black da rubutu red a gabanshi an rubuta PERFECT, da manyan haruffa,tsintsiyar hannunshi ɗaure da agogo na HUBLOT,haɗe da wani siririn bracelet na maza silver colour ya yi kyau matuƙa gaya…tattaunawa suke yi akan wani kayansu da jami’an sintiri na kan teku suka kama a gaɓar tekun meditareniya yana koƙarin kutsawa yankin turai.amma sam hankalin Sadeeq ba ya tare dasu tunaninshi yana kan yarinyar,tun jiya baiyi magana da ita ba,haka kuma duk sanda ya tuna ta sai gabanshi ya yanke ya faɗi,…Ɗan taɓa shi na kusa dashi ya yi yace, “Man kai muke saurarafa, ya kaji shawaran da Musty ya bayar”.

Firgigit Sadeeq ya yi ya dawo hayyacinsa,sai a lokacin ya ɗago ya lura da duk occupant dake wurin shi suke kallo da alamar suna jiran ji daga bakinshi.ɗan muskutawa ya yi ya miƙe ya fara bayani cike da ƙwarewa da sanin makaman aiki,tsawon minti uku yana magana sannan ya zauna ya na faɗin “I think dis will be way out to us Insha Allah.”

Gaba ɗaya wurin ya ɗau tafin dake nuna sunji daɗin bayaninshi amma banda Musty da ya haɗe rai kamar hadarin gabas na agusta.ƙara mikewa Sadeeq ya yi gami da faɗin, “Just a minute ina dawowa,yana ƙokarin fita daga kujeranshi, musty yace, “But this is serious issue man, bai kamata ka tashi ba bayan kasan halin da muke ciki,”.

“Don’t mind i just want to ease my self,ko hakan laifi ne?” Sadeeq ya faɗa yana kafe musty da firgitattun idanunshi..musty ji ya yi tamkar ya tashi ya shaƙo sadeeq har sai ya daina numfashi sannan ya sake banza, its about time, karka damu,zuciyar shi ta bashi amsa…..

Toilet dake cikin babban ɗakin taron ya shige haɗi da rufe kanshi,ya tabbata idan ya ci gaba da zama babu abin da zai fahimta matuƙar baiji muryar pretty ba, saidai kira har huɗu ya mata ba a amsa ba, ganin mutane suna ta jiranshi yasa shi tura mata gajeruwar saƙo ya fito, lokacin da ya ƙira kuma time ɗinne Jabeer ya shigo ɗakin Maryama….Bayan ya fito nan suka cigaba da tattaunawa kan matsalolin da yanzu kasuwancin nasu ke fuskanta gami da hanyoyin da zasu warware su,sai wajen sha biyun dare suka watse taron kowa zuciyar shi cike da tarin ƙiyayya akan mutum ɗaya wato sadeeq saidai ba kowa ke nunawa ba,yawancinsu suna kokarin ɓoyewa tare da tanadar mashi lokaci…..kimanin minti talatin ne ya maida shi gida daga inda suka yi taron nasu.Tun a hanya yake ta ƙara gwada layin ta amma ga mamakin shi ya ji switch off,”what the f**k” ya faɗa da karfi ya na buga steering motar shi, har ya iso gida kiran Maryama ya ke yi amma sakamako ɗaya matat MTN ke sanar da shi wato wayar tana rufe..ko da ya iso gidanshi kasa kwanciya yayi sai safa da marwa ya keyi a tsakar parlour nshi.

……………………**…………………..

Jabeer ya daɗe yana addu’oi sannan ya miƙe ya zare rigar jikinshi ya dauko wandon ya laluɓa cikinshi ya fitar da wasu bunch of keys,walking slowly ya nufi kofar bedroom ɗin yana wani devilish smile,without making any sound ya buɗe kofar kana ya mayar ya rufe,duk da akwai ɗan duhu a ɗakin, hakan bai hanashi ganinta ba kwance bisa gadon, kusan rabin kafafunta a ƙasa,da complete kaya a jikinta ko ɗan kunne bata cire ba wanda hakan ke nuna bata shirya ba baccin ya yi awon gaba da ita. a bakin gadon ya zauna yana ƙare mata kallo, ba tare da ya shirya ba ya matso daidai fuskar ta ya ɗaura hannunshi saman lallausan gashinta da ɗankwalin kanta ya zame ya bashi daman fitowa,gently ya ke shafawa kana ya ɗan hura mata iska saman fuskarta.

Kamar a mafarki nake jin tafiyan abu a kaina kamar kuma gaske ga wani daddaɗan kamshi da yake bakuntan kofofin hancina wanda mutum ɗaya na sani da wannan kamshin duk duniya. a hankali,ɗan motsi na yi kaɗan amma ban farka ba dan wani irin nishaɗin da nake ji wannan mafarki yana bani,…juyin da tayi ya ba Jay daman saƙala hannunshi a wuyanta ya zare sarkar dake maƙale jikinta, cikin dabara ya kuma cire mata ɗan kunnen dake kunnenta,hannunshi ya mayar saman kanta ya cigaba da shafa gashinta zuwa kan wuyanta cikin nutsuwa da yanayi na soyayya,…zuwa yanzu kam na fara dawowa daga rakiyar wannan mafarki domin wani yanayi marar misaltuwa da nake ji a jikina,kamar an tsikare ni na farka, ina kokarin tashi muka haɗa idanu dashi yana zaune daga shi sai boxer mai dan faɗi,faffaɗan kirjinsa da ya tale tsabar daga ƙarafa a bayyane sai gargasa dake kwance lib lib, duk da dare ne kuma akwai duhu kaɗan amma naga hakan ne ta ɗan hasken dimm light da na kunna dazu,wani irin zabura na yi na buɗe baki zan kurma ihu ya yi hanzarin cafkoni ya rufe min baki da sassanyan tafin hannunshi haɗi da mannani da kirjinsa tsammm tamkar zai maidani cikin kirjin,duk da mutsu mutsun kwatar kaina da na fara hakan bai hanani jin yadda kirjinsa ke gudu fiye da ƙima ba.

Matso da bakinshi jay ya yi daidai saitin kunnena cikin wani salo ya furta, “wa na kama yanzu?”…ƙara rudewa na yi ina ta fizgar kaina amma na kasa sakamakon ba riƙon wasa yai mini ba.

A bangaren Jabeer kuwa gaba ɗaya ya fara loosing control nashi dan haka baisan ma mai ya ke cewa ba, “Uhmmm wa na kama yanzu, guduna kike yi ko pretty? kin taɓa ganin inda amarya ta ke gudun angonta?”.

Waɗannan da makamantan su Jabeer ke faɗawa maryama a kunne ba tare da shi kanshi yasan me yake faɗa ba saboda yadda hannunshi ke yawo a jikinta. Iya ruɗewa na ruɗe, ban taɓa tsammanin hamma jay zai iya riƙeni haka ba duk fizgar da nake don in kwaco kaina na kasa sai ma sauƙar rigar lace ɗina naji a ƙasa,Inna lillahi, wannan wani irin abin kunya ke faruwa da ni ni maryama? wani irin ihu na saka lokacin da ya sake min baki da hannunshi, da sauri ya ƙara rufe bakin haɗe da kunce zargen da ke ɗaure da zani na ya janye zanin ya yar a ƙasa, daga ni sai bra da panti da underwear, haka hamma jabeer yayi nasarar kaini tsakiyar gadon ya kwantar dani shima ya kwanta gami da matse ni tsam a jikinshi yamin filo da damtsen sannan yaja bedsheet ya rufa mana,duk abun nan da yake yi hannunshi na saman bakina, ɗauken hannun ya yi ya mayar saman kaina ya cigaba da shafawa da alama shafa gashin yana bashi nishaɗi.wani irin kuka na sanya jin ya cika min baki kuka na ke yi mai cike da sheshsheƙa, yatsar shi manuniya ya ɗaura saman leɓena idanunshi a lumshe kana kirjinsa na gudu da mugun speed da har a nawa kirjin ina ji ya ce,

      "Shshsshhhsssshhht".....

💫MARYAMA💫

            BY 

        Ummu Fadeela

Typing📲

Episode 27/28…..

……………Yatsar shi manuniya ya ɗaura saman leɓena idanunshi a lumshe ya furta, “Shhhsshhshttt, bacci pretty”.

Daga haka bai ƙara bani damar yin magana ko kuka ba ya rufe idanunshi gam haɗi da matse ni sosai tamkar dai zai maida ni ciki ko mai tsoron kar wani ya kwace masa ni.da haka bacci mai cike da nishaɗi da annashuwa ya ɗauki Jabeer yayinda ni kuma kamshin turarensa na oud essential ya cika man hanci ya hanani nutsuwa gefe guda kuma irin riƙon da ya min da ko numfashin kirki bana iyawa.tunani ne suka min rubdugu nima bansan sanda bacci ya ɗauke ni ba…..

Sauƙar numfashinta a hankali ne ya tabbatarwa Jay cewa ta yi bacci,a hankali ya ɗan sassauta riƙon da ya mata yana gyara mata kwanciya yadda zata zama comfortable,still kanta yana saman damtsen hannunshi suna fuskantan juna,addu’a ya yi masu su duka sannan ya gyara masu duvet ɗin kana ya cigaba da shafar gashin kanta wanda yana cikin abin da ke burgeshi a gun ɗiya mace,balle na Maryama da ya kasance na musamman,da haka bacci na gaske mai cike da mafarkai barkatai ya ɗaukeshi….

A hankali ya fara buɗe idanunshi sakamakon hasken rana da ya ɗan shigo ta window ɗin dakin,da sauri ya gama buɗe idanun yana mai tasbihi da tsarkake sunan Ubangiji ganin karfe shida ta yi, Jabeer zai iya cewa tunda ya mallaki hankalin kanshi sallar asuba bata taɓa kubce masa ba matuƙar yana halin lafiya sai yau…idanunshi ya sauƙar a kanta,tana kwance a jikinshi kamar yadda ya sakata tun jiya bai jin ko motsi ta yi,hannu ya sa ya shafa saman fuskanta yana ɗan murmushi kaɗan kaɗan,a can kasan maƙoshi ya ce, “Pretty!”

Mar mar ta farayi da idanu,tun kiran sallar farko idanunta ke buɗe sakamakon sabo da tayi na tashin asuba suyi sallah a gida da kuma baccin rashin sukunin da tayi,saidai yadda zata tashi daga jikinsa ne ya zame mata matsala dan wani irin masifaffen kunyar shi takeji.

Zare hannunshi ya yi daga kanta a hankali ya fara kokarin miƙewa,jin ya sake ta Maryama tayi wani irin juyi sai gata a karshen gadon,kamar rufe ido ta miƙe da sauri ta sauƙa saman gadon ta maƙure jikin gini tana ta zare ido kamar tayiwa sarki ƙarya,dogayen laps nata farare sol Jabeer ya bi da kallo dariyan abin da tayi na cinsa amma ya danne,bin inda yake kallo na yi da ido….zaro ido nayi gami da kwalla ƙara da karfi na durkushe a wajen ina haɗe jikina waje ɗaya….Jabeer could’nt help it sai da ya yi dariya,sannan ya miƙe ya fita ɗakin ganin matuƙar ya ci gaba da zama sai 8 zaiyi sallah.

A gaggauce ya cika bokiti da ruwa da kuma babban buta ya shiga bayi,saida ya gabatar da uzurinsa sannan ya yi wanka kamar yadda ya saba safe da dare kana ya janyo butar ya fara wankan tsarki,baiyi niyyar kusantar ta ba har sai ta saba dashi kuma ta amince masa, amma yana son ya cire kunya a tsakaninsu dan samun happy home shiyasa yai mata abin da yai jiya,sai dai da ƙyar ya iya controlling kanshi….Babban towel da ya shiga dashi ya ɗauko gami da goge jikinsa ya saka wata boxer daban ya fito,yana shiga ɗakin fittt ya ga gilmawarta ta fice a guje kamar walƙiya,shafa kanshi ya yi yana ɗan murmushi,…..har Jabeer ya idar da Sallah Maryama bata shigo ba, ita ko tana maƙure bakin kofa ta ɗauro alwala tun ɗazu amma ta rasa yadda zata shigo dan wani irin kunyar shi da take ji mai haɗe da ɗan tsoro tsoro.

Da hanzari jabeer ya cire jallabiyar da ya yi sallar ya rage daga shi sai singlet da boxer ya na ƙoƙarin fitowa ita kuma ta yi shahadar kutsa kanta cikin ɗakin,karo suka yi ba tare da kowannensu ya kula ba da hanzari ya riƙo ta ya bata wani irin hug yana sauke ajiyar zuciya, hannunshi ya ɗaura saman gashinta duk da sanye take da hijab babba, ya na shafawa murya a shaƙe ya ce, “Morning my angel,how was your nyt?hope you enjoy it?”.

A hankali yake maganar kuma kusa da kunnena,ga riƙon ba zatar da ya min hakan yasa jikina sakewa,sai dai duk da mutuwar da jikina ya yi na hamma jay ya fi nawa dan yadda muryarshi ta koma fa yadda kafafunshi ke rawa suna son kaimu ƙasa,da wannan raunin da ya samu na yi amfani yana gab da ɗora bakinshi saman nawa na hankaɗa shi na shige ɗaki a guje na maƙala sakata dan na san ko na sa makulli a banza ne zai buɗe kamar dai jiya. zama na yi a bakin gadon ina sauƙe numfashi sama sama,tsakanin jiya da yau duk sadda hamma Jay ya taɓa jikina sai in riƙa jin tamkar an jona mun electric shock haka kuma gabana ya dinga faɗuwa,the worst part of it kuwa shi ne I like the feeling da na ke ji duk sanda muka samu body contact ɗin, ya Salam! na faɗa ina dafe goshi na…..

Jabeer dake jin kanshi yana yawo a sararin samaniya,baiyi aune ba yaji ta tureshi,akayi dace kuma gaba ɗaya karfin shi ya koma kanta,hakan ya sa ya yi baya baya ya faɗa saman kujera mai zaman mutum ɗaya dake gefenshi,da gudu ya ga shigewarta ɗaki.Ba haka yake so ba,so ya ke suyi zama mai aminci zama mai cike da shaƙuwa da soyayya,baison yadda take nuna ta na jin tsoron nan nashi ko kaɗan,amma ta ya zai cire mata tsoron?ɗan murmushi ya yi yana shafa kanshi jin wani tunani ya faɗo mashi,a hankali ya kwantar da kanshi jikin kujerar haɗi da lumshe idanu,sauri ya ke dama yanason yin exercise ko kaɗan ne amma gabaɗaya Maryama ta kwance mashi notinan jikinshi baijin zai iya taɓuka wani abin azo a gani ko da ya fita ma…Jabeer na zaune a wajen doing nothing bai san iya adadin minutes da ya kwashe ba ya jiyo sallamar fatima,saida ya maida jallabiyarshi sannan ya amsa labulen palon ta ɗaga haɗi da shigowa bakinta ɗauke da wata sallamar.

“Ina kwana Hamman mu,”cewar Fatima lokacinda ta ke duƙawa kasa.

“Lafiya lau Fati ya su Innarmu, ina baffa da su daada?”ya amsa haɗi da tambayarta fuskarshi ɗauke da murmushi.

“Duk lafiyan su,inji Innarmu in kawo muku abin karyawa ta faɗa tana matso da kular da ta shigo dashi ta re da tea flask….

Still smiling Jay ya ce, “ki ce da innarmu mun gode miƙewa Fati ta yi har ta kai kofa sai kuma ta juyo ta ce, “Hamma Jabeer Ina antynmu?”.

“Antinku ta na wani aiki kaɗan a ciki idan ta fito zan faɗa mata kin zo”.

Da “to” ta amsa kana ta ta koma gida…Buɗe food flask ɗin ya yi yaga doya ce aka soya da kwai sai kamshin spices ke tashi tea flask ɗin kuwa tea ne a ciki as he expect shima sai tashin ƙamshin su ginger ya ke yi.a gefe ya musu mazauni ya daga ledar jiya da dare da ba wanda ya ttaɓa ya fitar da kayan shayin suma ya ajiye a gefe,ledar kazar kuma ya fita da ita zuwa kitchen.girki ba baƙon abu bane ga duk ɗan talakan da ya je jami’a, dan haka Jay ya fara ƙoƙarin warming kazar luckily kuma da akwai stove mai cike da kerosine a cikin kitchen ɗin da Innarmu ta siyawa Maryama komai yana zaune a muhallinshi dan haka kunnawa kawai ya yi haɗi da ɗaukan karamar tukunya ya ɗaurayeta sannan ya jefa kazar a ciki…..Bayan mintuna kaɗan ya samu plate ya juye yasa wata ya rufe saman namar ya shigar ɗaki ya kuma dawowa ya ɗauki wata tukunyar madaidaici ya cika da ruwa ya mayar saman stove ɗin ya rufe,wasu plate din guda biyu, fork, knife, da kuma cup ya dauka suma ya shigar ɗakin….anan tsakar ɗakin ya jere komai yadda ya kr so sannan ya nufi bakin kofar, murya ƙasa ƙasa ya ce, “Pretty fito kiyi breakfast gashinan Innarmu ta turo mana favourite food na ki”, Ina zaune bakin gado bayan na gabatar da sallah counter ce a hannuna ina azkar duk abin da ya ke ina jinshi, lokacin da Fati ta shigo ji nayi tamkar in fito in rungume ta amma na kasa saboda tsoro da kunyar hamma jay da nake,…sosai ya Jabeer ya ke ma ta magiya kan ta fito su karya amma ko gezau Maryama ba ta yi ba,kasancewar yana son zuwa can gida kafun baffanmu ya fita yasa shi dawowa kan breakfast ɗin ya ɗeba komai yadda zai iya ci sannan ya haɗa shayi ya fara karyawa a ranshi yana aminta da shawarar da zuciyar shi ke bashi wanda ya ke ganin ita ce hanya ɗaya tilo da zai cire wannan tsoron a tsakaninsu, a gurguje ya gama ya maida kayanshi da ya cire jiya dan ba wasu kayan a nan dole sai ya je gida ya ɗauko akwatinshi,bakin kofar ya kuma dawowa pleadingly ya ce, “Plsss Pretty ki fito ki yi breakfast ni fita ma zanyi, don Allah karki zauna da yunwa plsss wife, ya ƙare da sassanyan muryar da wanda ya taɓa tsintan kanshi a irin wannan bahagon soyayyar ne kawai zai iya karantar abin da ke zuciyarshi….har ya juya xai fita sai kuma ya dawo cikin nutsuwa ya ce, “da akwai ruwan wanka a kan stove na ɗaura maki karki manta dashi kero ya ƙare, ki fito plssss ni zan fita yanzu,byeee take care of your selfff.

Tun da ya fara magana na ajiye counter ɗin hannuna ina jinshi amma na kasa furta komai time da ya ce ya ɗaura min ruwan wanka a take naji idanuna sun cika da hawayen da ban san dalilinsu ba,ba tare da na shirya ba hawayen suka fara sauƙa haka kuma banyi tunanin sharesu ba, inajin fitar shi kusan da minti ishirin still ina zaune ga wani irin yunwar da ke kwaƙular yan hanjina,ba dan na shirya ba na fito, komai yana nan yadda ya barshi da sauri sauri na haɗa tea mai kauri na ajiye gefe na ɗauki doya yanka biyu hannuna yana rawa na bude plate ɗin kazar dake ta tashin kamshi,dou dai ta fara sanyi kam,amma ban kula ba na fara mata cin yunwa ina bi da shayi kamun in ankara sai kasusuwa na gani dan haka ban samu cin doyar ba na mayar cikin kula.

Kwanukan na tattara na fitar inda aka tanada musamman dan wanke wanke a gefen kitchen nan na ajiye su kular doya da ta shayin kuma na mayar kitchen na adana, ganin ruwan da ya ɗaura sai tafasa take yasa ni juyewa a babbar flask na ƙara ɗaura wani.baho na ɗauka na da kwando nazo na wanke yan kwanukan da sukayi datti na shigar na jere komai yadda ya kamata sannan na dawo ɗakin duk da babu datti na ɗan kakkaɓe sama sama na fesa freshner take ko ina ya ɗauki kamshi, ina turo baki gaba na ɗaga farar jallabiyar shi dake tashin kamshin mayataccen oud dinnan na linke kana na sama mashi wajen zama a bedroom,saida na tabbatar komai ya min yadda na keso sannan na je na juye ruwan na shiga wanka,….lokacin da na fito har shabiyu ta kusa mai na shafa da ɗan turare sama sama na shirya cikin riga da siket na wani atamfa blue black sosai farar fatata ta haska aciki, tunanin Sadeeq da Siyama na maƙale a raina kana gefe guda kuma tunanin inda hamma jay ya tafi nake yi.

A hankali na ɗaga gefen katifata na ɗauko wayar, ina ƙoƙarin kunnata dan kiran Sadeeq naji ana kwaɗa sallama a waje,da hanzari na ƙara turata kasan gadon na fito ina amsawa,wasu mata ne su biyu da yaransu kusan biyar suka shigo,saida na isar dasu ɗaki muka gaisa na fahimci ashe makwafta ne suka shigo ganin ɗakin amarya,saidai kamar sun buɗe kofa ne,nan jama’a suka dinga ɗiɗɗikowa wai da sunan ganin ɗaki tuni sun ɓata man sharar da nayi,har bayan azahar wasunsu na nan,musamman yara,kamar daga sama Allah ya turo min su Fati da Salima ɗauke da wata kular ta abincin rana,…fati ce tayi karfin halin korar yaran bayan ta basu sauran doyar safe da ya rage da tea,tare muka ci abinci da yan ƙannena da nake ji tamkar na shekara ne ban gansu ba, bayan mun gama salima ta wanke kwanukan da muka ɓata fati kuma ta hau shara da mopping har da su kunna tiraren wuta a burner,take gida ya ɗau kamshi da walkiya sak na amarya, a bakin su fati na ke jin wai hamma jay sun fita da baffanmu wani waje tun da safe har fitansu basu dawo ba….sai maghrib su fati suka tafi suka barni cike da kewa, duk yadda na so su tsaya sai ya dawo ƙi suka yi da dabara ma suka gudu na shiga wanka lokacin a darare na shige ɗaki da zan murza makulli naga wayam, sakata ma haka Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un na furta ina zare ido, wa ya taɓa kofar nan,? ko dai akwai aljanu a gidan nan. zaro ido nayi na dawo palo da gudun gaske, saidai bazan iya fita waje ba da kyar na gabatar da sallar maghrib wacce bansan ko abin da na karanta a ciki ba tsabar yadda nake tsorace ina cikin wannan halin aka kira isha,shima na gabatar ba tare da ina cikin nutsuwa ba, wani irin kuka ne ya kwace min na fara kukan a hankali hankali cike da tsoro,na jima ina kuka har kaina ya fara ciwo sosai amma ba hamma jay ba dalilinshi, wajajen karfe takwas na dare ya nufo gidan hannunshi ɗauke da ledar kazar da ya siyamata da kuma fresh milk,a ranshi yana tunanin wane hali ta ke dan yasan maryama da ɗan karen tsoro kamar farar kura,ana sallar isha suka dawo daga inda sukaje da baffa tafiya mai cike da nasara cikin farin ciki ya shigo gidan dake mamaye da duhu dulum wayar hannunshi ya haska lokacinda ya iso bakon kofar palon, wani irin ƙamshi ne ya ziyar ci hancinshi gefe ɗaya kuma ya na jin sheshshsekan kuka sama sama,da hanzari ya faɗa palon yana dallare tocin wayarshi,tana maƙure jikin kujera akan sallaya idanunta sunyi jawur tsabar kukan da ta ci,.”Pretty” ya ambata da ɗan sanyin murya kaɗan, tun da ya haska toci ta kara damƙe jikinta dake rawa waje ɗaya tana ayyana shikenan tata taƙare bataji shigowar shi ba sai jasken toci ta gani so ta ɗauka wani abune daban, jin muryarshi yasata tasowa da gudu ba tare da tunanin komai ba ta rungumeshi gam gam tana sakin wani sabon kuka mai cike da shagwaɓa, and that’s turn him on………
💫MARYAMA💫

           EPISODE 29/30

       BY

    Ummu Fadeela


 ELEGANT VERIFIED WRITER'S.

___________Bayanta yake shafawa gently,da sanyin murya mai nuna halin da ya ke ciki ya ce, “what happened pretty?ki daina kukan haka kar kanki ya yi ciwo,…” kamar wadda ya ce ta ƙara karfin kukan ta buɗe murya tana kuka mai cike da shagwaɓa,haɗe da bubbuga ƙafafu a ƙasa,wani irin yamutsawa jinin Jabeer ke yi sakamakon taɓarar da ta ke masa,yayinda yake jin ƙafafunsa suna ƙoƙarin gaza ɗaukarsa, da shaƙaƙƙiyar murya ya ce, “me ya sameki ne MARYAMA?akwai abin da ya faru bayan fitata ne? yi shiru ki faɗa min mene ne?.”

Da kuka ta ce, “ba kai ne ba ka tafi ka barni kuma kasan inajin tsoro ni kaɗai,”

Baya baya ya koma da ita haɗi da zama saman kujera ya ajiyeta saman cinyarshi,.still holding her tightly ya ce, “Sorry wife gani nan na dawo,daga yanzu ban ƙara fita ko ina idan dare ya kusa,kinyi haƙurin?”. ya faɗa saitin kunnena.kaina na kifa saman kirjinsa saboda wani irin kunya da na ke ji,hakan da nayi kuwa ba ƙaramin ƙara birkita shi ya yi ba, amma yayi ƙarfin halin cewa, “Ohk idan har kinyi haƙuri then wipe your tears and smile ima da wani labari mai daɗin gaske da zan baki”.

Da sauri na ɗago kaina ina jin wani irin excitement dan na gama sawa a raina cewa maganar makaranta ta zaimin dan yanzu shine kaɗai labarin da zan ƙirashi mai daɗi a wajena.shi ya sa hannunsa duka biyu ya goge min hawayen kana ya riƙe duk kumatuna ya ce, “Bani son ƙara ganin waɗannan hawaye masu tsadar da sukafi gold daraja a wajena,ki daina zubar min su a banza kinji hayatie na?”. Ba tare da na ce komai ba ya ci gaba da magana.

Yana kallon cikin idanuna still bai sake min kumatu ba ya ce, “Albishir!”.

Cike da annuri da ke kwance saman fuskata da kuma zaƙuwa na son jin abin da zai faɗa na ce “Goro”

Ɗan chukling ɗina ya yi a gefen ciki, ta ke na fara dariya, ya ce, ” yawwa ko kefa amma da kin haɗe rai kamar wacce zanyiwa albishir ɗin kishiya,…Murmushi na yi nayi wannan karon har dimples nawa suka loɓa,ɗan yatsarshi ya ɗaura saman dimples ɗin gami da faɗin, “tha’s my wife”….

(Nasan mai karatu zaiyi mamakin yadda ni maryama na sake da hamma jay,wato ya yi bala’in sanin makamar ƴa mace a cikin zuciyata ba ni son abin da ya ke min, amma gangar jikina ya kasa janyewa daga gareshi,wannan wani sirrine dake tattarw dashi da ba kowanne ɗa namiji Allah ya bawa ba.)

Still looking into my eyes,ya ce, “Albishir!”, turo baki na yi gaba na ce, “kai dai hamma jay ba na ce goro ba,”

Jabeer bai gajiya da kallon kyakkyawar baby face na ta dake cike da shagwaɓa, yana jin wasu abubuwa suna bijiro mashi cikin kai…Iska ya hura min a kunne ganin yadda na kafeshi da idanu ba tare da nasan nayi hakan ba.Da sauri na rufe idon ban ankara ba naji saukan wani sassanyan kiss saman idanu na, da sauri na kuma biɗewa ina ƙoƙarin tashi amma bai bani dama ba.

Cikin low voice ya ce, “Na samu aiki pretty!”.

Wani irin miƙewa na yi da sauri na tsaya haɗi da ɗaura hannayena duka biyu saman bakina, rsabar murna na ma rasa abin da zance.Tashi yayi shima ya rungumeni ta baya gami da zuro kanshi ta saman kafaɗata ya ce, ” Kina farin ciki ko pretty?,….nima ina farin cikin cewa na samu aiki yanzu zan iya ɗaukan nauyin karatunki dan ganin kin cika burinki,…Ɗan ajiyar zuciya ya dauƙe,sannan ya cigaba da cewa, “amma baki tambaye ni wani irin aiki na samu ba?, bai jira na bashi amsa ba ya ci gaba da faɗin,

“Na samu aikin koyarwa a makarantar firamare, Insha Allah duk wata zamuke samun naira dubu talatin da uku,kinga ai ba kananan kuɗi bane,wannan ne sugullan da muka yini yi tare da baffanmu a yau kuma alhmdllhi mun kammala komai,”. ya ƙare da murmushi yana shafa fuskata zuwa saman wuyana…..

A hankali na fara jin wani abu mai kama da zare yana kwancewa daga cikin ƙwaƙwalwata yana bin jikina har zuwa tsakar kafata…”aikin karantarwa a firamare?dubu talatin da uku ne hamma jay ke kira da manyan kuɗaɗe a hakanma sai yayi wata ɗaya cur sannan ya same su?33k ai ko monthly allowances da nake fatan mijina zai ke bani baikai ba…..A cikin kunnena ya raɗa min, “hmmm kinyi shiru baki ce komai ba,”..

Gyara tsayuwa nayi da niyyar matsawa daga wajen,hakan ya bashi daman juyowa yana shigar da idanunshi da suka sauya kamanni cikin nawa, zaro ido nayi da sauri kirjina na bugawa ganin abin da hamma jay ya fara…….

——————–

Wannan dare dai Sadeeq a cikin ruɗani ya yishi,duk yadda ya so daure wa kasawa yayi a autoreadialling yasa layin Maryama sai kira yake duk kuwa da cewa matar nan ta MTN tana tabbatar mishi layin da yake nema a kashe take,zama yayi a ƙasan rug dake bakin gadonshi ya riƙe kanshi da hannu biyu, “What’s happen to me?,meke damu na ne?” ya yiwa kanshi tambayar,kome ya tuna kuma ya yi saurin sauƙe hannunshi yana katse ƙiran da yake ta zuba wa Maryama,kana ya juya akalan ƙiran zuwa kan wani layi ya ɗaura saman kunnenshi haɗi da lumshe idanu kamar mai bacci.

_***___

 FEDERAL LOWCOAST GOMBE.


       GOMBE STATE.

Cikin ɗaya daga jerin gidaje na alfarma dake shaƙe a anguwar mai ɗauke da tsarin zamani na shiga,daga compound ɗin gidan zaka iya fahimtar mamallakin wannan gida ya samu na duniya kam saidai yayi harin lahira,gida ne na alfarma mai ɗauke da bene hawa ɗaya, sai wani babban duplex shima mai kama da aljannar duniya a gefen hagun babban building ɗin, daga inda kake kana iya hango boysquarter’s a can karshen gidan bayan su garden swimming pool da kuma wawaken parking space,kutsa kai na yi cikin gidan bayan na buɗe kofar palon,tsayawa faɗan haɗuwar wannan palo dai ɓata lokaci ne A kalla paluka ukune cikin downstair ɗin da kuma kitchen da store da sauran bedrooms.

Zaune ta ke bisa stool dake gaban dressing mirror a ɗaya daga ciki kyawawan ɗakuna kuma mafi girma dake upstair,tana ɗaure da babban towel da ya kai har guiwanta tum daga kirji,gashin kanta mai walƙiyar da kallo ɗaya zaka mishi ka san ba ƙaramin laushi zai yi ba a baje har saman kafadunta,hannunta ɗauke da handrayer tana busar da gashin,duk da a zaune ta ke amma zaka iya fahimtar bata cika tsawo ba kuma baza’a ƙirata da gajera ba,kai tsaye zamu iya ƙiranta baƙa amma ba ƙirin ba dan da gani skin nata yana samun kulawa ta musamman sakamakon shining dim da ya ke yi,idanunta farare tas da ɗan madaidaicin baki mai ɗauke da cikakkun lips irin mai tsoka ɗinnan kana da jerarrun haƙora farare tas masu dauƙe da babban wushirya a tsakiyarsu,she’s just a black beauty, a ƙalla zata kai shekaru ashirin a duniya,tana gyara kanta amma fuskarta cike da annuri da ganinta zata yi fara’a, bayan ta gama ta shafa mashi mayuka masu daɗin kamshi sannan ta ɗaure gashin da band hot red kana ta kama jelar ta kitsa shi ya sauƙo har gadon bayanta ya kwanta lib gwanin sha’awa, hair spray ta fesawa gashin sannan ta ɗaga container ɗin lotions dake wajen ta fara dubawa, duk ajiyewa tayi dan ba wanda ya mata ta ɗauki body spray ta yiwa jikinta wanka dashi kana ta ɗau wani kwalban humra ta dinga bin lungu lungu a jikinta tana gogawa, take ɗakin ya ɗau wani irin kamshi har yana hawa kai amma ita ko a jikinta kamar ma hakan wani nishaɗi yake bata,.tana tsaka da goge gogen turarukarne wayar dake zaune kan mirror ɗin ya ɗau ƙara,dagawa tayi dan ganin mai ƙiran a wannan lokacin, Imoji ɗin love guda biyu da ta gani fuskar wayar ne ya sata picking cikin gaggawa tana faɗaɗa fara’ar dake fuskarta.

Cike da ɗokin murna mara misaltuwa ta ce, “Yayaaaa!”.

A ɗaya bangaren Sadeeq ya ɗan muskuta daga zaunen da ya ke kasan rug ɗin ya yi murmushi ƙaɗan wanda baisan ma yayi ba yace, “Lilsis,kin manta da yaya ko?”.

Wannan karon turo baki tayi ta ce, “Ba wani nan yayaa so kake kar inyi korafin ka manta dani, amma sau nawa ina ƙiranka ko amsa wayata ma bakayi”

“Ohhh sorry my lil, kinsan yayannaki lebura ne so ba ko da yaushe nake da lokacin kaina ba,”

Cikin fara’ar da yake ɗabi’arta ta ce, “To yayaa Allah ya bada sa’a amma….sai kuma tayi shiru”

“Amma me?” ya tambayeta dul da ya dan abin da zata faɗa….”Just to told you munyi missing naka” ta faɗa da sanyin murya.

“Where’s Mom?” ya tambayeta ba tare da ya bi ta kan maganar da ta faɗa ba, Mom tana side ɗin Abbu ba ta jima da fita ba,in kai mata wayar ne?”.

“No ki barta,kawai idan ta shigo kice mata am on my way tomorrow morning bala yaje ya ɗauko ni a airport, ohk?” wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyarta da sauri ta miƙe har towel nata na kwancewa ta ce,”Da gaske kake yayaaa”.

“Da wasa nake lilsis” ya kwaikwayi abinda ta faɗa da irin muryarta, dariya ta kumayi ta ce, “Allah ko kayi suprising namu bari inje in faɗawa Mom byeeee” .

Ba tare da ta jira jin abin da zai ce ba ta yanke wayar ta nufi ƙofa da ɗan gudunta…karo suka ci da wata dattijuwar mata fara sol kai da ganinta kasan ba ƙaramin kyau ta yi lokacin kuruciya ba,baya ta dawo tana haƙi kamar wacce tayi gudu mai nisa.

“Wai sai yaushe zaki girma ne KHADIJA? kullum kina girma kinacin ƙasa,yanzu me ya haɗaki da gudu haka?”kafun budurwar da aka ƙira khadija yace wani abu mom ta gama shigowa ɗakin tana bubbuɗe hancinta.

“Me nake ji haka khadija?yanzu perfumes nawa ne kika bulbular a jikinki kamar mara lissafi ko?.’

Rungumeta khadija tayi cike da farin ciki ta ce, “Sorry Mommy,!bazan sake ba, “bata bawa mom daman magana ba ta ci gaba da faɗin, “Albishir Mommy,yanzu yayaa ya ƙira wayarki na ɗauka ya ce min yau in sanar dake gobe zai zo da safe, bala ya je ya ɗauko shi a airport,plsss, mommy nizan je ɗaukoshi karki faɗa mishi plsss plssss plssss Mommm.” ta ƙare tana ɗan bubbuga ƙafa a ƙasa…

Sake baki kawai Mommy tayi tana kallonta, “say something mana mom”.

“To Allah ya kaimu zaki jira goben ya yi ai ko,? irin wannan rawar kan da kike yiwa MAN shi yake sa shi yana basar dake ke kuma baki gane ba”.

“Nidai ki barni kawai mom, ta faɗa tana turo baki…yauwa bari inje in fara haɗa masa favourite nashi kamun ya iso.”

” Na shiga uku ni hauwa mutumin da sai gobe zaizo ne kike ƙoƙarin shiga kitchen tun yanzu?”

“Ahhhh na manta ne mom”cewar khadija tana dawowa bakin gado ta zauna……..
💫MARYAMA💫

                EPISODE 31/32

TYPING📲

    BY.

         UMMU FADEELA.

Assalam alaikum Sunana Zee arts Graphic Designer ce ba muna graphics ba atoh 😂😂😂
Ina yan kasuwa, marabuta, amare, kai har ma yan siyasa da Sauransu wann naku ne , kuzo ayi muku kayataccen design na abubuwa kamar haka 👇🏻👇🏻👇🏻

 • BRAND LOGO – LOGO DESIGN
  -FLYER DESIGN -INVITATION CARDS
  -BANNER -POSTER DESIGN
  -BOOK COVER -STICKER
  -WATERMARKS -BUSINESS CARD
 • CERTIFICATE -POLITICAL POSTER
 • INSTAGRAM HIGHLIGHTS
  Da ma wasu abubuwan da dama akan farashi mai sauki🥰🥰, kuyi min mgn ta wnn lambar idan kun shirya domin ganin samples sai kunzo 👇🏻👇🏻
  What’s app number: 07011988593….

__________Zaro ido nayi dan ganin hamma jay ya matso da bakinshi daidai nawa bakin, da sauri nayi ƙoƙarin juya fuskata saidai an samu rashin sa’a inda ya sauƙe min wani irin light french kiss saman lips nawa,sannan ya zarce zuwa kunnena kamar mai rada ya ce, “muje kici kayan dadin da na siyo maki”.wani irin shock naji ya bani a take har saida jikina ya jijjiga.

Duk da yanayin da na shiga amma na make kafada da fadin, “ni banso, kawai ka kaini wajen innarmu ina son inganta”…Na fada ina turo baki gaba.

Murmushi yayi yana shafa kanshi as usual ya ce, “wajen Innarmu kike sin zuwa?”

“Ehhh” na fada da sauri. Wani murmushin Jabeer ya kumayi ya ce, “Ohk zan kaiki amma on one condition sai kinci abinda na kawo maki,”.

“Nidai na koshi” na fada cikin turo baki gaba….Saman kujera ya zauna yana harde kafafu ya ce, “ohk then baki shirya zuwa wajen innarmu ba kenan?”.

“Allah hamma jay na shirya dan Allah ka kaini kaji”na fada pleadingly…Tasowa yayi zuwa inda nake tsaye ya kama hannuna har imda ya ajiye ledar da ya shigo dashi kasa kasa ya yi da murya hadi da fadin “kazace faaa”…..

Duk yadda Jabeer yaso ta ci kazar nan yau Maryama ki ta yi,duk kaunarta ga kaza kuwa har abun ya bashi mamaki,da ya dage sai ta ci ma kuka ta sanyamashi,da kyar tasha fresh milk mai sanyin gaske dan kadan….Ganin tana bata mishi lokaci ga dare yanayi ne yasa shi cin namar sama sama sannan ya ce taje tayi wanka su tafi,wani irin zaro ido nayi har hakan ya bawa jabeer dariya.

“Wanka kuma hamma jay a cikin duhun nan? nifa nayi wanka dazu da maghriba faa”.

“Ohhh sorry na manta ne kinyi wanka,amma ni banyi wankan ba, kuma kinga na wuni zirga zirga yau, let me freshen up sai mu tafi,”

Wasu hawaye ne suka shiga silalowa maryama cikin hawayen ta ce, “kai dai hamma jay kuma kana ganin dare yanayi kace wanka zaka shiga?”.

“Wanka mana pretty, ko so kike inje wajen innarmu ina tsamin datti ta ce bakya kula mata dani?” ya fada in a naughty way,Bai jira jin abin da zan ce ba ya fice daga dakin bayan ya kunna min light na wayarshi….Bayan kamar minti ashirin ya shigo dakin daure da babban towel din da bansan inda ya samoshi ba don bai fita da komai ba, sai wani dan karami yana ta goge kanshi da,cikin mintunan da ya kwashe dinnan ji nayi tamkar in bishi toilet din tsabar yadda na zak’u inje wajen Innarmu tamkar na shekara ban gansu ba haka nake ji.

Da sauri na rufe idanuna ganin yadda ya shigo ba tare da ya bi ta kaina ba ya shige bedroom nanma ya kwashe kusan wasu mintina ishirin d’in bansan me yake aikatawa ba,shikuwa jabeer tunda ya shiga ya kwanta rigingine saman gadonta kafafunshi suna kasa ya yi filo da hannunsa duka biyu ya zubawa fan dake saman ceiling na d’akin ido kamar mai karantar wani abu,a hankali ya lumshe idanu jin wani abu na mishi motsi a jininsa.

Gajiya na yi da zama a palon na mik’e cikin sand’a na lek’a d’akin, yana kwance har lokacin, turo baki na yi na karasa shiga dakin a hankali nake takawa har zuwa bakin gadon na ja na tsaya ina k’arewa hallitar fuskarsa kallo,…Kara shagwabe fuska na yi na ce, “shi ne kazo kayi baccinka ka manta da ni ko?”.

Shiru jabeer baice komai ba,kara matsowa na yi gab da shi na sa hannuna ina dan bubbuga nashi hannun da yayi matashin kai dashi,nacigaba da ce wa, “Hamma Jay shi ne ka yi baccinka ka barni ina ta jira ko?”.Jabeer dake jin bakon yanayin dake tattare dashi yana k’aruwa a hankali ya sauke wani irin ajiyan zuciya sannan ya sa nashi hannun ya janyota ta fada kanshi…

Banyi aune ba naji ni jikinshi,bude rinannun idanunsa ya yi ya zuba su a kaina yana min wani irin kallo mai gigita tunani,kallon kallo muka fara yana kasa ina samanshi,..ta ke na daburce na fara kokarin kwatar kaina amma na kasa, da shakakkiyar murya ya ce, “Kina son zuwa wajen innarmu da gaske?”.

Da sauri na gyada mishi kai hadi da cewa, “ehh da gaske plsss”…

Yunkura ya yi dani hadi da mikewa ba tare da ya sauke ni daga jikinshi ba har muka fito tsakar palon sannan ya dire ni, ya ce, “ki tayani muyi shafa’i da wutr sai mu tafi, kinga ko mun dawo dare ya yi sai ki shiga daki kiyi baccinki nikuma in kwana anan”. Ya fada yana nuna saman three seater dake palon.

“Ba tare da tunanin komai ba na ce, “da gaske kake hamma jay”.

Dage min gira guda daya ya yi yace, “Ehh mana prettyn hamma jay”.

Banjira ya kara cewa komai ba na nufi hanyar fita dan da gaske nake ina son zuwa naga innarmu…

Har na je kofa ya ce, “tsaya mu fita tare akwai duhu,da gaske kuma akwai duhu din dan ko tafin hannunka baka iya gani,shi ya saka mana ruwa a buta muka daura alwala tare,sannan yaja akwatin da ya dawo dashi daga gida muka shiga dakin,bedroom ya wuce da akwatin ya fitar da jallabiyarsa da kuma boxer ya saka bayan ya shafe jikinsa da oil perfume,kana ya feshe jikinsa da turarensa mai dan karen dadi oud essential.Abin sallah ya shimfida kusa da gado ita kuma ya fitar mata da hijab da wata riga mara nauyi.

Palon ya dawo ya samu maryama zaune saman kujera ta matse hannunta a tsakanin cinyoyinta,kamshin turarensa ne ya sanar dani wanzuwarsa a wajen,kamun in dago sai ji nayi hamma jay ya sungumeni tamkar wata yar baby har cikin dakin sannan ya dire ni yana nuna min kayan da zan saka.

“Ni na jikina ma zaiyi sallah,ai dashi naayi maghriba da isha ma” na fada haka kawai na ji gabana yana faduwa kirjina kuma yana ta tsalle.

Baice komai ba ya hau saman sallayar dake dan gaba kadan, hijab nawa na saka na hau wacce ke bayan nashi muka fara salla, raka’a biyu muka yi bayan munyi sallama na ga Hamma jay ya daga hannu sama yana ta kwararo addu’oi ameen kawai nake cewa amma har ga Allah a kasan raina haushin bata mana lokacin da ya ke na ke ji…Bayan wani lokaci ya juyo gabana kaina ya rike nanma ya yi addu’oi sosai ba tare da na samu zarafin hanashi ba, mikewa ya yi sannan ya nade abin sallar ya ajiye kan bedside drawer, ya ce, “ki canza kaya mu tafi karki bata min lokaci kuma” ya fada with seriousness.tun ban tambayeshi abin da ya hanamu yin sallar wutr ba.

Cikin nutsuwa nace, “Ni haka zanje fa hamma jay dazu ne fa na sa kayan nan ba abin da nayi dasu kuma sai salla, bakin gado ya koma ya zauna yana harde kafa sannan ya ce, “then yau ba zuwa ganin innarmu kenan baby”.Ganin yadda yayi maganar tankar ba shi ba yasa ni juyawa zan dauki rigar da ya ajiye min din, sai kuma na dawo ina tura baki na ce, “to ka fita mana sai in sauya kayan”.

“Kina bata mana lokaci fa,” ya fada cikin basarwa tamkar bai ji magana ta ta farko ba. “ko dai kin fasa zuwa ne?”ya cigaba da maganar.

Ba yadda na iya dan inason zuwan, na dauki rigar zuwa edge na dakin inda wardrobe nawa ya ke nmhar na zuge zip din siket nawa na juya a firgice na rike rigar sakamakon hada ido da mukayi dashi, “wayyo hamma jay ni ban yarda ba Allah ka fita kawai,”

Dariya ta bashi sosai ganin yadda tayi da fuska dan haka ya dara abinshi sannan ya ce, “to na rufe idona ki canza da wuri dare yanayi.”

“Uhm uhm ni ban yarda ba Allah wayo kake min kuma”.

“Da gaske na rufe idanu na idan kinaso ma ki juya abinki sai ki cire rigar, idan kuma kika yarda na irga goma baki sauya kaya ba zamu fasa tafiyar ne sai nan da wata biyar.”

  "To ka rufe idon"

Rufe idanu jabeer ya yi yana murmushi da shafa beard nashi, da sauri na juya na cire rigar dama ba bra a jikina dan rigar ta kamani kadan zip na siket na kama na zuge, a hankali ya bi kafata ya sauka kasa ya rage daga ni sai underwear, na kama rigar da ya fitar min da niyyan idan na sa sai in cire undies din kawai naji saukar hannunshi saman kirjina kana bare chest nashi mai cike da lausasan gargasa saman bayana,wani irin shock ne ya ziyarcesu a tare,juyo ni yayi without thinking twice ya hade bakinmu waje daya,…Wani irin kiss mai cike da zallar soyayya da bayyanawa zuciyar Maryama irin asalin kaunar da ya ke mata jabeer ke aika mata, kafafunshi da ya ji suna neman gaza daukanshi ne yasa shi daga ta cidak zuwa saman gadon,kusan minti goma Jay ya kwashe yana romancing pretty, yayinda a nata bangaren ta kasa yin ko kwakkwaran motsi dan Jay ya riga da ya gama kashe mata duk wani gaba na jikinta da salonshi mai ban mamaki,kana jikinta ya amshi sakonninsa yadda ya kamata, lokacinda ta ji bakin jabeer na karanta addu’ar kusantar iyali ne ruhinta ya dawo jikinta hade da tunaninta, wani irin yunkura tayi da zabga ihu mai azabar karfi tana ture shi amma ina karfin ba daya ba, kuma a lokacin Jay yayi nisan da ko da loudspeaker aka kirashi bazai ji ba,…Yunkura ta kuma yi, hakan ya ba jabeer dake ta neman hanya daman wucewa da kyar wani ihun ta kumayi a daidai lokacin…
💫MARYAMA💫

EPISODE 33/34

   BY

UMMU FADEELA

_ Ƙanƙame ta Jabeer ya yi jikinsa na rawa tamkar ana kaɗa masa gangi a lokacin da ya samu nutsuwa, kafun a hankali ya faɗa gefenta jikinsa gaba ɗaya yana saki kamar ana zare masa laka,a hankali ganinshi da jinshi ya fara ɗaukewa kafun wani lokaci da bai iya tantancewa ba duhu ya mamaye ganinshi gaba ɗaya idanunshi suka rufe kana numfashinshi ya ɗauke cakkk ya tafi doguwar suma…..a nata ɓangaren itama Maryama tuni ta sume tun ba’aje ko’ina ba dan Hamman nata bai zo mata da salon wasa ba,plus yadda abin ya zo mata a bazata hakan ya haddasa mata ɗaukewar numfashi na wucin gadi…

(Wannan shi ake ƙira haihuwar guzuma, ɗa kwance uwa kwance,..ina jin dai ba iya Maryama zaku gasa ba team JAY harda oga kwata kwata🙆)…..

A hankali ya fara buɗe idanunshi da suka mashi nauyi matuƙa sakamakon iskar asubahi da ta fara busoshi .A kan ta ya sauƙe jajayen idanun nashi kana ya na sauƙe wasu irin tagwayen ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda ya yi tseren doki,Duk da baya iya ganinta saboda duhun da ke a ɗakin.Ta ke abubuwan da suka faru suka fara dawo masa cikin ƙwanyarsa dalla dallah tamkar a lokacin suke faruwa,hannunshi ya sa akan waist nata ya janyota zuwa jikinshi ya matse ta gam yana jin kuka na taho masa amma ya kasa yin kukan sai ajiyar zuciya kawai,…Har lokacin Maryama bata dawo hankalinta ba tana cikin suma.

Kamar wanda aka mintsina jabeer ya tashi tuna cewa tun wani ihu da tayi cikin dare bai ƙara jin motsinta ba,laluɓen wayarshi ya fara jiki na rawa,da ƙyar ya tsinto ta a acan gefe ya kunna light ya dallare fuskar Maryama da shi, kwance take ba alamun numfashi tattare da ita,fuskarta ta kumbura ta yi jajur hakama idanunta sun haye suntum duk da a rufe suke,wanda hakan ke alamta irin kukan da ta sha,ga wasu busassun hawaye layi bibbiyu kwance saman fuskar.

Dam dam darandam…haka kirjin Jabeer ke bugawa tamkar haɗuwar ƙarfe da ƙarfe,a rikice ya fara girgizata da iya ƙarfinshi ya na ambaton sunanta, “Pretty! pretty!!Maryamaaa!!! wani irin wawan tsalle ya yi ya dira daga gadon,ya manta da rashin karfin da ke tattare dashi ganin ba alamar numfashi a tare da ita. A tamanin ya fita palo ya ɗau ledar pure water guda ɗaya da wani gudun ya koma ɗakin yana tsinke bakin ledar da haƙwaranshi.Tamkar bakin pampo haka Jabeer ya hau bulbula mata ruwan saman fuskarta har zuwa kirjinta ba tare da ya damu da yadda ya ke jiƙa gadon ba…still ya yi a wajen zuciyar shi na bugawa da karfi karfi ganin ya juye mata ruwan amma bata farfaɗo ba,karasa hawa saman gadon ya yi ya tallabi kanta ya ɗaura bisa cinyarsa yana jijjigata da iya karfinsa…ba abin da ya ke fita a bakinshi sai ƙiran sunanta ba ƙaƙƙautawa, amma ko gezau, Maryama ba ta yi ba.Iya ruɗewa Jabeer ya ruɗe idanunshi sun kaɗa sunyi jajur da su…

Kamar daga sama yaji tana sauƙe wani irin ajiyar zuciyar da ya sashi kuma tallafo kanta ya matse a kirjinsa kamar mai tsoron kar a ƙwace masa ita ya ce, “Pretty pretty buɗe idanunki ki ganni, ni ne,hamma jay na ki ne,dan Allah ki buɗe idanunki ki ganni”, ya faɗa yana ƙara matse ta gam gam.
Sama-sama kamar a cikin iska Maryama ta ke jiyo muryar Jabeer,yayinda take ta kokawa da numfashinta wanda ya yi nisan zango…..Wani irin fizga ta yi da ƙarfi ta sa ki marayan kuka mai karya zuciyar mai sauraro.

“Alhamdulullah” Jabeer ya furta kana ya lumshe idanunsa yana shafa bayanta a hankali alamar rarrashi…duk yadda ta so ta zame kanta daga jikinsa kasawa ta yi dan ji take kamar an ɗaɗɗaureta ne da igiya ga jikinta da ya ɗau zafi zau tamkar wuta ko hannunta bata iya motsawa, a gefe ɗaya kuma wani irin tsanar Jabeer ne da kuma tsoronshi suka ma ta dirar mikiya lokaci ɗaya…

Ganin lokaci na tafiya ne ya sa Jabeer sassauta riƙon da ya mata yana zame ta bisa gadon,ƙara Maryama ta saki mai ƙarfin gaske sai dai bai fita da ƙarfin ba saboda dishewar da muryarta ya yi.

“Sorry Pretty, I don’t mean to hurt you,sorry please, I don’t really know what came over me.”Ko kallon inda ya ke bata yi ba har ya gaji da sambatunshi ya fita cikin rashin sanin abun yi…zagaye tsakar gidan Jabeer ya fara tamkar soja yana tunanin mai ya kamata ya mata,a gefe ɗaya kuma wani irin farin ciki ne fal ranshi, ji ya ke tamkar ya tsaga zuciyar shi ya jefata ciki kana ya ɗinke cifff abinshi,duk yadda yake tsammanin abin, it beyond his expectation kamar yadda ta bashi wannan precious gift ɗin da bazai taɓa mantawa dashi ba, dole shima ya samo something special da bazata manta dashi ba ya bata as pride gift, murmushinsa mai kyau ya yi yana shafa kai ya ce, “… kitchen ya faɗa daga karshe jin zai rasa sallar asubahi,stove nasu ya kunna ya hawar da ruwan zafi,..babban flask ya janyo da nufin idan ruwan ya yi ya juye ciki, sai ya jishi cike da ruwa.

A bocket ya juye ruwan flask ɗin ya surka ya shiga toilet na dashi bayan ya ɗauko wani boxer da towel a ɗakin…Bayan wani lokaci kadan ya fito sanye da wankakken gajeren wandonshi da towel rufe a kafaɗunshi,ruwan da ya hawar sai zaɓalɓala yake hakan ya sa shi juyewa da dan sauri sauri,wani irin tsalle Jabeer ya yi yana yarda tukunyar gefe haɗi da fara yarfe hannu kamar ƙaramin yaro sakamakon taɓa shi da ruwan ya yi lokacin juyewa,yana cigaba da yarfe hannun ya kuma ɗaga tukunyar ya cika da ruwa ya mayar bisa stove ɗin,tamkar soja haka jabeer ke tsaye kan ruwan har shima ya tafasa ya juye cikin bocket ɗin ya surka sannan ya mayar ɗaki.

Lokacin da ya koma ɗakin Maryama ta ci kuka har ta galabaita ga muryar dama ta dishe.

Ranƙwafowa ya yi kanta cikin sanyin murya ya ce, “Sweet wife!”

Wani irin bugawa kirjina ya yi jin muryarshi dab da kunnena,da gaske wani tsoron hamma Jay ne ya dirar min dare ɗaya.

“Pretty ki tashi kiyi wanka na haɗa maki ruwa kar time na salla ya wuce,”pretty”ya ƙara faɗa yana shafa kumburarriyar fuskata.

Ko motsi banyi ba, ba dan banji shiba sai dan yadda na ke jin ko ina na jikina a ɗaure.Ganin ta na ɓata lokaci ya sa Jabeer ya sunkuce ta ita da bedsheet ɗin kamar yar baby ya fara takawa zuwa waje.ƙanƙameshi gam Maryama ta yi tana fashewa da wani kukan dan yadda ta ke ji kamar zata mutu.

Bai tsaya ko ina ba dai banɗaki ya fara ƙoƙarin sauƙeta,sai dai a nan ake yinta,duk yadda Jabeer ya so ta tsaya da ƙafafunta abin ya faskara sai rawa da jikinta ke yi idanunta na tsiyayar da hawaye,.sosai yanayinta ya bashi tsoro dan haka cikin sanyin murya ya ce, “Pretty ina ke maki ciwo,?baki da lafiya ne?”tamkar zai yi kuka ya ke maganar.amma ko uffan maryama ta kasa faɗa ba don bata da abin faɗa ba sai dan yanayin da ta ke a ciki.

Saman ɗan dakalin da aka yi musamman dan wanka ya ajiyeta yana ya ye bedsheet ɗin zaro ido Jabeer ya yi zuciyar shi na bugawa ganin bedsheet ɗin ya yi kaca-kaca da jini kai kace kaza aka yanka,naɗe wa yayi da sauri gami da ajiyewa gefe ya fara mata wankan ganin da gaske bazata iya ba,…da ace ina da iko bazan barshi ya taɓa ni ba, amma inda nake ko yatsata na motsa ciwo ya ke min.

Ina ji ina gani hamma Jay ya wanke ni tas ya kuma ɗaukata kamar baby ya maida ni ɗaki haɗi da kwantar da ni saman kujera ya rufe ni da towel nashi. ɗakin ya koma ya ɗan goggoge saman gadon inda ya yi staining sannan ya canja bedsheet ya fitar min doguwar riga ya dawo palon, kimtsani ya yi ya kuma ɗaukata again zuwa saman gadon ya kwantar da ni haɗi da lulluɓa min wani lallausan duvet…kafun Jabeer ya gama hada hadan har gari ya fara haske,dan haka ya shimfida abin sallah kawai a gida ya zura jallabiya ya gabatar da sallah,sosai ya gabatar da addu’oin godiya ga Allah, sannan ya koma toilet ya haɗa ruwa ya wanke bessheet ɗin da ya baci tas ya shanya saman igiyar dake tsakar gidan.

Da sauri sauri ya gama ya koma ɗakin.zuwa lokacin jikin Maryama ya gama ɗumewa da zazzaɓi sai rawar sanyi ta ke yi haƙwaranta suna bugun juna, “Subhanallah,pretty!meke damunki?pretty baki da lafiya ne? ko mu tafi asibiti?gaba ɗaya Jabeer ya rikice ya zama wani abin tausayi shima jikinsa ba ƙarfi mazantaka ya ke nunawa kawai amma shima da zai samu dama kwanciya zai yi.Hannu ya sa saman wuyarta da sauri ya ɗaga jin yadda ya yi wani zafi kamar wuta.shidai Jabeer kanshi ya ɗaure ya rasa abin da ya kamata ya yi,gaba ɗaya komai ya tsaya mashi,waya kamata ya tambaya, “Innarmu” zuciyar shi ta bashi amsa ba tare da tsayawa dogon nazari ba ya ɗau wayarshi ya fara dialling layin innarmu,ringing biyu ta ɗaga cikin sallama.amsa sallamar ya yi yana faɗin, “Barka da asuba Innarmu,ya muka tashi?”

“Lafiya Alhmdllh” cewar innarmu.

“Jabeer,ya kuke?lafiya dai ka ƙirani yanzun nan?ko dai akwai abin da kuke bukata ne Fati ta kawo muku…”

Inna ta ƙara faɗa jin jabeer baice mata komai ba kuma ga katin shi yana tafiya,. A ɓangarenshi kuma samun kanshi ya yi yanzun da jin nauyin Innarmu abin da bai taɓa yi ba.

“Kana ta re da ni kuwa jabeer?ko dai baka jina ne?”

Shafa kai ya yi yana jin qani irin kunya na lulluɓeshi amma baida mafitar da ya wuce sanar mata ɗin gashi kuma ya kasa hakan,cikin dauriya ya ce,…..
💫MARYAMA💫

EPISODE/35

WRITING BY

UMMU FADEELA.

———–“Babana kana tare da ni kuwa?”.
cewar Innarmu jin Jabeer ya yi shiru bai ce komai ba. “kana jina?” ta kuma tambaya.

Da ƙyar Jabeer ya yi ƙundunbalar cewa, “am ehm dama Innarmu dama ita ce”,

“Jabeer ƙalau kake kuwa mai ke faruwa na tambayeka amma ka cika ni da In’ina”

“Innarmu ita ce bata da lafiya tun jiya kuma yau ko tsayawa bata iya yi, plsss Innarmu kizo ki ganta dan Allah” ya ƙare maganar da ɗan karaya a muryarshi.

“Subhanalla!mai ya sameta haka?” Inna ta kuma jefo mishi tambayar da ya kuma rikita shi.

Haka kawai fa Innarmu haka kawai ta kasa tashi da kanta ba abin da ya sameta.

“To sai kuje asibiti ai,ni mai zanzo in maku a gida?” cewar Inna tana yanke kiran.Wani irin murmushi yana bayyana saman fuskarta, ba tun yanzu ba tasan itace mutum na farko da Jabeer ke fara tunkara da damuwarshi tun yana yaro, kuma wannan shine tarbiyar da ta bashi na cewa duk abin da ya sameka ko ya shige maka duhu ka fara tuntuɓar iyayenka kamun wasu suji, kuma Alhmdllh Jabeer ya ɗau wannan tarbiyar sai dai batai zaton har a irin wannan al’amarin zai iya sanar mata ba, dan sarai ta fahimci abin da ya faru, and she’s happy da Allah ya nuna musu wannan lokacin,murmushi ta kuma yi har haƙwaranta na bayyana.

“Ah’ah na shiga uku ni jikar mutum huɗu,wai ba magana nake miki bane Dijah amma kin min shiru kamar wata shashasha”.cewar Daada da ta ajiye kayan da take ta aijin naɗewa tun bayan da Innarmu ta amsa ƙira ta zuba mata idanu.

“Ayya kiyi haƙuri Daada ban jiki bane ba”.

“Yo ina zaki ji ni dama gaba ɗaya kin ruɗe kin firgice,me ya samu takwarar nawa na ji kina ambaton sunan asibiti da safiyar nan?” ta tambaye ta tun bata dire maganar ba.

Murmushi ta kuma yi. a’a ba maganar murmushi bane Dijah faɗa min abin da ke faruwa, kar dai ace rashin haƙurin yaran zamanin ya nuna ya turmushe mana ƴa ba tare da ya dubi ƙanƙantar ta ba?” murmushi Inna ta kuma yi ta sinne kai ƙasa, ita tana rasa gane kan daada,komai ya zo bakin ta faɗa take tana manta cewar ita surkarta ce,kodan su ɗin yan uwane?

A firgice ta ɗago kanta tana zare ido sakamakon wani irin salatin da Daada ta rabka,haɗi da kiran sunan” lami, lami”

Har tana tuntuɓe Inna lami ta shigo ɗakin tana tambayar “lafiya Daada”?

“Inafa lafiya ƴannan,Jabeeru dai ya cika tantirin mara kunya lamba ɗaya, ima faɗa miki lamba ɗaya na bugawa a jarida shafin farko,yanzu inba rashin kunya ba bazai jira mu tafiba tukun ya ida rashin kunyar tashi ba,yau ni naga jaraba da farar safiyar nan? amma ko zuwa ganin ɗaki bamuyi ba ace yaron nan ya turmushe yar mutane daren jiya kuma tsabar rashin ta ido yanzu ya ƙira uwar wai yar bata da lafiya? tir wannan zamani da ya yara basa girmama ƙimar mata,mu a lokacinmu basai yarinya tayi shekaru uku a ɗaki ba tare da mijin ya riƙe ko dan yatsanta ba, amma jiba ki gani daga kai mashi yar kwana biyu har ya haiƙe mata.”faɗa daada keyi ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.

“Yanzu ni abin da ban gane anan ba daada shine,laifine dan Jabeer ya haɗa shimfiɗa da matarshi,ina ce takanas kika taso daga nijar dan shaida ɗaurin aurensu?amma kinzo kina ta bambamin faɗa dan kawai ya aikata abin da yake na halal.kinata wani haɗa zamaninku da ake da karancin wayewa da wannan zamanin”cewar inna lami da maganganun daada ya tunzurata.

“To dama nasan ba kirki ne dake ba ai lami, yanzu sai ki iya kawo min duka, wuce muje muga mai ya aikata mata, wataƙila ma ciwo dan banzan ya ji mata ya kuma kasa gasata.”

“Kin wuce ne ko sai na ɗaike ki a ka?”.inji daada ganin inna lami na tsaye ƙiƙam.Daada ya za’ayi mu wani je gid…..”

Wani kallon da innarmu ta watsa mata ne yasa ta yin shiru ba dan ta so ba, “kuje kawai lami wataƙila akwai abin da zaki taimaka mata dashi, ga can abin karinsu da Fati zata kai idan anjima dama ki ɗauka”

Ba don taso ba ta yafa mayafi haɗi da bin bayan daada wacce har tayi nisa tana ta sababi, ita a ganinta wannan sirrinsu ne bai kamata wani ya sani ba.

Turus daada ta tsaya a tsakar gidan tana ƙarewa babban zanin gadon dake shanye tsakar gidan yana ta ɗigar ruwa kallo,juyowa tayi haɗi da kallon inna lami da ta ja tunga ta tsaya itama tace, “Lami kin gani ko?” munafuƙin har ya wanke zanin gado”

Murmushi kawai Inna lami tayi tana bawa zuciyarta tabbacin dole fa daada tana bukatar uzuri dan shekaru sun ja,dan ma dai akwai karfin jiki.

        ************

Zama Jabeer ya yi bakin gadon haɗi da dafe kanshi cike da rashin sanin abun yi lokacin da Innarmu ta yanke wayar, ya daɗe a haka ba tare da yasan what next ba.

“Ya Allah” ya furta ya dafe kanshi dake sara mashi gami da juya kanta jin wani irin hucin zazzaɓin da take fitarwa ga kukan da take amma baya fita.

Kanta ya tallafo zuwa kan cinyarshi ya kwantar gami da fara shafa dogon gashinta zuwa saman kumburarriyar fuskarta, “Sorry pretty” kawai Jabeer ke faɗa idanunshi sun kaɗa jajur dasu….a wannan yanayin ne kuma ya fara jiyo magana kamar daada a tsakar gida,bai gama tantancewa ba yajiyo sallamar inna lami a bakin ƙofar ɗakin.

A hankali ya sauƙe kan Maryama da yai mata matashi da cinyarshi zuwa kan pillow sannan ya miƙe yana gyara mata kwanciya,haɗi da shafa kyakkyawar fuskarta da ta kumbura tayi haske fayau.Sannan ya fita.

“Haan ya kika tsaya daga waje baki shiga ba?gidan baƙonki ne ko dai shi jabeerun ne ya kafa allon sanarwar kar wanda ya shiga mishi ɗaki”.?

“Eh musamman ma idan wanda ya zo ɗin ban gaiyyace shi ba.”Cewar Jabeer da ya ji maganar da daada take yi lokacin da ya ke fitowa.Risinar da kai ya yi ƙasa ya ce, “Barka da zuwa Inna”

Da murmushi Inna lami ta ce, “yauwa barka ka dai ango,ya ɗiyata ɗin Innarku ta ce bata ji daɗi ba”.

Yana shafa kanshi ba tare da ya ce komai ba, daada da ta ɗaure fuska tamau ta ce, “kaga ja’iri mara kunya zaka bamu hanya ne ko yaya?.”

Ɗan matsawa yayi fuuu ta shige ɗakin ba tare da ta kalleshi ba,ɗan dariya kaɗan Inna Lami tayi tana kallon Jabeer da still kanshi ke kasa ta ce, “Daada yanzu sai an haɗa mata da uzuri,dariyan yayi shima yana gyaɗa kai da faɗin “haka ne kam”.

Sosai sukayi mamakin halin da suka tadda Maryama da zuwa lokacin jijinta ya ƙara yin tsami dan rashin amfani da ruwan zafin da basu yi ba tun asuba ɗin, “dama nasan za’ayi haka,inba rashin imani irin ma alhassan da dijah ba ina Jabeer lutete dashi ƙiran samudawa ina maryama da take yar firit da ita? ai kowa yasan daman cutar ta kawai za’ayi to gashin nan dai tun ba’aje ko ina ba kun fara gani”.

Daada kenan ke ta sababi ganin Maryama sai maƙyarƙyata take tamkar an jiƙa kyanwa.shigowar Inna Lami ya sata yin shiru.

Ruwan zafi Innan ta haɗa daidai zaman mutum cikin baho sannan ta kama Maryama da dambe da komai ta tsoma ta ciki, ihu ta ke yi tana ƙanƙameta,duk da ta fahimci irin azabar da take ci hakan bai sa ta barta ba don shine gatan da zata mata.a hankali ta fara jin ruwan yana mata daɗi har da lumshe idanu ganin haka inna lami ta fita ta barta a bayin….

……………………..*………………………

          GOMBE

Tsabar doƙi Khadija kasa bacci tayi a ranar sai juyi kawai take a kan gado,ƙiran sallar farko a kunnenta dan haka ta tashi ta fito a hankali ta kama handle ɗin kofar ta buɗe without making any sound,sauƙa ta fara yi daga stairs ɗin cikin sanɗa dan kar Mommy ta jiyota,saura baifi steps uku ba ta gama sauƙa taja ta tsaya tana turo baki gaba gami da kama bakin rigar baccinta tana wasa dashi.

Mommy ce zaune downstairs idanunta sanye da glasses tana operating laptop dake gabanta…ɗan sauke madubin idon kaɗan tayi zuwa ƙasa tana kallon Khadija da taƙi gaba taƙi baya.Hannu Mommy ta sa ta yafitota haɗi da nuna mata gefenta, da sauri ta gama sauƙowa tazo ta zauna gefenta ɗin tana mata side hug “morning Mommy”.

“Morning dear,ina zakije da yanzun nan ko Salla ba’ayi ba?”.

“Mommy zan jiƙa rice ɗin da zan wa yaya girki dashi ne,kinsan fa ya ce morning flight zai bi, and ba wani nisa tsakanin port da nan” ta kare maganar cike da shagwaba, shafa kanta Mommy ta yi ta ce, ” God bless you dear, je ki jiƙa but be fast kar jam’in salla ya wuce ki.”

“Thank you my momm” ta faɗa tana bawa mommy peck a hannu ta shige kitchen ɗin da ɗan gudunta.iya tsaruwa wannan kotchen ɗin ya tsaru, babu ce kawai babu a cikinta, store ɗin dake manna cikin kitchen ɗin ta shiga bayan ta dauki mazubi mai ɗan girma kaɗan,farar shinkafa ta ɗiba kofi biyu ta fito ta kunna tap ta zuba ruwa akan shinkafar sannan ta ajiye a gefe ta fita,lokacin da ta fito babu mom a palon ta haura sama, dan haka itama hayewa ta yi ta shige ɗakinta direct toilet ta shiga ta ɗauro alwala babban hijab har kasa ta ɗaura saman riga da wandon baccinta ta gabatar da rak’atal fajr,tana zaune bisa pray mat ɗin da qur’an a hannunta har aka tada sallar asubahi,da ta kammala yau ko azkar batayi ba ta yaye hijab din gami da linke shi ta ajiye saman bedside drawer.gashinta ta naɗe cikin hula sannan ta sauƙo kasa, babu kowa palon har yanzu kuma gari da ɗan duhu dulum dulum,kitchen ɗin ta koma ta janyo apron ta ɗaura akan pyjamas nata ta fara aiki.Ruwa ta jona a kettle sannan Shinkafar ta duba ganin ya mata yadda ta ke so ta wanke shi ya fita tas ta juye cikin blender haɗi da markaɗa shi yayi luƙui,wasu glass bowl babba da ƙarami ta ɗauko ta juye a cikin babban ta ajiye blender ɗin cikin sink.

Babban cokalin miya ta ɗauka ta debi markaɗaɗɗen shinkafar ludayi daya da kaɗan ta zuba cikin karamin bowl ɗin sannan ta koma kan kettle nata da zuwa lokacin ruwan ciki ya tafasa kashewa tayi ta ɗaga ta zuba tafasashshen ruwan akan ƙulli ludayi daya da kaɗan ɗin da ta zubawa karamin bowl ɗin, take ya haɗe ya zama tamkar kunu,juyashi ta dinga yi har yayi sanyi ƙalau da yake sauri take yi,bayan yayi sanyi ta hadesu da sauran ɗanyen ƙullin ta juyasu suka hade jikinsu sannan ta zuba yeast daidai ta zuba baking powder shima daidai da ƙullin ta kana sugar (according to your taste) sai gishiri ɗan kaɗan.,ta juyasu sosai ta rufe da babban marfi ta barshi a wajen.

Gaban frizer taje ta buɗe ta fara tunanin da mai zata haɗa miyar kifi ne ko gajeren ƙashi or peppe chicken.murmushi tayi har babban wushiryarta na bayyan tuna irin amincin dake tsakanin yayan nata da kaza,thou SINASIR da jajjagen danyen kifi yafi daɗi amma bari tai masa peppe chicken ɗin kawai.

Wata dakwalar kazar gidan gona ta ɓanɓaro kasancewar ta dasƙare, cikin ruwa ta jefa ta barshi ya yi melting ta koma kan kayan miya ta jajjaga attaruhu da tattasai mai ɗan yawa kana ta dau plate ta daura curry powder da maggi thyme garlic and ginger powder tumeric soysource da sauran kayan spices da take bukata gyara kazar tayi bayan tayi melting ta yayyanka su into peaces sannan ta wanke ta zuba kayan kamshi da albasa ta ɗaura kan gas wani albasar tayiwa yankan slice mai ɗan yawa shima ta ajiye gefe, da sauri sauri take aikin.fry pan ta fitar ta ɗaura bisa gas, wata tukunyar ta kuma zubawa ruwa haɗi da mint leaf ginger cinnamon da sauran kayan shayi ta daura a gefe, sannan ta koma kan ƙullinta da zuwa lokacin ya taso yayi kyau, fry pan ta ɗaura saman gas shima ta shafa mai ta fara suyan sinasir ɗin ta, take gidan ya baɗe da kamshin abubuwa kala kala, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama soyawa ta zuba cikin food warmer mai dan karen kyau shima tea ɗin dake ta tashin ƙamshi ta juye a tea flask da sauri sauri ta soya kazar ta ta haɗa peppe chicken that look so mouth watering kasancewar ya samu kala mai kyau. shima ta juye a warmer duka ta fitar ta jere saman dining, sai a lokacin cooks na gidan suka shigo dan fara aikin breakfast.

A gurguje ta faɗa wanka ganin karfe takwas ya wuce,tsawon minti talatin ta kwashe tana dirzar jikinta sannan ta fito tana goge jikinnata mai ɗan karen sulɓi da towel, duk da kasancewarta baƙa, amma tana da glowing skin,da shike ita ma’abociyar kamshi ce nan ta fara bulbilawa kanta turare kala kala daga na jiki na hammata, na bayan kunne, na gashi ko ina khadija tana da turarenshi na mussamman, sai da ta gama sannan ta fara shafa haɗaɗɗen manta wanda shima ke cike da ƙamshi,
(Ƴar uwa ki kasance mai yawan amfani da turare, domin mace mai ƙamshi darajarta da ƙimarta daban yake.)

Kasancewarta ba ma’abociyar kwalliya ba a take ta gama shirinta cikin wani tsadadden abaya ash colour ta yane kanta da mayafin abayar sannan ta ƙara feshe jikinta da wani turaren ta ɗauki jakarta ƙirar channel ta rataya ta sanya wasu takalma sau ciki suma na kamfanin channel ɗin ta zari wayarta ta kama hanyar fita tana duba agogon dake tsintsiyar hannunta,zaro ido tayi ganin lokaci ya tafi ashe bata ankara ba.

Da sauri har tana tuntuɓe ta faɗa ɗakin mommy, amma bata sameta ba, dan haka ta fita tana zumburo baki ta nufi side na abbu.still tayi a wajen tana lumshe idanu riƙe da hannun ƙofa bayan ta shiga ɓangaren abbu ɗin sakamakon ƙamshin turaren da ta shaƙa cikin hancinta ……….
💫MARYAMA💫

     BY

    UMMU FADEELA

             TYPING 📲

EPISODE_ 36

  ELEGANT VERIFIED WRITER'S

___________Turo baki tayi gaba ganin duk sun zuba mata idanu, “ya kika tsaya a can mamana ki ƙaraso mana” cewar abbu da ya bar hirar da suke ya juyo ɗauke da murmushi.

Takowa take yi cikin palon cike da yauƙi irin na yan mata masu ji da lokacinsu idanunta ƙyam a kanshi, “Ya Allah!karfa inyi abin kunya”cewar Khadija dake dab da isowa.

A ƙasa ta zauna kusa da ƙafar Mommy bayan ta cire takalman ƙafarta. “Good morning Abbu.” cewarta, “Yaya muka tashi Mamana?hope all is well?”

Ƙara risinar da kai Khadija tayi cike da girmamawa tace, “Alhmdllh, Abbu”

“Masha Allah” tsohon mai cike da ƙima da haiba ya faɗa yana maida kallonshi kan Sadeeq dake ta aikin danna wayarshi.A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin kamar da Sadeeq ke yi da Abbu, a wajenshi ya ɗauko baƙar fata da tsawo kamar daren layya,😜yayinda ya ɗauko yanayin zubin hallitar fuskar Mommynsu.hakan yasa shi zama kyakkyawan gaske haɗe da kuɗi da gyaran jiki da kuma hutu.

“Bakiga yayanki bane duk ɗokin da kika kwana kina yi ɗin sannan ki kasa gaishe shi?”. cewar Mommy tana shafa kan Khadija da ta kwantar saman kafarta.Ɗagowa Sadeeq yayi suka haɗa ido murmushi ya mata haɗe da ɗage gira guda ɗaya,amma sai ta turo baki gaba idonta na cika da kwallah ta ce,duk abin da suke iyayen nasu na lure da su, ɗan mirmushi kawai Abbu yayi yana ɗauke kai.

“Mommy ba shi ne ba” kamar jiran ta furta hakan take ta fashe da kuka mai cike da shagwaɓa.

“Ya salam!wai yaushe zaki girma ne Khadija,you’re no longer a baby fa”

“Mommy ina shi ne ya yi tahowarsa kuma bayan nace maki zanje in ɗaukoshi a airport ɗin,maimakon ki hanasa tahowa sai na gama shiryawa.”

Gefe abbu ya yi da kai yana ƙunshe dariyarsa,yayinda Sadeeq ya zaro ido jin abin da ta faɗa,mommy kuwa kanta ta cigaba da shafawa a hankali ta ce, “Ohhh sorry,kinganshi nan haka muka ganshi da sassafen nan kamar wanda aka jeho ko bala ma bai jira ya je ba,inajin ma taxi ya shiga,amma na miƙi alƙawarin ke zaki kaishi idan ya zo tafiya ohk?maza jeki ki gaida shi”.

Da rarrafe Khadija ta iso wajenshi kasancewar ba bu nisa tsakaninsu,ɗan gefe kaɗan da shi ta zauna tana langaɓar da kai gefe haɗe da tunzuro baki gaba ta ce, “Sannu da zuwa yaya,shi ne tun asuba ina kitchen dan haɗa maka breakfast da kafi so kai kuma kaƙi jirana in zo in ɗauko ka ko?wai ma wani irin flight ka bi ne haka da sassafen nan?ko dai private ne?”.

Ajiye wayar shi Sadeeq ya yi haɗi da riƙe kumatu yana ta kallon bakinta dake ta zayyano bayani ba tsayawa,ajiyar zuciya ya sauƙe jin ta yi shiru ya ce, “Kin gama tambayoyin naki duka?” gyaɗa mashi kai tayi,gami da kafe shi da kyawawan idanunta, “are you sure?” ya kuma tambayarta. “ehh mana yaya”.

    "Ohk,to ina kwana" 

Da sauri ta rufe idanunta da hannayenta duka biyu tana dariya…Murmushi ya yi ya ce, “Mom kamar ji nayi kince yarinyar nan ta zo ta gaishe ni, amma maimakon gaisuwa sai ta buge da tambayata kamar sabuwar yar jarida”.

Duk dariya suka sanya Abbu yana miƙewa ya shige bedroom nashi.

“Kai dai yaya na manta ne fa,” cewar Khadija still hannunta saman fuskarta…”Yauwa MAN kaji ai ta manta ne” cewar mommy da murmushi saman face nata.

“Murmushi ya yi shima yana shafa beard nashi, “Yaya ina kwana to, ka kawo min tsarabata?” khadija ta faɗa bayan ta buɗe fuskarta, tun bai amsa mata ba ta cigaba da cewa na shirya maka wani abu mai daɗi yaya ta so muje kaci,”.

“Hmmm,ji ta kamar wani girki ta iya yen yen yen sai anje aji ba wani abin kirki”.

Hannunshi ta kamo haɗi da miƙewa ta fara janshi wai ya tashi, sai dai ko motsa shi ta kasa yi wajen.

“Da gaske fa yaya ya yi daɗi ka tambayi mommy ma kaji,kafun mommy ta basu amsa Abbu ya fito daga bedroom hannunshi ɗauke da wasu tarin takardu ya ƙaraso palon yana zama a kujerar da take tashi ce shi kaɗai ke zama kanta,ganin haka ne ya sa khadija sakin hannun Sadeeq.

“MAN Idan kayi karin kumallo ina bukatan ganinka,”tsungunar da kai Sadeeq ya yi haɗi da cewa, “Insha Allah”.kana ya miƙenya bi bayan Khadija da har ta iso ƙofa jin abin da Abbu ya faɗa.Da ƙayataccen murmushi iyayen suka bi ƴaƴan nasu, kafun Abbu ya ce, “Ya kamata zuwa yanzu yaron nan ya fara wani motsi fa,gimbiya”

“Nima abin da ke raina kenan yallaɓai,tunda ta kusa ƙare makarantarta kawai a fara shiri kar abubuwa su zo su kacame mana gashi abu ne tuwo na maina,” dariya mai ɗan tsayi Abbu ya yi sannan ya ce, “Ina jinjinawa uwar amarya kana uwar ango,” cike da barkwanci ya faɗa yana ɗaga mata hannu alamar jinjinawa, itama dariyar ta sanya ta ce, “ahto gaskiya ne ai, gwara in aura masa abin da na raina da hannuna tunda dai naga sun haɗa kansu, akan ya ɗauko min yaran yanzun nan da suke raba mace da ɗanta tunma basu shigo ba”.
(To,na shigenge.Mommy ya da haka?.kar dai kisa Maryaman mu ta sake reshe ta kasa kamo ganye).

“Hakane kam gimbiyata Allah ya tabbatar mana da alheri, yanzu muje a bani breakfast kar yunwa ya min illah….A jere suke sauƙowa daga stairs ɗin cike da tsohuwar soyayya har suka shigo dining area ɗin,Khadija dake serving Sadeeq sai surutu take zuba mishi kamar zabiya ta janyowa Abbu kujera ɗaya zuwa baya, sannan ta janyowa mommy ma nata,plate din da ta zuba sinasir guda uku ta turawa sadeeq gabanshi sannan ta ɗau wani bowl mai shape na heart ta zuba peppe chicken da ke ta zabga kamshi ta ajiye masa haɗi da black tea da ya sha kayan kamshi.

“Tanks” ya faɗa kasa kasa yana jan kamshin abincin.

“Abbu kai ma in sa maka wannan ɗin?”. “Mamana abin na rowa ne kenan”.rufe fuskarta tayi ta ce, “a’a fa abbu shi ɗinma dan yana so ne”. “to samin guda ɗaya inji.ɗaya ta sanya mishi hadi da p chicken ɗin ta janyo wani plate ta zuba mishi ainahin breafast da cooks sukayi ta haɗa ta ajiye gabanshi, haka ta sawa mommy ma sannan ta zuba nata ɗan kaɗan tamkar na ƴar baby ta zauna,Sadeeq da ke ta aikawa cikinsa haƙƙinsa dalilin daɗin da abincin yai masa ya ce, “Bani soft drink”. da sauri ta kuma tashi ta janyo orange juice da tasan yana so ta zuba nishi a dogon glass cup ta miƙa mishi sannan ta fara cin nata a hankali kamar ba ta so…da kanshi ya janyo kular sinasir ɗin ya fara zuba wani bayan ya gama cin wanda aka zuba mishi.

Mommy ne ta yi dariya ta ce, “Ta nan ka fi ƙarfi ai, a dafa kaci har da ƙari, amma ka kasa kawo mai girka maka na din din din,”

Sosa kanshi ya fara kamar munafuki ya ce, “Mom dama fa zan faɗa maku cewa na kusan yin aure, kusan dukkansu uku a tare suka ɗago yayinda murmushi ke bayyana saman fuskar su, saidai take murmushin ya fara fading sakamakon jin abin da ya cigaba da faɗa.

“Mom sunantan MARYAMA, bafulatanar Adamawa ce sai kin ganta Mommy kyakkyawa da ita…Wani irin tari ne ya turnuƙe khadija ta ke ta fara tarin har idanunta na ƙwalalowa waje sakamakon tsokar kaza mai cike da yaji da ta sa a bakinta.

“Subhanallah! sannu khadija,cewar mommy da ta taso da sauri bayan tayi namijin ƙoƙarin tashi daga shock ɗin da Sadeeq ya bata.bayanta ta fara bubbugawa a hankali tana shafawa,hannu na rawa Sadeeq ya tsiyaya ruwa a cup ya kai bakinta, ba tare da musu ba ta ƙarɓa ta sha ƙaɗan ta zauna tana ta maida numfashi sama sama duk sannu suƙa ringa mata tana ɗaga musu hannu gami da gyaɗa kai…

——————–**
BAYAN KWANA BAKWAI.

Zuwa lokacin Maryama ta samu lafiya ta dawo normal,sai dai har lokacin tsoron Jay ta ke yi babu kusanci ko kaɗan a tsakaninsu,bayan ya aikata abin da ya aikata ne kuma dan su sami kusanci su zama abu ɗaya,sosai hakan ke affecting nashi, a cikin kwana bakwai ɗinnan har ya fara fita a kamanninshi dan wani irin ramewa yake kamar ba angon sati ɗaya ba, irin annurin nan da ake gani a fuskar sabbin angwaye sam babu a wajen Jabeer, shi ya ke gaba ɗaya aikace aikacen gidan kamar shara da wanke toilet da kuma mopping girki dai har yanzu innarmu ke turo musu ta ce sai sun samu kamar wata ɗaya, amma a zahiri tausayin jabeer ta ke yi dan tasan bashi da kuɗin yin cefane kullum, dabararta shine nan da cikar watan ya fara ɗaukan albashi,tunda ya fara zuwa wajen aikin da ya samu na koyarwa, idan ya dawo kuma gidan ba daɗi haka yake tafiya wajen aikinshi na da inda suke buga gadaje, gaba ɗaya jabeer ya sauya a take rashin nutsuwar zuciyarshi ta bayyana akan fuskarshi, ita kuwa bata da aiki saidai tayi wanka da sallah sai kuma ɓuya, duk sanda ta ji motsin shigowarshi gida duk abin da ta ke yi sai ta bari ta gudu ta ɓuya a bedroom nata,dan tuni ta yiwa ƙofar wani dabara yanda take iya rufeshi yaƙi buɗuwa ta waje…a ɓangaren wayarta kuwa kusan kullum sai ta tuna Sadeeq,amma da zaran ta ɗaga wayar zata ƙirashi sai ta ga kamar Jabeer na tsaye a kanta haka zuciyarta zaita bugawa ba shiri take mayar da wayar maɓuyarta.

Yauma kamar kullum,misalin karfe biyu na rana ya dawo gidan daga makaranta duk ya yi gaje gaje da chalk lamarinka da sabon shiga,ga wasu takardu a hannunshi ga uban yinwar da ya kwaso haɗi da ƙishirwa da ranar da ake ƙwalawa ya haddasa mashi, randar dake tsakar gidan ya buɗe ya kwankwaɗi ruwa sosai sannan ya sa kai cikin palon bakinshi ɗauke da sallama ba bu kowa palon sai kular Inna dake tabbatar masa na abincin rana ne, ajiye tarkacen dake hannunsa ya yi akan one seater ya shiga bedroom ɗin da yau Maryama ta manta bata rufe ba, kwance ya sameta saman gado ta yi ɗai ɗai abinta tana ta sharar baccinta peacefully, ya daɗe tsaye kanta yana ƙare mata kallo kafun ya fito a hankali dan kar ya tada ita, abincin dake palon tuwo da miyar ɗanyar kubewa ya ɗiba a plate ya zauna ya fara ci, yana tunanin mai zai sayawa Pretty ta ci,dan yasan bazata ci tuwo ba sai dai ta zauna da yunwa,…kasancewar ya yi sallar azahar a makaranta, wanka kawai ya shige bayan ya gama cin abincin ya fita da kwanukan,…Bai wani jima a bayin ba ya fito ya shafa mai sama sama ya fesa turare, duk abin da ya ke yi a hankali yake yi dan kar ta tashi, wani three quater ya sanya ba tare da yabi ta kan riga ba ya hau gadon haɗi da janyota jikinshi ya lumshe ido yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya,cikin bacci na jini jikin mutum ga mayataccen kamshinshi da ko a cikin mitum ɗari zan bambance nashi da ya cika min ƙofofin hanci.

Mutsu mutsun tashi na fara amma ya hanani damar hakan sai ma wani irin iska da hura min cikin kunne murya can kasa kasa ya ce, “bacci plssss”.

Rikicewa na ƙara yi jin yanda yayi maganar da wani salo a muryarshi, buɗe baki nayi zan yi ihu dan gaba ɗaya baccin ya gudu sai luguden tsoro da ƙirjina ke yi, amma kamar yasan abin da zanyi ya yi saurin rufe bakina da tafin hannunshi, ya kuma ce wa, ” Shhhhhit Bacci” shiru na yi ina zare ido ƙirjina na dukan tara tara.

A maimakon baccin da hamma jay ya furta sai na ji ya canza hanya,dan kuwa ɗan yatsanshi ɗaya ya ɗaura saman lebena bayan ya sake min baki ya fara zagaye lips ɗin a hankali da yatsarshi,a hankali na yake zagayewa idanunshi a lumshe, cikin lokaci kaɗan jikina ya fara amsan saƙonshi, da ga haka wasan ya sauya salo….

       ................

Siyama kwanaki takwas ta kwashe tana jinya a asibiti,an mata treatment sosai ciki harda haƙorin roba da ta nemi a sanya mata a inda haƙorinta ya fita, yanzu ma da take zaune gaban dressing morror ɗinta, takaici ne fal ranta sakamakon haƙorin da ta wangale baki take kallo a mirror ɗin . (Lallai za ki san ko ni waye Maryama,wato kinyi aurenki kinacan kina farin ciki a gidan ki ko?tabbas kin taro match) siyama dake kallon kanta a mirror ta faɗa kamar mahaukaciya…

BAKWA COMMENT YANZU, ABUN MAMAKI CIKIN AWA ƊAYA IDAN NAYI POSTING A WHASAPP MUTUM SAMA DA ƊARI BIYU KE KARANTAWA,AMMA COMMENT YA NA GAGARARKU.SHI SHARHI YANA ƘARAWA WRITER ƘWARIN GUIWA NE KO BATASO YIN TYPING BA SAI KUGA TA MAKU,MU GYARA PLSSS, I REALLY TIRED DA IRIN SU TANKS,MUN GODE,GODIYA MUKE, AND SO ON, KUNA SHARHI KODA DA WORD GOMA NE..
💫MARYAMA💫

       BY

UMMU FADEELA

TYPING📲

      EPISODE 37/38.

Sosai Jabeer ya samu shauƙi da farin ciki a kasancewarsa da Maryama yau,dan ko kaɗan bata bashi tangarɗa ba, idan baiyi mistaken ba ma kamar harda reply ta ke masa,ba shakka gangar jikinta ya amshi saƙon yanayinshi har ya isarwa zuciyarta.

Bacci ne ya kwasheta bayan lafawar komai, a hankali Jabeer ya fara ƙoƙarin rabata da jikinsa dan ya tsabtace kansa,gashinta da ya barbaje saman fuskarta ya gyara mata zuwa baya,leɓenta dake matuƙar burgeshi ya shiga shafawa yanajin wani irin ƙaunarta yana ratsa jini da tsokarshi,ranƙwafowa yayi daidai goshinta ya manna mata kyakkyawar sumba sannan ya miƙe murmushin da na kasa fassara na menene shimfiɗe saman fuskarshi.

Ruwan zafi Jay ya ɗaura mata sannan ya cika babban buta ya shiga yayo wankan tsarki.lokacinda ya fito ana ta ƙiraye ƙirayen sallar la’asar, dan haka jallabiya ya sanya ya wuce masallaci, ana idar da sallar kuwa bai ɓata lokaci ba ya dawo gida dan gaba ɗaya hankalinshi yana kanta,ruwa mai ɗan zafi ya haɗa mata zuwa bayi kafun ya koma ɗakin, har lokacin Maryama bacci ta ke yi ba alamar ma ta motsa hannu ya kai saman fuskarta yana cigaba da shafawa cike da nishaɗi bayan ya durkusa bisa guiwowinsa a bakin gadon, sannan cikin sassauta murya ya fara ƙiran sunanta, “Pretty!,Pretty!!”.

Buɗe jajayen idanuna na yi wanda suka min nauyi kaɗan na sauƙe su kan hamma jay dake durkushe a kasa hannunsa na yawo tsakanin kaina zuwa fuskata,ido ɗaya ya kanne min haɗi da cewa, “Barka da tashi my SWEET WIFE!”

Turo baki na yi gaba cikin muryata da bata fita mai kyau sakamakon baccin da nayi haɗi da ture hannunshi na ce, “Ni ba Sweet ba ce ba”.

Wani kayataccen murmushi ya yi yasa hannu kan dogon hancinta yaja kaɗan gami da faɗin, “Ke kinma fi sweet daɗi a wajena baby girl,ko in nuna maki ne practically?”ya faɗa yana miƙewa, haɗi da ɗaukata cadaƙ kamar yar baby,rufe idanuna na yi gam ina buga kirjinshi da hannayena biyu da faɗin, “Ni Allah bana so ka sauƙeni, wayyo innarmu, ni dai ka sauƙeni”.

Bai dire ni ko ina ba sai bayi, “in maki wankan ne my sweet?” ya faɗa cikin kunnena bayan ya ajiye ni, turasa na yi da ƙarfi har sauran kaɗan ya faɗi kasancewar abin ya zo masa unexpected amma ya yi ta maza ya coge gami da dafa bangon bayan gidan da hannu ɗaya,”ni dai ka fita banson ganinka kuma” na faɗa ina sinne kai ƙasa.

“Yanzu kuwa sahibar ruhina” ya faɗa yana ƙara matsoni, “Ki tabbatar kinyi harda ɗaya wankan fa,kin iya ai?,ko dai in koya miki yadda ake yi”. ya ƙare maganar da ɗan dariya cikin muryarshi.bugunshi na fara yi da hannuna duk ta inda na samu ina binshi hale da cewa, “Allah hamma jay bana so, nidai bana so”har saida na tabbatar ya bar bayin sannan na koma ciki na zauna,haka kawai naji wani murmushi ya suɓuce min wanda ban shirya masa ba,lumshe idanu nayi na buɗe ina tuno yanayin da na shiga ɗazu,
(Masu karatu kar kuga laifina, wato hamma jay na dabanne na tabbata ko a cikin maza shi ɗin Namiji ne.Duk sanda ya ke nuna min irin wannan soyayyar na kan manta da wani burina da mafarkina,shi kaɗai nake iya hanga da gani a duniyata).
Wanka na yi na soso gami da na tsarki,sai da na gama na tuna banzo da wani kaya ba kuma babu zanin wanka ko hijab a tattare dani rasa yadda zanyi in fita na yi dan haka na koma na tsaya cike da rashin sanin abinyi.

Yau ya shiga cikin rana mafi farin ciki a rayuwarshi fuskarshi cike da annuri ya koma ɗakin bayan ta koroshi daga toilet,saman three seater ya kwanta haɗi da ƙurawa ceiling ɗin ɗakin idanu na tsawon lokaci, lokaci lokaci yana sakin faffaɗan murmushi wanda ke ƙawata fuskarshi,tunawa da yayi cewa bata shiga da wani zani ba yasashi miƙewa da ɗan sauri ya shiga ya ɗaukar mata zanin da yasan tana wanka dashi gami da babban hijabin da ya gani kan pray mat nata.ba tare da knocking ba kawai Jabeer ya faɗa banɗakin, wani ƙara Maryama dake tsaye har lokacin ta sake tana kaiwa durƙushe da haɗe jikinta waje ɗaya. “Wayyo Allah na, ni dai ka fita,Innarmu kizo kice mashi ya fita ni dai banaso”.

Dariya ta bashi sosai dan haka ya dara abinshi, cikin son ƙara zolayarta ya ce, “Yauwa kinga na fi son ganin ta bayan dam…..”Kafun ya ƙarisa ta yi wani irin miƙewa a tamanin ta maƙale shi ta baya,,ƙanƙameshi ta yi ƙam tana sakin wani kuka da faɗin ita bataso ya fita.

“To pretty ta ina zan fita bayan kin maƙalƙaleni haka”. “ehh ni dai ka fita ko in haɗa ka da Daada”. juyi ɗaya ya yi ya kuma ɗaukarta cidak yana kareta da kayan dake hannunshi har ɗaki sannan ya ajiyeta, cukuikuye kayan tayi ba laifi ya ɗan rufe mata jiki kaɗan.dan haka ta juyo masa baya tana cuno baki gaba.

Rungumarta ya yi ta baya yana sako kanshi saitin kunnenta ya lumshe idanu yana shaƙar ƙamshin sabulun da tayi wanka dashi, cikin wani salo da ke nuna duk abin da zai faɗa daga cikin zuciyar shi zai fito ya ce, “Thank you for today wife, yadda kika faranta min kema ubangiji ya faranta miki daga yanzu har abada,”.da sauri na ja baya jin tsikar jikina tana tashi, bai yi yunƙurin bina ba ya ce yana kallon agogon dake manne ɗakin, “ki kimtsa da wuri zamuje gaida su Innarmu da kuma sallama da su Daada zasu koma gobe”.

“Da gaske ka ke hamma Jay?”.na faɗa da wani irin farin ciki.

“Da wasa nake Sweet wife”. cewar Jabeer yana mimicking muryarta,sannan ya ɗora da faɗin, ” ki hanzarta kar ki ɓata lokaci,.Gaban wardrobe namu ya tsaya gami da buɗewa ya zaro kayanshi jamfa da wando na wata farar shadda da ya ɗinka lokacin aure,palo ya fita yana ƙara tabbatar min in shirya kan lokaci.

Kasancewata ba mai son yawan kwalliya ba,mai na shafa nayi yan goge gogen turaruka a jikina haɗi da shafa lip balm saman lebena,duk da banyi kwalliya ba amma fuskata tayi wani washar da ita ɗan kumburan da ta yi saita bayar da wani sirrin kyau,da ɗan sauri sauri na ke shiryawa cikin atamfata orange colour dinkin riga da zani da ya matuƙar ƙawata jikina.abin sallah na shimfiɗa na gabatar da sallar la’asar da ta kubce min,tun ban idar ba nake jiyo muryar hamma jay yana sanar dani in fito ko ya shigo ya ɗaukeni, dan haka ko addu’ar kirki ban ba na zaro gyale na mai ɗan girma shima orange colour na yafa haɗe da ƙara feshe jikina da turare ban ɗauki jaka ba sai takalmata flat baƙaƙe da na saka kasancewata doguwa ban cika sanya takalmi masu tudu ba.

“Masha Allah” na furta lokacin da na tsaya gaban mirror ina ƙarewa kaina kallo ba ƙaramar kyau nayi ba, idan banyi kuskure ba harda wasu yan kumatu naga na fitar ga wani irin sheƙi da walƙiya da jikina ke yi.

Juyowa nayi da niyyar fita amma na yi turus ganin hamma jay da ya sauya kaya zuwa farar jampar da ya ɗauka tsaye bakin ƙofar shigowa ya yi folding hannayensa akan kirjinsa,fuskar shi ɗaure tamau ba bu alamar dariya.Ɗan muskutawa yayi yana zuba hannayenshi a aljihu gami da watso min wani kallon da ya kusa tsaida min gudunar jinin jikina ya ce, “Ina zakije a haka?” ya faɗa yana nuna ni da bakinsa daga kasa zuwa sama.

“Haan Hamma Jay shiryawa na yi fa zamutafi”.na faɗa tamkar zan fashe da kuka ganin yadda ya yi da fuskarshi lokacin tambayar.

“Canza kayan nan to, sannan ki tabbatar kin sanya hijab har ƙasa if not ba bu inda zaki bini”.

Fashewa na yi da kukan da nake ta riƙewa tunda ya fara maganar,matsoni ya yi sosai har muna shaƙar numfashin juna ya fitar da hannunsa daga aljihu yasa ya dago haɓata dashi,kallon cikin ido muka yiwa juna kafun inyi nasarar janye nawa idon zuwa ƙasa.

Cikin sanyin muryar da ba ko yaushe hamma jay ya ke magana da ita ba sai in abu ya taɓa zuciyarshi ya ce, “Maryama bazan amince maki fita a haka ba,kin buɗawa kanki turare,kin sanya mayafi mai bayyana jikinki…..” sai kuma ya yi shiru yana sauƙe wani irin ajiyar zuciya, a hankali ya kamo hannuna bayan ya sakar min fuska,cike da salo ya ke murza min tafin hannun yana kallona ya kuma cewa, “Pretty ina tsananin kishinki, sau tari nakanji tamkar in tsaga zuciyata in sanya ciki ko zan huta da yanayin da nake ji game da ke,pretty har kullum ina ji a raina da tabbatarwa ƙaunarki ce jarabtata,shin kin taɓa ganin inda aka ajiye zinariya tsirara? nasan baki taɓa gani ba, a auduga ake sanyata sannan sannan a adanata cikin akwatin ƙarfe mai tsananin tsaro kana a kefata a glass, iya wannan akwatin dake tabbatar da akwai zinariya a ciki ake iya hangowa ta cikin glass ɗin, to haka kike a wajena my wife, kin ma fi wannan zinariya daraja a idanuna, plsss and plsss love ki taimaka ki tayani adana kanki ba dan ni ba sai dan tarin ƙaunar da nake maki marar yankewa.” Jabeer ya kare yana mai sakin hannuna da juya min baya sakamakon kaɗawa da idanunshi sukayi jajur.

Da farko kukan taɓara na keyi,amma tun bayan da ya fara magana naji kukan gaske ne ke tahomin harda sheshsheƙa, sosai maganarshi da yadda ya yi ta cikin sanyin murya mai cike da rauni ya sanyaya min jiki na.Haka kawai na samu kaina da bin umarnin shi dan kuwa wardrobe na buɗe haɗe da fitar da babban jilbab nawa har ƙasa na sanya,juyowa ya yi yana sakin murmushi mai sanyi ganin yadda jilbab ɗin yai matuƙar karɓata fiye ma da gyalen, ” Ya salam!” Jabeer ya furta yana ɗaura hannu saman gashinsa gami da yamutsawa, “mu tafi to” na faɗa ina Allah Allah kar yace ya fasa,.

“Ki sanya nikaɓ” ya faɗa a can kasan maƙoshinsa, “kai dai hamma j… “.

Tun ban kai aya ba ya katse ni ta hanyat langwaɓar da kai gefe gami da sassauta murya ya ce, “Plssss mana wife”. komawa na yi bakin mazubin kayana ina jin wani irin haushi haushi a raina haka na fitar da niƙab ɗin na sanya, na kama zan ɗaure amma ya yi hanzarin riga ni kama igiyar yana ɗaure min ta baya cikin salon soyayya ya kamo hannuna ya sumbata cike da shauƙi ya ce, “You look so beautifull my love”. bai jira na ce komai ba ya kama hannun nawa muka fita,key ya sanyawa kofar palon sannan ya zare ya jefa a aljihunshi muka fita, kofar gidan kuwa kwado ya sanya mishi ya rufe gam sannan muka jera cike da sha’awa da burgewa muka nufi gidanmmu.

      ..........*******..........

Sake gwada layin Maryama a karo na ba adadi siyama ta yi amma still switch off ake sanar mata, lallai yarinyar nan ni zata rainawa hankali ba?, tabbas bata san waye siyama ba,nifa duk harkar da zata kawo man kudi komai hatsarinta sai nayi,ajiyar zuciya ta sauke tana tuna irin dukiyar da Sadeeq ke dashi matukar ta jefa wannan kyakkyawar Maryamar cikin rayuwarshi yadda ya kamata ba karamar ganima zata kwasa ba,sai akayi dacen tun batayi wani yunkuri ba shi da kanshi ya fada kaunar yarinyar gashi yanzu an mata aure,”what a lost?”siyama ta fada tana dafe goshinta da hannu biyu… ,yanzu haka dan shi ta canja layi tsabar yadda ya matsa mata da kira cikin sati dayan nan tun tana mashi karya har karyarta ya kare,.

Da hanzari ta daga wayarta ta tattaba kana ta karashi kunnenta,zuciyarta na tabbatar mata aikata abin da ke mata yawo a ciki.

“Barka da yammaci ranka ya dade,ka dade kayi kargo kayi shekaru irin na dabino Allah ya ja zamanin gagara badau mai ba yan maza tsoro.”Siyama ta fada cike da jinjinawa da karramawa.

Daga daya bangaren dan dukununun mutumin dake zaune bisa wani buzu da shirgegen carbi a hannunsa gefe kuma kasa ne mai laushi cike da wani tray da sauran tarkace irin na malaman tsubbu, dariya yayi mai fadin gaske sannan ya ce,” hajiya Siyama yau kin tuna damu kenan,kasuwar ne ta tsaya?ko bakin wasu kikeso a garkame maki?.” ya fada cikin amon muryarshi marar dadin sauraro.

“Ba ki daya yallabai,wato ina yarinyar dana kawo maka sunanta kwanan baya za’ai aiki a kanta nazo na fasa dinnan?na dawo yanzu inason muyi aikin amma zamu canza ba irin na farkon bane,”

“An gama hajiya, yanzu wani iri ne kike bukatar ayi?”.

Shiru Siyama ta yi cike da nazari kafun daga bisani tayi wani murmushi ta fara magana, tsawon mintuna shida tana maganar sannan ta yanke wayar gaba daya tana jin wani irin reliefe a ranta…..

Alhamdulillah summa Alhamdulillah.saura page daya mu gama Maryama book one, yayinda duk amsoshin tambayarmu zai kasance a book two.

And na yi making mind dina cewa book two din zai zama paid tunda nayi kokarina na ganin kuna bani kwarin guiwa ta hanyar sharhi amma abin ya gagara so yanzu zamu bude group normal da kuma vip, zan ringa kokarin yin update sau bakwai a sati a vip and 5times a week a normal group, idan nayi update sai in koma gefe insha shayi da burodi in kwanta babu ruwana da neman Data dan ganin sharhinku. Thankyou all my solid fanss ana mugun tare😘😘😘.

💫MARYAMA💫

   BY 


  UMMU FADEELA

TYPING📲

           EPISODE 39...

__________Da wani irin gudu na je na rungume Innarmu da ke faman dakan kalwa a tsakar gida ta hada uban zufa na fashe da kuka,da ace da ne ko kallon inda take bazan ba tsabar yadda na tsani wannan sana’ar ta innarmu, amma abin mamaki cikin ƙasa da kwana goma kawai da ban ganta ba wani irin azababben kewarta na ke yi.

“Ƙalau kike kuwa Maryama?” cewar Inna tana ƙoƙarin rabani da jikinta,ƙara rungumeta na yi ƙam cikin kuka na ce, “Na yi kewarku Innata,shi ne ko kije ki ganni kuma”.

Dariya Innarmu ta yi mai cike da farin ciki ta ce, “Tunda banje ba ba gashi ke kinzo inda nake ba”.

“Haaan waye wannan kuma haka?,ya zaka tsaya wa mutane haka sandandan aka kamar dogari?” cewar Daada dake shigowa gidan ɗauke da kaya niƙi niƙi a hannunta tayi arba da Jabeer dake tsaye hannuwanshi zube cikin aljihun rigarshi sai kallon Maryama da Innarmu ya ke cike da sha’awa,haka kawai ya samu kanshi da tuna mahaifiyarshi a yau ɗin.

Juyowa ya yi yana shafa kanshi haɗi da yin murmushi,ya ce, “Kai wannan tsohuwa kin cika jarabar tsiya, daga shigowa ko sallama babu kin fara yiwa mutane hayaniya a k….” kaga jaraba can kan ubanka Hassan da uwarka Dijah ba ni ba”.Kwalalo ido ya yi waje gami da faɗin, “Rufamin asiri in gama da duniya lafiya, me iyayena suka miki, a’a babu ruwansu gaskiya” ko kallonshi bata yiba ta wuce fuuu abinta,tsayawa tayi kusa da su Innarmu tana ƙarewa Maryama dake sanye da niƙab, baka ganin komai a fuskarta sai idanunta kallo, ta ce,” waye wannan kuma haka kamar an ɗaure ƙyanwa a baƙar leda?. wannan dai ba halin ƙwarai bane gaskiya,yo ko shi mai ahlari ma ai da ya tashi sanar mana inda yake al’aura a jikin mace ya ce, “ko ina na jikinta al’aurace amma banda fuska da tafin hannunta”,amma ke tsabar iyayi yar miji daɗi kin wani ƙaƙabawa fuskarki niƙabi kamar mai ɓoye muni,ku dai ku dinga yin gaskiya a al’amuranku wllh nidai ba ruwana.” bata basu daman bata amsa ba ta shige abin ta.

Innarmu da Maryama da tun shigowar Daada suka juyo suna saurarensu da Jabeer kafun ta sauƙe masu nasu rabon ta yafito Jabeer dake tsaye har lokacin baida niyyar karasowa fuskarta ɗauke da murmushi ta ce, “Babana tare kuke tafe ashe?sai kunyi haƙuri da daada fa dan shekaru sun ja sai an haɗa mata da uzuri,ƙarasowa ya yi cike da kunyar Innarmu da ya samu kanshi a ciki yanzun ya durƙusa kusa da ƙafarta ya ce, “Barka da yammaci Innarmu”.

“Barka ka dai babana ya hidima?” kara sunne kai kasa ya yi ba tare da ya ce komai ba.ganin baice ɗinba ya saata faɗin “Allah ya maku albarka baki ɗayanku,ku ƙarasa ciki ina zuwa”…

Ɗakin Innarmu suka shiga suka tadda ilahirin mutan nijar suna ciki sai haɗa manyan ghana must go suke na shirin komawa gobe wanda yawanci kaya ne yan kasuwan cikinsu irinsu inna lami suka sara a ciki dan komawa dashi nijar, ya ye niƙab nata Maryama ta yi suka gaggaisa sannan jabeer ya fita ya barta anan shikuma ya wuce wajen oga zubairu kafinta, duk da yau ba aiki zaiyi ba dan kayan dake jikinsa sai dai ya tayasu hira.

Zaune suke suna ta hira a ɗakin harda Innarmu da ta gama dakan kalwarta, yayinda Daada ke ta tsokanan Maryama wai ko tayi ciki ne daga aure sati ɗaya ta tsirar da wani uban kumatu da walkiyar da bata santa dashi ba,Inna lami ke shigar mata ita kuwa sai kumbura take tana cuno baki gaba,a ɓangaren innarmu kuwa wani irin daɗi ta ji da maganar na daada tare da addu’ar Allah yasa hakan ta kasance da sai ta fi kowa murna tuna irin shekarun da ta kwashe kafun ita Allah ya bata Maryamar.

Sallamar da Umaimah ta yi ne ya tsaida maganar da daada keyi,tana ɗaga labulen ɗakin Innarmu gami da shigowa ciki, a tsanake suka gaisa da mutan da ke ɗakin na kama hannunta muka tafi ɗakina dan ƙule nake da ita, ko zama ba muyi ba na kama ƙugu nace, “Idonki kenan Umaimah?shi ne ko ki ƙara waiwayata ko?wato duk abin da zai faru ma ya faru babu ruwanki ba?”.

Dariya Umaimah ta yi sosai tana kamo hannuna ta ce, “Relax mana amaryar hamma jay,ba gashi ke kinzo ba, kuma ki tambayi innarmu kullum ta Allah sai na zo gidannan kuma sai na tambayek….”

“Ban gane ba?baki san hanyan gidana bane da bazaki je ba, gaba ɗaya taku nawa ne daga nan zuwa gidan nawa fisabilillahi Umaima amma ki ka manta dani faa”.cewar Maryama tana katse Umaimah daga maganar da takayi.

“Uhmmm ashe kinyi gida amarsu” cewar umaimah tana dariyar shaƙiyanci,da jana zuwa kan gado muka zauna,sai a lokacin na tuna abin da na faɗa amma sai na fuske tamkar ban ji mi ta ce ba, itama fuskewar ta yi tana canza maganar da cewa, “So me labari?” ta ƙara yin ƙasa ƙasa da murya yadda ni kaɗai zan jiyota ta ce, “Nasan zuwa yanzu hamma jay ya gama cika aiki, ya lamarin yake ɗan bani labari mana,shin ya biki a hankali kuwa yadda nag…..”

Wani wawan marin da Maryama ta ɗago zata ba Umaimah ne yasata yin baya da sauri tana gimtse sauran maganarta haɗi da kwanciya saman gadon tana ƙyaƙyata dariya,zuwa can kuma ta yi shiru tana janyo filo ta matse a kirjinta ta ce, “Ohhh my dear yusuff ina kake ne.”

Cike da mamaki Maryama ke bin ta da kallo, ta rasa mi Umaimah ta gani a jikin wannan soloɓiyon yusuf ɗin da ta nace masa, ita dai tasan ko a ƙafa aka ɗaure mata shi zata cire ta gudu shi ba kyau ba shi ba kuɗi ba, kai ina impossible.hira suke ta yi irin na aminan da suka daɗe basu haɗu ba, yawanci hirar kuma Umaimah ke yi haɗi da zolayar Maryama,ƙiran sallar maghrib ne ya ɗaga su suka gabatar da sallar haɗi da cin shinkafa da miyar stew da yaji nama da Inna ta girka musamman dan Maryama,ba laifi kuwa dan ta ci sosai,rabonta da abinci tun breakfast na safe.Sallama suka yi da Umaimah ta koma gida da alƙawarin zata zo mata cikin satin nan su wuni Insha Allah.

Jabeer bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha,suka shigo tare da baffanmu suna ɗan tattaunawa sama sama akan aikin koyarwar da ya fara.abinci Innarmu ta zuba musu bayan sun zauna bisa babbar tabarmar da suka shimfiɗa a tsakar gidan kamar kullum,…Maryama ta fito tazo gaban baffa ta durƙusa gami da gaisheshi tana jin wani irin hawaye yana kawowa idanunta,amsawa ya yi cike da kulawa gami da faɗin “Allah ya maku albarka mamana”. sun daɗe suna tattaunawa har misalin karfe takwas da rabi sannan baffanmu ya ce su tafi hakannan dare ya yi,nan fa ake yinta domin kuka Maryama ta sanya wai ita bazata bishi ba, sai da ƙyar da suɗin goshi baffa ya rarrasheta suka tafi tana ta sauƙe ajiyar zuciya da alƙawarin gobe da asuba zasu zo raka su daada zuwa park….

Hannuna Hamma Jay ya kama bayan mun iso gida har kan kujerar mai zaman mutum uku, zama ya yi sannan ya janyo ni saman cinyarsa ya zagaye waist ɗina da hannunshi guda, ɗaya hannun ya sa yana share min hawayen dake cigaba da gangaro min saman fuskata har lokacin ba tare da ya ce komai ba,a hankali ya gangara da yatsar shi saman lips nawa ya fara shafawa yayinda idanunshi ke cigaba da rinewa,ƙoƙarin tashi na fara inajin kukan na komawa amma ya ƙara damƙeni da kyau, da wata iriyar murya yana ƙara matsoni ya ce, “Plssss wife! ki yi haƙuri da ni, i know that tun ba muyi aure ba sai kin jure da yanayi na, nasan ni ɗin mai yaw….” Bai ƙarasa ba ya haɗe bakinshi da na nata ya shiga aika mata zazzafan saƙonni…(Ni dai jan ƙafata na yi na bar musu ɗakin ina tambayar kaina shi kam baya gajiya ne?)…

   *********----------**********.

A hakali ta buɗe idanunta ta sauƙe su kan Mommy dake zaune kan stool dake gaban dressing mirror ta zabga tagumi, “Mommy” ta faɗa cikin murya ƙasa ƙasa,da wani irin sauri mommy ta taso har kujerar da take kai yana ƙoƙarin faɗar da ita ta hayo gadon tana kama hannun Khadija haɗi da shafa kanta cike da tausayawa ta ce, “Sannu dota na,ina ke maki ciwo yanzu?.

“Babu ko ina Mommy, kawai zan sha ruwa”.sauƙa gadon tayi ta buɗe karamin fridge dake ɗakin ta ɗauko ruwan haɗi da zubawa a cup ta dawo gareta ɗaga kanta tayi ta bata a baki sosai ta sha ruwan saida ya ƙare ta koma ta kwantar da kanta tana lumshe idanu.

“Sorry dear!tabbas Man zaisan ni na haifeshi ba shi ya haifeni ba, shi har ya isa ya ga tsabar idona yaceman wata can yar talakawan da suka kasa sata even school yake SO ba ke ba,lallai duk wacce ya yi gangancin shigar da ita cikin rayuwar mu da sunan aure ba ke ba tabbas sai ta gwammaci ɓarin cikinta uwarta tayi akan haifota duniya har ta san ɗana,ke kaɗaice matar Man kima dake zai zauna har gaba da abada idan ya nuna min taurin kai kuma wallahi wallahi kap zuriyar su yarinyar zan kulle sannan shikuma ba abin da zai hana in…….”

Da sauri Khadija ta rufe bakin Mummy da hannunta tana girgiza kai hawaye na tseren gudu saman kumatunta.

“No Mommy,don’t do such, wannan ba halinki bane,tunda ya ce bai sona to bai sona ɗinne da gaske, ki barshi ya auri zaɓin zuciyarshi,ko kin takura ya aureni ma daga ƙarshe zumuncin da ake son ya yi kyau ne zai ɓaci, ki barshi kawai Mom,ki barshi kawai” ta faɗa tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.sosai tayi kuka sannan ta cigaba da faɗin, “wannan shine tawa kaddarar mom, SON MASO WANI, da daɗewa nasan yaya Sadeeq bai sona amma na dagewa zuciyata cewa with time zai canza amm…..” wani kukanne yaci karfinta, tana share hawaye ta ce, just leave him mom, leave him ya auri wacce ya ke so,matuƙar zai yi farin ciki da ita ki barshi wannan shine asalin so wllh zan tayashi ƙaunarta.” Kai da kaga yanayinta kasan she’s hurting inside, kawai ƴarfin hali ta ke yi.

Rungumeta mommy ta yi ta ce, iam giving you my word Khadija bazan canza akan abin da na faɗa ba, wllhi Allah ɗaya kenan duk wacce man ya kawo gidan nan da sunan aure sai ta gwammaci mutuwarta akan rayuwarta, ke nake so ya aura, ke ɗin amanata ce, ke ɗaya tilo nake gani in tuna gaba ɗaya iyayena da sauran yan uwana da na rasa sanadiyar hatsari, ƙanwata khadija kawai Allah ya barmin bata yi waccan tafiyar mai cike da tashin hankali ba saboda cikinki dake jikinta, koda ta haifeki kuwa bata shayar dake na sati biyu ba itama Allah ya amshi abin shi, taya zan maki riƙon sakainan kashi Khadija? dole in haɗaku aure da tilon ɗan da na mallaka a wannan duniyar ku haifo mana wasu zuriya masu albarka,” share hawaye masu zafi mommy ta yi tana shafa bayan Khadija dake kwance lamo a jikinta sai sheshsheƙa ta ke yi, ta cigaba da faɗin, ba dai ya gudu ba, inace ba ƙasar ya bari ba,?zan wanke ƙafata inje har can wajen aikin nashi ai ba baƙona bane zai san uwa uwace. Yanzu ta shi muje in kaiki hospital dan sau biyu dr, yana zuwa kina bacci.”

Cikin shagwaɓa Khadija ta dafe kanta dake sara mata ta ce, “Mommy Allah ba inda ke mani ciwo fa, kawai ki barshi sai dare, ta faɗa tana komawa ta kwanta saman gadon haɗi da lumshe ido, are sure dota?”

“Sure Mom, i just want to freshen up” cewar khadija.

“Ohk bari in haɗa maki ruwa to”. bayi mommy ta shige ta cika mata ruwa a baho daidai yadda zata ji daɗinsa sannan ta fito tana kamata.

“Zan iya faaa” ta faɗa tana ƙarfin halin miƙewa ita kaɗai ta wuce bathroom ɗin kamar zata faɗi,saida Khadija ta shiga ruwan ta daidaita kanta,sannan ta samu kanta da fashewa da wani irin kuka gami da toshe bakinta da hannuwanta duka biyu..tsawon lokaci ta kwashe a bathroom ɗin tana kuka har saida taji tamkar zata shiɗe kamun ta canza ruwa ta ɗauraye jikinta ba tare da tayi using soap da spounge ba.fitowa tayi daure da babban towel,ganin babu mommy a palon ta fada saman gado ta lulluba da duvet nata.

   ..............'''''''''''''''''''''...............

Da hanzari siyama ta kimtsa dan amsa kiran da aka mata a ranta tana fadin ba’a bori da sanyin jiki,da dan hanzari ta zari yalolon mayafinta mai kama da abin tatar kamu ta yafa hadi da daukar jakarta ta rataya ta bar gidan.

Zaune take gaban mutumin wanda kai tsaye bazamu kirashi boka ba dan yafi kama da malaman zaure duba da irin tarkacen dake dakin nasa na aiki,abin da ke hannunshi ya mika mata ya cigaba da fadin, “ki tabbata kin sanya wannan karkashin harshenki kamun ki mata magana, ina tabbatar maki idan kika aikata haka ko wuta kikace ta shiga bazata maki musu ba”.

Cike da murna Siyama ta karbi dan karamin layar da ya mika mata tana juya shi fuskarta dauke da farin ciki, ta zaro wasu kudade masu auki daga jakarta ta mika mishi tana godiya ta bar gidan, abinda ya rage mata kawai yadda za’ayi ta je gidan Maryama dan harga Allah tsoron haduwarta da jabeer take dan tsab zai iya guntule mata kafafu ba mutunci ne da shi ba.

Kwanaki uku Siyama ta kwashe tana jiran jin kira daga wanda tasa aikin leken asiri, don haka yanzu da taga kira da layinshi ba karamin dadi ta ji ba,kara wayar tayi a kunnenta cike da zakuwa, daga daya bangaren yaron dake makale jikin wani lungu ya ce, “Hajiya mutumin naki ya fita fa,kuma da alama zai juma dan haka kiyi gaggawan zuw..”

Ba tare da ta jira jin karshen maganar ba ta yanke kiran tana ganin agogo wanda ya nuna mata karfe bakwai da mintuna arba’in na safiya,hijab kawai ta saka har kasa kamar mutuniyar kirki ba tare da ta bi takan wanka ba ta suri jakarta tayi gaba, mamarta na tsaida ita ta yi breakfast ma ko kulata batayi ba.

Yau na tashi bana jin dadin jikina gabadaya kasusuwana ina jin tamkar ana kwankwasa min su dan haka ko dan sharar da nake yi kwana biyun nan ban ba hamma jay ne ya yi komai na gidan sannan ya shirya ya tafi inda yake aiki, shayi kawai na iya sha dan haka tun fitarshi nake kwance saman doguwar kujera kamar kayan wanki,cikin wannan halin ne naji ana sallama a tsakar gida kamar da muryar siyama, da kyar na mike daga kwancen da nake inajin zuciyata na bugawa da sauri sauri nayi karfin halin amsawa,labulen palon ta daga gami da shigowa fuskarta dauke da murmushi, cike da zolaya ta ce, amarya bakya laifi, gaba daya kin manta damu kina nan kina kurbar romon dimokoradiyar soyayya abinki.

Dariya ta bani sosai, dan haka na saki murmushi na ce, “wace ni in manta dake Siyama,kawai dai al’amuranne suka zo a haka amma wallahi kina makale a raina,ki zauna mana?” na fada ina nuna mata kujera, babu musu kuwa ta zauna harda daura kafa daya kan daya tana taunar cingam kas kas, ta ce, “yanzu wannan akurkin gidan aka kawoki Maryama?,duk wannan kyawun a wannan gidan zai kare kenan?”

Wani irin abu naji ya soki kirjina da ban gama tantance menene ba, “Hmmm” kawai na ce ina mikewa da kyar hadi da kokarin boye hawayen da suka cika min ido na ce “bari in kawo maki ruwa Siyama”.Wani irin zaro ido Siyama ta yi tana bin Maryama da bata san tanayi ba kallo har ta bacewa ganinta.

Da sauri ta zaro layarta dake cikin jaka ta makala shi kasan harshenta ta yi gum.

“Dauke da ruwa cike da jug da kuma cup guda biyu bisa tray Maryama ta shigo hadi da dire su gaban Siyama ta ce, “Bissimillah ga ruwa”.

Da kallo Siyama ta bi ruwan sannan ta dago suka hada idanu da ita tana yamutsa fuska ta ce, “Yanzu fisabilillahi kina amarya amma ko dan ruwan leda baza’a ajiye maki ba balle na gora, sai dai ki kare a ruwan randa? a gida kisha na randa a gidan aure ma kisha na randa? kai ina, gaskiya maryama da sake a rayuwarki,bansan sanda na fashe da kuka ba dan a take naji zuciyata tamin bakikirin, nace, “to ni yanzu ya zanyi?”.

“Ba yadda zakiyi Maryama sai hakuri ni yanzu bama wannan ya kawoni ba, Oga Sadeeq ya takurani da kira wai lallai lallai sai na hadaki dashi.” Cewar siyama tana fitar da wayarta daga jaka.

Zaro ido nayi ina dafe kirji na ce, “Sadeeq kuma Siyama? shikenan kin kashe ni, kin sanar masa an min aure ne?” ba tare da ta bani amsa ba naga tana miko min waya hadi da fadin “karbi kuyi magana,”

Haka kawai na samu kaina da kasa yi mata musu ma sa hannu na karba hadi da kara wayar a kunnena cikin sanyin murya na ce, “Salamu alaikum”.Daga daya bangare Sadeeq ya lumshe idanu yana jin wani abu marar fassarawa yana mishi yawo a jikinsa, cikin kamilalliyar murya yace, ” Pretty!is this you?”.

Hakan kuma ya yi dai dai da shigowar Jabeer gidan yana sallama sakamakon kasa nutsuwa da yayi a makaranta tuna yadda ya bar maryama a kwance……

Idan Allah ya kaimu gobe zamu gama book one Insha Allah, duk mai bukatan a dama dashi a book two zai biya naira 300#kacal dan shiga Normal group, posting sau biyar a sati banda weekends ko naira 500# kacal for VIP group, group update everyday…Zaku biya ta acc👉0056115042, Asma’u Isa. Unity bank. Sai ku tura evidence of payment ta 08104875999. Sai na jiku manyan mata.Thankyou all…

💫MARYAMA💫

By

Ummu Fadeela

Typing📲

Episode 40.

END OF BOOK ONE

Let say something about yesterdays episode kafun mu ɗora…nasan da yawanmu zamuce asirin Siyama ya kama Maryama, well,kar mu manta da waye Maryama da irin rayuwarta da tunaninta tun tasowarta,wanda shine ma dalilin da ya sa ta kai kanta wajen Siyama inda ita kuma tayi amfani da damarta wajen cimma wani buri nata itama,kunsan yadda rayuwa take yanzu yawanci mutane basa taimako dan Allah,sai sun duba idan na taimakeka ni kuma wani riba zan samu,hakance ta kasance tsakaninsu, musamman da ya zamo taimakon da Maryama ta je nema totally ya sauƙa daga tsarin yarinyar kirki.. ,kasancewar ɗan canjin da aka samu a zamanta da Jabeer kuma ba shi ke nuna tayi hankali ba, a’a ta yiwu wani dalili ne can na daban wanda ke ɓoye, so for me, ina ganin asirin ya samu halinta ne, thou an ce tsafi gaskiyan mai shi.Allah ya sa mu dace, muje zuwa my guys dan jin yadda za’a warware zaren da aka saƙa tun farkon labarin…

____________Tun fitar shi gidan da halin rashin lafiyar da ya barta a ciki sai hankalinshi ya kasa kwanciya,hakan yasa yana kammala period a school da shike English yake ɗauka kuma shine first period, sai ya nemi excuse ya dawo gida, kasancewar cikin kwana biyun akwai ɗan jituwa a tsakaninsu dan ta ɗan rage tsoronshi,hakan ba ƙaramin daɗi yake mashi ba,har ya ɗan fara farfaɗowa daga ramar da ya fara a kwanakin farko na auren nasu.

Da sallama ya shigo gidan…Hakan kuwa ya yi daidai da amsa ƙiran da Maryama ta yi na Sadeeq har yana tambayarta, “Pretty! is this you?”.

A matuƙar firgice Siyama ta miƙe jikinta na maƙyarƙyata,sai dai abin da bata sani ba shi ne Maryama ta fita razana dan ita sumar zaune ta yi a inda take ko miƙewar ta kasa, da ace za’a tsaga jikinta a lokacin ta tabbata baza’a samu ko ɗigon jini ba.a ɓangare guda kuma Sadeeq na ta faman faɗin “Hello,hello” amma no respond.

Kamar wacce aka yiwa alluran ƙarfi ta miƙe da sauri har tana tuntuɓe ta kamo hannun Siyama dake tsaye a wajen tamkar statue kana ta rarumi jakarta fitt suka shige bedroom ɗin.

Wardrobe ɗinta ta buɗe gefen da babu kaya ta tura Siyama ciki haɗi da tura mata jakarta,duk kuwa da ya mata kaɗan amma haka ta takure jikinta ta shige tana ta zaro idanu kamar ɓera a cikin gari,take ta fara haɗa wani uban zufa numfashinta na ɗaukewa lokacinda Maryama ta tura marfin wardrobe ɗin gami da rufewa kiribb babu ta inda ɗan adam zai shaƙi numfashi.
(Wayyo Siyama ke dai kullum haɗuwar ki da Maryama bata zuwar maki da daɗi😢)

Maryama na sanya kai da shirin fitowa shikuma yana ƙoƙarin fitowa,dan haka sukayi karo,a rikice take har bata kallon gabanta, kallo ɗaya zaka fahimci tabbas babu nutsuwa a tattare da ita.riƙo hannunta ya yi da niyyan su shiga ɗakin amma sai ita ta janyo nashi hannun zuwa palo,sosai hakan ya bashi mamaki amma sai bai nuna ba ya bita kamar raƙumi da akala,a tsakar palon ya tsaya haɗi da janyota ya rungumeta ta baya yana shafa hannayenta da suke da ɗumi kaɗan kaɗan alamar tana jin zazzaɓi. “Wife ya jikin naki,?tunanin halin da na barki ya hana zuciyata nutsuwa gami da koyar da ɗalibaina yadda ya kamata,ko dai mu tafi asibiti ne?”.Ya karishe yana shafo wuyata.

“Am,ehm, ehh, a’a ” birkitota ya yi da sauri suna fuskantan juna kallon cikin ido ya mata duk ƙoƙarin da tayi dan janye nata idanun kasawa tayi,babu abin da Jabeer ke hangowa cikin idonta sai tsananin tsoro,tsoro mai tsananin gaske. “Wife!are you okay?.” Jabeer ya yi tambayar yana ɗan jijjiga shoulder ɗinta.”Mai ke damunki duk kin birkice haka?” ya faɗa yana kai dubanshi da ƙarewa palon kallo.

Da ƙyar ta yi gathering courage ta ce,”Babu komai fa,kawai dama.. am.. shi..ƙyanƙyaso,eh yauwa ƙyanƙyaso na gani ina bacci a nan ya hau min jikina faa”. sai kawai ta fashe masa da kuka.

Rikicewa ya yi sosai yana haɗata da jikinshi ya matse gam haɗi da sauƙe ajiyar zuciya ya ce, “Sorry wife,ƙyanƙyason nan bai kyauta mana ba, amma duk inda ya shiga yau a tsakanin bedroom da palon nan sai na fitar dashi na kashe shi yanzun nan ma kuwa,dan ya shiga hurumin da ba nashi ba, ni kaɗai ke da hurumin taɓa jikinki dan haka dole in hukuntashi daidai da laifinsa, and da yamma zan siyo mana dettol da izal mu zuba musu a toilet ɗin dan nasan daga can zasu shigo mana nan,” ya faɗa gami da sakin maryama ya juya zai shiga bedroom ɗin dan neman kyankyaso.

Zaro ido nayi ina dafe kirji, da wani irin speed na bishi banyi wani tunani ba na damqe shi ta baya na sanya hannuna duka biyu saman kirjinsa ina sakin wani kukan da wannan karon na shagwaɓa ne.

Cakkk Jabeer ya tsaya yana sauƙe wani irin ajiyar zuciya mai nauyi kafun ya yi ƙarfin halin cewa, “Pretty bari in nemo shi mana dan kar ya ƙara hawar miki jiki.”

“To ai na riga da na kashe shi tun dazun da tsintsiya na fitar dashi ma waje na jefar kuma tun a lokacin ƙaɗangare ya cinye,” na faɗa ina ƙoƙarin saisaita nutsuwata.

“Sure?” ya tambayeni bayan ya juyo yana ɗaga min gira.

Gyaɗa mashi kai kawai nayi, amma deep down zuciyata tsalle take yi tamkar zata tsinke ta faɗo ƙasa, “So ya jikinnaki?” kin hana ni zama a school da tunaninki.”

Cikin turo baki gaba nace “Nikam lafiyata qalau ka zo ka koma kar a nemeka, na riga da na warke,” “Hmm ban yadda ba korata kike son yi da wayo kawai wife”.Jabeer ya faɗa yana lakace hancina da yatsarshi.

“Da gaske Hamma Jay na warke faa Allah ka koma kar a nemeka”,

“Ohk zan koma amma sai kin bani wani abu mai daɗi wanda zan yi ta tunawa dashi a can”.

“To ni mai nake da shi wanda zan baka, gashi Innarmu bata turo abincin rana ba” na faɗa ina turo baki gaba, bakin nawa yake kallo cike da sha’awa, kafun cikin nutsuwa ya ɗaura yatsarshi saman leɓena kamar yadda ya saba ya fara zagaye leɓen kamar mai tafiyar tsutsa still yana kallon cikin idona, bakinsa ya kawo daidai nawa a hankali ya furta, ” wannan yafi min abinci daɗi” kamun in ankara ya bani wani sassanyan sumba a lokaci ɗaya idanunsa suna sauya kamanni.bai ƙara cewa komai ba ya juya da sassarfa har ya iso ƙofa kuma sai ya tsaya yana kallon tiren da na kawowa siyama ruwa dashi, da ido ya tambayeni “wannan fa?”.

Da sauri na dawo daga suman tsayen da nayi na ce, “maƙwafta ne suka shigo min da na kawo masu ruwa shine ban fitar ba”.

Yana shafa gashin kanshi ya ce, “Ya kamata mu samu ruwan leda wanda zaki ringa bawa baƙi idan sunzo ko?”.

Bance komai ba sai Allah Allah nake ya tafi,shima bai ƙara cewa komai ba ya sa kai ya fice yana ƙara jaddada min cewa in kula da kaina.na kusan minti uku tsaye a wajen bayan fitarshi sannan na yi ƙarfin halin fita da sauri na sanya sakata a asalin ƙofar shigowa gidan na dawo, a bakin kofar palo na ga takalman siyama,Alhmdllh na furta ganin hankalinshi baikai kansu ba, da hanzari na afka ɗakin na buɗe wardrobe ɗina jiki na rawa,gajab Siyama ta fado kasa tana zabga wani irin tari yayinda idanunta ke ƙwalalowa waje suna kakkafewa, jikinta kuwa kai kace a kogi aka tsundumata tsabar yadda ta jiƙe gajab da gumi.Ruwa ruwa,shine abin da ta ke ta ambata a tamanin na koma palon,wannan ruwan dai da ta gama yi man izgili a kanshi, shona tsiyayo cikin kofi na ɗaura bisa bakinta, cikin sakan ɗaya kuwa ta shanye tas tamkar zakanyar da ta shekara bata sha ruwa ba, hijab nata na zare mata haɗi da fara yi mata firfita da shi..

Kusan mintuna talatin sannan Siyama ta dawo hayyacinta,duk da haka dai tana bukatar hutu dan haka bance mata komai ba kamar yadda bata ce man komai ba da ƙyar ta lallaɓa muka dawo palo,hasken da wayarta ke ta faman yi ne yasata ɗagowa tana jingina da jikin kujerar da take zaune a kai, tana miƙomin wayar bayan ta yi picking gami da sanyashi handsfree ta ce, “Oga Sadeeq”.

Hannu na rawa na karɓa ina karawa a kinnena ba tare da nace komai ba amma zuciyata bugu ta ke sosai tamkar ana surfa masara a turmin daka Hamma jay ne ke min gizo a idanuna, ina da ilimi na san cewa hakan is haram, amma na rasa dalilin da ya sa na kasa ƙin amsar wayar, daga ɓangarenshi ya ce, “Oh baby girl you want to kill me right?.” zaro ido nayi na ce, “mai yasa kace haka?, “

Lumshe idanu ya yi ya ce, “Just forget it,bazaki fahimta yanzu ba sai kin ɗan ƙara girma,now you’re a small baby,na fi son sai kin kammala degree na ki by then kin ɗan ƙara girma kaɗan,atleast idan na faɗi maki abin da ke raina bazaki min yarinta ba.” ya fada in a naughty way. “hmmm” kawai na faɗa ina jina tamkar wata sabuwar hallita a doron ƙasa. Cigaba ya yi da faɗin,

“Munyi maganar makarantar ki da Siyama, ta ce parents naki sun amince dan haka na tura mata jamb registration fee naki, dan haka sai kuje kuyi register dan kar lokaci ya ƙure and kiyi ƙoƙari kar ki bani kunya plsss,,amma kafun nan inason ki turamin layin dad naki za muyi magana dashi.”

Zaro ido nayi a lokaci guda kuma ƴawun bakina ya kafe ƙam, dan haka na kasa buɗe bakin bare har in bashi amsa.

“Ki ce mashi babanki bai nan idan ya dawo zaki hadasu”. Siyama dake saurarenmu tun fara wayar tamu ta faɗa ƙasa ƙasa yadda ni kaɗai zan iya jiyota.hakan ko na faɗa mishi,baice komai ba sai jaddada min da yayi cewa da zarar ya dawo in haɗasu dan magana mai muhimmanci zasuyi.

Mun kwashe wani minti talatin ɗin muna hira da Sadeeq,tun ina amsa masa da eh a’a, har dai na sake na manta da yanayin da nake ciki na cigaba da cin amanar hamma jay ta hanyar hira da wani ƙato da ba muharramina ba har ina ƙyaƙyata dariya.haɗe hannaye siyama ta yi cikin juna ta ɗaura habarta bisa hannayen tana ta kallona yayinda abubuwa dayawa ke bijiro mata a kai tana ta murmushi.da ƙyar ya yanke ƙiran bayan munyi sallama.a wajen muka hau tattauna yadda za’ayi in samu fita har muje muyi registern jamb ɗin ba tare da an samu akasi hamma jay ya sani ba…mun yanke shawara kan cewa idan ya fita aiki ranar litinin tunda sai ƙarfe biyu wataran yake dawowa zata zo da wuri ta ɗaukeni muje mu dawo tun bai taso daga makarantar ba.


Hakan ko akayi kwanci tashi asarar mai rai,ranar litinin misalin ƙarfe takwas da rabi Siyama ta zo min, dama na shirya tun wajen takwas da hamma jay ya fita a gidan dan yau fitar wuri ya yi,dama shiya dafa mana shayi ya sayi bread da madara da ƙosai da shi muka karya dan zazzaɓin da na kwana dashi, gashi ya dakatar da innarmu turo mana abinci tun kwanaki huɗu da suka wuce shi ke dafamana a nan gidan watarana kuwa takeaway yake yo mana,dan haka ta na isowa bamu ɓata lokaci ba na sanya hijab tare da nikaɓ muka wuce bayan na kulle gidan da ƙwaɗo,ba mu wani ɓata lokaci ba acan ɗinma muka kammala muka dawo sai jiran ranar rubutawa,ina ta godewa Allah, Hamma Jay bai dawo ba, a ɗaya ɓangaren kuwa wani irin farin ciki nake ji marar misaltuwa zan cika burina na tafiya jami’a, sai dai tambayar da nake yawan yiwa kaina shine ‘ta yaya zan tafi makarantar?”.(nima dai nace ta ya MARYAMA?).
*
Haka muke ta gurgura rayuwar da kullum kwanakinmu ke raguwa aiyukkan zuciya mabanbanta kama da ga na sharri haɗe da na alkhairi suke wanzuwa a bayan ƙasa,a cikin yan kwanakin da na zauna jiran ranar jarabawar abubuwa da yawa sun faru, ciki har da cikar wata ɗaya da samun aikin hamma jay yayinda aurenmmu ke cika wata ɗaya da kwana biyu, sai dai abin takaicin shine, wata ɗayar ta ƙare ba tare da an biya malaman primary albashi ba, kowa dai yasan yadda aka rena ma’aikatan ƙananan hukumomi a ƙasar nan,to hakance ta kasance dan haka abubuwa sun mana tsauri kaɗan,dama rufin asirin abincin da innarmu ke kawowa ne tinda ya hana kuma ɗan kayan garan da aka min shine muke ta ci har i zuwa yanzu da al’amuran ke taɓarɓarewa,da ka ga hamma jay kasan yana cikin damuwa amma babu wanda yake iya faɗawa,wurin aikinsu kuma ba wani abin arziƙi ake samu a can ba dama, babbar damuwar shi shine yaso yayi suprising Maryama da salary ɗinshi na farko ta hanyar yi mata registern jamb ya kuma sai mata waya ko da ko yar ƙaramace, baijin daɗin yadda take zaune haka babu waya,amma abin ya faskara and lokacin yi registern har ya wuce, ya so ace ya cika alkawarin da ya ɗaukar mata, sai gashi abincin da zai ajiye a gida ma yana neman gagararshi, don haka a yan kwanakin kullum da jan ido yake dawowa gidan na aiyukan wahalar da yake zuwa yi duk don ya samo mata abin da zata ci mai daɗi ko da ko shi bai ci ba..

Maryama kuwa a yan kwanakin sharafin soyayya take sha ita da Sadeeq ɗinta thou bai fito fili ya bayyana mata yana sonta ba amma idan suna waya mantawa take ita matar aurece ya yinda shima yake mance cewa bai sanar mata yana sonta ba,kullum ƙarfe tara na safe yake ƙiranta kamar yadda ta bashi time wato in jabeer ya tafi makaranta, sai kuma ƙarfe huɗu, ida jabeer ya dawo ya yi shirin ya tafi neman gumin halak,nan suke baje kolin hirarsu abin ba’a cewa komai, itama siyama tana can tana ta bada ƙaimi wajen zuga Maryama da cewa ita ba kalan matar da za’a fita daƙo sannan a ciyar da ita bane,ita matar hutu ce,zugi dai kala kala,sosai kuma hakan ke tasiri a rayuwar gidan nasu dan ɗan kulawar da yake samu a da sam yanzu bata bashi fuska,idan ya zaunar da ita da nufin suyi magana sai ta hau shi da masifa tamkar ɗanta tun bata iya fitowa fili ta faɗi abin da ke ranta har ta kai ga Maryama ta dubi tsakiyar idanun Jabeer ta ce masa , “Ni ba kalan matar talaka bace da sai ya fita ya nemo sannan ya ciyar dani ba, ni matar manya ce”.

Waɗannan maganganu sun daki jabeer sosai har ta kai ga bayan kwana biyu saida ya ziyarci asibiti dan ganin likitan da ya ke bashi magani lokaci lokaci,sai yanzu ya fahimta, sai yanzu abubuwan da suka yi ta faruwa a baya kafun aurensu ya ke dawo masa dalla dallah a cikin kai tare da auna komai akan mizani,sai dai hakan bai hanashi cigaba da nema ba dan ya ciyar da ita da kuma sauran buƙatun ta,haka kuma bai rage koda kaso ɗaya cikin dari na tarim soyayyar da yake mata ba.sai dai duk sadda ya tuna da kalamanta sai ya rumtse idanu tsabar yadda suke sukarshi, cikin lokaci kaɗan Jabeer ya bushe kamar wanda ya yi shekara yana jinya, sosai hankalin Innarmu ke tashi idan ta ganshi, sai dai tambayan duniya ta mashi akan abinda ke damunshi amsar dai ɗaya ce, “babu komai innarmu yanayi ne kawai”).ba don ta yarda ba, sai dai kawai ta bishi da addu’a da kuma nasiha irinta iyaye masu ƙaunar ƴaƴansu.tabbas jinyar zuciya wani lokacin tafi ta zahiri..

        ******

Yau muke rubuta jamb,dan haka hamma jay yana fita nima na shirya yau ni naje wajen Siyama ba ita tazo ba muka rankaya centern da zan yi jarabawar, ..cike da farin ciki na rungumi siyama bayan na fito a jarabawar da ta ɗauke ni 2hrs cikin murna na ce, “Siyama wallahi ba bu wani wahala gaba ɗaya na amsa tambayoyin har ma da ƙari Insha Allahu zanyi nasara,haɗe rai siyama tayi tamau tana jin wani irin haushin Maryama mai haɗe da hassada, amma sai tayi saurin ɗagata tana ƙaƙalo fara’a gami da bubbuga bayanta tace “Insha Allah”.

Bayan sati biyu sakamakon jarabawarmu ta fito a cikin wannan sati biyun sosai hamma jay ke haƙuri da ni dan ba ƙaramar wahala nake bashi ba, ko ɗan yatsata na daina yadda ya taɓa,gaba ɗaya ya koɗe ya fice a hayyacinsa…haka yau ma na fita ba tare da izini ba na fita nida siyama zuwa cafe dan duba result ɗin. Alhmdllh na samu nasara fiye ma da points ɗin da ake buƙata, tun acan Siyama ta sanar da Sadeeq abin da ke faruwa cike da ƙwarƙwasar da ban san ta iya shiba,sosai ya tayani murna da sanar min da zaran admission ɗina ya fito zai sanar min,dama university of portharcourt Siyama ta cike min a first choice, ko da na tambayeta dalili mai yasa bazan nema a arewa ba sai ta ce,a can zan fi nutsuwa in yi karatu tunda babu wanda na sani sai Sadeeq a can and shikuma je’s busy with his work dan haka zanyi karatu na cikin salama.And that’s the begining of everything.da ya samu rayuwata…Da cikin farin ciki muka kamo hanyar gida ina cike da ɗoki,tunga siyama taja ta tsaya a inda suka sauƙa daga keke napeep ɗin daya dawor dasu tana kallon maryama da ta marairaice murya tana tambayarta, “Yanzu Siyama yaua zanyi im sanar da hamma jay na yi jarabawar jamb har na samu nasara?”.

Ɗan ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta matso dai dai kunnena ta fara magana ta yadda ni kaɗai zan jita,… zaro ido na yi kirjima ya bada wani irin sauti darrraammmm har saida na kusa faɗuwa kasa jin abin da siyama ta faɗa, girgiza mata kai kawai nake hawaye na silalo min cikin kuka nace , “Ina Siyama bazan iya aikata wannan ba,Hamma Jay ne fa? ina sam bazan iya ba”.

“To shikenan tunda bazaki iya ba, sai kije ki zauna da hamma jay ɗin muga idan zai iya biya maki ki cigaba da karatun sannan kin san tabbas kina karkashin wani kuma Sadeeq bazai biya maki makaranta ba, so go and think before lokaci ya ƙure maki, ba tare da ta ƙara ko kallona ba ta wuce abinta.

Da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata zuwa gida, wata sabuwar faɗuwar gaba ce ta sameni ganin kofar gidan a buɗe bayan na rufe kamun in fita, da jan ƙafa na ƙarasa shiga har cikin palon, tunda nayi arba da takalmin jay a bakin kofa yawun bakina ya kafe, amma sai na aro jarumta na yafa ina ɗaure fuska maganganun siyama nayi min yawo a kai…

Kwance yake kan doguwar kujera sanye da jallabiya,rigingine idanunshi a lumshe yana ya ɗaura hannu ɗaya saman kashi ɗaya kuma ya ɗaure saitin zuciyarshi,turus na yi na ƙame a wajen ina ƙare masa kallo sai yai na ankara da irin ramar da yayi.

Rinannun idanunshi da suka kaɗa suka yi jawur tamkar borkono ya sanya cikin nawa yana miƙewa da ƙyar, “Ina kika je?”ya faɗa cikin wata iriyar murya da ba tashi ba..”Ina kika je na ce!” ya kuma faɗa da ɗan karfi,shiru bance komai ba sai dab rawar da jikina ke yi.Tasowa yayi zuwa inda nake yana ta rumtse idanu gami da cije lebe, ya amshi takardar da ke hannuna ya bude yana karantawa, wani irin jiri ne ya kwashi jabeer saura kadan ya fadi kasa ya dafe kujera yana fadin “Ya Allah”.

Karfin jalin cewa nayi, “Wannan sakamakon jarabawar da nayi ne na jamb wani mai kudi ya biya min mai sona,mai son cigaba na, mai son inyi karatu,kuma na samu admission a university of por….

“Shuuuttt up!” jabeer ya fada da karfi yana dafe zuciyarshi.

Bazan yi shiru ba jabeer,”jabeer!” ya maimaita. Ehh bazanyi shiru ba sai na fadi abin da ke raina, na gaji, na gaji, na gaji da wannan bakar ta talaucin da na tashi a ciki sannan na tunkari karewa a ciki, bazan yadda ba, dole ne ka amince in tafi makarantar nan….Hayaniya takeyi sosai har bakinta na kumfa, ita kanta bata san abinda take fada ba, duk abin da ya zo kan harshenta furtawa kawai ta ke yi, banda rawa babu abinda jikin jabeer keyi,tunda yake bai taba ganin tashin hankali makamancin wannan ba arayuwarshi, anya wannan prettyn shi ce kuwa? any….

   ******

Cikin kuka Umaima ta fito daga gidansu kamar zata shide, har zata shiga gidansu maryama kuma ki me ta tuna ta fasa ta nufi hanyar gidanta tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare,a tsakar gidan ta tsaya tana sallama amma babu amsa saidai kamar tana jiyo hayaniya a cikin dakin hakan yasa batai wata wata ba ta afka ciki, aikuwa tayi mugun gani, dan maryama ce tsaye ta cakumi wuyar jallabiyar dake jikin jabeer sai masifa take, har idanunta na fitowa tamkar mai shigar aljanu.Jabeer kuwa na tsaye kikam sai kallonta yake fuskarshi yayi jajawur sai digar zufa ya ke yi labenshi yana ta rawa kar kar kar.

“Da gudu umaimah ta karaso gabansu har ta manta tashin hankalin da ta ke ciki ta fara jan maryama.

“Maryama are you mad?are out of your senses?how dare you kike aikata such things kamar baki je islamiyya ba?.

Ina maryama tayi nisa bata jin kira sai ma lumshe idanu tayi ta bude shawarar siyama na kai kawo a kwakwalwarta kamar ana buga mata karfe, cikin wani irin karsashi ta hankade umaimah gefe sannan tana kallon cikin idon jabeer tace,

“Jabeer idan har ka cika dan halak cikin uwa da uba ba shege ba yanzun nan ka sake ni!”

Wani irin ihu umaimah ta yi zata damke bakin maryama amma ta kara hankada ta, a hankali jabeer ya lumshe idanunshi, yana jin wani irin bugu da zuciyar shi yayi sau daya sannan ya dira ya ya balle daga jijiyarshi ya fada cikin cikin cikinsa da kyar ya motsa baki ya ce,

“Maryama na sake ki saki daya, tun bai gama cewa ba maryama ta juya da sauri zuciyarta na bugawa ta fice daga dakin,da sauri umaimah ta juya zata bita amma wani karan da Jabeer ya saki lokacinda ya kai kasa ne ya sata juyowa a tamanin tayi kanshi yana kallonta murya kasa kasa yace,

“kice da innarmu kar ta mata fada dan tana dauke da cikin gudan jinina da ko ita bata san da hakan ba, idan abinda ta haifa ya girma kice ya dinga yiman addu’a, Umaimah ina SONTA,ina SONTA, daga haka bai kara cewa komai ba,sai wasu irin gudajin jini da suka fara biyowa ta bakinshi,daga haka idanunshi suka kafe, wani kara umaimah ta saki tana mikewa hadi da fara yin baya baya cikin lokaci kadan itama duhu ya mamaye ganinta ta fadi kasa sumammiya kusa da jabeer, a daidai lokacinne kuna Maryama ta tare abin hawa ta shige……..

Alhamdulillah a nan na kawo karshen MARYAMA book one, ga mai bukatar book two zai biya 300# for normal group, 500#for VIP,bambancin a update ne ta acc.0056115042 Asma’u Isa Unity bank.

Ko katin MTN ta 08104875999, sai ku tura shaidan biyanku ta 08104875999 sai na jiku mutanena nasan real fans nawa bazaku bani kunya ba, ba sai na ambaci sunayenku anan ba sai na jiku one love dearies.

08104875999….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button