MARYAMA – EPISODE 03

        by 

UMMU FADEELA.

EPISODE 03.

…. Yana kwance kan katifar shi yayi rub da ciki daga shi sai boxer, ya cusa kanshi a cikin katifar,still tayi a wurin rike da ledan da ta kawo masa na yan sakwanni kafun ta turo baki ta juya da nufin barin dakin, juyi daya tayi taji ya damko hannunta, cikin muryar da ba tashi ba yace.

“Ina kuma zaki je? koba wurina kika zo ba”?.

Dago kai tayi da sauri suka hada idanu jin yadda muryar shi ya shake,cikin sauri kuma ta maida fuskarta kasa sakamakon arba da tayi da kakkarfan jikinsa fari kal da zara zaran gashi kwance lib lib, bazaka taba dauka cikin jikinsa zai kasance haka ba kasancewar yadda fuskar sa ke kode da aiki cikin rana,.

Kame kame ta fara cikin rawar harshe tace. “am emm dama,..dama na rage maka ne,kuma bansan har ka yi bacci ba,tana fadin haka ta kwace hannunta ta ajiye ledan ba tare da ta yadda sun hada ido ba ta fita a dakin,.

“Maryama”

Ya fada a kasan makoshinsa,amma bata juyo ba,shafa kanshi yayi ya koma bakin katifar ya zauna.

Washe gari da asuba hamma jabeer ya fito kamar yadda ya saba kafun ya tafi masjid sai yayi wanka,sanyi ko ruwan sama basa hanashi yin wannan wanka sanye yake da wando three quater jikinsa ba riga sai towel nashi da ya rataye a wuya hannunshi daya rike da kwandon wanka daya hannun kuma rike da bocket,cika bocket din yayi da ruwan rijiya mai dan dumi kana ya wuce bayinsu dake hanyar fita,saida ya gabatar da uzurinsa kafun yayi wanka a gaggauce jin ana kokarin tada sallar asuba, doguwar jallabiya fara kal ya zura wanda ya ajiyeshi musamman dan zuwa masallaci…

Anan masallacin ya zauna ya gabatar da atkhar nashi har wurin karfe shida kafun ya fito zuwa gida inda yabar baffa acan, zare jallabiyar yayi bayan ya shigo dakinshi ya kuma shiryawa cikin wani katon wando three quarter wanda girman wandon ya kusa buhun siminti yasa da wata riga armless daka gani kasan a gwanjo ya siyesu ya fito ya nufi wata tsohuwar karfen mota mai girman gaske da alamar kuma zatayi nauyi wurin dauka,nan ya hau daga karfen da sauri sauri niko nace bayajin nauyinta ne ko dai kawai tsabar jarumta ce.

Duk tsananin sanyin da ake kwadawa na hunturu take jabeer ya fara hada wani irin zufa mai bada mamaki gaba daya jikinsa ya jike da zufar tsawon lokaci yana motsa jikinshi kafun innarmu ta fito hannunta rike da carbi zata shiga madafa,ajiye karfen yayi yace “barka da safiya innarmu”.

Da murmushi tace, “barka ka dai jabeeru har an soma ibadar ne?”

Dariya yayi yace “ibada kuma innarmu”?

Tace “yo inba ibada ba me zance, ka maida daga wannan karfe kamar sallar farilla,ni tsorona ma kar wataran ya fadi maka a kirji mu shiga uku,kwata kwata na kasa fahimtar ma’anar wannan dage dagen da kake kullum ta Allah.”

“Wannan shine mazantakan ai dijah”.

Suka jiyo muryar baffa dake shigowa daga masallaci.Innarmu tace “to Allah ya kyauta amma dubi yadda daga karfen nan ya maida mishi jiki kamar irin na yan danben nan da ake haskowa a talabijin suna laftar junansu,dukkansu dariya sukayi kafun inna ta shige madafa jabeer kuwa ya gaida baffa wanda yasa kai cikin dakinsa shima.

“Ina kwana baffanmu”.

Ya jiyo Daddadan muryarta cikin kunnuwanshi.lumshe idanu jabeer yayi kafun ya bude, cikin kasala wanda yake halittarta ta sunkuya ta fara sharar dan tsakar gidan nasu ba tare da ta ga inda jabeer yake ba duk da cewa tasan yana wurin a irin wannan lokacin…”Morning pretty!” ya fada lokacin da ta iso kusa da shi a sharar tata.

“Ina kwana” ta mayar masa ba tare da ta yadda sun hada ido ba, murya kasa kasa yace “kawo tsintsiyar in tayaki,maqe kafada tayi hadi da turo baki gaba,…Gudar dari biyu ya zaro daga aljihun shi murya kasa kasa yace “ga wannan ki tura salima ta siyo miki kosai da madara kisha da tea nasan yau innarmu dumamen tuwon jiya zata yi.”

Da sauri ta dago kanta suka hada ido tayi saurin sauke nata idanun ,tana mamakin yadda jabeer ya haddace duk wani motsinta na rayuwa.Koda shike ba abun mamaki bane duba da labarin da innarmu ke bata a kullum cewa jabeer ne ya rene ta tun tana cikin tsumma shiyai yayenta lokacin da aka cire ta a nono,duk inda zashi tana makale a kafadar sa inka cire makaranta shima dan yasan baza’a barshi bane,innarmu tana yawan cewa jabeer ya ci kashi na da fitsari na, a kaina ya koyi yiwa yaro wanka da saka napkin,so ba abun mamaki bane kenan idan yasan fassarar duk wani motsi na.

Sauke ajiyar zuciya nayi kafun na miko hannu zan karba muka hada ido yamin wani kyakyawan murmushi mai shiga zuciya,amma ni iya bakin zuciyar ta tsaya baikai ga shiga ciki ba.

“Mayar mishi kudin nan kafun in fito in sare hannun nan naki da wuka”.

Duk muka juyo sakamakon jin muryar innarmu dake tsaye bakin madafa,fuskarta ba alamar wasa tace “idan bazata ci abunda duk gidan zamu ci ba sai ta zauna haka kokuma ta dau azumi, amma wannan iskancin nata ya isheni haka,kai kuma da shike solobiyo ne sabulalle sai kake biye mata, to duk kujini da kyau ba a gidan nan za’ayi haka ba, duk ina lure daku ai kai ka daure mata kugu take zuba mana isakanci son ranta,ita yar uban waye da bazata ci tuwo ba,?.

Shiru sukayi dukkansu basu motsa ba, da masifa mai dauke da fushi innarmu ta kuma tambayar ta “ke yar ubanwa nace, waye ubanki a garin nan da bazaki ci tuwo ba,?”.

To ku bari randa kuka tare a gidanku sai ku yi duk tsiyar da zakuyi idan ma kafar ka take so sai ka guntule ka dafa mata parpesu dashi kaji ko ROMEO.

Murmushi jabeer yayi yace “ayi hakuri innarmu, ko kallonshi batayi ba maryama kuwa na tsaye gefe ko uffan ba ta ce ba,wani kallon zaki shiga hannuna inna ta mata kana ta koma madafa tana ta sababi.

Bakin rijiya jabeer ya nufa yana shafa lallausan sumar shi,bokiti ya janyo hadi da jefa guga ya fara diban ruwa, jin karar juye ruwa cikin randa yasa innarmu fitowa harta na tuntube tasan jabeer ne ke jan ruwan bayan yasan aikin maryama ne, kullum aikin kenan ko ya taya ta shara ko diban ruwa kai har wanke wanke yana mata idan ya paki idon innarmu, baki a bude tace, “anya jabeeru kanka kalau yake kuwa,anya kana son ganin daidai nan gaba kuwa, ajiye botikin nan kafun in haure ka.bansan yaushe ka zama sauna ba, idan anyi auren naku haka zaka je ka shashance a rasa waye matar waye mijin,to wllh tun wuri kayiwa kanka fada, kayi wa kanka karatun ta nutsu.

Yana sosa kanshi yace “innarmu aikin ya mata yawa ita kadai gashi zata tafi islamiyya shisa nake taimaka wa.Zuwa yanzu innarmu ta tabbatar da maryama bazata taba samun miji irin jabeer ba,duk kuwa da ta lura da irin take taken ita yar tata.

Fatima jabeer ya kwalawa kira, jiki na rawa ta fito dan baya musu da sauki ya mika mata bokitin yace “ki cika randunan can gaba daya yanzun nan,and daga yau ke zaki ringa diban ruwa a gidan nan right? ya fada yana kallonta gyada kai tayi ya kira salima ma yace ita zata ringa yin wanke wanke…Komai innarmu bata ce ba ta shige kitchen ta barsu.Maryama kuwa shararta taci gaba dayi happingly.

Bayan ta gama share tsakar gidan wanka tayi ta shirya cikin uniform na islamiyyarsu tasa hijabi har kasa ta dau litattafanta ta fito,zuwa lokacin karfe takwas ya kusa tuni jabeer da baffa suka fita jabeer ya tafi wurin aikinsa baffa kuwa ya tafi kasuwa inda yake saida danyen kayan miya.

A tatstsaye maryama tasha kunu rabin kofi shima saida innarmu ta matsa mata,shigowar umaima itama shirye cikin uniform ne yasa maryama ajiye kofin hannunta ba tare da inna ta kula ba dan tana amsa gaisuwan umaima ne gami da tambayarta lafiyar yan gidansu, “duk suna lafiya cewar umaima”.

Maryama tace “innarmu sai mun dawo karmuyi latti,” tace “Allah ya baku sa’a ku kula da kanku,idan kun dawo ba lallai ki same ni gida ba,zan dafa farar shinkafa da wake in zuba a kula sai ki aika su salima idan sun dawo makaranta su amso ganyen salad wurin baffanku ki yanka mana,” cikin fara’a ta amsa da “to innarmu, sai in mana harda miyar ma ko?.

Ungo naki” cewar inna ja’ira shiyasa naga kina fara’a to da mai da yaji za’a ci, turo baki maryama tayi suka fice daga gidan.

Sannu a hankali suke tafiya, umaima na mata hirar saurayin ta yusuf…Juyo dara daran idanunta tayi wanda suka dan sauya kala sakamakon ciwon marar dake dan damunta kadan kadan amma take dannewa ta sauke akan ta kafun cikin sanyin muryarta mara hayaniya tace “kinsan Allah umaima kina bani mamaki,ni banga abun so a wurin yusuf ba wanda har kike rawan kai haka, mutum aljihu duk annakiya amma kin like masa kamar wani gwamna,ko kuma dan gwamna, nifa har yau banga talakan saurayin da zan yiwa so irin na hauka kamar yadda kike wa wannan yusuf din ba, dan juya ido tayi taci gaba da fadin, babban gida mai bene, manyan motoci na hawa, zuwa honeymoon a kasashen turawa, saudi duk shekara uwa uba inyi karatu mai zurfi, wanda ya mallaka min wannan ne kawai zanyi wa so na hauka, kai ko taka ni yake kullum bazan damu ba, amma bazan yadda iyayena talakawa sannan in kare a auren miji talaka ba ina impossible.”

Uhmmm kece kike ganin saida arziki ake soyayya maryama, amma for me arziki ba itace soyayya ba,mata dubu nawa ne suke cikin irin daular da kika lissafo koma fiye da wanda kika lissafa amma basu da farin ciki da walwala?kiyiwa kanki fada tun lokaci bai kure miki ba maryama,ki dena yadda kyale kyalen duniya da kyan da ake fada kina dashi su rude ki,wllh zakiyi nadama idan baki sauka akan wannan jirgin takardan da kika hau ba, ki kama hamma jay, dan wallahil azeem baki da mai sonki kamar sa kuma bazaki taba samun mai sonki kamar shiba, karki manta sadaukarwar da,yayi akanki can baya kim… …Da sauri maryama ta katse ta ta hanyar fadin kinga karki bata min mood dina, na rasa meyasa mutane suke son alakanta ni da hamma jay. Bayan ko da wasa bamu dace ba, nidin matar manya ce ba matar kafinta ba mai aiki a karkashin wani, wannan sadaukarwar da kike magana kuma dama can Allah ya nufa ta dalilinshi zan samu, so ku sarara min inshaki iskar duniya dan Allah.

Ko uffan umaima batace mata ba domin idan maryama tana irin maganganun nan duk abunda zaka fada mata bazata fahimta ba, mutane sun riga da sun saka mata virus a kwakwalwa tun tana yarinya cewa ita matar manya ce dan ta kasance kyakyawa gashi abun ya bita har zuwa girmanta, da haka suka iso islamiyya…Wurin misalin karfe goma ciwon marar da maryama take ji ya tsananta dan har wani rawa jikinta keyi ga idanunta da suka kada sukayi jawur sai zufa take sharcewa ganin hakan ne yasa mu’allim nasu yace taje gida tasha magani….Tun daga nesa ya hango ta tana tahowa, daga yanayin tafiyarta yasan ba lafiya, kureta yayi da ido har ta shiga gida kafun ya dauke idonshi cikin dakiya ya nufi ogansu don yasan innarmu bata nan, gashi yaga yanayin maryama akwai damuwa yace “oga zubairu minti daya zan dau abu a cikin gida”

Ba tare da tunanin komai ba ogan su yace ba damuwa…Da kyar maryama ta kai kanta daki ta ajiye jakar litattafanta kana ta zare hijabinta da rigar ta,daga ita sai farar vest da dogon wandon islamiyyarta, kwanciya tayi rub da ciki tasa filo daidai cikin nata yanda zai matse mata shi dan sosai yake mata azaba yayinda dogon sumarta ya bazu saman gadon, duk da ta cire kaya hakan bai hana zufa jike ta sharkaf ba…

Kamar yadda duk muka sani ba wanda bai son ci gaba a rayuwa, nima ta bangare na haka ne…I know ina da solid fans da za su patronizing dina a littafin maryama koda naira nawa nace, kuma ina alfahari da ku…Littafin MARYAMA na kudi ne zaku biya naira 300# kacal ta wnn acc. Din👉0056115042….Asma’u Isa…Unity bank. then show your evidence of payment via 08104875999.

Patronize me and read happily, thank you all😘.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*