Hausa Novels

MAKARANTAR KWANA HAUSA NOVEL

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

Related Articles

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Tuesday 3/1/2023 January Second

_Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah da yabani baiwar rubututa littafai daban daban Ina k'ara godema Allah 🙏, Allah ka k'aramin baiwa hak'uri dama juriya had'ida lafiya musamman ta idanuwana AMEEN YA ALLAH_

     *Ina godiya Kuma Ina k'ara godemuku MASOYANA Adik Inda kuke inajin dad'in nuna soyayyarku gareni dama littafaina Ina godiya Sosai 🙏 Allah ya k'ara Muna hak'uri da juna Ina sonku Adik indakuke Ni takuce Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 da bazarku nake rawa Akoda yaushe*

  ```HAPPY NEW YEAR✨💫🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳All,,,, Allah kahad'amu da Alkairan dake cikinta ya karemu daga munanan Abubuwa Allah ka zab'a Muna shuwagabanni nagari masu tsoron Allah, Allah ka kawoma k'asar mu Nigeria Zama lafiya da tattalin Arziki mai Amfani, Allah kaimuna maganin wad'an nan masifun ya Allah, Allah kaban lafiyar idona Allah, Allah ka Azurtani nasamu na sauya touching d'in wayata, Allah kaimuna Arziki Mai Amfani, Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌🤲 Ameen Rabby Happy NEW YEAR ONCE AGAIN🥳🥳🥳🥳 Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 ce dai😍```

                     _BISMILLAHI         RAHMANI RAHEEM_

FREE PAGE 1 TO 5

"Ni dai wallahi Alhaji da zaka sauk'i shawarata danace kada Akai basma *MAKARANTAR KWANA* Dan wallahi bawani Alfanu Aciki,"

   "Zuwaira!!! Yakike Abu Kamar basma ba y'arki bace? Da Ace ba y'arki bace danace to Hassada da rashin so had'ida kishi kike nuna mata, makarantar ce bakison tayi basma fa y'arki ce,"

Cikin fad’a fad’a ya k’arasa maganar,

 "A'a Alhaji wallahi ba hakabane nice zaune da yaran Nan kaga nafi kowa sanin halayyarsu nidai banyar da Akaimun yara makarantar kwana ba wallahi Koda maza Balantana macce, wato dik maganar da nafad'a ita k'itayi takafe sai makarantar kwana shikenan Allah yasa Alkairi",

Cikin k’osawa da zancen tayi maganar

“To kingani ko kefa kiyi fatan Alkairi kawai zaifi dik wad’annan maganganun na banza yara nawa sukayi MAKARANTAR KWANA Basu lalace ba no samun matsala sai ita, tin tana secondary yarin Yar nantake maitar Shiga boarding school Amma kika Hana kuma ta hak’ura to yanzu tagama secondry jeka kadawo ta buk’aci taje MAKARANTAR KWANA higher level kema saikiyi hak’uri taje Kawai,”

Yana ta fad’a yabar gidan duka.

 Shigowa Namir yayi yace" Wai mama me Akawa Abba Naga yafito yanata fad'a har waje,"?

 Hunmmm"Ai kasan gatanar gizo Bata wuce k'ok'i Namir Akan maganar basma ne wai ita sai makarantar kwana shine shikuwa yane momata yanzu haka sungama komai ko sani Banyi ba sai Yanzu Wai gobe basma zata *MAKARANTA KWANA*,"

MAKARANTAR KWANA!!!! Fa kikace Mama innalillahi basma d’in,”?

“Hunmmm saikayi kuma Namir,”

Cigaba da Aikinta tayi ranta nab’aci game da maganar.

Dogon tinani Namir Yashiga tabbas Idan basma taje MAKARANTAR KWANA To Akwai matsala Amma idan hakan Alkairi ne Allah ya tabbatar Abinda ya fad’a A ransa Kenan…………..

_TO WAI WACECE BASMA??????????_

Muhadamu NEXT PAGE Dan Dani littafin dai zai bada citta in Sha Allah kuma zai fad’akar… Fatana kukasance dani had’ida tayani sharing dama bada comment d’inku Akai…………….

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 10 to 20

     Basma ƴace ga Alhaji Musa su uku rak  iyayensu suka haifa, Zuwaira itace mahaifiyar su macce kamila Maitsoron Allah, Namir shine babba sai basma sai Autar su Husna, Mama tayima yaran tarbiyar saidai Abba Yana son Basma sosai wanda yakan Mata dik Abunda take so, 

Basma yarinya ce Fara maik’yau Wadda dika shekarunta bazasu haura 18 zuwa 19 ba takasance yarinya Mai kurin tsiya tanada d’agawa had’ida jidakai, idan tafito baruwanta nacewa Kai Babba ne tagaidaka muddin baka mataba to bazaku gaisaba tanada farin jinin samarin inda suke yawan bibiyarta suna sonta Amma saita gadama take kula Wanda taso, Koda tasoka idan taga Wanda yafika to zata barka, Ayanzu saurayinta d’aya Wanda takeso Sosai Sadeq,. Sadeq Yaro ne matashi maik’yau rayuwar su zata iya zama kamar d’aya saidai shi yakan kula Mata sosai Amma Abayan idanuwanta, Basma tanada k’awa d’aya Hafsat Wadda Suka shak’u Sosai Koda sunyi fad’a basa jimawa suke shiryawa Hafsat kamila ce idan kaga sunyi fad’a to Hafsat tanuna Mata tayi badaidai bane ita kuwa batason gaskiya, tare sukayi secondry Ayanzu dasuka kammala basma tadage Kan sai MAKARANTAR KWANA zatayi Higher d’inta inda Hafsat Batama da labarin zuwan Basma boarding…
Su Hafsat basada k’arfi sosai sud’in talakawa ne shiyasa take gida zaune Bata shiga wata makarantar ba Amma ita kam tadage Akan bazatayi boarding d’in ba……… ………….

MUNDAWO LABARIN

   "Kifito muje Basma kefa k'ad'ai nake jira"

cewar Abba Yana sake Mata Hong da motarsa

 "Abba ganinan yi hak'uri, mama natafi sai nazo muku hutu ko inkozomin visit,"

“Allah ya tsare Amma kikula Koda yaushe kiji tsoron Allah”

“To mama”

Dagudu ta isa motar suka wuce,.

Dama Already Abba yagama komai tana zuwa Aka Bata d’aki tareda sauran student,

      "Hey sannu ku Ni bak'uwa ce sunana Basma musa fatan zamu Zama k'awaye daku dan gaskiya kunmun,"

“Dago Kai D’ayan tayi ta k’are Mata kallo sannan tace zauna, Ni sunana Nusy Samir ita Kuma sope Sadeq munji dad’in had’uwa dake Domin daganinki kema wayayya ce,”

Murmushi tamusu sannan ta zauna tace”haka Ake yawan fad’a Inada wayewa,”

Dariya sukayi “lalle tafiyar mu zatayi dake”

            ...........

Ahaka rayuwa tasoma tafiya inda Suka shak’u dajuna dik Inda d’aya zata Saida d’aya, sannu Ahankali har Suka soma janta fita birthday Wai na K’awarsu dik da tsaro da masifar shugabar makarantar Amma sukan fice ba wanda yasani.

  Bestyna"zoki wanka mun bayana bana Kai wallahi Kuma kinsan banson datty wallhi Kuma hannuna baya kai,"

“To ganinan zuwa”

Batinanin komai sope tashiga toilet d’in tak’arb’e soso tana wanka mata bayan ta, “Kai K’awata gaskiya dole shafiq ya mak’ale Miki Kinga k’yakykyawar surarki kuwa? Kai gaskiya kin had’e ta ko Ina wallahi,” hannu tasa tana k’ara tattab’a jikin Basma itakuwa dariya kawai take,

Daganan Suka wuce wurin Dan Abun yasoma k’azanta nidai fitowa nayi nace Allah shirya……………

  _To Allah ya shiryamuna kawai Amma mafi yawan y'an BOARDING SCHOOL Saidai Allah ya gyara bance dika haka suke ba Amma da gyara gaskiya, Allah kashiryamu ka shirya zuri'armu Baki d'aya Ameen

BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 25 to 30

            Exam suka Fara inda Basma tamaida hankali gun Exam d'in dik da rawar kanta Amma takan maida hankali gurin karatu,

Fitowa sukayi holl d’in tana D’an ya mutsa fuska,

Shafiq ne ya k’araso indatake Yana k’arb’ar questions paper d’in hannunta Yana fad’in”kada dai Exam d’in Bata miki dad’i ba”?

B’ata fuska tasa keyi “Eh wallahi dik da irin dagewa ta saida Naga Abunda baimun ba,”

“Wannan shine Abunda nake gaya miki kawai kimanta wani Karatu ki more lokacinki idanma kikaso winning muddin kina tare Dani Zaki Sami results maik’yau,”

“Ni bangane Ina ka dosaba Shafiq nifa Karatu nazo ba shashanci ba bazan tab’a Aikata Abunda kakeso Dani ba domin ba haka nake ba,” wafce paper ta tayi tareda yin gaba cike da Jin haushin maganar shafiq,

Tinda tazo yake uzzira Mata tagama fahimta baida tarbiya shine yakeson ruguza Tata,.

WAYE SHAFIQ?

Shafiq yaro ne tantiri Wanda bashida tarbiya Sam baya samun kwab’a gun iyayensa sungama sangartashi Saboda sunada kud’i Kuma Shine kawai garesu.. mahaifinsa babban D’an siyasa ne,.

Wannan kenan

Dogon tsaki shafiq yaja haryana hurar da iskan bakinsa cikin Haushi, "Wai Ni zata kira D'an iska badan inason taba wallahi da sai tabar makarantar Nan Amma kozata bar makarantar Nan wallahi saina Ida manufata Akanta,

“Haba Bros Wai Akan Wannan banzar kake wahalar da kanka takesaka Ciwon Kai kawai Koda k’arfi ne ka Ida manufarka Awuce wurin ko kuma kafita sabgarta”

“Bazan iya Barinta ba Amma zanyi Amfani da shawarar ka ta k’arshe zatasan da shafiq take wasan,”

Tafa hannu sukayi

“muje muhuta”

Sope ce ta k’araso gurinsu tana sauke numfashin wahala Dan gudu tayi kafin tasa mesu
” Ya Akayi ne Naga Kamar kana fushi Kuma shirin tafiya polo zakuyi bada niba,”?

“Waccan banzar Wai basma itace take faman wahalar da Bros Wai meye shawara,”

“Hunmmmm bar Komai Ahannuna Kawai muje dama kaina yana juyamun inason Shan wani Abu Dan chaza k’wak’walwata”

 Zama Basma tayi dik wani iri take ji yau sope tasaba Mata da romance idan batayi ba Sam batajin kwanciyar hankali................

 BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 35 to 40

   Nusy ce tashigo d'akin bako sallama mita Kawai take Akan sope Bata jira taba tawuce, cire kayan jikinta tahauyi daga ita sai pant da breziya tazauna tana cigaba da jininta,. Jin shuru still basma batayi magana ba yasa tajuyo ta kalleta tana fad'in"Wai ke ruwane yaci mak'ad'i koya dama badake sukaje partyb ba,"?

Batayi magana ba haka Bata motsa ba,

Ganin hakan yasa nusy Kai hannu tana tab’a ta tace”Wai bakida lafiya ne,”?

Da k'yar tafurta" marata ciwo kizo ki tausamun,"

“Mene? Ni a’a wallahi Basma nifa dik iskancina bana less Wannan sai sope kibari tadawo tare kuka saba iskancinku Dan haka kijirata taimako d’aya zan iya miki kitashi muje Asibitin makaranta Adubaki ,”

Banza tamata Dan dik Bata buk’atar Komai daga cikin wad’an da talissafa ga Ciwon Yana damunta,

Ganin tamata shuru ba Ansa yasa tamik’e tahau yin harkar gaban ta,

Harkusan yamma sannan su sope Suka dawo, tananan kwance tana Murk’ususun ciwo inda Nusy ke charts da wayar ta ba Abunda ya dameta

“Ya Salam Sweety na meke damunki haka,”?

Tafad’a tana wani fad’awa Kan gadon,

Azafafe Basma tahanyo supe suka Soma kiss juna, Cikin jind’ad’in hakan yasa sope ta k’arasa cire Y’ar rigar jikin Basma itama tacire tata take suka Lula duniyar masha’a d’insu….

 _Wa'iyazu billah,, lees Yana d'aya daga cikin masifu masu ratsa duniyar y'an matanmu na yanzu wanda basai *Y'AN MAKARANTAR KWANA* ba ko inama zaka iya samun hakan Wanda ya riga ya Zama ruwan dare gama duniya 🌍 Amma gaskiya mafi yawan samun hakan A *MAKARANTAR KWANA* ne Ake samun hakan, masifa ce Babba wadda Allah Yana fushi da masu Aikata hakan, laifine Babba laifin Aikata zina wanda ha shakka wutar 🔥 Allah zataci Naman mazinata tsakanin Namiji da macce Amma gwanda shi da akata masha'a tsaknin macce da macce ko namiji da Namiji wllh muji tsoron Allah tinkan mushiga kabarinmu yakamata mugyara shi domin da munshiga ba hali Saidai mu girbe Abunda muka shuka tazarce Zakiya zakayi Kai Wannan Mai Aikata halin irin wannan.... WANNAN SHAWARA CE KAWAI 🙅 DAGA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 Allah kashiryamu shiriya ga Addinin Musulunci... Ameen.................................................._

 BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 45 to 50

  ```Nifa duka littafaina bantab'a cin zarafin kowa kowa Aciki ba kawai inayine Saboda gyara rayuwar wasu Al'umma kawai idan Abunda narubuta yazo daidai da halayyarki Dan Allah 🙏 bansanki ba bansan haka kike ba Kawai Ni nasan dakwai masuyin hakan ne to Dan na WA'AZANTAR cikin sauk'i shiyasa nake Zama na K'IRK'IRE labaruka Dan gyara rayuwar mu Amma Ni bantab'a kallon rayuwar wata ko wani nazauna nayi littafina Akansa ba Kuma bantab'a karanta littafan wasu Marubuta ko wasu y'an film nakwaso fasahar su ko idea d'insu nazo nayi Amfani da ita cikin littafaina naba a'a Bahaka Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 take ba Ina Zama na nazarce labari da Abubuwa masu ma'ana Dan nakawo nawa gyara cikin hikima ga Al'umma kowanne littafina da baiwar da Allah yamun nake rubututa shi da k'wak'walwata nake shiyasa nake AMFANI da *BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍* WANNAN Kuma haka yake basirar kowa yakamata tazama Arzikinsa Nagode ina sonku masoya Adik inda kuke Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar takuce🤸‍♂️🥰```

BAWAI IYA PAGE BA DIKA LITTAFAINA NAKUNE MASOYA🥰

             ........ Nishinsu kawai ketashi cikin d'akin

Dogon tsaki nusy taja had’ida fad’in”Allah ya shiryaku inkuna da rabo”

Ficewa tayi daga d’akin gaba d’aya..

****************

Hafsat! Hafsat!!! “Haba Dan Allah kitsaya ki saurare Ni Mana tind’azu fa naketa Miki magana Amma kinmun banza kuma fa kina jina,”

 "Kayi hak'uri bawan Allah nifa  na gayama idan nadawo daga makaranta bana son tsayawa dakowa Saboda badaidai bane," Bata jira Ansarsa ba tawuce Abunta

Murmushi kawai yasaki tare da komawa baya ya hau motarsa yawuce,

Jabir kenan d’aga Tahir Auwal Mai gidan kaji,.

Jabir shine kawai iyayensa Suka Haifa baida k’ane Kuma baida wa shine kawai Allah yabasu, Tahir Auwal Yana da gidan kaji dayawa k’wayak’wai kuwa mota mota suke SIYARWA suna Aikawa gari gari, dika Wannan dukiyar Jabir shike kula da ita Kuma tana hannunsa saka makon mutuwar iyayensa dika biyu hakan tafaru ne saka makon hatsarin mota dasuka samu, Allah bainufa zaimutu ba shiyasa tafiyar batayu dashi ba, tinyana Yaro hannun kakansa Auwal yatashi yasami tarbiya sosai dik da cewar Rik’on Kaka yakan lalace amma sam banda Jabir, Rabi itace kakarsa mahaifiyar babansa mutuniyar kirki ce Kuma Bata tab’a haihuwa ba hakan yasa take masifar son Jabir, Mata dayawa suna Nuna masa k’auna harda dangin mahaifiyarsa Amma Sam baicika biyesu ba saboda sanda baida Yana neman taimako k’insa sukayi sai Yanzu suke binsa saboda Anga yanada,

Dukiyarsa takansa yafito neman Aure inda ba’a Sansa ba kuma saiya nuna baida, wannan Kenan.

Yau sungama Exam d’insu duka Kuma Anbasu hutu su sope kuwa Saida Suka sake b’arje Ayarsu sannan suka rabu da basma kowa Yana cikin missing d’in d’an uwansa,

Bata jira zuwan Abba ba tafito tana neman mota,

Shafiq ne ya k’araso gurin da motarsa yace”Basma na zo musauke ki Mana tinda Muna gari d’aya Anguwa ce kawai daban,”

Kamar bazata shigaba Kuma saita shiga ganin ba shik’ad’ai bane,

 Motar tad'au shuru bamai magana sai can Shafiq yace'"Basma nasan kinajin haushina koma halayyata Amma wallahi zan iya dainawa saboda sonda nake miki idan kina tantama kiban dama kigani"

Batayi magana ba dai Amma tanajinsa kawai

Saida suka Isa har k’ofar gidansu ya sauketa yanemi number ta, tabashi tashige gida Abunta

Murmushi kawai yasaki Yana dukan sitarin motarsa shikawai yasan manufofin dake ransa.

  Gidan tashiga da Sallama

Mama dake wanke wanke ta Ansa tana d’agowa kafa Mata ido tayi nad’an lokaci

Kafin tace,” Basma yanaga kinyi haske Kuma ba Rama saima k’iba dakika k’ara,”……………………….

  BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

     *Page 55 To 60*

     "Mama haske kuma saikace Wadda take bleaching bayan ko man gyaran fata bana shafawa A school fa nake, k'iba Kuma tinda banada yunwa ai ba Abinda zaikawomin ita Abba fa yamun shopping Sosai Kaya masu Dad'i dayawa ga......,"

“Kinga ya Isa uwar surutu Abunda natanbaya daban Ansar da Zakiban daban ke Mai Wayo ba, nidai bazan gaji da cemiki kiji tsoron Allah A koda yaushe banda biyewa y’an iskan makaranta, Saboda inason ki da shiriya shiyasa nake miki fad’an so kanki,”

“To Nagode mama zankiyaye”

“Ah y’ar baba kindawo Ashe yanzu nake Shirin na d’auko ki Ashe kindawo waya maida Miki ne halan,”

 "Eh Abba wani d'an Ajinmu ne wallahi ya kawoni,"

“To jeki huta,”

………………………….

Kamar yadda ya saba yauma hakan ne, wasu ya mutsatstsin Kaya ya saka, inda ya Saba tsawa danjiran ta fito islamiyya Nan yatsaya,

Fitowa sukayi ita k’ad’ai tafara tafiya saiga Basma tafito Daga d’aya k’ofar ta islamiyyar su

“Hafsat D’an jirani mana Nadawo tinjiya Kuma naje gidanku yanzu Akace kina makaranta”

"Eh, Ashe kinshiga *MAKARANTAR KWANA*"?

“Eh nashiga wallahi, kiyi hak’uri bangaya miki Abun yazo A kaitsaye ne,”

“Uhunmmmmmm to Allah yataimaka kidai rik’a kula Kawai”

      Daidai lokacin suka iso inda yake binsu Abaya yafara suna tafe suna firarsu, 

Sallamu’Alaikum “Dan Allah kutsaya mana inata magana tind’azu”

Juyowa Basma Tayi tak’are masa kallo tsaf tindaga sama zuwa k’asa, saikuma tafashe da dariya harda tafawa,

“Yo Kai bawan Allah neman sadaka hauka ne da har zaka tare y’an Mata kana wani d’auka sallama haka,”

Kallonsa Hafsat tayi tamaida kallonta gun Basma dake masa wani kallo tace,"Basma kibari Bafa Almajiri bane gurina yazo dama Yana yawan bibiyata Ni yake so, kuma na fad'amai yaje gidanmu ba Wai Kan hanya ba,"

“Mene saurayinki wannan Abun? Hahhhhhhhh wayyo cikina yaushe Kika lalace haka Hafsat harkika fara kula marasa Aji k’ima talakawa marasa hankali k’ask’antattun mutane marasa A…….”

“Ya Isa!!!!! Nace ya isa haka Basma ya Isa!!!!!!!!!!”………………………………………..

   _BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

 *Page 66 To 70*

     .......... Cike da mamaki tamaida kallonta gareta tace"To Kenan harkun zama d'aya bansani Amma I kace shine Kawai ke sonki Baki tab'a kulasaba to idan hakane Jin haushi name bayan Baki sonshi,"?

"Amma ai baikamata kaci zarafin mutum gabansa ba, Kuma ya kike neman walak'anta D'an Adam bayan Allah da kanshi ya karrama d'an Adam why Basma meyasa kikeson wannan rayuwar bayan batada komai face dana sani A k'arshe ki.......,"

“Enough!! Enough!!! Hafsat kunnuwa basada lokacin sauraren banzayen kalamanki Atinaninki kece kawai Mai ilimi ko kamilalliya? To ya isa, nidai nafi k’arfin matsiyaci irin Wannan, sannan keda kikaga zaki iya togaki gashi saiya Aureki da tsiya ya cidake da tsiya nidai nafi k’arfin shi ke hatta ke fa bawai Ina binki bane saboda narasa k’awa no…. Kawai Dan Kar Ace nayi Karatu ke bakiyi ba shiyasa nabarki Amma ke kanki kinsan Arzikin bana yaci uban na bara, babbar yarinya kamata maiji da kyau Aji wayewa ga boko baidace Aganni da Mara Boko kamar ke ba so daga Yanzu munyi hannun riga bani Kuma bake kuje ku Ida tsiyarku BASMA tawuce Nan,” Mtswwww taja doing tsaki tare da barin

Hafsat kuwa mamaki ne ya hata katab’us Wai yau Basma ke cimata mutunci harda cemata tsiya kenan tana nufin tsiyar ta hanata cigaban karatun ta? Why BASMA Saboda kinje MAKARANTAR KWANA Shine kike zagina haka?

Wasu zafafan hawaye suka Soma zuba daga idanuwanta Zuciyar ta nata tafasa da

Abunda batasani ba dik kalamannan Nan data fad’a Azuciyar ta dika Afili tayisu, Sarai yaji Kuma ransa yasosu Sosai da Wannan cin mutunci data Mata Abainar jama’a

“Kiyi hak’uri Allah Yana tare dake Kuma Nima zankasan ce dake indai maganar karatu ne ni Nan namiki Alk’awarin daganan har birnin sin dik inda kike buk’atar zuwa zaka wallahi muddin kina Ina raye Koda bazaki Aure niba ni zanmiki saboda Allah gobe ki shirya Zaki k’arb’e Ainahin bak’o na musamman”
Yana Gama maganar yabar wurin cike da b’acin Rai

Mamaki yasa tabishi da kallo toshi waye dazaice zaimata tsaye tayi Karatu wane bak’o zatayi A gobe,?

Rashin Ansa yasa takwashi kafafu jiki ba k’wari tayi gida……………….

Kuyi manage da Wannan Page d’in wallahi Banda lafiyar ido, idona ciwo suke Wallahi kutayani Addu’a Allah yaban lafiya

  _BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

 What's app number 07064904617 or 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 75 to 80

     Wani k'yakykyawar matashin saurayi na hanga sanye da dakakkiyar shadda Fara sol tasha Aiki kansa sanye da hula takalminsa da da Agogonsa dika iri d'aya Bak'ak'e, durk'ushe kasa na hangosa Agaban Malam sani wato mahaifin Hafsat, 

“Baba Ni sunana Jabir Tahir Auwal
Kuma ni maraya ne iyayena sunjima da rasuwa Amma Ina hannun kakana watak’il ma kasanshi Auwal Mai gidan kaji wanda dik familyn mu sana’ar mu Kenan Saidai mahaifina Tahir yafi samun d’aukaka A sana’ar, Abunda yakawoni shine Ina neman Auren Hafsat wanda najima Ina bibiyarta Kuma saita nunamin nazo wurinka na neme izininka kawaiw shine nazo”

“To masha Allah kayi kyan Kai kaima Amma bana yanke hukunci nik’ad’ai ba Saboda tanada hakken sani hakama mahaifiyar ta, saina fad’a musu koma mene kaji Abakinta, Sosai nasanshi Ai babanka Allah yajik’anshi mutumin kirki ne”

“Ameen Ameen baba Nagode, sannan Abu nagaba najima Ina burin ganin tacigaba da Karatu zanyi k’okarin had’a komai nanda sati biyu tafara zuwa”

“Mungode D’an Nan Amma kajin kirar da maganar karatun kabari idan har ta Amince Akayi Auren naku saika sata Acan badamuwa bane ai,”

“To baba Nagode, ga wannan Asai goro dan Allah,”

“A’a Nagode kad’auki k’ud’in ka Kawai”

Mik’ewa yayi yana barin wurin had’ida cewa”a’a wallahi baba ai sadaka ce badan Ina neman Auren yasa nabaka ba sadaka ne kawai Ama iyayena Addu’a”

“To Nagode Allah shiyi Albarka,”

“Ameen baba sai Anjima”

Yashiga motarsa yawuce,

Shiga gida Baba yayi ya fad’amusu Komai Sosai Mama tayi Amanna Kuma itama Hafsat Tace dik Yarda sukayi daidai ne, tajima tana mamakin dama shine Alhaji Jabir da takejin Ana yawan fad’ar Alkairansa lalle wani Abu sai ikon Allah yau shine ke neman Aurenta lalle dik Yarda mutum yazo maka kada ka walak’anta shi.

Cikin kwanaki k’alilan Hafsat da Jabir Suka d’inke da soyayya sosai harma manya sunyi magana Nanda wata d’aya za’ayi bikin su…

Dik Abunda Ake Basma batada labari Domin Hutunsu ya k’are Takoma makaranta Ancigaba da ta’asar da Akasaba Amma Yanzu sun jone Sosai da shafiq Domin Yana sakar Mata kud’i ba k’ad’an ba,

Saidai haryanzu ba wanda yasan halin d’aya daga cikinsu ita batasan munanan halayyarsa ba shima baisan nataba..

Alhamdulillah kusan Ayau su Basma suka kammala karatunsu na b’angaren health Kuma Alhamdulillah Basma Tayi winning results d’inta Murna gunta Kam ba’a magana,

Kuma Asannan iyayen shafiq suka nema masa Auren Basma

HAUSAWA SUKACE RANA BATA K’ARYA SAIDAI UWAR Y’A TAJI KUNYA Hunmmmm Karin maganar ne haka fa namu na hausawa😊

Ayaune dubanni mutane suka shaida d’aurin Auren MASOYAN Hudu Hafasat sani da jabir Tahir Auwal Mai gidan kaji, sai basma Musa da Shafiq Abba Carpenter

Ansha shagali Sosai kowa yayi tasa rawar…………………. Ankai Amare kowacce gidanta Jabir Kam d’auke matarsa yayi Suka wuce Abuja Acan suka Sha Amarcinsu, Hafsat taga tarairaya da soyayya gurin Jabir musamman daya sameta A budurwarta kyautuka Kam tasha Dan har gida ya sauyawa iyayenta bayan wasu kwanaki yad’auke ta sukatafi honey moon Malesia Acan yasata school Abunta………

B’angaren Basma kuwa Daren farko A BAK’INCIKI tayishi Domin Abuge Aka maida shafiq gida yasha giya Kuma Wannan dik Aikin sope ne Domin ta lashe takobin rabasu dama tona Asirin Basma gareshi……………………

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

What’s app number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

 *Page 85 to 90*

           Hunmmm"Ai Wallahi Nusy bazan bar Basma tazauna lafiya da Shafiq ba" cewar sope tana tauna chinwgom k'at k'at irin na gogaggun y'an bariki,

“Hunmmm nidai kibi sannu kisani koyanzu kincutar da ita kinje fata harkar less sannan kina zina da mijinta kinayi da ita wannan wane irin muguwar rayuwa ne Dik ba Abinda yajamana bala’i A wannan rayuwar face MAKARANTAR KWANA ga,”………

“Enough Nusy banda time sauraranki waima keda kike Shan sheesha da yawan charts ga kallon blue film Wai ke Zaki Kira Wani d’an iska,”

“Kinga Sope nibanzo danki cimin zarafi ba, Kuma Allah ya shiryar Dani nadaina komai damacan shairin MAKARANTAR KWANA ne Kuma Yanzu na Gama na had’u da mutanen kirki na shiryu, Kuma ni Aure na zanyi keda bakida Alamar shiriya gaki ga duniya,”

Zaune take ta rafka uban tagumi tana faman tuna tunane, shigowa yayi tareda banko k’ofar da k’arfi idanuwansa A juye ga Alama dai buge yake yawo shaye shayensa kamar yarda ya Saba,

Mik’ewa tsaye tayi tana zubda hawaye had’ida cewa”dama Kai mashayi ne Shafiq Kuma mazina ci Ashe yaudara ta kayi na Aure na? Wallahi kacuceni ka zalunceni bazan tab’a yafe maka ba Kuma sai..,”

Wanketa da kyawawan Maruka har sau uku yayi Yana fad’in,” ke Dan ubanki Ni…Zaki… Kira… Mazina..ci? Ai..kuwa.. zakiga zinar yau.,”

Bata Ankara ba Kawai ya zare belt’s d’insa ya hauta da duka ba k’atk’au tawa ihu take bamai taimakonta saida yamata lilis sannan ba Imani ya Afka mata, Ranar taci wuya wuya iya wuya Kuka Tasha har hawayenta Suka k’afe saida wahala ta sumar da ita ba tausayi Kuma bayan yabiya buk’atar sa ya d’auko ruwa masu mugun sanyi A firij ya watsamata A firgece ta farka tana D’an ihu da y’ar muryarta Domin harta shak’e Saboda wahala, Yana tangad’i Yana masifa”dama ke ba cikakkiyar macce bace Ashe? Ke karuwa ce Kikasa na Aureki? Amanda yazo bakinsa ne Dik yawanke mata jiki da Aman giyar Mai masifar wari,

Kuka take Sosai Bata ko iya motsi tana BAK’INCIKI Dana nadamar rayuwarta gaba d’aya gashi ba gari d’aya suke da iyayenta ba Balantana takoma gida,

Saida ya Gama Amansa Tass kanta bako Imani sannan yabar wurin Yana cewa “idan nadawo Baki gyaramun palourna ba wallahi sainayi miki Abunda yafi Wannan karuwar banza kawa”………….

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

MAKARANTAR KWANA🌒☄️

FREE BOOK

(BOARDING SCHOOL🌌)

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Page 95 to 100

   _FINAL! FINAL!! FINAL!!! PAGE_

MONDAY 9/1/2023 JANUAR

  ```Alhamdulillah,   Ina godiya ga Allah daya sake bani dama da ikon Fara Wannan littafin lafiya dama kammala shi lafiya A yau Alhmdllh, Ina godiya ga wad'an da suka nunamin soyayya ga Wannan littafin wad'an da kemun magana private dama group Dana WhatsApp zuwa Facebook, inagodiya Alhmdllh Allah yabamu ikon d'aukar darusuka masu kyau dake ciki kuma Allah kabamu ikon nisantar marasa kyau Alhmdllh Ina godiya ga Allah Kuma Ina godiya gareku duka MASOYANA💞💞💞💞💞💞💞🥰🥰............```

              Da k'yar tasamu da rarrafe taje toilet A wahalce tagasa kanta tana kuka da nadamar Shiga *MAKARANTAR KWANA* gabaki d'aya Dan gani take Ayanzu inda Bata Shiga *MAKARANTAR KWANA* ba da Wannan bala'i bazai faru da itaba, Kuka tasake tafashe Dashi tana Dana sanin walak'anta Samarin da tayi Abaya Tabbas ba babban bala'i irin *MAKARANTAR KWANA* data Shiga data sani data d'auke shawarar Mama, 

Zaune yake A gafen gado kansa na Sara masa Wai yau shine zai Aure macce Wadda ba virgin ba me hakan ke nufi,

Sope ce tafito toilet tana tsane kanta da towels kallonsa tayi ganin kamar Yana tinani tazauna gegensa tana fad’in “Masoyi meke damunka haka kake wannan tunanin,”?

“Hunmm wani Basma zata cuta Ashe ba virgin bace karuwa ce Banfa sameta A macce ba,”

“Hunmmmm kaima dai kanada son Jan zance to bari na gayamaka Abunda baka saniba Basma dai ba karuwa bace Kawai ita y’ar less ce lesbian take macce da macce”

Mik’ewa tsaye yayi cikin tsananin mamaki da tsoron maganar yake fad’in “Matar tawa take lesbian, innalillahi wa’inna ilaihin raju’un, Wannan ba Komai bane face shairin MAKARANTAR KWANA

 "Hunm nadai gayama gaskiya, kaga katashi kamai dani gida,"

  wani yanayi yakeji narashin jind'ad'i baiyi magana ba  mik'ewa kawai yayi, tabi bayansa  motarsa ya fisge bayan tashiga A fusace yaja motar ransa sai suya yake masa wai matarsa y'ar lesbian ce wannan wane irin bala'in rayuwa ne? Ya farmasa haka?

“Subhanallah Shafiq katafi sannu kada ka salwantar da rayuwar mu mana”

Ko kallanta baiyi ba Balantana ya saurare metake fad’a ko gabansa baya gani shik’ad’ai yasan bak’in cikin da yakeji

Rawar motar tafara Kan titin tana neman k’wace Masa dik iya k’okarin sa naganin ya tsaida motar Amma yakasa

Sope sai ihu take,

Jikake gafffffff motar tadake wani k’aton icce, kansa ya dake sitarin motar,

Sope kuwa ganin motar na rawa yasa tabud'e Anata wayon Wai tafice kada hatsarin ya faru da ita,

Cikin Rashin sa’a k’atuwar mota tazo bazato ba tsammani kawai saitabi takanta take kanta ya watse Awurin jini yatsartu Sosai, mutanen gurin duk sun rud’e sunshiga tashin hankali sakamakon ganin wannan hatsarin, wasu cikin sauri Suka nufe motar suka ciro Shafiq yajima da Suma,

Asibiti Aka wuce dashi inda Sope kuwa sai tattara sauran Naman jikinta Akayi bako neman y’an uwanta suka Mata sallah,

Direct Emagency Akashiga dashi likitoci da dama Suka rufu kansa, bincike Akayi har Akasamu number Ahlinsa Aka buga Aka fad’a musu, take sukazo

Anan Ake sanar musu cewar yasami matsalar huhu saboda shan giya sannan kansa ya daku zaid’au dogon lokaci Yana jinya Kuma yasami karaya A k’afarsa ta haku da hannunsa nadama,

“Innalillahi Alhaji munshiga uku”

“Kinshiga uku dai dik waya ba yaron Nan hanyar lalacewa dika kece nayita fad’a Amma sam Baki saurara ta ko kibari shi ya d’auke fad’ana Amma Ina ke gaki wayayya Kuma Dole sai yaron yayi Karatu A MAKARANTAR KWANA Ai ga irin ta nan, yanzu matarsa yakamata muje mud’auko”

Baijira Ansartaba yafice Asibitin,

Yunwa da tsakanin Azabar duka da k’asanta kemata yasa take Kuka da k’yar tad’an mike Amma takasa tsayuwa da rarrafe tafito waje garin saukowa Kan steps d’in tahard’e Kawai tafad’o k’asa jikake kaf kaf kaf kanta sai bibbigewa take Koda yakawo k’asa harta jima da Suma,

“Nifa hankalina ya kasa kwanciya tinda Akakai Basma Ace bawani labari gaskiya yau katashi muje”

“Ni kaina hankalina ya kasa kwanciya Amma nasan Inada Akace sunkoma tashi muje mana”

 Kusan Atare suka shigo gidan bayan sungaisa 

Ganinta A yashe sukayi Bata numfashi ga jini natabin fuskarta,

Salati mama tasa had’ida kamata bawani b’ata Lokaci Aka wuce da ita Asibiti, bayan gama dubata likita yake fad’a musu Anmata f’yad’e ne,

“F’yad’e??”

Suka maimaita kalmar Atare,.

“Eh”

Mahaifin shafiq ne yayi k’arfin halin yimasa bayanin tanada Aure ai,

“Amma wane irin Mara Imani ne Kuka Aura Mata haka? To yayi Rashin Imani kanta kuma ga Alama yarinyar tana lesbian tasami matsala gaskiya bazata sake samun wani ciki ba Dan dukanda Akamata da Kuma lesbian d’inda take hakan ne Kuma….”

“Innalillahi kingani ba da y’ata ba y’ar iska bace amma gashi sanadin MAKARANTAR KWANA y’ata tafad’a harkar less innalillahi wa’inna ilaihin raju’un wallahi kacutar dani Alhaji” Kuka mama tasa Sosai.

“Kunga ba kune k’ad’ai kece cikin wannan bala’in ba na MAKARANTAR KWANA mu kanmu muna ciki saboda D’an mu shaye_shaye zinace zinace Abunda baifara ba dika Silar MAKARANTAR KWANA Saidai mu d’auke hak’uri Kawai”

    _BAYAN WASU WATANNI_

Shafiq yasami sauk’i Saidai Ayanzu ya shiryu ya koma shuru shuru Kuma ya neme yafiyar matarsa da iyayensa, fitowa sukayi waje Dan An sallamesu gaba d’aya,

Hafsat na hanga suna shigowa Asibitin itada mijinta ga ciki jikinta sai shagwab’a take masa,

Da kallo Basma tabisu cikin mamaki Basma tace”Hafsat da gaske kece Kuma Wannan shine mijin naki,”?

“Wai Basma kece kika dawo haka? Ina karatun ki Ina Kuma mijinki,” eh wannan shine mijina jibril Tahir Auwal Mai gidan kaji wanda kika sani dai Kuma Yanzu haka nazama midwafe Dan nayi Karatu A Istanbul”

Kuka tafashe dashi tana rok’on yafiya had’ida Bata labarin komai ” wallahi Ni Hafsat nayi Dana sanin Shiga MAKARANTAR KWANA A can na gurb’ata tarbiyata na had’u da k’awayen banza da mazinacin miji Mara tsoron Allah, dukanmu nida shi da sope muna Dana sanin Shiga MAKARANTAR KWANA

“Kiyi hak’uri Basma k’addara ce takan riske kowanne bawa Amma Inafatan hakan Yazama izina gareku dama wasu y’an baya, bama kune cikin bala’i ba Dan ku Kuna raye koba komai zaku neme Gafarar Ubangijinku ita zamu tama rok’on Allah yafiya”

Taimako tabasu Sosai inda tawuce Abunta sukuwa ko wanne cike da danasani yawuce suna kuka had’ida nadamar Shiga MAKARANTAR KWANA……………

ALHAMDULILLAH……. Anan nakawo k’arshen wannan littafin nawa maitaken MAKARANTAR KWANA Allah yaban ladan Aikin k’warai danayi ciki Mara kyau kuma Allah ya mun Afuwa…….

  _Muna da Rai muke tuba Idan mun mutu ba maganar tuba saidai musha wahala tareda k'arb'ar Aikin da muka shuka A kabari,. Allah kaha nemu da mugun Aiki Ameen_

TAKU HAR KULLUM MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 CE

_BASEEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button